Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idon ta ta rufe.

Ya dade yana matar mata da zuciya da kalaman sa masu tsada da dadi.

Sai da idon sa ya sauka kan agogo yaga shida da rabi.

Da sauri ya ajiye ta agefe, ya mike ya shiga Ban daki. Sai da yai wanka, sannan ya fito da towel daure a kugun sa.

Najwa kuwa tinda ya barta ana bata ko.motsa ba, har ya fito.

Daukar ta yai gaba dayan ta yai bandaki da ita.

Yana shiga ya saka ta a bawon wanka, wanda ya cika mata da ruwan dumin.

Da sauri ta bude idon ta. Ganin shi ba riga yasa tai saurin rufe idon ta.

Rigar ta yake kokarin cirewa wannan yasa ta riker hannun sa.

Kai ta girgiza alamar bata so.
Ya ce,
"Please rigar kawai zan cire miki."

Hannun sa da ta rike ta saka. Rigar ya cire mata, kirjin ta ya tsaya kallo wanda duke jajir dasu a cike, abin sha'awa.

Hannun sa ya kai ya shafe, da sauri, ta bude idon ta tare dayin wata irin ajiyar zuciya.

Fuska ta marairaice, ta ce,
"Hamma please ka fita. Kaji har an tada sallah ko."

Murmushi yayi, ya ce,
"To kiyi sauri ina jiran ki."

Ya fita ba dan yaso ba, sai dan yadan itama tana jin kunyar sa ne shiyasa.

Yana fita, ta maida idon ta, ta lumshe, sai da ta dauki minti biyar sannan tai wankan ta fito daure da towel.

Batai tsammanin ganin sa ba, amman tana fitowa sai ji tayi an dauke ta.

A kan gado ya dire ta, jikin ta ya tsane mata ya dauko mai zai shafa mata.

Kallon sa tai ta ce,
"Kaje sallah kuwa?"

Ya ce,
"Ina fa kafin na fita har an iddar shiyasa nayi a nan."

Kallon sa tayi ta ce,
"Wai Mami tasan kana nan?"

"Eh man!"
"Wayoo Allah Hamma dan Allah ka fita kaji, yanxu ai wannan abin kunya nema."

Kallon ta Najib yai ya cee,
"Dan ina tare da matata shine abin Kunya.."

"Haba Hamma, nidai kaje gani nan fitowa."
Murmushi yayi, ya ce,

"To bari na shafa miki mai."
"A'ah wallahi nagode."

Ta fada tana daukar hijab ta zira.
"To ina jiran ki, kuma Allah in baki fito ba sai na zo na dauke ki da kai na."

"Naji."
Ya mike ya fita yana kallon ta.

Yana fita ta sauke ajiyar zuciya.




*INDABAWA*

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*152*

*To me zance, banda abincewa haka nan banda abin yi sai dai godiya. Da fatan Alheri gareku masoya. Allah barmu tare gaba daya. Ameen*

*Nima ina kaunar ku gaba daya da wanda na sani da wanda ban sani ba gaba daya. Nagode Allah bar zumunci*



Yana fita ta sauke ajiyar zuciya.

Shiryawa tayi cikin wata atamfa, orange kala, me adon brown da yellow, dinkin riga da siket ne, ba karamin zama yayi a jikin ta ba.

Haka Atamfar ta amshe ta tai mata kyau sosai. Sosai ta dawo amaryar ta.

Zama tayi ta kasa fita saboda Mami, kunyar Mami take ji, ta fita su hadu.

Najib kuwa yana fitowa daga bangaren sa, yaga Sumaiyya da Mami a falo suna kallo, gaban sumaiyya da kayan marmari tana ci.

Zama yayi gefen Mami ya ce,
"Mami nah."

Hararar gefe tai masa, ta dauke kai. Dariya yayi ya ce,
"Me nayi mami?"

Bata bashi amsa ba. Ganin ya dau kusan minti ashirin da fitowa yasa shi turawa Najwa sakon yana jiran ta fa.

"Hamma dan Allah ka bari ni kunyar Mami nake ji."
ta maida masa da reply.

Murmushi yayi, ya tura mata,
"Allah in kika bari nazo ko tam!"

Tana ganin sakon tai saurin mikewa ta dauki wani yellow mayafi ta yafa, sai turare da ta kara feshe jikin ta dashi.

