Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nufi kitchen. Idomie ta dafa masa sai kwai da ta soya masa.

Lemo ta dauko ta kawo masa.

Lokacin har yayi wanka yayi sallah, yana zaune yana kallon labarai.

"Kayi hakuri kaga dare yayi, ka ci wannan."

Ta fada tana ajiye masa. Baki ya tabe ya dauka ya dan ci kadan ya barta.

Dan shi indomie ba abar cin sa bace.

Washe gari da safe ma sai da ya tashe ta ta hada masa break.

Amman abin haushe tea da bread ne kadai. Ko dan kwai bata soya ba bare dankali ko ta dan gasa bread din.

Da kan shi ya shiga kitchen ya soya kwai ya dauka ya tafi wajen aiki.

A ransa ya fara gajiya, da wannan halin nata. Tin yana zaton ciki ne ko rashin lafiya yanzu ai abin ya wuce haka. Tinda taji sauki.

Ace mutum bazai gyara gida ba tin safe har dare haka nan girki bazai zo ya  tadda shi ba.

Zai iya cewa tsawon wata ukun nan da sukai, be taba cin girkin ta ba, daga indomie sai snack da take aikawa a siyo mata.

Da wannan bacin ran ya je gun aiki.

Najib mutun ne me son a kula dashi. Amman sam ita bata san wannan ba.

Ko irin kula in ya tafi babu bare taga ya dade ta kira shi.

Yana zuwa ya tattara komai ya bawa wani abokin sa, dan ya ce zai je Katsina da Kano zai yi satu biyu.

Yana dawowa ya hau shirya abi da zai bukata.

Ranar ma a bangaren sa ya kwana kuma Summy ko a jikin ta.

Da safe ya hada musu break ya gyara dakin sa da ko ina na gidan wanka yayi ya shirya sannan ya karya.

Ita kuwa gimbiyar tana can gado tana bacci, sai da zai fita ne, ya shiga dakin nata.

Zama yayi a gefen ta ya fara busa mata iska a cikin kunnen ta.

Mika ta farayi, hannun sa ya daura akan dukiyar fulanin ta yana shafawa a hankali a hankali.



*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *121*




Mikar takeyi ba qaqautawa a hankali ta bude idon ta.

Da shi tayi tozali, yana sanye da farar shadda an mata aiki da brown zare.

Brown din hula ya saka, idon sa sanye da tabarau, sai tashin kamshi yake.

Wani kyau ya kara mata tare da yi mata kwarjini.

Son sa da kaunar sa suka kara dirar mata a zuciyar ta.

Mikewa tayi zaune, tayi kasa da kai, dan jin kunyar sa.
"Ina kwana?"

Ta gaisar dashi a hankali.

Ido ya bita da shi abinda ta dade bata masa ba yau ta masa. Ba komai bane face gaisuwa.

Amsawa yayi ya kawar da tunanin da yake,
"Har ka shirya?"

"Eh! Zan tafi ga break din ki can a daining."
Ya fada yana mika mata kudi.

Kalla tayi, tai murmushi kawai ba tare da ya masa godiya ba.

Mikewa yayi, ya ce,
"Na tafi ki kular min da kanki."

Kai ta gyada masa kawai.
"Baza kimin addu'a?"

"A dawo lafiya."
Ta fada tana mikewa tsaye.

Hanyar bandaki ta nufa,
"Sai ka dawo."

Ta fada tana shigewa. Kai ya girgiza. Wannan wace irin yarinya ce, ace mijin ta zai yi tafiya ba damuwar komai.

Sannan ko dan rakiya babu. Murmushi yayi kawai ya juya ya fice.

Jakar sa ya dauka, ya fita driver ya kai shi gidan Mami yai mata sallama. Daga nan  airport aka shige dashi.


Tin safe Mami ta shiryawa su Najwa kayan da zasuyi amfani da shi.

Najwa da Zahra tare suka tafi Abuja. Suna zuwa kuwa Mami ta fara nan nan da su.

Mami ba karamin dadin zuwan su tayi ba.

Haka su Bara'atu sai hira suke kamar sun san juna bama Zahra da tafi Najwa magana.

Najwa kuwa sai dai tayi murmushi ko ta bisu da magana.

