Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya ci.

Bara'atu kuwa ba abinda bataiwa Najwa.

Sai da cikin Najwa ya isa wata daya sannan ta samu sauki take iya cin abinci ta daina aman nan.

Sumaiyya kuwa bata san halin da ake ciki ba.

Hamma Salim kuwa sai da yazo ya duba ta, mamin ta dai ta waya tai mata sannu.

Haka nan abokan Najib sai da suka zo, duk da Najwa bata da lafiya karba hannu bibiyu ta dinga musu.

Kowa yasan da cikin Najwa sai murna da Allah sanya alheri ake yiwa Najib.

Duk matan abokan Najib da suka zo sai sunce yanzu yai aure dan akwai fuska.

Khaleel da Khadija ma sunzo amman aranar suka juya.

Khadiya sai zolayar Najwa take.

Bangaren Najwa dai tinda aka gano tana da ciki bata rasa baki yan barka.


Kamar ko da yaushe yau Ranar kwanan Najwa ne wannan yasa tin safe take gyara bangaren nata dan tinda ta fara laulayi bata taba jin karfi jiki kamar yau ba.

Bangaren nan  nata sai da ta maidashi kamar sabo dan gyara.

Abinci kuwa ta daura masa danbun shinkafa wanda yaji kayan lambu sai farfesun kiji da tai masa.

Lemon kwakwa tai masa wanda yaji Madara yai sanyi.

Wanka taje tayi ta caba ado cikin wani Bakin three quartern wando wanda gwiwar sa net ne.

Wata farar riga ta saka wacce duk jikin ta net ne.

Kallon kanta ta tsaya yi a mudubi, cikin ta ta shafa wanda baza ka taba cewa akwai cikin wata biyu a gun ba.

Sai dai kirjin ta da ya ciko.
Kiran Sallah magariba taji anayi wannan yasa ta dauki wata doguwar riga ta saka.

Sai da ta idar da sallah sannan ta janyo wayar ta, Zahra ce ta kira.

Dagawa tayi ta ce,
"Yar uwa ya kike yau naji ki shiru?"

"Ina lafiya na kira naji ya lafiyar Babyn mu ne."
Dariya Najwa tayi ta ce,

"Yana lafiya. Ina Baby Fauwaz?"
"Kingan shi nan yayi bacci."

"Allah sarki a gaida min da Yaya Mustapha muna nan zuwa muma nan ba da dadewa ba."
Allah kai mu. Sukai sallama.

Zata iya cewa tin da ta samu cikin nan akwai wadan da kullun sai sunzo dubata ko ai mata waya wai ya Babyn su.

Ita abin har mamaki yake bata.

Tana zaune akai sallar isha'i sai da tai Sallah sannan ta mike ta cire kayan jikin ta zauna da adon da taiwa Najib.

Tana taga taji shigowar sa, kallo ta bishi da shi bayan ya fito.

Bangaren ta ya kalla,  ya shige bangaren Sumaiyya.

Tana tsaye a taga har ya fito, a hankali ta fita daga dakin ta sauka kasa.

Yana shigowa ta fada jikin sa tana masa sannu da zuwa.

Kallon ta kawai yake yana hadiyar yawu. Dan ba karamin rikita shi tayi ba.

Janshi tayi cikin daki, ta bashi lemo me sanyi yasha.

Kayan jikin sa ta taya shi ragewa. Sannan ta kama hannun sa sukai sama.

Wanka tai masa, wanda Najib ya zama kamar gunki duk inda tai dashi nan yake yi.

Har ta gama ta shirya shi cikin kayan bacci, falo tayi dashi inda ta gabatar masa da abincin da ta shirya masa.

Najib be kara  shagala cikin jin dadi ba sai da yaga abinda ta dafa masa.

Nan ya zage yana ci yana zuba mata santi. Sai da yaci ya koshi sannan ya hau zuba mata albarka.

Najwa na jin dadi a duk sanda ya ke saka mata albarka.

Shi da kansa ya dinga ciyar da Najwa har ta gama.

Yanzu duk wani aiki da zatai indai me wuya ne sai ya hanata da kansa yake rage mata wasu aiyuka.

Gata da sangarta ba wanda bata samu gun Najib, ta yadda ta kuma tabbatar da ita ta daban ce agun sa.

