Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

security.


Black din glas ne a fuskar shi, sanye yake da light blue din yadi kalar na jikin Daddy daka gansu kaga Uba da Ɗana.


Fuskar nan kamar ta kullun ce yau ma babu murmushi ko kaɗan a fuskar shi.


Sosai airport ɗin ya cika da mutane hakan yasa Security sai kara tura mutane baya suke masu daukar rahoto da sauran mutane.


Daddy ne ke daga masu hannu sai Momy sai Nifra itama da take sanye da Suit pink color itama Black din glas ne a fuskar ta.


Sai Kursim dake kusa da ita cikin doguwar riga, su duka sunyi kyau.


Motar Daddy da Momy ne a farko sai motar Kursim da Nifra.

Anuwar motar shi shikaɗai ne a ciki.


Suna zama Kursim ta kalli Nifra tace;"Meyasa Prince ya shiga mota shi kaɗai ?nayi tunanin a tare zamuje"

Kallon ta Nifra tayi tare da murmushi tace;"ko dasu Dad bai shiga mota tare da su, shi kaɗai yake shiga motar shi ya zauna, kafin Sister Manal ta rasu motar su guda, amman tun daga lokacin da ta rasu idan zamu yi tafiya shi kaɗai yake zama a mota guda, mun taɓa zuwa wata Umara mu duka motar da zai shiga nayi saurin shiga lokacin da yake kokarin shiga, wallahi juya wa yayi ya nufi wata ya shiga, Manal Kaɗai ce a duniya ke juya shi"

Murmushi Kursim tayi cikin ranta tace sai mai fura.

Shiru Kursim tayi tana tunanin da wannan MANAL din nada rai da bata san wane kalar gata da so za'a nuna mata ba.

Idan mutum ya mutu ana mantawa dashi cikin watanni amman ita gata tayi shekaru da mutuwa amman mutuwar ta kamar yau akayi ta.


Jin shirun yayi yawa yasa Nifra tace;"zan baki wani sirri game da Yaya Anuu idan kina son kiga murmushi to kusan ci wajen da yara suke yana son yara sosai, ina maki fatan samun su da wurii"


Mamaki Kursim take yadda lokaci guda Nifra ta chanza.


Nifra ta fahimci Kursim sai tace;"kiga na chanza ko? Na chanza ne saboda yadda kika nuna murna ranar Birthday din sister Manal"


Murmushi Kursim tayi cikin ranta tace,lalle yau taga karshen so, shi family din idan kana so a soka saika nuna kauna ga Manal waccr bata duniya, to wannan MANAL da tana duniya da kila ko ganinta ba zasu samu damar yiba saboda matsayi.


Dai-dai lokacin motar su ta tsaya a cikin sauri aka bude masu tare da aza masu red din carpet a kasa.


Nan ma wajen cike yake da yan jarida da muta ne, banda daukar su photo babu abinda ake, har suka kai wajen kofar shiga.


Tana waigowa taga Yarima tafe shi da Daddy sun jera Dad na rike da hannun shi.

Wani kyau da annuri ta ga ya kara.


Juyawa tayi tabi bayan Nifra ta shiga ciki.



**************

Zirga-zirga nike a cikin dakina na kasa fidda shawara.


Hannuna nasa cikin rigata na azashi bisa ciki na, jin motsi hakan yasa hawaye masu zafi suka zubo man.


Nayi saurin gogewa na koma na zauna nayi ta gumi.


Jin motsin Baba yasa nayi saurin fitowa.


Lokacin ya juya da keken sa zai fita, nayi saurin isa kusa dashi nace;

"Baba fita zaka yi?? wai daman haka nace ina son zuwa wajen Shatu idan kasamu lokaci"


Murmushi yayi yace;"yi hakuri Nana na manta shab wallahi abun na raina kullun ina son ince maki kishirya mantawa nike"


Nayi murmushin karfin hali nace;"ba komai Baba daman nayi kewar tane".


Yace;"kada ki damu dauko mayafin ki muje, daman kwana biyu ina son in fadi maki ina ta kokarin zuwa Gubi ne wajen tsohuwar matar Yaya bata san ya rasu ba, yana da kyau ta sani duk da sun rabu, ina kokarin inbar maki kudi masu tsoka waɗan da zasu isheki har indawo".


