Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyau kadaicewa da mace".

Kallon shi take daman yana da ilimi ko dai dan bai son ta ne??


Kashe ido tayi cikin shagwaba tace, "Prince gidan bai maka bane? Amman nan gefen gari muke, daga nan sai University's din Katsina sai fita gari".

Hanyar mota ya koma tabi bayan shi.

Bude mashi motar tayi ya shiga ya zauna ta rufe, ta koma ta tada motar suka fita.


***************


Yau ma kamar kullum inda muke zama muka zauna, Shatu tace, "Allah yasa mu sai da da wuri muje cikin gari kamin Jabe ya dawo".

Muna nan zaune yau kam babu kasuwa.


Gashi lokaci sai tafiya yake Shatu tace; "yau babu kasuwa saboda dan sanyin da aka tashi dashi, kin san ba kowa ke shan fura ba idan akwai dan sanyi".

Mike tayi da kwaryar Nonon ta tace, "muje".

Kallon ta nike cikin mamaki nace; "amman fa kinsan bamu saida ba, kuma kin san Inna ba tada uzuri ko kadan".

"Na sani amman duk masu sayen furar mu, sai suce yau basu sha akwai dan sanyi, kin ga idan muka shiga binni kila mu samu masu saye ko, nima so nike ki saida ko dan Inna, ki samu raunin jikin ki ya warke kamin tayi maki wani".

Cikin amincewa da murna nace lallai Shatu na sona, nima na mike da kwaryar furata nace, "muje mu gani".

Tafiya muke har muka iso wajen wata makaranta inda muka ga maza da mata, wasu na shiga wasu na tsaye, kallo na bisu da shi dan ganin su nike wasu mutane na daban.

Shatu ta fini wayewa saboda da ita ta saba shiga burni, ni ko yaune rana ta farko da na tsallako burni.

Saida Shatu ta rike min hannu saboda yadda jikina ke kyarma, ganina nayi tamkar wata duniya naje, wai dama haka Burni yake da kyau?? Ya Allah yasa muna da rabo a gidan Aljannah, dan ni da birni sai gani sai hange, lokaci guda imani ya kara rufeni, ganina wata Alkarya wadda ban taba tunanin zuwa ba.


Kasan kafata na kallah naga shi kan shi wajen tafiyar mota ankayata, shi ba kamar jar kasar garin mu ba, haka Allah ya tsara ma kowane bawa rayuwarsu, kuma wadannan haka suke rayuwa cikin jin dadi.

Shatu ta katse min tunani, "lah Nanah kinga munzo wajen gidajennan da nike baki labari a birni, gasu can kin hangosu?".

Baki na saki ina kallon ikon Allah, jikina sai kara kyarma yake.

"Ni dai Shatu mu bar wajen nan tsoron mutanen nan nike, kuma ga mota na wuce tsoron su nike saboda ba irin na garin mu bane, ace mota ma hadda mai suffar kwado".

Dariya Shatu tayi tace; "shi yasa nace mu shiga yau Burni dake, ni kam na saba gani, ke nifa hadda malamin lafiya na taba gani, na taba bin yan matan tudu tallah wajen asibiti sai ma kinga masu fararen kaya kamar ba mutane ba".

"Tab ni kam ban ma iya zuwa ni dai mu rabe yau kinga wata rumfa chan muje babu mutane".

Wajen rumfar muka yi muka sake kayan mu, Shatu tace; "to taya za'ayi mu sai da sana'a ba mutane?? Kuma kin san idan Jabe yazo bai iskemu ba sai munyi fada, kin san bashida hakuri".

Hawaye har sun kawo min, jikina har yanzu kyarma yake ga faduwar gaba.

Muna nan zaune ko sai ga wasu yan makaranta maza suka ce, "yan mata furar ku nada dadi, mu saya?". Shatu tayi saurin cewa, "Eh akwai dadi ga nono mai kyau".

Nan fa suka yi mana ciniki jin dadin furar yasa suka ce mu dawo gobe tayi dadi zamu samu ciniki anan dan nan yan makaranta ke tsaya hawan mota, har ma dai idan akwai rana, Shatu tayi murmushi tace; "To mungode zamu dawo in dai za'a barmu mu zauna anan".

