Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke, *Princess Amrah* Ina yinki. Allah kara basira da zakin hannu. Allah saka miki da alheri.
*Ameen*




Summy kuwa bata tashi dawowa ba sai karfe dayan dare, lokacin Najib har yayi bacci.

Ganin fitilar barandar sa a kunne wannan ya tsorata ta. Amman ta dake tayi cikin dakin ta.

Kwanciyya tayi tana sake sake a ranta taje ko kar taje  daga baya zuciyar ta, ta yanke mata hukunci akan tayi kwanciyyar ta. Ai kuwa haka akayi.

Washe gari da safe ta tashi da wuri ta shiga kitchen ta saka masu aiki su shirya mata break dan akwai abinda boka ya bata ta saka masa a abinci.

Dankali tasa aka soya masa sai ruwan tea da farfesun kayan ciki.

Bangaren sa ta kai masa wanda shi ko tashi beyi bama.

Dakin ta, ta koma ta zauna tana jiran fitowar sa.

Sai karfe sha biyu ya tashi yana tashi yayi wanka ya shirya cikin wani farin yadi.

Wayar sa ya dauka ba abinda ya gani sai sakon Najwa.

Murmushi yayi ya kira ta.
"Barka da safiya ranka ya dade."

"Barka kadai  baby na. Kin tashi lpy."
"Lafiya lou Alhamdulilah. Ya ka tashi?"

"Na tashi lafiya Amarya ta. Yasu Mami."
"Lafiya suke."

"Masha Allah daman zan fita nace zan kira, zanje wajen Mami, daga nan zan leka asibiti."

"To Yallabai! Allah ya dawo dakai lafiya Allah tsare min kai. Ka kular mana da kan ka."
"Kedawa?"

"Antyna man."
"To sai anjima."

Sukai sallama shi sai a lokacin ma ya tina da Sumaiyya.

Fita yayi, har zai fice daga gidan ya dawo dan duba ta.

Tana zaune a falo ba laifi tayi kyau da ita.

Tana ganin shi ta mike, kallon ta yayi ya dan yi murmushi.

Zama yayi, ya ce,
"Ina kika je jiya."

Kame kame ta fara yi. Kallon ta yayi yaga ba alamun gaskiya a tare da ita.

"Kiji tsoron Allah dai ki sani duk abinda kike Allah na ganin ki. Kuma Allah zai tambaye ki. hakanan duk abinda kike kina tsoron Allah kuma ki sani in ni da wanda kika je gareshi baya ganin ki Allah na ganin Kuma zai nuna aranar Alkiyama ranar da babu yafiya komai yazo karshe. Kiji tsoron Allah ki sani raba 'da da mahaifi ba abune me wahala ba. Amman in har Allah ya baki nasara to ki sani Allah ya jarabbce ki da babban laifi kina addu'a Allah ya yafe miki. Ni dai mijin kine kuma bazan so wani abu maea kyau ya same ki ba. Ki sani abinda kikai min na yafe miki."

Mikewa yayi ya nufi hanyar fita. Baki ta tabe ta bi bayan sa.

"Kayi hakuri."
ta fada dai dai lokacin da zai shiga mota.

"Naji."
"Kaci abinci to?"

"No i am fasting."
"Sai ka dawo "

Ta fada tana shigewa ciki.

Kallon ta ya tsaya yi, ya girgiza kai, ya tada motar ya fice.

Gidan Su Ya nufa kai tsaye bangaren Dady ya nufa suka gaisa, Dady na zolayar sa  Ango Ango.

Shidai sai washe baki yake. Dady ya ce,
"Maman ka ta ce min wai da sumaiyya zaku tafi ko?"

"Eh!"
Ya bashi amsa.

"To Allah yasa albarka."
"Ameen Dady."

Momy ce ta shigo ta ce,
"A'ah Najib ne ya shigo."

"Eh Mami. Ina kwana?"
"Lafiya lou son ya sumaiyyan?"

"Tana lafiya tana gaishe ki"
"To muna amsawa."

Fita yayi, ya nufi bangaren Baba. Acan ya tadda su Talle zama sukai suna tsare tsaren yadda zasu bikin.

