Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hadisai da kisso shi.

Littafi yayi dadi sosai komai yabi shi daki-daki.

Juya bayan littafin nayi,dan ganin sunan littafin,FANNUL TA'AMULI BAINAR ZAUJEN,murmushi nayi nace"lalle Baba na sona duk abinda yasan zan karu shiya keyi man,ko ya azani hanya,ina mai bukatar a barni na zabi miji,mai irin suffofin da mai littafin nan ya saka,ba irin Lado,da ace kowa ce mace zata karanta tashi lalle kam da ta karu da yawa.



Ya kamata iyaye su sani koda addini ya basu damar zaba ma 'ya 'yan su miji,to hakan ba yana nufin kowa ne namiji ba,ai addini ya bada kalar mijin da ya dace,yanzu idan aka aura man Lado,Inna bata tunanin mako mata da yaran da zan haifa.

Anya nayima yaran da zan haifa adalci,idan na zaban masu Lado a matsayin Uba??

Shiru nayi ina tunani lokaci guda hawaye suka wanke man fuskata.


************
Wanka Kursim ta fito,cikin sauri na shirya,ta kira ma aikatan part dinta,tabasu gyaran zogalan suyi mashi hadi kamin ta dawo.

Ta wuce part din Umman ta cikin fargaba mizata ce mata game da raunin fuskarta.

Tana isa masu kula da part din Umman ta suka ce tayi wajen Abban ta,hamdala tayi dan batason Umma tasan akwai matsala,dan tasan halin Umman ta yadda take sonta ace wani ya fitar mata jini,kila idan Umma taji,tasan bazata barta ta auri Annuwar ba.


Waya tayi aka kawo mata zogalan,ta kalli zogalan yayi kyau kamar wani abincin kasar waje.

Tace"Nasan zaka soshi,tunda ita komi nata mai dadi ne,lalle wadan nan mutanen Aljanu ne"kai tsaye tayi sashen shi.

Kaf..!!sukayi karo,saura kadan zogalan ya zube,tayi saurin rikewa,tare da ja daga baya!!

Kallon shi take cikin mamaki!!

Tace"Ina zakaje bayan ruwa akeyi tun dazun??kuma ai daka kirani nazo na kaika"juyawa yayi ciki tabi bayan shi.


Zauna tayi kusa da kujerar da yake zauna,ta aje mashi zogalan,tace"gashi nan na kawo maka"kallo yabi zogalan dashi,kamar baita ba ganin zogala ba.


Spoon ya dauka yafara chii,yana ya mutsa fuska kamar.

Yana tamnewa sai yayi murmushi,yana kallon zogalan.

Mutuwar zaune Kursim tayi,lalle sun gamu da Aljanu.

Miyasa yake son komi nata??hadda zogalan ma,hadda sakar ma zogalan murmushi,lalle zata saka a bin cika mata mutane ne ko Aljanu.

Inama Hanan zata gane,maganar da take fada mata da gaske ne,akwai matsala fa akan mai furar nan.


Koka min ta gama tunanin da take,har ya chinye babu komi.

Cikin sauri ta zuba ruwa ta aje mashi,baiko kalli ruwan ba.

Dauka tayi ta mika mashi ya amsa,tareda sakar mashi murmushi.

Juyar da fuskar shi yayi wani waje.

Yana gamawa ya mike tsaye,ya juya zaiyi hanyar bedroom dinshi.

Cikin sauri tasha gaban shi,ta langwabar da kai,ta reda da aza kanta bisa kirjin shi,tana shafawa tace"please Prince mu koma mu zauna fira fa nazo muyi,kuma inaga har yanzu ba'a dauke ruwan ba"tana maganar kamar zatayi kuka.

Tana gamawa yasa hannu ya fizge ta daga jikin shi,ya saketa ta fadi TUSS...!!


Yayi gaba kamar ba mutum yayi ma haka ba.

"Wash"Kursim tace,tayi saurin tashi daga faduwar da tayi.

Tabi bayan shi,lokacin har ya shige cikin daki.

A bakin Wadirop ta iske shi,zai cire kayan jikin shi.

Yana cire rigar suka hada ido.

Kallon shi take tamkar yau ta fara ganin shi.

Cikin sauri ya maida rigar ya tako inda take tsaye.

Ganin yadda ya chanza yasa hankalin ta tashi.

