Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suma sunyi tas.

Na fito ta miko min Fantekar zogala tace. "ki dauki ashirin kici abinchi salan ki batar man da kudii".

Nace, "wallahi Inna akwai nisa zuwa Katsina, dan Allah kiban ko na ragin hanya ne".

"Lallai ma yarinyar nan, ni zaki fada ma nisan Katsina, ba'a ba BATAGARAWA kuke tallah ba yaushe kuka shiga Katsina?? to bari kiji daga Yau kasa zaki dawo kuma ai ba cikin gari kuke shiga ba ba iyakar ku nan bakin titi ba?? Bace min da gani!".


Na nada gammo na aza fantekar, ga nauyin kaya ga tafiya ga gajiyar aikin gida, lallai kam, kowa ne bawa da kalar tasa Jarabta ni kuma matar uba, na juya nazo fita muka yi karo da Ma'u saura kadan na saki fantekar zogalan.

"Wayyo Allah Innan mu ta kona ni, ashe zogalan bai huce ba ta aza min fanteka a goshi. "nace amman Ma'u baki son gaskiya".

Inna na zuwa ta wanka min mari tace, "yar bakin ciki fuskar tata zaki kone, toh ta Allah ba taki ba!". Ma'u tace cikin kuka, "daman tace sai ta rabani da Kabiru na shi ne zata kone min fuska dan ya bar ganin kyau na". Fantekar dake kaina Inna ta sabke ta fara Jibga ta kamar kayan wanki tana cewa, "yanzu bakin ciki kike min na zama sirikar dan Mai garii?? Shegiya ai gara na kashe ki damu rasa Kabiru, gidan sarautar kike ma bakin ciki kuma sai ta shiga".

Ko da ta sakeni na wahala tace, "tashi ki tafi sai kinje tallar".


Saboda wahala idona har rufewa yake gashi ta fasa min jiki inda ta bugan da takalmi.

Da kyar na aza fantekar bisa kaina, takalmina daya ya tsinke haka nasa shi na fito ina kama bango.

Babu mai sona a cikin garin yanzu, daban ratse ma mutane ba duk inda na wuce sai ace shegiya ce, malam ya tsinto ko ya yima wata ciki, tunda shi kullum cikin yawo yake,wani yace;

"Amma yarinyar tana ban tausayi sai nayi wata shidda ban gan ta ba saboda bata shiga jama'a", dayan yace, "to wai ya aka yi aka san ita shegiya ce??".

"Matar shi ya fada ma wa, ka san wasu matan ba rufin asiri, ita kuma ta barbada gari". Duk da banda kuzari amman na kagara n abar wajen, sai wani daman diyan zina ance kyau garesu ga shedanan.


Ina wuce su duk inda na gifta da kalar nasu zancan, wasu kuma sai suce Liman bazai iya aikatawa ba sharrin matane, saboda kishi yasa take cewa haka.


Ina fita gari na samu wata bishiya na zauna saboda kaya da suka shigan man cikin kafa, ga kaina na wani irin zafi har cikin kwanyata, ga jikina wani wuri duk ya fashe zafi ta ko Ina, gashi yau garin zafi ake yi ga rana.


Wai daman haka rashin galihu yake?! Ina ma zan samu wanda zai ce yana sona nabar masu gidan su, kai hadda garin ma yanzu banda madafa sai Allah, ya Allah kayi mini magani.

Zafi tako ina nike ji, hawaye nake yi masu zafi, shin wacece ni, nima diya ce kamar saura??

Wannan wace irin duniya ce nake ciki, kayar data shige min cikin kafa duk na fidda, kana na samu leda na daure takalmi na.

Ganin an kusa a zuhur kuma Ina hangen kauyan mu yasa nayi saurin mikewa, ji nayi jikina yayi min nauyi hakanan na aza Fantekar a kaina, na fara tafiya kamar zan fadi, ina cije lebe ina runtse ido, juya wa nayi saboda kukan shanu da naji. "lah Nana!". Inji jabe dan gidan su Shatu"da kyar na dago kai nayi murmushi, "ina zaki haka jikin ki duk ciwo?".

Nace, "Katsina zanje nan BATAGARAWA kamin ka shiga cikin gari inda motocin garin mu ke tsayawa".

Yace, "Amma dai ba'a kasa ko? Me yasa baki hau babur ba? Gashi duk jikin ki da ciwuka".

Nace Jabe taimaka man ka sauke min fantekar nan, faduwa zan yi".

Cikin sauri ya sauko daga bisa amalanken shanun su, yana sabluke min naji kaina ya rike saboda nauyi"yace muje kihau Amalanken na taimaka maki bari na gyara buhun hunan ciki"na daga kai.


A ciki na zauna shi kuma yana jan Amalanken na dukar da kaina ina hawaye,inama ba'a haifeni ba a cikin duniyar nan.



**************

A hankali yake tafiyar har ya iso inda Momy ke zaune"tace Prince ina zuwa nagan ka cikin shigar manyan kaya?gashi Dadyn ku yana Meeting"zanje naga Abie.


"Zo nan!", tace tare da da nuna kusa da ita,"kallonshi take, bayan ya zauna cike da kauna da tausayi tace;

"kayi hakuri, ko wane dan Adam yana da tashi jarabawa mu kuma wannan ita ce tamu Jarabtar, kayi hakuri ka amshi Kursim a matsayin Manal, ko dan lafiyar Mai martaba, ka tausaya ma Anty Amina hakuri take amman abun na damunta, dan bata da yadda za tayi, kuma yarinyar za kaji dadin zama da ita, Lawyer ce ta mallaki hankalin kanta, kaga tana da dubaru kalar nasu na Lawyers ta san yadda zata zauna dakai, haka Dadyn ka zaiyi farin ciki nima haka".


Shiru yayi sai kuma ya kalleta yayi murmushi tare da daga kai alamar aminta.


Nifra ce ta shigo falon cikin wasu hadadun riga da wando rigar kayan kamar Suit Amman ba Suit bane.takalman ta Pink wasu higher hill masu belt ta daure kafar ta dasu sai stones din su Blact yalwataccen gashin kanta ta kamashi waje daya ya sabko har a kafa darta wani kalar hulane akan ta.

Kallo daya Annuwar yayi mata ya dauke kai.

"Momy zanje na dawo yanzu", tace amman kin san idan kuna Nigeria baku fita ko??".

"Momy daga ni sai driver zan fita bana bukatar jiniyya".

"kina hauka ne??".

"Baza ki fita ko ina ba bace min dagami".

"Please Yaya Anu said something mana".

Momy bari mufita tare zanje airport sai akaita inda zata amman ko One hour ban yadda kiyi ba".

Momy tace, "to shikenan", tsalle Nifra tayi tare da rungume Annuwar tare da manna mashi kiss a kumatu"thank you so much Broth!", raba ta yayi daga jikinshi yayi gaba tabi bayan shi.


Suna fitowa security suka rufa masu baya, motar Soja uku gaba uku baya haka suka sasu tsakiyya.


*************

Ranar dake bugun gadon bayana hakan yasa jikina naji kamar ana tsikarina, na dago daga duken da nike.


Muna kaiwa yace; "Nanah munzo", nace to jabe na nagode ina gaida Shatu".

"Zata ji yau ita kiywo ta tafi bata tallah yau sai dai gobe".

Nace, "to shikenan nagode".

Na aje fantekata inda na saba zama ni da Shatu duk sai naji babu dadi ni kadai haka jiyama ni kadai yauma.


Dan danan zogalata ta kare koda yamma tayi har na saida,na isa inda zan hau mota,sai kuma na tuna Inna tace kasa zan dawo,na juya Matii yace"yar gidan Liman mantuwa kikayi ne da zaki koma"nace a'a zanje a kafa akwai ganyen da zan dibar ma Innata a bisa hanya,yace "amman ai kwai nisa daganan kizo ko tudu na kaiki sai ki ida"nace kayi hakuri Matii yau banda kudin mota"shiru yayi yana kallona sai kuma yace bakomi muje daga yau zan dunga daukar ki inde nazo wannan tashar"nace to nagode.


Na kama na hau yauma gefe na zauna kamar kullun,bana shiga cikin yan matan Tudu,daman sunfi na kauyan mu rashin kunya.


Yauma su kade suka kama habaicin su,yau basu san ban koda lokacin su zafi da radadin da jikina keman sun isheni,zafi har cikin kaina,muna isa Tudu na sabka naje nayima Matii godiya yace bakomi,yima kaine,duk na ina cikin wahala amman naji dadin taimakon shi,saboda bainuna kyama taba,kuma dan garin mune yasan komi a kaina Amman Tudu yake zaune dan tafi kauyen mu,kauyan mu ko hanyar Mota babu saide ka yanki daji da Mota amman Tudu akwai hanyar Mota kuma sukeda Kansila.


Sauri nike cikin daji babu kowa sai karar tsuntsaye,haka naita ratse a cikin gonaki har na isa.


Ina shiga duhu ya fara sabkowa nayi sauri nabi ta baya na nufi gida.

Gabana na faduwa nayi sallama.

Baba na iske cikin gida tsaye shida Inna yana fada.

"Alhamdulillah"shine abinda ya fito daga bakin Baba"yace sannu Nana kindawo kiyi hakuri nafita ban fadi maki ba daga salar asuba na wuce wani kauye chan gabashin mu dan nasamo mashi wani magani akwai nisa shiyasa daga masallaci na wuce"nace ba komi Baba andawo lafiya??

Kallo ya bini dashi.

"Me nake gani a fuskar ki kamar sawon hannu??".

Nace; "umm daman...".

"Ai ko kila faduwa tayi fuskarta ta bugu".

Cewar innah. Nace, "eh daman dazun na buge".

"Allah ya sawaka".

Yace, daga haka bai ce komai ba. Yace, "tafi kiyi sallah sai ki aza maganin a tukunya??".

Innah tace, "Amman dai ai lafiyar ta kalau daman akwai maganin karin lafiya da baka yar kin taka ba".

Kallon ta yayi yace, "amman kinsan tana da rauni a cikin cikin ta ko".

Amman Malam shekara nawa da wannan rauni kuma bai taba tashi ba??".

Baiyi magana ba ya bar wajen.


"Miko min kudina".

Na warware zani na na bata, tace, "malam ya biyo ta gona yace na debe mashi Zogala dan haka yanzu Fura zamu yi, kwana biyu har ya tuho. "to nace tare da tunanin kirbin fura gobe ga jikina yayi tsami ko Ina ciwo yake min.

Alwala nayi tace, "ga tuwon ki chan Madafi idan awaki suka cinye kin huta".

Naje na dauko cikin wata roba, miyar ya kadan ko rufe tuwon bata yi ba.

Bayan na gama Sallah naci abinci, na aza kaina bisa gadon karan dake dakina, ina runtse ido saboda zafii.

Ina zaune naga dare yayi na mike nace bari naje dakin Baba.

Yau yana zaure saboda babu sanyi,nayi sallama na cire ta kalma na na zauna"yace kin aza magani ko dan kullun zaki ringa sha kamar ruwa har ya sallace yazamana ba daci"ciwon zai shafe insha Allah kamar baki taba yiba saboda kin girma yanzu kullun da ciwon nike kwana dan kada ya hanaki haihuwa ciwon nada matsala amman yanzu wannan maganin insha Allah shine waraka gefen cikin ki zai zama lafiya kalau"nace to Baba Allah ya saka da Alkhairi yace"Amin Allah ya kawo maki dauki a cikin rayuwar ki kisamu sauki"na mike naje na aza maganin nadawo na zauna.

Ya mikoman wata leda yace"ga kyautar ki ga kuma Sabon littafi"na amsa cikin murna nace nagode Baba Allah ya biya yasaka maka da Aljannah"Amin ya ammabata cikin jin dadi"har na bude yafara biya man saiga Ma'u da sallama kamar ansata dole"yace ke sai yanzu zaki fito"nide nayi saurin boye ledar da Baba yaban kada ta gani.

Juyar da kai tayi tace"kaina keman ciwo"baice komi ya idaman na mike nace Baba saida safe"yace ga magani na amso maki wajen Kabiru"(saurayi Ma'u dan Mai gari shikade keda kyamis shima ba karatu yayiba koya mashi a kayi).


Na amsa nace nagode nabar wajen cikin sauri ina boye laidata cikin Hijab.

Ina zuwa daki nace Wash na bude ledar,Turare ne irin na dure nayi murmushi nace kyautar turare tana faran taman rai inason kamshi,sai kuma naji wata leda daman tun chan naji kamshi shiyasa nayi saurin tashi kada Ma'u ta jiyo.

Miyau na har tsun kewa yake tun naman sallah rabona da Nama dan ko Baba ya kawo saide na hangeshi,naci na koshi na dugun kune takar dar,na fito na yadda ta bayan gida nasamu kohi naje na debo ruwan magani na nataho daki Ina jiran su sha iska,maganin da Baba yaban na balli biyu nasha,magani naji ya huce nasha na kwanta.

Duk wahalar dana sha yau amman naji raina yayiman haske.

Saide faduwar gaban dake ziyar tata lokaci zuwa lokaci narasa minene dalili?

Nayi addu'a na juya bisa gadon karana.



*************

Tunda ya iso gidan baije part din kowa ba saide abinci da aka cikashi dashi.


Ganin karfe tara na dare yasa ya fito domin zuwa part din Mai martaba.

Ko Ina na gidan bayi ne, duk inda ya gifta banda kirari babu abinda ake.


Wani abu mai kama da kaho kalar suffarshi amman na silver ne, aka fara hurawa, wannan shine shaidar yarima ya fito, kamin minti daya ta ko Ina fadawa ne ke fitowa cikin azama a jere.

Wasu na shimfida capet inda zai taka wasu na nadewa, ata kuma sai saka turaren masu dadin kamshi suke cikin lokaci kadan gida ya dauki kamshi gidan ya zama tamkar safiya.


Kirari ta ko Ina kamshi tako ina.

Har ya isa part din Mai martaba.

Fadawan dake bin bayan shi ya daga hannu suka juya, wadan dake tsaye bakin kofa Mai martaba suka fara kirari;

"Allah ya taimaki sarki na gobe mai jiran gado ., duk Al'umma nama Yarima sannu da zuwa tareda fatan farin ciki a rayuwar yarima, sarauta gado ce ba haye ba shine babba dan babba jirgi mai masoya da yawa,Mai martaba yace ayi maka iso yana farin cikin ganin Yarima a wannan lokacin!". Aka bude ya shiga, ido hudu suka yi da Mai martaba ya dukar da kansa a kasa, saboda yadda Abie yayi masa kwarjini.


A kasa kusa da shi ya zauna tare da da dukar da kai cikin muryar sa mai sanyi yace;

"Allah ya taimaki Mai martaba, tuba nike ayi min afuwa ba zan kara kuskure irin wannan ba".


"Taso kadawo inda nike ina bukatar naji dumin Yarima na".

Murmushi yayi ya hau kujerar dake kusa dana sarkin.

Cikin kulawa yace, "Na san baka ci komi ba".

"Naci", inji Yarima bayan tun Breakfast din da yayi a Abuja.

"Kayi hakuri Yarima na san kana cikin matsala, amman insha Allah Kursim zata kawo karshen matsalar". Shi ine Yarima shiru yayi amman ya san abinda ba zai yiwu bane.

"Ina jin ciwon yadda magajina ya kasa farin ciki tsawon shekara bakwai, na san kana son Manal Amman mahaifanta tama, shekarar Abdulrahman ashirin bai samu haihuwa va sai akan Manal, kaddara ta raba su kuma ya dangana haka Mahaifiyar ta, ka duba kaga tsawon shekarun da suka yi ba haihuwa kasan ko ba karamin so zasu yi mata ba, da ace Uba na sayan ran dansa da Abdulrahman ko tsiyacewa zai yi yafi son diyar sa akan komai, kaddara ce ta raba su kuma ya dangana, ina so kaima ka dangana".

Kara dukar da kai yayi.


"Yanzu an shirya komi gobe zaka wuce Katsina, kuma na san zaka ji dadin zaman garin".

"To Abie, duk yadda kace haka zanyi bana bukatar fushin ka akaina".

"Ina son ka zama mutum kamar kowa, tun da Manal tabar duniya ka rufe karatu jin dadin rayuwa bama ka zama kasar, dan kada ka shiga jama'a, dole na damu, ina son ka zama kamar kowa, da ana sayen farin ciki da tuni na siyo maka".

Murmushi yayi wanda ya dade bai yi irinsa ba, yace, "Abie ka kwantar da hankalin ka, gobe zanje amman dan Allah arage min kwanaki".

"Cikin jin dadi yace, "ba zai yiyu ba, ina so ku saba, kaga sai asaka bikin kamar sati biyu".


"To shikenan Abie yanzu sai da safe".

Murmushi Abie yayi har da hawayen farin ciki.

"Kaje Ammin ka ta ganka, na san zata yi farin ciki".

Daga kai nayi na fita ina murmushi.

Lalle mahakurci mawadaci, yau addua'r sarki AbdulAziz ta karbu.

Ta hanyar da Mai martaba yake bi yabi yaje part din Hajiya Amina.


Zaune take cikin kayataccen falon ta, waya take kuyangunta na kasa.

Sallama yayi ya shigo dauke da Murmushi a fuskar shi.

Baki Hajiya Amina ta saki tana kallon shi cikin mamaki.

Ajiye wayar hannun ta tayi, ta mike cikin azama taje gaban shi.

"Wannan shine Yarima na, ko an chanza min ne kodai mafarki ne kalar wanda na saba?"

"Allah ya taimaki Uwar gidan sarki ya kara lafiya da daukaka wannan ba Mafarki bane,Yarima dan sarki jikan sarki shine a gaban ki".

Hannu ta saka ta jawo shi tace, "muje".

Ba musu ya bita, Bedroom suka nufa, kuyangu suka bisu da kayan marmari.

Suna zama bakin gado Yarima ya daga hannu.

Kuyangun suka ce, "muna godiya kuma muna farin ciki da ganin magajin sarki a yau!". Suka bar wajen.


Hawayen dake bin fuskar Ammi yasa hannu yana gogewa.

"Ya isa haka Ammi na tuba na san na bata maki".

Saukowa tayi takai kanta kasa tayi Sujjada.

"Yanzu Yarima na zai zauna dani zaibi umarnina kamar yadda yake ada".

Daga kai yayi tareda murmushi.

Tace, "jiya kanwar ka ta haihu.Na kiraka na fada maka waya a kashe".

Me ta samune?".

"MANAL ta haifa". Murmushi yayi ya rungume Ammi.

"Ta samu matsala amman nan da sati biyu zata dawo, yanzu suna Spain a chan ta haihu".

"Allah ya raya akan sunnah".

"Amin". Sun dade har dare yayi kana yayi sallama ya nufi part dinshi.


Lumshe ido yayi tare da shakar kamshin falon shi.

Kai tsaye toilet yana nufa cikin saurin ma a'ikatan daya ya nufi toilet daya ya tsaya cire mashi alkabba.

Koda ya shiga an hada mashi ruwa a cikin bahon wanka ruwa masu kamshi shi komi nashi mai kamshi ne.

Bayan ya fito ya iske kayan bacci ya saka tareda takalma yauma bakin window yazo yayi tsaye yana tunanin zaman da zaiyi a wata masarauta.


Har dare yayi kana yaje ya kwanta tareda Addu'ar bacci.

Bayan yadawo sallar asuba ya kwanta sai wajen tara ya tashi.

Cikin sauri ya mike toilet ya shiga yayo wanka koda ya fito an chanza zanen gado angyara dakin sai kamshi dake tashi.

Kaya ya saka tareda saka Alkyab.

Ganin jikuna yayi ana fita dasu na kayan shi, murmushi yayi yanufi part din Hajiya.

Yauma kamar jiya saida akayi shelar fitowar Yarima shiyasa kamshi ta ko Ina a gidan.

Tare da mai martaba da Ammi suka yi Breakfast, bayan sun gama Ammi tace yaje part din iyayen shi su gaisa(kishi yoyinta)

Dakin Hajiya Sa'adatu ya fara zuwa ita kebima Ammi sai Hajiya Hadiza suma mamaki ne a tareda dasu amman suka boye.

Kannan shi cikin sakin fuska duk suka gaisa.

Ban kwana yayi da Ammi, mai martaba har bakin motocin da zasu kai shi airport yake, gida ya zama kamar ana wani biki,kide-kide da bushe-bushe kalar na sarauta kamshi kota Ina.

Hannu mai martaba yasa ya bude mashi murfin mota.

Murmushi yayi yace, "nagode".

Ya shiga ya kulle har suka fita yana wajen tsaye.

Lumshe ido yayi yana tunanin, saboda faduwar gaba dake ziyartar shi. Addu'a yake sai kuma yaji sanyi na shigarshi.

Lokaci guda ya ji yana son zuwa garin Katsina, har ma yana mantawa da neman aure za shi, ya rasa dalili sai kuma yaji daukin zuwa garin yake chan.

Komi zai faru a katsina??

🤭OHO😅😜


*Qurrah*
[1/28, 3:02 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: *JARABTAR MU*



*Writing by-Qurrah*


Page -7-8



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*~Addu'ar Wanda Ya ji Tsoron Faruwar Wani Abu Mummuna saboda Kambun Baka~*


Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Idan dayanku ya ga wani abu da ya kayatar da shi ga dan uwansa, ko ga kansa, ko ga dukiyarsa, to ya roki Allah ya sanya albarka gare shi; domin kambun baka gaskiya ne.


Page -7-8


DEDICATED TO.....MY SISTERS😘



_Bissimillah Rahmanir_ _Rahim_



----------------Kuka nike tamkar raina zai fita,dalilin kukan da nike kaina har ya fara ciwo,wannan wane rashin kauna ne??arasa wanda za'a hadani dashi duk kauyan nan sai Lado,miyasa Inna zata man haka??nikam bari Baba yazo idan har yana sona ya kaini wajen dangin Uwata,koya suke nasan zasu soni,zanyi biyayya akan komai amman banda wannan saidai idan Baba ya furta da kanshi babu yadda zanyi,dole nayi mashi biyayya tunda Uba ne musulunci ya bashi damar ya zaba ma diyarsa Miji nagari,wata zuciyar tace "kenan yanzu idan Baba yace ki aure shi kenan yarda zakiyi?"

Runtse ido nayi kamar ina magana da wani,nace;" to ya zanyi tunda shi ya haifeni"

Nayi ta gumi ina jiran shigowar Baba.


*************

A hankali Kursim ke yin tako rigar data saka kuyangu na dauke wa,saboda jan kasa da take.


Tsaye yake ana saka mashi Alkyabba madubi aka kawo mashi,dai-dai fuskar shi ya kallah ya dauke kai,yayi hanyar fita cikin dakin,dogaran dake tsaye bakin dakin suka fara kirari,bai kula yabi hanyar da zata sadashi da lambun da aka hada dominsa,tafe yake tareda da yan jagora.

Yana zuwa ya zauna ya dagama na bayan shi hannu"godiya muke dan sarki jikan sarki"daga hannu yayi saboda baison haya niyyar suka bar wajen,sai guda da ya tsaya ya gyara mashi Alkyabba shi tareda cewa"Ina nema izini wajen shugabana zanbar wajen koda abinda kake bukata?"tare da dukar da kanshi a kasa.

Da kai yayi mashi nuni yabar wurin.


Lumshe ido yayi ya rasa mike mashi dadi,a hankali ya bude idon shi jin kamshi mai dadin gaske ya bugi hancin shi.

A kan fuskar Kursim idon shi ya sabka"murmushi ta sakar mashi irin wanda tasan kowa ne namjii tayi mashi sai ya rude"kauda kai yayi har ta iso,matan dake tare da ita suka gyara mata riga ta zauna bisa kujerar dake kusa dashi,ta daga masu hannu subar wajen "suka ce godiya muke Gimbiya sarauniyar kyau farin cikin Sadauki Yarima Annuwar" murmushi tayi da alama taji dadi suka bar wajen ta maido kallon ta ga Yarima,tana kara gyara zama.

Lumshe ido tayi cikin zuciyar ta tace, "daman nasan zanyi fama dakai Yarima" ta bude fararen idanun ta akan shi.

Tare da cewa; "Nayi farin ciki da ganin Prince dina a cikin ƙoshin lafiya, Masarautar da mutanen cikin ta suna farin ciki da ganin Prince Annuwar a cikin wannan gida,da zuciya zata bude idon ka domin kaga abinda ke ciki na tabbata da zakaji kaina kuma zaka ban gurbi na zama abokiyar rayuwar ka,zan amince ma kowa ce ukuba inde Prince zai zauna dani,zan kansan ce mai hakuri da juriyya akan abin da nikeso".


Ko motsi baiyi ba daga inda yake zaune tamkar ma baijin yaren da take magana ba, da turanci tayi maganar amman tamkar da wani yare wanda bai taba jiba,saboda yadda yana yinshi ya nuna,babu alamar yaji maganar ta,kuma yaji duk abinda tace saide tamkar dutse haka yake.

Jim tayi tana tunanin me zata ce sai kuma tayi murmushi ta bude baki zata yi magana, "umm....!!"daga hannu yayi a hankali cikin muryar shi wacce take kamar yana rada yace "Am feeling sleep" baki ta saki tana kallon shi "Take this;he said" wani abune ya miko mata kamar gift "No need tace" it is not money" ya fada.

Sai a lokacin ya kalleta yace"it is a shame that you should visit a person like me and go away empty handed".

Amsa tayi tace"thank you"baice komi ba ya mike itama ta mike"take care of your self"ya dan waigo yace"thank you"taji dadi sosai thank you da yace mata"ashe tun dazun yana jina?? lalle koba yanzu ba kalmomi na zasu yi tasiri kenan a zuciyar ka "tsaye tayi har ta dena hangen shi.

Tana juyowa suka hada ido da Hanan,tare suka sakar ma juna murmushi Kursim tace "tun yaushe kike nan kinzo ki min sa ido ko?"dariya Hanan tayi tace"muje ciki Princess akwai magana amman fa ba ido nasa maku ba yanzu nazo wajen, lokacin ku duka kun mike,lallekam naga ansha soyayya"duka Kursim takai mata tareda cewa,"banson wulakanci".


Tare suka jera suka shiga part din Kursim,kuyan gunta suka kama mata ta cire rigar, lokacin an hada mata ruwa cikin bahon wanka,shiga tayi tana sinsinar kamshin ruwan tana lumshe ido,idan ta tuna Cool voice din shi,kamar mai motsa baki,shiru tayi cikin ruwan tana hangon fuskar shi jinta take tamkar yana kusa da ita,haka tayita lumshe ido, saida taji maganar Hanan kana tayi sauri ta fito tana daure da towul,a gaban mirror ta zauna,kuyan gunta suka gyara mata kai suka fidda mata kayan da zata saka,zasu safa mata Mai ta daga hannu,suka fita.

Hanan na bisa gado na latsar wayar ta.

Har Kursim ta gama"wai kinsan wani abu inji Hanan?"girgiza kai Kursim tayi"wallahi ban taba ganin guy din da zaiyi kyau da soyayya ba kamar wannan"bata fuska Kursim tayi tare da cewa"mikika gani kenan har kin kalleman miji ko?"

Dariya Hanan tayi tace"ohh sorry my friend bamu haka da ke,kawai de wasu colour eyes na gani wajen shi,wanda kallon su kade zai iya ruda mace"Yanzu de shikenan ya isa nifa ba kyaun shi yasa nike son shiba haka kawai Allah ya hada jini na da nashi.

Kallon kawai Hanan keyi"kinsan dawa nike chart yanzu?wallahi da Ammar nike chart wanda muka hadu dashi a New York kin tuna kika hana mashi number naki,nabashi nawa wallahi sonki yake kamar mi"mtsww Kursim tayi tsoki tare da cewa.

Banison ka Hanan ki dena"i told him that a woman without a husband is like a cloth in the market,idan yayi kokari zai sameki"

"Are you in your senses?"

Kallo Hanan tabita dashi cikin mamaki daga magana duk ta rude kamar wata matar aure"please Hanan kideman haka,tun farko kinsan Annuwar nike so,jina nike tamkar matar shi"zaro ido Hanan tayi"daga mata kai Kursim tayi alamar tabbatar wa"shiru Hanan tayi,tana

Please Login or Register in order to submit comment