Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi."

"Kar ki damu, kinsan ban kwana a gida ba. yanzu zan biyo ki kwantar da hankalin ki."
"Yauwah nagode nagode."

"Kar ki damu."
Ta kashe wayar.

Kwanciya Summy tayi tana sakawa da warwarewa.

Tsaki takeyi, a mike tsaye
"yanzu Najib aure ze karayi." Tab ai wallahi bazata sabo ba."

*INDABAWA**NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*131*


*Hajiya Nafisa. Our lovelly Anty. U are like Mother to us. Really love u. Tnx for ur Care. May Allah bless you.*
Ure  so special to me. Tnc for ur love.

*Allah ya barki da mijin ki ya yara Ya'yan ki, Allah kara miki lafiya da nisan kwana.*

*So much love Anty na.*

*Allah kara hade kan mu, dukkan marubuta.*
*Ameen*


Kallon sa Dady kawai yayi, tunani Najib ya tsaya yi.

Number Najwa ya kira bugu daya ta daga, kafin tayi magana ya ce,
"Wai Number wa kika turon ne?"

Shiru tayi, ta ce,
"Wacce Number?"

"Number da Address da kika turon jiya."
"Oh na Uncle dina ne."

"Uncle din ki?"
"Eh! Menene?"

"A'ah babu komai zan kira ki anjima."
Ya kashe wayar kan sa ya dafe.

Kara kiran ta yayi, dagawa tayi,
"Please dan karai.min resending kinji."

"Toh!"
Ta katse wayar. Ta tura masa.

Number Dadyn ce dai, wayar Dady ce tayi kara,

Dubawa yayi yaga dan uwan sa ne, dagawa yayi, da sallama.

"Assalamu Alaikum!"
A can bangaren ne aka amsa masa da.

"Wa'alaikum Salam Dan uwa."
"Na'am dan uwa ya gida ya iyalai."

"Lafiya Alhamdulilah!"
Najib mikewa yayi ya hau sama dakin Mami ya shiga.

Mami na zaune ta kalle shi, gani tayi ya canja lokaci guda.
"Lafiya Najib?"

Kan gadon ta ya fada yana fitar da wani irin numfashi, dafashi tayi, ta ce,
"Najib lafiya?"

Zai yi magana Dady ya shigo kallo  su ya tsaya yi.
"Mami na kasa ganewa ne?"

"Me ka kasa ganewa?"
"Mami ta kuma turon Address din da Number duk na Dady ne wallahi."

"Toh!"
Mami ta fada tana Kallon Dady da sai murmushi yake yi.

"Dady kana jifa."
"Naji Mamin Najib, kinsan wa Najib yake so ne?"

"A'ah!"
Ta fada tana zukuwa taji wacce yake so.

"Najwan kice fa?"
"Najwa ta."

"Eh Najwan Ahmad."
Ido ta zaro, ta ce,
"Da gaske?"

Murnushi yayi, ya ce,
"Yanzu Ahmad ya kira ni yake fada min Najwa an fito amman ya bada Number ta da addrss dina. Kinga kuwa ai ita ce."

Najib dake kwance tini ya mike da sauri yana kallon Dady.
"Dan Allah Dady da gaske."

Ya fashe da Dariya, Dady ya rumgume yana murnar da farin ciki.

Mami kuwa kallon sa ta tsaya yi, a ranta ta ce,
"Allah ya amsa addu'ar ta da ta su Baffah kenan. Ba ahada su ba sun hada kan su."

Najib ne ya kalli Mami, ya  ce,
"Mami tunanin me kike?"

Murnushi tayi, kawai ta zauna a gefen su.
"Wai kar dai kace daman baka san Najwa ba yarinyar da rainon ka ce,"

Dariya yayi ya ce,
"Mami kibar wannan zancen, wallahi abin ma abin kunya."

"Wallahi kuwa. Ace mutum da kanwar sa be san ta ba."

"Na santa man, kinsan tin da na bar kasar bana ganin ta ko nazo."
"Allah ya kyauta."

