Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

pen๐Ÿ–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'ar Da Wanda Ya yi Mafarki mara kyau zaiyi.*

ุฃูŽุนููˆุฐู ุจูุงู„ู„ู‡ู ู…ูู†ูŽ ุงู„ุดูŽู‘ูŠู’ุทูŽุงู†ู ุงู„ุฑูŽู‘ุฌููŠู…ู ุซูŽู„ุงูŽุซู ู…ูŽุฑูŽู‘ุงุชู.
a'uzu bi-l-lahi mina shaytani r-rajeem (3)
Wanda ya ga abu mummuna a mafarki, to sai ya yi wadannan abubuwan:-
- Ya yi tofi ta gefen hagunsa sau uku.
- Ya nemi tsarin Allah daga shaidan da kuma sharrin abin da ya gani, sau uku.
- Kada ya gaya wa kowa wannan mafarkin.
- Ya juya daga kwibin da ya kasance yana kwance a kansa.


Idan ya so, ya iya tashi ya yi sallah.


DEDICATED TO.....MY SISTERS๐Ÿ˜˜


Bissimillah Rahmanir Rahim



Page-83-84



---------------Kulle idona nayi ina tunanin kode mafarki nake, anya kuwa gaskiya ne?

A hankali na bude idona naga babu kowa a dakin cikin sauri na juya nasa hannu biyu na ture shi.

Yana zaune yana kallona na dauki wani katon hijab dake bisa abin sallah na saka na fito ina fitowa a parloun na iske su Mummy zaune suna magana ita da Ammie.

Mikewa sukayi Ammie ta kamo ni nide kaina a kasa.

Ammie tace;"Ina marar kunyar yake bai fitowa ne shi?"

Nayi shiru ina murmushi ina murza yatsun hannu na.

Mummy tace;"kina gani fa yaga Kulsoom a tsaye amman koya saki MANAL saima fizgarta yayi ta fada jikin shi, hakan ba daษ—i ai sai ya boye kwadan shi a gaban matar shi, wannan ai cin mutunci ne idan mu iyayen shi mun san halin shi da kuma abinda ke tsakanin shi da Manal ita fa Kulsoom tun jiya ta kulle dakin ta tana kuka wai ashe tun a London baya kulata zanyi maganin shi".


Ammie tace;"Allah ya shirya shi, bansan yama akayi yasan tana nan ba saboda shifa yasa na boye ta amman saida ya ganota bari naje naji da baki".

Mummy tace;"muje kiyi wanka ke ake jira duk mutane sun halarta, haddasu Hajiyar mu duk sun iso".

Nace;"to Mummy"


Koda muka isa naga Kakata mahaifiyar Mummy hadda kuka ta rungume ni babu abinda take sai hamdala sai sauran yan uwan Mummy ne kowa sai tabani yake yana cewa lallai itace kamar su maidani ciki saboda kauna, Mummy tace aje a haษ—a man ruwan wanka.


Ina fitowa na iske abinci naci Nifra ce ta shigo ita da wata wai ita zata man kwalliya duk abinda ake yara na suna raina nayi kewar su sosai amman babu halin tambaya ko Inna tun jiya rabona da ita haka Baba babu yadda zanyi na jure, motsi kaษ—an zanyi za'ace minake so.

Haka akayi man kwalliyar ni kaina dana kalli kaina a madubi saida nayi mamaki.

Wani doguwar riga Mummy ta aje man tace;"idan angama zaki je airport keda Malam Liman tarbo iyalen sa tun jiya Dad dinku yayi waya azo dasu".

Cikin murna nace;"nagode Mummy"


Na lumshe ido ina tuna kauyen mu da Shatu da Jabe Ma'u matar Kabiru dan maigari, kirarin ta na tuna nayi murmushi.

Ko yaran Shatu nawa? Allah Sarki kila Jabe yayi aure haka dai naita tunanin yan kauyen mu Mani koya chanza wannan motar da kullun saita lalace a hanya ohow.


