Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

siyayya.

Dan ranar Khaleel zeje gun Mqtar da ze aura, shi kuma Najib ya ce, ba ranar ze jeba.

Wanna yasa basu hadu ba yau. Iin garin ba dadi yasa ya mike ya haye sama.

Kwanciyya yayi, Sai la'asar ya tashi yaje yayi sallah sannan ya dawo gidan.

Mami na bayan gida. Dan haka dakin sa ya shige yaje yayo wanka ya shirya cikin dark blue rin wando da bakar riga. Sosai yayi kyau turare ya dauko ya feshe jikin sa da shi.

Kasa ya sauka yayi bayan gida. Mami ce zaune da Baba Tani.

Gaisar da Baba Tani yayi sannan ya wu gun Mami.

Ya fada mata ze dan zaga gari. Mami tayi masa Addu'a Allah kiyaye hanya

Baba Tani kuma ta ce, masa ya samo mata sirika.

Ya fita yana dariya dan shi abin ma dariya ya bashi.

Ya jima akan titi yana zagayen gari. Kan BUK road yayi, sabuwar kofa ya gani,

Ganin kotar ta burge shi yasa ga danna hancin motar sa cikin kofar,

Tafiya yake cikin nutsuwa dan waninirin nishadi yake ji na dibar sa.

Dan unguwar ta burge shi. Yana zuwa dai dai Karshen hostel din School of Hygiene aka tsaida su dan an taso yan makarantar Fadimatu.

Gee yayi da motar sa, yana kallon dayan gef3n titin.

Kamar an ce, ya dago kansa, ya hangi wata yarinya. Kyakyawar yarinya. Rike da hannun kanwar ta.

Fara ce, daguwa, tana da manyan idanu duk da kanta akasa yake amman yana ganin alamun manyan idanun nata.

Hancin ta dogo dashi siriri. Sai dan karamin bakin ta. Fuskar ta doguwa me kyau da ita.

Tafiya take cikin nustuwa daga gani kasan yarinyar akwai tarbiyya da hankali.

Sanye take da kayan makaranta. Ruwan omon  dogon wando, rigar jikin ta kuma ta wuce gwiwa sai hijab  wanda yake dogo har gwiwar ta, ruwan daurawa. ba karamin burge shi tayi ba.

Ya shagala da kallon ta har ta kure masa. Wannan yasa ya dawo cikin hayyacin sa.


Motar ya tayar, yaje yayo Uturned, amman wani abin haushin sam bai gansi ba sama ko kasa babu su babu alamar su.

Ya jima a unguwar yana zgaye amman sam be ga ko me kama da ita ba.

Duk sai yaji jikin sa ya mutu, dan ba wacce yake son kara gani sai ita.

Kiran sallah magariba shi ya dawo dashi hankalin sa. Massalaci dake nan kusa da katin dan Aljannah nan yaje yayi sallah.

Yana idar wa yayi gida. A massalacin unguwar su yayi sallah isha'i sannan ya shige gida.

Mami tana kasa tana kallon labarai a BBC ya shigo. Tin daga sallamar da yayi tasan ba lafiya ba.

Kallon sa ta tsaya yi. ta ce,
"Najib lafiya kuwa?"

Murmushi ya kakaro,
"Lafiya lou, na gaji ne."

"Anya?"
"Eh!'

"To sannu,"
"Yauwah!"

Ya zauna a gefen ta. Ido ya lumshe ba wacce yake gani sai Wannan yarinyar.

Yana jin Mami na waya da Dady amman yayi shiru sai kace me bacci.

Sai da Mami ta mika masa wayar sanna ya bude idanun sa. Karba yayi ya kara a kunnen sa.

ya ce,
"Dady ina yini?"

"Lafiya lou, me yake damun kane."
"Ba komai Gajiya nayi ne."

"Ayyah sannu kaje kayi wanka ka kwanta."
"Toh!"

Ya mikawa Mami wayar.

Sai da suka gama wayar sannan ta ce.
"Son tashi muje muci abinci."

Dan kar ta shiga damuwa yasa ya mike suka fara cin abincin, kadan yaci ya mike yace ya koshi.

