Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda duniyar ta fita raina sai addu'ar kariya da nike daga sheɗanu.


Koda na iso Batagarawa nan ma ba mutane na wuce na cigaba da tafiya saida na iso barandar mu sannan na zauna na jingina da bango.


Haka nayi zaune ina hawaye ina kara makyalewa a bango duk da ba motsi sai an dauki lokaci mota ke wucewa.



Ina nan zaune safiya ta fara waye wa.


Ganin gari ya fara haske yasa nayi saurin mikewa kada cikin 'yan garin mu wani yazo.


Nabi titi ina tafiya Yau itace rana ta farko da kafata zata shiga birni.


Jikina sai kyarma yake ina kalle-kalle har na iso wajen wasu gida je masu yawa kala daya.


Sakin baki nayi na tsaya Ina kallon su.

Karar Babur ya maidoni daga shagalta ina kallon gidajen.


Mai Babur ne yace;"Yarinya tafiya zaki yi kizo na wuce dake wajen nan yana wahalar samun abun hawa da safe, idan kika ce zaki jira Napep('yar kurkura) anan zaki dade baki samu ba"


Ban ma fahimci mi yake nufi ba to kawai nace na hau Babur din.


Yace;"Ina zamuje?"


Nace;"inda ake hawan motar Gwamnati zamu".


Yace;"daman tafiya zaki yi banganki da Kaya ba ai, bari nayi sauri yadda zaki samu motar farko"

Nidai bance komai ba saboda bansan yadda abin yake ba.

Muna zuwa naga mutane ma tafiya ana sabke ni wasu dake tsaye bakin tashar suka zo suna tambayar yarinya ina zaki? Da kyar nasamu nace Bauchi saboda tsoro ya kamani wani daga cikin su yace na bishi.

Na bishi ina zuwa yace ga ciko na samo shikenan motar farko ta cika a bude ta biyu.

Na shiga akace ina kayana za'a daure nace banda Kaya.


Hakan yasa aka rufe mota tare da fita muka dauki hanya.

Nide na kasa natsuwa sai satar kallon motar nike saboda ban taɓa ganin irin taba.


Matar dake kusa dani tace;"Yarinya ina zaki haka tafiya mai nisa ba kayan sawa?? Kamar ma baki wanke fuska ba".


Na dukar dakai nace;"eh ina sauri ne domin na samu mota"

Tace;"kin koyi sa'a dan wajen wani ne har an rubuta sunan shi ya biya kudi yace bari ya dawo shiru bai dawo ba saida aka bada kayan shi ga mota ta biyu"

Nayi murmushi sai kara damke zobe na nike.


Haka akayita tafiya tun idona biyu har bacci ya daukeni



**************

Yau koda ya tashi da wuri ya shirya ya kira Momy tace sun tafi karfe goma jirgin su zai sabka.


Ya zauna yana jiran jin mizai faru.


Cikin hadiman shi yasa yana zaune bisa Bed din shi daya na warware mashi kayan dazai saka na tarbar ta, kayan da Daddy yasai mashi ne sai yanzu ya buda su.


Kayan ne gasunan amman ya kasa zabar wanda zai saka idan zata zo.


Wayar shi ya dauka ya kira Jawad kanan shi.

Cikin mamaki Jawad ke gaida Anuwar bai tsaya amsawa ba yace;"inason ayiman wasu order kaya a yau nikeso su iso dan gobe zanyi amfani dasu kuma da safe".


Jawad yace;"baka ga kayan da Daddy yasa akayi maka order ba? Duk kayan dake a wadirof dinka sabbin zuwa ne dan wallahi bazaka same su anan ba"


Jin shiru ya aza ya kashe Jawad ya maimaita;"Hello"

Tsoki Anuwar yayi yace;"kagama naka surutun idan bazaka yiba nasa Usman"

Jawad yace;"abinda kakeso shi za'ayi zanyi masu magana sai aturo maka ka zaba a waya"


Murmushi yayi ya kashe wayar saura kuma aka maida.


Baifi ten minutes ba saiga shi sun shigo.

Wani Indian Prince Suit ne ya gani ya dade yana kallon su Nevy Blue wunyi kyau sosai suya zaba.


Yana turama Jawad su yakira shi.