Sumaiyya kuwa a ranta ta ce,
"Ko ina Najwa, dan tinda tazo bata ji wani yai maganar ta ba."

Bata gama tunanin ba ta jiyo takun tafiya, daga jin takun kai kasan tafiyar ce me daukar hankali, ga wani kamshi da ya cika dakin tin kafin wanda ke tahowa ya karaso.

Daga nesa ta hango ta amman bata gane ko wace ba, dan haduwa tasan me tahowar ta gama haduwa.

Kallo ta maida gare ta. Inda shima Najib duk hankalin sa ya koma kanta.

Sai da ta karaso falon sannan Summy ta gane wacece. Tsaki tayi ta dauke kai. A ranta kuwa tana cewa
"Gaskiya Najwa ta kara wayewa da iya ado."

Ita kanta tasan Najwa ta wuce mata amman taki ta yadda da hakan.

Mami ce, tayi murmushi, ta ce,
"Najwa sai yanzu kika fito, baki ci abinci ba."

Murmushi yake Najwa tayi dan kunyar Mami take ji har ga Allah.

Bama yanzu da Najib ya  kara mata wata.

Kasa tayi da kai, ta ce,
"Nayi bacci ne."

"Sai kika ga yayan naki ko?"
Wayyo kunya kashe Najwa.

"Uhmm."
Ta zaune a gefen kafar Mami.

"To ga Antyn ki."
Mami ta fada tana nuna mata Sumaiyya.

Ita sai a lokacin ma ta ganta,
"Lah ai ban lura da ita ba."

"Ina yini? Kuna dawo lafiya?"
Ta gaishe ta.

"Lafiya lou"
Ta amsa kamar zatai kuka.

Mami ce ta kalli, Najwa ta ce,
"Kije kici abinci."

"Toh!"
Ta fada tana mikewa. Duk abin nan da ake idon Najib na kan Najwa.

Ya kasa dauke ido daga kallon ta. Jin zata bar wajen yasa shima ya mike ya ce,
"Nima bari na ci abinci tinda Mami bata ta tawa sai taki."

Murmushi Mami tayi kawai. Bayan Najwa yabi.

Tana zama sai gashi. Kallon sa tayi, ta ce,
"Allah Honey ka daina min haka."

"Me nayi?"
"Ai kafini sani."

"Kinga zuba mana abinci muci yunwa nake ji dazu kasa ci nayi da ban ganki ba."

Abincin ta zuba masa ta dauki wani  plate zata zuba wani da sauri ya kamo hannun ta ya ce,
"Me zakiyi?"

"Abinci zan zuba mana."
"Wannan kuma fa?"
Ya fada yana nuna na gaban shi.

"Naka ne."
"To muci tare."

Zatai magana kenan ya duba  yayi wajen bakin ta dashi.

Falo ta kallo taga Mami ma waya take dannawa, baki ta bude ya bata. A haka har suka gama.

Mikewa tayi,
"Ina kuma zaki."

Ya tambaye ta.
"Wajen su Talle zani."

"Kibar mijin ki a ina."
"Haba Hamma ga su Mami nan."
Ta yi gaba.

"Allah kiyaye hanya."
"Ameen!"

Ta fita, ta kofar kitchen ya fita da sauri, kafin ta karasa bangaren har ya rigata zuwa.

Tana saka kafa taji har an janyo ta,
"Innalilahi wainna illahir rajiun."

Ta fada tana, yin addu'a a ranta. Rumgumeta yayi,
"Ya ce,
"Yi hakuri na tsoratar da Baby nah ko?"

Duka ta kai masa yai saurin barin wajen a guje ta bishi ya fito daga bangaren Baba da gudu.

Binsa tayi a guje, da gudu sukai bayan gida duk yadda taso.ta kamashi ta kasa, wannan yasa ta tsaya tana maida numfashi.

Dariya ya tsaya yana yi. Kujera ta samu ta zauna dan ba karamin gajiyar da ita yayi ba.

Karasowa yayi wajen ya zaune, haki takeyi, wannan yasa ya koma kitchen ya dauko mata ruwa.

Sai da ta sha ta nutsu sannan ta ce,
"Allah sai na rama.kuma!"

"Yi hakuri kinji."
Mikewa tayi zata bar wajen. Da sauri ya kamo hannun ta.

"Wai ina zaki ne?"
"Wajen Baba mana."