Kallo Mami tabishi da shi. Sama suka haye, a dakin Mami yayi wanka yasaka kayan baccin sa.

Ya kalli mami y ce,
"Mami bari na kwanta sai da safe."

"Allah tashe mu lafiya."
"Ameen!"

Yana zuwa daki yayo alwala sannan ya kwanta bayan yayi addu'ar bacci.

Ya dade yana juyi daga bisani kuma bacci ya dauke shi.

Cikin dare ya farka, kasa komawa baccin yayi, sai mafarken yarinyar yake.

Alwala yaje yayo ya tada sallah. Be kara runtsawa ba har aka kira assalatu.

Dakin Mami yaje ya tadda ta tashi, murmushi karfin hali ya sakar mata ya wuce masallaci.

Yana dawo wa yayi dakin Mami. Mami bata dakin. Kwanciya yayi.

Bacci ne ya duke shi, sakamakon rashin baccin da beyi ba jiya.

Ya jima  yana baccin dan har Mami ta gama masu kayan kari tayi wanka be tashi ba.

Sai karfe goma sha daya na safe sannan ya tashi, agogo ya duba, yaga karfe sha daya har da kwata.

Ban daki ya shiga yayo wanka ya fito ya shirya cikin wandon sa wanda da kadan ya wuce gwiwa. Da rigar shan iska. Wankan turare yayi ya sauko kasa.

Mami na zaune a falo tana kallo ya sauko. Ya durkusa a kasa ya ce,
"Mami ina kwana?"

Mami ta amsa da,
"Lafiya lou. Ka tashi lafiya."

"Lafiya lou Mami."
"Masha Allah! Son jiya me ya hanaka yin bacci, dan yadda yau kayi baccin nan me yawa ya shaida min bakayi bacci ba jiya."

"Son kar ka boye min damuwar ka ni mahaifiyar kace kuma indai bata fi karfi na zan yaye maka ita."

"Na sani Mami. Amman ban ki fada miki dan wani dalili ba sai dan naga abun kamar be da mahimmanci sai daga baya naga abin ya shige ni ta zama me babban matsayi a guna."

"Menenen wannan abun kuwa?"
"Mami jiya bayan na fita zaga gari ne, sai Allah ya sa na shiga ta sabuwar kofa, Mami muna shiga aka rike mu saboda yan makaranta da zasu tsallaka titi."

Numfashi yaja, ya cigaba da magana
"Mami garin kale kale na Allah ya daura ido na akan wata yarinya, nai ta kallon ta Mami, daga bisani zuciyata tace na bita, sai kafin naje nayo Uturned har ta bace min. Mami nayi neman, nayi neman amman ban ganta ba."

Wata ajiyar zuciya ya sauke, ya ce,
"Mami, tinda daga lokacin na nemi walwalata na rasa, jiya kuwa kasa bacci nayi Mami dana rufe ido na sai Na ganta."

Murmushi Mami tayi, ta ce,
"Son ya fada tarkon soyayya be sani ba."

Najib ya kalle ta cikin rashin fahimta
"Mami soyayya kuma?"

"Eh! Son yarinyar kake,"
"Tabb din."

"Ya yarinyar take."
Mami ta tambaye shi.

"Mami Yarinyar kyakyawa ce, kuma daga gani tana da hankali tarbiyya da nutsuwa da ilimi dan daga makaranta ma naga ta dawo."

"Tayaya kasani."
"Mami daga kallo ma kadai zaki gane haka a tattare da ita."

"To Najib Allah shige maka gaba. Allah bayyanata."
"Ameen."

"Son Anjima zamu gidan Uncle Ahmad dan sun dawo tin shekaran jiya."

"Haba ai ban sani ba da na shiga jiya."
"Anjima zamuje ai "

"Allah kaimu."
"Ameen!'

"Kuma kwana biyu Salim be kira ni ba."
"Kai kuma yayan kwabo baza ka kira shi ba."

"Kai Mami ni abubawa sun min yawa in ba yanzu da na dan samu hutun nan ba."

"Allah ya kyauta."
"Ameen dazu Munyi waya da Ummah tana gaishe ki."