Inda yake mata kai kace cikin ya girma dan sai ya dauka awanni yana hira da cikin shi kadai.

Duk abinda yasan tana so ko zai faranta mata yi mata yake.

Suna kan gado, kan ta a saman kirjin ta, sai shafa gashin kanta yake.

Dan mintsinar sa ta yi, ya  bude idon sa, wanda suke lumshe kamar me jin bacci.

"Baby na me kike so?"
Kallo  sa tayi tana aika masa da sakon soyayya kafin ta ce,

"Hamma ina son zuwa kano, ina son Ganin Mami da Dady da Hamma Salim da Basama da su Ummah. Hamma dan Allah ka barni naje."

Eh shima ya san ya kamata taje, aure shekara daya da watanni amman bata ga iyayen ta ba.

Gaskiya bega abinda Najwa zata nema yaki yi mata ba.

To amman beson tayi nisa dashi, amman dole ya barta taje, duk da daman yana da plan din nan da sati biyu zasu bar kasar.

Kanta ya shafa, ya ce,
Ki kwantar da hankalin ki, wani satin zakije jnsha Allahu kinji."

Kamkame shi tayi tana masa godiya. Ba karamin dadi taji ba.

Daga haka suka fara hirar soyayyar su, yana kara bata labarin akan irin yadda ya tsinci kansa akan soyayyar ta.

Wani abin tai dariya wani kuma tayi shiru tana godewa Allah da ya hada ta da wanda yake son ta.

Tana alfahari da samun Najib a matsayin mijin ta ba abinda zata ce sai godiya da Allah.

Da wannan tunanin bacci ya dauke su.

Kamar yadda Najib ma yake godiyar samun Najwa da alfahari da begen ta.


Washe gari tin da suka tashi da asuba basu koma bacci ba.

Tana gefen sa, yana shara da goge goge, yaki ya barta tayi komai.

Haka nan a kitchen ma shi ya hada musu kayan kari sannan ya dauki abar sa sukai sama dan yun wanka.

Tare sukai wankan bayan sun gama wasannin su.

Shi ya shiryata, yai mata kwalliya ya saka mata wani net less blue and pink, riga da zani ne.

Sosai kayan suka zauna a jikin ta, haka ma zanin ya zauna a kugun ta.

Bayan ta ya shafa, juyowa tayi ta kalle shi, ido daya ya kanne mata ya ce,
"Wallahi Zanin ma yai miki kyau. Ke komai kika saka kyau yake miki."

"Kai Love kai dai ka fiya kwada ni da yawa."
"To ai gaskiya na fada."

"Naji."
Ciki ta dafe ta ce,
"Ni muje yunwa."

"To ranki ya dade bari na saka kaya."
Ya dauki kayan ya saka.

A baya ya goyo ta suka sauko kasa. Dai dai shigowar Sumaiyya kenan.

Tana ganin su tayi saurin boya dan kar su ganta.

Lebe tazo yi musu dan tana son sakawa Najwa maganin na.

A kasa ya ajiye ta, ya dauko break din nasu suka fara ci.

Sai da suka gama ya ce,
"Baby bakya son cin abinci da yawa duk rakin yunwa, gaskiya Baby nan ya fito sai na zane shi yana takurawa Baby na."

Murmushi tayi ta matsa jikin sa ta kwanta akan kirjin sa.

Agogo ya kalla ya ce,
"Daga ni naje na dauko abu a bangaren Sumaiyya nazo muje a duba min Baby na."

Ya fada yana daga rigar jikin ta. Cikin yake shafawa yana masa magana kamar yadda ya saba.

Kan kujera ya mike ya kwantar da ita wannan yasa Sumayya barin wajen da ta labe da sauri.

Bayan gida tayi, shi kuma Najib yai bangaren Sumaiyya dan dauko takardun sa.

Yana shiga yaga bangaren ba kowa wajen duk yai kaca kaca ga kura.

Sai ledar cake da kwalin lemo da gwangwanin lemo.

Ciki yayi nan ma bata nan. Durowar gefen madubi ya janyo, me zai gani.

Maganin Zubar da ciki ya gani a wajen a ajiye.

Zama yayi a gefen garin ya dafe kansa. A ransa yana me fatan Allah yasa ba abinda ya gani bane.