"Gaskiya ban yadda ba. Haka kawai ga mijin ki kuma ki tafi ki bar shi."

Kallon sa ta tsaya yi, janyo ta yayi ya zaunar da ita akan cinyar sa.

Kanta ya kwantar a kirjin sa, yana shafar bayan ta ido ta lumshe.

Hira suke jifa jifa, yana tambayar ta. Sannan yana bata labarin aikin da yayo.

Abi kadan ya dago fuskar ta ya sumba ta a ido ko a wuya.

Haka dai. Sai wajen karfe goma sannan suka yi cikin gida.

Fitilar Baban falo a kashe take, sai ta falon sama suka gani a kunne.

Janta yai wai su hau sama wajen dady, amman ta ce, Aah dan ita kunya take ji.

Wannan yasa ya rakata bangaren sa. Zata rufe kofa kenan ya shiga.
"Baby kada ki sa key zan dawo kinji."

"A'ah nidai kai zaman ka wajen Anty nah"

Dakin ya shiga ya jawo ta jikin sa ya ce,
"Bazan iya kwana ba a gefen ki ba. Ki bari gani nan zuwa. Bari naje na gaida Dady na dawo."

Fita yayi yai sama wajen Dady.

Dady na falo suna hira da Mami ya hau saman, sai da suka gaisa sannan ya  mike zai tafi.

"Sumaiyya na dakin can,"
Mami ta fada masa, kai ya gyada kawai yayi hanyar dakin.

Tana kwance akan gado da kayan bacci. Tana ganin shi ta taso.

Kallon ta ya tsaya yi, karasowa tayi ta rumgume shi. Mamaki yake abinda sam bata masa.

Mutumin da yake a bukace ai dole ya biye mata. Ranar yaga gata gun ta dan kin barin shi tayi sai da ta gamsar dashi sosai wanda har gefin asuba idon su biyu.

Duk da hankalin sa na kan Najwa dan ya ce mata zai dawo, duk da ta ce, yai zaman sa a waje Antyn ta.

Najwa kuwa yana fita tai wanka ta saka kayan baccin ta ta shige cikin bargo.

Bacci me dadi ne ya dauke ta wanda tin da ta kwanta ko farkawa batai ba.

Najib kuwa Allah Allah yake a kira Sallah asuba yaje wajen sahibar sa.

A ransa yana addu'ar Allah yasa kada ta yi fushi.

Sai da yai wanka, sannan ya tafi massalaci, ranar ba zauna ba ya dawo yai waje Najwa.

Tana kwance tana baccin ta tinda tasan ba sallah zatai ba.

Kallon ta ya tsaya yi, a ransa ya ce,
'
"Sleeping beauty."

Fuskar ta ya shafa, ya kwanta a bayan ta ya janyo ta jikin sa.

Kansa ya daura a bayan ta. Bacci me dadi ya dauke shi.

Farin ciki kamar ya kashe shi yau gashi a jikin Najwa yana bacci.

Najwa kuwa cikin bacci taji dumi a jikin ta tini ta kara narkewa Jikin Najib.

Bacci sama sama yayi, dan wani yanayi da yake jin shi a ciki.

Yana mamakin irin son da yake mata.

Yana mamakin lokacin da ya fara son ta daga gani, kai Lallai ikon Allah sai shi.

Allah ne ke saka soyayyar bayin sa azuka tan mutan.

So ba ruwan da kyau, nasaba, Kudi, da sauran su. Indai son gaskiya ne koya mutun yake haka yake son sa.

Ko me mutum yake haka zai na burge shi. Duk wanda ya kwadaitu da wani abun jikin mace ko kudi da dukiya wannan da gyara acikin lamari sa.

Allah ka barmu da masoyan mu. Ameen.

Yana addu'a a kullun da Allah ya bashi Najwa yana farin cikin samun ta dan yasan ya gama dace a duniya kuma mace ta gari ita ke kokarin samar wa mijin ta gidan Aljanna.

Dan ita zatai jagorancin sa wajen sa shi ya kula da iyayen sa tare da tarbiyya a gare su.

Najwa ita ce, babban burin sa na duniya kuma Allah ya cika masa.

Ranar wani irin bacci sukai dan sam.basu san gari ya waye haka ba.

Dan har sha biyun rana ba wanda ya motsa a cikin.