Ranar litinin za'a kawo Najwa, dan haka da yamma za ai dinner daga nan za a kai ta gidan ta.

"To amman kusan me?"
suka amsa da
"A'ah!"

"A daren ranar zamu tafi nida Sumaiyya."
"Ayyah Yaya ko kwana baza kai ba."

"Ba hali dan a friday suke son sauka ta gashi har na dada kwana biyu, kinga dole na tafi a ranar."

"Allah sarki, Allah ya kaimu toh."
"Ameen!"

Ya jima a gidan dan su yasa suyi masa kayan sha ruwa.

Inda in dare yayi, zai zo ya sha ruwa. Karfe shiga ya shigo gidan ana shan ruwa ya sha ruwa sannan ya tafi massalaci.

Sai bayan isha'i ya dawo ya ci abinda suka shirya masa.

Yam ball sukai masa, da kunun gyada sai kunu aya da sukai masa.

Da zai tafi suka bashi masa da lafiyayar miya da taji nama sosai

Sai karfe tara ya koma gida. Sumaiyya na zaune a falo tana jiran dawowar sa dan ta sa an shirya masa abinci me magun guna nan.

Sai dai tin magariba take zuba ido bashi ba alamun sa. Ko da ya dawo, kuma ya ce ya koshi.

Haushi kamar me dan sauran na kwana biyu in be ci ba ya kare. Washe gari ma tin safe da ya fita sai dare bayan ya je gida yaci abincin sa ya koshi. Tinda yasan Ba yi ma abincin take ba.

Shima da ya dawo haka ta kara tarar da abinci. Amman beci ba. Ranar karshe da kanta ta shirya masa da sassafe ta kai masa daki.

Dataga zai fita bashi ta saka masa a mota.

Ranar murna Najib zai ci abinci me magani dan boka yace inda yaci bazai kara tunanin wata Najwa ba.

To yana shiga office, ya tada mami tayi masa ta aiko masa da ita wannan yasa ya bada abincin dan sai da zai tafi ma aka bashi fulas din.

Kullun suna makale da Najwa a waya kusan yini suke tare dan duk inda zasu je kai invitation card tare suke yini waya ta ce sunje can ta ce suna can. Da Khaleel shi ya dinga zurga zurga da ita.


Tin daga ranar da Sumaiyya taga Najib yaci abinci, ya bata kara yunkurin masa girki ba.

Ranan tana zaune ya sa a dauke ta akai ta ai mata visa, murna gun Sumaiyya kamar me.

Kuma ita bata ga yana wani shirin biki ba. Wannan yasa ta kwantar da hankalin ta.

Su Mamin Najib kuwa ana can ana ta shirye shiryen biki haka su Talle tin ana sauran kwana biyu suka daga suka tafi kano.


    ***********
Alhamdulilah komai yana tafiya dai dai a bangaren su Najwa inda yau ranar labara har an mata gyaran jiki lalle da kunshi.

Tafito amaryar dai sosai, fadar irin kyau da cikar da ta kara ma vata lokaci ne.

Kyau iyakar kyau Najwa tayi shi, tana daki, ita da su Zahra da Khadija matar Khaleel. Sai talle da bara'atu da wasu daga cikin class mate din dinsu da suka zo.

Duk sun yi ankon wani material fari ne adon  ja. Ba karamin kyau sukai ba.

Gidan ya cika da jama'a dan Najwa tace kamun gida take so.

Tana daki me kwalliya na mata, wani dark pink colour material ta saka me stone ajiki, akai mata nadin head da wani dark pink colour abu.

Silver jaka da takalmu ta saka, gaskiya Najwa ba kowa ne ya gane ta ba.

Kowa ka gani fuskar sa kunshe da murmushi da farin ciki.

Karfe Biyar aka kama amarya a dakin Mamin ta. Inda daga nan aka fito da Amaraya harabar gidan ana kida da rawa.

An mata liki sosai taga yan uwa dan duk anzo.

Ganin jama'a kamar kasa yasa Najwa fashe wa da kuka.

