Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa nasan ka iso, mikake so nayi maka order kaci" tana maganar tana kallon shi.


A hankali yace;"No need, i need to see My Papa"wani lokaci yana kiran Daddy da Papa saboda haka MANAL ke cewa to duk ya ambaci haka akwai matsala yana son yayi maganar MANAL.


Murmushi tayi tace;"Let me call him"

Yace;"okay, Thank you".


Da wayar ta ta kirashi bai dauka ba tana ta Kira amman saide a latse wayar.

Ganin haka tace ya kira shi da wayar shi.

Yana kira ko ya dauka yace;"Anuu mikake so katashi kenan?"

Yace;"yes Dad i need to see you"

Cikin sauri yace;"Am coming now"daga haka Anuu ya kashe waya yayi zaman jiran Dad.


Ba sufi ten minute ba saiga Dad ya shigo.


Cikin sauri Anuwar ya mike yaje wurin da Dad din.


Kama hannun shi yayi yace;"fadaman mike damun ka ina meeting ka Kira amman nace su bari mu ida gobe lafiyar ka kalau de ko?"

Bata fuska yayi yace;"Eh Dad kawai inason na fita kuma nasan baza'a barni naje nikade shine nikeso Dan Allah kabar ni nafita nikade"


Kallon shi yake cikin mamaki.

Yace;"Anuu dina wai miyasa duk ka chanza yanzu kafison zama karshen gari inda ba mutane amman nanfa ba Katsina bane kuma ba Spain bane yanzu idan ka fita kai kade yan jarida kade sun isheka dabi bayadda za'a yi kafita kai kade"


Bata fuska yayi baice komi ba Daddy yace;"idan kana bukatar zama bayan gari Mai martaba yace a Bauchi zaku zauna da Kursim sai kunyi wasu watanni kana yabar ka kabar kasar yau zansa aduba katon fili mai kyau wajen karshen gari a Bauchi a gina maka lambu wajen kada kadamu kaga zuwa anjima zaku bar Abuja kilani sai zuwa next idan abubuwa sunyi sauki in iso kayi hakuri Anuu dina dole na kare rayuwar ka, kodan tsoron kada a maimaitaman 'yar gidan jiya"


Ganin yadda yanayin Dad ya sauya yasa yace;"bakomi Dad zanje nasa a shiryaman abinda nikeso"


Yace;"No Anuu kaima ai nasa ammaka laifen ka na kishin laifi"

Yana maganar yana murmushi shima Anuwar murmushi daga haka yayi gaba.

Nifra dake kallon su tace;"why don't picking my call Dad?"dariya yayi yace;

"Nasan kiran naki bai wuci kice zaki wajen Friend dinkiba shiyasa na jira in fito ko kema kina bukatar laifen ne?"

Yayi maganar yana murmushi dariya tayi tace;"Eh Dad kaga daman inason naje Dubai nayi Shopping din kayan da zan saka bikin Yaya Anu nida su Walida"


Kama baki Dad yayi yana cewa;"sarkin 'yan yawo ba kinje Shopping ba a Spain keda Kursim ba"

Cikin shagwaba take maagana tana cewa;"please Dad"tana buga kafafu.

Dad yace;"ki tambayi Brother dinki idan yabar ku sai kuje keda Walida amman two days zakuyi saboda bikin".

Tsalle tayi tace;"thank you Dad"


A guje ta isa dakin Anuwar yana sama bedroom dinshi ta shiga cikin murna da tsalle.


A dakin Anuwar yana tsaye a bakin window saide yaji kaf an bude dakin.


Yasan Nifra ce shiyasa bai waigo ba.


Cikin sauri ta rungume shi tace;"please Yaya Anuu kabar ni nida Walida muje Dubai please don't say No"rike hannunta yayi yace;"Sakar ni sarakan yawo kuma ku kade zakuje?"

Tace;"a'a da friend din Momy zamuje"


Ya cireta daga jikin shi yace;"sai kundawo banda rawar kai"


Ta fita tana ihu tana tsalle.


Dawowa yayi bakin gado ya zauna.

Nifra yarinya ce amman miyasa ita bata burgeshi??