Jawad na dariya yace;"to bari kaji wallahi wani Prince din India ne zaiyi aure shine fa sukayi su amman bari naji idan zasu bada kalar su, idan abin yafi karfina zan hada su da Daddyn ka"


Anuwar yace;"okay"


Jawad yace;"please Broth kada ka kashe dan Allah wacece wannan da zakayi ma kwalliya ko kana neman auren wata Princess ne a wata kasar? Dan nasan wannan bana Kulsoom bane"


Kashe wayar shi yayi yana kallon kayan yasan zasuyi mashi kyau.


Lumshe ido yayi yana addu'ar Allah yasa ta soshi kada ace ta tsane shi saboda abinda yayi mata.


Kallon photunan MANAL yayi dake dakin yace;"sorry babe nayi maki alkawarin bazan so ko wace mace ba amman wannan dole na sota na cuceta da kananun shekaru nasan da kinada rai kema zaki tausaya Mata"


Daukar photon dake kusa dashi yayi nata ya manna a kirji yasa blanket ya rufe jikin shi tareda Lumshe ido kamar wanda ke bacci.


Babu abinda yake jira sai kiran Momy yaji antafo da ita.



*************

Koda na farka har yanzu tafiya ake.

Wani gari muka tsaya ganin kowa ya fita nide nayi zaune.


Matar kusa dani tace;"Baki fitowa ki sayi abinci idan zaki zagaya ki zagaya daga nan ba'a kara tsayawa sai Bauchi dan mun wuto Kano kadan duk kina bacci"


Nace;"to"


Na fito na sayi ruwa na wanke fuskata na sayi awara na kara sayen ruwa na koma mota babu kowa suna waje saicii nike hannu baka hannu kwarya saboda inajin kunyar cin abinci cikin mutane.


Jin dadin awarar yasa na sabko nazo na kara lokacin sun Fara komawa.


Ina Zama saiga matar nan ta dawo tana bala'i wai abincin wurin tsada.

Na mika mata awarata nace gashi;"tace a'a nagode nasiyo da kwai da kaji kayan wurin nan tsada gwara da baki saya ba wallahi shekara goma sha ina saida abinci nasan yadda harkar take amman sun nan saboda sun rena ma mutane wayo kamar ka roko"


Ta mikoman kazar nace;"a'a tabar shi nagode"

Tace;"ke kada kidamu ai kamar uwa nike wajen ki dan nabaki abu ai bakomi bane kuma abun kusa da bakii"

Daman miyau na ya cinke dan kusan wata kenan kullun cikin son kajin nike.


Na amsa na fara chii kallona take.

Tace;"diyata mijin ki rasuwa yayi ne?"

Na girgiza kai nace;"banda miji ai"


Kallona take har saida taga kamar na tsargu kana tayi murmushi tace;"To yanzu Katsina kike ko Bauchi"

Nayi shiru ta dafani tace fadaman diyata kila na iya taimakon ki dan duk wata Unguwa dake a Bauchi nasan ta kila neman dangin ki kikazo ko?"


Nace;"bansan kowa ba a Bauchi kuma banida 'yan uwa sai Baba na yana Katsina".


Murmushi tayi tace;"kada kidamu gidana akwai wajen zama zan rikeki har ki haife abinda ke cikin ki"

Nayi saurin kallon ta ta girgiza daga kai alamar tabbatar wa.

Tace;"yara masu kalar matsalar ki nasha rigesu kada kidamu munan ba komi bane zakiyi rayuwar ki cikin jin dadi kinji"


Murmushi nayi nace;"Nagode"

Naji Dadi sosai shikenan basai naje wajen Inna Rabi ba kilama aje nema na har chan saboda munyi magana da Shatu kila ta fadama Baba ga inda zani yanzu ko na huta shikenan.



Hankali ya dan kwanta cikin ma kila ta zubdashi.


Hakan yasa naci na koshi sai bacci.


Tadani naji anayi na bude ido a hankali naga matar nan ce tace;"muje har mun iso"


Cikin sauri na bude ido ba kowa motar tace;"muje nima har na tari Mai Napep din da zai kaimu kayana na ciki"


Na fito ina fitowa zobena dake kan jikina ya fado.


Nayi saurin dukawa na dauka.

Ta rike hannu na har mukaje wajen abun hawa.

Sai kallon abinda muka hau nike.