Duk da haka suna son Najwa saboda sun fuskanci ba wulakanci bane haka dabi'un ta suke.

Har dare suna tare dan tare sukai girkin gidan sannan suka tafi can bangaren Baba suka zauna hira.

Sai bayan isha'i suka koma bangaren Mami. Lokacin Dady ya dawo. Hira suka zauna sunayi yana tambayar su karatun sa.

Karfe tara suka shige daki danyin bacci. Zahra sai waya take da saurayin ta inda Najwa kuwa ta hau google tana duba abubuwa.


Ya sauka lafiya inda ya rasa ta ina zai fara neman ta.

Mami ya fara shaidawa ya isa lafiya, dan Mami har take fada masa zuwan su Najwa.

Yana kashewa ya kira Summy, shaida mata yayi sun isa lafiya.

Ranar da ya sauka a ranar yaje gidan Su Zahra dan gaida Dadyn su.

Ai kam sai da suka rike shi dan a gidan ma sai da ya kwana uku.

Sam Summy bata daukar waya ta kira shi, ba wai son sane ba tayi ba kawai dai girma  kai da yai mata yawa.

Gidan kuwa kura kamar me, dan bata shara abinci ma kuwa sai dai ta bayar a siyo mata.

Duk safiyar Allah da dare zai kirata su gaisa daga haka ita bata kara neman sa.

Motar gidan Su Zahra ya ke dauka ya fita, kullum sai ya zagaye garin da neman ta amman ko me kama da ita be taba gani ba.

A haka har yayi kwanankin da zai yi amman be ganta ba.

Kano ya wuce a ransa yana sawa da zai kuma dawowa.

Su Najwa kuwa suna can suna shan hutun su, dan wannan karan tafi jin dadin hutun saboda ga Zagra dasu Talle.

Wanda take burge su, kullum suyi ta jan su a jiki.

Zaune suke duk sunci kwalliya Najwa ce kadai a sama suna tare da Mami.

Itama tayi kwalliya cikin wani less me kyau da tsada.

Mami ma shiryawa take, kallon ta Najwa tayi, ta ce,
"Mami fita zakiyi ne?"

"Eh ko zaki?"
"Eh Mami zan raka ki."

"Ta dauko mayafin ki."
Mayafin ta ta dauko, sai wayar ta.

Kasa sukayi ido su Zahra suka zuba musu.

Kallon Mami tayi, ta ce,
"Ko kuma zaku ne?"

"Eh!"
Duk kan su suka hada baki wajen fada.

"To ku fito muna jiran ku. Ta kamo hannun Najwa sukai waje.

Gidan Najib suka nufa, Da Sallama suka shiga babban falon ta.

Dakin kaca kaca dashi, duk yayi kura dan ba gyara yake samu ba.

Duk kan su sai da abin ya basu mamaki.

Tana kwance, akan kujera tana kallo, sanye take da doguwar rigar atamfa.

Dago da kai tayi tana kallon wadan da suka shiga, Najwa ta gani da Zahra wannan yasa ta hade rai kamar wace taga mutuwar ta.

Bayan su kuma Su Talle ne, yaran da Summy ta tsana suma. Fuska ta kara hadewa.

Mami ce tayi musu magana,
"Ku shige mana kun tsaya akan hanya."

Wannan yasa Summy tasan tare suke da Mami.

Mikewa tayi tana kakalo murmushi, gun  Mami ta nufa, tana gaisar da ita.

Amsa wa tayi sannan suka samu waje suka zauna.

Zahra ce ta kalli Najwa ta ce,
"Gidan waye nan. Daman Sumaiyya tayi aure."

"Eh man kin manta muna yin jarrabawa. Amman bansan gidan waye ba."
Gaishe da ita sukai ta amsa musu a share.

Zama tayi kikam ba tare da ta kawo musu abin sha ba bare wani abu.

"Gidan ke kadai ko? Najib ya tafi ya barki."
Kasa tayi da kai ta ce,

"Ai har na saba ma."
"Da har zance ki taho gida ga kannen ki kwanayin hira."

Murmushi tayi ta bar maganar kawai.

Zahra ce ta kalli Najwa ta ce,
"Ke gidan Ya Najib ne ashe."

Baki Najwa ta tabe kawai.