Hajiyar su Mummy ta dafa ni tace;"Masha Allah lallai farin cikin gidan ta ya dawo ina ma Yarima murnar abokiyar rayuwar shi ta dawo, banson wane kalar farin ciki nake ciki ba farin cikin da muke ciki bai musul tuwa, abin al'ajabi shine zuri'a data shiga a tsakanin ku Allah zamuyi ma godiya munyi kewar ki kina a zukatan mu".

Murmushi nayi na rungume ta kana na goge mata hawayen fuskar ta.


Anuwar ne ya shigo da jallabiya a jikin shi yace;"Mummy please ina MANAL?"

Yayi maganar ne kamar zaiyi kuka Ammie ce ta shigo dakin, ta harare shi tace;"to marar kunya ba zaka kara ganin MANAL ba sai nan da One week kuma kabar part din nan ko kunyar sirikan ka bakaji"

Sai lokacin ya sosa keya ya gaida yan uwan Mummy dake a parloun.

yace;"Ammie miyasa baki tausayi nane idan bazan iya jure rashin taba kona one hour balle one week wallahi jiya banyi bacci ba shiyasa nazo muyi tare da ita Wallahi Ammie......"





Mummy tace;"Anuu idan ba haka akayi maka ba bazaka gyara ba ace sunan kana da mata amman ba abinda ya dameka da ita ba'a haka yanzu shawara zan baka ina so ka koma kamar yadda kuke ada kaida Kulsoom yadda kake nuna mata kauna da sauran su, hakan zaisa a baka MANAL cikin ruwan sanyi amman ace tsakanin ka da matar ka ko gaisuwa da kyar kake amsawa yarinya tazo da kibar ta amman abinda kake mata yasa duk ta rame ita kanta Hamrah ta rage samun kulawa gaskiya ka chanza"


Kallon Mummy yayi yace;"Amman Mummy kinsan daman auren dole kukayi man saboda babu MANAL yanzu kuma MANAL ta dawo Mummy kusan yadda zakuyi da ita"

Barin wurin Ammie tayi hanyar dakin da tasan MANAL na ciki ta nufa.

Cikin mamaki da tashin hankali daya bayyana a fuskar Mummy tace;"Anuwar kana cikin hankalin ka? kasan ko hauka kake baka fara sakin Kulsoom rashin adalcin namu zaiyi yawa sai a ce san kan mu yayi yawa duniya zata zagemu, to bari kaji wani abu nima ina goyon bayanta inde bazaka chanza ba to kaida Manal sai hange"


Daga haka tabar shi nan abin duniya ya ishe shi ya rasa taya zai bullo ma al'amarin daman kullun Daddy da Mummy ke goya mashi baya to yanzu Mummy ta cire hannun ta.


Part din Dad yayi kai tsaye yana zuwa ya hango wajen cike da mutane bai shiguwa gashi daga shi sai jallabiya ga idanun shi sun chanza.


Kai tsaye yaje part din shi a parloun su ya iske Kulsoom da kawarta.

Cikin sauri ta taso tazo tace;"Prince Hamrah bata da lafiya daman wayar ka nake nema"


Zaro ido yayi cikin hanzari yayi hanyar dakin yana zuwa ya isketa kwance cikin bargo

Saurin tallabo ta yayi yana taba jikin ta yana cewa;"Baby... Hamrah Baby.."

Ya kasa fadin magana duk ya rude Kulsoom ce ta shigo dakin tare da Hanan ganin yadda ya rude yasa suka kalli juna su kayi murmushi.


Magana yake Hamrah amman taฦ™i ta amsa sai Kulsoom tace;"tun jiya take kuka wai kabar son ta wasu yara kake so, nayi lallashi amman taki bari wai ba zata bari ba sai idan kadawo wajen ta"


Maida kallon shi yayi ga Hamrah dake kwance jawota yayi ya rumgume yace;"ina son ki Hamrah ta, amman su ai 'yan uwan kine kibar wannan maganar suna bukata ta fiye da ke saboda su basu san dadin uba ba".