Kodan ya dauke ta kamar Walida?

To miyasa ita kullun tana cikin mafarkin shi??

Kenan tausayin ta yake?


Idan yana tunanin ta yana mantawa da komi.



Zama yayi ya dafe kai yana tunanin taya zai iya rayuwa idan baigan taba??


*************

Wanka nayi nasaka kayana na dauki Hijab nida naje nace ma Inna zan fita bata ko kalleni ba hakan yasa na wuce.


Ina zuwa yau ta baya nashiga gidan Shatu da yake bayan dajine babu Danni.


Kofar dakinta a bude hakan yasa na tura na shiga.


Tana zaune tana damun fura jin sallama na yasa ta dago tace;"yanzu nike shirin aika maki ince kitafo na dafa maki taliyar leda"


Da kyat na isa jin ta kawai nike amman har duhu nike gani, bisa kafitar dake tsakar dakin ta na fada ina kuka.


Shigowa tayi tace;"lafiya de ko miyafaru?"

Nace;"wallahi idan Baba yasan da ciki a jikina bansan ya zaiyi ba Baba na ya yadda dani Shatu fiye da yadda kike tunani, yana alfari dani da kalar tarbiya ta inama ace na fada mashi tun farko ya zanyi ki taimaka ga kudi muje idan akwai yadda za'ayi nide azubdaman dashi"


A jiyar zuciya tayi ta goge hawayen da suka zubo mata tace;"a kwai hadari wallahi zaki iya rasa ranki ina tsoro na fada maki da kunne na naji 'yan matan tudu na maganar, yanzu kinsan wani Abu?"

Na girgiza kai tace;"na taba jin kamar ance ganyen bedi na zubda ciki idan aka daka shi sai a tsaye ruwan asha amman fa banda tabbas"

Cikin sauri nace;"nide muje mu gwada"

Tace;"Babu tabbas abinda yafi mutafi wajen Iya zaifi, kila tasan wani Abu"

Cikin sauri nace;"a'a muje musamu bedin nide nasan Iya bazata barmu na zubda cikin nan ba, kinga haka zata ce ya fara girma"

Shiru Shatu tayi tace;"kuma haka ne fa, to amman banda tabbas kada kisha bedi azo ba haka bane kinga babu tabbas kada ya taba lafiyar jikin ki kona yaron ki"


Nace;"nide muje na tsinko ko mutuwa zanyi bazan iya zama na haife wannan cikin ba banson Uban D'aba sannan ace ni shegiya sannan na haifi shege Shatu ki tausayaman wallahi zanyi iya karfina saina zudda shi"


Shatu cikin sauri ta rike tace;"bamu san abinda Allah zai yiba Nana ina hakurin naki da juriya akan wahala duk suna Ina? Ya kamata na baki karfin gwuiwa ki chinye wannan jarabawar kada ki zubda cikin nan kilama Alheri ne a rayuwar ki kila shine sanadin hutun ki kada kifara".


Fizge hannu na nayi nayi waje ina kuka.

Nanufi wajen wani katon iccen bedi da ke bayan gidan su Shatu



Qurrah
*_JARABTAR MU*_




*_Written by-Qurrahโœ๐Ÿผ*_

Page-41-42


*Word Counter 2504*




*~โœ๐Ÿฝโœ๐ŸฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ~*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~We are bearer's of so golden pen๐Ÿ–Š~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden penโœ,behold our words.~*

*~A product of our pen๐Ÿ–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Zikiri Yayin Fita Daga Gida.*

ุจูุณู’ู…ู ุงู„ู„ู‡ู ุŒ ุชูŽูˆูŽูƒูŽู‘ู„ู’ู€ุชู ุนูŽู„ูŽู‰ ุงู„ู„ู‡ู ูˆูŽู„ุงูŽ ุญูŽูˆู’ู„ูŽ ูˆูŽู„ุงูŽ ู‚ูู€ูˆูŽู‘ุฉูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ุจูุงู„ู„ู‡ู.

Bismil-lah, tawakkaltu alal-lah, wala hawla wala kuwwata illa billah.
Da sunan Allah (nake fita), na dogara ga Allah, kuma babu dabara, babu karfi sai da Allah.

