Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zuba albasa da kayan kamshi.

Sai da suka dahu sannan ta soye su. Kayan miya ta diba ta markada ta tafashe su ta soya.

Ruwan tafasa kajin da dashi ta tsaida ruwan miya.

Kayan kamshi da curry da magi ta zuzzuba, sai da miyar ta hadu sannan ta zuba naman da ta soya ta bar su suka karasa dahuwa tare.

Tafiya ta dafa musu da miyar kwai, nan da nan ta gama ta kai musu sama.

Karfe taran dare ta ce lafiya Honey be dawo ba.

Waya ta dauka ta kira shi, be dauka ba, sai daga baya ya kira ta.

"Am sorry Baby na, naje turawa Anty ki kudi ne, tana son ta dawo gobe kiyi hakuri gani nan."

"To Allah dawo da kai lafiya."

A ranta kuwa yana ambatar Sumaiyya taji faduwar gaba.

Addu'a tayi, ta shiga bandaki. Wanka tayi, tai brush sannan ta fito duk jikin ta a sanyaye,

Shiryawa tayi cikin wata, farar doguwar riga wacce da kadan ta wuce gwiwar ta, an mata ado da pusher pink din zare, kanta tai parking nashi, ta feshe jikin ta da turare sannan ta murje jikin ta da burhan.

Tini ta hau fitar da wani fitinan nen kamshi.

Falo ta dawo ta zauna tana kallo, daga karshe ta zame ta kwanta.

Ido ta lumshe ta rasa me yake damun ta.

Tana kwancen nan bata ji shigowar Najib ba.

Kiss kawai taji an manna mata a saman kirjin ta.

Ido ta bude da sauri, kallon sa tayi tai murmushi ta mike zaune.

Fuska ta marairace ta ce,
"Hamma kana jin yunwa ko?"

Kai ya girgiza mata, ya ce,
"A'ah ai bakya bari na da yunwa."

Mikewa tayi ta dauko katon farantin da ta jero musu kayan abincin nasu.

Zaunar da shi tayi, kallo ya bita dashi, cikin nutsuwa ta zuba masa, tayo gun sa ta fara bashi a baki.

Kallon ta yake yana bude baki tana bashi  har ya koshi ta bashi lemo ya sha.

Kallon sa tayi cikin kauna ta ce,
"Sannu Honey."

"Yauwah Baby na."
"Akwai abinda kake bukata."

"A'ah! Nagode Najwa Allah miki albarka."
"Ameen!"

Ta amsa da, janyo ta yayi, ya taba cikin ta, ya ce,
"Baby na baki ci abinci ba."

Fuska ta marairaice, ta ce,
"Honey bana son cin abincin."

"Saboda me? Me kike so na samo miki."
Kanta ta kwantar a kirjin sa ta ce,

"Shawarma nake so, amman kaga dare yayi."
Ajiye ta yayi akan kujera yace,

"Baby ko karfe nawan dare ne in kina bukatar abu dole na samar miki. Kamar yadda bakya bari na da bukatar komai."

"In zo muje?"
"A'ah kar a gane min ke."

"Please love."
"Toh! Ina zuwa."

Yayi cikin daki. Bakar doguwar riga ya dauko mata. Shi da kansa ya saka mata, sannan ya dago ta suka fita.

Hannun sa sakale da nata, a haka yake driving din, zata iya cewa yau ita ce ranar da ta taba fita tin da ta shigo gidan wata daya kenan.

A mota ya barta yaje ya siyo mata sannan suka ya dawo, garin ya zagaya da ita, sai sha dayan dare suka koma gida.

Shi da kansa ya bata a baki, har ta koshi. Tana gamawa suka kwanta.

Washe gari tin asuba bata koma ba, duk abinda ya kamata tayi ta fara yi, tai share sharen ta da goge gogen ta ta turare gidan ya dau kamshi.

Sai da ta tabbatar ta gama duk abinda zatayi sannan ta shiga kitchen.

Break fast ta hada musu, ta shige daki tai wanka, Najib na zaune yana aiki a system din shi ta fito daga wanka.

Sai da tayi kwalliyar ta sannan ta yo wajen sa, yana ganin ta ya ajiye system din ya janyo ta jikinsa.