Fita Najib yayi, bangaren su Baba yana basu Labari.

Ba wanda yakai su bara'atu murna.

Dady ne ya kalli Mami ya ce,
"Kinga ikon Allah ko? Allah ya amsa addu'ar Baffah da Ummah."

"Abinda na gama tunani kenan. Kaga Baffah akan haka har makka yaje yayi addu'a ashe Allah ya hada su bama mu sani ba. Alhamdulillah ai ni zanyiwa Ummah wannan albishir din."

Ta fada ta nayin dariya Dady ma dariyar yayi, ya ce,
"Uwar Amarya!"

"Wallahi kuwa tuwo na mai na. Kai Alhamdulilah ai kowa yayi kwadayin samun Najwa wallahi."

Dady ya ce,
"Mun gama magana ma, zanje na fadawa su Baffah wata biyu masu zuwa za'ayi komai a gama."

"Toh Allah yasa ayi da mu."
Dady ya amsa da
"Ameen!"

Najib kuwa tin lokacin ya fara shirin zuwa Kano.

Sunyi waya da Najwa be fada mata komai ba sai lokacin da zai zo.

Tin da ya fada mata ta fara shirye shiryen zuwan sa.

Girke girken da zatai masa, da kayan da zata sa duk sai da ta tanade su.

Tana son fadawa Mamin ta tana jin kunya.

Suna zaune a falo, ita da Salim ta ce,
"Hamman Jibi fa zai zo."

Kallon ta yayi, ya ce,
"Waye?"

"Shi man."
"Najwa kenan wallahi kin fiya kunya. Yanzu sunan nashi ma baza ki iya fada ba."

Shiru tayi, kai ya girgiza ya ce,
"Kin fadawa Dady da Mami ne?"

"Hamma wallahi bazan iya ba."
Dariya yayi, ya ce,

"To ya kenan?"
"Ka fadawa musu."

"To shikenan. Kinsan kuwa nan da wata biyu za ayi komai a gama."

Mikewa tayi daki da gudu, dariya yayi, ya nufi dakin Mamin su.

Zama yayi, ya ce,
"Mami 'yar ki dai ta mayar dani dan aike."

"Me kuma ta kuma aiko ka."
"Wai zai zo, shine ta kasa fada."

"Allah sarki Najwa. To menene? Yaushe zai karaso?"
"Jibi ne."

"To Allah kaimu zan fadawa Dadyn naku."
Duk abin nan da ake su Mami ba su san wa yake neman auren Najwa ba.

Mami, ta kalli Salim ta ce,
"Kasan har an kai sadaki da komai. Laife kawai zasu kawo."

"Ikon Allah Abin da zafi zafi haka."
"Wallahi."

"Allah sanya alheri ya kore duk wata fitina."
"Ameen Ya Allah."

Najib ma ya fadawa su Mami, ranar zuwan sa Kano, kuma yasan da an gama komai, daurin aure kawai ya rage da kai laife.

Sumaiyya ya sama ya fada mata duk halin da ake ciki, da zancen auren sa.

Ji tayi kamar tayi bindiga, kudi ya zube mata masu yawa tare da sabuwar mota ban da laife da ya jido mata ita.

Amman duk wannan abin basu burgeta ba. A ranta ta dauki alwashi sai taga bayan matar nan tasa.

A haka ya tafi ya bar ta, zuciyar ta kamar ta fashe dan bakin ciki.

Yana tafiya, ta kira kawar ta Jamila.
"Jamsy!"

"Na'am Summy lafiya kuwa?"
"Ina fa lafiya. Najib ne zai kara aure fa?"

"Aure kuma ana zaune lafiya."
"Kedai bari yanzu mene abin yi."

"Ki kwantar da hankalin ki. Zan shigo akwai wani malamin na anan nigar in nazo sai muje."

"Yauwah jamsy nagode sai kinzo. Dan Allah ki shigo da wuri dan abin yafi saurin yi."

"Kar ki damu, kinsan ban kwana a gida ba. yanzu zan biyo ki kwantar da hankalin ki."
"Yauwah nagode nagode."