Kulsoom tace;"Haba Prince kada kace haka mana yaran da yanzu haka koni banda ikon ganin su, saidai na kalle su a Nigerian News a TV amman gamu gida daya ba'a bani ikon ganin suba matakan tsaron da aka saka a part din su ko kai ba'a saka a part din kaba, sannan kace suna bukatar ka bayan....."


Daga mata hannu yayi yace;"banson irin wannan maganar a gaban yarinya taya kina neman saka mata tsanar 'yan uwanta kenan an fifitasu akan ta kada kiman ta farin cikin da akayi lokacin da muka samu Hamrah Daddy yana kokari akan ki da 'yar ki haka Mummy kisan kalar maganar da zakiyi".


Mikewa yayi yabar dakin da Kulsoom da Hanan suka kalli juna Hamrah ta aza kuka Kulsoom suka bishi koda suka iso parlor har ya shige dakin shi Kulsoom tace;"kin gani ko itama Hamrah dana dogara akan son da yake mata amman kalli saboda nayi mashi maganar yaran nan itama yabar ta, ya zanyi da rayuwata, ada gidan nan kullun cikin tattalin mu ake wane color food mukeso zamuci hadimai kullun cikin son kyautata mana suke. Amman lokaci guda sun chanza yanzu haka part din nan babu wata hadima ko guda shiko abincin bamu ciba duk daya ne tunda diyar so ta dawo, abinda keban mamaki ba Anuwar kaษ—ai ke haukan sonta ba ke hatta ma'aikata yadda kika san uwar suce ta dawo jiya bamuyi bacci ba yauma da alama saboda gidan yau yafi cika, ita walimar Nifra da mukazo anbar maganar ta ke intakaita maki ko beran gidan nan sonta yake balle mutanen gidan na shiga ukku na ni Kulsoom"


Hanan tace;"kiyi hakuri kinsan saboda ke nadawo Nigeria yau bai kamata kiyi saurin sarewa ba tun yanzu ya kamata kisa ka kissa a cikin al'amarin yanzu kinga babu yadda za'ayi naje maiduguri saboda Malam ya riga daya mutu bansan wajen wa zani ba, amman kafin musamu wani ya kamata muyi wani abu, ina da wata dubara idan kikayi amfani da ita zaki samu sauki kuma zaki samu shiga wajen iyayen shi fiye da baya"

Cikin sauri ta rike mata hannu tace;"ki taimakaman Hanan ke kaษ—ai kika rageman"


Tace;"ki shiga cikin jama'a ki nuna farin cikin ki komai za'ayi ayi dake ki boye kishin ki ki maida komai ba komai ba, zaki samu shiga fiye da tunani ki, hakan zaisa iyayen shi su fara jin tausayin ki tunda suna son ki kinga kenan laifi zai koma wajen Prince".


Ajiyar zuciya tayi tace;"nagode Hanan haka ne yanzu bari naje nafara bashi hakuri daga nan naje wajen Manal din amman kinsan yadda na gansu bisa gado dazun ji nayi kamar na saka ihu saboda azabar bakin ciki hadda fa jawota ta kara fadawa jikin shi abinda bai taษ“a man ba a gaban iyayen shiba".


Hanan tace;"ke dai ki boye kishi daman itace mace ta farko da kika fara tsana Anuwar ya ganta itace mace ta farko da kika taba kishi akan Prince ashe kishiyar kice Mai fura".


Tsoki Kulsoom tayi ta mike tace;"koma ki kula da Hamrah tunda yau Babu masu kula da ita kafin su Mom dinku su iso"


Dariya Hanan tayi tace;"yau nice house girl kenan?"


Kulsoom dakin Anuwar ta shiga yana nan zaune kallon pictures din su shida twins ranar da aka haifesu yake.

