Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

سُبْحَانَ اللهِ العَظِيمِ.
Subhanal-lahi wabihamdih, wasubhanal-lahil-'azeem.
Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da Shi; tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma.


Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, ya ce; "Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; Fadin:
سُبْحَانَ اللهِ، والْحَمْدُ للهِ، لَا إِلَهَ إلاَّ اللهُ واللهُ أَكْبَرُ.
Subhanal-lah, walhamdu lillah, la ilaha illal-lah wallahu akbar.

Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah ne Mafi girma.
… Shi ya fi soyuwa gare ni daga dukkan abin da rana ta hudo a kansa".


Daga Sa'ad bn Abi Wakkas, Allah ya yarda das hi, yace; mun kasance a wajen Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya ce; "Yanzu dayanku yana kasa aikata kyawawan ayyuka dubu a kowace rana? Sai wani mutum cikin wadanda suke zaune tare da shi ya ce; "Ta yaya dayanmu zai aikata kyawawan ayyuka duub? Sai ya ce; "Ya yi tasbihi (ya ce;
سُبْحَانَ اللهِ.
Subhanal-lah.(3)

(Tsarki ya tabbata ga Allah)
... Sau dari, saia rubuta masa kyawawan ayyuka dubu, ko a kankare masa zunubai dubu.

Jabir, Allah ya yarda da shi, ya ce; Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Wanda ya ce;
سُبْحَانَ اللهِ العَظِيمِ وبِحَمْدِهِ.
Subhanal-lahil-'azeemi wabihamdih.

Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tare da godiya gare Shi.
... Za a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna.


Daga Abu Musa al-'ash'ari, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce mini: "Ya Abdullah bn Kais! Ba na shiryar da kai ba zuwa ga wata taska daga cikin taskokin aljanna ba? Sai na ce. Shiryar da ni. Sai ya ce: ka ce:
لاَ حَوٍلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللهِ.
La hawla wala kuwwata illa billah.

Babu dabara babu karfi sai da Allah.


Daga Samura bn Jundub, Allah ya yarda da shi, ya ce Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Mafi soyuwar zance a wajen Allah shi ne;
سُبْحَانَ اللهِ، والْحَمْدُ للهِ، ولاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ واللهُ أَكْبَرُ.
Subhanal-lah, walhamdu lillah, wala ilaha illal-lah, wallahu akbar.

Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah ne mafi girma.
... Babu komai a gare ka ko da wane daya daga cikinsu ka fara'.



Sa'ad bn Abi Wakkas, Allah ya yarda da shi, ya ce; "Wani balaraben kauye ya zo wajen Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, sai ya ce; koya mini wadansu kalmomi da zan rika fada. Sai ya ce; ka ce;
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، اللهُ أَكْبَرُ كَبِيراَ والْحَمْدُ للهِ كَثِيراً، سُبْحَانَ اللهِ رَبِّ العَالَمِينَ، لاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللهِ العَزِيزِ الْحَكِيمِ.
La ilaha illal-lah, wahdahu la shareeka lah, Allahu akbaru kabeera, walhamdu lillahi katheera, subhanal-lahi rabbil-'alameen, la hawla wala kuwwata illa billahil-'azeezil-hakeem.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; babu abokin tarayya a gare Shi. Allah ne mafi girma (Ina girmama Shi) girmamawa. Kuma godiya ta tabbata ga Allah da yawa. Tsarki ya tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Babu dabara babu karfi sai da Allah, Mabuwayi mai hikima.
... Sai mutumin ya ce; "Wadannan na Ubangijina ne, ni kuma nawa fa/ sai yace ka ce;
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي، وارْحَمْنِي، واهْدِنِي، وارْزُقْنِي.
Allahummagh-fir lee, warhamnee, wahdinee, warzuknee.

Ya Allah! Ka yi mini gafara, K aji kai na, Ka shirye ni, Ka azurta ni.

