Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mikoman mai blue na saka doguwar rigace dai-dai jikina tayiman kyau sosai aza d'ankwalin nayi bisa kai saboda ban iya daurawa ba.

Parlour na fita ina jiran ya fito.

Sai gashi shima yadine jikin shi blue yayi kyau sosai nayi murmushi nace;"yau dakin Ammie zan kwana, yanzu idan naje bansan mi zance ba budeman na wuce dan Allah"

Murmushi yayi yace;"baki biyani daukowar danayi ma Shatu ba daman na daukota danki biyani, sai gashi har yanzu baki biyani ba, kinga kenan sai kin biyani kana na gyale ki, muje a part din Abie zamuyi break nayi waya"

Ido na zaro hawaye zasu zubo nace;"na shiga Ukku Yaya Anuu miyasa zakaman haka yanzu shikenan kowa yasan dakin ka na kwana nashiga ukku yanzu dawane ido zan kalle su"


Murmushi yayi yace;"wasa nake munyi magana da Nifra na fada masu da safe kikazo waje na"

Murmushi nayi nace;"muje"

A part din Abie mukaje duk mutanan gidan na nan hadda su Baba dasu Inna muka gaisa da kowa naje kusa da Baba na zauna na rike hannun yaron Ma'u yayi murmushi.


Abie nan yayi jawabi tare da kara masu Baba godiya da Inna(Maifura) kana yace yanason Baba ya dawo Bauchi da iyalen shi da zama.


Baba yace a'a saboda akwai iyalen Yayan shi da yan uwa kamar bai masu adalci ba.

Mai martaba yace bakomi sunyi maganar da Dad duk za'a dauki nauyin su naji dadi sosai dan nasan duk abinda akayima Baba baza'a a biyashi ba abinda yayi man ba ya dauki tsana da zargin jama'a saboda ni, yabar garin su gaskiya nasan baza'a biya Baba ba kodan kaunar daya nunaman.


Sannan Inna har tadawo cikin gidan daman Yaya Sani an yantashi daga hadimi ya koma D'an gida naji dadi sosai sai Shatu da Dad yace ta zauna har tasamu miji tunda batada aure naji dadi sosai haka aka tashi nanufi part din Ammie achan naci abinci.


Na iske Ammie a daki na zauna tace;"Daman ke nake jira ki gama anshi sha"

Ta mikoman wani abu cikin cup babu gardama nasha.

Tayi murmushi tace;"Nasan Yarima babu hakuri shiyasa na baki kikasha yanzu gobe zaku Abuja su Malam (Baba) Kuma gobe zasu wuce Katsina domin ban kwana kinga dole aje wajen dangi ayi masu bayani kada suji shiru"

Nace;"Ammie nima inason na bisu inason zuwa kauyen mu"

Shiru Ammie tayi tace;"gaskiya hakan ya kamata bari zan ma Maimartaba magana"

Murmushi nayi nace;"yawwa Ammie"

Tace;"yanzu kinci abinci zuwa anjima kadan akwai kaza na nan nasa aka dafa maki"

Murmushi nayi bance komi ba sai yanzu nagane abinda take nufi da bashi da hakuri da tace Yaya Anuu baida.


Fira muke sosai su Farhana suka shigo nabar dakin nayi parlo nan tasa aka daukoman kazata naci ni kade kana nayi part din Inna nabar su nan.


Muna fira da Inna tabani itama wani abu na tamna sannan itama taban wasu ruwa wai Yaya Sani tasa ya samo mata iccen nide nasha hakanan badan nasoba saboda yadda sukeda da'ci.