Kuma yanzu mitayi mashi??

Kallon ta yayi tun daga sama har kasa kana yace"ke wace irin mutum ce??na tsani ta kura,bani son a cika matse man,sannan dan yana gidan ku zaki shigoman daki bata reda naiman izini ba,haka aka koya maki"kallon shi take idon ta cike da hawaye.

"Bana son ganinki kada ki kara shigo man daki inba da izini na ba,idan nan gidan kune,banda iko dashi saina kama daki a Hotel"kuka Kursim take sosai wannan wane irin kaskan cine??

"Fita"yace cikin tsawa!!

Cikin sauri tabar dakin tana kuka da gudu.

Zama yayi bakin bed dinshi ya rike kai,mizaima yarin yar nan tabar zuwa inda yake.

Jinshi yake tamkar wanda yayi shekara.

Wayar shi ya dauko ya danna kiran Abie.

Yau kamar zaiyi kuka,babu ko gaisuwa yace"Abie wallahi zan maka biyayya akan duk abinda kace,amman kabar ni nadawo gida na gaji"shiru Abie yayi.


Sai chan yace"wani abu akayi maka?"cikin sauri yace"a'a kawai dai ban saba da garin bane"Abie yace"to ai bakayi abinda aka turoka ba dan har yanzu banga alamun so ko shakuwa ba".

"wallahi Abie zanyi duk abinda kakeso na tuba"cikin sauri Abie yace"harda auren Kursim kenan"shiru yayi ya kasa magana.

Abie yace"nabaka nan da kwana biyu kayi tunani"daga haka ya kashe wayar.


Shiru yayi ya rasa abinda ke mashi dadi.

Bayan yayi shirin kwanciya bacci yaki zuwa.

Tashi yayi ya tsaya bakin window yana kallon taurarin dake a sama.

Yarasa minene mafita yanzu.

Kode ya amince idan antashi auren ya gudu yaje wata kasa ne?.

Haka za'ayi,sai kuma ya tuna wani abu sai yayi tsoki.


A ban garen Kursim tana komawa korar masu aikinta tayi ta fada tsakiyar gado tana kuka.

Lalle kam duk wahalar da take,bazai taba sonta ba.

Baita ba yaba mata ba kullun a kwayar idon shi idan ta kalla babu sonta a ciki ko kadan.

Haka tayi ta kuka har dare yayi nisa.

Kode ta yafe Prince dan babu alamun sonta gashi bai dauke ta da daraja ba,bata da muhimman ci kenan a rayuwar shi.

Kila idan na aure shi ya chanza,to taya zan aure shi??

Haka tai ta ihu ita kade tana bazan iya ba!!

Har barawo bacci yayi gaba da ita.

A ban garen Annuwar ya kasa samun mafita har dare yayi nisa

************

Koda na tashi da safe yauma kamar kullun nasan aiki na,haka nayi nagama,na fara aikin fura.

Na daka sai ga Ma'u ta fito daga dakin Inna tana mika tare da hamma,ta kalle tace"Nanan duwa"nayi shiru tasan na tsani sunan.

Tace kibar wannan abun kizo ki sayawo man waina tashar Ado.

Nace"amman ai'kin ga aiki nike,sauri nike da fita tallah da wuri,gashi zanje diban zogala"shiru tayi tana kallo na,yaushe har nayi bakin da zan fadi mata magana.


Juya wa tayi cikin sauri ta koma dakj,sai gata ta fito tare da Inna.

Wata katuwar muciyar tuwo Inna ta dauko tayo kaina tana fadin.

"Daman jiya da bakin cikin ki na kwana na rashin zuwan Lado,kuma yanzu dan na kyale ki shine zaki bata ma yar tawa rai,yarinya mai Uwa da Uba,dakuma gata gaba da baya,shine saboda bakin ciki kike so ta zauna a cikin hawala,yunwa ta kamata da gatan ta"ganin da gaske tayo kaina tana kara fadin"ai gwara na sabattaki da ki sabatta min ita da yunwa,ko kin mutu Uban ki kade keda takaici,itafa?"

Nayi hanyar waje ina cewa"Dan Allah Inna kiyi hakuri"ganin idon ta ya rufe yasa nayi saurin fita.