ุงู„ู„ู‘ู‡ูู€ู…ูŽู‘ ุฅูู†ูู‘ู€ูŠ ุฃูŽุนู€ูˆุฐู ุจููƒูŽ ุฃูŽู†ู’ ุฃูŽุถูู€ู„ูŽู‘ ุฃูŽูˆู’ ุฃูุถูŽู€ู„ูŽู‘ ุŒ ุฃูŽูˆู’ ุฃูŽุฒูู„ูŽู‘ ุฃูŽูˆู’ ุฃูุฒูŽู„ูŽู‘ ุŒ ุฃูŽูˆู’ ุฃูŽุธู’ู„ูู€ู…ูŽ ุฃูŽูˆู’ ุฃูŽูุธู’ู„ูŽู€ู…ูŽ ุŒ ุฃูŽูˆู’ ุฃูŽุฌู’ู‡ูŽู„ูŽ ุฃูŽูˆู’ ูŠูู€ุฌู’ู‡ูŽู„ูŽ ุนูŽู„ูŽู€ูŠู‘ .

Allahumma innee a'uzu bika an adilla aw udalla, aw azilla aw ozall, aw azlima aw uzlama, aw ajhala aw yujhala alayya.

Ya Allah! Ina neman tsarinka daga na bata ko a batar da ni, ko na zame ko a zamar dani, ko na yi zalunci ko a zalunce ni, ko na yi wauta ko a yi mini wauta.


DEDICATED TO....MY SISTERS๐Ÿ˜˜


Page-41-42




----------------Cikin wani irin tashin hankali ya farka daga baccin da yake.

Ya rike kanshi daya ke sarawa ga zufa dake zubo mashi duk sanyin A-C dake cikin dakin.


A hankali ya furta;"mike samun wannan yarinyar? A kwai matsala kenan?".

Kasa komawa bacci yayi yatashi yayo wanka yayi alwala yazo ya fara sallah daya gaji yafara karatun Al-qura'ani.


***************

Tana isowa ta shakeni tace;" fadaman gaskiya ciki ne dake?".


Na girgiza kai nace;"wallahi Inna wani abu naci gidan Shatu shine ya kumburan man da ciki shine yasa cikina murdawa".

Shiru tayi tana kallo na haskani take karayi sai tayi murmushi ta fita.


Ma'u tace;"Inna baza'a kira Mai Amalanken ba? tanajin jiki"kallon ta Inna tayi tayi tsoki tabar wajen.

Ma'u tazo ta kamani ta maidani bisa gado.


Cikina kara juyawa yake haka nayita kwallah Ma'u naban baki sai chan da aka kusa asuba kana bacci ya daukeni.



**************

Shagalta yayi dayima yarinyar nan addu'ar sosai har saida akayi asuba kana ya tofa ya tashi yayi masallaci.


Babu abinda yake a cikin sujadar shi inba addu'a ga yarinyar da yayi refing dinta.


Ana gamawa ya mikama Mai martaba hannu suka gaisa yayi part din shi.


Bacci yake son yi amman daya kulle ido sai yaji kukan ta.


Tashi yayi ya zauna tare da yin tagumi duka hannuwa biyu.




*************

Sai da safe kana na farka na mike naje nayo alwala na dawo nayi sallah jikina zafi hakan yasa na koma gado na kwanta.


Ina komawa sai bacci mai nauyi ya daukeni.

Cikin baccin naji haya niyya ga kamshi Mai dadi har cikin dakina.

Nace bari naga suwaye kamshin yaman dadi sai kara shaka nike ina lumshe ido.

Tashi nayi nayi waje ganin takalma masu kyau kofar dakin Inna yasa na saki baki dan bantaba ganin kalar suba.


Kamshin dana fito waje yafi yawa hakan yasa nayi wajen dakin Inna Amman da mamaki an turo kauren dakin ta.