"Ina Amsawa."
"Jibi nake son naje naci dambum tsohuwa."

Mami ta harreshi ta ce,
"Son Allah ko?"

"Yi Hakuri Hajajuna"
"Bari naje na shirya dan yau ina son ganin Mami nah."
Ya fada yana mikewa

Daki ya shiga, wata farar shadda ya dauka ya saka, sai bakar hula da takalmi, sosai yayi kyau.

Najib ba dai kyau ba, kome yasa kyau yake masa duk arahar abu in yasa kyau yake masa dan sai ayi tsammanin me tsada

Najib akwai farin jini dan yan mata da yawa na son sa, rashin samum fuska shi yake sawa basa tunkarar sa.

Najib akwai kyauta, bai da kyamar na kasa dashi ko mara shi dan shi yawancin masu aikin su abokan sa ne.

Ya iya mu'amala da mutane dan duk yadda kakai da fada ko wani hali zai iya tafiyar dakai cikin kwanciyyar hankali.

Bai da fada, kuma sam ko ka tabo shi zai dauke kai sa.

Yana da dabi'u masu kyau. Wanda da kowa zai iya zama kuma a zauna lafiya.



*INDABAWA*

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*



PAGE *66-70*



Yana gama shirin sa yayi dakin Mami. Lokacin ita ma ta shirya cikin wata atamfar ta fara da ja.

Farin mayafi ta yafa da jaka da takalmi tayi kyau da ita.

Sun fito ya bude mata gidan gaba.
Suka dau hanya.



*-*-*-*-*-*

"Assalamu Alaikum!"
Wata murya me dadi da sanyi tayi sallama a cikin wani katon gida.

Me gadin gidan dake gefe, ya washe baki, ya amsa masu da
"Wa'ailaikum salam!"

Suma fara'a dake kan fuskar su ta fadada. Suka zube a kasa. Suna gaishe shi.
"Baba ina yini?"

"Lafiya lou Basma da *Najwah* kun dawo lafiya."
Ya amsa musu cikin sakin fuska.

Suma cikin fara'a suka amsa masa.
"Lafiya lou."
"Masha Allah!"
Suka mike suka shige ciki.

Da sallama suka shiga katon falon nasu, wanda ya Wadatu da kayan alatu, kujeru ne a jere a dakin gefe kuma kayan kallo.

Sai can gefe kuma wajen cin abinci ne, sai matattakala da zata sada ka da saman gida.

Mahaifiyar su suka hanga akan sallaya da carbi a hannu tana jan sa.

Da gudu Basma tayi gun Maman tasu ta haye cinyar ta.

Basma ta ce,
"Mami nah Ya gida."

Mami ta amsa tana shafa kan ta.
"Lafiya lou Basma."

*Najwa* ce ta karaso dakin, itama a jikin Mami ta zube,
"Mami sannu da gida."

"Yauwah!"
"Ya gidan?"

Mami ta ce,
"Lafiya alhamdulilah."
"Masha Allah!"

Ta mike tayi sama, tana cewa,
"Basma taso a cire kayan makarantar ko?"

Basma ta amsa da
"Toh! Adda."
Ta mike ta bi bayan ta.

A saman ma wani falo ne shima wanda aka saka masa Kujeru da kayan kallo.

Wani daki ta bude, daki ne me kyau a kasa masa gado madai dai ci, da katuwar durowa, sai labulaye.

Basma ta fara cire wa kayan jikin ta, ta dauki wadan da suka cire dazu ta saka mata.

Riga da wando ne, irin Pakistan din nan. Ruwan hodar riga da ruwan gayen wando.

"Jekiyi alwala magariba tayi,"
"Toh Adda."

Ta shige ban dakin dake dakin tayo alwala, ta fito tayi Can falo.

Kayan jikin ta *Najwa* ta cire, ta sa irin kayan da ta sakawa Kanwar ta Basma.

Alwala tayo, ta fito ta hau kan sallaya tana tasbihi, har akayi kiran sallah magariba sannan ta mike ta tada sallah.

Sai da tayi isha'i sannan ta yo shafa'i da wuturi sannan tayo Falon gidan nasu.