Yan uwa kuwa kowa da gudun mawar sa. Mami ta samu kudi Najwa ma an bata gift daga kawayen ta.

Su Basma kuwa ana tsakiyar fili ana ta rawa.

Hamma Salim kuwa sai liki ake ana bikin Kanwa.

Kowa yaci ya sha ya koshi anyi taron ranar lafiya an tashi lafiya cikin farin ciki da annushuwa.

Anyi hotuna da vedios
Washe gari akai budar kai.


*INDABAWA*

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page *148*


Ranar Alhamis akai budar kai kamar yadda aka tsara.

A ranar da dare Najib ya iso Kano, yaso yaga Najwa amman sam bai samu dama ba.

Ranar Juma'a akai dinner, ranar Najwa tayi kwalliya cikin dark blue din material wanda jikin sa duk stones ne, fadar irin kyau da tayi bata baki ne. Amman tayi kyaun da duk wanda ya ganta sai ya kalleta ta ya kuma.

To a bace daman can da kyan ta bare yanzu da aka kara mata kayan ado, kwalliyar ba wata me cika fuska bace, simple ce amman tai kyau abinta.

Wani green kalar material aka anko wanda suma duk sukai kyau.

Ango kuwa yaci farar shadda wacce akai masa aiki da dark blue din zare. Yar ciki da babbar riga.

Gaskiya duk wanda ya kalli Najwa da Najib yasan sun dace da juna kowa sai addu'ar zaman lafiya yake musu, sai hotuna da vedio ake musu.

Duk ibda suka juyo cemera ne ke haska su. Masha Allah yan uwa da abokan arziki duk sun hallici wajen.

Anyi barin kudi kamar ba'asan zafin su ba. Haka nan an kashe kudi wajen kayan abincin da aka tanadarwa jama'a.

Komai dai anyi shi cikin wadata da girama. Najib kuwa idon sa kafe akan fuskar Najwa duk dagowar da zatai sai sun hada ido. Da ta gaji ta kalle shi ta gefen ido ta ce,
"Please love ka rage wannan kallon mana baka ga mutane ba."

Numfashi yaja yayi ajiyar zuciya ya ce, "mutane kuma. Allah Baby ba wanda nake gani anan wajen sai ke kadai. Ji nake kamar na hadiye ki. Naso an daura auren tin yau da duk abinda nai miki nasan babu laifi aciki."

Ganin zai bullo da wata maganar yasa ta bar maganar. "Baby!"
Ya kira sunan ta, cikin wata irin murya.

"Na'am! Honey."
"Ajiyar zuciya ya sauke ya ce in mun koma gida ina son magana da ke."

"Allah kaimu gidan lafiya."
"Ameenn!"

Anyi dinner lafiya an tashi lafiya inda aka tashi taro kowa na farin ciki da fatan alheri.

A ranar ma dai basu samu damar haduwa ba.

Washe gari yini akai, inda amarya ta shirya cikin wani red material me adon blue/green colour sai duwatsu da ke jiki.

An mata nadi akan ta me kyau. Ta yafa wani blue/green din net haka jakar da takalmi duk kalar sa ne.

Ango Najib kuma ya shirya ya shirya cikin wata blue din shadda me kyau sai kyali da Haske take.

Zan iya cewa wajen bikin kamar wajen taron family ya zama dan wajen ya tara yan uwan su na nesa da na kusa gaba dayan su.

Haka suka dinga bin yan uwa suna gaida su tin daga Baba Amina kakar Najwa, da su Ummah, da Mamah duk sai da suka bisu suna gaisar da kakanin su hadi da iyayen su. Sannan suka koma wajen zaman su.

Yau ma harkar girma kawai aka zuba. Gaskiya bikin ya kayatar dan in nace zan tsaya fadar irin yadda abin ya gudana zan jima ban gama bada bayanan ba. Amman bikin yayi iya yi.

Sai da fatan alheri kawai.


Washe gari daurin aure, tin sassafe me kwalliya tazo ta tsarawa amarya kwalliya ta gani ta fada. Amarya ta shirya cikin wata briwn shadda me adon yellow ajiki  sai milk mayafi da takalmi da ta saka.