Dauka ya karayi, yaga iya adadin da aka sha sha. In bazai manta ba, duk cikin Sumaiyya zubewa yake, wani yana sani wani bema sanin da shi.

A kalla shekara ta shida kenan tana wannan abun.

Waya ya zaro, yai magana akan azo a saka masa Cemara a duk bangaren gidan sa.

Abinda zai dauka ya dauka ya fita.

Yana mamakin mene aibun sa da har Sumaiyya zata ki hada zuri'a dashi.

Abin mamaki yake bashi dan ya jima yana cewa tazo suje asibiti a  duba mene matsalar yawan barin ta amman taki.

Da haka ya koma bangaren Najwa ya dauke ta suka tafi asibiti.

A Office din sa akai mata duk abinda za'ai mata.

Tana kwance a gadon dake office din shi kuma yana duba patient din sa.

Tana lura da yanayin sa ya canja tin daga lokacin da Ya fita daga dakin ta dazu da safe.

Damuwa karara take gani akan fuskar sa wanda da yaga zata gane sai ya sakar mata murmushi.

Yana zaune taji yana amsa waya akan ya amshi key din bangaren Najwa yayi abinda ya kamata sannan yaje bangaren Sumaiyya ma ya saka.

Wayar ya kashe yana mikewa yayo gun Najwa.

Kallon sa Najwa tayi dai dai lokacin da yake yaye rigar jikin ta.

Cikin ta yayiwa kiss sannan ya dago ya kalle ta.

Kansa ta shafa ta ce,
"Me yake damun My honey?"

Murmushi yayi ya ce,
"Me kika gani."

"Haba love kada ka manta zan iya ganewa ko baka fadan ba."
Mikewa tayi zaune. Ta kamo hannun sa, ta marairaice murya  ta ce,

"Dan Allah love ya fadan damuwar sa ko na san hanyar da zanyi na kawar masa da ita."
Kallon ta yayi ya hada goshin su gu daya ya ce,

"Ke nake so damuwata na kasance kullum a jikin ki."
Ya fada yana kanne mata ido daya.

Murmushi tayi, taja hannun sa, ta  ce,
"Bayan wannan akwai wata please ka fada min."

Kallon ta yayi ya kalli cikin idon ta sosai. Lallai Najwa na son sa dan ita ma har ta shiga damuwar ganin halin da yake ciki.

"To zan fada miki but sai abinda nake zargi ya zama hakan tukkunna."
Murmushi tayi, ta ce,

"Ka tabbata?"
"Eh!"

"To ka rage damuwar ko?"
"Zan rage."

"Ki kwanta ki huta sai mu tafi ko?"
fuska ta shagwabe ta ce,
"Please muje gun Mami man."

"Ki mata me?"
"To ina ruwan ka?"

Ta fada tana murguda baki.
"Iyee haka ma kika ce ko?"

Ta mike zai bar wajen kamo shi tayi da sauri tana cewa,
"Yi hakuri yi hakuri da wasa nake maka fa."

Kwafa yayi ya ce,
"Tashi mu tafi to!"

Mikewa tayi tana saukkowa daga gadon."




Sumaiyya kuwa tinda Najib ya fita daga gidan itama ta fita wannan yasa bama tasan anyi wani abu a gidan ba.

Sai yamma ta dawo da kawayen ta, suna zaune suna hira. Ta kalli daya a cikin su ta ce,
"Ni na rasa wane irin ne Najib ace duk lokacin da ya kusance ni sai ciki."

Tayi tsaki, ta ce,
"Dazu daga yin test wai ciki ne dani, anjima nake son shan magani yadda kafin ya dawo guna gobe ya fita ma."

"Gaskiya ai kece kiyi planing kin tsaya wasa."
"A'ah ai da mahaifar ma zanje a cire min."

Dariya sukayi, suka ce,
"Ai kuwa dai da yafi."

"Zanyi shawara da Hauwa duk da nasan da kyar ta yadda."
"Ke kuma da yake ga uwar ki ko?"

"A'ah ba haka bane naga tana da hankali akan mu na."
"Kutt me kike nufi. Mu bamu da hankali kenan. To sai dai kace mara hankali duk cikin mu muna da hankali dan kiji."