Suka ce, "kada ku dama ai tsoho ne angina sabo, wajen babu jama'a amman zamu yi maku tallah sai ku biya mu!". Suna maganar suna dariya.

Ita ma Shatu dariya take tace, "mun yarda sai Allah ya kaimu gobe, sunana Shatu ita kuma Nanah yar gidan Liman". Suka ce, "lallai yar gidan Liman kin iya fura".

Ni kam banda kyarma da zufa babu abinda nike, ga maganganun Baba na man yawo akaina samarin birni basu da tarbiyya, kullum hudu barshi akan na rike mutunci na duk da yana cewa ya aminta dani bai jina a duk inda zan shiga zan kiyaye.


Daya daga ciki yace, "Shatu kina ban kawar ki mai kyau?". Nan na kara jin gabana na faduwa, dariya Shatu tayi tace, "in dai kana mana tallah asan wajen zaman mu tunda nan babu mutane".

"Kada ki damu Allah ya kaimu". Muna cikin haka abokan su suka zo suna cewa me suke anan?? Nan suka fada masu, suma suka ce a basu harda manyan yan mata.

Zaunawa suka yi nayi tunanin gida yan matan zasu da tasu, kawai sai naga suma sun zauna zasu fara sha.

Cikin mamaki nake kallon su, taya za'ayi mace taci abinci cikin maza?? Lallai yan matan birni ba suda kunya, maganar Baba ashe haka ne.

Suna sha suna fira dayar da aka kira da wani suna da ban iyaba tace; "wallahi aboki ka taimake mu daman yunwa muke ji, amma duk da haka saina rama dukan da kayi man cikin makaranta". Hannu ta daga ta kaima namijin bugu.

Ban san sanda nace; "Subhanallah...!!". Tare da runtse ido kada naga an aikata haram da idona, mace ta kai hannun ta jikin namiji.

Su duka suka juyo suna kallo na rakube waje daya, suka ce, "lafiya wani abu ya cijeta mike samunta?".

Shatu da yake ta fahimci abinda ya faru sai tayi saurin cewa; "kanta ke mata ciwo ga jimuwar nan a koshin ta, shine ta taba taji zafi saitayi kara"wayyo sannu su duka suke cewa harda ku mutafi wani wuri shima sunan sa wuyar fadi,Wai a cikin makaranta cikin sauri nace"a'a kubar shi na gode"mun dan samu ciniki duk wanda yazo wuce sai ya tsaya ganin mutane wajen,har saura guda hudu cikin kwarya ta itama Shatu Nono ya kusa karewa.



************

Tafiya suke tara inda zasu sai ta hango wani waje yayi kyau da alama wurin kamar Company ne amman gefen shi anyi wajen zama mai kyau na ma'aikata,waya tayi baban ta tace ya tambayar masu izini ga wajen da suke.

Jim kada ya kirata yace suje su zauna.

Suna zuwa aka bude mata,cikin girmamawa tayi parking ta fito,yanzu ma ita ta bude mashi ya fito.


Suka zauna ta kalleshi tayi murmushi, tana tunanin shawarar Hanan.

A kan ta sakar mashi jikinta ai na miji ne,dole zaiji wani abu game da ita,tunda kalaman ta basuyi tasiri akan shiba.

Murmushi tayi tace cikin zuciyar"lallai kam shi ba dutsi bane"sai Kuma tayi wani tunani mutunan da yace bazai iya zama da itaba ba ita kade cikin gida inaga tashiga jikin shi.

Kusa dashi ta matsa, bai ce komai ba,hannunta ta saka a cikin nashi, lumshe ido tayi.

Cire hannun shi yayi, ta bude ido, wani kallo yayi mata yasa tasha jinin jikinta, sai ma matsawa da tayi tace, "sorry". Bai ko kalleta ba.

Ta rasa me zata yi mashi??

Mikewa yayi yaje ya dan yi tafiya kadan ya tsaya.

Kallo tabi inda yake kallo.

Wasu yanmata su biyu ta hango cikin rumfa, gaba dasu sun juya baya, ba'a ganin fuskar su.

"Me kake bukata?". Lumshe ido yayi yace; "su waye a chan mi suke yi,naga su kadai zaune?".