Naita kallon gari tare da mamaki yadda yake da kyau har muka isa wata unguwa gidan a bakin titi yake.


Ta bude na dauko mata kayan ta tace;"a'a da kinbar su keda bake kade bace"


Kunya naji na dukar da kai a kasa.


Ta kama kayan ta shiga dasu.


Ta nunaman wani daki tace;"ga dakin ki nan, daman na kori wata ne saboda butulci tayi man hadda kayan sawa amman kila sunyi maki yawa sai nakai nan makwabta a rage maki"


Nace;"Nagode"


Tace;"Suna na Asabe mai abinci, amman suna kirana da Hajiya, minene sunan ki?"


Nace;"Nanah"

Tace;"zan maki duk abinda nikeso kamar diyata, amman fa duk abinda nasaki zakiyi"


Nace;"insha Allah zan maki biyayya"


Tace;"to bari nasa akawo maki abinci dan nasan ciki akwai takura, shiyasa ma idan hankali ya kwanta nan da kwana biyu idan kina so nakai ki wajen likitina ya rabaki da shi"


Cikin murna nace;"yawwa Hajiya wallahi daman banson na haihu saboda inason komawa gida wajen Baba".


Tayi murmushi tace;"idan nayi maki wannan aikin ai nima ba tafiya zakiyi ba sai kin biya la'ada"

Bangane nufin taba hakan yasa nayi murmushi kawai na mike nanufi bandaki saboda yin alwala.


Na dawo na shiga dakin kallon dakin nike yayi kyau sosai hadda gado ga wajen saka kaya.


Rufin dakin mai kyau sosai ba kalar namu bane kasan ma bantaba ganin Shiba.


Nayi hamdala na saka Hijab naje inda abin sallah yake shinfide na tada Sallah.


Na gama biyan sallolina kana na linke abin sallah.


Naga abinci mai kyau ga kaji a ciki da ruwa a gefe.

Na zauna nacii na mike na fito.

Na iske wani yaro yana wanke-wanke


Nace;"Hajiya aida kin gyaleshi ni zanyi maki"

Tace;"Tafi ki huta ga gajiya atare dake, inada masu aikina ke aikin jawo customers amman ba yanzu ba saina rabaki da wannan abun na cikin ki kana".


Nace;"to nagode Allah ya saka da Alkhairi".


Na mike na koma daki na kwanta.

Na lumshe ido nace;"Allah na gode maka".

Jin motsin cikin yasa na aza hannu na bisa cibiyata.

Nace;"Shatu idan na rabu dashi ban maki aldalci amman kiyi hakuri".

Na kwanta na Lumshe ido ina tunanin magan ganun Shatu.


Mutuwa ake idan akaje zubda ciki........?
Sabo ne wajen Allah Kuma.......?
Anya zan iya kode na hakura nabar cikin nan, nasha abinda zai zubda min ciki amman yaki zubewa.

Anya ba akwai matsala ba.

Mikewa nayi na zauna bisa gado ina shafa cikina gabana na faduwa.


Kode nabar cikin nan na hakura dasu Baba?

Inason Babana yanzu mizan yi kenan??


*************

Bacci ya dauke shi yana farkawa yayi part din Momy cikin sauri.

Yana isa wajen Momy ya iske Momy a parloun ta.

Tsaye take tana kaiwa da kamawa wa a cikin parloun


Ganin har ya shigo bataji shigowar shiba yasa yake tunanin lafiya mike damun Momy haka har ya shigo bata san ya shigo ba kuma kamar hawaye take kode rasuwa akayi a family dinsu?


Yace;"Momy"

Cikin daga murya, tayi saurin kallon shi.


Cikin sauri ta iso inda yake ta kama duka hannayen shi biyu.

Tace;"please Anu zauna"

Ya zauna yana kallon ta mike faruwa ne da Momy itada zata bashi labari mai dadi antaho da yarinyar amman ya haka.


Momy ta kalleshi hawaye suka taru a idon ta tace;"sorry Anu kowa da kalar JARABTAR SHI WANNAN SHINE JARABTAR MU"



Kasa gane mitake nufii yayi yace;"Momy fadaman mike faruwa?"


Momy da kyat ta nemo na tsuwar ta motsa baki zatayi magana........