"Baby na kin iya kwalliya, kinyi kyau."
Murmushi tayi, ta ce,
"Nagode My love. Amman ya kamata ka tashi kai wanka ko? Kaga zamu gidan Mami."

Kallon ta yayi ya ce,
"Toh! Karfe nawa ne?"

Baki ta dan turo ta kalli agogon dakin ta ce,
"Kalli fa har goma da rabi, kaga kafin kai wanka muyi break wajen sha daya fa."

"Bari na karasa aikin."
"A'ah jeka zan karasa maka."
Kai ya make ya ce,
"A'ah ni na gaji ma, hannu na bazai iya cudani ba."

Kallon sa tayi, ta motse baki ta ce,
"Honey wayo ko? To muje nai maka."

"Yauwah Baby nah."
Ta kamo hannun sa sukai ban daki.

Da kanta tai masa wanka wanda daga nan tare suka yi wankan bayan sun gama wasa da ruwan su da soyayyar su. ita ta gyara masa fuska dan har aski tai masa.

Suka fito tana rumgume dashi, da kanta ta tsane masa jiki, sai da suka dau awa daya a wanka ya shirya shi.

Wajen break ma haka ya dinga mata shagwaba sai lallaba shi take yi da kyar suka gama ta shiga ta shirya cikin wata Ash kalar atamfa, me adon ja.

An mata dinkin riga da siket dinkin yai mata kyau, turare ta burshine jikin ta dashi.

Ita ta taya Najib shiryawa cikin ash kalar shadda sai maiko take.

Cikin akwatin ta, ta bude ta dauko, atamfa turmin biyar sai shadda kala biyu, kayan kwalliya ta diba duk ta zuva a wata katuwar jaka.

Da kyar Najwa ta  iya fito da jakar daga daki, Najib na ganin ta ya karaso wajen ta.

Kallon ta ya tsaya yi bayan a amshi jakar hannun ta.




*INDABAWA*

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*158*



*Makawa* marubuciyar *Furen Juji* jinjina gare ki, da fatan Alheri gareki Allah kara basira. Allah shige miki gaba.

*Ameen!"


Kallon ta yayi, ya ce,
"Wannan kayan fa?"

Murmushi tayi, ta ce,
"Nasu Mami ne."

Bai gane me take nufi ba, dan haka ya saka a mota kawai.

Ya bude mata gidan gaba sai da ta shiga sannan ya rufe ya koma dayan bangaren.

Suna tafiya suna hira, Najwa tace,
"Honey ina jin kunyar Mami wallahi, Allah yasa kar ta gane wani abu ya shiga tsakanin  mu, wallahi ba zan iya hada ido da Mami ba wani irin nauyin ta nake ji."

Murmushi Najib yayi, ya ce,
"To mu koma tinda kunyar ta kike ji."

Hannun sa ta kamo ta ce,
"Haba dai ai kuma ina son na ganta, kasan ita ce kamar Mami na a garin nan."

Murmushi yayi yana jin dadin inda Najwa ke son Mamin sa.

Shiru sukai, can ya kalli Najwa ya ce,
"Na fada miki yau Antyn ki zata dawo ko?"

Kallon sa tayi, ta ce,
"Eh Allah kawo su lafiya."

"Ameen! Kinga yau bangaren ta zan koma kenan."

A ranta tayi tsaki ta ce,
"Har wani zumudi ma kake."

Kan ta, ta dauke tana kallon waje! Duk maganar da yake jin sa kaawai take amman sam ba fahimta take ba.

Wani abu ne ya danne mata kirji, da tana tunanin bata da wannann zafafen kishin amman yanzu ta gane ba haka bane.

Ba dole ba, ta kishin wani ya samu soyayyar da take samu daga mijin ta.

Yanzu fa sai tayi kwana koma ta ce kwanaki bata ganshi ko jin dumin shi ba.

Cikin minti kadan duk mood dinta ya sauya, yana lura da halin da ta shiga, to amman me yafi ta shiga halin saboda sam baya son yin nesa da ita.

A haka suka karasa gidan Mami da saurin ta, ta fita tayi cikin gidan.

Mami na falo tana jin sallamar Najwa ta mike ta taro ta, Jikin Mami ta fada tana murnar ganin ta.

Suna daga tsayen yan aikin gidan suka fara shigo da kayan da tazo dashi.