Nace;"Inna Yau wurin ki zan kwana tare dasu Farhana"

Tace;"Haba Nana saboda fa ku huta yasa na dauke yaran ba wajena suke kwana ba b'angaren Fulani (Ammie) suke kwana kona mahaifiyar ki wanibi kuma Nifra ke zuwa tace suje su kwana"


Nace;"toni Inna gaskiya nagaji a daki daya fa muke kwana dashi amman babu wanda yasani, ina tsoron kada a sani"


Zaro ido Inna tayi tace;"yanzu a daki daya kuke kwana baki fadaman ba nayi maki wani abu"

Nace;"nifa Inna babu abinda ke shiga tsakanin mu"

Tace;"rabani da wannan maganar yaran zamani to yanzu ya kikeso nayi maki shida matar shi nayi maku katan ga, to hakan bazai yiyuba yau nizan shirya ki kuma har bakin kofar Yarima saina kaiki"

Nace;"Kai Inna yanzu goya mashi baya zakiyi"

Murmushi tayi tace;"har yanzu da sauran ki to bari kiji ba'a sake da dama ki chanza tunani ba'ayi ma maza haka"

Mun dade muna fira da Inna duk firar da muke tana kwatan taman yadda zanyi kula miji ne tareda bani labarai nada cikin hikima.

Na dade kana na nufi wajen su Baba nan muke fira dasu Shatu da Ma'u firar mu lafiya kalau cikin kwanciyar hankali labarin kauye muke hadda wakokin kauye nazuwa rafi da daddali da sauran su.

Saida mukaci abinci dare a tare kana nayi masu bankwana nayi part din Mummy.

Nan na iske su Farhana suna wasa.
Mummy tace;"yau ina zaki kwana gobe zamuje Abuja ada hadda ke amman yanzu Dad dinki yace zakije Katsina muma zamuje wajen iyayen Shatu amman mu daga Abuja zamuje sai dan Dad dinki keda meeting"


Nace;"to shikenan Mummy bari naje na kwanta"

Farhana tace;"Ummie saida safe nikam wajen Mummy zan kwana Farhan yace ni kuma wajen Uncle"

Nayi murmushi na fita kai tsaye part din Inna na nufa zan wuce wani waje naji ankama hannu na nayi saurin waigawa nagan shi.

Murmushi yayi man niko tsoro ya kamani.


Zan kwace ya daukeni yayi part din da muke kwana.

A toilet ya sabkeni ya fito na kulle nayi wanka na fito.

Ko kamin ya fito har nasaka kayan bacci na saka turarurruka na hau gado na kulle ido nida tsiya nayi bacci.


Jim kadan naji shi ya hau gadon na daure banyi mutsiba.

Juyowa yayi dani Ina kallon shi nan idona ya fara kyarma.

Murmushi yayi yafara mani wasu wasanni haka dai tun ina turjewa haka yayi galaba akaina.

A ranar Yarima ya kara kusanta ta, nasha wahala tamkar budurwa shi kuma babu abinda yake sai kalamai masu dadi.

Bayan munyi sallar asuba muka koma bacci da safe na shirya nan ma saida ya kara gajiyar dani da kyat nabar part dinshi.

Part din Mummy komi an hada mana na tafiya.

Saida na sake wani wanka kana na chanza Kaya na fito mukayi ma kowa bankwana amman ga mamakina banga Anuwar ba sai Kulsoom data rakomu.

Banda su Farhana zamu tafi, su Mummy zasu tafi dasu a chan zamu hadu.

Har zamu shiga mota ban ganshi ba duk nabi na rude anaman ban kwana hankali na yana ga hanya kozai fito hakanan nashiga mota.

Bayan muje airport Yaya Sani ya mikoman waya yace;"Inji Yarima na amsa"

Haka a airport nayita tunanin zaizo har muka bar Bauchi bai zoba.

Muna isa Katsina kai tsaye Dan-musa muka nufa amman bamu kwana ba munde gaisa da mutane Baba yayi masu bayani bayan la'asar muka nufi Katsina muna zuwa muka wuce Batagarawa.


Anan ne wajen tashar motar naga Matii ya d'an fara manyan ta da motar shi ta kara tsufa sosai mamaki nake daman mota na irin shekaru haka kuma tsohuwa.

Kallo suka bimu dashi na saida motar muka fito dani da Shatu dasu Baba.

Naje wajen Matii na ina Isa ya duka kasa.