Tace"idan kika fita,kika dawo kinsan sauran kizo ki idaman fura ta,yar bakin ciki da Lado yazo jiya,niyyah ta yau ko tallah bakiyi,dan yadda Lado ke kashe ma Mace kudi idan yana neman aure shine ni kike mani bakin ciki,to wallahi gwara na sabatta ki,dawa ne bakin ciki zanji kenan?kibata man kibata ma diyata baki isa ba zaki dawo ki iskeni".

Nide ina lade jikin katan ga inajin ta.


***************

"Morning Princess Am back wooo"ta ida maganar cikin waka.


Yadda taga Kursim yasa tayi saurin karasawa bisa godan!

Bubbuga bayan ta take tana cewa"Kursim Hanan ce bude idon ki,miya same ki"a hankali Kursim ta bude ido tana kallon Hanan.

Da fuskar ta wadda hawaye suka bushe.

Jikin Hanan Kursim ta kwantar da kanta tace"Hanan ina tsanar kaina saboda son da nike mashi,bazai taba sona ba,kiyiman addu'a,Hanan yace kada na kara rabar shi,baison ganina,dami zanji da son shi,koda kiyayyar da yake man?"ta ida maganar cikin kuka.

Hanan tace"miya farune?"nan Kursim ta fada mata komi.

Cikin sauri Hanan ta zame jikinta ta mike tsaye!!

Idon ta sun rufe ranta a bace"Kursim tace minene haka ina zaki?"kai tsaye tace"Umma zan fada mawa,chin kashin yayi yawa koda ke ba Princess bace,wulakan ci yayi yawa,baison darajar dan Adam ba,Umma zan fada mawa nasan zata taka mashi burki,yasan dawa yake tare"cikin sauri Kursim ta rikota tace"ki rufaman asiri kada kowa yaji,wannan sirri nane,nafa da maki,idan har kina sona da gaske,kawai kitaya ni da addu'a,idan kuma kika fada ma Umma baki man adalci ba,kinfi kowa sanin Umma".

Dawowa tayi ta zauna tare da yin tagumi ranta a bace.

Kallon Kursim tayi tace"wallahi na rantse maki,sai Prince ya duka da kafar shi yana rokan ki,akan ki aure shi,kiba shi jikin da yake wulakan tawa,sai ya nemi hada jiki dake,na rantse naki"shiru kursim tayi.

Tana tunanin taya za'ayi hakan ya faru,lalle kam har yanzu Hanan bata san waye Prince ba.

Taya za'ayi ya duka mata har yana rokan ta,wannan maganar bazata yiyu ba.

To amman mi Hanan zatayi ne??


*************

Tashi nayi ina lekan Inna dake tsaye da muciya taki koma daki.

Nasan idan Inna ta buga man,muciyar nan kila ai ban iya tashi.

Yanzu ya zanyi kenan,gashi Inna batajin lallashi idan ranta ya baci zuciyar ta makan cewa takeyi.

Ju yawa nayi,karaf idona suka hadu dana Lado!!

Yana bisa jakin shi,rike da sanda wadda yake bugun jakin da ita.

Washe man jajayen hakuran sa yayi,yana niyyar sabko wa.

Haba ai bansan lokacin da nayi cikin gida a guje ba.

Nafisan azabar Inna akan kallon Lado.

Kaf...!!mukayi karo da Inna!!

Zaroo ido nayi waje tamkar zasu fito...!!

Qurrah
*JARABTAR MU*




*Written by Qurrah*


*~Page-19-20~*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*~Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.~*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


DEDICATED TO....MY SISTERS😘


Page-19-20



_Bissimillahir Rahmanir_ _Rahim_



----------------Mari ta kai man,wanda saida na duka kasa,ina ɗagowa ta sake marina a dayan bangaren kumatu na.

Na dafe kunci tare da sakin wani irin ihu.

Lado ne ya shigo zauren da gudu!!

Ganin shi yasa Inna ta fara cewa "yanzu ki samu miji kamar Lado a garin nan shine zaki dinga gudun shi,duk garin nan wake kashe ma mace kudi kamar shi?Dan Allah kayi hakuri Malam Lado,kila ma kunya ce tasa ta gudu,amman aiba halinta bane"

Washe katon bakin shi yayi tare da wasu jajayen hakoran shi da goro ya ba ta hakuri yace ba komai ,yana sosa keya yace"kada adamu Inna ai babu komai ,sai a hankali zamu saba"


Sakin baki nayi ina kallon shi,tsoho kamar wannan yana duka ma Inna,ko kunya baiji ba hadda su cewa Inna.