Kallon su Mami ta tsaya yi ta ce,
"Kayan waye wannan?"

"Mami nice na kawo miki."
"Kai Najwa bakya gajiya ko?"

Kai Najwa tai kasa dashi, sai da suka gaisa, Mami take tambayar ta,
"Najwa ya kuke ince dai kuna zaune lafiya?"

Cikin nauyin da kunya ta ce,
"Lafiya lou ba komai Mami."

"A'ah fa in yana miki wani abun na fada miki ki sanar dani ko?"
"Mami ba abinda yake min sai kyautatawa."

"To masha Allah Najwa naji dadi abinda nake so kenan. Allah kara baku zaman lafiya da fahimtar juna. Allah tsare mun ku."

Najib da yake shigowa, ya ce,
"Ameen Mami,"

Mami ta kalle shi cike da jinndadi da farin cikin yadda ya koma itama Najwan ta koma.

Durkusa wa yayi ya gaishe da ita. Su Talle da suka samu labarin zuwan su da gudun su suka yo falon Mami.

Kai Najwa ta dauke dan ta ce, sunyi fada tinda basu zo mata ba.

Hakuri suka dinga bata, har ta sauko. Saida suka gaisa sannan suka koma wajen Najin.

Shima mikewa yayi, wai yayi fushi shine suka farayiwa Najwa magana bashi ba.

Duk kan su dariya sukayi, komawa yayi ya zauna suka gaisa.

Mami ta mike ta ce,
"Bari na fadawa Dady zuwan ku, Bara'atu aje a daura abinci kunga su Najwa sun zo."

Sama tayi, su Talle sukai Kitchen, Kallon Najwa yayi ya hango damuwa fal akan fuskar ta,

Kan cinyar sa ya janyo ta ya ce,
"Wai menene? Me yake damun ki?"

Shiru tayi tana kallo bene, ta ce,
"Haba Hamma dan Allah ka sakeni, kar Mami tazo ta ganmu a haka ni wallahi ina jin nauyin ta."

Ya ce,
"Ba zan sake ki ba, sai kincire damuwar dake ranki, kar Mami ta zargi ko wani abu nai miki."

"To naji yi hakuri,"
Sakin ta yai ta koma inda take da zama.

Mami ce ta sauko hade da murmushi akan fuskar ta, ta ce,
"Kuzo muje."

Suka mike suka bi bayan Mami.

Najwa ta gaida Dady cikin jin kunya.

Dady yaji dadin yadda ya ga ta kara kyau, ga kulawa da yaga Najib na mata dan ya kasa dauke idon sa daga kallon ta.

Dady nasiha ya kuma musu me ratsa jiki ya kara sanar musu da hakkin juna su da ya rataya akan su.

Mami ma ta kara musu nasiha, ta fada musu yadda zasu zauna lafiya da kula da junan su.

Daga nan suka sauko sukai bangaren Baba, Baba na zaune tana kwadan rama, ta yanka tumatur dinta a gefe, Najwa na gani yawun ta ya tsinke.

Baba na ganin Najwa ta hau washe baki. Tana murnar ganin ta.

Sai da suka gaisa sannan take tambayar su ya gida, suna zaune har ta gama kwadan ta dauko faranti ta zuba musu.

Najwa murna kamar taga me, haka ta fara ci tana wani lumshe ido, Najib ma hannu ya saka yana ci.

Yana kallon yadda Najwa ke nishadin cin kwadan, Sosai take ci, dan da yayi saura farantin ma ta dauke wai ya ishe shi.

Shi kuma ya ce, be ishe shi ba, gudu suka fara a bangaren Baba. Baba dake daki ta fito ta ce,
"Lafiya?"

Najwa ce ta marariraice fuska ta ce,
"Baba bashine babba ba wai bazai barmin ba sai dai na bar masa,"

"Toh!"
Baba ta fada tana kallon Najwa, a take ta gane tana da yaron ciki, wannan yasata ce,
"To ka bar mata kafin ku tafi zan kara yo muku wai shikenan."

Kafa Najib ya hau bugawa a kasa, yana fadin,
"Ni gaskiya ban yadda ba, yanzu duk kun fi son Najwa akai na. Nidai ban yadda ba sai naci."

Yana can rigimar sa, ta shige dakin Baba sai kwanon ta fito dashi a hannun ta dan har ta gama.