Qurrah
[2/26, 8:11 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *_JARABTAR MU*_







*_Written by-Qurrah✍🏼*_


*Page_45-46*



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


Addu'ar Shiga Bandaki.
(بِسْمِ اللهِ)اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبائِثِ.
(Bismil-lah) allahumma innee a'u'zu bika minal-khubthi wal-khaba-ith



DEDICATED TO.....MY SISTERS😘


Page_45-46

_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_



-----------------A hankali Momy tace; "Ta mutu jiya da daddare".


Saurin mikewa Anuwar yayi jikin shi har kyarma yake ya rike kanshi yana cewa; "No! No!! No!!! Please Momy kice wasa ne"


Ganin ta kasa motsi yasa yazo yana girgiza ta yana cewa; "Momy bana son irin wannan wasan kada ki sake pls taya zata mutu tabar ni kamar dai ni nafi kowa rashin sa'a a rayuwa Momy zanje da kaina sun yaudare ki basu jeba wallahi".


Momy ta miƙa mashi wayar hannunta ta danna wani Vedio.

Fuskar Inna ce ta bayyana tana kuka tana jan majina tace;"Ai munyi rashin Nana ɗiya tace tana da biyayya jiya tace man zata je wajen dangin Baban ta shine na barta ta tafi ashe ban kwana muka yi da ita".

Ta ƙara fashewa da kuka gwanin ban tausayi tana goge hawayen ta da Hijab din jikin ta tace;

"Tunda ta tafi hankali na bai kwanta ba, ashe tana zuwa ta iske yaran su zasu je yin icce ta bisu a dajin maciji ya sareta ta mutu koda aka kawo ta gidan su Babanta ta mutu".


Wani kuka Inna ta fashe dashi sannan tace; "yanzu haka saurin da nike chan zanje domin kuwa yanzu da safe aka aiko man, daman ita kaɗai ce gare ni hakan yasa idan na tafi bazan ƙara dawowa garin nan ba, zan tafi nima wajen dangina, nagode maku sosai".


Ta ida maganar ta a cikin kuka mai taɓa zuciya.

Wani irin ihu yayi ya buga wayar a bango ta tar watse.


Momy banda hawaye babu abinda take, ko motsin kirki ta kasa.


A fusace ya bar ɗakin yayi part din shi.


Yana zuwa ya kori hadiman shi cikin tsawa ya rufe ɗakin.


A bakin mirror ya tsaya yana kallon kanshi.

Yace;"meyasa ban da sa'a a cikin rayuwa ta ne? meyasa duk abin da naso sai ya nisan ceni? Nayi alkawarin bazan sake son wata mace ba ballan tana hakan ta kara faruwa dani".

Rike kanshi yayi idanun shi sunyi jawur tamkar garwashi.


Wata irin kuwa yayi, ya zudda kayan dake jere bisa mirron tare da kallon kan shi a mirror hannu yasa ya nushi mirror ya fashe ya zube ƙasa.



Ya kara buga hannun shi a bango yana kiran; "Why! Why!! Why!!!".


Hawaye suka zubo mashi rabon da yayi hawaye tun ranar mutuwar MANAL saidai fuskar shi da idon shi su chanxa amman ba dai hawaye su zubo ba.


Hannun shi na jini ga glas ya shiga jikin shi amman kamar ma baiga abinda ke faruwa dashi ba.


Kwankwasa ɗakin ake Momy ce dan yana jin muryar ta.


Toilet ya shiga yana son yin wanka bai san tayaya zai haɗa ruwan wankan ba ma.

Idan yana cikin ɓacin rai idan ya shiga cikin ruwa yana ragewa.


Tsaki yayi ya fita ya zauna a bakin bed ɗin shi.


Rike kanshi yayi dake masa zafi yayi.


Gaf! Yaji an bude kofa Momy ce tana maida numfashi kamar wacce tayi gudu.



**************

Na kasa fidda shawara guda na koma na kwanta ina shafa ciki na.


Ina kwanciya aka kira sallar magriba na tashi nayi sallah, sai ga Hajiya ta shigo tace; "mi kike so kici yanzu".


Nayi murmushi nace komai ma Hajiya.

Tayi murmushi tace;"bari asamo maki abu mai dan dadi".


Ta fita na cigaba da Azkar ana kiran sallah na mike nayi Isha'i.