Shiru tayi kawai. Ana magariba suka tafi lokacin ta shiga daki ta balli maganin ta sha.



Sai dare Su Najwa suka dawo, inda bacci kawai suka kwanta.

Washe gari kamar yadda ya saba shiga bangaren kowa haka ya shiga na Sumaiyya tana kan gado a kwance ya shiga.

Mikewa tayi tana kallon sa! Gaskiya Najib kyakyawa ne bama in yana dakin Najwa tafi ganin kyan sa.





*INDABAWA*

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*163*




*INDABAWA Hausa Novel group tnc for love nd supporting.*
Allah barmu tare Ameen.




Kallon sa take a ranta tana fadin sai ta san yadda ta raba Najwa da shi.

"Ya kika tashi?"
ya tambaye ta yana zama a kan kujerar gaban madubi.

"Lafiya lou! Ya Najwan?"
Ta tambaya

Kallonta Najib yayi, kafin yace,
"Tana lafiya, kinsan masu ciki sai da  lalashi."

Zabura tayi jin ya ambaci ciki.
Kallon ta yayi ya ce,
"Lafiya?"

"A'ah ba komai."
Ta fada cikin rashin gaskiya.

Kafada ya dage ya ce,
"To ni zan fita sai na dawo."

Bama taji me yace ba saboda ta tafi tunanin Najwa na da ciki.

"Tab ai bata isa ba, ciki tazo ta haihu, ta gaje dukiyar sa."
Ta fada a fili.

Dakin ta fara zagayewa tana tunanin abinda zatayi.

Ta jima kafin tayi  tsalle na tuna abin yi.

Sai da ta tabbatar Najib ya bar gidan sannan tayi wanka ta shirya.

Najwa kuwa tana can ta raka mijin ta tana masa addu'a.

Falo ta koma tana zaune tana waya da Hamma Salim.

Suna gamawa ta mike dan zagawa bayan gidan.

Sanye take da dogon hijab har kasa fuskar ta tayi kyau tana tafiya tana kallon wajen dan duk kallon da take masa ta taga ne bata taba zuwa gun ba.

Kamar ance ta kalli gefe taga Sumaiyya wata faduwar gaba tayi da sauri ta fara karanta addu'a a cikin ran ta.
*Allahumma inna naj'aluka finuhurihim wana uzubika min shururihim*

Gaba tayi, ta zauna a gun da aka tanadar dan zama a huta.

Ta jima a gun dan sallah azahar ita ta tashe ta.

Bangaren ta ta koma, tayo alwala ta tada sallah.

Tana idar wa ta shiga kitchen, tayi miyar ta tin jiya dan haka ta daura farar shikafa da taliya sai kwai da ta dafa.

Tayi hadin Kabej da dankalin turawa da bama da waken gwangwani.

A firij ta saka sai lemon Mangoro da tayi.

Falo ta koma zama tayi da bismillah tana shafa cikin ta. Addu'a ta tofa a cikin nata. Waya ta dauka, ta kira zahra. Mikewa tayi ta dauko Maltina a cikin firij ta dawo ta zauna.

Suna gama waya tayi waya da Mami, Mami na kara jan hankalin ta akan ta dage da addu'a da karanta alkur'ani ko dan cikin jikin ta.

Godiya Najwa tayi Mami na saka mata albarka.

Tana gamawa ta kira Mamin Najib ta gaishe ta, tambaya ta hau yi mata me take so?

Ba abinda take bukata dan haka Mami ta barta.

Sumaiyya kuwa tana can tana leken Najwa har ta bar wajen sai da ta dauki awa wajen biyu sannan ta shiga daki ta dauko maganin da aka bata da Maganin zubar da ciki tayi bangaren Najwa.


Tana cikin bude Maltinar zata sha kenan sai ga Sumaiyya ta shigo.

"Innalillah wainna illahir rajiun!!"
Ta fada a cikin ranta.

Karasowa tayi ta  kalli Najwa ta kalli dakin, ta ce,
"Yauwah daman Abinci nake son in kinyi ki zubo min yunwa nake ji."

Mikewa Najwa tayi tana ajiye Maltinar akan table din dake gefen ta.

"Lah Anty ba komai. Bari na kawo miki."
Tayi cikin kitchen din.