"Naga dazun da muka wutosu kamar fura suke saidawa".

Girgiza kai yayi ya koma ya zauna.


Chan Kuma sai ya mike ya nufi wajen, tayi saurin cewa; "Prince ina zaka?".

Ba tare da ya waigo ba yace; "wurin ina son fura".

Tafiya yake bai ji amsar taba.

Ta saki baki tana kallon shi.

Me zai yi wajen masu fura???


Qurrah
[1/28, 3:02 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*



*Writing by Qurrah*


*~Page 13-14~*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

Istigfari (Neman Gafara) Da tuba zuwa ga Allah

Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Na rantse da Allah! Ina neman gafarar Allah, kuma ina tuba zuwa gare shi, a kowace rana sama da sau saba'in.

Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, "Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Allah. Domin ni ina tuba a kowace rana zuwa gare shi sau dari.


Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, "wanda ya ce;
أَسْتَغْفِرُ اللهَ الَّذِي لاَ إِلَهَ إلاَّ هُوَ الْحَيُّ القَيّوُمُ وأَتُوبُ إِلَيهِ.
Astaghfirul-lahal-lazee la ilaha illa huwal-hayyul-qayyoomu wa-atoobu ilayh.

Ina neman gafarar Allah, Allah babu abin bautawa da gaskiya sai shi, rayayye, Mai tsayuwa da komai, kuma ina tuba zuwa gare shi.
... Allah zai gafarta masa zunubansa ko da zunubin gudua daga fagen fama ne".



Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, "Mafi kusancin da Allah yake kasancewa da bawansa a tsakiyar karshen dare ne. Don haka idan kana da ikon kasancewa cikin masu ambaton Allah a wannan lokacin to ka kasance".


Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi, "mafin kusancin da bawa yake kasancewa da Ubangijinsa yayin da yake sujada ne, don haka ku yawaita addu'a (a cikin sujada)".

Kuma manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Hakika a kan lullube zuciyata, kuma ni ina neman gafarar Allah sau dari a rana".

DEDICATED TO.....MY SISTERS😘


Page-13-14



_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_


---------------Da tunanin yadda zata hana Prince zuwa wajen ƴan fura tayi bacci,saboda ta rasa mafita,gashi Hanan dake taimaka mata,bata dauki maganar serious ba,haka dai tayi bacci da mafarkin masu fura.


Tunda safe yau Prince ya tashi ya shirya,fadawan shi sai mamaki suke ina Anuwar zai je??shi da bai dauki komai da muhimman ci ba amman yau kamar wanda zaije wani waje mai muhimman ci,haka dai suka zuba ma sarautar Allah ido.



****************
Na farka da asuba,sabon na saba yin sallah akan lokaci,yau da yake bani sallah komawa nayi na kwanta,kafin gari yayi haske.


Bacci yayi min dadi dan kwance nike,ina mafarkai masu daɗi juyi kawai nike bisa gadon karana,fuskata dauke take da murmushi.

Shahhhh....naji saukar ruwa bisa jikina.

Cikin sauri na bude ido tare da mikewa tsaye!!

Inna ce tsaye tana huci tamkar za kan ya tace;Dan Uban ki har kin isa yau dan uban ki bai nan kice ba zaki je wajen tallah ba??daman ta munafurcice tallar kenan,wato tallar ta ganin idon shi ce ko,to kinyi a banza,daya na nan da bai nan tallah sai kinje ta dole"kudina na tuna kila sun jiƙe,bance mata komai ba nayi saurin daga zanen da na'aza bisa gadon karana,a ƙarƙashin shi kudin suke.

Na dauko naga duk sun jike.

Kallona take cikin mamaki tace;"daman Nana sata kike yi??shine dalilin da yasa baki cin abincin gidan nan a cikin wannan ƴan kwana kin nan?"

Idona ya ciko da hawaye na fara cewa;"wallahi tallahi Inna ba kudin ki bane Baba ne yaban yace sai in sayi wani abu, kafin ya dawo,wallahi ban taɓa maki sata ba"cije leɓe take tama rasa me zata mata.

Kuka nike sosai ganin yadda Inna take cika tana batsewa akan wannan lamarin.