Duk wanda ya kalli Najwa sai ya yaba da kyan ta tare  da mata addua.

Ango Najib kuma ya shirya cikin wata milk din shadda wacce ta shadda an mata aikin brown zare. Masha Allah Najib ba dai kyau ba. Bare kuma ranar tashi ce, Najib sai washe hakora yake ya kasa rufe bakin sa.

Karfe 10:30 aka daura Auren *Muhammad Najib Abubakar da Amaryar sa Amina Ahmad.*

Inda daurin auren ya samu halartar manya manyab jama'a banda kusoshin gwammnati har da sarakuna.

Daga nan suka tafi walima inda nan aka ci aka koshi aka sha abarkwanci daga nan gidan su Najwa Angwayen su ka wuce.

Najwa na ganin karfe goma da rabi tayi hankalin ta ya tashi duk ta rasa nutsuwar ta jin take kamar ba ita ba. Dan komai da ake sama sama ake yin sa.

Ana daura aure Mustapha mijin Zahra ya bugu yana fada mata. Buda Zahra tayi, su Talle suka kalle ta suka ce,
"Anty an daura ne."

"Eh an daura su Najwa an zama matan aure."
wajen Najwa ta karasa ta ce,
"Amaryar mu  an daura aure Allah bada zaman lafita. Allah kade fitina."

"Ameen yan dakin suka amsa dashi."
Sai wajen karfe daya su Najib suka karaso gidan su Najwa lokacin Najwa na daki tayi shiru ta rasa me zatayi ma.

Maman Sumaiyya ita tazo ta kira Najwa kan angwaye na sitting room suna jiran ta.

Zahra dasu Talle da Khadija da wasu daga cikin kawayen ta su suka rakata dakin dasu Najib suke.

Najib na ganin shigowar ta ya mike yayo wajen ta. Hannun ta ya kamo suka shiga daga ciki. Hotuna aka dinga dauka sai da suka gama da abokan su sannan suka shiga cikin gida dan yi da yan uwa.

Anan  sukai da kakkanin su da iyayen su. Da kannen mahaifan su da matan yayen su Dady. Sun sha hotu inda Najib duk hankalin sa na kan Najwa da yaga ta canja.

Ita kuwa Najwa sai inda akayi da ita dan duk jikin ta ya saki.

Suna gama hoto yaja hannun ta suka fita harabar gidan. Kallonbta ya tsaya yi, Ya ce,
"Baba lafiya?"

Bata kai ga bashi amsa ba abokan wasan su suka shigo gidan nan fa suka fara jan ango da amarya sukai hoto suna ta hira a hankali Najwa ta zame daga wajen.

Dakin Mami ta shiga dan nan ne ba kowa a ciki kwanciyya tayi akan gado tana me lumshe ido, wani sanyi taji yana shiga cikin zuciyar ta. Kanta kuma kamar wacce aka sauke mata wani nauyi.

Ta jima a kwance anan sannan ta mike ta koma cikin jama'ar ta. Karfe biyu ta ta shiga ta canja shiga zuwa atamfa super pink colour ce an mata adon blue. Tayi kyau ita ma.

Ranar ma dai kamar wani yini aka karayi inda masu kidan kwarya suka zo suka buga aka sha rawa.

Kowa ya watse akan gobe za'a dau amarya akai ta gidan ta.

Washe gari tin safe aka shirya amarya cikin wata Atampa holland riga da zani sannan aka rufa mata wata bakar Alkebba baka me adon golding coolour dakin Dady aka ka ta, tana kuka.

A gefen kafar sa ta zaune, kallon ta Dady yayi shima ya goge yar kwallar da ta zubo masa, ya ce,
"Allah miki Albarka. Allah miki Albarka. Allah miki Albarka."

sai da ya fada sau uku sannan ya ce,
"Ban da abinda zan ce miki Najwa dan nasan duk na gama fada miki a baya. Sai dai Najwa ina me kara fada miki kiji tsoron Allah ki rike mijinki da amana sannan ki masa biyayya. Ka san hanyar da zakiyi ki samo aljannar ki a karkashin kafar mijin ki. Ba abinda zan ce Najwa sai da Allah miki Albrka Allah ya baki yayan da su miki biyayya kamar yadda kikai mana. Allah kuma ya saka miki da gidan Aljanna baki taba min komai ba Najwa Allah miki Albarka."