Nace;"matii baka ganeni ba yace eh Hajiya bansan kiba"

Shatu tayi daria yace;"a'a Shatu ina kika samu wadan nan mutanan hadda motar soja a bayan su kuma naga kina dariya kuma naga kin chanza ina kika samu wadan nan kayan jikin naki tode mafarki"

Murmushi nayi nace;"Matii zakaje kauyen mu yau"

Nayi maganar kalar yadda nake mashi cikin mamaki yake kara kallona yace;"yar gidan Liman...?"

Nayi dariya nace;"kaga gama Baban chan dasu Ma'u sun fito ashe"

Nan Shatu ta fadi mashi sunan Dad ya zaro ido yana mamaki.

Nace;"Matii daman motar nan na nan? har yanzu tana lalacewa?"

Murmushi yayi yace;"Ban dade da gyarataba ta dade gareji tana son injin amman yanzu lafiya kalau take, amman fa tana tsayawa"

Mukayi murmushi na fidda kudi masu yawa daga jikar hannuna da Mummy ta cikata da yan dubu na bashi kana mukayi ban kwana yace zaizo har gida ya karaman godiya idan na huta zuwa gobe



Muka koma mota muna isa kauyen mu gidan mu muka nufa.


Nan Sani yaje ya kawo katihu daga Katsina muka gyara gidan sosai.

Gidan su Shatu muka nufa nan Naga su Jabe harda iyali an aje ya girma saida Daddare kana Yaya Sani yazo ya daukeni.


Na shiga dakina duk ya kara mutuwa hawaye suka zuboman Baba ya shigo yace;"Dena kuka dare yayi kizo muje dakin Innar ki tana chan ta gyara maki kafita"

Nace;"A'a Baba a dakina zan kwana kallon gadon karana nayi dake jingine da sauran kayana gasunan har sun fara shigewa cikin kasa.

Baba yace;"har nasaida gidan, Wanda ya saya yaki cikaman kudin rabi ya bada dana gaji na maida mashi kudin shi saboda yace baidasu ban taba tunanin zamu kara kwana a gidan nan ba gobe su Maimuna dasu Auwalu zasuzo"

Nayi murmushi saiga Sani yace;"Dad yace amaidani a Katsina na kwana sai fada yake"

Na girgiza kai nace;"Yaya Sani anan zan kwana zanba Dad hakuri"

Yace;"to bari ya daukoman katifun da ya siyo akwai saura"

Nace;"a'a yabar shi"

Ya juya ya fita mukayi ban kwana da Baba na sabke gadon karan da duk gara ta cinye nasa zane na kwanta hawaye nake sosai.

Saiga Inna tana kirana tace;"minene haka Nana ga shimfida chan anmaki hadda sabon bargo da zanan gado Sani ya siyo muje ki kwanta"

Inna tayi-tayi nakiya harda kuka nayi mata akan ta gyaleni

Tunda safe na tashi na share gidan na debo ruwan rijiya nayi wanka.

Fita nayi gonar Baba naje tana nan anan naga Jabe na kiwo yakoje ya kiraman Shatu mun dade kana naje gidan su Ina zuwa sai Yaya Sani a rude su Dad su inso yanata fada inanaje.

Ina zuwa muka gaisa yace;"Manal bade anan kika kwana ba banace ki zabi gidan su Kulsoom ko G-hourse ko Hotel ba miyasa zaki kwana Nan"

Ina daga Ido naga Anuwar na kara kallon shi cikin mamaki.

Nace;"Dad kayi hakuri"

Mummy tace;"a fitoda su Farhana"

Suna fitowa sukazo suka rungume ni suna murna.

Muka shiga gida aka shimfida masu tabarma.

Bayan su gaisa da Baba Dad da Mummy nabin gidan da kallo Mummy tace;"Ina wayar da Yayan ki yabaki tun jiya yake kira a kashe shiyasa yau tun da safe ya sai gashi sai muka taho wayar faduwa tayi ne"


Nace;"ban iya kunna waba tana daki bisa gado"

Nifra tace ina dakin na nuna mata taje ta dauko ta kunna.