Mami ta hanga ita da Basma na zaune.

Gefen su taje ta zauna, ta ce,
"Mami su Hamma da Dady basu dawo ba."

"Eh basu shigo ba amman nasan yanzu dau suna hanya."
"Toh Allah dawo dasi lafiya."

Mami ta amsa da,
"Ameen. Ya makarantar?"

"Lafiya Mami."
"To Allah bada sa'a."

"Ameen."

Mami ta kalli Basma ta ce,
"Basma ana dai gane karatun ko?"

Basma ta ce,
"Eh Mami."

"Masha Allah. Allah kara basira."
*Najwa* da Basma suka amsa, da
"Ameen."

Dai dai lokacin su Dady da Hamma Salim sukayo sallama.

Da gudu Basma tayi gun Dady ta rumgume shi tana, ce wa.
"Dady oyoyo!"

Shima rumgume ta yayi,
"Oyoyo Basma ta."

Ya karaso cikin dakin. *Najwa* ta kalli yayan ta. Ta ce,
"Hamma Salim sannu da zuwa ya hanya."

"Lafiya lou *Najwa.* "
"Masha Allah."

Ta juya gun Dady, ta ce,
"Dady sannu da zuwa."

Dady ya, amsa mata, da
"Yauwah!"

"Ya hanya, ya aiki?"
"Lafiya Alhamdulillah!"

"Dady Allah kada budi."
"Ameen *Najwa* "

Mami ce ta masa sannu da zuwa sannan suka mike sukayi sama.

Ya Salim ma sama ya yi dan rage kayan jikin sa.

*Najwa* ce ta kalli Basma, ta ce,
"Yauwah Basma, biyo min haddar da zaku bayar gobe."

"Toh Adda! Suratul Mulki ce."
Nan ta fara rairowa ta tare da fitar da ko wanne hukunci.

Karatun nata me dadin sauraro da fitar da ko wacce harafi,

Sai da ta gama sannan tace ta karanto mata tauhidin da tayi musu yau aji.

"Basma, karanto min Tauhid din da na karanta muku a aji."

"Toh Adda."
Ta dauki littafin ta, ta fara karanto mata.
"Su sa'al:-Man kala kalaaka?
Tambaya:-Wanene ya halice ka.

Ja jawabi.:-Allahu huwa lazi kalaqani, wa kalaqa kulli shai'in
Amsa:-Allah shine ya halice da dukan komai."

"Masha Allah! Da kyau."

Mami ce ta sauko, ta ce,
"ah lalai Autata kina kokari kema."

"Mami so nake nima na zama kamar Adda."
"To indai kina so sai kin dage kinga itama ba. A zaune take ba."

Mami ta kalli *Najwa* ta ce,
"Toh *Najwa* Menene tsarki gaba daya. Da bayani akan sa."

*Najwa* ta ce,
"Mami a cikin wani littafin Fikihul miyasir. Malamin yace,
Abubawa biyu ne ke sa ayi tsarki da karamin hadasi sune
tusa, fitsari, maziyi, da wadihi. Wadan nan alwala suke wajab tawa
Janaba, nifasi, haida, sune babban hadasi su wanka suke wajab tawa.

Sharadi ne ayi tsarki dan ingantuwar sallah.
Tsarki, :- shi tsabta, dan kawar da dukkan datti da dauda.
Kawar da najasa daga jiki, da wanka, dan kawar da bababn hadasi, haka ma alwala tsarki ce kamar yadda taimama ma take tsarki."




*INDABAWA*

NAJWA*



*BY MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


DEDICATED TO *RASHIDA ABDULLAHI KARDAM*
*AUNTY RASH*


PAGE *71-75*

Mami ta ce,
" *Najwa* mane dalili nayin tsarki."

"Shima Malam min yace, dalilin tsarki dan ingantuwar Sallah shine,
Manzon Allah (SAW) Yace, "Sallah bata karbowa ba tare da anyi tsarki ba."  Musulimu da turmizu da ibn maja suka rawaito shi.

Wata fadar Annabin ma, yace, "Mabudin Sallah shine tsarki. Abu dawud, turmuzi su suka rawaito su.