Ina gamawa ta shigo da kayan abinci.

Ta aje a gaba na tace; "Gashi nan tuwon shinkafa ne miyar Ganye nasan zaki soshi ga gasasshen nama nan".


Nace; "Hajiya bani da bakin maki godiya nagode sosai Allah ya saka maki da Alkhairi"

Dariya tayi tace; "ba komai yima kaine".

Ta juya ta fita na sabko naji dadin abincin sosai naci na sha ruwa.

Na bude nacii naman sai kamshi yake sosai, naci na koshi, nayi hamdala naji cikina ya motsa na shafa cikin ina murmushi, lalle idan na rabuda shi shikenan zan koma wajen Baba.


Wani tunani nike yanzu fa saboda cikin nike cin kayan dadi gashi haramun ne zubda ciki idan na mutu yanzu wuta za'a sanii?.

Hankali na ya dan tashi nace; "wazan tambaya yanzu saɓo ne idan mutum ya zubda ciki??"


Shiru nayi na kasa fidda shawara, na hau gado na kwanta.


*************

Momy tace; "Anuu menene yaji ma kanka ciwo haka?? Kaifa musulmi ne kuma kasan Allah yana Jarabtar bayin sa, kila yarinyar nan ba Alkhairi bace shiyasa Allah ya amshi abunsa, kayi hakuri dan Allah kaɗau ki hakan kaddarar kace bawa bai isa ya kauce ma kaddarar saba kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka gobe za'a fara biki kayi hakuri ka daure kodan lafiyar Daddyn ka, sannan yanzu kasan su mai Martaba basu san da wannan al'amari ba, idan ka chanza zasu yi zargin wani abu, kuma kasan duk mai Martaba yaji ka taɓa yima karamar yarinya fyaɗe hankalin shi tashi zai yi sosai, ban san ya zasu dauki abun ba kayi addu'ar Allah yasa haka yafi Alkhairi sannan kasa ta a cikin addu'ar ka hakan shine soyayya".


Sai a lokacin ta numfasa tana kallon shi tace;"nasa anba iyayen ta kudi masu yawa wa'inda duk inda zasu je to zasu ishesu rayuwa na wani lokaci"


Kama hannunshi dake jini tayi tace;"taso muje part dina, a gyara dakin a chanxa abun da ka fashe ga hannun ka jini na zuba muje"


Mikewa yayi tana rike da hannun shi har suka isa part dinta.


Da kanta ta gyara mashi hannun shi taba shi magani ya sha.


A zuciyar Momy ta rasa ya zata yi ta so ta fada mashi gobe za'a fara bikin shi a Abuja, amman takasa ta yaya zata gaya mashi yana cikin wannan halin kuma idan ango baije ba akwai matsala ga hannun shi da raunii.


Ta gumi tayi ta rasa mafita akan al'marin Prince.

Tana zaune parlour sai ga daya daga cikin hadiman ta tashigo, kallon ta tayi cikin girmamawa ta duka tace;"sako ne daga Mai martaba"


A hankali tace;"ace mai sakon ya shigo"


Ta juya sai ga Sani ya shigo daman shi an saba dashi a ko ina, ya dukar dakai ya kai gaisuwa cikin girmamawa sannan yace;

"Mai martaba yana neman Yarima yace ya kira wayar shi bai dauka ba Allah yasa yana cikin koshin lafiya"



Tace;"yana lafiya Amman yana hutawa kace za'ayi mashi magana"


Tashi yayi yana godiya ya fita.


Mikewa tayi bedroom ɗin ta ta nufa inda tabar shi.


Yana tsaye bakin window hannun shi mara rauni yana cikin aljihu idon nan nashi jawur tamkar garwashi.


Momy ta isa inda yake tace;"Mai martaba yana neman ka, amman baza kaje ba, dan hankalin shi zai tashi idan ya ga rauni a hannun ka, nasa a chanza maka abubuwan daka bata, zanje part din Ammie yanzu"


Ta juya tabar shi nan.


A hankali ya furta meyasa iyayen shi ba zasu fahimce shi ba.

Runtse ido yayi yana istigifari meyasa yakasa yadda da mutuwar MANAL da wannan yarinyar mai fura?? A matsayina na musulmi bai kamata ace nakasa yadda na mutuwa.