Tana shiga ta buga kara da Mummy da Dad da sauran mutane sukayi wajen ta.


Muna zuwa tace;"Mummy kalli bazan iya shigaba dakin ba manyan windows duhu sannan kalli wanchan abu kada ya tsirine kuma sama wayar take"

Na kalleta cikin mamaki dan a tunanina maciji ta gani tunda kusa da daji muke.

Nace;"ai wannan shine dakina kuma wanchan ai gado nane"

Su duka suka shiga suna kallon dakin Mummy hadda kwallah.

Nace;"Mummy nifa nasa kaina kwana anan ina kaunar wurin ne Mummy"

Rungume ni Mummy tayi Nan baya yayi masu jagoranci zuwa gidan su Shatu.

Nida Yaya Anuwar da Nifra mukace kasa zamu hadda Ma'u nace mata mutafi.


Nan na nuna masu gari bayan munje gidan su Shatu muna hanyar dawowa saiga Lado kusa da gidan mu gidan mu mutane sun zagaye mutanan gari hadda mai gari mata da maza.

Ma'u tasha toka tayi tsoki Lado ya sabko da kyat daga bisa jakki duk ya kara tsufa.

Yace;"Ma'u yau kece a garin inasu Rabi'u yanzu daga dawa nake naji ance kunzo hadda baki"

Tace;"Nana mutafi"

Ya kalleni ya gwale ido yace;"Nana ce haka?"

Ma'u tayi tsoki ta tafi muka gaisa nayi mashi kyau.

Nifra tace lallai da ba'ayi cikin su Farhana ba aka koreki da labari baiyi dadiba aka hadaka da wannan abun ai an cuceka.

Muna zuwa muka iske Yaya maimuna tazo da Yaya Auwalu muka gaisa sai da mukayi fira kana mukayi bankwana zamu wuce nayima Yaya Maimuna kyauta mai tsoka sosai nace saitazo.

Muka wuce muna zuwa motocin su Mummy zasu wuce.

Na shiga dakina ina kallon shi nayi murmushi na fito na iske Inna daki ta shirya muka fita nida Anuwar muke mota daya yanzu.

Muna zuwa bakin hanya naga Matii na sabke yan tallah da mutane.

Nasa aka tsaya hakan yasa su Mummy suka tsaya naje inda Matii yaceman yazo jiya matakan tsaro suka hanashi shiga yau ma yaje amman ba'a bashi ba nace bakomi nan na fadama Anuwar Dad yayi mashi kyautar mota naji dadi sosai Matii sai godiya yake kamar zai kwanta hadda kuka.

Muna zuwa Katsina muka wuce a airport.

Koda muka isa gida kai tsaye part din Inna na nufa nida Shatu dan a wajen Inna zata zauna.

Dare nayi Anuwar yazo mutafi naki yadda yaje sai yayi kwana biyu ga matar shi.

Fushi yayi ta tafi kwana biyu na koma part din shi.

Ranar naga soyayya nan yake fadaman su Farhana dasu aka koma Abuja sun koma hannun Mummy.

Nayi murmushi Bayan kwana biyu aka ba Baba gidan da aka ginama Yarima na shakatawa nakusa da Gubi mallaka mashi takaddu Babu harda kuka nima naji dadi sosai, Dad yayi haka saboda gidan na kusa da ruwa koda zaiyi noman rani ga kayan itace.


Inna aka daukeman ita aka maidata wajen su Farhana a Abuja

Shatu ta koma wajen Ammie.

Yau Koda na tashi babu lafiya hakan yasa na koma part din Ammie daman wajen Kulsoom yake.

Kwana mukayi ba lafiya tun da safe Ammie ta kira Anuwar aiko yazo, yana zuwa yabi ya rude dan nayi yaushi sosai ko hannu van iya dagawa yakira Doctor, Doctor na zuwa naga Doctor Mubarak.