Yayi shiru Mami ma kasa magana tayi sai dai albarka da take sanya mata kawai.

Mama Bilkisu yayar Dady matar gwamann Kaduna ita ta kamo ta zata mikar da ita. Da sauri Najwa ta fada jikin mahaifin ta. Tana kuka.
"Dady ka yafe min."

"Ba komai Najwa na yafe miki baki taba min komai ba Najwa na yafe miki. Alherin Allah ya tabbata a gareki Najwa. Allah faranta miki. Allah bada zaman lafiya."

Jikin Mami tayi tana kuka tana neman yafiyar ta. Mami dauriya kawai take dan ita ma gab take da yin kukan.
"Baki taba batan ba Najwa kullun burin ki faranta min. Allah kima ya baki masu faranta miki. Allah ya kare ki ya bada zamab lafiya."

Ta daga ta, ta mikawa Mama Bilkisu ita. Karbar ta tayi tana rarrashin ta dai dai zasu fita kenan sai ga Hamam Salim nan tare da Basma.

Da gudu Basma ta karaso gun yayar ta ta tana kuka ita ma. Najwa na ganin su ta rumgume su tana kuka kamar ranta zai fita.

Suma kukan suke, lallashin su, aka dinga yi. Tare suka shiga dakin Mamamah wato Takwarar Najwa mahaifiyar Mahaifin Najwa.

"A'ah ya haka kuma. Haba Najwa ta. Haba Najwa ta ai sai ki dagawa iyayen ki hankali. Gashi kin sa ya  uwan ki kuka ko nima kina son nayi ne."

Kai Najwa ta girgiza. "To In dai bakya son nayi kiyi shiru ki daina kinji."
Kai ta gyada mata.

"Yauwah koke fa kuma kuyi shiru ai Najwa bata bar ku ba. Bakwa ganin wanda ta aure yayan kune wanda rayuwar sa ma yayi a cikin gidan ku duk kun zama daya. Dan Allah ku daina kuka."

Ta karasa maganar tana lallashin Najwa sai da ta dan tsagaita da kuka sannan  ta fara mata nasiha akan aure da zama da kishiya.

Ta ja hankalin ta sosai akan ta rike abokiyar zaman ta lafiya kuma sosai maganar Mamamma ta shige ta.

Mamama da kanta ta saka ta a mota dan kai ta gidan Baffah inda shima nasihar ce da jan hankali akan zaman aure tare da hakuri da juna.

Ummah kuwa cewa tayi ai ta gama da ita tin ba yau ba. Daga nan gidan su Mama aka kai ta daga can suka shige gidan Su Mamin Najib inda iyayen ta suma sukai mata nasiha da jan hankali.

Gaskiya inda Nasiha na fitowa a jiki da tini ta fito a jikin Najwa dan jama"a da yawa sun mata kuma duk ta dauka ba ta wacce ta yada.

Daga nan suka shige filin jirgi, da Mama Bilki da Maman Zahra kanwar Mami da Kawayen Najwa Zahra da Khadija da mutun biyar yan  ckul din su sai Salim da Basma da wasu yan uwan su, su goma haka suka tafi.

Suna zuwa aka turo motocin da zasu dauki Amarya. Gidan Mami aka shige da Najwa inda suna zuwa, Mami da kanta taje ta kamo yar ta.

Daki aka basu a sama ita da kawayen ta. Aka tarbe su da duk abinda suke bukata. sai da akai sallah sannan suka sakko da Najwa dan kaita wajen Mami.

Mami nasihar tai mata inda Baba ma ta mata ta ta.  Sama suka koma inda Mami ta ce bayan magariba zasu je reception dan haka za'a aiko da me shirya ta.

Najib kuwa ana can an shiga busy ga amarya an kawo ta yau gashi yaune tashin su.