"Kar ki damu."
Ta kashe wayar.

Kwanciya Summy tayi tana sakawa da warwarewa.

Tsaki takeyi, a mike tsaye
"yanzu Najib aure ze karayi." Tab ai wallahi bazata sabo ba."

*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*132*


*Ummu Ayda na gode sa kaunar ki gareni da littafi na. Nagode Allah bar kauna. Ameen*




Baffah da kansa yaje ya dauko Najwa dan ya ce, acan zasu je ta sauki bakon nata.

Duk abinda zatayi amfani dashi sai da ta diba sannan ta tafi.

Ranar da zai sauka tare da Ummah suka shiga kitchen suka tare shi da abinci kala kala na gargajiya da na zamani. Hakan nan lemo ma.

Ba wanda yakai su Ummah murnar hadin nan.

A gidan su ya sauka, da yamma ya kira ta, ta bashi address din inda take.

Murmushi yayi da yaji tana gidan su Ummah.

Kayan da ya kawo musu ya diba ya fito.

Cikin wata light brown din shadda an mata aiki da dark brown din zare dark brown din hula ya saka da takalmi.

Idon sa kuma sanye da farin tabarau ba karamin kyau yayi ba.

Sai tashin kamshi yake.


Ummah da kanta tasa aka kawo mata me yin kwalliya wai sai an wa Najwa kwalliya duk hakurin da ta bawa Ummah kin yadda tayi.

Me kwalliya ba karamin kwalliya tayiwa Najwa ba.

Dan tayi kyau ke kyace amarya ce.
wata atamfa ta dauka jikin ta siiblue, da orange a jiki.

An mata dinkin riga da siket, dinkin ya zauna a jikin ta sosai.

Dauri akai mata shima me kyau wanda ya kara fito da kyan ta.

Turare Ummah ta bata ta feshe jikin ta dasu.

A falon Ummah aka jere masa duk abinda zai bukata.

Biyar da rabi ya kirata yace, ya karaso.

Ummah ta fadawa ta fita shigo dashi. Yana tsaye a jikin motar sa ya harde hannun sa a kirji.

Kofar da zata fito ya zubawa ido. Duk gaisar dashin da suke hankalin sa na kan Najwa da ta fito.

Baki ya saki da hanci yana kallon ta. Har ta karaso be san ta karaso ba. Sai da ta tafa hannun ta sannan ya dawo cikin hankalin sa.

"Hamma wannan kallon haka."
ta fada kan ta a kasa.

Murmushi yayi, ya ce,
"Ai ke din ce."

Dan hararar sa tayi, ya ce,
"Ni shige muje."

"Haba sarauniyar mata, ina nasan gidan da zanyi gaba."
Gira ta daga, ta ce,

"Haka ne fa."
Tayi gaba ya biyo bayan ta.

Har babban falo ta dire shi, sannan ta zame kasa ta gaisar dashi.

Kasa amsawa yayi, sai kallo da ya bita dashi.

"Hamma!"
Ta fada a shagwabe.

"Menene?"
"Ina gaishe da kai kayi shiru."

"Ayyah yi hakuri wallahi duk na rasa control di nane."
Ido ta zaro, ta ce,

"Hamma gidan mutane fa."
"Gidan mu dai. Ba gidan kakan nn ki bane."

"Nan ne."
"To ai gidan da zamufi shan soyayyar mune."

Baki ta rufe da hannu tace,
"Dan Allah ka bari man."

Dariya yayi, ya ce,
"To na bari. My beauty."

Murmushi tayi, sanna suka gaisa dashi.

Lemon kwakwa wanda yaji madara da dabino ta zubo masa. Ya sha sanyi.

Amsa yayi yana mata godiya. Yana kurba ya lumshe ido, yana me jin wani sanyi a cikin jikin sa.

A hankali a hankali ya dinga sha, snaks ta mika masa, sosai ya ci.

Dan kasa cin girkin da tayi ma yayi, har magariba yana gidan dan sallah yaje ya dawo.