Yayi murmushi yace;"Nana bari na aunaki"

Na kalleshi daman ya ganeni?

Yace;"kinyi mamaki ai nazo bikin Walimar ku nan nikejin labarin komi, nakoga Teema ta gidan Hajiya da yara biyu nan nabata labari jiya tazo tace nayi mata hanya tana son zuwa ba'a bari ta ganki"

Nakoji dadi na bashi Number ta nace yabata yana gama abinda zaiyi yace;"Prince Congratulation princess nada....."

Ai bai idaba ya rungume ni Ammie sai murna take Kulsoom ma data shigo sai murna suke.

Wannan ciki danayi har su Mummy saida sukazo waina koma a chan nayi rainon ciki Prince yaki yadda saboda Mai martaba yace babu inda zashi yanzu sai ya koyi zaman Fada.

Kusan kullun Ammie na tare dani haka Yarima.

Ana gobe zan wuce saiga kiran Teema na dauka tace itace tana waje.

Nasa ake aka taho da ita duk ta ya mutse kamar ba Teema ba 'yar gayu, nace;"Subhanallah! Teema lafiya kikayi baki haka?"

Tace;"Nana naji komi wajen Doctor kinji dadin ki, Kuma fari ai daman na maine yanzu nabar shafawa nayi aure barikin abubuwa sun faru nabar gidan Hajiya naje na auri wani tsohon saurayina saiya fita ya samo yanzu yaran biyu duk mata gasunan"

Nace;"Allah sarki Allah ya yara yanzu Ina Hajiya"

Tace;"Hajiya babu mai sayen abincin ta saboda ana zargin tanada HIV shiyasa bamai zuwa saye yanzu icce take saidawa a bakin gidan ta komi ya kare idan kika ganta duk ta tsufa abinda tayi ke bibiyarta tunda lokacin Number Maman Doctor Mubarak tasamu ta kirata tace mata ta Karuwa yake so waitayi cikin shege wai so yake yace nashine kuma banashi bane hakan yasa tunda safe tazo ta tafi dashi, a lokacin ni tasa na samo mata kawai saboda zai taimaka maki yanzu ai ga abunta tagani lokacin tayi amfani da dama ta lalata yaran mutane tasasu hanyar banxa yanzu Allah yayi masu sakayya"

Mun dade muna fira kana Teema ta tafi tace yanzu zatabiya taba Hajiya labari nayimata kyauta mai tsoka tanata godiya.


Bayan kwana biyu naji wai Doctor Mubarak keson Shatu naji dadi sosai Ma'u Kuma Yaya Sani zaiyi ta biyu suma naji dadi dan yanada hali mai kyau sosai.

Tare da Anuwar mukaje Abuja daga chan muka wuce Spain a chan zanyi renon ciki hadda Mummy shi kuma Yaya Anuwar Dad yasa ya koma.

Bazan iya musulta yadda nasha gataba a wajen Mummy.

Anan na haihu nasamu namiji aka saka mashi sunan Abie.


Muka dawo anan Bauchi akayi biki nan na iske Kulsoom da ciki anyi bikin su Shatu da Ma'u.

Kullun kowa cikin kokarin faranta man yake inajin dadin yadda ake nunaman kauna.

Yau na samu tsarki daman tunda nazo ina wajen Ammie.

Prince ya shigo na kalle shi ina shayar da Sultan.

Yace;"Gaskia yau zaki koma dakin ki"

Nayi murmushi nace;"daman ni daki gareni a gidan nan?"

Yace;"to shikenan yau anan zan kwana"

Ammie ce ta shigo tace;"daman nagaji nima da wannan zaryar taka ace mutum baida hakuri"

Ya sosa keya yace;"Ammie....."