Yanzu haka sabon gidan da ya kera shi yaje yana ganin yadda aka shiryawa Sumaiyya bangaren ta. Da mn komai shi ya sake mata.

Katon gida ne gari guda. Me ginin zamani, Bangare biyu ne a cikin gidan daya na facing din daya.





*Indabawa*

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*149*


Katon gida ne gari guda, me ginin zamani. Bangare uku ne, biyu na facing juna.

Da farko da ka shiga gidan katon gate ne, sai harabar ajiye motoci, wanda yake katon gaske.

Daga can gefe wani madaidaicin asibiti ne wanda aka zuba duk abinda ake bukata.

Bangarori Biyun sune na sumaiyya da Najwa, na Najib na tsakiya.

Kowa part din sa yana dauke da katon falo sai daki guda biyu a kasa da daining area. da ban daki da kitchen, sai bene wanda shima falo ne, sai dakunan bacci guda uku a ciki.

Haka part din Najwa shima yake. Sai wata kofa dake gefen ko wanne part wanda zata sada ka da bangaren Najib.

Bangaren sa katon falo ne, sai Dakunan bacci guda uku daya kuma an zuba kayan karatu a ciki.

Dakin sumaiyya ya cika mata kaya a ciki dan duk dakunan ba wanda be zuba mata kaya ba.

Kitchen kan sa ya cika mata da kayan amfani duk da yasan ba aikin take ba.

A bayan gidan kuwa wani katon lambu ne, cike yake da kayan marmari wandanda ba rani ba damina kullim da ya'ya a jikin su, amman a tsakiyar lambun ruwa ne ke gudu. Can gefe swimming pool ne.

Sai wajen zama da akai masa wata yar rumfa, An saka wasu kujeru masu kyau a wajen. Duk gidan an kawata shi da fulawoyi abin sha'awa.

Gidan gaskiya ya gaji da haduwa dan duk abin more rayuwa an saka a ciki.


************
Sumaiyya kuwa tinda Najib ya tafi biki suka daga Niger dan samun yadda zasu da taimako.

Hakuri bokan ta ya bata, sai bayani akan magani da zai bata tayi amfani da dhi. Ya za a dace akan sa.

Zai yi aiki ne akan duk lokacin da Najib zai kusanci Najwa bazai iya ba, zai zamar mata kamar mace. Hakan zai sa ta gaji ta fasa auren.

Sumaiyya ba karamin dadi taji ba dan haka ta tafi da murnar ta dan tasan duk amaryar da ba'a kusan ce ta ba na wasu lokutan dole ta hakura da auren bama in tayi tunanin haka yake dole a fasa auren.

Da karfin gwiwar ta ta tafi tana jin dadin nan da wasu lokuta zata rabu da Najwa. wannan yasa ta sa a ranta zata nuna bata da wata damuwa akan auren bare a gane akwai abinda zata gudanar nan gaba.

Tana komawa gida ta kira Najib a waya abinda yai matukar bashi mamaki kallon screem din wayar yayi har wayar ta katse ta kuma kira. Dagawa yayi cikin sanyin jiki dan besan me zata ce masa ba ko ba lafiya ne.

Dan  yasan Sumaiyya inda ba shi ya kira ba ko za a mutu baza ta kira shi ba.
"Assalamu Alaikum!"

Ya Fada, da "Hello!"
Ta amsa masa sallamar. Wannan ya kara tabbatar masa da Sumaiyya ce dan sam Sumaiyya ba ruwan ta da Sallama.

"Ya aka yi ne Sumaiyya?"
"Lafiya daman na ce yau za'a kawo amarya ba abinda za'ayi ne."

"Toh!"
Ya fada a ransa yana dauke wayar a kunnen sa dan kara tabbatar da menyin magana.

"Sumaiyya!"
Ya kira sunan ta.

"Na'am!"
Kai ya jinjina ya ce,
"Anjima da magariba za ayi party, dan haka zan aiko a dauke ku shikenan."

"To sai anjiman."
Ta kashe waya tana kallon kawar ta da ta shirya mata duk plan din ta.