Tarik Ibn Ashyam al-Ashja'i, Allah ya yarda das hi, y ace; "Idan mutum ya musulunta, sai Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya koya masa sallah, sannan ya umarce shi ya rika addu'a da wadannan kalmomin.
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي، وارْحَمْنِي، واهْدِنِي، وارْزُقْنِي.
Allahummagh-fir lee, warhamnee, wahdinee, warzuqnee.

Ya Allah! Ka yi mini gafara, Ka ji kai na, Ka shirye ni, Ka amintar da ni daga bala'i, Ka azurta ni.

Jabir Ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi, ya ce Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Mafificiyar addu'a ita ce (fadin):
الْحَمْدُ للهِ.
Alhamdu lillah

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah.
…. Kuma mafificin zikiri shi ne (fadin):
لاَ إِلَه إِلاَّ اللهُ.
La ilaha illal-lah.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.


Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Ayyuka nagargaru masu wanzuwa su ne (fadin):
سُبْحَانَ اللهِ، والْحَمْدُ للهِ، لاَ إِلَهَ إَلاَّ اللهُ واللهُ أَكْبَرُ وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إلاَّ باللهِ.
Subhanal-lah, walhamdu lillah, la ilaha illal-lah, wallahu akbar, wala hawla wala kuwwata illa billah.


Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah ne Mafi firma, kuma babu dabara babu karfi sai da Allah.







_Bissimillahir Rahmanir_ _Rahim_


---------------Cikin zafin nama Inna ta fizge laidar dake hannu na, tace, "ke har kin isa dan Ma'u na cin abinda Lado ya kawo ki fizge, to kinma kan ki, ba zaki ko lashe ta ba!".

T ajiye laidar a gaban Ma'u dake zaune, baki a sake tana kallona.

Nace; "wallahi Inna haka yace, wannan laidar naci ni kadai kada na ba kowa, ga laidar da yace ita ce taku".

Wani kallo tayi min, tace;

"Idan baki fita dakin nan ba, idan na ingiza ki sai bakin ki ya fashe!!".

Cikin sanyin jiki na bar dakin.


A dakina na koma na zauna, yunwa nake ji sosai, saboda yau sau guda naci abinci, shi yasa wani lokaci ma nafi aon zuwa tallar, dan zanci na koshi.


Fitowa nayi a hankali nake tafiyar dan kada Inna taji motsi.

Daman ni a duhu nike kwana banda fitila, har nakai Madafa, a hankali na bude tukunyar dake bisa murhun, na lalubi luddai na motsa naji akwai dumamen tuwon jiya.

Cikin sanda na koma daki na, na dauko roba ta da nake cin abinci, kalar ta almajirai na dawo na dauki guzurai biyu na koma.

Na zauna na saka hannu cikin tuwon, naji kamar ya lalace, ina kaiwa baki na zubo shi kasa.

Miyar kuka ce tayi tsami, zafin da aka yi jiya da daddare tuwon dawa ne, kila hakan yasa ya saki.


Nayi zugun tare da tagumi ina hango kajin nan gaban Ma'u, jin cikina na juyawa yasa na nasa hannu naci haka nan ina chi, ina runtse ido har na gama.

Ina gamawa naje nasha ruwa na dawo nayi addu'a na kwanta, tare da tunanin Baba.


*************

Yinin ranar da Kursim da Hanan a tare suka yini part din Kursim, sai da magriba suka je wajen Umma suka yi fira har dare yayi sosai kana suka dawo a gajiye.

Duk Hanan ta tsara haka ne dan kada Kursim taje wajen Prince.


A bisa kujerun parlon shi yake, ya aza kafafun shi bisa center table, yana rike da remote a hannu, ya rasa me zai kalla tunda ba kallo yake ba.


Wani tunani yayi sai yayi saurin naimo Baby tv, murmushi yake yana kallon cartoon din ciki, lumshe ido yayi tare da rungume pillow din kujerun shi, a hankali yace"MANAL", tare da kara rungume pillown a kirji.

Bude ido yayi ya ganshi rungume da pillow cikin sauri ya saki pillon, ya kashe tv, ya zauna ya rasa mike mashi dadi.