Ma'u ce tsakar gida tana kiran Inna,sai gata ta leko tace;"Inna me akayi maki ne" kallona tayi Ina zubar hawaye "tace Ma'u wannan yarinyar sata take man, haba shiyasa naga ƴan kwana kin nan har kiba take yi,da ka gan ta bata tare da yunwa,kuma bata cin abincin gidan nan "kallona Ma'u tayi sama da kasa.

Ma'u tace;"toke kuma Inna sai kikai mata me?"

"Aike Ma'u nama rasa me zan mata domin na huce ta kaicin na,dan bugun da zan mata saita kasa tashi,kuma ga tallah ta,kada nayi asarar Yyu "taɓe baki tayi tace; "gashi kuma idan taje birni ina son ta siyo min yadilan (powder),kawai ki dinga kirga mata".

Daga haka Ma'u ta fita Inna tace; "sai ki tashi ki fara aikin fura,kuma akwai surfen dawa da zaki man,sannan yau hadda zogala zaki fita dashi tunda Baban ki bai nan kije gonar shi ta gefen gari ki ɗibo,sannan idan kin dawo Lado yace zai zo" jin maganar Lado yasa nayi saurin dago kai!!

Inna tace; "ko ba zaki fita ba ne ba??dan haka kada kiyi dare,saboda zuwan shi yasa naki bugun ki,dan nasan zan samu fiye da abinda kika sata" ta fita tana surutai tana bala'i da kudi na a hannun ta.

Bango nabi na zauna tare da fidda wasu zafafan hawaye,ina son yin aure kodan barin gidan nan,amman banson auren Lado da an fadi Lado ma gaba na faduwa yake,ga rashin son Lado,gashi duk lokacin da aka fadi sunan shi sai faduwar gaba ta zo min.


Mikewa nayi na cire kaya na da suka jike,Ina tunanin daukar zogala da fura.

Na fita domin aikin fura zuciyata a cike take da ƙunci.



**************

Kursim kamar kullum yauma ta shirya cikin Dubai Abaya,red tayi mata kyau sosai ta kalli kanta a mirror tayi murmushi.

Cikin takun isa da kasaita ta isa bakin mota,ta jingina da mota tana jiran fitowar Yarima,kwakwalwar ta tabar aiki ta rasa me zata yi mashi ta hanashi zuwa wajen masu furar nan.

Ƙamshin turaren shine ya bigi hancin ta,ta lumshe ido,ta bude su a hankali bisa fuskar Yarima.

Fuskar nan tashi yau a sake hadda wani murmushi kamar bashi ba.

A hankali tace;"wow this smiling is killing me" wannan shine murmushi na farko data taba gani a fuskar shi,duk kyan shi da take gani,sai ma taga yau yafi kullun kyau.

__________________


Cikin sauri naje na ɗibo zogala na gyara na ɗaura da huwar fura na kirba,sannan na ɗaura zogala naje nayi wanka,sauri nike saboda kada su Shatu su wuce,dan nasan Jabe babu mutunci.


Na shafa mai na saka kayana,komai nawa na shirya shi,na taɓa fantekar zogalan nan naji zafi,na naɗa gammo na saka kwaryar furar cikin fanteka.

Na kama naji nauyi na kalli Ma'u da ta fito wanka, nace;"Dan Allah Ma'u kama man na kasa azawa akwai nauyi"


Dariya tayi tace; "amman wallahi Nana kin fiye son jiki,koni dai diyar gata, mai Uwa da Uba,ina iya aza wannan kayan,to bare ke,amman bari na taimaka maki ko dan yadilan dita" zuciyata jin ta nike tamkar zata fito dan bakin ciki.


Ta iso ta kama man muka daura tace;"lalle kam akwai nauyi, ashe jakin Lado zai huta, idan akayi auren,wannan karfi da kike dashi,ai kuwa kin taya shi dauko mana amfanin gonar Kabiru"


Kallon ta nayi na wuce, saboda yadda hawaye suka taru a idona.

"Meyasa mutane suke mantawa Allah shike badawa,kuma shike yin yadda yaso,idan na auri Lado haka Allah ya rubata,bawa bai isa ya kauce ma jarabawar shi ba"da kyar nike tafiya saboda nauyi,chan nesa na hangi Amalanken su Shatu.