Hannu ya saka a cikin dauɗaɗɗiyar rigar shi da tasha faci,ya dauko jakka biyar(dubu Daya) yaba Inna.

Jikin Inna har kyarma yake wajen amsa,tare da cewa "kai Malam Lado basu yi yawa ba" kara washe baki yayi yace "kada kidamu ban son ta fita tallah ne yau".

Kallon banza nayi mashi,taya za'ayi mutumin dake jan jaki yayi wannan kyautar,ga matan shi chan su ne suke ciyar da kansu,yaran shi tamkar almajirai haka zaka gansu, Allah dai ya shirya wasu mazan,kallar su Lado,gida bai koshi ba ankai waje.


Dunguzar da Inna tayi min tasa na dawo daga duniyar tunanin da nike tace "bakiji yana magana tun dazun? Matsa "ta turani har saida na kusa fada mashi.

Kana ta dunga godiya har kasa takai,ta harareni ta shige ciki,tabar mu a zaure.


Kuraman ido yayi yana kallona,yana lasar labban shi tamkar wani maye sai kara matsoni yake.

Sai a lokacin na kalli jiki na,riga da zane ne,saman rigar ya matseni sosai,komai nawa yafito fili,kusan ma rabin kirjina a bude yake, saboda yadda rigar ta kamani.


Cikin sauri na warware Dan kwalin kaina,nan gashina ya bayyana baki silik,ga doguwar jela data sabko bisa baya na,da ɗan kwalin na rufe gabana.

Kasa magana yayi sai wani in-inah yake,yana kara lasar bakin shi,yana zaro ido,ƙut kakeji yana hadiye miyau.

Daya matso sai in gusa,da kyar ya iya furta"nikam bazan iya jira ba,nan da sati guda nike so a kai man ke,zan baki kulawa kinji,dan idan na aure ki sai nayi wata ban fita ba,zan maki komai kike so kinji"


Kara ɓata fuska nayi na turo baki,jikin shi har kyar ma yake,yasa hannu zai tabo bakina.

Nayi saurin matsawa tare da sakar mashi harara tamkar kwayar idona zata fado.

Yace "kiyi hakuri yar gidan Liman,wallahi komai naki kyau gare shi,kin san yanzu dole na koma gida ban iya zuwa wajen aiki,jikina har kyar ma yake "ya fiddo kudi yace "ga wa'innan duka ki dauka,kibar ni ko taba ki inyi naji sauki,har da bakin nan duk garin nan babu mai irin shi sannan ga..."daga mashi hannu nayi nace ya isa haka.

Dan nasan kirjina zai ce,na kulle su da ɗan kwalina amman yadda yake kallon wajen tamkar ya samu wani abun kallo.

Ya miko man kudi,nace"wallahi koka fita cikin zauren nan ko nayi maka ihu kwarto,yadda har gidan ka sai sunji,kuma su fito na nunaka,kuma kasan harda matar ɗan ka"

Cikin sauri yace" Allah ya baki hakuri,duk me yakawo wannan daman dadin mu naso muji,na dauke maki wannan wahalar da kike ciki,kullum nazo na dinga biyan Innar ku,tabar aza maki tallah"kallon shi nayi.

Nace "nafison wahala ta kashe ni da inyi abinda kake so ,niba jahila bace, ba zan saba ma mahaliccina ba saboda abin duniya,kaje chan ka nemi dai-dai dakai"

Magana nike amman har yanzu ya kasa dauke idon shi daga kaina,kuma da alama magan ganuna basu yi mashi zafi ba.

Washe hakora yayi yace"zan tafi zan turo maki da sako kinji? kici fa kada kibari wani yaci "ganin yadda yake wani kara matsowa yasa nayi ciki da gudu.

Kici bis mukayi da Inna!!


***********
Kwance yake cikin bargo saboda yadda kan shi ke mashi ciwo,jiya kasa bacci yayi saboda rashin samun mafita.

A tunanin shi Kursim zata shigo, saboda yana son furar nan,kuma yasan tana da ita, shiru-shiru babu Kursim har rana tafarayi,gashi sosai kanshi ke ciwo, runtse ido yayi saboda yadda kan ke ciwo.