Tashi yayi ya koma bedroom ya zage labulen dakin shi yayi tsaye bakin window.


Sani ne ya shigo tare da sallama, Prince ya jiyo yana kallon shi yace; "Allah ya taimaki magajin Sarki ga abinci nan daga Gimbiya Kursim".

Hannu ya nuna mashi alamar ya fita, ya juya tare da cewa; "godiya nike, Allah ya kara lafiya da daukaka jikan Sarki". Bayan ya fita yana nan tsaye sai kuma ya tuna wani Abu, cikin sauri ya fito parlo.

Wajen abincin ya nufa yaga wani Jug, yayi saurin budewa, kamshin furar ya bugi hancin shi.

Lumshe ido yayi tare da sakin murmushi,yace; "Thank you Kursim".

Yayi maganar a fili tamkar Kursim na gaban shi, haka yayi maganar.


Sani ya iso cikin sauri ya matso kusa dashi, yace, "idan Yarima yayi man izini,zan zuba mashi furar". Da hannu ya nuna mashi ya dauko mashi Jug din, ya dauko Jug.


A bedroom ya zauna, Sani ya zuba furar a cikin cup ya mika mashi.

Ya amsa tare da yima Sani murmushi.

Cikin sauri Sani yace; "Allah ya tabbatar da farin ciki a rayuwar Yarima Anuwar".

Ya juya cikin mamaki. Anya ba tare da mai furar nan zasu koma ba, zanyi magana da martaba yace cikin ranshi.


Furar yake sha yana lumshe ido, lokaci guda Kursim ta shiga zuciyar shi, saboda ta bashi abin da yake so.

Sai yanzu yaga bai kyauta ba, tsaki yayi yace a fili; "ya kamata ta tsaya inda na ajiye ta, ban son shishigi, ba sai na kira Mai martaba ba zan zauna saboda fura nan, ina son furar". Ya lumshe ido.



A gajiye suke hakan yasa kowa na naimi wajen bacci, Hanan tace; "dazu fa ina jin ki, kyale ki nayi saboda Umma kina ba Lantana umarnin hada kayan abincin Prince".

"Mtwss!". Tayi tsaki tace; "ai da kin bar shi baki kai mishi sauran furar ba ai dole yaci abinci, wallahi dan ina tare da Umma kada tayi zargin wani Abu yasa na kyale ki".

Dariya Kursim tayi tace; "ban son Doctor's da daukar zafi ba, masu hakuri aka sanku, wallahi na san idan ba furar aka kai mashi ba bazai ci komi ba, kuma ai kinga bako ne".

Hanan tayi tsaki tace; "ni fa yanzu nafi tsanar mai furar nan akan Manal, saboda Manal dan ya sota 'yar uwar shi ce, kuma kin ce an daura masu aure, kin ga ita matar shi ce, da sauki dan ya sota, amman ita fa wannan ace baicin komi sai nata, ni wallahi baccin kin hana ni, da tuni nasa an ruguje barandar an kore su".

Kursim tace; "lallai Hanan akwai daukar zafi".

Nan suka cigaba da fira har dare yayi nisa, kana sukayi bacci.


Haka a bangaren Anuwar ya yita tunani iri-iri har yayi bacci.



*************

Tun asuba na fara aiki, saboda yau da ta jiya data yau zan hada, haka nayi aiki zuwa karfe goma na gama komai.


Har lokacin Ma'u bata tashi daga baccin da take yi, ina ji Inna na cewa wannan wane irin bacci ne haka, har rana ta fito baki tashi ba, sai wani murmushin banza kike.

Ni dai bance komai ba nayi wanka, na fito na dauki kaya na, nace; "Inna na tafi".

Tace; "kada ki daukan min kudi". Na daga kai nayi gaba.

Na bar ta tana ta masifar wannan wane irin bacci ne haka Ma'u keyi??

Yau inda muke haduwa babu su Shatu, ga kayan sunfi na kullum nauyi, da kyar na iso nan din, ina ga ace naje birni dasu.