Damke hannun shi yayi wanda yaji rauni, wani irin zafi yake ji amman kara damke hannun yake yana cije leben shi har saida yayi jini, sannan ya fara maida numfashi.


Momy ce da Ammie suka shigo ɗakin ganin abinda ke faruwa yasa suka yi saurin isowa.


Ammie tace;"Lafiya Yarima mike faruwa?"

Momy tayi saurin cewa; "kin gani baida lafiya ba zai samu zuwa Abuja ba gobe, yace man da ciwon kai ya tashi sosai kinsan halin shi da taurin zucciya shine fa ya buga hannun shi a glas"


Ammie tace;"Haba Yarima yanzu fa ka girma ya kamata ace kabar taurin ran nan, kamanta tayi man alkawarin ba zaka taɓa kara saka kan ka irin wannan abun ba"


Shiru yayi bai tanka ba saboda bazai iya magana ba.


Ganin Ammie na hawaye yasa yayi saurin rike hannunta yana kirgiza kai.

Rumgume Ammie yayi yana sakin ajiyar zuciya.


A hankali yace;"Ammie Uwa zata iya yima diyar ta karyar mutuwa?"

Cikin sauri Ammie ta ɗago fuskar shi tana kallon shi cikin mamaki meyasa yace haka?


Daga kai yayi, ganin abinda yayi yasa Momy cewa;"Anuu dina ya kamata ka huta hakanan kaji"


Rike hannun Ammie yayi yana jiran amsa.

Shafa sumar shi tayi tace;"duk wata Uwa dake duniya indai ita ta haifi diyar ba zata iya yi mata kazafin mutuwa ba, domin kuwa yi mata fatan mutuwa wani babban al'amari ne kaji ko"


Daga kai yayi Ammie tace;"miyasa ka tambaya ne, wani abu ya faru?"

Momy tayi saurin cewa;"a'a ya kamata ya kwanta ya huta kinsan ciwon Kai"


Mikewa yayi yace;"zanje dakina"


Daga haka yabi ta gaban su ya wuce su duka suka bishi da kallo cikin so da kauna

A tare sukayi ajiyar zuciya.


Yana zuwa daki yayi salloli ya koma ya kwanta.


Zafi sosai a jikin shi sai kyarma yake hakan yasa ya jawo blanket ya rufe jikin shi.



************

Ina bude ido naji ana sallolin asuba na tashi na shiga inda Hajiya ta nuna man tace bandaki ne cikin daki na.


Nayo alwala na dawo nayi raka'atanul fijir na zauna ina lazumi da hannu saida aka tada sallah kana nima na tashi na tada Sallah.


Ina gamawa na duba dakin ko ina babu alkur'ani nace a fili;"kila ba musulma bace Hajiya ta rika shiyasa tayi mata butulci tunda gashi ba Qur'ani a cikin daki, dan nasan musulma bazata iya zama daki babu Qur'ani ai bun kunya ne gareta"


Sai kuma nayi tunani nace kila kuma ta tafi da abunta bari safiya tayi na amso daya daga cikin na Hajiya.


Haka na zauna na fara tilawar na Kai har safiya ta waye.


Naji masu aikin Hajiya na aiki a tsakar gida.


Na mike zanje gaida Hajiya.

Ina zuwa bakin kofata mukayi kicibis zata shigo cikin dakina.

Na duka har kasa na gaida ta tace;"Haba Nana aini kamar Uwace anzama daya basai kinyi wahalar dukawa ba".


Nayi murmushi ta nuna man wani Abu tace;"ga wadirof nan akwai kaya ki duba a ciki naga bakida kiba wadan na sukayi maki saiki fidda kamin nadawo zan karo maki wasu wadan da sukayi maki yawa kuma ki ajesu waje daya idan nadawo kiban dan kada a tara maki tsumma"


Cikin murna nace;"lah Hajiya kibar su kala biyu ma sun isheni basai kin sawo man wasu ba"

Tace;"a'a nafison ki fito kiyi kyau, duk da kyaun ki ko wane irin kaya kikasa kyau suke maki ko tsumma ne bare sabbi, tunda nike bantaba cin karo da mai kyaun ki ga kuruciya shiyasa komi kikeso zaki samu"


Washe baki nayi nace;"Hajiya Nagode"


Tace;"bakomi yanzu za'a aiko maki da abinci idan bai maki ba ki fada akawo maki wani"


Ta juya ta fita na mike na buda inda ta nunaman nafara fiddo kayan duk babu kalar da nasani ganin kayan nike wasu iri ban taba ganinsu ba.