Jin kamshin yafi yawa wajen dakin ta yasa na matsa jin kamshin nike kamar abinci saboda yadda nikejin dadin kamshin







Hancina nakai wajen kauren ina sun sunar kamshin sainaji anfara magana

Na girgiza kai nace;"Babu kyau labe bari nabar wurin kada Inna taji motsina"

Har na juya naji sunce;"Muna son idan anzo neman mai furar nan kuce ta mutu".


Ido na zaro wace mai fura kenan hakan yasa na dawo.


Inna naji tace;"ku suwaye kuma mike tsakanin ku da ita? diyar mijina ce ko sata tayi a birni dan zata aika"


Daya daga cikin su tace;"bake kika haifeta ba kenan?".

Cikin sauri Inna tace;"Allah ya kyauta idan ma laifi tayi ku dauketa ku tafi daman ta tar watsaman farin ciki gida".


Jin wannan maganar yasa zukatan su yin sanyi bukatar su zatazo da sauki.


Kudi Hanan ta fiddo ta aje gefen Inna tace;"duk kudin nan nakine inde zakiyi mana Abu guda daya tak".

Cikin sauri Inna tace;"wallahi komi kukace inyi zanyi akan mayyar yarinyar nan gatanan ta hana diyata farin ciki, tama diyata asiri wallahi komi kukace zanyi".


Murmushi sukayi Hanan tace;"za'a zo neman diyar ki" sai kuma tace;"yi hakuri namanta diyar mijin ki, idan sukazo duk abinda suka baki kada ki amsa zamuzo mu baki wadda yafishi idan sukace kece mahaifiyar ta kice eh ki amsa masu cikin jimami ina nufin hadda 'yan hawaye mukeso idan kinada saurin kuka, idan suka tambaye ki ba'asi kice ta mutu"

Cikin sauri Inna da Kursim suka kalli Hanan.


Kursim tace;"zasu tambaye ta miya kasheta".

Banji maganar da dayar tayi ba saboda muryar ta bata da karfi.

Murmushi Hanan tayi ta kalli Inna tace;"miza kice masu hakan zaisa nasan zaki iya wannan aikin, nasan kina bukatar kudi to bari kiji idan aiki yayi kyau kason ki saiyafi haka".

Cikin sauri Inna tace;"zance taje icce a daji maciji ya sareta ta mutu, dan ko diyar makwabtan mu haka ya faru da ita kinsan yaran mu na zuwa daji icce".


Murmushi su duka sukayi;"Hanan tace Amman gaskiya na yarda baki sonta hakan zaisa aikin mu yayi kyau to shikenan zamu tafi".


Babu abinda ke fitowa daga idona sai hawaye.


Har sun mike Kursim tace;"mijin ki ya rasune?".

Inna tace;"a'a yayi tafiya kila gobe ya dawo ko jibi badai zaiyi sati ba, kuma idan yana nan wannan aikin bazai yiyuba".


Su duka suka kalli juna Hanan tace;"kila suzo yau, insha Allah zamuyi nasara".

Jin zasu fito yasa zanyi baya naji Inna nacewa;"Amman baku fadiman laifin da tayi maku ba har za'azo neman ta".

Hanan tace;"kada kidamu wannan tsakanin mune kide kiyi aikin ki zamu fada maki amman sai mun dawo lokacin idan aiki yayi kyau amman babu tabbas din mu zamu dawo saboda yanzu muna cikin hidima Amman de nayi maki alkawarin kara maki kudin da sukafi na hannunki kila aikowa zanyi".

Inna tace;"ba komi nide inajiran Kudi".

Hanan tace;"kada ki damu"jin zasu fito yasa nayi daki da gudu.

Na zauna nakasa tuna komi su waye wadannan mutan nan??


Zufa nike sosai akan mi inada rai za'ace na mutu, waya turosu??


Haka nayita sabbatu har rana tayi hankali na ya tashi.


Jin ana kiran sunana yasa na fito.

Ma'u ce tsaye da wani yaro da sabuwar samira akan shi.


Yace;"Shatu tace akawo ma Nana".

Gani yasa Ma'u tace;"wai Shatu tace akawo maki injide ba irin na jiya bane?"

Nace;"Bari na duba ina Inna?"