Manzo Allah na kuma cewa, "Tsarki yanki ne na imani, kuma sharadi ne na cikar sallah." Musulimu ne ya rawaito.

"Na'am! To wanda ya kiyaye tsarki yana da falala."
"Eh yana da falala domin yana daga cikin wadan da Allah yake so."

Allah madaukakin sarki yana cewa,
Lallai Allah na son masu tuba, kuma yana son masu tsarki."

"Masha Allahu!"
Dady ya fada dan duk tambayoyin da Mami ke yi mata na tsaye yana ji.

Lokacin Hamma Salim ya sauko, kallon su yayi. Ya ce,
"Mami nifa yunwa nake ji."

Mami ta Ce,
"To ai mu ku muke jira ko?"

Suka nufi wajen cin abincin nasu. Tuwon shikafa Mami tayi miyar agushi da taji naman kasuwa sai kamshi ke tashi.

A katon faranti ta saka musu tuwon sannan ta zuba miyar a wani tangaran me zurfi.

Hannu suka wanke sannan sukayi Bismillah suka  fara cin abincin gaba dayan su a mazubi daya.

Abin gwanin sha'awa. Suna gamawa *Najwa* ta kwashe kayan takai kitchen.

Falo ta dawo ta zauna suna hira. Karfe tara duk suka haye sama kowa yayi dakin sa.

*Najwa* ce ta cirewa Basma kaya, tasa mata kayan bacci sannan tasa tayo alwala.

Basma ta ce,
"Adda wai saboda me muke yin alwala kafin mu kwanta."
Murmushi *Najwah* tayi.

"Saboda kariya daga shaidanu, sannan alwala tana kan kare zunubai. Kankare zunibai shine kamar kin taba abinda Allah ya hana to duk lokacin da kike yin alwala zununin da kika kwasa wajen taba wa, in dai kika wanke hanu a lokacin alwala kina wanke zunubin da kika kwasa  shi. Haka nan baki. In kinyo Abinda Allah ya hana in kinje kurkure shi to kina wake zunuban da ya dauka. 

To haka yake har ki gama alwala kina wanke zunuban da kika kwasa ne. Kinga ko dan haka ai yana da kyau muna alwala me kyau sannan kuma a koda yaushe ko?"

"Eh Adda!"
"Sannan akwai lokacin da Manzon Allah (SWA) yake cewa sahaban sa,
"Shin in fada muku wani abu. Wanda in har kayi shi Zaka samu lada sannan kuma kan karar zunibi ne."
Suka amsa da eh suna son sani.
sai ya ce,
"Duk wanda ya aikata alawala a lokacin da rai bata so, to tabbasa Allah zai yafe masa zunuban sa koda sukai kumfar kogi ne."
Kinga Alwala kam abar rikewa ce."

"Adda mene a lokacin da rai bata so."

*Najwa* tayi murmushi ta ce,
"Kamar da sanyi in ana muku muku to kuma kayi alwala. To wannan irin wadan nan  lokaci sune zakayi abinda rai bata so."

Kai Basma ta ke gyadawa.
"Kin gane."

"Eh na gane Adda."
"To kwanta da hannun dama."

"Adda shima dan me in zamu kwanta kike sani kwanciya da dama."
"Saboda Manzon Allah ko me zaiyi da dama yake, shaidan la'ananen Allah ne ke yin abu da hagu, kuma duk wanda yayi abu da hagu da gangan to Allah yayi hani da haka. Dan haka akwai hadinsin da Annabi yake cewa, in zamuci abu muci da dama haka nan in zamu sha ruwa shima musha da dama.

kuma malaman mu suna hurar mu da duk abinda zamuyi muyi da dama.

Kuma duk abinda Manzon Allah ya hne mu dashi yana da kyau mu hanu.

Akwai wani Mutum lokacin Manzon Allah (SAW) da yake cin abinci da hagu. Sai ma'aiki (SAW) Ya ganshi sai yayi masa magana sai ya ce,
"Shi baze iya ci da dama ba."
Manzon Allah ya ce, "to shikenan."
Tin daga ranar daman sa ta daina aiki sai hagu.