Tare da Baffah suka shigo, Baffa na tsokanar sa da bazai bashi Najwa ba.

Dariya yayi, ya ce,
"Ai Baffah da kun kaini kabaru kuwa, dan nasan na rasa Najwa na rasa rayuwata ne."

"Ja'iri toh nagodewa Allah da ya hada Najwa da me son ta kamar ka. Allah baka ikon rike ta amana.
Najib na dade ina rokan Allah ya bawa yarinyar nan miji na gari kamar yadda kai ma nake maka addu'ar nan.
A duk cikin jikokina kun fita zakka. Bbawai nafi son ku bane. A'ah, kai Allah ya baka hankali da nutsuwa tare da ga ilimi. Kuma kuna amfani dashi. To haka ma Najwa. In ka zauna da Najwa nasan zaka gane nagartar ta.
Najib na baka amanar Najwa karike min ita hannu bibiyu,"

Kasa Najib ya dauka daga kan kujera, hannun Baffa ya kama ya ce,
"Baffa na maka Alkawarin bazan taba  yarda amanar nan taka ba. Zan rike ta hannu bibiyu insha Allah, ka tayani da addu'a Allah bani ikon rike ta."

Kansa Baffa ya dafa, yana shi masa albarka.

Dai dai lokacin su Najwa suka fito daga dakin Ummah.

Kallon su take yi cike da sha'awar su, Falon suka karasa,

Kan Najwa a kasa, ta ce,
"Baffa barka da dawowa!"

Kallon ta yayi, Cikin so da kauna, ya ce,
"Yauwah Najwa ya bakon naki."

Fuskar ta, ta rufe a jikin Ummah, dariya su ka, saka gaba dayan su.

Najib kuwa murmushi yayi, yana kallon ta. Ji yake kamar yaje ya rumgume ta.

Ummah ya kalla, ya matsa kusa da ita, ya ce,
"Tsohuwa me ran karfe ina yini?"

"Kai ni ban amsawa ace, tin dazu ka kasa zuwa kazo ka gaushe ni."

Dariya Baffa yayi, ya ce,
"Ke dai kishi kike kawai."

"Affuwan uwar gida na, amaryar taki ce akwai siye mutane, Allah Ummah in ina tare da ita bana iya tina koma."

Hannu ta fara tafawa tana salati. Najwa kuwa kara makale Ummah tayi, a ranta kuma tana mamakin ko Najib yasan san su haka ne.

Sun jina suna hirar su da tsokana tsakanin su ta jika da kakanni sannan Baffa ya kalli Najwa da har lokacin ta tana makale da Ummah.

Kai ya girgiza, yana murmushi, a ransa yana jin dadin halin Najwa na Kunyar nan.
"Najwa ai sai a bashi abinci ko?"

Kamkame Ummah tayi, Ummah ta ce,
"Oh ni "ya su, dan Allah sake ni, kai haka kake fama da ita da wannan kunyar tata."

Dariya Najib kawai yayi, a ransa kuma ya ce,
"Allah dai yasa kar wannan kunyar ta cuceni. Amman kuma tana mata kyau."

Da kyar ta mike ta hada masa abinci a babban falo.

Bema ci ba, sai kallon ta da ya tsare ta dashi.

Da zai tafi ya kaiwa Su Ummah kayan da ya kawo musu yai musu sallama.

Abincin ta kwashe ta saka masa a motar sa.

Sai da ya zauna sannan ya miko mata tata ledar.

Da kyar ta amsa tana masa addu'a. Inda sukai dashi akan gobe zai dawo.

Cike ta shige ciki da jin kunyar kakannin nata.

Kayan da ya kawo mata ta dire musu tayi cikin Dakin Ummah.

Kwanciyya tayi, tana tunanin Najib. Ta tabbata son Najib ya vama gauraye jikin ta, zuciyar ta kuma sonsa kadai ta sani ta kuna saba dashi. Rabata da Najib ba karamin abu bane.

Yanzu ta gane ba karamin kamu son sa yayi mata ba.