Tana fitowa ta mika masa farantin, amsa yayi sai dai gani yayi wayam ba komai, da gudu ta fice daga bangaren Baba.

Baba na fadan ta daina gudu amman ina ta fita bayan ta ya rufa ya bita da gudu shima.

Tana zuwa bangaren Mami bata zarce ko ina ba sai kitchen inda su Bara'atu suke girki.

Har can ya bita ya rutsa ta, tana ganin sa, ta sha mur sai dai ina shi abin ma dariya ya bashi.

Binta yake tana matsawa har ta kai bango, ya rufa kanta, ya ce,
"Wa na kama."

"Haba Hamma!"
ta fada tana nuna masa su Bara'atu.

Baki ya tabe, ya janyo ta jikin sa, da sauri tayi kasa binta yai da sauri shima.

Mikewa tayi ta fice ta kofar kitchen, tana fita ya fito shima.

Hannun ta ya kamo ta fada jikin sa,
"Baby na!"

"Uhmm!"
"Ina son ki."

Shiru tayi, tina ba ita kadai ce me shiba.
"Baby kinyi shiru tunanin me kike yi."

Kai ta girgiza ta ce,
"Ba komai!"

Kallon ta ya tsaya yi, yana kallon idon ta. Son sa ya ke gani tare da tsantsar kishin sa.

Jikin ta ya janyo ta, ya matse ta kamar zai maida ta ciki.

Ajiyar zuciya ta hau saukewa dan kukan zuciya take yi tin dazu.

Kiran sallar da ake shi yasa ta dago ta ce,
"Kaje kai sallah."

Ta juya tayi cikin kitchen, alwala taje tayi tai sallah.

Ta jima tana addu'a Allah ya rage mata kishon nan nata.

Tana zaune akan sallaya ya shigo dakin, a gaban ta ya zauna, ya ce,
"Baby me yake damun kine?"

"Wai me ka gani ne? Ni ba abinda yake damuna."
"Karya kike kina boyen wani abu."

"To ni bana boye komai."
"Shikenan gara ki fadan tin ina gare ki kafin Antyn ki ta dawo ta dauke miki ni."

Take ya kara ganin mood din ta ya sauya, mikewa tayi, aranta tana kara cewa,
"Shi bazai iya danne son ta a gabana ba."

Kallo ya bita dashi har ta fita a dakin, murmushi yayi yabi bayan ta.

Mami ce ta hawo saman ta ce,
"Najwa kije kici abinci an gama,"

"Lah Mami nayo miki miya ma tana cikin wannan fulas din."
"Au haba ai ban gani ba. Baari naje naga kayan."

Ta sauka Najwa nabin bayan ta. Abubuwan da taiwa Mami, Mami ya gani tana sa mata albarka.

Sai kayan da ta kawo.musu tare da su Bara'atu.

Sosai Mami taji dadi sai albarka take saka mata.

Ranar dai anan suka yini, dan sai da yai sallah magariba ya ce, tazo su tafi.

Mami ta ce,
"Ai ka tsaya kuci abinci ko?"

"A'ah! Mami zamu biya mu dauki Sumaiyya ne ta dawo."
"To shikenan Allh Yayi Albarka Allah bada zaman lafiya."

"Ameen!"
Najib ya dinga amsawa da.

Najwa kuwa kan ta a kasa ta rasa me yake mata dadi, ita dama Hamma zai barta ta kwana a gidan Mami da taji dadi.

Dady sukaje yiwa sallama, ya bawa Najwa dubu hamsin, kin amsa tayi, Dady ya ce,
"Haba Najwa, kada kice zaki yi haka mana, mufa iyayen ki, ke da Najib baki da banbanci a gun mu, kinga da Najib na bawa abu da sauri zai amsa ya saka a aljihu, yana godiya, to kema haka nake so. Ke da nake son in kina da bukata ki zo ki fada min. In ina da hali nai miki in yafi karfi na nayi iya inda zan iya. Dan Alah kada ki kara haka kinji ko?"

Najwa tasa hannu biyu ta karba, tana godiya.

Mami kuma kaya ta hado mata da turaruka.

Bangaren su Baba sukaje yi mata sallama!

Baba ce ka dai zaune a falo, su Talle na cikin daki.