Gashi shi kaɗai ne a part ɗin shi,tun jiya yace bai son kowa sai idan shi ya kira su,hatta Sani da kullum suna tare sai idan yana tare da Kursim,shi kaɗai ke raba su.


Wayar shi ya jawo,ya shiga Call long dinshi, number Kursim yake nema yasan tana kiran shi,sau daya ya taɓa daukar kiranta,tunda yaji itace bai kara dauka ba,amman duk da haka kullum cikin kira da Message take.


Kallon number yake amman ya kasa kira,sai ma tsakin daya ke faman yi.


Kashe wayar yayi baki daya,ya juya ya runtse ido.

Yanzu laifin iyayen shi yake gani,saboda me zasu kawo shi a nan?


Wanka Kursim tayi,Hanan tasa aka shiryama Kursim abinci.

Tare suka zauna bisa kujerun Dining table,da kanta Hanan ta zubama Kursim abinci.

Kallon Kursim tayi da tayi tagumi,cire hannun Hanan tayi,kana Kursim ta kalle ta.

Dan karamin tsaki Hanan tayi,ta cigaba da chin abincin.

Har ta gama Kursim bata ko taɓa abincin ba.

Hanan ta dauki wayar ta tayi kira"Hello akwai jirgin da zaije Abuja yau?"kallon ta Kursim tayi cike da mamaki!!

Sabke wayar tayi,ta dauki hand bag ɗinta tace"zan je gida,daga chan na wuce Abuja yau babu jirgi sai gobe,zanje a chan na kwana,sai anjima"dafe kai Kursim tayi.

Tace"Haba Hanan saboda matsala fa kika zo kuma shine zaki koma,bayan komai ba muyi ba,idan kika barni dawa zanyi shawara,Umma ce kuma kinsan halinta,ki taimaka min"rike jakar ta tayi.

Dawowa Hanan tayi ta zauna bisa kujerar falon Kursim.

Tace"wallahi Kursim ban iya daure wa,zuciyata zafi take min,meyasa zakiso wanda baison ki,bayan ga mutane da yawa suna bukatar soyayyar ki,kiyi tunani,bawai ban son soyayyar ku bane ba,a'a nima ina maki fatan kisamu abunda kike so amman wulakan ci yayi yawa,gashi yau saboda baki ganshi ba kin kasa chin abinci,duk kinman ta wulakancin da yayi maki jiya"shiru Kursim tayi.

Da fata Hanan tayi tace"ya kamata yau kada kije inda yake,dan yasan ya maki laifi,kuma ai karema yana da rana,wallahi a yau sai yayi kewar ki,mutum fa ance rahama ne, please ki daure"dariya Kursim tayi.

Tace"I can't do that"zaro ido Hanan tayi,dariya Kursim tayi tare da bugun bayan Hanan.

Tace"Ohh sorry My Friend Am just kidding"dariya Hanan tayi.


***********

Kunne na Inna taja kamar zata cire,zanyi kara ta tushe man baki,ta ja ni ciki,ingizani tayi na fada akan turmi.

Tace"Amman wannan diya da wulakan ci kike,yanzu ina kallon an baki kudi,amman ƙiri-ƙiri kika ƙi karba, saboda kada na amfana da ke,yan kudin da nike so na tara,na saima Ma'u samiru da tasho shi dasu kike ma bakin ciki,kada na fidda diya ta kunya ko?"


Cikin kuka nace Inna jikina fa zai taba.


Mari takaiman tace"duk iskan cin da kikeyi idan kinje tallah kina dawowa da kudi, saboda su a hannun ki kike ajesu,shiyasa su ba zaki hanasu ba,sai Lado,duk iskan chin shi, bazai yishi cikin zaure ba,iyakar shi ya shafe ki,to miye a ciki tunda ya aje maki kudi,daman tunda naga yana lasar baki nasan za'a rina addu'a nike tayi Allah yasa ki bashi haɗin kai, ashe saida kika yi halin naki na bakin ciki "kuka nike sosai.

Nace"Haba Inna hakan mafa zina ne,mutane ke daukar wannan ba komai ba ,amman wallahi haramun ne,namiji ya taɓa jikin mace,Inna duk kan gabobin jikin mu ranar gobe kiyama duk sai sun bada sheda akan mu,hakan dakike dauka ba komai ba,to wallahi Inna Zina ce,bata yadda kike tunani ba, sannan ba ta yadda kika san ake Zina ba kawai a fili ba, to zina harta Ido akwai,wallahi Inna bazan iya ba "Kalamaina mai makon su saka Inna tayi laushi saima har zukata da su kayi.