Ina nan zaune sai ga Shatu tare da Jabe a amalanken su.

Na mike nace yau na riga wasu, ina dariya.

Shatu tace; "lallai kam wannan furar fa ina zaki kaita? To taya ma aka yi kika daukota bisa kai?".

Dariya nayi nace; "haka nan na dauko ta amman fa da kyar na iso, har da ta jiya da ban yi tallah ba, shi ne ta hade min, shi yasa tun kamin ayi kiran sallah na fara aikin furar".

Jinjina kai tayi, fuskar ta kamar zata yi kuka tace; "Jabe sauko mu kama mu daura bisa".


Muna tafe muna fira, tana ban labarin yan uwan Maman ta dake burni, wai sun ce bata isa aure ba, dariya muke yi, nace;

"Basu san duk rugar ku babu mai girman ki ba, lallai kam, kin san birni sai sun girma sosai suke aurar da yaran su".

Haka dai muka yi ta labari na ban dariya har muka isa.


************

Yau ko da Kursim suka tashi, Hanan da kanta tayi mata Makeup kana tasa aka hada mata abin Break, suka ci Kursim ta dauki na Prince.


Tana zuwa ta iske a parlo zaune cikin kananun kaya yayi kyau sosai, hankalin shi yana a tv.

Ta kai kallon ta a tv, cikin mamaki take kallon shi.

"Me yasa yake kallon cartoon??".

Jim tayi tana tunani sai tace; "MANAL".

Juyowa yayi cikin sauri.

Tsuru-tsuru tayi kamar marar gaskiya, ashe a fili ta fada.

A hankali ta shigo ta ajiye mashi kayan Breakfast din.

Tace; "ina kwana, an tashi lafiya?". Ya amsa da kai.

Ta zuba mashi ta tura a gaban shi.

Ta tashi ta nufi bedroom din shi,ta iske a gyare, ta leka toilet din shi, nan ma a gyare, tayi tsaye tana tunanin mezata yi mashi ta burge shi??


Waya tayi Hanan, tace a aiko mata burner da turaren wuta masu kamshi.

Jim kadan ta fito ta ganshi zaune ya gama ci, fita tayi ta amso ta dawo.

Ta jona a bedroom din shi ta zuba turaren wuta, nan fa kamshi mai dadi ya fara tashi.

Ta dawo falo ta jona ta saka turaruruka masu kamshi, kamshi sai tashi yake mai dadin gaske, yana zaune rike da waya a hannu.

Bayan ta gama ta dawo ta zauna tace; "ko kana bukatar wani abu?"

Kai ya girgiza tace; "fura ta kare muko ma ko musiyo?".

Mikewa yayi yana kallon ta.

Murmushi tayi tare da mika mashi hannu ya mikar da ita.

Juya wa yayi ya fara tafiya, ta mike tabi bayan shi.


Suna isa suka shiga mota babu mai yima kowa magana.

Kursim tana tunanin mezata yi ta burgeshi.

Shi kuma yana tunanin ya za'ayi idan ya koma gida babu fura?

Haka har suka isa wajen, idon shi a lumshe sai da yaji mota ta tsaya ya bude ido.

Ta fito ta bude mashi suka fito.


****************
Na fara sabawa da 'yan makaranta, hakan yasa yau hadda ni ake saida furar.


Shatu tace; "amso mana kudin mu wajen mutumin can dake tafowa". Na duba banga kowa ba.

Nace, "yana Ina?".

Tace, "gashi can wajen inda mata da mijin can suke zaune, daga nan kiyi masu tallah kinga yanzu suka iso".

Nace; "to".

Na doshi wajen ina tafiya tare da tsalle, zuciya ta cike da farin ciki.


***************

Kama hannun shi Kursim tayi, tana murmushi, hannun su sarke cikin nata, lumshe ido tayi tana jin sanyi a zuciyarta.


Jin ya saki hannun ta cikin sauri, yasa ta bude ido.