Karfe sha biyu, Najwa ta farka, zata mike taji ta kadandane a jikin sa.
Kai ta daga, taga ya rumgume mata kam ajikin sa kamar wanda za'a kwace masa ita.

Ganin kar ta tashe shi yasa ta lafe a jikin sa, a ranta ta ce,
"To yaushe ya dawo bata ji shigowar sa ba."

Can ta ce,
"To ina bacci ma ta yaya zan san dawowar sa."

Kai ta daga ta kalli agogo karfe sha biyu da arbain da biyar.

Ido ta zaro, ta ce,
"Na shiga uku yau ban taya Mami aiki ba."

Ido ta lumshe, dai dai budewar nashi idon.

Kallon ta ya tsaya yi, ya kasa dauke ido daga kanta.

Kiss ya kai mata a saman idon ta. Da sauri ta bude idon ta.

Kafe ta yayi da ido, wannan yasa tai saurin yin kasa da idon ta.

Dan bazata iya jurar kallon cikin idon sa ba.

"Baby na!"
"Uhmm!"

Kawai ta fada. Sakin ta yai, ya mike. Daukar ta yai ya kai ta bandaki ya hada mata ruwa sannan ya fito.

Yana fita tai saurin saka key ta koma ta cuda jikinn ta tai wankan.

Towel ne kawai a ban daki wannan yasa ta ce,
"Hamma please help me with my Hijab.

Shiru taji wannan yasa ta dauka ko baya dakin.

Fitowa tayi ta zauna a gaban mudubi zata shafa mai, hago shi tayi ta jikin mudubi yana karasowa wajen ta.

Kai ta dukar kasa tai saurin mikewa tayi gefe.

Hijab din ta, ta dauko ta saka.
kallo  sa tayi, ta ce,
"Kaje kai wankan."

Shiga ban dakin yai kawai. Yanayin sa duk ya canja yai sanyi da yawa.

Cikin sauri ta shirya ta saka wata doguwar rigar atampa, me A shape, rogar ta mata kyau ta zauna a bayanta.

Haka nan gaban rigar ya tashi, batai kwalliya ba sai hoda daman lebe da ta shafa kawai.

Turare ta dauka tana ambaliyar sa.
Kofa taji an kwankwasa wannan yasa, taje ta bude,

Mami ce, hanya Najwa ta bata ta shiga.

Amman Mami ta tsaya, daga waje. Da sauri Najwa ta durkusa ta gaida ya.

Mami ta amsa, sannan, ta ce,
"daman zan fita ne, nace bari nazo na fada miki naga baki fito ba."

Kai Najwa tai kasa da shi dan kunya ta ce,
"Wallahi bacci ne ya dauke ni."

"Ba komai. Ba break din ku can. Yanzu zan dawo."

"To Mami adawo lafiya."
"Allah yasa."

Ta juya ta fita. Tana tafiya Najib ya fito, fita Najwa tai da sauri dan dauko masa break fast din shi.

Kunun Gyada ne Mzmi tayi shi wanda yasha madara, sai dankali da ta soya da kwai. Sai ruwan tea.

Duk haka ta hado ta kawo musu nan. Tana shigowa har ya shirya cikin kananun kaya.

Yana cikin fesa turare ta shigo da sauri ya karasa ya amshi kayan hannun ta.



*Indabawa*

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*153*

*Rukayya Nagode sosai da son littafin nan da kike. Allah bar zumunci nagode nagode da kulawar ki a gareni. Allah bar kauna*




Yana karbar kaya hannun ta ya ajiye, ya janyo ta jikin sa.

Rumgumeta yayi, yana shinshina wuyan ta, ya ce,
"Baby kinyi kyau. Kamar a dauke ki a gudu."

Maballin rigar sa take karasa saka masa, ta ce,
"Ai kafini yin kyau kalle ka fa."

Gaban mudubi ya matsa da su, suna kallon juna ta cikin mudubi.

"Haba wama zai hada"
"Me fa?"

"Kyan ki danawa."
Murmushi tayi, ta ce,
"Mu da ake cewa muna kama. Bayan ka fini kyau."

Kansa ya kai wuyan ta, yana shinshinawa ya ce,
"Allah kin fini kyau shiyasa nake addu'a Allah yasa Ya'yan mu su dauko kyan ki."

Dariya tayi, ta ce,
"Su dauko naka dai."