Ina gamawa takaiman bugu a baki tace"har kin isa kice zakiman wa'azi, saboda tsabar bakin ciki irin naki kada na fidda diyata kunya,to kudi sai kin samo su,yau ba zaki fita tallah ba dan kada Lado ya ganki,amman kishir ya gobe dana yau dana gobe zaki hada"shiru nayi na wuce na isa wajen daki na,na ci gaba.


Da cewa "da ache inada Uwa na tabbata bazata aikeni zuwa aikata Zina ba,mutane suna daukar hada jiki da namiji ba komai bane ba,sun manta Ubangiji haka yace kada mu kusanci Zina,kusan tar ta ma haramun ne inaga aikata ta,ta kowane irin yanayi ana aikata Zina,jan dogon numfashi nayi,inama ace inada mahaifiyar da zata azani akan turbar gaskiya".

Ya Allah kasa na zama uwa tagari ga 'ya'yana.

A hankali nike dakan saboda jiki na babu kwari.


***********
Sai wajen azuhur ya farka daga barci,ya mike waya ya kira Sani yazo ya hada mashi ruwan wanka.

Bayan ya fito sallah yayi ya shirya cikin kananun kaya.


A falo ya fito ya zauna abinci aka hada mashi a gaban shi.

Haka ya yini,lalle maganar Hanan gaskiya ce mutum rahama ne, saboda yau Anuwar jinshi yake yau garin yafi kullun rashin dadi saboda yadda ya yini shi kaɗai.

Hakan yasa tunani yayi mashi yawa.

Lambun kusa dashi ya fita,yayi tsaye hannu cikin aljihu yarasa me zaiyi ya gaji da garin nan laluba wayar shi yayi yakira Abie yace mashi shi dai ya amince gobe ya koma gida.


Ya laluba aljihun shi babu ita.

Dan guntun tsaki yayi,ya tuna tana daki,kuma a kashe.

Hanyar dakin shi ya nufa tare da tunani iri-iri shi dai ya rasa mafita, amince wa da auran Kursim shine mafita.

Tsaye yayi yana tunanin kamar zaiyi missing din wani abu.

To minene kenan???


Kursim zaune suke a falon ta Hanan na bata labarin abinda ya faru Abuja,daga kai kawai take hankali ta baya tare da ita.

Tana son ganin Anuwar ta kowane hali.

Waya Hanan ta dauka ta latsa Kira.

Tace"Hello Doctor,kaga message dina ina bukatar medicine din da na rubuto maka, okay babu a Katsina sai Legos Ina bukatar ayima order dinshi yanzu,ina bukatar shi a yau"Kursim kallon ta tayi kowa ne magani ne babu a Katsina sai Legos??

Tsaki Hanan tayi tare da cewa"why dis question"sai tayi tsaki ta kashe wayar.

Kursim tace"Hanan wane magani ne babu katsina har sai Legos?"tsaki tayi tace"manta kawai"Kursim bata damu ba suka cigaba da firar su.


************

Ina gama aiki na kaima Inna bako ta kalleni ba, saboda wai inama 'yarta bakin cikin samiru,idan abin kirkine tasa 'yar tata mana.

Daki na koma naje nayi wankan tsarki,naji dadin samun tsarki,ina son daukar qur'ani dan dashi kaɗai nike samun sauki.


Daki na koma na gabatar da Sallah.

Addu'a kawai nike Allah ya maido da Baba lafiya,ko mike faruwa bai dawo ba,anya lafiya??

Hakade nayita tunani.

Nafito zanyi alwallar isha'i,Inna ta fito da alama fita zata yi ,tunda matan kauyan mu na aure basu fita saida daddare.

Tace"kinsan Lado yace zai zo ko,to bari duk abinda ya kawo ko lasawa kikayi,sai na shaƙe ki ya fito,ki kaima Ma'u ta aje tana daki"kai na daga.

Ta fita tana bala'i tana kara fadin idan naci sai ta shakeman makoshi.

Ni dai naje nayi Sallah,ina gamawa saiga yaro ya shigo ana kiran Nana.

Cikin sauri Ma'u tace kace gatanan.