Da sauri Sumaiyya ta matsa tana saka mata magungun nan a cikin maltinar.

Tana gama zubawa kenan sai ga Najwa. mika mata tayi.

Amsa tayi. Ta ce,
"Sannu."

"Yauwah!"
Daukar matlinar tayi zata sha, dakatar da ita Sumaiyya tayi dan ta tabbata kwayar bata narke ba.

Ta ce,
"Najwa sai naga kamar maltinar da sanyi ko?"

"Eh!"
"Ai kuwa ba ason masu ciki suna shan kayan sanyi ki bari ta dan wuce ko."

"Toh!"
Najwa ta ce, ta ajiye.

Tana nan a tsaye dan so take ta narke taga ta sha ta tafi.

Najib ne ya kira, dagawa tayi tana masa ya aiki ya ce mata ai yana hanya.
Addu'ar dawo gida lafiya tai masa sannan ta kashe wayar.

Sumaiyya na tsaye tana kallon ta. Sai da tabbatar da kwayar ta narke sannan ta ce,
"Ki sha ai ta rage sanyi. Bari naje naci abinci.'

Dauka Najwa tayi tana kurba, juyawa tayi tafi cikin murna da jin dadi.

Ko falo bata rufe ba taji shigowar Najib da sauri ta shige ta rufe kofar ta.

Bangaren Sumaiyya ya yi, yana shiga ya ga alamun rashin gaskiya a tattare da ita

"Allah ya shirya ki."
kawai ya iya fada ya fito daga bangaren nata.

Najwa kuwa tana can tana shan malt din ta har Najib ya shigo.

Da sauri ta taro shi tana masa sannu da zuwa.

"Yauwah Baby na. Sannu da kokari."
Suka koma cikin falo.

Abincin sa ta gabatar masa ta zuba masa sannan ta dauki ragowar malt din ta karashe.

Kallon ta yayi ya ce,
"Ke dai kinfi ganewa kwadayi ko?"

"Love to ba Babyn ka bane."
"Ai shi yasa nace sai na Zane  shi ya fito."

Dariya tayi, ta kwana akan kujera. Mintin ta uku da kwanciyya taji cikin ta na hautsinawa.

Da sauri ta mike tana fada.
"Innalillahi wainna illahir rajiun."

Kallon ta Najib yayi, ya ce,
"Menene?"

Kasa magana tayi sai cikin ta da take nuna masa.

Kwanciyya tayi tana juyi da sauri Najib yayo gun ta. Yama rasa abinda zai yi.

Cikin minti biyu sai ga fara kumfa na fitowa daga bakin ta.

Da gudu ya dauke ta yai ma Dariver magana ya fito da mota.

Asibiti suka nufa da gudun gaske. Yana zuwa yayi office dinshi da ita.

Da gudu sauran ma'aikatan asibitin suka karaso office din.

Shi kasai mata komai yayi sai hawaye dake zubowa daga idon sa.

Hannun sa kuwa duk ya baci da jini abinda ya kara daga masa hankali kenan.

Addu'a yake aran sa yana Cewa Allah yasa cikin be fita ba.

Mutum mutumi ya zama ya kasa koda motsawa daga inda yake.

Da kyar ya iya ciro waya ya kira Mami ya shaida mata abinda kefaruwa.

Mami cikin tashin hankali ta taho asibiti.

Najib na ganin ta ya fada jikin ta yana kuka sai kace karamin yaro.

Lallashin da take yi tana kwantar masa da hankali.

Likitoci sun fi biyar ne suka rufa akan Najwa.

Har magariba suna kan ta da kyar Mami ta lallaba Najib ya tafi massalacu Dan yayi sallah.

A can ma addu'a ya dinga wa Najwa. daga massalaci ya Koma cikin.

Ba kowa a dakin sai Mami dake zaune a gefen ta. Ta zuba tagumi, Kallon sa Mami tai masa nuni da hannu alamar yazo.

Kamar karamin yaro haka ya je wajen ta. Najwa ya kalla ya ce,
"Mami me sukace yana damun ta.?

"Kaga Najib ka kwantar da hankalin ka, ba wani abu bane kaje Dr Farouk yai maka bayani. Kasan dai kowa da kaddarar sa dan haka ayi hakuri a rumgumi kaddarar da Allah ya saukar mana kaji."