Kallo daya yayi mata ya dauke kai ta iso ta duฦ™a tana hawaye tasan kuka yana saurin karyar mashi da zuciya tace;"nasan nayi kuskure amman kayi hakuri bazan ฦ™ara ba ni kaina ina kokarin fahimtar da Hamrah amman taฦ™i ganewa amman nasan zata so 'yan uwanta kuma zata saba da rashin ka, kayi mana afuwa mun tuba amman muma zukatan mu suna cikin farin ciki akan samun MANAL kuma twins dinta na Kane munyi farin ciki sosai ina matuฦ™ar jin dadi dana tuna nice salar haduwar ku a Katsina ina alfahari da hakan".


Kallon ta yayi saiya tuna maganar Mummy sai kuma magan ganunta sukayi tasiri a zuciyar shi kama hannunta yayi ya mikar da ita yace ta goge hawayen ta taje su shirya hadda Hamrah idan tana iyawa suje wajen Ammie a tare.

A tunanin Kulsoom magan ganunta sunyi tasiri a zuciyar shi hakan yasa cikin murna ta fita.


Tashi yayi yaje ya shirya yana fitowa suka hadu a parlo harda Hamrah sunyi kyau sosai yana murmushi yaje ya kama hannun Hamrah suka fita.



Kai tsaye part din Ammie sukaje Ammie na ganin su tare ta washe baki ta kama hannun Hamrah ta azata bisa jikin ta.

Anuwar sai kalle kalle yake a parloun Ammie tasan abinda yake nufi ta share tana mashi magana saide yace umm yana kara kallon hanyar Bedroom din Ammie.


Wata kuyanga ta shigo ta zube tace;"Allah ya taimaki fulani mutan Katsina sun iso anje a dauko su daga filin jirgi Gimbiya MANAL Kuma....."


Anuwar ya maida hankalin shi yaji me za'ace akan MANAL din Ammie ta daga hannu kuyangar bata ida magana ba.


Ammie tace;"gani nan zuwa"

Ta mike tace;"Ni zan fita saina dawo Hamrah ga abinci chan nasa aka dafa maki dan nasan kinaso kici kafin na dawo na dauke ki kije wajen 'yan uwan ki".




Kulsoom ce ta kunna TV tana kallon Nigerian News.


MANAL ce aka nuno tare dasu Nifra a airport din Bauchi sai daukarta ake tamkar ba itaba kayan jikinta kansu abin kallone ballan tana yadda aka tsara kwalliyar, wurin ya cika sosai mikewa Anuwar yayi rai bace ya fita.


Part din Abie ya nufa dan yasan Dad yana chan.

Su duka ya iske iyayen nashi ya kalli Dad yace;"Dad miyasa MANAL zata fita ba tare da izinina ba nifa mijin tane Dad ka taimaka ta dawo maza sai kallon ta suke a Nigerian News naganta Dad wallahi banson kowa ne namiji ya ganta Dad bata da Hijab fa"


Su duka sakin baki sukayi suna sauraren shi Abie ne yace;"ni nace taje ita da Malam su taro iyalan Malam da suka iso yanzu Daddyn ka yasa aka dauko su dan yaga bukatar haka a tare da ita kuma duk kallon da mutane sukayi mata baidame kaba na tsawon shekaru da fitar da tayi duk basu dame kaba sai wannan? To ita matar taka Kulsoom da ko ina na Nigeria photunan ku suke yawo ita ya akayi baka yi magaba ba itama ai matar kace"


Shiru yayi duk yabi ya rude babu mai tausayin shi yau ko abinci bai ciba.




Suna tsaye a airport tana kusa da Baba tareda Yaya Sani daman yaran duk inda suke Inna na wajen su rabonta dasu tun jiya.


Nifra ce ta rike hannu saiga su Inna sun fito daga cikin jirgi hadda Ma'u da yaran ta.



Kukan tafarayi sun kusa iso ta ruga ta rumgume Ma'u kana ta rumgume Inna su duka kuka suke.


Nifra taje ta kamo hannun ta suka shiga mota kuka take sosai duk abinda Inna tayi mata hakan baisa ta tsane ta haka Ma'u jinsu take tamkar wane sashe na rayuwar ta.


Hannunta cikin nasu sukayi part din Abie.

Nace;"naji dadi Inna daki warke"

Tace;"ai yanzu Alhamdulillah ido, kafa ce tayi saura yanzu itace dole duk inda zani saida sanda kiya feman duk alhakin kine ke bina, nayi nadamar biye ma zuciya da son abin duniya Allah ya nunaman abu na su kudin dana amsa basuyi man Rana ba nayi dama kiyafe man Nana"


Zata cigaba da kuka MANAL ta rumgume tana goge mata hawaye kamata tayi tace suje ciki


Inna kamar tana tsoron taka kasan dakin saboda yadda taga wajen Ma'u da Yaranta sai raba ido suke daka gansu kasan bakin shiga ne.

Abie yace;"suna bukatar hutu kuma su samu natsuwa akaisu sashen da aka sabke Malam zuwa dare Sai a zauna idan hankali ya kwanta"

Mike sukayi jiki na kyarma dan da Nana kade suke sakin jiki duk sun rude kamar tsoron mutanen suke.


Kulsoom ce da Hanan sukayi sallama a parloun fuskar Kulsoom dauke da murmushi tayo inda MANAL take.


Zata rumgume ta Inna ta shiga tsakanin su tana kara kallon Kulsoom tana kallon Hanan da itama hankalin ta akan Inna ta zaro ido.


Kulsoom ta kalleta cikin mamaki haka dakin kowa hankali shi ya dawo kansu kowa da kalar tunanin sa miyasa Inna ta dakatar da Kulsoom daga rungumar MANAL.


Kulsoom da bata gane Inna ba a tunanin itace wadda MANAL ta zauna a gidan ta nan gumi.


Inna sai kara bude ido tana kallon su kowa dakin abin ya shi mamaki.


Na yanje MANAL kusa da Kulsoom tace;"wallahi sune...... wallahi sune.."


Abie yace;"Lapia minene ya faru?"


Inna tace;"sune wallahi..... itace......."








MARYAM ANKUDII
*JARABTAR MU*

Page-85-86


*Written by-Qurrahโœ๐Ÿป*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~โœ๐Ÿฝโœ๐ŸฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ~*

*~We are bearer's of so golden pen๐Ÿ–Š~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden penโœ,behold our words.~*

*~A product of our pen๐Ÿ–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*

Addu'ar Tafiyar Da Kuncin Zuciya

ู„ุงูŽ ุฅู„ูŽู‡ูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู ุงู„ู’ุนูŽุธููŠู…ู ุงู„ู’ุญูŽู„ููŠู…ู’ุŒ ู„ุงูŽ ุฅูู„ูŽู‡ูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู ุฑูŽุจูู‘ ุงู„ุนูŽุฑู’ุดู ุงู„ุนูŽุธููŠู…ูุŒ ู„ุงูŽ ุฅูู„ูŽู‡ูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ู’ ุฑูŽุจูู‘ ุงู„ุณูŽู‘ู…ูŽูˆูŽู‘ุงุชู ูˆุฑู‘ุจูู‘ ุงู„ุฃูŽุฑู’ุถู ูˆุฑูŽุจูู‘ ุงู„ุนูŽุฑู’ุดู ุงู„ู’ูƒูŽุฑููŠู…ู.
La ilaha illal-lahul-'azeemul-haleem, la ilaha illal-lahu rabbul-'arshil-'azeem, la ilaha illal-lahu rabbus-samawati warabbul-ardi warabbul-'arshil-kareem.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, mai girma (wanda babu abin da yake girmama a gare shi), mai hakuri (mai jinkirin azaba tare da ickakken ikon aiwatar da ita). Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin Al'arshi, mai girma. Babu abin bautgawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin sammai Ubangijin kasa, Ubangijin Al'arshi, mai yawan baiwa.


ุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุฑูŽุญู’ู…ูŽุชูŽูƒูŽ ุฃูŽุฑู’ุฌููˆููŽู„ุง ุชูŽูƒูู„ู’ู†ููŠ ุฅูู„ูŽู‰ ู†ูŽูู’ุณููŠ ุทูŽุฑู’ููŽุฉูŽ ุนูŽูŠู’ู†ุŒ ูˆูŽุฃูŽุตู’ู„ูุญู’ ู„ููŠ ุดูŽุฃู’ู†ููŠ ูƒูู„ูŽู‘ู‡ู ู„ุงูŽ ุฅูู„ูŽู‡ูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ุฃู†ู’ุชูŽ.
Allahumma rahmataka arjoo fala takilnee ila nafsee tarfata 'ayn, wa-aslih lee sha'nee kullah, la ilaha illa ant.

Ya Allah! Rahamarka nake kauna, don haka kar ka kyale ni da kaina ko da kiftawar ido ne, kuma ka kyautata mini sha'ainina dukkansa; babu abin bautawa da gaskiya sai kai.


ู„ุงูŽ ุฅูู„ูŽู‡ูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ุฃู†ู’ุชูŽ ุณูุจู’ุญูŽุงู†ูŽูƒูŽ ุฅูู†ูู‘ูŠ ูƒูู†ู’ุชู ู…ูู†ูŽ ุงู„ุธูŽู‘ุงู„ูู…ููŠู†ูŽ.
La ilaha illa anta subhanaka innee kuntu minaz-zalimeen.
Babu abin bautawa da gaskiya sai kai. Tsarki ya tabbata gare ka, lallai ni na kasance daga cikin azzalumai.

ุงูŽู„ู„ู‡ู ุงู„ู„ู‡ู ุฑูŽุจูู‘ ู„ุงูŽ ุฃูุดู’ุฑููƒู ุจูู‡ู ุดูŽูŠู’ุฆุงู‹.
Allahu Allahu rabbi la oshriku bihi shaya.
Allah! Allah ne ubangijina, ba na yin tarayya da shi da wani abu a cikin bauta.



DEDICATED TO.....MY SISTERS๐Ÿ˜˜

Page-85-86

Bissimillah Rahmanir Rahim



---------------Baba yazo ya kama hannun Inna daga MANAL yace;"kuyi hakuri Rakiya nada matsalar ido kila ciwon ne ya tashi yasa take ganin mutane ba dai-dai ba, ko kuma shiga jirgin nan ne ya rudata tunda har yanzu a tsorace take kuyi mana afuwa"

Tunda ya fara maganar Inna ke kallon shi ya ja hannunta yace;"mutafi mana"

Inna ta fizge hannunta tace;"wallahi bazan jeba yau saina tona asirin komai a yanzu sannan zan fadi duk kalar rayuwar da Nana tayi idan yaso su kasheni na huta, zuciyata yau tas take tunda ga Nana har ta yafeman saboda haka bani da wani fargaba komi zai faru saide ya faru".

Ta kalli sauran yan dakin tace;"kuyi man afuwa na zalinci yarinyar ku amman nayi nadama nayi kuka har nagaji nayi Dana sa ni a kan abinda na aikata, rayuwar Nana ta zama darasi ga kowa".

Nan Inna ta fara basu labarin zaman da Nana tayi a gidan ta da ukubar da tayi mata tun tana yarinya take tallah haka take yawo babu ko takalmi a kafarta har ta girma har zuwan su Kulsoom gidan babu abinda Inna ta rage.

D'akin duk kuka suke idan ka cire Mai martaba da Daddyy da Anuwar, amman har Baba kuka take haka itama Innar dake bada labari.

Tana idawa taje gaban Manal tace;"kiyi man duk hukuncin daya dace dani ban taษ“a jin labarin mace azzaluma iri na ba, rashin hakuri da tsananin kishi da zargi sun kaini sun baro ga son abin duniya daya rufe man ido, hakan yasa na kaucema hanyar kirki nazamo azzaluma na gina ramin mugunta na fada a ciki na lalata tarbiyar diyata da kaina sannan nazo nayi sanadin saka rayuwarta cikin wahala ko wannan kaษ—ai ya isheni bakin ciki a duniya Nana tun a duniya Allah yayi maki sakayya lallai yau ni naga ribar hakuri kiyafe man".


Manal ta duka tana kuka ta rike hannun Inna tace;" Inna miyasa zaki fadi abinda ya wuce? Inna wallahi bantaba rikeki a raina ba kitashi Inna"


Mummy dake Kuka tazo ta kama Manal tace;"tunda nike a tarihin rayuwata ban taba tunanin akwai mutane masu kalar rayuwar da kikayi ba koda ban sanki ba labarin ki kawai naji na tabbata saina zubda hawaye ballai ace yar ciki na ita tayi wannan rayuwar Allah mai iko"

Kuka Mummy keyi sosai ta kara rungume diyarta a jiki Ammie suka taso sukazo Suma hawaye suke"

Mummy tace;"a lokacin da Anuwar yaban labarinki haka kawai naji inason taimaka maki haka Nifra har sabani muka samu da Dad dinki Amman na daure a lokacin bikin Anuwar da Kulsoom ya hanani zuwa da kaina nayi aike ashe jini nace"

Anuwar yace;"Mummy kun kara yadda dani ko daman nace maku banji a jikina ta mutu, Ammie idan baki mantaba har tambayar ki na taba yi nace Uwa zata iya yima diyar ta kazafin mutuwa? Kikace a'a daman rashin yadda danayi da mutuwar ta yasa naje da kaina"

Ya kalli inda Kulsoom take tsaye tana hawaye yace;"miyasa kika hanani ganawa da abinda nakeso? Miyasa kika nisan Uba da yaran sa? Kinsan kinada kaso da yawa a cikin wannan Al'amarin miyasa zaki yaudare mu?"

Kuka take sosai tace;"Anuwar wallahi......"

Naga mata hannu yayi hakan yasa tayi shiru.

Daddy yace;"Nima yau son kaina yasa nayi nadama naji kunyar hada ido da diyata na hana ayi taimako ashe jini na nayima rashin adalci lallai son kai ba karamin cuta bane garemu Allah yasa mudace, yasa mana tausayin juna da jin kan juna"

Abie yace;"Alhamdulillah...babu abinda zamuce saide muce mun godema Allah Anuwar kayi hakuri Kulsoom tayi ba dai-dai ba, ba agareka ba har a wajen mu to amman haka Allah ya tsara dan haka ina mai baka hakuri, sannan wannan labari na wannan baiwar Allah ba komi bane a cikin rayuwar Nana face darasi muna rokon Allah ya bamu hakuri da juriyya a cikin wannan rayuwar tamu, dan haka zamu iya zuwa kowa yayi Sallah iyalen Malam Kuma a kaisu a part din da aka sabki Malam"

Farhan ne da Farhana suka shigo tare da Jawad da Inna na bayan su.


A guje sukazo suka rungume MANAL suka ce;"Ummie munyi kewar ki sosai muna tareda Baban mu da Inna da kuma sabon Kawun mu kin ganshi ko yana kama da Baban mu amman Baban mu yafishi kyau saboda Baban mu nadaban ne"


Kowa saida yarinyar ta saka shi murmushi yadda take maganar Inna ta kalleta tace;"Nana wannan ai kece ta biyo ta kalli Farhan ta kalli Yarima tace ikon Allah wannan Kuma ga wanda ya biyo, yaran waye masu kyau haka kamar naku keda wannan"

Ta nuna Yarima MANAL ta dukar da kanta a kasa Mummy tace;"yaran sune daman mijin tane, cikin da kuka korota dashi sune ta haife a gidan Inna ga yaran nan da suna jarirai"

Ta nuna mata picture din dake a bango Yarima da twins.

Inna tace;"ba'a gidana ta haihuba saide ranar data haihu ranar tazo gidana, tayi zamane anan gidan wata Hajiya mai saida abinci anan bayan gidan"

Nan Inna tabasu labarin da Nana tabata tun daga randa suka hadu da Hajiya har zuwa yau.


Yarima ya kalli Kulsoom yace;"duk kece kika yi sanadin haka yanzu baccin da Allah ya azata akan hannu na gari da irin gidan Hajiya ne daba zan yafe makiba wannan baso bane kin cutar dani kinsan na tsani karya inhar kina sona miyasa bazakiyi zaman gaskia dani ba"


Kulsoom ta goge hawayen dake bin fuskarta tace;"wallahi Yarima ka yadda dani sonka ne ya makantar Dani na aikata haka a tunanina mayya ce ko aljana saboda yadda kakeson ta ni kuma ina ganin idan har kana cikin hankalin ka bazaka kulata ba saboda yadda naga ni baka kulani ba balle yar fura mai saida fura shiyasa nayi haka, amman kayi adalci kada kamanta inason ka itafa wadda kakeso shin tana sonka ne ni sone yaja nayi haka"


Inna tayi murmushi tace;"Yarinya banso nayi maku kutse a cikin lamuran ku akwai wani sirri da ban fadaba saboda sirrin Nana ne amman dole a fada anan tunda abin yazo a haka kiyi hakuri Nana baki fadaman ba amman zan maki kutse a lamarin ki"

Ta kalli Anuwar tace;"Kaine namiji na farko da Nana ta kasa boyen kishin ta akan ka, sannan kaine namiji na farko da Nana ta fara so tayi kukan so harta gaji jinin da kabata takan zauna tana kallon hannun ta tamkar zataga jinin ka a jikin ta tsabar so zuciyar ku a hade take "


Kowa dakin shiru yayi yana al'ajabin wannan Al'amarin basu taba haduwa ba amman zuciyar su ta hadu.


Inna tayi murmushi ta kara cewa;"Son da take makane yasa tayi sadaukar da abinda ya kasan ce kamar gadon yaran ta shine abu mafi muhimmanci a rayuwar ta tazo dumin tabaka shi nayi mamaki sosai kalar son da Nana ke maka ban ida shiga ruduba saida naga ta dauki wannan zoben Wanda Uban yaran ta yabata zata baka ashe kaine Uban su kuma mijin ta itace MANAL din da ake magana kaji amman ke yarinya kibar maganar Nana bata son shi"



Nakasa gane farin ciki nake murna nayi mataukar mamaki da Inna ta fahimci halin da nake ciki kuma bata taba nunaman tasani ba, na dukar dakai saboda yadda naji an tona asirin zuciyata.


Abie yace;"Alhamdulillah wannan abu nasu akwai ban al'ajabi a ciki yanzu abinda yafi kowa ya tafi yayi Sallah Yarima kuma naga ka dauki abinda Kulsoom tayi da zafi eh gaskia tayi ba dai-dai ba Amman muna neman mata afuwa a wajen ka duk da laifin ta Babba ne amman inason kayi hakuri bawa baya kaucema kaddarar sa Allah ya rubuta hakan saiya faru dan haka tunda har Nana da yaran ka suka dawo babu abinda zamuyi sai godiyar Allah abar maganar haka"


Mummy ta kama jikokin ta tare da Anuwar suka fita.


A tare muka nufi part din da aka sabke Baba.

Koda muka isa an aje masu nau'o'in abinci.

Inna har yanzu tana hawaye saide tasa gefen zane ta goge hawayen ta.


Na nuna masu yadda zasu amfani da bandaki mukayi Sallah a tare mukaci abinci.

Nan muka fara fira nace;"Ma'u Shatu ta haihu?"


Ma'u tace;"Umm ai Shatu ta wahala bayan tahowar ki itama mijin ta dake zuwa birni neman

Please Login or Register in order to submit comment