Tana godewa Allah da ya bata shi, tana kuma addu'a Allah yasa shine Alheri a rayuwar ta.

Ido ta lumshe, fuskar sa ta gani tana sakar mata da murmushi me santaya zuciya. Itama murmushin ne ya subuce mata.

Fulo ta jawo ta rumgume, a ra ta kuma tana cewa
"yanzu fa sauran wata biyu ta zama mallakin Najib."

Wata fadywar gaba taji kirjin ta yayi, wanda sai da ta dafe shi.

Ita tsoron sama takeyi gaba daya.

*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*133*


*UMMU AFFAN MY KAWALLI. REALLY LOVE U. TNC FOR UR CARING ND LOVE. ALLAH KARA MANA ZUMUNCI YA BARMU TARE. AMEEN*





Ita tsoro ma takeji gaba daya. Dan Najib yadda yake son kasancewa tare da ita tasan bazai taba daga mata kafa ba.

Gashi taji ana yawan fadar First Night akwai wahala. Wata faduwar gaban ta karaji.

Juyi tayi, tana tina yadda take da raki ciwo kadan tai masa kuka, bata son komai ya taba ta.

Ba abinda ta kuma tinowa sa lokacin da cinnaka ya cije ta a makaranta ta saka kuka ita ce har clinic.

Bare kuma first night. Bata taba mantawa wani littafi da Zahra ta karanta take bata labaton yadda amaryar ta sha jiki, wai jar da su dinki.

Idon ta, ta bude ea sauri wanda suka rine sukai jajie dasu alama ta jin tsoro.

Lumshe su ta kuma yi, a ranta kuma tana cewa,
"Ai kowa da haka ya saba. Da kuma haka duk aka same mu. Abinda baya kisa a da sauki."

Ta fadi hakan ne dan kawai ta bawa zuciyar ta hakuri.

Wani tunanin ya kuma fado mata, tab kuma ace da safe da wane ido  zaka kalli mijin.

Tab ai shikenan kuma, kullum idon mutum a rufe zasu kasance.
Zahra ta tuna, wacce ko a washe gari ma sai nan nan take da Mustaphan ta.

"Tab!"
Ta fada a fili, tana mikewa zaune.

Kayan jikin ta, ta cire ta shiga bandaki tayo wanka.

Kayan baccin ta, ta saka, ta dauki hijab ta zira ta nufi kitchen dan taji tana jin yunwa.

Cake ta dauko ta lemo, tayo Falo, su Ummah suna zaune suna hira.

Sai da taci ta koshi ta dauke kayab da tayi amfani dasu sannan ta yi musu sai da safe.

Har ta juya Baffah ya kira ta. Komawa tayi ta zauna a gefen kafar sa.
"Najwa!"

Ya kira sunan ta, amsawa tayi da
"Na'am."

"Allah yayi miki albarka. Allah ya baki zuri'a ta gari."

"Ameen Baffah."
"Najwa ki rike Najib hannu biyu dan Najib mijin aure ne. Kinji."

Kai ta gyada masa,
"Shikenan dauki kayan da ya kawo miki kije ki gani kema."

"Toh Baffah nagose Allah daxa girma da lafiya."
"Ameen Najwa."

Kayan ta dauka, tayi musu sai da safe.

A kan gado ta juye kayan, wasu hadaddun Dogayen riguna ne, sai riga da siket da mayafai masu kyau.

Hadi da jaka da takalma masu kyau dasu. Sai turare kala biyar duk masu kamsgi da tsada.

Kai ta girgiza, ta ce,
"Hamma badai son wahala ba. Nagode Allah kara budi."

Kayan ta mayar cikin leda ta saka a durowar Ummah.

Alwala tayi ta kwanta, lokacin karge sha dayan dare.

Wayat ta, taji tana kara, dubawa tayi, murmushi taui ta dauka da sallama.

"Assalamu Alaikum."
A speaker ta saka wayar ta ajiyr a gefen ta.

"Wa'aikaum salam!"
"Sannu Hamma na kaje gida lafiya. Ya hanya?"