Ciki ta shiga tai musu sallama suka fito tare dan rakasu.

Yana tsaye yana kallon su har suka karaso gun su.

Sallama sukai musu suka rabo cikin son juna suna mata godiyar abunda ta basu.

Ko a mota ba wanda ya cewa da dan uwan sa kala.

Sai da suka kusan karasawa Airport sannan ta ce,
"Hamma dama a gidan Mami ka barni na kwana, ni ji nake bazan iya kwana ni kadai ba."

Wani kallo ya wurga mata wanda tai saurin kame bakin ta.

Bai yi magana ba itama bata kara gigin masa magana ba har suka karasa Airport.

Abinda bata sani ba shima bakin cikin rashin ta da zai yi, sai dai ba yadda zaiyi.

Wannan abin na damun sa, sannan ta ce zata koma gidan Mami bayan zai na ganin ta ko yaya ne yaji dadi.

Fita yayi, itama ta fita. Sumaiyya suka hango zaune da akwatin ta a hannu.

Fuska Najwa ta saka tayi wajen ta, dan amsar akwatin ta.

Tana karasawa ta juyar akwatin ta alamar bata so.

"Sannu da zuwa Anty,"
Nan ma bata amsa ba.

Sai gefen Najib da tayi ta rumgume shi. Shi kuwa Mamaki ya tsaya yi, kiss tai masa.

Kai Najwa ta dauke tai gaba abin ta.

Gidan baya ta shiga zuciyar ta na mata zafi kamar zata fashe.



*INDABAWA*

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*159*


*Anty  Safiyya Huguma*  *Ina mika gaisuwata gare ki. Allah ya dafa Allah kare mana ke Ameen*

*ina yin ki, ina son ki irin da yawan nan.*





Tinda taga abinda takewa Najib ta dauke kai, ta lumshe ido kawai.

Duk abinda take masa ma bata sani ba dan idon ta na a rufe har taji anyi parking.

Ido ta bude sai taga sun fita, ba gida suka zo ba wannan yasa ta koma ta kwanta.

Basu fi minti goma ba sai gasu sun dawo.

Leda ya ajiye mata a gefen ta, ya tada mota suka tafi.

Suna zuwa gida ya fita ita ma tabi bayan shi.

Bangaren Sumaiyya suka yi, ita kuma tayi bangaren ta.

Tana shiga ta fada saman gado ta fashe da kuka.

Ta jima tana kuka kafin ta tashi ta shiga bandaki.

Wanka tayi, ta dauro alwala. Doguwar riga kawai ta saka ta tada sallah.

Sai da ta iddar ta jima tana addu'a. Kasa tashi tayi daga inda take, tafi awa biyu zaune a wajen sannan Najib ya shigo.

Da fara'ar sa ya shigo dakin ya na kallon ta,
"Baby na kinci abincin."

Ledar da ya gani ajiye a gefe ita tasa yasan bata ci ba.

Ledar ya dauko yaje ya dauko plate, da cup a kasa.

Dawowa yayi, ya zuba mata farfesun kayan cikin, ya zuba mata lemon.

Shi da kansa ya dinga bata, har ta ce, ta koshi.

Daga ta yayi, ya cire mata rigar jikin ta ya saka mata kayan baccin ta.

Bandaki ya kai ta ya wanke mata baki sannan ya Kai ta kan gado ya kwantar da ita.

A hankali ya dinga shafa kanta yana jijjigata har bacci ya dauke ta.

Ya jima zaune a dakin, kafin yaji karar wayar sa.

Sumaiyya ce, dauka yayi, masifa ta farayi,

"Mallam in a can zaka kwana ai sai ka fada min, kaje ka wani zauna daga zuwa mata sai da safe."

Be magana ba sai wayar da ya kashe kawai.

Ya mike ransa a bace, inda ya tsaya ta mishi abinda take so yanzu bazai tsaya ba.

Abinda yasan ko da gigi Najwa baza ta yi ba kenan.

Addu'a yai mata ya kashe fitilar dakin. Yana fita ta mike. Wani kuka ta fashe dashi.

Lallai tayi wauta da take daukar Najib nata ne ita kadai, dan sam mantawa take da wata Sumaiyya.

Data ga baccin bazai zo ba, sai ta mike ta dauro alwala ta hau yin sallah.

Har asuba idon ta biyu tana karatun alkura'ani.