Ganin gidan a kaca kaca sai Mami tayi zaton ko bata da lafiya ne ko laulayi take yi.

Kallon su Bara'atu tayi ya ce, ku tashi ku gyara mata gidan.

Mikewa sukai har su Najwa suka dura cikin dakunan suna gyarawa.

Kallon ta Mami tayi, ta ce,
"Nawa Najib maganar me aiki ko dan irin haka amman ya nuna baya so."

Wani sanyi Summy taji, ta ce,
"Mami nima naso nai masa maganar wallahi."

Murmushi Mami tayi, ta ce,
"Ki kwantar da hankalin ki zan kawo miki wata. Najib ba dai rigima ba sai ya ce shi baya son masu aiki."

"Nagode Mami."
"Ba komai."

Abinda yasa Summy bataiiwa Najib magabar yan aiki ba shi.

Khalil ya taba gaya mata Najib baya son masu aiki.

Kuma ranan da tai masa maganar taga yai mata fada,

To komai tana yine yadda bazai bata masa rai ba.

Yanxu kuwa da Mami ta kawo maganar ai bazai kiba dan ita bazata iya wannan wahalar ba.

Najwa ce tayi musu girki, su kuma suka gyara can dakunan.

Firij din kitchen din ta bude ta dauko wa Mami lemo ta kai mata har falo.

Harara Summy tabi Najwa da ita. Ita kuwa bama tasan tanayi ba.

Suna gamawa suka zubawa Mami sannan suka kaiwa Summy.

Sosai taci tana yaba dadin abincin. Dan duk ciye ciyen ta bata taba cin me dadi wannan ba.

A kitchen suka zauna suka ci suka koshi.

Gidan tini Yayi kyau ya dau haske, sai tashin kamshi yake.

Ita kanta taji ddin gyaran da har a jikin ta sai da taji gidan ya canja.


*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH
*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *122*



*Kuyi hakuri kwana biyu page daya nake turowa. Wamnan yasamu ne saboda bana samun lokaci ssai.*

*Anayin maneji*

*Masoya littafin  nan. Naga sako nagode. Allaah barmu tare*


Ranar sai dare suka bar gidan.

Mami kuwa sai nan nan take da ita.

Ko da yaje Kano damuwar rashin ganin ta bata bar shi ya sake ba.

Dan duk a matse ya ke. yaje gidan Khaleel inda kulawar da yaga Khadija na bashi ba karamin burge shi tayi ba.

Duk da tana da ciki bata da kasala da kwiya. dan gidan tsab dashi abin sha'awa sai tashin kamshi yake.

Yana zuwa aka tare shi da abinci me rai da lafiya ga hadin lemo.

Sosai yaci abincin dan Najib baya wasa da cikin sa.

Ba yadda Khaleel beyi dashi ya kwana a gidan ba yaki.

Zuwan sa Kano yayi ziyara yan uwan da kakanin sa. Inda suke ta masa tsiya be kawo amaryar sa ba.

Wanda ya dade be ganshi bama wannan karan yaje ya yi musu abin arziki.

Ana jibi zai dawo ya fadawa Mami, Mami ganin yar aikin da zata kaiwa Sumaiyya bata zo ba. Tasa su Najwa suka tattara suka tafi gidan Summy dan su taya ta tarbar me gida.

Tunda suka je take cika tana batsewa su kuwa ko ta kanta basu bi ba.

Inda sai hirar su suke, su dafa abinda suke so, su sha abinda suke so.

Duk da abin na mata zafi amman tasan baza ta iya hanasu ba.

Ranar da zai dawo ba ta tashi a bacci ba ma sai karfe Ukun rana.

Lokacin sun gyare gidan tsab sun turare shi.

Najwa da Zahra ne suka gyara bangaren Najib.

Inda suka ce Najwa ita zata Masa girki. Fried rice tayi da hadin salad sai waina masa da yake su Bara'atu su  fada mata yana son ta.

Sai farfesun kayan ciki da tayi masa da hadin lemoka da kunun aya.

Kafin magariba sun gama komai gida sai tashin amshi yake.

Sun shirya zasu tafi Najwa tayi bangaren sa ta hada masa ruwan wanka dan tasan i yanzu dai yana hanya.

Tana dawowa suka shige mota. Jeep ce wannan yasa Najwa ta shige can baya, su kuma suka zauna a tsakiya.