Akwai Hadisin da Manzon Allah yake cewa.
"Duk abinda muka hane ku, to ku nisan ce shi. Haka duk abinda muka umarce ku ta ku aika tashi dai dai gwargwadan iyawar ku."

Wannan na nuni da in ance manson Allah (SAW) Ko Allah ya fada a cikin kurani, ya ce kada kuyi abu kaza to ku guje shi. Kamar da Manzon Allah ya ce,
"kada kuyi Sallah a makabar ta, kada ku zauna akan kabari." To kada kuyin. In anyi ba kyau tinda har yayi hani dashi
Haka kuma kamar da Manzon Allah ya ce,
"kuyi sahur domin a cikin sa akwai albarka." Wannan in kayi ka samu lada in baka yi ba babu lefi a ciki."

" Allah bamu ikon bin dai dai. Ameen. Gaskiya Adda kina burgeni komai. kina yin sa cikin sani da addini."

Murmushi *Najwa* tayi. Ta ce,
"Haka nake son kema ki kasance."

"Nima ina son hakan."

"To Karanta, kulhuwallahu Ahad, kul'azubi bi rabbil Falak, da Bira bil Nas. Sai ki karanta ayyatul kursiyu."

"Toh su mene ne amfanin karanta su."

"Dan samun tsari daga shaidanu, kuma duk wanda ya karanta ayyatul kursiyu, daga farko har karshe sannan ya kwanta, to yana da mai tsaro a gareshi daga Allah, kuma shaidan bazai kusance shi ba har ya wayi gari."

Kai Basma ta jinjina sannan ta karanta a fili ta tofa a tafin hannun ta, ta shafe jikin ta dashi.

"Toh subhanallah 33
Walhamdulillah 33
Wallahu Akbar 33,"

Suma duk tayi su a fili. Ta ce,
"Bismikallahuma amuti wa ahaya."

Fada tayi ita bayan ta fada.
"To ki rufe idon ki, kiyi bacci."

"To Adda sai da safe."
"Allah tashe mu lafiya."

"Ameen."

Ban daki ta shiga. Wanka tayi sannan ta dauro alwala. 

Tana fitowa ta shafe jikin ta sannan ta saka kayan baccin ta irin na kanwar ta.

Addu'a tayi sannan ta shafe jikin ta. Ta kwanta.

Karfe hudu na asuba ta mike. Alwala tayo ta tada sallah tana idar wa ta dauko alkur'ani ta fara karantawa.

Karfe biyar da minti ashirin ta tashi Basma dan suyi sallah.

Raka'atanil firjir suka gaba tare, sannan sukayi sallah asuba. Sai da suka idar sannan Basma ta dubi *Najwa* ta ce,

"Adda ina kwana?"

*Najwa* ta amsa
"Lafiya lou! Kin tashi lafiya."

"Lafiya lou Adda!"
"To dauko kur'anin ki."

"Yauwah Adda wai me da me ake karantawa a cikin wadan nan raka'a biyun."
"Wanne fa?"

Basama ta ce,
"Raka'atanil Fijir mana."

"Oh Basma yanzu har kin manta."
"Eh wallahi Adda."

"Toh raka'ar farko, zaki karamta fatiha da suratul Kafirun (kulliya ayuhal kafirun), ta biyu kuma. Fatiha da suratul ikilas (kul huwallahu Ahad)."

"Yauwah na tuna."
"To Bismillah! Mu fara karatun."

Nan take suka fara karatu tun daga Fatiha har Suratul A'la (Sabi).

Sannan sukayi addu'a. Kasa *Najwa* ta sauka ita kuma Basma tayi dakin Dady.

Falon nasu a share a goge sai tashin kamshi yake yi.

Kitchen ta nufa, fulawa ta debo ta dama tayi funkaso, sai miyar kaji da tayi.

Ruwan Tea ta tafasa sannan tayi farfesun kayan ciki.

Sai da ta gama komai sannan ta ta wanke kwanukan, ta gyare kitchen din.

Falo ta jere komai sannan ta haye sama, Basma tayiwa wanka sannan ta shirya ta cikin kayan makarantar ta.