Murmushi nayi na dauko Hijab dina na hau bayan keken shi, muka fita.


Muna tafe yana ban labarin Gubi a chan ciwon ya kama dan Uwan shi, shi yaje ya taho dashi, shima malami ne yan uwan shi malamai suka yi mashi sammu shekara tara kenan yana kwance, a chan ya auri matar shi Rabi tana da kirki ba su taɓa haihuwa ba daman tana da yaran ta daga baya ya aure ta mijin tane itama ya rasu uban yaranta, anta surutu a kauyen daga zuwan malami ta aure shi ba'asan asalin shi ba.


A lokacin shi ba ƙone a garin amman lokaci guda yayi kaurin suna aka san shi a kauyuka na kusa dasu da kauyan su, hakan yaja kiyayya daga malam garin shine wani yayi mashi sammu yana da son zumunci kuma yana zuwa wajen iyalin shi, jin shirun da suka ji sai hankalin iyalin shi ya tashi gashi ni kaɗai nasan garin saboda ni kaɗai ne naje daurin auren shi, hakan yasa na shirya naje.

Koda naje na iske shi duk ya rame nan nasan abinda ke faruwa nace zan dauke shi mu koma gida dangin Rabi suka ce saidai araba auren daman suke taimaka mata kuma sun gaji, suka ce saidai a raba auren tunda ba zuri'a a tsakanin su, ba zasu yadda subada 'yar uwar suba taje wata uwa duniya, daman wai saida suka yi yar jejeniya, kuma gata da manyan & ƴaƴa, haka yayi mata saki guda muka kama hanya, ina yawan zuwa garin harma dai cikin rani, suna da wani Gulbi(korama)nan kusa dashi nike noman rani.

tana da mutunci mun saba da ita sosai, bata taɓa ɓataman ba haka nima ina mata biyayya.

Nayi ajiyar zuciya, yace;"ni kaina ban san barin ki saboda yadda na sameki wannan tafiyar, shiyasa nike so na baki kudi wadan da zasu isheki, munyi zaman mutumci da ita ya kamata tasan komai, wallahi yanzu idan naganta kunyar ta zanji, saboda tun lokacin da yabar garin sau biyu naje tsawon shekara tara, gashi ta nuna ma dan uwana soyayya, kiyi hakuri dole tasa zan barki, tafiyar kwana biyu an azabtar dake ina ga kusan sati biyu zanyi"shiru nayi nima Rabin nan taban tausayi nasan yanzu ta kara tsufa.


Haka yayta bani labarin kirkinta har muka isa wasu gidaje na fulani.


Yace; " a yadda akayi man kwatance nan ne, zanje kasuwar kauyen Mahuta sai na dawo zan biyo na dauke ki"

Murmushi nayi nace;"Allah ya taimaka Baba Allah ya bada sa'a"


"Amin Nana"ya juya ta tashi na kalli wajen gida guda ne amman kwai bukkoki kalar na fulani a ciki.


Ina shiga naga yara suna wasa ga iyayen su chan ƙarƙashin inuwar bedi.

Nayi sallama suka juyo suna kallona.

Duk kauyen cinmu sai naga nafi wadan nan lalle Allah mai iko haka duniyar take.


Suka amsa da Hausar su wadda bata fita dai-dai suna kara bina da kallo.


Har na fara tunanin kodai ba nan bane gidan?

Sai kuma naga wani gini ya banbanta da sauran dakin kasa su kuma sauran duk bukkoki ne, kuma an shafa mashi farar kasa, nayi ajiyar zuciya nace kila gidan ne.

Na gaida su nace;"Dan Allah nan aka kawo Shatu".

Budar bakin su suka ce;"kece Nana ta gidan Liman?"cikin mamaki na girgiza Kai.


Ai kafin nayi wani Abu yaran dake wasa sun ruga suna fulatanci suna ambatar sunana.

Sunyi dakin nan na kasa mai fentin farar kasa.

Sauran matan suka washe baki daya tace;"ai kullun sai Shatu tayi maganar ki, tai ta aiken Jabe yazo dan ta aike shi wajen ki yaki zuwa"murmushi nayi.


Dayar tace;"ga ma tanan zuwa"

Nayi saurin juyawa na ganta ta rugo a guje tana dariya.