Kiss ya kai mata a kumatu, ya janyo ta wajen abincin su.

Ita ta hada masu komai a plate daya, sai tea da ta hada shi kuma ta hada masa kunu.
Sai da ta tabbatar da yya koshi sannan ta hau ci itama.

Suna gamawa ta tashi zata debe kayan hannun ta ya rike ya amsa ya ce yana zuwa.

Minti kada sai gashi ya dawo rike da wani akwati me shegen kyau.

Ajiyewa yayi a gaban ta, daukar ta yai ya saka a kan cinyar sa.
Akwati  ya jawo ya ce, kinga Tsarabar ki. Ya bude akwatin duk kananun kaya ne a ciki, da shimi da body hook da dogayen wandu na, da riguna masu bin jiki, sai mini skit.

Yana dagawa yana nuna mata, sosai ta dinga nuna jin dadin kayan da ya kawo mata.

Sai wasu hadadun cover shoes da sandal masu kyau. Wanda suke hade da jakun kunan su.

Kaya dai masi kyau da kyan tsari da tsada ya jido mata.

Rumgume shi tayi, ta ce,
"Hammana nagode Allah ya sa kama da alheri,"

Bakin su ya hade gu daya wanda yasa tayin shiru.
Sai da suka dau mintina sannan ya zare bakin sa daga nata.

Idon ta a lumshe ya kwantar da kanta a saman kirjin ta.
"Najwa ina son ki."

Murmushi tayi, rigar jikin ta ya fara kokarin cirewa.

"Hamma!"
Ta kira sunan sa kawai.

"Gwada miki kayan nake son yi."
shiru tayi har ya gama cire mata rigar jikinta.

Ya rage daga ita sai bes da dogon farin siket.

Kallon ta ya tsaya yi, shine latsa can taba can, sumbaci can haka dai ya jima kafin ya dauki wata, daga cikin  kayan ya saka mata.

Rigar iya vinya ce, wannan yasa ya cire mata underwear nata, me net ce, dan duk ana ganin kirjin ta. Wanda aka shirya stones a wajen.

Rigar ba karamin kyau tai mata ba. Ja ce.

Mikar da ita yayi, ya ce,
"Bude idon ki gani mana."

Budewa tayi a hankali. Ita kanta kallon kanta ta tsaya yi. tayi kyau.

Jin shi tayi ta baya ya rumgume ta, ya ce,
"Ina kaunar ki Baby na."

"Nima haka.!"
Ranar a daki suka yini abinda ke fitar da Najib sallah ne.

Mami sai yamma ta dawo, dan ko abincin rana sai talle yasa ta kawo musu.

Yana makale da Najwa sai kace za'a kace masa ita.

Sumaiyya kuwa tana can tana son zuwa Kano, ko dan taga Antyn ta Kaltum.

Wannan yasa ta ce,
Zata fadawa Mami dan tasa ya barta.

Har yamma Mami bata ga motsin Najib da Najwa ba wannan yasa Mami cewa a yau zasu zo su bar mata gida.

Tana zaune a falo, Sumaiyya ta shigo, gefen Mami ta zauna ta ce,
"Mami daman so nake kisa baki akan dan lah Najib ya bar ni naje gida gobe kinga na jima banje ba."

"Kada ki damu ki je ki shirya kayan ki zan fada masa in ya dawo."

"To Mami!"
tayi daki, tana Murna.

Sai magariba sannann Najibbya fito daga bangaren sa.

Mami na falo, a zaune, kallon sa tayi ta ce,
"Zo nan son"

Matsawa yayi kusa da ita. Ta ce,
"Wallahi ka fiya takura ace ka matse yarinyar mutan. To kazo ka hada naka ya naka ku tafi."

Kasa yai da kai yana cewa,
"Aah Mami sai gobe ai yanzu dare yayi ko?"

"Kaci gidan ku. Daman dazu Sumaiyya take ce min tana son zuwa gida sai dai bata sani ba ko zaka barta"

Wani sanyi yaji dan yasan ko bazan zai samu ya sake da Najwa in sun koma.

A fili kuwa nuna wa yayi ba komai Allah kaita lafiya.

Ya tafi massalaci sai bayan isha'i ya dawo, dakin da Sumaiyya ke ciki ya shiga

Tana zaune, ya kara sa gefen ta, ya ce
"Mami ta ce wai zaki je gida ko? To me kike bukata. Ki rubuta min yanzu a tanadar miki ba sai goben ba."