Ma'u ta shigo d'akin ta zauna bakin gado tace"Nana ana maki sallama,kuma ina ga Lado ne"shiru nayi raina a ɓace.

Tace "Haba 'yar kanwa ta tashi mana kada Inna ta iskeki kinsan sauran,kuma duk abinda ya baki ki amso kinji kanwata"shiru nayi ina kallon Ma'u.

Lalle duk turbar da Uwa ta aza diyar ta dashi take tashi,duk halin su daya da Inna,ta riga ta azata akan kwadayin abin hannun wani,wai yau Ma'u kece man kanwa magana cikin lalama,saboda kwadai.

Tashi tayi sai gata da wani gyale mai kyau,ta mikoman tace"saka shi kitafi,har mutunen ki nasaka maki(turare) kinji"har ta juya sai ta dawo tace"kada ki yadda ya bata maki rayuwa,kada kisakar mashi jikin ki,wallahi garin nan,idan mace tayi cikin shege korarta ake,kada ki yadda,kuma kada kice ma Inna nace maki wani Abu kinji"daga kai nayi.

Lalle ashe Uwa ke koyama diya hali marar kyau kenan,kila Ma'u ba halin ta bane,Innar ta ke koya mata.

Tare muka fito har bakin zaure ta rakoni tace"kinji abinda na fada maki,kila Inna so take a kore ki daga kauyen nan,shiyasa tayi haka ki kiyaye kodan Baba"kai na daga tare da murmushi,yau itace rana ta farko da Ma'u ta yiman abin arziki.

Na shiga cikin zaure ita kuma ta juya cikin gida.

Har kasa na duka nace ina wuni ya amsa yana washe hakora.

Laidar hannun shi ya mikoman yace"kici kaza ce kada ki sam ma kowa,kinga tasu Inna cikin bakar leda,gobe zan dawo,ya fiddo kudi yaban"

Na amsa nayi godiya yace "banson godiya nide burina kici kazar nan ke kadai "na daga kai.

Yanzu kam mamaki yaban,bai wani tsaya kallo na ba,ya juya yace sai ya dawo gobe.

Nace kila Allah ya shirya shi,tunda Allah shike shirya bayin shi.


Ina zuwa na kaima Ma'u duka nace a jema Inna tace "kidau leda guda mana tunda leda biyu ne"girgiza kai nayi,na wuce dakina.


Man tawa nayi ashe gyalen Ma'u ne,dakin su nayi,ina shiga na iske Ma'u ta bude kazar ledar da yace tawa ce tana chi.

Kallon ta nike tana chi hankali kwance sai kuma na tuna ai yace kada na sake naba kowa.

Innalillahi!!

Cikin sauri na fizge ledar!


Inna ce tayi sallam ta shigo ta iskeni rike da leda, Ma'u dai kallo na take cikin mamaki!!

Shiru nayi tomi zance ma Inna??

Towai ma meyasa yace inchi ni kadai??

Mike cikin kazar ne??


Qurrah
*__JARABTAR MU*__



*Written by Qurrah*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



DEDICATED TO....MY SISTER'S😘


Page-21-22






Falalar Tasbihi, Da Godiya Ga Allah, Da Yin La ilaha Illal Lah, da yin Kabbara

Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, ya ruwaito cewa; Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; wanda ya ce;
سُبْحَانَ اللهِ الْعَظِيمِ وَبِحَمْدِهِ.
Subhanal-lahil azeem wabihamdih.
(sau dari)
... A rana, za a kankare masa zunubansa ko da sun kasance kamar kumfar teku ne (wajen yawa).

Abu Ayyub Al-Ansari, Allah ya yarda da shi, ya ruwaito daga Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, cewa ya ce: "Wanda Ya ce;
لاَ إِلهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ. (عشر مرة).
La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, wahuwa 'ala kulli shayin

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai; babu abokin tarayya a gareShi. Mulki ya tabbata gare Shi kuma Shi mai ikone a kan komai.
(sau goma).
To kamar wanda ya 'yanta bayi hudu ne daga cikin 'ya'yan (Annabi) Isma'ila.


Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi, ya ce; "Akwai wasu kalmomi biyu masu saukin fada a harshe, masu nauyi a kan mizani (na ayyuka ranar kiyama), masu soyuwa ga (Allah) mai yawan jin kai (su ne).
سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ

Please Login or Register in order to submit comment