Na amshi Samirar na bude cikin mamaki nike kallon samirar kaza ce ciki.


Nace;"kace Nagode kaji bari na baka"

Yaron yace a'a nayi-nayi ya ki amsa wai tace idan ya amsa bazata dan mashi ba idan ya koma, kuma zata gane cikin kudina naje na dauko mashi Muttala na bashi.


Nace;"Ma'u muci mana".

Tace;"Allah yasa Inna batanan tun da nadawo ban isketa ba kila tayi wajen yawon ta".

Tace;"nikam saide ki dan man tunda baki da lafiya".

Nace;"saide ki iyaba"

Tasa hannu ta dauki kadan nace ta kara.


Na zuba mata ganin bata dauki da yawa nayi daki miyau na har gudawa yayi na fara ci rabon da naci kaza ai har na manta

Inachi amman babu dadi nakasa gane wake keson ace na mutu minene alakata dasu, hakan yasa banwani ciba saboda yadda gabana ke faduwa

************


Part din Momy yayi na cikin gidan su.

Jallabiya ce a jikin shi Milk daka ganshi kasan akwai matsala a tare dashi

A parlour dinta ya zauna masuyi mata hidima suka gaida shi baiko kalle su ba sukabar wajen yana nan zaune sai gata ta fito.


Tace;"lafiya nagan ka haka kamar ba ango ba gasu Walida da Nifra nan zasu wuce Dubai shine mukayi bankwana sai anfara biki zasu dawo sai Monday kenan, amman kai kana Abu kamar ba ango ba".

Jin bazata tsaya ba yace;"please Momy kiyi wani abu mana banfa yi bacci ba yarinyar nan cikin baccina tazo tanaman kuka tana cewa na taimaka mata, Momy wallahi kukan ta jinshi nike cikin kai jin shi nike tamkar na MANAL kinsan na tsani kukan mace".


Ya sabko daga bisa kujera yazo inda Momy take tayi mutuwar zaune ko motsi ta kasa ya kama hannunta yace;

"Momy idan bakiyi wani Abu ba a yau to zan batama iyayena zan gudu naje neman yarinyar nan bazan iya cigaba da rayuwa ba idan bata nan"


Ganin hawaye sun zobama Momyn yasa yace;"Momy ki yadda ba Aljana bace wallahi mutum ce ina kaunar ta na bata mata rayuwa Kuma karamar yarinyar idan banji kanta ba Allah bazai barni ba".

Momy ta goge hawayen ta tace;"na yadda mutum ce kuma na maka alkawarin zan kawo maka ita inde tana duniya insha Allah yanzu zansa ane mota".


Wayar ta ta dauka;"Hello Hajiya Fatima inason zanyi magana da Mai gidan ki yanzu idan da yana nan"


Wayar tana hannun Momy yana Jin abinda ake fadi tace;"Allah ya taimaki first Lady yanzu gashi ma yana gida".


Cikin girmamawa ya gaidata tace;"tanason suyi mata aiki cikin awannin nan zata aiko mutanen ta aje dasu, nan ta fada mashi inda suke zama tace tanason agano sunan garin su yanzu".


Cikin girmamawa yace angama yanzu zakiji komi game da ita.

Sukayi ban kwana ta aje waya.

Tace;"Kaji yanzu za'ayi komi zamusan sunan garin su sannan zuwa gobe zan tura amintattun mutane suje gidan gobe".


Murmushi yayi yace;"thank you so much Momy"murmushi tayi tana shafa sumar kanshi.


Ya danji sauki a ranshi kenan ko gobe ana iya tafowa da ita.


A dakin shi ya koma yayi wanka ya shirya ya fito.


Kamar kullun yana fitowa akayi busar ya fito.


Hakan yasa gidan ko ina kamshi ke tashi.


Hankalin shi a kwance yaje dakiunan abokan zaman Ammie suka gaisa ya wuce part din Mai martaba dan yasan zai iske Ammi achan.


Yana shiga Ammie tayi murmushi tace;"Ango ne a part dinmu sai kamshi kake"


Murmushi yayi ya isa inda suke suka gaisa.


Nan Mai martaba ke bata labarin Yarima ya koma san fura.