Kallon shi tayi yana kallon yarinyar dake saida fura, tana tafowa da dan gudun ta.

Tace; "lafiya me ya faru?".

Bai ko ji me tace ba.

Yace, "kalar tafiyar Manal". Cikin sauri ta kalle shi.

Ta zaro ido! tare da cewa; "Innalillahi!!".


Qurrah
*_JARABTAR MU*_



*_Written by Qurrah_* ✍🏽




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



DEDICATED TO....MY SISTERS😘



Page-23-24





Daga Cikin Ayyukan Alheri Da Kyawawan Halaye

Jabir bn Abdullahi, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Idan duhun dare ya gabato – ko kuma almuru ta yi – to ku hana 'ya'yanku fita, domin shaidanu suna bazuwa a wannan lokacin. Idan sa'a ta gota a cikin dare, to sai ku bar su. Ku rufe kofofi, kuma ku ambaci sunan Allah (yayin da kuke rufewa), domin Shaidan ba ya bude kofa rufaffiya. Ku zuge bakin salkunan ruwanku, kuma ku ambaci sunan Allah (yayin da kuke zugewa), kuma ku rufe kwanukan abincinku, ku ambaci sunan Allah (yayin da kuke rufewa); ko da ku dora wan;i abu ne a kan kwanukan. Kuma ku kashe fitilinku na a-ci-balbal.

Allah ya yi tsira da Aminci da albarka ga Annabinmu Muhammadu, da alayensa da Sahabbansa baki daya.



_Bissimillahir Rahmanir_ _Rahim_



-------------------Tafiya nike inajin nishadi a zuciya,haka kawai na rasa minene dalili??


"Nana! Nana!! Nana!!".

Na juya cikin sauri jin yadda Shatu ta kirani.

Shanu ne na hango sunfi su dari sun nufo barandar mu, na yadda abinda ke hannu na na juya a guje.


Ina zuwa na dauke kwaryata, muka haye bisa dan tudun barandar.

Zasu shigo Shatu tace; " ajiye min inzo". Daga kai nayi, saboda har yanzu cikin tsoro nike, ina tsoron kada su fasa ma Inna kwarya.

Wajen fulanin dake tare dasu ta nufa, suna tafe suna chin awara sun saki shanu bisa titi.

Cikin fada take maganar da fulatanci, hakan yasa ban gane me take cewa ba.

Nan naga kamar suna bata hakuri, ta juyo ta dawo inda nike tace; "kai wallahi mutanan mu sai a hankali, yanzu barcin da baki yi nisa ba, ai da sun mana barna". injina kai nayi nace;

"Allah mungode maka da sun fasa kwaryar Inna".


*************

Ganin yarinyar ta juya a guje yasa Yarima yin azama, domin chimmata.

Hannu Kursim tasa ta rike mashi hannu, tana cewa; "please Anuwar kada kaje, kaga ga Shanu kuma yaran chan kauyawa ne, zasu iya guduwa idan suka ganka, ko ni sai da nayi masu dubara, tsoron mutane suke tsabar kauyancin su".

Kamar ma baiji me ta ce ba turo ta yayi baya ta fadi kanta ya bugi mota.

Yayi gaba cikin sauri ita kuma ta buga wata irin kara.

Saurin dafe kanta tayi tare da mikewa cikin azama.

A guje taje tasha gaban shi.

Tace; "yanzu idan ka tsorata su, baza su kara zuwa ba kuma furar nan ita kadai kake sha, gashi yarannan nan suke samun ciniki, idan kayi haka baka kyautaba, hakan ba soyayya bace, ka kyale su mana idan har kana son Manal, ko dan kalar tafiyar MANAL da mai furar chan tayi".


Kallon ta yake kamar mai son ganin wani abu a fuskar ta.

Daga kai tayi alamar tabbatarwa, ga hawaye na bin fuskarta.


Hannun shi taja suka koma inda suke zaune.

Tace; "Bari naje na siyo maka furar yau da wuri zamu koma, gobe akwai wani nadi da za'ayi, bazamu zoba zan amso mai yawa sai a saka a Freezer dake dakin ka".