Murmushi yayi, dan Najwa akwai kula,
"Lafiya Alhamdulilah! Na barki lafiya?"

"Lafiya. Hamma angide fa  Allah kara budi da arziki. Allah yasa ka gama lafiya. Allah rabaka da iyayen ka lafiya. Suma Allah ya saka musu da alheri."

Tin da ta fara addu'ar ya lumshe ido, muryar ta tana katsa shi har cikin jijiyoyin jikin ta.

Rasa abinda zai furta yayi, sai dai fuskar sata gaza buye farin cikin da yake ciki.

Shiyasa kullun a ransa yake dada godewa  Allah da ya kawo masa Najwa a dai dai lokacin da vyafi bukatar sa.

Irin su Najwa sune matan aljanna ya fada a rasan.

"Ameen Ameen Baby nah, kema Allah miki albarka. Ya baki ya'ya na gari masu mimi biyayya. Allah ya sakama su Mami da Dady da alheri. Ina alfahari dake. Kece, Nurul Kalbi nah."

Murmushi tayi kawai, sai kuma ta ce,
"Hamma bari na barka ka kuma kira Anty na. Kaga tib da kazo bakuyi waya ba."

Murmushi kawai yayi, ya ce,
"Kar ki damu sai da mukai waya sannan na.kira amarya ta."

"Hamma kenan."
"Love, ni ki canja min suna."

Murmushi tayi, ta ce,
"To ka bari sai  anyi abin."

Dariya ya saka ya ce,
"Menene abin?"

"Kai Hamma. Kasani fa."
"Wallahi ban gane ba. Kinsan abin da yawa fa wanne daga ciki."

"Oh har yawa ne dasu, wanne da wannene to?"

Murmushi yayi, ya ce,
"Bari na lissafo saii ki zaba a ciki."

"Toh!"
"Kinga akawai, Aure ko, da kuma lokacin da zan maida ke matata sosai..."

Wayar ta katse. A ranta tana, cewa,
"Hamma ya fiya neman rigima."

Bata gama maganar zuci ba ya kira.
"Baby na lafiya?"

"Lafiya lou."
"To kina ji?"

"Eh, amman ni wanda nake nufi in anyi auren."

Dariya ya saka, ya ce,
"Baby na akwai ki da wayo."

"Ai ka fini."
Murmushi yayi, ya ce,
"To shikenan. Kije ki kwanta sai da safe kiyi alwala da addu'a "

"Insha Allahu, Allah tashe mu lafiya."
"Ameen!"

Alwala ta kuma daurowa tayi addu'a ta tofe dakin da jikin ta.


Washe gari ma yazo a gidan suka yini, sun sha hira anan yaci abincu sai magariba ya tafi.

Shima dan yana son yaje gun Khaleel ne. Sun rabu akan gobe zai dawo.

Tana daki tana duba wani littafi Mamin Najib ta kirata.

Dagawa tayi da sallama ta gaishe da ita,
"Mami ina yini?"

Daga can bangaren Mami ta amsa mata, tare da tambayar mutan gidan.

"Suna lafiya, yasu Dady, dasu Bara'atu da Hamma Najib."

Murmushi Mami tayi, ta amsa da suna nan kalau.

"Najwa ashe kuma biki ya taho ko? To Allah yasa ayi damu,"

Najwa tin da Mami tayi maganar biki tayi shiru dan kunya take ji akai maganar.

Mami ta gane shiyasa tayi mata sallama. Ta kashe tana me jin dadin wannan halin na Najwa.

Shiyasa takewa Najib kwadayin ta.

Sai ta tina lokacin da taso ta hada su ya nuna tayi masa karama.

Yanzu kuma ai gashi nan ita din ce dai.

Murmushi tayi, tana duba kayan lefen Najwa banda wanda Najib ya kawo ga wanda Dady ya hada mata.

Masha Allah!  ta rurufe kayan ta matsar gefe.

Gidan Khaleel ya nufa, kai tsaye a falo ya same su.