Takarda ta miko masa dan ta gama rubuta komai take bukata.

Kudi ne take so har dubu dari biyu, shikena abinda ta rubuta.

Wayar sa ya dauka ya mata transfer atake, sai dubu hamsin da ya bata tai wa yan gida tsara ba.

Ba godiya bare komai, haka nan ya debo mata atamfofi da shadda takai gida.

Ranar a dakin ya kwana, dan yasan in ta tafi zata dau a sati biyu.

Yau ma da asuba ya nufi wajen Najwa. Najwa kuwa tana zaune tana karatun alkur'ani ya shigo.

Kallon sa tayi, ta dukar da ka ta kasa, ta ce,
"Ina kwana Hamma?"

"Lafiya lou Baby na. Ya kika tashi?"
"Lafiya lou "

Zama yayi a gefen gado ya ce,
"Zo nan."

Mikewa tayi a hankali ya nufi wajen sa. A saman cinyar sa ya zaunar sa ita.

Kallon ta yayi, ya ce,
"Jiya nazo miki sallama naga kinyi bacci."

Shiru tayi, hijab din ya fara kokarin cire mata. Yana cirewa wata rigar bacci ta bayyana

Rigar da ta gama tafiya da imanin sa. Gaba daya ya rasa me zai yi.

Rumgume ta yayi, yana jin son ta na dada shigar sa. ji yake kamar ya maida ta ciki dan so.

Sun jima a haka, ita ce, ta ce,
"Hamma zan je na taya Mami aiki."

"Tashi muje tare toh."
"Kaji ka. Mungode."

Ya sakata, mikewa tayi ta dauki hijab din ta, faita tayi.

Mami na kitchen tana hada break Najwa ta karaso, gaishe ta tayi cikin girmanawa sannan ta fara taya ta aiki.

Suna cikin yi, sai ga sallamar sa nan, Mami ya gaisar, Najwa ta gaisar  dashi duk dan Kar Mami tayi zaton suna tare.

Amsawa yayi yana wani murmushi,
"Mami fa ne zan taya ku."

Ya fada yana bin bayab Najwa da kallo.

"Kaje ka huta."
"A haba Mami yaushe rabon na taya ki aiki. Mami kawai kije ki kwanta zamu karasa ko My Honey."

"Uhmm!"
Kawau Najwa ta ce.

Murmuahi Mami tayi ta fita. Tana fita ya saki aikin da yake yayo wajen ta.

Rumgume ta yayi ta baya, Numfashi ta ja, ta ce,
"Ina aikin da kazo taya mun?"

"Uhmm Uhmm ba kece kika kirani ba."
"A'ah ni ba ruwa na."

A haka dai suka gama aikin yana rike da ita,

Zata dauki basket taje ta jere a daining ya amsa ya ajiye.

Jikin sa ya janyo ta, ya rumgine ta. Dan har ga Allah besan me zaiyi yana jin sasaucin abinda yake ji a ransa ba.

In yaji ta a jikinsa, yana dan jin sauki. Suna a haka Sumaiyya ta shigo kitchen.

Najwa da take ta jutawa kofa baya, bata ga shigiwar ta ba.

Yana ganin Sumaiyya yai murmushi ya ce,
"Kin tashi?"

Najwa najin yai magana ta fara kokarin zamewa daga jikin sa.

Sumaiyya kuwa Banza tai masa ta dauki abinda zata dauka tai waje.

Tana fita ya sake ta ya ce,
"In ina rike ki kkna son na sake, sai na yi miki a gaban Mami."

Ido ta zaro, ta  ce,
"Yi hakuri,"

Yai waje da sauri. Suna yin break suka fita shi da Sumaiyya dan shirin tafiyar ta. Anjima ne.

Tinda duka fita basu dawo ba sai wajen karfe uku. dan da kyar suka samar mata tashi a ranar wanda da yamma zasu tashi.

Suna dawowa ta nufi gida ta kwashi abinda take son kwasa, daga nan kuma ta dawo ta debi kayan ta.

Ko Abinci bata tsaya ci ba, Najib ya dauke ta suka tafi bayan tayiwa Mami sallama.

Najwa da Mami na falo, a zaune, wasu kaya aka kawo, take taya Mami zaba.