Har an bude musu gate zasu fita ya danno hancin motar sa cikin gidan.

Tsayawa Drivern su yayi har sai da ya fito suka gaisa.

Karasowa yayi wajen motar yana leka kansa ta taga.

Bara'atu ce ta ce,
"Sannu da zuwa Yaya. Ya hanya?"

"Lafiya ya amsa mata da. Gaisar dashi sukai gaba dayan su.

Sai da suka gama sannan Najwa ta ce,
"Ina yini Hamma Najib?"

Tsigar jikin sa ce ta mike, jin muryar ta me dadi da sanyi ta doke shi.

Amsawa yayi yana son ganin fuskar ta. Duk da yaso yasan muryar tata.

Ganin zasu fita ne yasa ya barsu kaf ya tsaida su.

Bangaren sa ya nufa dan watsa ruwa. Yana shiga da gajiya ya tadda an hada masa ruwa.

Murmushi yayi a ransa dan yasan ba Summy ce da wannan aikin ba.

Dan tin daga harabar gidan yaga canji kuma yasan Mami ita ta aiko su dan su dan yi masa gyara.

Wankan yayi cikin farin ciki dan ruwan sai kamshi yake masa.

Sai da ya shirya ya nufi bangaren ta.

Tana zaune tana sana'ar tata ta kallo, tin wankan safe vata karayi ba.

Fuskarta sai maiko take yi. A gefen ta ya zauna.

Kallon ta yayi, itama haka dan tayi kewar sa.

Mamakin ta yake, bako sannu da zuwa bare ai masa ya hanya.

"Ya gidan?"
Shiya tambaye ta.

"Lafiya? Ya kake?"
Mikewa yayi be bata amsa ba.

Dan ba wannan abin ya kamata ya fito daga bakin ta ba.

Daining ya nufa, Fulas din dake daining din su kansu abin kalla ne.

Be taba ganin su a gidan ba, to ita da ba girkin take ba tayaya zai gansu.

Fulas Fulas din ya bude wani kamshi je ya doki hancin sa.

Masa ce an mata miyar nama miyar kanta abar a ce banda wani kamshi da take fitar wa.

Yawu ya hadiya. Zubawa yayi ya fara ci. Ji yayi kunnen sa kamar zai cire dan dadi.

Abincin yake ci cikin kwanciyar hankali a ransa ya a cewa wannan ba girkin su Bara'atu bane.

Summy kuwa kamshin girkin shi ya taso ta daga kallo  da take, dan ita ma sai taji yunwa.

Fried Rice din ta zuba ta fara ci kai ta fara gyadawa dan dadin girkin.

Yana gamawa da masar ya dauka ya saka a friji haka ma fried rice din.

Falo ya koma ya zauna biyo shi tayi ta zauna akan cinyar sa.

Kirjin ta, ta manna da nashi, tini hankalin sa ya tashi.
Romancing junan su suka fara daga nan ya dauke ta cak yayi dakin baccin sa da ita.

Su Najwa na komawa gida suka fara hada kayan su dan monday zasu fara lecturer.

Mami duk ba dadi taji, amman ya zatayi, goma ta arziki ta hada musu inda tasa a nema musu jirgi dan gobe suke son dira a kano jibi su wucce Katsina.

Gata kuma sai makaranta. Dady ma sai da ya basu kudi me yawa har airport suka raka su. Sai da suka ga tashin sanan suka juyo.

A kano ma suna dira har an zo daukar su. Mamin Najwa da murna ta tare su.

Inda da yamma ta kaisu shopping da kanta daga nan zooroad suka wuce ta karbo kusu dinkunan su.

Da dare kuma sukaje yiwa kakannin su sallama.

Kowa sukaje sai dai ya sanya musu albarka tare da addu'a.

Washe gari suka mika Katsina. Inda acan ma sai kewar su ake yi.

*Bayan Wata Biyu*

Karatu yayi nisa dan har sun kusa fara jarabawa first semester level three.

Komai lafiya yake tafiyar musu, inda har lokacin Najwa bata kula wani bare har ta tsaya da su.


Mami tini ta aika wa su Najib da yar aiki. Duk rashin son yar aiki da bayayi.