Ina isa Jabe nata masifa shi ya gaji tun ɗazu ga rana Shatu tace "ai gama ta nan "kallona take.

Minike gani haka?!!

Nace"ke dai kama min na sauke wannan kayan nagaji"ta kama na sauke na shiga amalanken na zauna.

Tace "kai Inna bata da Imani" zaro idoo nayi!!

"Miye haka zaki ce Inna ta bata da imani,kin taɓa ganin marar imani ya shiga Aljanna? banso kina kiran ta da wannan kalmar ki daina babu kyau,mu dai yi mata addu'a Allah yasa ta gane gaskiya ta dauke ni a matsayin ɗiyar ta" girgiza kai Shatu tayi,muka cigaba da tafiya.

Muna zuwa bakin gari Shatu tace;"mu wuce cikin gari zamu fi ciniki harda ma zogalan nan, kinga yan zogala sunyi yawa nan"nidai ɗaga mata kai nayi,Shatu taji dadi tace;"wallahi yau sai kinje kinga mai kyan nan,mijin matar nan ta jiya"ɗaga kai nayi, saboda tunanin zuwan Lado ya isheni.

Dana runtse ido saina ga fuskar shi da wanga lallen bakin nan nashi duk goro.


***************

Kasa dauke ido tayi har ya iso inda take tsaye,saurin rufe bakin ta tayi da ta bude tana kallon shi,tace;"Morning"daga kai yayi,ya nufi bakin mota,ta iske shi inda yake tsaye ta bude mashi,ya shiga ya zauna ta kulle.

A jiyar zuciya tayi,sannan ta zagayo ta shiga ta tada motar.


Wani hadaden wuri ne tayi parking tace;"muje"wani kallo yayi mata duk ta ruɗe.

A hankali ya kama hannun kofar motar ya bude tare da turawa,sakin marfin yayi yana maida numfashi alamar ya gaji.

Kallon shi take cikin ranta tace;"towai shi miya iya kenan komai wahala yake ganin shi"kafin ta ida tunanin ta har ya fice daga motar.


Ta fito cikin sauri daga motar.

Ganin shi tayi ya nufi hanyar fita get din.

Ruɗewa tayi cikin sauri ta bishi tana kiran sunan shi.

Ganin yana tarar mashin yasa ta zaro idoo.

Tace;"wayyo Allah na ina kuma zashii??"


Qurrah
[1/28, 3:02 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*


*writing by-Qurrah* ✍🏽
Page-11-12


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*~Abin da ake fada idan za a yanka dabba, ko za a soke ta.~*


بِسْمِ اللهِ واللهُ أَكْبَرُ اللَّهُمَّ مِنْكَ ولَكَ اللَّهُمَّ تَقَبَّلْ مِنِّي.


Bismil-lah wallahu akbar, allahumma minka walak, allahumma taqabbal minnee.

Da sunan Allah, kuma Allah ne Mafi Girma. Ya Allah! (wannan dabba) daga gare Ka take, kuma mallakarka ce. Ya Allah! Ka karba daga gare ni.


Page-11-12


DEDICATED TO......MY SISTERS😘



_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_



----------------Cikin sauri ta isa inda yake;"please Prince mukoma"cikin shagwaba tayi maganar kamar zatayi kuka.

Hannun shi ta kama suka isa wajen.

Zaunar dashi tayi;" tace banson ka wahala barshi na amso maka"daga kai yayi alamar tabbatar wa,saboda shima bazai iya zuwa wajen ba yayi mashi nisa.

Tafe take har takai inda rumfar su Shatu take sallama tayi su duka kallon ta suke,kamar sunga wanii photo,ko wata kalar halitta.

Tsoki tayi ta daure fuska tace kai Prince ya cika fitina,yanzu duk abincin da aka tara mashi baici ba,sai wannan furar,cikin zuciyarta take maganar.


Shatu ce tayi karfin halin cewa;"sannu,me kike sone"kamar kada tayi magana sai ya mutsar fuska take tace;"kuna da fura ne?"

Cikin sauri Shatu tace;"Eh"

Kamar wadda bata son magana tace;"kudama mani,kuyi sauri na sayi furar kune dan naga kuna da tsabta,bana son kazanta kada kisa man hannu "cikin sauri Shatu ta fara dama mata furar da ludde.