Tana gama zaba ta ce,
"To gasu nan, naki ne. Aje a ci amarci dasu."

Kasa Najwa tai da kai, magana Mami ta cigaba da yi, ta ce,
"Najwa mijin ki ya dawo dan haka yau zaki tare a gidan ki. Komai na riga da na gama tinda ma koya miki komai da komai. Sai amfani dasu da naken son kiyi. Najwa Allah baku zaman lafiya."

"Ameen!"
Ta amsa kanta a kasa, kibar wannan kayan anjima me dinkin zai zo ya amsa na sa a kawo miki."

"To Mami nagode."
"Ba komai ai ke 'ya ta ce."

Bangaren Bqba tq mike tayi, tana shiga su talle suka jau tsokanar ta wai miji ya dawo an yada su.

Baba ita ce me kare ta. Ita dai murmushi take.

"Anty Najwa ashe yau zaki tare, to Allah kawo kazantar daki."
Talle ta fada.

Bara'atu ta ce,
"Anty amman dai zamu kai ki ko?"

Najwa ta ce,
"Kai gidan ku, wai sunan kakar ku gare ni ne."
Ta mike ta fita tana dariya suma dariyar suke.

Bacci take ji gashi la'asar tayi, daki kawai taje ta kwanta dan ta dan samu karfin jikin ta.

Tana kwance Mami ta shigi part din Najib, bedroom din ra shige kai tsaye, kayan ta, take son hada mata, wannan yasa ta bude durowa duk abinda yake nata ta jide mata a akwatin ta.

Sai da ta gama tsaf ta fito da akwatin a hannun ta. Sama tayi ta shige bandaki kai tsaye, ruwan wanka ta hada mata wanda suka sha turaruka a ciki.

Lokacin goshin magariba ne, wannan yasa, sai da akai magariba sannan Mami tasa tai wankan.

Tana fitowa ta hau shiryawa, mai ta shafa, sai hoda da ta  shafa da man lebe, kwalli ta saka a idanun ta wanda suka kara kyau da girma.

Taba cikin shiryawa Mami ta shigo da kaskon turaren wuta.

Ajiyewa tayi ta bude doruwar ta, ta dauko mata wata Farar a tamfa, wacce akai mata ado da purple kala.

Atamfar tayi kyau, wata farar Alkebba ta dauko mata.

An ma atafar dinkin riga da siket, dinkin ba karamin amsar Najwa yayi ba.

Tana gama shiryasa mami ta mika mata kaskpn turaren ta zuba mata turaren wuta na jiki.

Nan da nan kamshi me dadi ya turare dakin.

Sai da ta gama Mami ta zaunar da ita asaman gado.

Akasa ta sauka.




*INDABAWA*

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*154*

*Sandaf Aikin ki yana kyau. Allah kara basira da zakin hannu. Allqh ya dafa miki.*

*Ameen!"




Tana sauka kasa, ta saki murmushi tayi wajen kawayen ta

Ta ce,
"Sannun ku da zuwa,"

"Yauwah Hajiya ya gidan ya amaren."
"Lafiya Alhamdulilah. gata can an gama shiru ku take jira kawai."

"Allah sarki su Najwa an zama manya, Allah duk lokacin da zan kai amarya sai na tina lokacin mu. Allah dai ya bada zaman lafiya."
Wata daga cikin kawayen Mami ta fada.

"Ameen!"
Duk kansu suka hada baki suka amsa.

Waya Mami ta daga, ta kira Bara'atu, tana dagawa ta ce,
"Kuna ina ne, ku fito zaku tafi fa."

Ta kashe wayar cikin minti biyu sai gasu nan sunco kwalliya sai kace masu zuwa wajen biki.

Sama sukai, Mami tabi bayan su. Dakin da Najwa take, suka isa, tana zaune a gefen gado ta lula can tunanin Najib.

Suka shigo dakin, buda Talle ta saki,
Ta ce,
"Amarya kinsha Kyau."

Ta fada tana daga mayafin kanta. Hawaye taga yana zarya akan fuskar ta.

Hawayen ta hau goge mata tana bata hakuri.
"Haba Najwa me ne abin kukan ke da zakijr wajen me sonki. Dan Allah ki daina wannan kukan abinda kullum muna tare."

Hawayen idon ta, ta goge jin shigowar Mami, Mami ta kalle su

Please Login or Register in order to submit comment