Nima na ruga muka rungume juna muna dariya.


Tayi ma sauran magana da fulatanci ta kama hannu na muka nufi dakin ta.


Muna tura kofa naga wata 'yar baranda ansaka gadon karfe ƙarami,wajen zama ne, sai kuma bandaki, muka shiga dakin ta daya sha kayan jere na kauye da gadon karfe mai rumfa, lalle an kashe mata kudi dakin cike yake da tasoshi.

Muka zauna bakin wata katifa dake kasa itama ansa mata zanen gado.


Ta mike ta kawo mani ruwa cikin kofin silver ta zuba min ta zuban cikin karami, ta dauko wasu kwanoni ta ajeman.

Tace;"kai lalle ba sai na tambaya ba duk kin chanza kin kara fari da kyau lalle addu'ar mu ta amsu yanzu baki cikin wahala sai addu'ar miji na gari"

Nayi murmushi nace;"bar abincin nan wata magana nike son yi ina zargin wani abu"

Ɓata fuska tayi tace;"wallahi sai kinci abinci na, kuma kalar abincin yan burni ne nasan baki taba cin taba, yarinya taliya ce kalar ta leda kinsan neman kudi mijina yake zuwa duk rugar nan ni kaɗai ke chinta, kema sai kinci kinji, munyi maganar daga baya kuma na rantse".

Nayi murmushi karfin hali nace;"ina mijin yake?"tace;"jiya ya koma tun bayan auren mu baije ba sai jiya ya koma"


Ta zuba man ina dan danawa naji da dadi nayi saurin ci, dan danan na cinye nasha ruwa naji cikina ya cika.


Nace;"wallahi na rikece Shatu"tace;

"Kamar ya bayan naga har kyau kin kara ina ta murna naga kinyi haske"

Nan na fada mata abinda ke faruwa.

Kasa motsi tayi sai sakin baki da tayi tana kallona.


Na matsa kusa da ita ina hawaye nace;"ki taimaka man Shatu ki fadaman cikin ne da gaske?"


Ta goge hawayen da suka zubo mata tace;"lalle da gaske ciki ne dake, yanzu ya zamuyi?"

Na fadi mata muzubar da cikin idan tasan wani abu da ake sha.


Tace;"wallahi ban sani ba kuma ance mutuwa ake,ta taɓa jin wata suna magana kinsan yaran tudu basu da kunya daya tayi ciki aka je zubar mata da cikin ta mutu, suma kenan da suke kusa da asibiti kuma a birni akaje amman ta mutu, kuma ance haramun ne".


Yanzu ya zanyi kenan?

Tace;"kawai ki gudu wajen dangin mahaifiyar ki"cikin kuka nace;"na fada maki ban san komai game dasu ba, ko wajen dangin Baba bani zuwa dasu Ma'u Kaɗai ake tafiya, yanzu ya zanyi kenan?"


Tace;"Kuma Baba bai taɓa fada maki yana da yan uwa wani gari ba da sai ki gudu a chan".

Na girgiza Kai,tace;"ki dai yi tunani"nayi shiru Ina tunani.

Sai chan nayi shiru Ina tunani nace;"yawwa saidai wata basu da zumunci saidai alakar mutunci kuma yace tana da mutunci amman fa da nisa kuma chan zashi"

Tace;"yawwa ya sunan garin,koma dai minene indai ba zata cutar dake ba"

Cikin sauri nace;"Gubi"

Tace;"to minene sunan babban garin kamar nan katsina Batagarawa kinga Katsina ne babban birni Batagarawa kuma mai bi mashi "

Nayi shiru ina tunani nace;"cikin labarin bai ambaci sunan Babban binnin ba"


Tace;"toki tambaye shi cikin hikima"na daga kai duk jikina ya mutu.

Tace;"lafiya naga kamar baki amince da shawarata ba?"

Nace;"Ina tunanin anya zan iya guduwa inbar Baba? Nidai nafison nima ya zube ai ina jin ana cewa wasu cikin su ya zube"

Tace;"Ina tsoron kada ki rasa ranki kinji fa abinda ya faru da yarinyar tudu wallahi bazan baki goyan baya ba, kije ki rasa rayuwar ki kuma kinyi ma Allah laifi ina maki fatan ki cinye jarabawar ki Allah zai taimaka maki"nayi shiru nidai kam bazan iya guduwa ba.