To yaya zaiyi sai yanzu ya gane daman can Sumaiyya kazama ce bata damu da ganin datti ta gyara wajen ba.

Haka nan girki ba iyawa tayi ba. Wannan yasa sai ya dawo da dare yake girka abinda zai ci.

Dan shi bazai iya cin abincin waje da na masu aiki ba.

Ita kuwa wani sabon san jiki ne ya same ta dan wanka ma da kyar take iya yi kullum yini take kallo sai chatting da kawaye.

Katsina ya kara shiryawa zuwa, wannan zuwan ba karamin addu'ar yayi na Allah ya hada shi da ita ba.

Tin da ya dira ya fara jin kwarin gwiwa wannan yasa yai wanka ya shirta ya fita.

Su Najwa kuwa sun koma hostel saboda jarabawar da suka fara.

Bikin wata mate din su za'a yi wannan yasa suka shirya zuwa Green house dan siya  mayafan da zasu amfani da shi.

Kamar hadin baki shima ya shirya ya tafi store din dan siyan abubuwan da zai danyi amfani dasu.

Shigar su kenan shima ya iso wajen, ciki shima ya shiga ya fara daukar abinda yake so.

Sai da ya gama tsab sannan ya nufi wajen biyan kudin.

Kamar daga sama ya hango ta tsaye a gun tana biyan kudin.

Kallon ta ya tsaya yi sosai, ganin zai kara rasa damar sa yasa ya ajiye kayan ya bi bayan su.

Motar da suka shiga yabi baya, a hankali a hankali har suka  karasa bakin gate din makarantar su.

Bin su ya cigaba dayi har suka karasa bakin hostel din su. Sai da suka shiga sannan ya samu wasu yan mata ya ce,
"Dan Allah yan matan can neke son ku kira min."

Kai yarinyar ta jinjina kai ta ce,
"Allah yasa su zo, dan basa kula samari."

Ta fada tana yin cikin dakin nasu.



*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *123*

"Allah yasa su zo, dan basa kula samari."

Ta fada tana yin cikin dakin nasu.

Kallo ya bita dashi, har ta kure masa.

Tana shiga dakin suka gaisa, sannan ta ce,
"Anty Najwa da Anty Zahra wani ne a waje yace dan Allah kuje wai."

Kai Najwa ta dauke ta hau kan gadon ta, dinkin da suka amso ta dauka tana karawa da mayafin da suka siyo.

Zahra kuwa kallo  ta, ta tsaya yi.
Je kice gamu nan."

Ta juya ta fita. Fada masa tayi, kudi ya debo ya bata kin amsa tayi sai da kyar.

Yarinyar na fita Zahra ta matsa gun Najwa tace,
"Wai ke mene haka kinji dai abinda aka ce ko? Kinsan waye?"

"Ban sani ba dan haka bazani ba."
Mikewa Zahra tayi ta Dauki Hijab din ta. Tayi waje.

Tin daga nesa take kallon sa tana son tina a ina ta sanshi.  A ranta ta ce, ko me kama dashi ta sani ne.

Karasawa tayi wajen sa da sallama.
gaisawa sukai cikin girmama shi.

Fuskar sa dauke da murmushi ya ce,
"Dan Allah kiyi hakuri nasan baki sanni ba, amman dan Allah yar uwar ki da kuka shigo yanzu nake son gani."

Kallon sa tayi, gayen yayi beda makusa kuma kowa zai yi kwadayin samun sa.

A fuskar nagarta kuwa daga kallo kasa mutunin kirki ne.

"Kinyi shiru?"
Ya katse mata tunani.

Murmushi tayi, ta ce,
"Najwa yanzu bazata iya fitowa ba kanta ke ciwo magani ta sha har ta kwanta ma."

"Ayyah to ki mata sannu amman dan Allah gobe zan dawo ko zuwa anjima."

Amsa masa tayi da
"Ba komai."

Godiya yayi mata ya shiga mota ya tayar.
Zuciyar sa kamar kankara dan murna da farin ciki.

Daga nan gari ya shiga zagayawa cikin nishadi abinda be taba yi ba a garin katsina ba kenan.

Tana shiga daki ta kara sa gefen gadon da Najwa ke zaune.