Kawar  ta ce,
"ko kefa!"
Summy ta ce.
"Ke dai bari."

Sukai shiru saboda shigowar wasu kawayen Sumaiyya. Kallon
"Yau fa zamu daga. Amman naga ko maganar bai yi min ba...."

Wayar ta ce, ta katse mata tunanin tana kai duban ta taga Najib ne.

Dagawa tayi, ta ce,
"Ya ne?"

"Maganar tafiya nan zan miki, karfe sha biyu zamu daga dan haka ki zama cikin shiri."

"To shikenan sai anjima."
Ya kashe wayar.

Ihu ta dauka ta ce,
"Tafiyar fa na nan. Amarya zata zauna gadin gida kenan."

*******
Tin karfe biyar ake wa Najwa kwalliya inda har Magariba ba a gama ba.  iya gajiya Najwa ta gama gajiya daman jikin ta ba gwari ga rashin cin abinci da ta kasa ci.

Ana gamawa ta saka wata doguwar rigar material baki, me ado golding stones, golden jaka da takalmi ta dauka.

Haka nan dankunnen ta da sarka duk golding ne. Ina ka ga farar mace cikin bakin abu.

Kowa ya shirya dan har an debe jama'ar dake cikin gidan.

Najwa aka bari kawai ita da Mami dan Najib be karaso ba.

Najwa na daki, Mami ta aiko Talle ta fito da ita dan Najib na falo yana jiran ta.

Talle na shiga taga Najwa ta saki baki tana kallon ta.

"Anty ke ce kuwa? Wannan in Ya Najib ya ganshi ai sai ya zauce."

Murmushi Najwa tayi ta ce,
"Ke kin fiys tsokana."

"Uhnn tashi muje yana kasa yana jiran ki."

Ji tayi gaban ta ya fadi. mikewa tayi a hankali ta bi bayan Talle, tafiya take kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki.

Wanda tafiyar kan ta ba karamin daukar hankali take ba. Najib tin tana stair ya zuba mata ido, yana sanye da wata golding colour shadda wacce sai kalli take, kansa sanye da hula kalar kayan sa. Gashin kan sa ya kwanta ta gefe.

Fuskar sa sai fitar da sheki take,  har ta karaso be san ta karaso ba saboda kallon da yake mata. ba karamin hankalin sa ta dauke ba.

Sai da Talle ta zungure shi sannan ya motsa. Kallon ta yayi ya ce,
"Malama tafi ki bawa mutane waje."

Dariya ta yi ta ce,
"Eh ai na gama maka tinda na dauko maka ita. Bari nai muku hoto ko?"

Ta dadauke su, tana dariya.
"Gaskiya Ya Najib kun dace da juna."

"Kije ana jiran ki."
Ido ta bude tayi waje. Da saurin ya matsowa wajen ta. Baya tayi, tana kallon sa.

Binta yake yi tana kara matsawa har ya kaita jikin bango, hade ta yayi da kirjin ta yana shakar kamshin turaren ta.

"Hamma!"
Ta kira sunan sa, cikin shagwaba.

Hannun sa ya saka ya zagayo dashi ta kugun ta.

Wani irin abu taji na yawo a jikin. Kamar yadda shima ya ji.

"Baby u look soo beautiful than every day."
"Naji pkease sake ni kar Mami tazo kaga yanzu zata sauko."

"Wacce Mami da ta riga da ta tafi."
Ido ta zaro kirjin ta na tsanan ta bugo.

Hannun sa ya saka yana shafa fuskar ta zuwa saman kirjin ta. Idon ta, ta matse tsam, kirjin ta ne ya tsanan ta bugu.

Bakin sa ya matsar dai dai nata, dai dai lokacin da wayar sa ta hau bugawa.

Dauka yayi yace,
"Mallam gani nan."

Ya kashe wayar. Yana rumgume ta a jikin sa.
Tashin bugun kirjin ta yaji ya dago ta da  sauki yana kallon ta.

"Lafiya kuwa?"
Ya tambaye ta yana daura hannun sa akan kirjin

Please Login or Register in order to submit comment