Najib kuwa a can Sumaiyya ta amshe shi hannu biybiyu, dan itama ba karamar kewar sa take ba.


Da asuba Tana zaune akan sallaya ya shigo dakin.

Tana ganin shi ta saki murmushi, ta ce,
"Barka da Asuba, da fatan kun tashi lafiya."

Shima murmushin yayi, yana karantar yanayin Najwa kafin ya amsa mata,
"Lafiya lou. Ya kwanan kadai ci."

A ranta tace, "Kaji Hamma da neman magana ai dole ni ya tambayen ya kwanan maraici tinda shi be yi kwanan maraicin ba ya samu me debe masa kewa."

Idon ta ya tsurawa ido, wannan yasa ta janye su daga kallonsa, mikewa tayi tana cire Hijab din jikin ta.

Janyo ta yayi ta fada jikin sa. Ido ya lumshe yana jin wani sanyi na jin Najwa a jikin sa.

Ko ya Najwa ta rabe shi sai jikin sa ya fada masa, wannan yasa ya rumgume ta a jikin sa.

Rada ya farai mata, ya ce,
"Me ya hanaki bacci."

Kai ta girgiza masa kawai, daukar ta yayi kamar Baby yayi kan gado da ita.

Lallabata yake kamar Baby har tayi bacci. Sai da ya tabbata baccin take sannan ya tafi bangare  ta.

Gimbiyyar ko motsa batai ba, ya tashe ta, ya tashe ta amman taki tashi.

Hakura yayi, ya tafi part din sa da tun da ya dawo be je ba.

Najwa kuwa bata tashi farkawa ba sai karfe bakwai.

Shima yunwa ce ta tashe ta. Da sauri ta nufi kitchen ta feraye doya, ta daura akan wuta, sai ruwan zafi da ta daura.

Sama ta koma tana gyara dakin ta, sai da ta gama da duk dakunan sama sannan ta sauko kasa.

Doyar ta sauke, ta juye ruwan zafin a fulas.

Kasa ta gyara da dakunan ta turare ko ina sannan ta koma kitchen din.

Doya da kwai ta soya sai farfesun hanta da tayi.

A falo ta ajiye tayi sama dan yin wanka. Tana fitowa ta tsane jikin ta, ta shafa mai ta saka wata doguwar rigar mayerial pink kala.

Dinkin yai mata kyau, hoda kawai ta shafa sai man lebe da kwalli amman tayi kyau sosai.

Turare ta feshe jikin ta dashi, sannan ta sauko kasa

Lokacin karfe taran safe. Zama tayi tana kurbar tea din.

Najib kuwa tin karfe takwas yai wanka ya shirya cikin bakin wando da bakar riga.

Yayi kyau da shi, ya kuma haske da kwarjini.

Bangaren Sumaiyya yayi, tana kwance ko motsa batai ba.

Tsaki yayi ya zaune gefen gado, abinda Najwa batai masa kenan.

Ai kafin ya tashi ta gyara bangaren, tai masa break tai wanka tana jiran tashin sa.

"Sumaiyya! Sumaiyya!!"
Ya kira ta, mika tayi ta gyara kwwanciyyar ta.

"Sumaiyya dan Allah ki tashi mana safiya tayi fa."
"Haba Najib wai mene haka ne, kai ma kasan ka gajiyar dani amman kazo kana in tashi. In tashi in maka me?"

Ta gyara kwanciyya ta kara jan bargo.

Kai ya girgiza ba wacce ta fado masa sai Najwa wacce duk lugwigwita tan dazai yi bazata taba nuna masa ba, bare har taki yin girki ko gyara gidan.

Mikewa yayi, ya ce, bari yaje ya gano Najwan sa.

Da sallama ya shiga dakin, tana zaune tana kurbar tea, duk yunwar da take ji ta kasa cin abinda ta dafa kuma fa ita taji tana son doyar.

Amsa masa tayi, tana murmushi, karasowa cikin dakin yayi, ya zauna a gefen ta.

Zamewa tayi ta ce,
"Hamma ina kwana?"

Murmushi yayi, ya ce,
"Lafiya lou har kin tashi, keda baki bacci ba."

"Hamma inna biye ta bacci wa zai gyaran gida."
"Gani!!