Rike kai yayi idanun shi jawur kamar garwashi.

Kai kawai yake rikewa tare da girgiza shi, ganin yanayinsa yasa tayi gaba.


Fura mai yawa ta siya ta dawo, ko da ta dawo yana cikin mota.

Kulle motar tayi tare da zagayawa ta shiga.

Ta kalle shi fuskar nan tashi ta chanza, yatsun hannun shi yake kallo.

Tada motar tayi, ttayi hanyar fita, kanshi na kasa har suka isa gida.

Da karfi ya bude motar ya fita ko kamin ta fito har ya bace.


Bata tsaya kulle motar ba, tabi bayan shi cikin sauri.


Har gudu take tana isa dai-dai lokacin da ya banko kofar dakin shi.

Cikin azama tayi sauri kaiwa.

Banko ta yayi ta dawo, jarab ta fadi kasa.

Ya rufe dakin, cikin sauri ya isa bedroom tare da fadawa bisa gado.

Rike kai yake tare da buga kai.

Me yasa kowace mace take mashi kama da Manal??

Cikin filo ya saka kanshi dan bai son ganin gudun da yarinyar nan keyi.


Hanan ce take tabi da hannayen ta, tare da iso wa inda Kursim take kwance.


Kallon ta tayi ranta a bace tace, "yanzu princess din mu ce a kasa, because of Dah' namiji!". Tsaki tayi ta kama ta suka tashi.

Kursim kasa magana tayi dan ko kadan bata ganin laifin Anuwar.

A wannan lokacin ita tausayi ma yake bata.

Shiru tayi tana tunanin yanzu menene mafita??



**************
Yau zuciyar ta fal da farin ciki.

Haka sukai ta ciniki har yamma furar ta bata kare ba saboda tafi ta kullum yawa.


Hakanan suka tashi yau babu tsoron Inna ko kadan a zuciyar ta Shatu ce ma keta cewa Allah yasa kada Inna ta bigeta.

Ni kam zuciya ta Yau tamkar wata wadda akayi ma wani Albishir.

Haka suka kwashi kayan su suka nufi. magama bakin hanyar kauyan su.

Nan suka iske jabe na jira Shatu ta siyo mana awara.


Muka hau mukaci muka sha ruwan cikin kokon ruwan jabe.

Muna isa Shatu tace, "nifa gobe ban zuwa". Zaro ido nayi, tare da cewa; "innalillahi! toni yanzu ya zanyi ni kadai". Dariya tayi tace;

"Zan turo jabe ya kai ki hadda nono ki saida man, Baffa ne ya hana ni zuwa tallah,
wai tunda sati mai zuwa ne". Shiru nayi duk farin cikin da nake ciki sai naji ya gushe.

Jiki na babu kwari nace; "to Allah ya kaimu". Haka mukayi bankwana mu duka kowanne kamar yayi kuka.

Jiki ba kwari nayi sallama.

Na iske makwabtan mu tsaye cikin gidan mu,kusan gidan cike, sai maida magana ake.


Ga hawaye shabe-Sabe a fuskar Inna.


Amman abun mamaki Ma'u tsaye take,idon ta babu ko alamar kuka.


Tace tomi ke faruwa??


************

Kursim tace"miya kaiki wajen part din Anuwar??"

Hanan tace"to sarkin 'yan kishi yanzu na shigo na amso sako,ina fitowa mota na hange ki,ko rufe mota bakiyi ba kinyi ciki a guje,ni na'aza ma wani abu ya faru shine na biyo ki"girgiza kai tayi.


Kursim ta kalle ta tace"Maganin minene mugani??"cikin sauri Hanan ta dauke hand bag dinta.

Tace ba ruwan ki,kada ki tabaman jaka.

Kursim ta kalle ta cikin mamaki!!

To wane magani ne wannan Hanan take buyewa??


Anuwar ya kasa samun natsuwa jin shi,yake tamkar yau abin ya faru.