Tace;"kinga idan Baba ya tafi tunda mijina bai nan kizo nan ki ringa yini tunda kina amai ga Kuma kasala,tunda baki yadda da guduwar ba, kinga Koda Inna zata gane idan Baba na nan abin zai zo maki da saukii"

Na daga kai alamar amincewa



Haka muka yini sai yamma Baba yazo muka tafi muna dagama juna hannu.


Muna tafiya ina bayan keken shi nace;"wai Baba ya sunan Babban birnin garin su Inna Rabi?"

Yayi murmushi yace;"kin taba jin sunan Bauchii...!"yaja maganar.

Nayi shiru kamar Maison tuna wani abu, na girgiza kai alamar a'a

Yace;"to sunan Babban birnin su kenan"

Nayi shiru tare da kara mai-maita Bauchiii.....


*************

Har dare bata ga Anuwar ba hakan yasa hankali ta ya tashi ina yaje kada ace katsina ya tafi.


Yana dakin shi a bakin window hannu cikin aljihu.


Yana kallon sararin samaniyya.

Yanzu me zaiyi kenan??

Wata dabara ta fado mashi ya juya yayi hanyar fita.

Part din Momy ya shiga.

Yana zuwa ya isketa tana magana Daddy na kusa da ita waya take.


Shima kusa da Daddy yana zaune remote a hannun shi.

Bayan ta gama ta maida hankalin ta wajen Anuwar tace;"Anu ya kake ne?"

Yace;"Momy yaushe Kulsoom zata koma?"

Daddy dake kallon News ya juyo yana kallon shi cikin Mamaki.

Daddy yace;"miyasa ka tambaya?"

Kai tsaye yace;"ina son zuwa ne"

Daddy yace;"Babu inda zaka, saboda aljanar yarinyar nan kake son zuwa kuma ba zaka ba gobe zamu wuce Bauchi, ita kuma zata wuce Katsina"


Shiru yayi ya kara hade rai Momy tace;"kada kadamu kabari agama biki kana kaji Anu na, zan taimaka maka nima saboda kace karamar yarinya ce zuciyata ta sosu"

Kallon ta Daddy yayi cikin mamaki yace;"kina hauka ne biye mashi zakuyi ku bata man siyasa ace dana yayi ma karamar yarinya fade, bazai yiyuba, ba'a gidan nan ba"

Nan ya cigaba da fada yana daga murya har Nifra da Kursim suka jiyo tare suka shigo


Cikin fushi Daddy ya juya idon shi har ja suka yi.

Zuciyar Kursim tayi fari tas taji dadi amman bata bayyana ba.

Shiru falon Nifra ta matsa kusa da Momy tace;"Momy wallahi nima yarinyar taban tausayi haka yace fa iyakar ta girma na, Amman ace an mata fyade abun tausayi ce please Mom kiyi wani Abu"

Kallon ta Kursim take cikin mamaki lalle maganar Daddy Aljana ce wannan yarinyar taya za'a yi ace har ta saye zuciyar su bayan zuciyar Anuwar data saye.

Maida numfashi tayi ta juya


Nifra ta tashi taje inda Anuwar yake zaune ta kama hannun shi tace;"zan taimaka maka Yaya please kasaki ranka nima ina son yarinyar kodan kalar tafiyar sister na"

Murmushi yayi suka hade hannun su Momy ma ta aza nata bisa nasu.

Su kalli juna sukayi dariya.

Momy tace;"Nayi alkarin zan taimaka maka da duk karfina Anu dina"

Nifra ma tace kamar yadda Momy tace

Anuwar yayi murmushin nasara, tareda lumshe ido ya hango gudun ta.



Qurrah
*_JARABTAR MU*_

Page-37-38

*_Written by-Qurrah*_




*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*Zikiri Yayin Fita Daga Gida.*

بِسْمِ اللهِ ، تَوَكَّلْـتُ عَلَى اللهِ وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُـوَّةَ إِلاَّ بِاللهِ.

Bismil-lah, tawakkaltu alal-lah, wala hawla wala kuwwata illa billah.
Da sunan Allah (nake fita), na dogara ga Allah, kuma babu dabara, babu karfi sai da Allah.

اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعـوذُ بِكَ أَنْ أَضِـلَّ أَوْ أُضَـلَّ ، أَوْ أَزِلَّ أَوْ أُزَلَّ ، أَوْ أَظْلِـمَ أَوْ أَُظْلَـمَ ، أَوْ أَجْهَلَ أَوْ يُـجْهَلَ عَلَـيّ .

Allahumma innee a'uzu bika an adilla aw udalla, aw azilla aw ozall, aw azlima aw uzlama, aw ajhala aw yujhala alayya.

Ya Allah! Ina neman tsarinka daga na bata ko a batar da ni, ko na zame ko a zamar dani, ko na yi zalunci ko a zalunce ni, ko na yi wauta ko a yi mini wauta.


DEDICATED TO....
MY SISTERS😘


Page-37-38



_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_



--------------Muna shiga ya jin gine keken shi a bango, na dauko buta na zuba mashi ruwan alwala na juya nima na zuba na fara alwala.


Duk abinda ake a kan idon Inna amman bata tanka ba, sai harare-harare da takeyi.


Na shiga daki na shimfida kallabin da nike sallah bisa nayi sallah kana na zauna Ina karatun Al-qura'ani har akayi isha'i kana nayi sallah na juya na hau gado na kwanta.



*************

Goyan bayan dasu Momy suka bashi yasa yaji zuciyar shi cikin farin ciki.


Har mantawa yayi da wani auren Kursim da za'ayi.


Haka yayi bacci zuciyar shi cikin farin ciki.


A bangaren Kursim tana daki abin duniya ya isheta game da supporting din da yasamu wajen su Nifra da Momy.


Yanzu ya zatayi kenan??

Cikin sauri ta dauki wayar ta ta kira Hanan.


Tace;"Hanan akwai matsala fa"shiru Hanan tayi.

Shirun da tayi yasa Kursim kara mai maita maganar.

Hanan tace;"nasan matsalar ki ina tunani ne, matsalar bazata wuce shegiyar mayyar mai furar nan ba, koba ita bace matsalar?"

A jiyar zuciya Kursim tayi tace;"wallahi itace yanzu kinsan matsalar guda ce Momy?"

Nan Kursim tabata labarin yadda akayi yanzu.


Hanan tace;"kibari gobe kina iso kiyiman waya inzo musan abinda zamuyi tun kamin asamu matsala dan Momy tana power zatayi amfani da Power dinta wajen taimaka mashi sati guda yayi yawa sungano kauyan su, dan haka gobe kina iso kiyiman waya"


A jiyar zuciya tayi tace;"Nagode Hanan saina iso wallahi da kyat zan iya yin bacci"

Hakade Hanan taita kwantar mata da hankali.



*************

Tun da asuba Baba ya kwan kwasaman kofa na mike na bude na gaishe shi.


Yace;"tafiya zaiyi a Katsina ake hawa motar Bauchi kuma tunda safe suke tafiya"


Ya mikoman kudi masu yawa yace;"gashi nan ki rike nayi shawara natafi Yau saboda jiya wani abokina da muka hadu kasuwa yake fadiman akwai mota daga Katsina har Bauchi kuma cikin saukin kudi dan na gwammanati ne shine zanje ya kaini, kinga nasamu sauki basai nayi wahalar tafiyar nan ba daga nan sai naje Kano kana na hau ta Bauchi ga mota cin basu da kyau amman yace man ita wannan motar bamu ko kwana, kinga kenan bazan dadeba kila iyakata kwana ukku saboda banson na dade saboda ke, ki kula kinji"


Nace;"to Baba Allah ya tsare adawo lafiya, zan kiyaye insha Allah, kuma daman inason in tambaye ka zan dan je gidan Shatu da yake mijin ta bainan yana bida birni"

Yace;"yawwa nima hankali na zai kwanta amman kidinga dawowa nan kina kwana kuma kada ki kai dare"

Cikin jindadi nace;"to Baba adawo lafiya"

Ansar jikar hannun shi nayi, dakin Inna ya nufa ya kwan kwasa ta fito.

Ta kalleni duk da akwai duhu amman akwai fitila hannun Baba.


Bata ce mashi komi ba saide tayi tsaye a bakin kofar dakin.

Ma'u ma tafito tana murzar ido tace;"Baba lafiya de?"