"Haba dai ai kafi karfin haka."
"A'ah! Kedai kin wuce nan a guna."

Fulas din gabata ya janyo ya ce,
"Me kike hada mana ne?"

Tura masa tayi gaban sa, tana mikewa. Cup ta dauko masa ta hada masa tea, ta mika masa abincin.

Fuska ta marairaice ta ce,
"Hamma ni na kasa cin abincin ma."

"Ah saboda me?"
"Nima ban sani ba."

Janyo ta tayi, yana taba jikin ta, ya ce,
"Me kike so to?"

Kai ta girgiza ta ce,
"Hamma gurasa nake so?"

Ido ya zaro yace,
"Gurasa?"

"Eh!"
Ta fada idon ta na cikowa da kwalla.

Mikewa yayi tayi saurin kamo shi, ta maida shi ya zauna.

"Ka zauna ka karya ko?"
"A'ah bari na nemo miki abinda kike so tukkunna."

"A'ah honey ka fara karya wa."
Komawa yayi ya zauna.

Yana ci, yana mata santi sai da ya gama ya mike, kamo shi tayi, ta ce,
"Ka huta man."

Zama yayi, dai dai shigowar Sumaiyya kenan da kayan bacci.

Kallon ta suka yi, fuskar ta a daure ta ce,
"Wallahi Najib kaji tsoron Allah, ranar girkin nawa kazo wajen ta ka zauna."

"Yi hakuri Anty!"
Najwa ta fada.

"Rufe min baki shegiya munafuka ai ke kika jawo shi."
Ran Najib ya baci, dan haka hannun Najwa ya kama kawai yayi sama da ita.

A falo ya zaunar da ita, ya ce,
"Zan fita office amman sai na fara nemo miki gurasar ki kula da kan ki, kinji."

Har ya juya ta kamo hannun sa, jikin sa ta fada tana kuka.
"Hamma dan Allah kayi hakuri kada ka kula ta."

Lallashi ta yayi, sai da ta daina kukan yai masa light kiss a lips din ta.

"A dawo lafiya Allah kiyaye hanya. Allah bada sa'a"
"Ameen My Naj!"

Ya sauka kasa, har lokacin fada take, hannun ta ya kama ya yi bangaren ta dashi.

Suna shiga ya saketa, ya ce,
"Wai Sumaiyya mene haka ne?"

"Ai dole ka fadi haka, ka tafi gun ta da safe wannan adalci na?"
"To naji, bayan wannan sai kuma me?"

"Yauwah ka kalli kayan dakin ta kuwa Sun fi nawa, anya ba kai kayi mata ba."

Kallon ta ya tsaya yi, ya ce,
"Da farko da kika ce naje dakin ta da safe, ni a yadda zan tsara mu kwana girki kwana biyu kowa zai nayi.
sannan da safe zanje gun wacce bana girki haka nan in na dawo daga aiki, sau da dare zan je bai sallama.
Zancen kayan daki da kikayi kuma ni ban taba ganin kayan My Naj ba sai da muka tare, ban san wanda yai mata ba."

Yai shiru sanman ya ce,
"Bana son yada girma kinje gaban kanwar ki kina masifa bakya ganin sai ta raina ki."

"Ai kuwa da naci uban ta."
"Ke banson iskanci, Najwa matata ce, kuma kanwata kinsan bazan taba bari ki mata wani abu ba.  Dan haka ki kula da kanki. Kuma yanzu bazan dau iskancin ki ba, ki gyara bangaren ki ki mana girki kafin na dawo."

Ya juya ya fita. Sai da ya samowa Najwa gurasa sannan ya aika akai mata.

Najwa na ganin gurasar nan ta tashi ta soyata da kwai, da lemo ta dinga sha.

Inda tana gamawa sai bacci. Ba ita ta farka ba sai karfe daya.

Ba wanda ta tuna sai Najib, waya ta dauka sai missed din sa ta gani.

Kiran sa tayi, yana ganin kiran ta ya dauka.

"Barka da aiki Honey!"
Ta fada bayan ya amsa sallamar ta.

"Yauwah Baby na ya gidan?"
"Lafiya Alhamdulilah! Ya aiki?"

"Alhamdulilah! Kinci gurasar."
"Eh ai bacci ma nayi shiyasa ban kira

Please Login or Register in order to submit comment