Kai ya gyada dan sam bajin abinda Mami take fada yake ba. Najwa kadai yake kalla yana can tunanin me ya same ta da halin da yanzu take ciki.

Fita yayi daga office din shi ya nufi office din Dr Farouk.

Kallon sa Dr Farouk yayi ya ce,
"Dr Najib Kaje kaga Najwan ne?"

"Eh naje me yake damun ta ne?"
"Zauna muyi magana man."

Kai ya girgiza alamar bazai iya ba.
"Fada min abinda ya samu Najwa kawai dan shi kadai ne zai kwantar min da hankali."

Dafa shi Farouk yayi, ya ce,
"Haba Friend cool ur mind Najwa tana lafiya, sai dai An sawa Najwa guba a abinda ta ci ko ta sha, haka nan tasha maganin zubar da ciki."

Kai ya hau girgizawa yana fadin,
"Najwa bazata taba aikata haka ba, Najwa bazata taba gigin zubar da ciki ba. Tabbas akwai wanda yai mata haka. Ai kuwa duk wanda na gane da hannun sa a cikin wannan al amarin bazai ji da dadi ba."

Kallon sa ya mayar kan Farouk ya ce,
"A wane hali take ciki yanzu?"

"Eh to tana da rai sai dai abinda ke cikin ta ya zube ayi hakuri haka Allah ya kaddara ina maka jaje Allah yasa haka ne mafi alheri."

Ido Najib ya damke, yana jin wani zafi a zuciyar sa da idanun Sa.

Ido ya bude, Wanda sukai Jajir dasu sai kace jini.
"Nagode!"

Ya fada cikin raunin murya ya juya ya fita. Office din shi ya shiga.

Akan gadon da Najwa take kwance ya kifa kansa.

Mami ce ta matso ta dago shi, ta ce,
"Haba Son ka zama jarumi me karbar kaddara me kyau da mara kyau. Allah ya jarabbe ka yaga yadda zakayi ka daure kaci wannan jarrabawar. Insha Allahu zakaga abu me kyau nan gaba."

Kai ya gyada mata kawai yana goge hawayen idon ta.
"Taso kaci abinci."

Kai ya girgiza mata. Ya ce,
"Wallahi bazan iya ba. Mami bari naje massalaci ga kiran Sallah isha'i."

"Allah bada sa'a sai ka dawo."
ya fita.

Sumaiyya kuwa tinda taga fitar Najib da Najwa a hannu kuma hankalin ta ya tashi sai yanzu take na damar abinda taso aikatawa.

Kirjin ta na dukan uku uku take da haka ta kira Anty ta.

Antyn ta sai karin gwiwa da ta dada mata ta nuna kar ta damu ai ba asan ita bace.

Da haka ta samu ta dan kwantar da hankalin ta.

Najib ya jima a massalaci yana addu'a Allah ya tayar mata da Najwa.

Sai wajen goman dare sannan ya dawo cikin asibitin duk ma'akatan asibiti tausayin Najib suke dan yanzu suma kara tabbatarwa da irin son da yakewa Najwa.

Cikin kan kannin lokaci ya rame yayi zuru zuru.

Yana shiga gun Najwa ya je ya kalle ta, ya tofa mata addu'a sannan yayi wajen Mami.

"Mami kinji me ke damun Najwa?"
"Naji Najib amman ban san wanda zai mata haka ba."

"Insha Allahu koma waye asirin sa zai tonu."
"Ya kamata ka tafi gida ko?"

"Gida Mami. Wallahi Mami ba zan iya barin Najwa ba. Dan Allah Mami ki barni agun ta dan Allah Mami hankalina bazai kwanta ba in nayi nesa da ita."

Kai kadai Mami ya kada ta ce,
"Zauna kasha ko ruwan zafi ne."


Da kyar yasha dan cewa yayi Najwa bata ci komai ba shima bazai iya ci ba.

Dadyn sa baya gari dan haka besan me yake faruwa ba.

Ranar tare suka kwana da Mami da Najib.

Najib ko runtsawa be ba. Daga yayi sallah yayi sallah yai addu'a zai zo ya kalli Najwa.

Cikin kan kanin lokaci tayi rama sosai, ta kara fari.