Ni kam mutuwar zaune nayi daman akwai kalar wa'innan mutanan a duniya,gaskiya idan kazo birni ganinka zakayi kamar kaje wata duniya.


Shatu ta mika mata ta amsa tace;"daya ta biyo ni ta amshi kudii" Shatu ta mike dan ni ko motsi banyi saboda Al'ajabi.

Ina nan zaune nayi tagumi ina jin zafin ciwo,ga tunanin auren Lado ya hanani sakat, banda faduwar gaba babu abinda nike.


Jim kadan sai gata da gudu cikin murna tace;"Nanah taso kiga wani Balarabe,mijin wannan matar, "mikar dani take amman jikina tamkar babu lakka a jikin,na kasa motsi.


Kama kaina nayi nace;"Shatu muje gida banda lafiya"kallona take"tace kinga kudin da suka bamu jakka biyar,nace babu chanji suka ce na dauka,gobe ma mukawo"girgiza kai nayi na dauki kwaryata nayi gaba.

Bayana Shatu ta biyo tana kirana,harda dan gudu ta hada ta iskeni inda nike tace,"wai mike damunki ne??naga yau baki da walwala ko dai ciwon ne,ga kudi munsamu muje a saka maki magani Mana"kuka yazo man.

Cikin kuka nake maganar nace;"Shatu bani da sa'a a rayuwar nan,an haifeni cikin wahala,na tashi cikin wahala,kuma Shatu zan mutu cikin wahala,tunda nayi wayau ban san wani abu ba waishi so,daga Baba saike cikin duniyar nan ke kaunata,ina bukatar a nuna man kauna nima,ina bukatar namijin da zai soni dan Allah ya kula dani don Allah, "kuka take tamkar ranta zaifita.

Itama Shatu hawaye take tace;"nasan kina cikin wahala,amman har kullun ke kike fada man komi na da iyaka,nasan ba kowa ne mutum ne zai iya jure halin da kike ciki ba,amman nima yau zan fada maki kiyi hakuri kodan Baba"

Kuka nike sosai cikin kukan nace;"Inna ke son ta aura man Lado mai jakkai na kauyan mu "zaro ido tayi.

Kulle bakin ta tayi tace; "Amman koni da ba kauyan ku nike ba amman ai nasan halin da gidan Lado suke ciki, wannan wace irin kiyayya ce??Inna zata kaiki cikin wahala?"

Nan na fada mata abinda ya faru jiya.

Tace"wallahi kada ki yadda duk abinda zata yi maki,idan kinji ba zaki iyaba ki gudu ki tafi wajen dangin Innar ki,nasan zasu goya maki baya"toshe bakina nayi saboda yadda kuka na ke kara karfi,jin an fadi dangin Inna ta.

Kallona Shatu tayi tace;"kada ki damu duk inda dangin Innar ki suke nasan zasu soki,karma dai idan kakar ki na nan"cikin koɗaɗɗiyar muryata nace"Babu mai sona wallahi duk duniya sai ku biyu,idan suna sona miyasa ba zasu zo inda nike ba,shekara wajen nawa,kinga kenan ba su Sona"lalle kam yau naba Shatu tausayi saboda yadda hawayen ta suka kasa tsayawa.

Ganin kukan ta yasa na tsagaita nawa nace;"Shatu ki daina kuka hakanan"jan majina tayi tace"dole nayi kuka saboda ina tausaya maki,saboda zanbar ki ke daya,babu mai taimaka maki"kallon ta nike cikin mamaki!!

Nace;"Ina zaki kuma Shatu idan kika brni wahalar zata yi man yawa,wajen ki kaɗai nike samun sauki,gashi yanzu Inna ta daina bani kudin babur,kona ragin hanya ta daina ban,idan bakinan kenan kasa zan dunga zuwa??"


Hawaye Shatu take tace;"kada ki damu ,daman kunyar fadi maki nike an kusa yin aure na,nan da mako biyu za'a sakani a lalle,amman insha Allah kafin lokacin Allah zai kawo mafita"kuka nike duniya zata min zafii kenan??