Ganin halin da yake yasa Sani buga kofa ya bude,amman ya kusa awa babu ko motsin Anuwar.


Daya bude ido fuskar MANAL ke dawo mashi.


Idan ya runtse ido karamar yarinyar nan mai fura yake gani,tana nufo su a guje.



Bai ga fuskar taba, amman ya kasa natsuwa ganin abin yayi tamkar yau ya faru.


Shiru yayi tare da rike kanshi yana tunanin anya zai kara koma wajen nan??


Meyasa suke tsoron muta ne, Yana bukatar shawarar Sani.



Yana so ya koma kallar mutanan garin su ko dan ya samu kusan chi da ita.


Mikewa yayi cikin sauri yazo bakin kofa.

Yana budewa yaga duk fadawan shi a tsugunne bisa gwuiwowowin su, a bakin kofa.

Kowanne fuskar shi tamkar an mashi mutuwa.


Suna ganin shi suka yi saurin mikewa tsaye.


Suka ce tare da dukar da kansu kasa; "tuba muke idan mun bata ma Yarima rai,yayi mana duk hukun cin da ya dace damu"tare da kai gwuiwoyin su kasa.


Sani ya kalla,ya taso cikin sauri ya iso inda yake tsaye.


Da kyat maganar ta fita,ya nuni da su tashi,yace Sani ya biyo shi.



Suka tashi tare da godiya.


A falo ya zauna yana tunanin taya zai fara mashi bayani.


Me zai ce mashi ne?


Yace; "ina son a samo min kalllar kayan da kauyan garin nan ke sakawa".


Cikin sauri Sani ya kalle shi!!.



Qurrah
*_JARABTAR MU*_



*_Written by Qurrah_* ✍🏽




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



DEDICATED TO....MY SISTERS😘

Page-25-26








FALALAR ZIKIRI
Allah Madaukakin Sarki ya ce:
فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُواْ لِي وَلاَ تَكْفُرُونِ
Fazkuriniy Azkurkum Washkuruliy Wala Takfuruni.
Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" [Bakara, aya ta 152].

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْراً كَثِيراً
Ya'ayyuhallazina Amanuzkurullaha Zikran Kathiran.

Ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa". (Ahzab aya ta 41).
وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيراً وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْراً عَظِيماً
Wazzakirinallaha Kathiyran Wazzakirati A'addanlahu Lahum magfiratan Wa'ajran Aziyman.
Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambatonsa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma". [Ahzab, aya ta 35]
وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعاً وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالآصَالِ وَلاَ تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ
Wazkurrabbaka Fiy Nafsika Tadarru'an Wakhiyfatan waduwanaljahri Minal kawli Bil'guduwi Wal'asali Walatakun Minalgafiliyna.
Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kankan da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba (saka-tsaki) tsakanin asirtawa, da bayyanawa, da safe da marece, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu". [A'araf, aya ta 205].
Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye da matacce ne". (Duba Sahihul Bukhari tare da Sharhinsa Fat'hul Bari (11/208). Muslim ya rawaito shi da lafazin; 'Misalin gida da ake ambaton Allah a cikinsa, da wanda ba a ambaton Allah a cikinsa kamar misalin rayayye ne da matacce". (1/539).)
Kuma ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Srkin da yake mallakar ku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku daga ciyar da zinariya da azurfa kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka ba mu labari. Ya ce: Ambaton Allah Madaukaki". (Tirmizi (5/459), da Ibn Majah (2/1245). Duba Sahih Ibn Majah (2/316). Da Sahihul Tirmizi (3/139).)
Kuma ya ce: "Allah madaukaki yana cewa: Ni ina tare da zaton bawana da ni, kuma ina tare da shi idan ya ambace ni idan ya ambace ni. Idan ya ambace ni a cikin ransa zan ambace shi a cikin raina, idan ya ambace ni a cikin jama'a zan ambace shi a cikin jama'ar da ta fi su alheri, in ya kusance ni taki daya zan kuance shi tsawon

Please Login or Register in order to submit comment