Fuskar ta dauke da murmushi. Sai ya sumbace ta sannan yake komawa ya kara tada sallah.

Haka yai tayi har akai sallah asuba ya tafi massalaci. Sai bakwai ya dawo cikin office dinshi.




*INDABAW

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*164*



*Na gaida ku yan kungiyar HAJOW Allah ya kare mana ku gaba daya.  Allah kara mana hakuri da juriya da son junan mu. Ina alfahari daku.*

*Maman mu maganin kukan mu Hajiya Nafisa jinjina ban girma gareki. Allah Ubangiji yasa kifi haka, Allah tasare mana ke da yan uwan mu.*







Bayan ya dawo Mami ta tafi gidan dan ta kimtsa.

Acan tayo musu abinci, Sannan suka taho tare dasu Bara'atu.

Shi kuma yayi wanka ya shirya ya dawo kusa da Najwa yana kallon ta.

Komai da yake yi karfin hali ne amman jikin sa babu gwari ko kadan.

Duniyar tai masa zafi ya rasa abinyi, tsoro yake ji tsoro ba kadan ba ma.

Yana son Najwa, ya fada ya kara fada Najwa ita ce Rayuwar sa.

Son Najwa shine jinin jikin sa. Zai iya sadaukar da komai dan samun farin cikin Najwa.

Kai be ki ya bata rayuwar sa ba ma. Najwa duniya ce, duniyar sa me zaman kan ta.

Samun mace kamar Najwa ba abune mai sauki ba, ya tabbata ya rasa Najwa bazai samu wacce zata maye gurbin sa ba.

Yana rasa kalmar da zai mata bayanin irin son da yake mata, amman yana jin dadi in ya nuna mata son da yake mata a rayuwar auren su.

Ya tabbata tana yadda, Ya tabbata yana sata farin ciki ya mantar da ita duk wani abu wanda yasan komai manta shin take a lokacin shi kadai take gani da tinawa tare da bashi kwarin gwiwa wajen isar da sakon da yake son isar wa.

Yana son Kalar soyayyar da Najwa ke nuna masa, ya tabbata ba kowa yake samun kwatan abinda yake samu ba.

Ya tabbatar da shima Najwa na son sa. Be son bacin ran ta ko kadan farin cikin ta shine abin son sa a koda yaushe.

Yarinya yar albarka me daraja da girma a gunsa.

Ai inda sai namiji ya daga kafa matar sa zata shiga Aljanna to ya tabbata kafar sa a dage zata kasan ce kullum dam Najwa ta samu Aljanna madaukaki ya ta daban.

Yana son Najwa yana kaunar ta, be taba jin son ta ya ragu ba sai daduwa da yake.

Amman duk lokacin da ya kama wacce tai wannan abin bazai taba barin ta haka ba.

To wai mema Najwa baiwar Allah tayi da har za'a salwantar da rayuwar ta.

Kai ya dafe, idon sa yayi jajir zuciyar sa tai zafi sai tafasa take.


Ahaka Mami ta dawo ta same shi. Tare suke Talle da Bara'atu har da Baba.
Duk sai da suka tausayawa Najwa. Kowa Addu'a yake Allah tashi kafadun ta.

Suna bawa Najib hakuri kan ya karbi kaddarar da Allah ya saukar masa.

Su Talle kamar suyi musu kuka, dan Najwa ba sawa ba cire wa koda suka zo gidan ta anan suka kara tabbatar da Najib yayi dacen mata.

Komai ta debo su, komai ta gano su zata bawa me zasu ce da Najwa in ba addu'a ba.

Sun san irin so da shakuwar dake tsakanin Najib da Najwa suna sha'awar su da kwadayin samun irin wannan zaman auren a tsakanin su.

Su kan su sun kara yabawa Najib wajen samo  Najwa da yayi.


Kallon sa Najib ya maida kan Najwa dake. Kwance, Ba abinda take sai fitar da Numfashi ta cikin oxygen, amman daga haka ba inda yake motsi a jikin ta.

Mami ce, ta dubi Najib cikin tausayin yada shima ya rame ya koma wani iri, ta ce,
"Na fadawa Baffah dasu Mamin Najwa abunda ya sameta, suna mata sannu, su Baffah sunce

Please Login or Register in order to submit comment