Siket ne, dogo baki da farar riga me dogon hannu, da dan karamin hijab, sai bakin takalmi da farar safa.

Ta feshe ta da turaruka sannan itama tayo wanka. Ta shirya cikin wata super holland blue (ruwan omo) da baka.

Riga da siket ne, sosai tayi kyau. Fatar ta, ta kara gaske da sheki.

Batai kwalliya ba, amman fuskar ta tayi kyau.

Kasa suka sauka! Mami da Dady na zaune, Ya Salim na gaban firij yana shan ruwa.

"Dady ina kwana?"
*Najwa* ta zube a kasa tana gaishe da mahaifin nata.

"Lafiya lou Uwata *Najwa* kun tashi lafiya?"
"Lafiya lau Alhamdulillah!"

Ta juya gun Mami, itama ta gaishe ta, sannan ta gaida Yayan ta Hamma Salim.

Sai da suka gama gaisawa sannan suka nufi wajen cin abinci.

Sai da suka gama sannan Hamma Salim ya dauki Basma ya kai ta makaranta.

Dady kuma ya tafi wajen aikin sa. Gidan ya rage daga Mami sai *Najwa* da tayi sama tana duba littafan makarantar ta.


*INDABAWA*

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Page*76-80*

Dedicated to *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*



Sai karfe sha biyun rana, sannan *Najwa*  ta sauko,  kitchen ta shiga kai tsaye, ta daura abincin rana.

Shinkafa ta dafa wacce taji kayan lambu, sai miya da tayi ta saka mata naman kasuwa. Sai peppe chicken da tayi musu.

Sai hadin salad, da lemon ginger wanda ta saka masa zallar ginger da lemon tsami sai suga. ta saka a firij.

Duk yadda Mami taso ta tayata amman sam *Najwa* taki yadda.

Dan haka sai kallo take binta dashi tana aikin ta

Tana son yar ta. Dan tana da ladabi biyayya ga ilimi, ga amdani dashi dan komai nata cikin nutsuwa da ilini take yin sa

Tana gamawa ta wanke wanje sanna ta jere kanukan a wajen da suke cin abinci.

Karfe daya da rabi ta shige ban daki dan yin wanka. Tana fitowa har Basma ta dawo.

"Adda ina yini ya gida?"
Murmushi *Najwa* tayi, sannan ta amsa mata da.

"Lafiya lou Basma. Ya makaranta?"
"Adda makaranta tayi ddi yau an mana test naci maki me yawa."
Murmushi *Najwa* ta karayi

"Masha Allah haka nake son kanwata"
Basma tayi murmushi.

"Nima so nake na zama kamar Adda ta, saboda na zama me ilimi da amfani dashi."

Murmushi *Najwa* tayi ta kamata, ta cire mata kayan makaranta, sannan suka shige ban daki tayi mata wanka.

Suna fitowa, *Najwa* ta shirya kanwar tata, cikin kayan makarantar ta.

Wanda suke a wanke a goge,  ta feshe ta da turaren ta.

"Basma maza je kici abinci kafin na sauko."
"Toh Adda!"

Tana fita itama ta shirta cikin kayan makarantar ta, ruwan omon riga da wando da ruwan daurawar hijabi wanda ya wuce gwiwar ta.

Bata fesa turare ba, sai humra da Ambar da ta cakude jikin ta dasu

Nan take ta fara fitar da kamshi me dadi, fuskar ta duk da batai kwalliya amman tayi kyau.

Jakar ta, ta dauka da ta Basma, sannan ta bude loka ta dauki Nikaf.

Kasa ta sauka lokacin har Basma ta gama cin abinci.

"Mami zamu tafi."
"Bafa kici abinci ba."

"Mami na koshi sai mun dawo."
"Toh shikenan."

Mami ta fada tana bin bayan su,


Najib da Mami ne, acikin mota suna tafe suna hira bin sha'awa.  Har suka shigo cikin titin sabuwar kofa.

Wani sanyi yaji ya ratsa shi, ganin sun shigo unguwar da ya hadu da yarinyar da ta burge shi.

Katon gida suka nufa, horn yayi me gadi ya bude masa, bayan sun gaisa.