Yace;"lafiya kalau Ma'u tafiya zanyi Bauchi...."

Bai karasa zancen ba Inna tace;"Bauchi! Wallahi na tsani garin nan saboda yarinyar nan yanzun ma Bauchin zaka kara zuwa ka kwaso mana wasu shaggun?"


Kallon ta yayi cikin mamaki yace;"su waye shaggu Rakiya?"

Kai tsaye ta nunani tace;"ai daga zuwa Bauchin ne ka kwaso ta yanzu wasu zaka kwaso"sai ta aza kuka tace;"wallahi Malam kwara ka fadaman gaskiya idan kanada mata a garin nan akan kaita zuwa kana kwaso man yara"shiru yayi.


Yace;"Amman Rakiya kinban mamaki waike wace irin mace ce? Mijin ki yazo yana fada maki zaiyi tafiya mai nisa irin wannan amman kina maganar kada kwaso maki shaggu, idan inada wata matar zan dauki dogon lokaci banje ba?? nide nazo ne dan na rokeki kada ki azabtar da Nana Allah yana kallon ki, kisani shi Dah idan ka rike shi bakasan mi zaya zama ba kilama itace zata rikeki, kila itace zataji kanki, dan haka kiji tsoron Allah kwana ukku zanyi ga Amana nan nabar ki, ke yanzu bai isheki ishara ba yadda kikaso ki dur kusar da rayuwar ta da auren Lado sai Allah yayi mata sakayya wannan ya isa ya zama darasi a gareki"

Daga haka ya juya mukabi bayan shi nida Ma'u.


Muna zuwa muka gaida abokin shi malam Habu dake bisa babur dinshi yana jiran Baba.


Yace;"Ma'u banson yawon nan naki ki kula kinji duk da ita 'yar uwar ki banjin ta nasanta da tsantseni da kula kuma kema inason ki kula da mutumcin ki kinji"


Tace;"insha Allah Baba zan kula sai ka dawo Lado yace zaizo jin magana Allah ya kiyaye Baba"

Baiyi magana sai girgiza kai yayi.

Jin yadda mahaifina ke yabo na akan zan kula da mutunci na yasa nayi sumar tsaye hawaye suka taru ido lalle idan yasan abinda ke faruwa akwai matsala nayi sake wani wanda bansani ba ya bataman rayuwa.


Malam Habu ya tada mashin jin banyi magana ba yasa Baba haskani yace;"lafiya zan wuce Nana"

Ganin hawaye yasa yace;"kiyi hakuri kinji saboda ke bazan dade ba ga 'yar uwar ki nan ku hada kanku kinji kuyi hakuri insha Allah zan dawo"


Hannuna Ma'u ta rike tace;"kibar kuka kinji yace bazai dade ba"

Daga kai nayi na daga mashi hannu.

A haka mukai ta daga mashi hannu har ya wuce muka koma cikin gida Ma'u tayi dakin Inna ni kuma nayi daki.


Kasa komawa bacci nayi na zauna bakin gado Ina shafa ciki na inajin motsi a cikin.


Kuka nike sosai tare da rokon Allah yayi man mafita gashi cikin nawa ya fara kun burowa da alama kato zaiyi.


Kullun Baba yana yabona yanzu idan yasan haka ya zanyi??


Shiru nayi inatunanin yanzu mizan fadima shi inama tun farko na fada mashi da yanzu an wuce wajen.


Amman kuma idan dana fadi mashi ai bansan ya zai dauki al'amarin Allah de ya kawoman Mafita.



***************

Tunda safe Kursim ta shirya taje tayima Momy ban kwana.


Hadda Daddy saida ya fito yana mata godiya akan kokarin da tayi sannan ya bata Dollars tana ta godiya haka wajen Momy tasha kyau.


Daddy ne yace baiga Anuwar ba ya kamata ace zai mata rakiya har airport itade Momy bata ce komi.


Ya kalli Kursim yace;"Kulsoom kije dakin shi kitado shi bai kamata ace kin wuce bakuyi ban kwana ba, duk dade kin kusa zama 'yar gida"


Tace;"to Daddy"cikin jin dadi tayi part din shi.


Yaune rana ta farko data shiga parlon shi.