Kallon ta tayi, ta ce,
"Sis gunki yazo, amman nace baki da lafiya. Ya ce anjima ko gobe zai dawo."

Kai ta dauke kamar bata ji ba.
"Wai kuwa lafiyar ki kalou kuwa? Allah ina jin sai na hada ki da Mami."

Harara ta tayi, mikewa tayi ta koma kan kujerar dake dakin. Tana magana

"Amman fa gayen ya gama haduwa da badan ina da Mustapha na ba da ba abimda zai hana in so shi."

Tsaki Najwa tayi ta dauki littafin ta tana dubawa.

Dariya Zahra tayi itama ta dauki littafin ta tana dubawa.

Besamu komawa a daren jiya ba dan haka yau tin karfe goma ya dira a makarantar.

A lokacin ma suna jarabawa yafi awa daya sannan aka fara fito daga jarabawar.

Yarinyar jiya ya hango, dan haka ya dago mata hannu.

Da sauri ta kasa wajen sa tana gaishe dashi.

Murmushi yayi ya amsa,
"Dan Allah Su Najwa zaki kara kira min."

"Toh!"
Ta amsa ta nufi library dan tasan suna can dan tin dazu suka fito.

Tana shiga ta hango su suna karatu. Karasawa wajen tayi, ta ce,
"Ina yini  ku?"

"Lafiya!"
Suka amsa, Najwa ta dauke kanta.

"Anty Zahra, dan Allah kizo inji mutumin jiya."
Murmushi Zahra tayi ta ce,

"Allah sarki yazo ashe."
Najwa ta kall ta ce,

"Sis taso muje."
Hararar ta Najwa tayi ta cigaba da karatun ta kawai.

Murmushi tayi, ta kalli yarinyar ta ce,
"Muje!"

Fita sukai Najwa na bin su da kallo da takaicin fitar Zahra.

Karatun ma kasawa tayi da kyar dai ta dawo da hankalin ta kan karatun ta.

Tana karasawa ya saki murmushi, gaishe shi tayi cikin girmamawa.

Amsawa yayi yana tambayar jikin Najwa.
"Jiki da sauki!"

"Tana ina ne?"
Ya tambaya.

"Zo mu karasa can."
Ta nuna wajen wasu bishiyoyi  da kujeru agun.

Can suka zauna. Kallon sa tayi ta ce,
"Bawan Allah a ina kasan mu da har kazo gare mu."

"Zan fada miki amman kada ki fadawa yar uwar ki."
"Saboda me?"

Ta tambaya cikin mamaki.
Murmushi yayi ya ce,
"Saboda ba yanzu nake son ta sani ba."Shikenan! Ina jin ka."
Kallon yayi ya ce,

"Sanin Najwa a guna abu ne da dade wanda zance na shekara uku da ganin ta. Abin mamaki kuma ba a garin nan ba."

Murmushi Zahra tayi ta ce,
"Ina ji."

"Na fara ganin Najwa ne a kano ta taso daga makaranta rike da hannun wata karamar yarinya. Abin alajabi kan nayo UTurned na zagayo har sun bace min."
Shiru yayi, ya cigaba da magana

"Ban taba soyayya ba wannan yasa na furtawa Mami mahaifiya ta. Ina fada mata ta ce, ai son ta nake abin ya bani mamaki dan a lokacin ban san so a rai na ba. Ashe so kan shiga ne ba sai an shirya masa ba."

Kallon Zahra yayi ya ce,
"Tin daga ranar kullum sai naje unguwar amman bana ganin ko me kama da ita.
Ganina na biyu da ita shine a Ado bayero mall shima kan na karasa wajen ta sun bar wajen.
Nasha wahala akan Najwa duk da ban santa ba."

Numfashi yaja ya ce,
"Tin lokacin ban kara ganin Najwa ba sai last year a garin nan. Kunje green house shima kuka guje min."

"Kinsan banyi wata da barin garin nan ba wajen neman ta, abinda ya dawo dani shima neman ta ne. Nayi addu'a sosai kafin na zo sai Allah ya amsa min addu'a ta. A ranar da na dira jiya  a ranar na ganku. Wannan yasa na biyo ku."

Kai Zahra ta jinjina tana tausaya masa.
"Ina son Najwa ba dan kyan ta ba. Haka kuma ba dan na santa ba. Allah shi ya daura min santa."