Hannuna taja mukayi siyayya yau harda nama ta sai mana,cikin kudin da muka samu,muka iso bakin hanya muka iske jabe yana jiran mu,sai fada yake,wai tun dazun yana jiran mu.

Muka hau Amalanken muka zauna nide banda tunani babu abinda nike ta bude mana naman,hakan naci saboda ta matsaman saina chi idan ba haka ba itama batacii.


Bayan mun kai kauyen mu a nata kiran magriba na sakko tace amshi;"ta saka man sauran chanjin a cikin hannuna "Jabe zaija Amalanke nace "Jabe tsaya mana kudin menene?"dariya tayi ta ɗagoman hannu Jabe na jan Amalanken tace;"chanjin kudin ne ki sayi wani abu domin kuwa kin fini bukata,ki fito gobe da wurii"nima daga mata hannu nayi nace;"nagode"na danji sanyi a raina nashiga ciki da sallama.

Inna na iske zata shiga daki da alamun alwala tayi.

Nashiga ciki nace;"Inna sannu da aiki" tsaki tayi sannan ta iskeni inda nike tsaye"bani kudi na nashiga daki"na warware zane na bata nace"Inna ina abinci na?"kallona tayi sama da kasa tace"banyi ba tunda Ubanki bai kawo ba,yana chan wajen neman maki magani sarkin yan ciwo daga gama fadin haka ta shiga ciki.

Nayi dakina daman bana jin wata yunwa,alwala nayi na shiga zanyi sallah sai naji alamar wani abu na bina,nayi saurin fita zuwa ban daki.

Nafito ina tsaki banson rashin Sallah ya iskeni yanzu ba.

Daki na koma na zauna na boye kudina gefen buhuna.


****************

A gajiye suka isa gida,kowa yayi part dinshi.

Yana zuwa masu kula dashi suka rufa mashi baya, toilet aka hada mashi ruwan wanka,ya shiga yayi wanka ya fito.

Ya fito yazo bakin mirror ya zauna,gyaran kai za'ayi mashi,hannu ya mika a bashi kum din,yayi nuni da a fita,mutum guda ke tsaye bayan shi,wanda daman ko a Bauchi haka suke,indai yazo to kullum yana biye dashi.


Hannu ya daga zai kai a kanshi yaji hannun shi ya rike.

Cikin sauri na bayan shi yace;"Subhanallah..!! Allah ya taimaki magajin sarki ka kawo na gyara maka,wannan ba aikin ka bane"maida hannun shi yayi,ajiyar zuciya yayi yace wai haka aikin nan ke da wahala??

Kallon shi yayi yana tsaye yace;"Sani wai haka wasu mutane ke wahala??"cikin mamaki sani yake kallon shi dan tunda yake dashi bai taɓa kiran sunan shi na asali ba, kai ko kallo ma bai isheshi ba bai yin magana ko da yana bukatar abu, saidai idan ya fahimta ya bashi abun.

Lalle yau ansamu wani sabon abu ya shiga rayuwar shi,ko menene shi abun oho??

Cikin ladabi yace;"Allah ya taimaki magajin sarki wani abu ka gani? "daga kai yayi.

A hankali yace;"wasu kananun yara ne guda biyu na hanga,daya da tazo amsar kudi,na sayi furar su,kayan dake jikinta da yadda ta ruɗe akan Princess ta bata One thousand shine abin yaban mamaki"Allah ya taimake ka kuma idan ka bin cika daga kauye suka fito,kuma suna doguwar tafiya,ga kaya akai"kai ya jinjina.

Shiru Sani yayi yana tunanin,yau itace rana ta farko a rayuwar Prince ya damu da wasu,idan ka debe Jarabtar shi(wato MANAL)bai taba yin maganar wasu ba sai akan yan matan nan guda biyu kuma yan kauye,ikon Allah yace.


A hankali ya gyara kanshi yaji ya gaji, lumshe ido yayi yana tuna furar nan mai dadi,a hankali yace;"gobe ma zan koma".


Wanka Princess tayi ta saka riga da siket English wears,ta saka wata hadadiyar kimono a sama ta daure wutsiyar ta a gefe.

Wayar ta tayi kara taga Hanan cikin sauri ta dauka"Hello

Please Login or Register in order to submit comment