Tunda take a rayuwar bata taba ganin parlon da yayi tsaruwar na Anuwar ba wannan wane irin sone Daddy kema Anuwar lalle idan ta samu shiga wajen Daddy ta gama komi.


Yanayin yadda akayi ginin benen dake cikin parlon shi kanshi abin kallo ne dan bata taba ganin kalar shi.


A hankali take takawa har ta hau sama inda ta iske wani kayatattacen parlon shida na farko ma ta rasa wane yafi kyau.


Kallon wajen take tanaso ganin inazata nufa duk ta rikice.


Sai chan ta hango wani korido tayi chan shikan shi wajen an hada shi da wani kalar kujeru kamar na kaba tana ganin su a Indian Fim jikin su hadda katifa kamar gado kamar kujeru haka suke.


Mamaki take taya za'ayi ace duk wannan wajen na mutum guda ne ace mutum guda ke rayuwa lalle antakura mashi zaman shi na Katsina.



Ganin kofofi yasa ta tura guda a hankali bedroom ne amman babu kowa sai wani kalar gado da yaune rana ta farko da ta taba ganin kalar gadon ko a fina finen kasashen waje bata taba ganin waje mai haduwar part din Anuwar ba.


Dakin dake kallon ta ta tura a hankali ta ganshi kwance yana bacci hankalin shi kwance cikin bargo.


Shiga tayi ta rasa miza tayi mashi.


Aje dan karamin gyalen ta tayi da hand bag dinta.

A hankali ta hau gadon ya dan motsa saita kame.

Ganin ya ciga da baccin yasa ta daga bargon ta tura kafafun ta ta matsa kusa dashi na rungume shi ta baya tana shafar bayan shi.


A hankali ya bude idon shi ganin abun yake kamar a mafarki wanene zai shigo mashi daki hadda rungume shi ta baya.



Wannan ai kalar rumgumar Manal ne ita ke rungume ni ta baya idan tana so intashi.


Murmushi yayi kila Nifra ce.


Kara lumshe ido yayi yana tuna yadda take mashi.


A guje take shigowa idan ta tashi bai tashi ba sai ta rungume bayan shi tare da manna mashi kiss tana dariya dole inde ta tashi to shima sai ya tashi.


Murmushi yayi yana taba kumatun shi.


Jin shiru yasa Kursim kara rungume shi jitake inama ace an daura auren ta zama matar shi.


Ganin time yana tafiya yasa tayi saurin tashi.


Jin an sake shi yasa yace;"Nifra ki gyale dan Allah bacci nikeji bana son takura bana hanaki shigoman part ba, idan kika kara saina maki duka kuma nace maki banason ana shigo man bedroom ko, wannan shine last warning idan kika kara nidake"

Daga haka ya kara lumshe ido yana matse filo a kirjin shi yana murmushi.


Ganin haka yasa Kursim tashi taje ta dauki gyalen ta da hang bag dinta tayi waje.

Kenan ita bata da matsayin da zai tunata yadda yake maganar kamar yasha wani abu ko har yanzu yana shan giya??


Wata zuciyar tace mata giyar soyayya ko.


Tana isa Daddy yace;" ankira wayar ki baki dauka ba kada jirgi ya tashi nasan Anuwar ne yakeson shiriritar dake kila yace sai yayi wanka ai kwara da kika baro shi"


Nan suka rakota har wajen mota ta tafi.


A dakin Anuwar yana koma bacci banda mafarki babu abinda yake sai mafarkin ya sake kusan mai fura.


Cikin sauri ya bude ido tare da addu'a a bakin shi.


Tashi yayi yaje yayi wankan tsarki kana yayi wanka ya dawo.


A bakin gado ya zauna yayi tagumi shiyama rasa gane kanshi.


Shin sha'awar karamar yarinyar nan yake koko sonta yake ko tausayin ta??


Yarinya tasa shi ya koma yin wankan tsarki duk yayi bacci.


A main parlo ya sabko ya iske Nifra kwance tana Chart yau kamar kullon kananun kaya ne a jikin ta.


Ita kade ce a parlon jin kamshin turaren shi yasa ta dago ta ganshi zaune yana latsar wayar shi.


Tace;"Yaya Anuu yaushe kashigo banji ko takon tafiyar kaba saide kamshin ka

Please Login or Register in order to submit comment