Nunfashi Zahra ta sauke ta ce,
"Najwa na da taurin kai Bawan Allah amman tana da saukin kai."

Murnushi yayi, ya ce,
"Sunana Najib."

"Ah kace Me sunan Yayan mu ne."
"Yanzu dai ina fatan Ba ta da wanda take so."

Kai ya gyada ta ce,
"Najwa bata kula kowa bare har taso wani. Duk yadda ake mata fada bataji indai akan samari ne."

"Alhamdulilah!"
Ya fada yana daga hannun sa sama.

Kallon sa tayi da alamar tambaya.
"Dole nayi Hamdala, saboda Allah naso na da har yasa Najwa bata kula samari bare taso wani a ciki."

"Kar ka fadi haka.  Dan kaima da wuya" ta kula ka. Jiya na mata maganar ka amman ko kala bata ce ba. Yanzu ma kaga taki ta fito."

Murmushi yayi ya ce,
"Ba komai yar uwa. Ya sunan ki."

"Sunana Zahra."
"Ke kanwar ta ce,"

"Ni Kanwar ta ce, mamana kanwar maman ta ce, a kano take tazo nan garin wajen Momyn mu ne."

"Allah sarki. Dan Allah ki tayani bata hakuri ta yadda mu hadu zuwa anjima zan dawo."

"Ba komai zan yi iya bakin kokari na dan na lura kai mutumin kirkine. Kuma Allah shi ya hada ka da Najwa insha Allahu zan baka ita."

"Nagode Zahra. Nagode Allah saka miki da alheri."
"Ameen Yayan mu."

"Kije kuci gaba da karatun sai anjima."
"Toh sai anjima."

Ta kamo dakin karatun nasu.
Najwa na ganin dawowar ta, ta sauke ajiyar zuciya.

Dan ita a tsorace take da ta fita. Hararar ta tayi kawai ta cigaba da karatun ta.



*INDABAWA*

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE

*124*


Sai karfe uku suka koma hostel lokacin har Momy ta kai.musu abinci.

Wanka sukai sannan suka ci. Basu dade da gama ci ba akai sallah la'asar suka mike sukai sallah.

Sai da suka idar suka fita shan iska.
kallon ta Zahra tayi ta ce,

"Sis na san kin girme ni. Amman kuma ina da abinda zan fada miki."

Kallon ta Najwa tayi ta ce,
"Ina jinki."

Durkusawa Zahra tayi ta kama kafafun Najwa ta ce,
"Dan Allah ba dan ni ba ki aminta da abinda zan fada miki. Bazanyi abinda zai cutar dake ba."

Dagota Najwa tayi. Ta rumgume ta.
"Zahra nasan kina so na. Son da bazai misaltu ba. Insha Allah zan aminta da duk abinda kike so gareni."

"Promise!"
Ta fada tana mika mata hannu.

"Nayi alkawari."
Ta kama hannun nata.

"Sis yanzu fa mu a level three da mun shiga four zamu ga har mun kammala."

"Haka ne."
"Me kuma zamu zauna yi a gaban iyayen mu. Duk da nasan ba mu wuce zaman gida ba."

"Haka ne."
"Amman dai kinsan aure shine cikar mutuncin yar mace. Kuma suma iyayen namu zasu so su ganmu a gidan mazajen mu."

Duka Najwa ta kai mata. Ta ce,
"Aure dai kike so ko?"

"In naso ma wani abu ne. Dan sunnah ai bazai qi sunnah ba."

"Haka ne Zahra."
Najwa ta fada tana kallon ta.

"Najwa ya kamata tin yanxu ki kama me son ki ba sai lokaci ya kure ba."
Kallon ta Najwa tayi.

"Eh Samari da yawa sun zo amman kin qi aminta dasu, Najwa soyayya bata taba hana karayu wallahi sai dai in kaso ta hanaka."

"To me ya kawo wannan maganar yanxu."

Murmushi Zahra tayi ya ce,
"Wani ne me suna Najib yazo yake son ki kuma da aure.
Najwa wallahi kika ganshi sai kema ya miki yana da hankali da nutsuwa ga tarbiyya ta magana ma sai kingane hakan.
in har kika bar Najib

Please Login or Register in order to submit comment