Lil N (Sunan da Yasmeen kanwar Khaleel ta saka mishi kenan.) na ganin shi ya taho a guje ya rumgumeshi.

Dagashi yayi shi ya rumgumeshi yana jin son yaron a cikin jikin sa.

Sai ya tina da tini shima ya a da kamarsa yanzu.

Tinanin ya kawar yana wa Allah godiya.

Zama yayi, suka gaisa, da sauri Khadija ta mike ta kawo masa lemo da abinci.

Wajen ta bari. Lemon kadai ya sha, ya rumgune takwaran sa a jikin sa.

*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*135*

*Fatitih kema kina raina. Nagode da kwarin gwiwa da addu'ar ku gare ni. Allah ya bar kauna.*



Har bakin mota suka rakosu suna sa musu albarka.

Sannan suka tafi da kewar ta. Itama ta yaba da su dan mutanen kirki ne.

Gidan Khaleel suka tafi can rigiyar zaki. Yana gida yana jiran zuwan su.

Dan har girke girke Khadija tayi musu.

Suna zuwa Khadija ta taro ta, ta zaunar da ita.

Haka Lil N na ganin ta shima yayi wajen ta.

Daukar sa tayi tana masa wasa. Khaleel ta gaisar, suka gaisa kamar sun san juna.

Lemo da Ruwa Khadija ta fara gabatar musu dashi, ruwan ta kurba kadai.

Sai wasa takewa Lil N, Najib kuwa ya zuba mata ido dan ba karamin kyau yaron yayi mata ba.

Hoto kawai yake daukar su ita bama ta sani ba.

Dagowar da tayi ta ya zuba musu ido yana musu vedio.

Hararar sa ta faki ido tayi, murmushi yayi, yai mata gwalo.

Kitchen Khadija ta shiga, Khaleel kuma yayi cikin daki.

Kallon ta yayi, ya ce,
"Baby nah Yaron ya miki kyau kamar naki."

Murmushi tayi kawai.
"Allah ya baki kamar shi nan da wata goma."

Kai ta girgiza kawai ta cigaba da yi masa wasa. Ta dauke hankalin ta daga kan sa ma.

"Tashi muje kuci abincin."
Kallon Khadija, Najwa ta ce,

"Ki bari sai anjima ko?"
Ta kalli Najib.

"A'ah ban yadda ba. Haka fa a gidan su Mamah ma, bata ci abincin ba."
Najib ya bata amsa.

Murmushi Najwa tayi ta kalli, Khadija ta ce,
"Allah Sis naci abinci, kafin mu fito, na miki alkawarin kafin mu tafi zanci."

Murmushi tayi, ta ce,
"To shikenan ai tayi alkawari kaga."

Khaleel ne ya fito, ya ce,
"Kanwata yana ta kura miki ko?  Allah sai kin dinga maganin sa dan akwai takura kina ganin shi nan."

Ita dai Najwa murmushi kawai take yi, fita sukai suka barsu Najwa kadai.

Dakin baccin su ta ja ta, suka je tana kallon hotu nan bikin ta.

Dan Lil N ma goya shi tayi har yayi bacci a bayan ta.

Khadija tayi tayi ta sauke shi taki.

Zaman da suka danyi da Khadija ba karamin sabawa sukai ba.

Khadija aranta ta ce,
"Yanzu Najib zai yi aure mace mai mutunci da iya zama."

Suna cikin daki suka dawo wajen magariba. Falon suka koma har lokacin tana goye sa Lil N.

Najib na ganin su ya dauko waya ya fara daukar hoton su.

Da taga abinda yake ma kai kawai ta girgiza tayi shiru dan baza ta iya masa magana ba.

Sallah magariba sukayi, sannan suka dawo. Abinci suka ci suka mike zasu tafi.

Kayan da Najib ya soyawa Lil N ya mika mata ta mikawa Khadija.
"gashi inji Hamma."

Kallon ta yayi, Ya ce,
"In jita dai. Nawa na nan zuwa."

Sukai sallama bayan sun yi musayar number junan su.

Har gida ya maida ita lokacin Baffah ya dawo suna falo shi da Ummah.

Yana ganin su ya saki fara'a ya ce,
"Kun dawo?"

"Eh Baffah mun dawo. Ya gidan?"
Najwa ta tambaye shi.

"Lafiya lou."
Sannan suka gaisa da Najib yana jansa.

Najwa ita dai tana mamakin Najib ya ja su Baffah yaje yaja su Abbah.

Tana farin cikin samun miji da ba ruwan sa.

Sai wajen karfe tara ya Mike yayi  wa Su Ummah sallama.

Ummah ce ta kalli Najwa ta ce,
"Kije ki rakashi man."

Mikewa tayi, tabi bayan sa. Tafiyar ta ya jiyo wannan yasa ya juyo yana kallon ta.

Murmushi ya saki, ya ce,
"Najwa tafiyar taki ma daban take."

"Ni dai muje."
Dariya yayi, ya ce,
"Bama zaki tsaya kiji ba kenan."

Har mota ta rakashi sukai sallama ya tafi.

Daki ta tafi tayi wanka ta haye gado. Kiran sane ya shigo dan har yaje gida.

"Love!"
"Na'am Hamma ya hanya?"

"Hanya lafiya. Ya na baro ki."
"Lafiya klo."

"Baby na gobe nake son na koma gida fa."
Gaban ta taji ya fadi.

Duk da tana matsa masa ya koma wajen matar sa da aikin.

"Amman Hamma kuma shine baka fadamin ba."

"Kiyi hakuri Baby na, bana son ki shiga damuwa ne."

Dan murmushi tayi, ta ce,
"To ya zanyi, amman da kafadan ai."

"Ayi min affuwa bazan kara ba to."

"Shikenan Allah kaimu goben."

"Ameen. Wallahi Ina kara son ki Najwa saboda hankalin ki da hakuri. Wannan yasa nake kara kwadayin zamowar ki matata."

"Hmm Hamma kenan. To kije ki kwanta sai da safe kiyi alwala da sallah kinji."

"Insha Allah sai da safe."

Sukai sallama. Wani abu taji ya tare mata kirjin ta. Tasan ba komai bane sai kishin Najib.

To ya zatayi, tinda Allah ya daura mata son shi.

Alwala taje tayo tayi sallah tana Rokar Allah ya rage mata zafin kishi.

Ta jima tana addu'ar sannan ta koma kan gado.

Bata kara sanin tana son Najib ba sai yau, gashi Najib ba nata bane ita kadai.

Kuka ta fashe dashi, ta jima a kwance dan sai wajen karfe uku ta samu tayi bacci.

Karfe biyar mike tayi sallah ta koma.

Ummah kuwa tin da ta tashi taga Najwa bata fito ba tasan ba lafiya ba.

Dakin ta, ta shiga ta ganta a kwance tana bacci.

Falo ta koma. Sai karfe goma ta tashi daga bacci.

Wanka tayi ta shirya cikin wata doguwar purple din riga.

Batayi kwalliya ba daga hoda sai man lebe sai turare da ta fesa.

Falo tayi, Ummah ta hanga, akan kujera, gefen kafar ta, ta karasa ta gaida ta.

Amsawa Ummah tayi tana leka fuskar ta,
"Najwa! Lafiya?"

"Lafiya lou Ummah."
"Amman naga idon ki ya kunbura haka."

"Lah Ummah wallahi bacci ne banyi ba jiya shiyasa."

"Saboda me to?"
"Kai nane yake dan ciwo."

"Sannu to, tashi kije kici abinci kisha magani."
"Toh!"

Ta mike, har ta fara tafiya ta juyo ta ce,
"Ummah yau fa Hamma zai koma."

Murmushi Ummah tayi, ta ce,
"Haka ya fada min."

Gaba Najwa tayi kitchen ta shiga tea kadai ta sha. Ta zauna tunani.

Sai daga baya ta tashi ta kwaba cake, tayi beaking nashi, meat pie ta soya shima dayake akwai dambun

Please Login or Register in order to submit comment