Mamaki take tace;"lalle kam ashe Iya Rabi ta shirya kenan"


Mai martaba yace;"ai ya huta dan Baban nashi kusa da garin su yasa ake Gina mashi Lambu gashi ga mai furar".

Dariya sukayi suna
mashi dariya.

Kama hannun shi Mai martaba yayi yace;"Subhanallah! Yarima ina zoben ka na sarautar gidan nan banace kada ki cire ba idan ya maka kadan za'a kaishi a buda maka kasan Darajar shi kuwa?"

Kallon mahaifin sa yake ya lumshe ido ya tuna lokacin da yake saka matashi.


Mai martaba yace;"kayi magana mana"

**************


Ina zaune saiga Ma'u ta kawo man wani tuwo tace;"ita ta gamashi yanzu na boye kada Inna ta gani"nace to na amsa na aje.


Ana sallar magriba naji shigowar Inna.


Na fito nayi alwala na koma daki nayi sallah ina nan zaune har akayi isha'i nayi na koma na kwanta nama manta da wani tuwo.


Sai da dare yayi kana naji yunwa na tashi naje na wanke hannu na dawo na dauki tuwon.


Ina bude langar naji banson kamshin miyar nade daure saboda yau kazar nan kade naci kuma rabawa dai-dai nayi naba Ma'u.


Haka naita tura tuwan saida naci sosai kana naje na wanke hannu.

Ga mamaki na sainaga haske dakin Inna gashi dare yayi sosai.


Daki na koma cikin raina nace komi Inna keyi haryanzu ohow?


Na koma na kwanta ina kwanciya naji cikina na juyawa zuciyata na tashi.


Bakina babu dadi abincin sai tukata yake.


Jin amai yazoman lokaci guda yasa nayi waje a guje.


Nan fa nafara kwaraya amai har saida na amayar da komi na cikina.


Ina dago zan samo buta na kuskure bakina naga Inna tsaye bakin kofa.


Tace;"Yau Allah ya toni asirin ki munafuka Yau gaskiya tayi halinta bakisan kyaleki nayi ba kada na kaiki gaban mai gari a duba aga ba ciki ace kazafi nayi maki daman banson ki".


Na mike na fara ja da baya.

Tace;"wallahi bazan barki ba ki bata Mana gari kila Bana aki ruwa saboda ke wallahi yanzu ko gidan Mai gari sunyi bacci sai sun tashi wallahi yau sai kinbar duniya bakar munafuka mai raba mata da miji sannan ki raba Uwa da diya, yau nasan mutanan garin nan sai sun jefeki daman bakisan saida akayi tashin hankali kana suka yadda kika zauna ba saida Ubanki ya rantse yace ke ba 'yar zina bace kana suka yarda kika zauna to yau asirin ki ya tonu idan ke ba 'yar zina bace to zaki haifi dan Zina kinga kuma garin nan ba shege".


Guda tayi tareda shewa.


Ma'u dake tsaye tace;"Inna amman kinsan korarta za'ayi kuma Baba yace yabaki Amana kullun idan muna karatu Baba saiya maimaita mana muhimmancin Amana sannan Hadisin da nike yana magana akan duk Wanda ya rufe asirin dan Uwanshi shima Allah....."


Wata fanteka ta dauka ta jefama Ma'u hakan yasa bata ida maganar taba.

Tace;"wallahi zan iya tsine maki akan wannan yarinyar kinsan ta dalilinta bakin cikin dana shiga shekara tara kenan ina Kumar bakin ciki yau itace ranar da tabon bakin cikina zai goge"


Cikin sauri ta bankade Ma'u ta dauko mayafi tace;"ki jirani kiga sakamako" ta juya ta fita cikin sauri.


Ma'u tayi saurin isowa inda nike ta hawaye.

Tace;"bakida hankali zaki tsaya baki nemi mafita ba, yan kauyan nan wallahi jahilayya ne kuma kinsani mune masu ilimin su zasu iya komi, idan aka fara bugun ki saikin suma kana a koreki a garin kiyi sauri ki gudu, akwai wasu Kudi danaga Inna na kirgawa tun kamin inyi bacci Inna ke kirgasu har yanzu sunanan bari na debo maki, kije wani gari sai Baba ya dawo ko idan kin haihu sai kidawo saiki ce sharri Inna tayi maki shiyasa kika gudu zanji da Baba".

Ina kuka nace;"Ma'u nagaji da rayuwar nan su kasheni bama koraba idan suna iyawa su kasheni nagaji tunda na tashi nike cikin kunci da wahala ina rokon Allah yasa haka shiyafi Alkhairi"


A guje Ma'u taje daki saigata ta fito rike da kudi dakina ta shiga.

Ta dauko buhuna tace;ga kayan ki Bari na daukar maki kala daya masu kyau dan duk sun zama tsumma wahala kawai z daukar su zai zama"


Kallon ta nike ina hawaye zuciyata ta riga da ta bushe naji zan dauki mutuwar nagaji da wannan rayuwar bazan zan taba hutawa ba.

Ni kuma haka tawa Jarabtar take.


Jin kara yasa na maida hankali.


Dan kwankwanin dana saka zoben da mutunan nan ya bani ya fado daga buhun sai haske yake.


Dauka tayi tace;"minenen wanannan Nana?"

Nayi saurin amsa ina kuka jin hayaniyya da haske yasa tace;"mun shiga ukku Inna tana iya komi yanzu haka ihu tayi kowa ya tashi mutanan kauyan nan ne Nana ki gudu kibar kayan ga Kudi"


Taja hannuna tana kuka na fizge.


Nace;"kila mutuwa ta zatasa Inna farin ciki su kasheni babu inda zani"


Jin hayaniyyar ta doso gidan mu yasa na kara damke akwatin da zoben yake hannu na tare da fidda wasu zafafan hawaye masu zafi inajiran mutuwa ta



Qurrah
[2/24, 4:37 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *_JARABTAR MU*_







*_Written by-Qurrahโœ๐Ÿผ*_


*Page_43-44*





*~โœ๐Ÿฝโœ๐ŸฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ~*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~We are bearer's of so golden pen๐Ÿ–Š~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden penโœ,behold our words.~*

*~A product of our pen๐Ÿ–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Zikiri Yayin Fita Daga Gida.*

ุจูุณู’ู…ู ุงู„ู„ู‡ู ุŒ ุชูŽูˆูŽูƒูŽู‘ู„ู’ู€ุชู ุนูŽู„ูŽู‰ ุงู„ู„ู‡ู ูˆูŽู„ุงูŽ ุญูŽูˆู’ู„ูŽ ูˆูŽู„ุงูŽ ู‚ูู€ูˆูŽู‘ุฉูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ุจูุงู„ู„ู‡ู.

Bismil-lah, tawakkaltu alal-lah, wala hawla wala kuwwata illa billah.
Da sunan Allah (nake fita), na dogara ga Allah, kuma babu dabara, babu karfi sai da Allah.

ุงู„ู„ู‘ู‡ูู€ู…ูŽู‘ ุฅูู†ูู‘ู€ูŠ ุฃูŽุนู€ูˆุฐู ุจููƒูŽ ุฃูŽู†ู’ ุฃูŽุถูู€ู„ูŽู‘ ุฃูŽูˆู’ ุฃูุถูŽู€ู„ูŽู‘ ุŒ ุฃูŽูˆู’ ุฃูŽุฒูู„ูŽู‘ ุฃูŽูˆู’ ุฃูุฒูŽู„ูŽู‘ ุŒ ุฃูŽูˆู’ ุฃูŽุธู’ู„ูู€ู…ูŽ ุฃูŽูˆู’ ุฃูŽูุธู’ู„ูŽู€ู…ูŽ ุŒ ุฃูŽูˆู’ ุฃูŽุฌู’ู‡ูŽู„ูŽ ุฃูŽูˆู’ ูŠูู€ุฌู’ู‡ูŽู„ูŽ ุนูŽู„ูŽู€ูŠู‘ .

Allahumma innee a'uzu bika an adilla aw udalla, aw azilla aw ozall, aw azlima aw uzlama, aw ajhala aw yujhala alayya.

Ya Allah! Ina neman tsarinka daga na bata ko a batar da ni, ko na zame ko a zamar dani, ko na yi zalunci ko a zalunce ni, ko na yi wauta ko a yi mini wauta.

DEDICATED TO.....MY SISTERS๐Ÿ˜˜


Page_43-44

_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_



--------------Hannu na ta fizga saida nayi kamar zan fadi tayi hanyar bandaki dani.

Tace; "Idan har Baba yana da amfani a rayuwar ki to ki gudu idan kuma baida amfani ki tsaya su halaka ki, kinga sai ki saka Baban mu cikin wani hali kibar shi da kunci, kuma hakan zaisa na tsane ki a matsayin ki na 'yar uwata, saboda Uwata ce silar halaka ki mahaifina kuma zai tsaneta idan hakan ta faru ba zai taba ya femata ba, idon Inna ya rufe amman naki a bude yake saboda ke kina da ilimi, ki ceci rayuwar gidan nan ki gudu kada tayi sadaniyar halaka ki, idan kika tsaya shikenan zaki silar tarwatsa mana rayuwa dan idan suka kashe ki mahaifina bazai kara zama da Inna ba kuma akwai zuri'a a tsakani".


Kalaman Ma'u sun karyaman zuciya jin hayaniyyar ta matso yasa tace; "ga kudin mota kiyi nisa damu ta yadda ba ษ—an kauyen nan da zai ganki, har sai kin haihu sannan kidawo zanji da Baba".


Na amshi kudin Ina kuka na rike hannun Ma'u itama kuka take.


Na kama katangar ban ษ—akin mu na dira daman karshen gari muke ina dirawa sai daji.


Banko waiga ba, nayi gaba da gudu ina kuka saboda yadda garin ko ina hasken fitila.


Cikin daji nike gashi tsakar dare gashi babu fitila sai addu'ar dake bakina inayi ina neman tsari.




**********


Mai Martaba tsare shi yayi da idanu yana kallon shi.


Kallon hannun shi yake babu zoben sai murmushi yake.

Ammie tace; "ko Kulsoom kaba zoben shiyasa a gaban mu ka shiga shauฦ™in so?"

Shiru yayi da Mai Martaba da Ammie suka kalli juna sukayi murmushi.

Mai martaba yace;"to ai idan itace babu damuwa duk da zoben Mai daraja ne amman babu matsala ai itama ta shigo cikin mu duk randa ta haifa mana jika sai ya zama mallakin shi, kaga kenan na gada daga kakan nina, babban jikana shima zai gada, ina alfahari da haka amman fa kace ta kula dashi sosai".


Murmushi yayi ya mike yace;"Abbie Ammie bacci nakeji".

Nan sukayi bankwana Prince ya fita zuciyar shi fal da farin ciki.


A part din shi ya shiga yana zuwa an hada mashi ruwan wanka kamar kullun ya shige cikin bahon wankan ya lumshe ido yace;


"Lalle Abie zaka samu jika daga gareta nan kusa dan gobe za'a kawota sai a daura rana daya da Kursim"

Lumshe ido yake yana kara shigewa cikin ruwan masu kamshi yana murmushi jin shi yake tamkar tana bisa kirjin shi.


Ya dauki kusan awa ukku cikin shauki da tunani iri-iri na yadda zai maidata Queen.


Cikin sauri ya fito yana goge jikin shi yana murmushin sleeping dress din dake bisa bed din shi ya dauka ya saka yazo bakin window yana kallon samaniyya.


Jin shi yake tamkar yaune ranar da zai angon ce.


Har saida dare ya raba sannan ya hakura ya dawo ya kwanta.


Filo yasa a kirjin shi yana shafawa tamkar ita haka yake jin shi, sai faman kara rungume shi yake yana murmushi.



** ***************


Ina tafiya a wahalce har nakai tudu ina zuwa garin tsit babu ko motsi na wuce nayi hanyar birni.


Ina tafiya ina hawaye babu ko tsoro a idona, ko kaษ—an saboda

Please Login or Register in order to submit comment