Fitowa Yayi, ya budewa Mami, sannan yace,

"Mami shiga gani nan."
"Ina zakaje?"

Kai ya sosa, yana murmushi. Itama Murmushi Mami tayi,

"Son yarinyar zaka nema ne."
"Eh! Mami dan naga yan makarantar na wucewa."

"Kar dai, ka tsayar da ita a hanya."
"Mami na bazan yi haka ba."

"Jeka sai ka dawo."
"To Mami."

Ya shige motar tasa, ya fita ya koma ta inda ya ganta ranan.


Suna tafe Mami da su *Najwa* , *Najwa* na saka nikaf a fuskar ta.

"Yau kuma *Najwa* "
Mami ta fada tana kallon ta.

*Najwa* ta ce,
"Wallahi Mami, ido yana min yawa a wajene shiyasa."

Murmushi, Mami tayi, suna shan kwana suka hadu da Mamin Najib. Na karasowa.

Murmushi ne ya sauka a fuskonkin su. Basma kuma tayi wajen Mamin Najib da gudu tana

"Oyoyo Mami nah."

Mamin Najib ta ce,
"Oyoyo Basma, za'a tafi makaranta ne."

"Eh! Ina Ya Najib?"
"Ya Najib ya fita yanzu zai dawo."

Mami ta karaso gun su *Najwa* rike da hannun Basma.

Har kasa *Najwa* ta durkusa tana gaishe da Mami ta amsa, cikin sakin fuska.

Mamin Najib ta ce,
" *Najwa* yan mata, za'a tafi makarnta ne?"

*Najwa* kanta a kasa ta ce,
"Eh Mami, yasu Hamma Najib, da su Dady."

"Suna lafiya. Tare muke da Hamman naku ai."

"Mami mu shiga daga ciki ko?"
"Toh! Najwa, ku tafi Allah kiyaye hanya."

SuKa hada baki suka ce,
"Ameen! Mami. Sai mun dawo."

Mamin Najin ta ce,
"A dawo lafiya."

Suka fice, duk da ta titi yafi saurin zuwa makarantar amman *Najwa* ta jasu suka bi ta bayan layi.

Ya jima zaune a cikin motar sa, yana jiran ganin wucewar su, sai da yaga baya ganin kowa sannan ya juya jan motar ya koma gidan su *Najwa* jikin sa duk a sanyaye.

Lokacin su Mami na daki ana ta hirar yaushe gamo.

Su Dady ba shiga, shima Najib ya shiga da motar sa.

Kallon suka bisa dashi, dan basu gane wanda ya shigi ba. Sai da ya fito sannan suka gane shi.

Salim ne yayi wajen sa, yana zuwa ya rumgume shi. yana cewa,
"Hamma Najib ka yadani."

Najib ya bubugi bayan sa, ya ce,
"Tayaya zan yada dan uwana."
Ya fada yana rumgume shi.

Sakinsa yayi, yayi wajen Dady, ya duka har kasa, yana gaishe da Dady, da sauri Dady ya dago shi yana mika masa hannu. Ya ce,

" 'Dana, ya kuke?"

Najib ya amsa, da
"Lafiya lou Dady!"

"Ya Mamin taka?"
"Mami tare muke tana ciki. Dady kun dawo lafiya?"

"Lafiya lou  mushiga daga ciki."

Suka yi cikin gidan hannun Najib rike da Hannun Salim.

Suna shiga Mamin *Najwa* ta mike ta kamo hannun sa. Ta ce,
" 'Dana, yau kaine a gidan namu."

Murmushi yayi ya dukar da kasan kasa. Ya ce,
"Mami ina yini?"

Mami ta amsa,
"Lafiya lou 'dana. Ya kuke ya aiki?"

"Mami komai lafiya."
"Masha Allah,"

"yasu *Najwa* da Basma."
"Sun tafi makaranta."

"Wai na jima ban gan Autar daru ba."
"Ai auta yanzu anzama yan mata."

" *Najwa* fa?"

"Baka manta da yar gidan naka ba."
Salim ya fada cikin zolaya.

Najib ya ce,
"Ina Salim!

Please Login or Register in order to submit comment