Daga mashi hannu tayi tace;"zan maida maka matar ka yau shikenan"

Yayi murmushi yace;"Nagode sosai Ammie na"

Bayan tafiyar Anuwar akace nayi bakuwa ina fitowa naga Hajiya na saki fuska muka zauna muka gaisa nace;"ba Hajiya bace"

Tace;"nice Nana dan Allah ki taimakaman kiyi hakuri da abinda nayi maki sharrin shedan ne"

Nayi murmushi nace;"Bakomi daga yanzu zan saka duk wata abaki abinda zaki sayi abinci baida matsala"


Tayita godiya Kulsoom data iskemu tace;"ba ita bace ta cutar dake ba? Naji kince Hajiya gashi tana rokon ki yafiya"


Nayi murmushi nace;"ita mana"

Tace;"Kuma zaki taimaka mata Bayan abinda tayi maki?"

Nace;"ai babu komi duk mutum yayi maka Sharri tokai ka maida mashi da Alkhairi hakan shine dai-dai saboda kada mutaru mu zama daya"

Tayi murmushi nima nayi na koma daki.

Vedio call muke dasu Nifra da Farhana da Farhan sunje shopping Dubai Anuwar ya shigo.

Na juya na kalle shi nan ya amsa sunayi.

Bayan sun gama yace;"Gobe za'azo maganar auren Nifra"

Nan nayi murna Sister ta zatayi aure.

Babu abinda zance saide nace Alhamdulillah rayuwata nakan zauna ina tuna nice Nana mai fura muna zaune da Kulsoom lafiya Dad ya sabka bisa mulki ya tattara iyalen shi sun koma Dubai da zama ina yawan zuwa Anuwar kullun cikin kokarin kyautata man yake haka nima.

Nifra tayi aure ta auri wani d'an kanwar Mummy ansha biki har a Dubai mun sha biki kana muka Nigeria.

Su Farhana sun girma suna wajen Mummy mu kuma mun koma Spain saboda a chan Anuwar yake aiki.

Yau mun tashi zamuje Bauchi munada bikin Jawad.

Koda muka isa wajen Inna na zauna.

Naje wajen Baba su Ma'u sunzo biki da Shatu munji dadin haduwa yanzu Ma'u da Shatu ne friends dina.

Muna rayuwa cikin kwanciyar hankali da kaunar juna ina zaune bedroom din Ammie saiga Anuwar ya shigo da Daddare.

A hankali ya furta;"Nanah Khadija"

Nayi saurin juyowa saboda yaune rana ta farko da wani ya kirani da sunan haka nayi murmushi.

Ammie tace;"Uwar tamu kake fadi haka saina fadama Mai martaba"

Mu duka mukayi murmushi yace;"muje dare yayi hakanan nagaji da jira"

Ammie tace;"Hali na nan ko kunyata bakaji tashi kibi mijin ki"

Mukayi ban kwana muka tafi part din yau wani salon sone yazo dashi na daban yau ko MANAL din ba'a cewa sai Nanah Khadija gaskiya a daren yau munsha soyayya.

Ina bisa jikin shi yace;"Allah nagode maka daka dawoman da Manal dina"

Nayi murmushi nace;"Allah na gode maka daka mallaka man Yaya Anuu a matsayin miji"

Murmushi mukayi tareda Hamdala.

Yace;"Nayi kewar ki da kika tafi jinayi duniyar ta isheni ina matukar kaunar ki kada ki kara tafiya kece abokiyar rayuwa"

Nayi murmushi nace;"bazamu kara rabuwa ba rabuwar da mukayi a baya babu yadda zamu saboda itace JARABTAR MU"


Alhamdulillah....


Anan na kawo karshen JARABTAR MU.

Allah ya yafe mana kura kuren mu...Ameen


BANIDA ABINDA ZANCE SAI DAI NACE ALLAH YA BAR KAUNA A TSAKANINA DAKU MASOYAN JARABTAR MU LALLAI NAGA KAUNA DAGA GAREKU INA GODIYA SOSAI NIMA INA KAUNAR KU SOSAI😍😍
INAJIN DADIN ADDU'AR KU NAGODE🙏


GOLDEN PEN ALLAH YA KARA BASIRA DA DAUKAKA ...AMEEN


MARYAM ANKUDII {QURRAH}
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment