Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fito har lumshe ido nake gani nake kamar zanji sautin shi a kunnena.




♦♦♦♦♦♦♦♦

Lallai maganin Kulsoom yayi aiki a jikin prince.

Dan yamanta da wata Nana ko kadan iyayen shi sun dauka Aljanar ce addu'ar su ta karbu ta rabu dashi saboda ko maganar dawowa Nigeria baya yayi kullun suna makale da juna



Har cikn Kulsoom ya isa haihuwa tasamu Baby girl Anuwar dam murna kamar ya hadiyeta yakeji.


Safiyar ranar su Mummy sukazo kasar.


Yarinya taci sunan Mahifiyar Kulsoom wannan zabin Kulsoom kuma Yarima bai damuba.


Nan su Mummy sukace zasu wuce da Kulsoom shi Kuma ya fara Karatu daddy dinshi ya shirya haka.


Anuwar yaki yarda saida Abie ya saka baki.


Kowa mamakin chanzawar Anuwar yake lokaci guda.


Haka suka baro Anuwar a Spain zai fara karatu.



♦♦♦♦♦♦♦♦


Zama mukeyi nida Inna na fahimtar juna.


Duk aikin gidan na maidashi kaina, Nike fura na gyara komi na gidan Babu yunwa ko kadan a gidan Inna.

Yau har yarana sun fara tafiya sosai daka gansu kasan basu cikin yunwa ko kadan yan kudin furar dasu Inna ke masu hidima duk da tana yawan samun alheri daga Mai martaba ko matar shi.

Koda yaushe cikin son Jin labarin Yarima nike kullun harso nake Sani yazo kozanji wani labari Amman shiru tunanin Yarima yasa na kasa sukuni kullun cikin tunani shiyasa kullun a rame nake Inna tarasa mike damuna saide taita Nasiha.



Yaune ina zaune da Yamma sai ga Sani ya shigo Farhana ce ta ruga tana gwaranci ya dauketa yana mata wasa, daman itacs keda son surutu Farhan saide yabita da kallo.


Muka gaisa na dauko mashi tabar ma Inna ta fito.


Ya washe baki yace;"Inna yau gidan a cike yake dan Gimbiya Kulsoom ta iso gidan saboda jama'a kamar ya fashe"



Inna itama cikin murna tace;"Masha Allah Gimbiya Kulsoom ta iso, ya abinda ta haifa? tareda Yarima suka dawo nayima Yarima murnar samun karuwa"


Jikina har kyarma yake na mike tsaye! Cikin sauri na fada daki.


Mai maita sunan nayi;"Gimbiya Kulsoom"

Lokaci guda naji na tsani sunan da matar daman yanada mata.

Wasu hawayene masu zafi suka wankeman fuska lalai na dauko abinda yafi karfina lallai ni bansan kaina ba.



Kuka Mai sautine ya kwaceman hawaye masu zafi ne ke fita a idona.

Lokaci guda naji wani abu ya toka reman makoshi a fili nace;"Daman yanada mata nake wahalar banza shikenan rayuwata a haka zata kare cikin wahala da kuncin rayuwa? To miyasa ma nake kishin sane? miyasa nakasa mantawa dashi banson miyasa ba kodan yaban jini inason naganshi ko zuciyata zata huta daga kuncin da take"


Kuka nake sosai tun sauti bai fita sosai har yafi.



Surutai nake tayi kamar mahauciyya lallai nasan nayi kuskure tsakanina dashi akwai tazara Mai nisa avinda bazaitaba. Yiyuwa bane.


Ina cikin surutaina naji andafani Ina waigowa mukayi ido hudu da Inna.

Zaro iso nayi nace;"Innalillahi"


Shikenan asiri ya tonu yanzu mizance mata??



MARYAM D'ANKUDII
*JARABTAR MU*

*Page-71-72*


*Written by-Qurrah✍🏻*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*Addu'ar Yayin da za a yi Barci:*

Idan mutum ya zo kwanciyar barci sai ya hada tafin hannayensa biyu, ya karanta wadannan surori na Alkur'ani, yana yin tofi cikin hannayen nasa;

(قل هو الله أحد)
(قل أعوذ برب الفلق)
(قل أعوذ برب الناس)
(Qul'huwallahu Ahad)
(Qul'a'uuzu Bi Rabbil Falak).
(Qul'a'uuzu Bi Rabbin Nas).
Sannan ya shafu su iy ainda zai iya na jikinsa; yana farawa da kansa, da fuskarsa da kuma gaban jikins.a ya yi haka har sau uku.



Ya Karanta Ayatul-kursiy:

(اَللهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ)
Allahu La'ilaha illahuwal Hayyul Qayyum… (Ilaa A'khiruhaa).
Har zuwa karshenta, wanda ya karanta ta yayin da ya zo kwanciya to ba zai gushe ba yana da wani mai tsaro gare shi daga Allah, kuma shaidan ba zai kusato shi ba har ya wayi gari.


{آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مِن رَّبِّهِ وَالْمُؤْمِنُونَ كُلٌّ آمَنَ بِاللّهِ وَمَلآئِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لاَ نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّن رُّسُلِهِ وَقَالُواْ سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ * لاَ يُكَلِّفُ اللّهُ نَفْساً إِلاَّ وُسْعَهَا لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ رَبَّنَا لاَ تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا رَبَّنَا وَلاَ تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْراً كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِنَا رَبَّنَا وَلاَ تُحَمِّلْنَا مَا لاَ طَاقَةَ لَنَا بِهِ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا أَنتَ مَوْلاَنَا فَانصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ}
Amanar rasulu bim aunzil ilayhi min rabbihi wa lmu'minuna, kullun amana billahi wa mala'ikatihi wa kutubihi wa rusulihi, la nufarriku bayna ahadin m-min rusulihi, la nufarriku bayna ahadin m-min rusulihi. Wa kalu sami'na wa ata'na, ghufranaka rabbana wa ilayka-l-masir.
La yukallifu l-lahu nafsan illa wus'aha, laha ma kasabata wa 'alayha ma kasabata, rannaba, la tuk'akhizina in nasina aw akhta'ana, rabbana wala tahmil 'alayna isran kama hamaltahu 'ala l-lazina min qabilina rabbana wa la tuhammilna ma la taqata lana bihi. Wa 'fu anna, wa ghfir lana wa rhamna. Anta mawlana fa-nsurna 'ala-l-qawmil-l-kafirin.

Manzon ya yi imani da abin da aka saukar gare shi daga Ubangijinsa, haka ma muminai; kowanne ya yi imani da Allah, da Mala'ikunsa, da litattafansa, da Manzanninsa, (suna cewa) ba ma rarrabewa tsakanin daya daga cikin Manzanninsa. Kuma suka ce mun ji (abin da Ka umarce mu da shi, ji na karba) kuma mun bi. Gafararka muke roko ya Ubangiji, kuma gare Ka makoma take. Allah ba ya dora wa rai (wani abu sai abin da yake da ikon aikata shi; abin da ya aikata (na alheri) yana gare shi, kuma abin da ya aikata (na sharri) yana kansa. (Ku ce) 'Ya Ubangijinmu! Kada ka rike mu idan uka manta ko muka yi kuskure. Ya Ubangijinmu! Kada ka dora mana, abin da za mu iya shi ba. Ka yi afuwa a garemu, Ka yi mana gafara, ka ji kan mu. Kai ne Majibincin al'amuranmu, sai ka taimake mu a kan mutane kafirai".


Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Idan dayanku ya tashi daga shimfidarsa sannan ya dawo ya kwarya, to ya karkade ta da gefen gyautonsa sau uku, sannan ya yi Bismillahi, domin bai san abin da ya maye gurbinsa ba bayan ya tashi. Idan ya kwanta ya ce;

بِاسْمِكَ رَبِّي وَضَعْتُ جَنْبِي، وَبِكَ أَرْفَعُهُ، فَإِنْ أَمْسَكْتَ نَفْسِي فَارْحَمْهَا، وَإِنْ أَرْسَلْتَهَا فَاحْفَظْهَا بِمَا تَحْفَظُ بِهِ عِبَادَكَ الصَّالِحِينَ.
Bismika rabbee wada'tu janbee wabika arfa'uh, fa-in amsakta nafsee farhamha, wa-in arsaltaha fahfathha bima tahfazu bihi 'ibadakas-saliheen.

Da sunanka ya Ubangijina na kwana, kuma da izininka ne nake tashi. In ka rike raina (da mutuwa), to Ka ji kanta, in Ka sake ta kuwa, ka kiyaye ta da abin da Kake kiyaye bayinka salihai da shi.


اَللَّهُمَّ إِنَّكَ خَلَقْتَ نَفْسِي وَأَنْتَ تَوَفَّاهَا لَكَ مَمَاتُهَا وَمَحْيَاهَا، إِنْ أَحْيَيْتَهَا فَاحْفَظْهَا، وَإِنْ أَمَتَّهَا فَاغْفِرْ لَهَا. اَللَّهُمَّ إِنَّي أَسْأَلُكَ الْعَافِيَةَ.
Allahumma innaka khalaqta nafsee wa-anta tawaffaha, laka mamatuha wamahyaha in ahyaytaha fahfazha, wa-in amattaha faghfir laha. Allahumma innee as-alukal-'afiyah.

Ya Allah! Kai ne Ka halicci raina, kuma Kai ne Kake karbarsa. Gare ka kadai mutuwarsa da rayuwarsa suke. In ka rayar da shi, to ka kiyaye shi; in Ka dauke shi, to Ka gafarta masa. Ya Allah! Ina rokonka aminci daga dukkan mummuna.

Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya zo kwanciya sai ya sa hannunsa na dama karkashin kuncinsa. Sannan ya ce;
اَللَّهُمَّ قِنِي عَذَابَكَ يَوْمَ تَبْعَثُ عِبَادَكَ. (ثلاثَ مراتٍ)
Allahumma qinee 'azabaka yawma tab'athu 'ibadak. (3).

Ya Allah! Ka kiyashe ni azabarka a ranar da Kake tayar da bayinKa (bayan mutuwa). (su uku).


بِاسْمِكَ اللَّهُمَّ أَمُوتُ وَأَحْيَا.
Bismika l-lahumma amutu wa ahya.
Da sunanka Ya Allah nake mutuwa kuma nake rayuwa.

سُبْحَانَ اللهِ، ثَلاَثًا وَثَلاَثِينَ
وَالْحَمْدُ ِللهِ، ثَلاَثًا وَثَلاَثِينَ
وَاللهُ أَكْبَرْ. ثَلاَثًا وَثَلاَثِينَ.
Subhana l-lah (33),
Al-hamdu li-l-lah (33),
Allahu akbar (33).

Tsarki ya tabbata ga Allah (Sau 33)
Yabo ya tabbata ga Allah (Sau 33)
Allah ne mafi girma (Sau 33).


اَللَّهُمَّ رَبَّ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ وَرَبَّ العَرْشِ الْعَظِيمِ، رَبَّنَا وَرَبَّ كُلِّ شَيْءٍ، فَالِقَ الْحَبِّ وَالنَّوَى، وَمُنَزِّلَ التَّوْرَاةِ وَاْلإِنْجِيلِ،وَالْفُرْقَانَ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ كُلِّ شَيْءٍ أَنْتَ آخِذٌ بِنَاصِيَتِهِ. اَللَّهُمَّ أَنْتَ اْلأَوَّلُ فَلَيْسَ قَبْلَكَ شَيْءٌ،وَأَنْتَ اْلآخِرُ فَلَيْسَ بَعْدَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ الظَّاهِرُ فَلَيْسَ فَوْقَكَ شَيْءٌ،وَأَنْتَ الْبَاطِنُ فَلَيْسَ دُونَكَ شَيْءٌ،اِقْضِ عَنَّا الدَّيْنَ وَأَغْنِنَا مِنَ الْفَقْرِ.
Allahumma rabbas-samawatis-sab'a, warabbal-'arshil-'azeem, rabbana warabba kulli shay', faliqal-habbi wannawa, wamunazzilat-tawra, wal-injeel, walfurqan, a'oothu bika min sharri kulli shayin anta akhithun binasiyatih. Allahumma antal-awwal, falaysa kablaka shay', wa-antal-akhir, falaysa ba'daka shay/, wa-antaz-zahir falaysa fawqaka shay', waantal-batin, falaysa doonaka shay', ikdi 'annad-dayna wa-aghnina minal-faqr.

Ya Allah! Ya Ubangijin sammai bakwai, Ubangijin Al'arshi mai girma, Ubangijinmu kuma Ubangijin komai, mai tsaga kwayar tsiri da kwallon dabino, mai suakar da Attauna da Injila, da Alfurkani! Ina neman tsarinka daga sharrin komai wanda kai ne mai rike da makwarkwadarsa. Ya Allah! Kai ne na farko, babu wani abu kafinka, kai ne na karshe, babu wani abu bayanka, kai ne bayyananne, babu wani abu da yake sama da kai, kai ne boyayye, babu wani abu da yake boyewa gare ka. Ka biya mana basussuka, kuma ka wadatar da mu daga talauci.


اَلْحَمْدُ ِللهِ الَّذِي أَطْعَمَنَا وَسَقَانَا، وَكَفَانَا، وَآوَانَا، فَكَمْ مِمَّنْ لاَ كَافِيَ لَهُ وَلاَ مُؤْوِي .
Alhamdu lillahil-lathee at'amana wasaqana, wakafana, wa-awana, fakam mimman la kafiya lahu wala mu'wee.

Yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ciyar da mu, ya shayar da mu, ya isar mana, ya ba mu makwanci. Da yawa wanda ba shi da ma'ishi, wala mai ba shi makwanci.


اَللَّهُمَّ عَالِمَ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَاطِرَ السَّمَاوَاتِ وَاْلأَرْضِ رَبَّ كُلِّ شَيْءٍ وَمَلِيكَهُ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ نَفْسِي، وَمِنْ شَرِّ الشَّيْطَانِ وَشِرْكِهِ، وَأَنْ أَقْتَرِفَ عَلَى نَفْسِي سُوءاً أَوْ أَجُرَّهُ إِلَى مُسْلِم.
Allahumma 'alimal-ghaybi washshahadah, fatiras-samawati wal-ard, rabba kulli shayin wamaleekah, ashhadu an la ilaha illa ant, a'oozu bika min sharri nafsee wamin sharrish-shaytani washirkih, wa-an aktarifa 'ala nafsee soo-an aw ajurrahu ila muslim.

Ya Allah! Masanin abin da ke fake da na sarari! Mai kagen halittar sammai da kassai! Ubangijin komai, kuma mamallakinsa! Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai kai. Ina neman tsarinka daga sharrin raina, da kuma sharrin shaidan da shirkarsa, da in tsuwurwurtawa kaina wani abu mummuna, ko in jawo shi ga wani Musulumi.

Ya karanta suratu As-sajdah (Alim lam mim, tanzilul) da suratul mulk (tabaraka).


اَللَّهُمَّ أَسْلَمْتُ نَفْسِي إِلَيْكَ، وَفَوَّضْتُ أَمْرِي إِلَيْكَ، وَوَجَّهْتُ وَجْهِي إِلَيْكَ، وَأَلْجَاْتُ ظَهْرِي إِلَيْكَ، رَغْبَةً وَرَهْبَةً إِلَيْكَ، لاَ مَلْجَأَ وَلاَ مَنْجَا مِنْكَ إِلاَّ إِلَيْكَ، آمَنْتُ بِكِتَابِكَ الَّذِي أَنْزَلْتَ وَبِنَبِيِّكَ الَّذِي أَرْسَلْتَ.
Allahumma aslamtu nafsee ilayk, wafawwadtu amree ilayk, wawajjahtu wajhee ilayk, wa-alja'tu zahree ilayk, raghbatan warahbatan ilayk, la maljaa wala manja minka illa ilayk, amantu bikitabikal-lathee anzalt, wabinabiyyikal-lathee arsalt.

Ya Allah! Na sallama raina gare ka, na maid a al'amarina gare ka. Na fuskantar da nufina gare ka, na dogara da kai (a cikin dukkan al'amurana) saboda kwadayin abin da keg are ka, da tsoron ka. Babu mafaka, babu matsira daga gare ka sai zuwa gare ka. Na yi imani da littafinka da ka saukar da kuma Annabinka da ka aiko.



DEDICATED TO.....MY SISTERS😘


Bissimillah Rahmanir Rahim



Page-71-72



---------------Kamoni Inna tayi daga inda nake tsaye ta zaunar dani bisa gado tace;

"Inaso ki fadaman gaskiya inde kin daukeni Uwa ki fadaman waye kike kishi kuma wakike so, daman sone ya sakaki cikin damuwa kusan shekara kenan, fadaman wakike so?"


Kaina na dukar a kasa nace;"Inna mijin yarana kuma ba zai aureni ba".


Inna cikin mamaki tace;"Saboda me zaiki auren naki bayan shiya fara sanin ki, ki fadaman wane gari yake ni zan je na iskeshi"

Ɗafe Inna nayi nace;"Dan Allah Inna kibar maganar addu'ar ki nake nema, inaso ya fita daga zuciya ta, inaso na manta dashi"

Inna tace;"To shikenan jeki dauki Farhana Sani ya wuce"


To nace tare da ajiyar zuciya Allah ya taimake ni bata ji sunan Yarima ba Allah nagode ma haka na ambata.


Haka muke rayuwa cikin kwanciyar hankali koda yaushe cikin addu'a nike Allah ya fitar man da Yarima amman kullun kara son shi nake jinake babu abinda nakeson gani kamar Yarima.

Rayuwa tayi nisa yarana sun girma ina tunanin halin da mahaifina yake ciki amman kullun na kasa fadama Inna gaskiya ina tsoro saide addu'a da nikema mahaifina.




♦♦♦♦♦♦♦♦


*After five years*


Hamrah!! Hamrah!

"Yes Mom"

Cikin sauri wata yar yarinya mai kyau kamar diyar larabawa ta fito daga daki cikin wasu hadaddun kaya.


Dad dinta dake zaune hankalin shi yana kan abi nda yake zanawa ta matso kusa dashi.

Tace;"Dad"

Dagowa yayi da murmushi yana kallon ta cikin sauri ta rungume shi tana murmushi.


Kulsoom dake kallon su tana tsaye tana murmushi tace;"Architecture Man zamuje shopping gobe zamuje walimar Nifra fa a London ya kamata muje musiya mata gift din da zamu bata, da kuma kayan amfani, Hamrah na bukatar shopping akwai kayan gyaran gashin da zata bukata"


Murmushi yayi yana kallon Hamrah dake kwance a jikin shi.

Cikin sauri ta mike tace;"please Dad don't say no"

Kulsoom tace;"mutafi"

Daga kai yayi cikin sauri Hamrah tayi mashi kiss a kumatu tace;"Thank you Dad"

Cikin murna da tsalle sukabar gidan.


Kallon abinda ya zana yake.

Macece da ciki a cikin gida tana tsaye bakin turmi kamar mai daka yarasa miyasa yayi zanen haka hakanan yakejin shi yau kamar Wanda ya manta wani abu yana kokarin tunawa.


Runtse ido yayi yana tunanin wani Abu kamar yanason tuna wani abu.


Tashi yayi jin kan shi na sarawa yayi bedroom dinshi.

Jin yanayin jikin shi duk ya chanza yasa yayi tsoki alwala yayi yazo ya dauki Al-qura'ani kozai samu saukin tsikarin da jikin shi ke mashi.


Yasin ya bude yana karantawa a hankali yaji ya fara samun natsuwa har ya gamata ya kulle yayi addu'a ya hau gado ya kwanta.


Cikin sauri ya mike daga mafarkin da yake jikin shi har kyarma yake saboda razana.


Kanshi ya rike dake juyawa gani yake kamar yayi missing din wani bangare nashi.

Dukar da kanshi yayi kamar yana son tuno wani Abu.


Kulsoom ce ta shigo da Kaya a hannunta cikin kwali bags cikin sauri ta aje ta iso inda yake ganin yanayin shi tace;


"Lapia Prince mike faruwa?"

Kallon ta yayi a galabai ce yace;"akwai wasu mutane dake bukatata ko ?? Nayi missing din wani Abu na rasa minene ki tunaman mi namanta a rayuwata"


Cikin sauri tayi saurin rikeshi tace;"Babu komi Prince mukade ne a rayuwar ka, baka manta kowa ba Dad Mummy Ammie Abie da sisters naka da Brothers dinka muke kenan muke cikin rayuwar ka baka neman kowa"


Janye jikin shi yayi ya kwanta baice komi ba.


Kasa motsi Kulsoom tayi zufa duk ta taso mata.

Cikin sauri ta safka daga bisa gadon tayi daki.


Bedroom dinta ta shiga ta dauki wayar ta ta kira Hanan wayar Hanan bata shiga daman tace mata zasuje Honeymoon ita da mijinta gashi bata kirata ba.


Duk sanyin garin Amman Kulsoom zufa take ta rasa mafita.



♦♦♦♦♦♦♦♦



Zaune nake a tsakiyar tabarma ina ba matan kauyen su Inna karatu.

Karatun ya samo asaline daga ranar da matar Sani ta iske ina koyama su Farhan Sallah ta zaune shine itama tace tana da gyara da yawa batasan haka akeyi kasan cewa basu karatun ba, tace zatazo ta ringa koya mata wasu abubuwa daga nan matan saurin ta suka fara biyota har makwabtan su suka fara, mace tafi ashirin wadda ta safke Qur'ani, yanzu haka saboda yawa da sukayi raba masu lokaci nake wasu da Daddare wasu da yamma, har nafidda malamai a cikin su masu tayani.


Bayan sun gama sun fita.

Murmushi nake hawaye na zubowa yau shekara shidda kenan rabona da mahaifina, burina dana mahaifina sun cika yau nike koyar da wasu, Yau wasune ke amfani da ilimi na yau nice a cikin jama'a suna nunaman so da kauna da kulawa babu kyama ko kadan a tare dasu.



Gaf!! Aka fadoman bisa jiki ana kuka Inna ce ta fito tana cewa lafiya miyasamu yar lelen tawa.


Tashi tayi daga bisa jikina tayi wajen Inna cikin kuka tace;"Inna kinga Hamisu kullun idan muna wasa sai yace bamuda Uba shiyasa ba'a samu firamare dinsu ba"


Shiru nayi na dukar dakai hawaye suka kawoman na tuna rayuwar da nayi cikin gori da kyama nima haka yarana zasuyi?

Sani ne ya shigo yace;"yanzu na duki Hamisun na korashi gida kiyi hakuri yan biyu kema kinada Baba kinji ai kowa yanada Baba"


Murmushi tayi tana goge hawayen ta cikin tsalle ta saki Inna tazo inda Yaya Sani ta rike shi tace;"da gaske Kawu Sani wanene Baban mu ya sunan shi?"

Tana maganar ne cikin farin ciki kamar ba ita bace ke kuka.

Riketa yayi yace;"ke Baban kuma na daban ne a cikin mutane"

Tsalle tayi Farhan dake tsaye ta kamoshi tace;"zokaji za'a fadamana sunan Baban mu, daga yau su Hamisu dasu Indo basa kara mana goriba kuma za'a sakamu a firamare taho muje"


Kamo shi tayi suka tsaya a gaban Sani tace;"Kawu fadimamu gamu"

Cikin murna take maganar hadda rike kugu.

Zugunnawa yayi dai-dai tsawon su ya furta a hankli yace;"Farhana Yarima....."

Bai ida maganar ba tayi tsallai ta rungume Farhan.


Jin sunan wanda akaba yarana a matsayin Uban su yasa na goge hawaye na mike tsaye nayi cikin daki da sauri.


Kuka mai sautine ya kubuce.


Yanzu haka yarana zasu tashi da kallan Uba idan suka girma fa aka fada masu cewa Yarima ba Uban su bane bafa??


Inna ce ta dafani tace;"ki daure ki dauki hakan jarabtar ki"



♦♦♦♦♦♦♦♦



Tun daga lokacin Kulsoom bata koma dakin Anuwar ba

Koda safiya ta waye shiri suke zasu wuce London wajen taron gama makarantar Nifra.


Yau tunda suka tashi babu wanda ya nemi wani tsakanin Anuwar da Kulsoom Anuwar kwata-kwata ji yake baison ganin Kulsoom din ya rasa dalili, shida ada bai iya bacci batare da itaba amman daren jiya jiyayi yanason kadeci kamar shekarun baya.



Yauma haka ta kasan ce ko a cikin jirgi daga ita sai Hamrah suke fira idan Hamrah ta sako shi saide yayi murmushi.


Suna isa daman jiran su akeyi aka dauke su sai makarantar su Nifra inda za'a gabatar da taron.

Sun iske su Dad da Abie da sauran Family a chan anji dadin ganinsu sosai.

Kowa sai daukar Hamrah yake, tare da nunamata so da kauna.


Anyi taro lafiya inda Nifra tazo Best student a cikin dalibai Dad yaji dadi sosai hakan yasa ya shirya mata hadaddiyar walima a Nigeria.


A zaune suke anata fira a cikin parlour yadda Walimar Nifra zata kasan ce.


Mummy ta fahimci daga Anuwar har Kulsoom babu mai sakewa a tunanin ta ko sun samu sabani.


Abie yace;"Amman d'anka zaije Nigeria ko"

Yana maganar yana kallon Dad.

Dad yace;"of Course"

Mummy tace;"ai idan baije walimar Nifra ba saimun samu sabani dashi"

Kowa yayi murmushi Anuwar da baison zuwa Nigeria haka kawai yaji yana son zuwa murmushi yayi ya rasa miya manta.


Kowa yasan Anuwar ya chanza a shekaru hudun da suka wuce, amman wannan haduwar Anuwar yana neman ya koma aina hin Anuwar dinshi.


Mikewa yayi yashiga lambun gida tsayuwa yayi yana tunanin da MANAL nada rai da sun haifi yara tunda yau gashi Nifra har ta gama karatu.

Shiru yayi yana tunanin wani abu, shekarar MANAL ashirin da biyu a duniya kenan?


Murmushi yayi ya saka hannu cikin aljihu.


Mummy ta iske tace;"Anuu"

Juyowa yayi da murmushi tace;"fadaman mike damun ka? Ko bakiyi farin cikin ganin Family naka ba?"

A hankali yace;"No Mummy"


Matsowa tayi inda yake yana kallon tsuntsaye dake wali a cikin Lambun.

Tace;"akwai matsala ko kayi missing din Nigeria ne, dan ka dade ya kamata ace kaje"


Murmushi yayi yace;"Mummy inaji a jikina kamar nayi missing din wani abu, amman narasa minene namanta sai nayi kamar na tuna saina manta"


Murmushi tayi tace;"gamunan mukade Family naka babu abinda ka manta"

Murmushi yayi tace;"yawwa akwai wani zane naka dana taho maka dashi a dakin ka nagan shi sai zuwa dare saina baka idan an natsu, kuma daman shawara nazo na baka"


Maido hankali shi yayi yace;"inaji Mummy shawara akan mifa?"

Tace;"Mai martaba yayi iya kawaici amman yana kewar ka sosai baido fitoba ya fada ne, kaji abinda yace yanzu a parlo basai ya fito direct ba yace kaje Nigeria ba yayi maganar ne cikin hikima kuma na fahimce shi, yarinyar ka tun tana jaririya rabonta da Nigeria batasan kowa ba a Nigeria saimu dake zuwa Spain, ya kamata kaje ko baka dadeba"

Murmushi yayi yace;"to Mummy, nima ai nayi Missing din Family dina"


Yana dariya yace;"hadda Furar Inna"

Yana ambatar fura yayi shiru kamar ya tuna wani abu.


Mummy juyawa tayi tana murmushi ta nufi hanyar parlo.

Shiru yayi yana tunani yace Sani twins Inna sai kumawa??

Dafe kai yayi gaban shi na faduwa yayi rashin alkawari rike kanshi yayi dake juyawa yace;"Nayim a Farhan da Farhana alkawarin zama Uban su sai gashi ban cikaba ya akayi naman ta dasu shekara nawa, nine fa Ubansu nine na zaba masu suna? Miyasa van zama Uba na gari ba?

Dafe kai yayi cikin sauri yabi ta baya ya shiga bedroom dinshi.

Zama yayi saiga Kulsoom ta turo ta shigo kallo daya yayi mata ta dauke.


Murmushi tayi ta shigo a cikin dakin.

Zuwa tayi ta hau gadon da yake zaune, matsawa tayi rungume shi tana shafa mashi gadon baya tanace;"Baby tun jiya naga ka chanja mike faruwa, konayi laifi?"


Ta fadi hakan tana kara kashe mashi ido tare da salo na Kiss.


Zare hannunta tayi daga cikin rigar shi, cikin murmushi ta fara balle mashi ma ballen rigar shi.


Rike mata hannu yayi cikin bacin rai ya nuna mata kofar fita.


Zatayi magana ya zaro ido ya daga mata hannun.

Ganin yadda jikin shi ke tsuma abin har tsoro ya bata ta mike jiki a sanyaye tabar dakin.



Tashi yayi ya kulle dakin ya kulle wayar shi.


Banda zufa babu abinda ke kararo mashi yanzu ina zaiga yaran Nan?


Yana son su da yawa tambayar kanshi yake miyasa ya manta komi na rayuwar shi??


Jin ana bugun kofar yasa cikin daga murya ke tambayar waye.


"Mummy ce"


Cikin sauri yazo ya bude mata dauke take da teren abinci amsa yayi ya aje bisa Coppe table din dake gefen gadon.


Zaunar dashi tayi ta zuba mashi abinci.


Zaiyi magana tace;"idan kanaso na baka ajiyar ka to kaci"


Ya danci abincin kadan Mummy tace;"Mike damun ka? bayan kaima burin ka na duniya ya cika, kazama Architect"

Murmushi tayi tace;"kada kamanta saboda MANAL yasa ka zabi Architect"

Cikin sauri ya kalleta tace;"Bazan manta ranar wata Friday na iskeku a bayan gida tana coloring din drawing din da tayi, kace mita zana tace kaine na zama dani a cikin gidan mu saboda inaso mubar masu Mummy nan mukoma wannan saboda nagaji da fadaman Mummy, kayi murmushi kace yayi kyau, amman bari na gyara maki, daka gyara mata tayi murna tace yafi nata kyau, tace maka idan zakayi karatu mizaka karanta kace medicine Dad ya zaba maka ta bata fuska kamar zatayi kuka tace a'a ita tafiso kaje ka karanto zane saboda ka zanata da gidan da zaku zauna kace to shikenan tace bata yadda ba saika mata alkawari ganin zatayi kuka kayi mata alkawari"


Cikin mamaki yake kallon Mummy lallai anyi haka.


Mummy tace;"murna ya kamata kayi ka sabke alkawari kuma ka zanata burinka ya cika, to Anuwar ka fadaman minene matsalar kodan Kulsoom bata kara haihuwa bane? Na mata magana tace ku duka baku da matsala Allah ne bai kawo ba wai har ganin Doctor kuna zuwa domin ku kara haihuwa, to inma shine nasan kanason yara da yawa amman kayi hakuri komi lokacine zaku samu koba yanzu ba insha Allah"


"Kayi murmushi Anuu dina"

Murmushi yayi ta mika mashi abinda ke hannunta.



Ya bude yana fudewa gaban shi ya fadi yace;

"Nanah Maifura...!"


Mummy cikin mamaki take kallon kode ya rude aljanar tasake yi mashi suffar MANAL ko Aljanar ta dawo mashi.



Mummy tace;"Kode MANAL"


Yace;"No Mummy Nanah ce"

Mummy kallon shi take cikin mamaki tace;

"Nanah....?"




MARYAM D'ANKUDII{QURRAH}
*JARABTAR MU*




*Written by-Qurrah✍🏻*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'a Yayin da Mutum ya juya a cikin kwanciyar Barci.*

لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ الوَاحِدُ القَهَّارُ، رَبُّ السَّمَوَاتِ وَاْلأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا، الْعَزِيزُ الْغَفَّارُ.
La ilaha illal-lahul-wahidul-qahhar, rabbus-samawati wama baynahuma, al'azeezul-ghaffar".

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, makadaici, marinjaye, ubangijin sammai da kasa da abin da ke tsakaninsu, mabuwayi, mai yawan gafara.


DEDICATED TO.....MY SISTERS😘


Bissimillah Rahmanir Rahim



Page-73-74



---------------Murmushi yayi yace;"Kada ki damu Mummy naga duk kin ruɗe, please Mummy ki fahimce ni wallahi ba Aljana bace Mummy mutum ce har mahaifinta na gani munyi magana a shekarun baya, Mummy bansan ya a kayi ba na manta da ita yanzu Mummy ina buƙatar taimakon ki idan muka koma Nigeria daga ke sai Ammie ne zaku iya fahimta ta, Mummy ki taimaka man, saboda tafiyar ta na kama data MANAL idan suna gudu hakan yasa na saka mata fuskar MANAL".


Ƙara riƙe hannun shi tayi tace;"Na yadda da kai Anuu amman kasan matsalar guda ce, ba zan goya maka bayan ka ƙara zuwa wannan kauyen ba, kai ko Katsina ban amince kaje ba, saidai abu guda zan maka ina so ka saka Sani yaje garin su yarinyar yaji minene labari sunji labarin ta idan babu labarin ta to taimako guda zan maka tunda kace baka san fuskarta ba cikin dare abin ya faru, kuma basu da hoton ta ina da wata dubara".


Cikin sauri

Please Login or Register in order to submit comment