Atamfa a ciki kala hudu ne sai leshi daman bantaba daura leshi saide nagan shi jikin Yaya maimuna diyar Inna.


Cikin murna nike kallon leshin kara tabawa nike a hankali nace;"Yau nice zan saka leshi?"

Kara tabawa nike ina juya nace bama kalar nasu Yaya maimuna ba wannan yafi kyau.


Kayan sunada yawa sosai inagama fiddowa na mike zan gwada leshin doguwar rigace amman ga mamaki ba kalar dinkin garin mu ba wannan tun daga sama har kasa fadin su guda kallo nike cikin mamaki.


Ina kallon ta saiga Hajiya ta shigo cikin shiga Mai kyau sai kamshi take tana tamnar cingam ga gilashi a idonta hannunta rike da jikka Mai kyau.


Sakin baki nayi Ina kallon ta tace;"Na shirya zani cefane kasuwa kin gwada kayan ne, dan nasan kala nawa zan kara".


Cikin sauri nace;"yanzu zan gwada".

Tace;"saka black and maroon din les din hannunki abu ga farar fata nasan zai maki kyau sosai gashi yanada tsada"


Banson yadda zan saka ba dan mamaki nike ai wannan rigar idan nasaka ta zata matseman jiki kila ko numfashi ban iyawa.


Ta mikowan wani Abu tace;"ga towul nan cire kayan ki kisaka".


Na amsa nayi hanyar bandaki tace;"ke ina zaki bade cire kaya ba to aini macece ko zindir kina cire kaya a gaba na".


Na dukar da kai saboda ban iyawa.

Karatun Baba na tuna akan tsiraici.

Taya zan fada mata komu mata haram ne kallon tsiraicin juna.


Tace;"lalle kanki na cikin kwali tafi ki chanza watarana a gaba na zakiyi zindir"


Nayi gaba na shiga banda cikin raina nace;"Allah ya rabani da nuna tsiraici na ga kowa"


Na cire kayana na daura wannan Abun naga duk cinyoyi na a waje.

Nadade saida naji tana cewa;"lafiya Nana naji shiru"


Kana nayi shahada na fito ina matse kafafuna.


Dan karamin tsoki tayi tace;"nifa banason kauyan ci wallahi zanyi fama kenan?"


Ta mikaman tace;"Ina bireziyar ki?"

na dukar da kai saboda kunya saida ta maimaita kana nace;"A garin mu sai anyi aure ake sakawa "


Ta kalleni naga gabana take kallo na, naji babu dadi kafafuna har kyarma suke.

Ni kaina kwanakin nan naga gabana yayi girma sosai ya ciko shiyasa kullun gidan Inna da Hijab nike yawo dan gabana har yafi na Ma'u sosai kuma basu Dade da yin haka ba.


Wani wuri ta buda saiga bireziyoyi da yawa da wando sun fito ta dauko guda.


Tace;"saka"


Nace;"ban iyaba bansan ya ake sakawa ba"

Ta matso kusa dani ta dauraman tace;"kinga yadda nayi gobe ke zaki saka da kanki"


Na daga kai ita ta nunaman nasaka rigar.

Tace;"zage zip din"

Nace;"ban iyaba"

Tace;"lalle ba karamin daji kika fito ba"

Tazo ta saka man Zip na kalli kaina rigar ta matseni tun daga sama har kasa kirjini sun fito sosai sunyi sama kusan rabi duk a bude.

Tace;"yi tafiya nagani zaki iya yin tafiya cikin street gwon"


Ina takawa naji kamar rigar ta barke na juya naga wajen kafata ne a baya duk ta bude har kusan kinyata.


Nace;"bayan rigar ya barke ana ganin jikina"


Tayi murmushi tace;"haka dinki yake wallahi ban taba ganin wadda kaya suke ma kyau kamar ki ai duk kyawun ki dakika saka kayan nan sai naga ada banga komi ba tobarai na

Please Login or Register in order to submit comment