Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ina wayar ta.

"Tana falo akan kujera."
Ta fada mata.
Summy wacce ta sandare a gun ta bita da kallo har tazo daidai in da take.

Wani kamshi taji tana fitar wa kamshin turaren da Najib ya aika mata dashi.

Falo tayi ta zauna ta dauki wayar ta. Missed call din Najib ta gani.

Ido ta bude, ta fara kiran sa.
"Ya Najib!"

Ta fada, Summy kallon ta, ta tsaya yi, bata ji me ya fada ba amman sai taga ta saka dariya ta ce,

"Muna kitchen muna muku girki, dan yaya yaci abincin da yawa ne."

Shiru tayi, ta ce,
"Toh mu dai muna gamawa zamu tafi, munyi missing Mamin mu."

Shiru ta kuma yi, sannan ta ce,
"To Yayan mu sai anjima."

Ta katse wayar. Bara'atu ta kwallawa kira.

Amsawa tayi ta ce,
"Ki sauri ki gama muje gida Mami na jiran mu."

Summy kuwa kallon talle ta cigaba dayi na yadda taga suna waya da Najib suna wasa da dariya.

Abinda basu taba yi ba. Zama tayi a gefen tana kallon TV.

Talle kuwa sai satar kallon ta take, ganin ba wani wanka da tayi bare kwalliya.

Mikewa tayi, tayi cikin dakin baccin su.

Kallo Summy tabi ta dashi. Gyara mata tayi ta hada mata ruwan wanka ta dauko mata wata atamfa acikin kayan ta, ta ajiye a kan gado.

Fitowa tayi ta ce,
"Anty Amarya ga ruwan wankan ki can na hada miki."

Mikewa tayi ta nufi dakin nata, ba tare da ta mata godiya ba.

Bangaren Najib ta nufi ta gyare masa shi ta turare masa. Ta juna masa ruwan wanka.

Tana fitowa taji kiran sallah magariba.

Alwala talle tayi, tayi sallah sannan ta mike ta shiga kitchen.

Lokacin har Bara'atu ta gama aikin ta.

Dakin Summy ta nufa ta ganta sanye da kayan da ta dauko mata, fuskar ta ba kwalliya daga hoda shikenan.

Kallon ta, tayi ta ce,
"Anty zo nai miki kwalliya."

Ta dauko kayan kwalliyar ta fara mata kwalliya.

Ba karamin kyau tayi ba, ita kanta da ta kalli kanta a mudubi sai da tayi murmushi dan taga tayi kyau.

Ba godiya ta mike ta tada sallah.tana idar wa ta kalli talel ta ce,
"Daura min dan kwalli man."

Karba talle tayi ta mata daurin sannan ta mike tayi waje itama.

Har Bara'atu ta jere kayan abinci a daining ta goge komai da jere shi.

Talle ce ta kalle ta ce,
"Tashi mu tafi."

"Baza kice abincin ba."
Bara'atu ta tambaya. Lokacin Summy ta fito daga Dakin ta tana tafiya dai dai.

"Ni A'ah girkin Mami zan ci. ya fi dadi."
Mayafin ta dake kan kujera ta dauka, tare da jakar ta.

Summy ta kalla ta ce,
"Antyn mu mun tafi sai wata rana."

Talle ta fice, bara'atu ta kalli ta, ta ce,
"Anty Mun tafi ga abincin can najere muku."

Ko kallon ta Summy batai mata ba. Kai ta girgiza a ranta tana tunanin a ina Ya Najib ya samu wannan matar da bata da mutunci.

Ai Tallen ce ma dai dai da ita. Ta fada a ranta tana yin waje ita ma.

Abincin da sukayi ta zauna tana ci, santi take, a ranta kuma tana cewa wannan abincin suka ki ci wai na Mami yafi shi dadi tab lalai.

Sai da ta cika cikin ta sannan ta koma falo taba taunar cigom tana kallo.

Suna fita drivern su ya dauke su, a dakin Mami suka tadda Najib da Mami na masa fada.
Falo suka koma.

Sanye yake da Farar shadda sai sheki take, an masa 'yar ciki da babbar riga.

Bakin takalmi ya saka da hula, sai agogon azurfa dake makale a hannun sa. Sai tashib kamshin yake yi.

Mami ce, take masa fada tare da nasiha akan kula da iyali.
"Najib yanzu ka girma dan ajiye iyali ba karamin abu bane. kaji tsoron Allah ka sani Sumaiyya amace a hannun ka in ka zulubce ka Allah zai saka mata. Kaji tsoron Allah ka sauke mata hakkin  ta dake kanka. Kada ka samo zalumtar ka duk abinda zatai maka.
Ka kula da cin ta shan ta da suturar ta.
Da kula da lafiyar ta ka bata kyakyawar kulawa.
Ina tai maka laifi ya nusar da ita ba fada ba. Dan Allah Najib kabi ta a hankali kasan mata."

"Insha Allahu Mami."
"Allah maka albarka, yashi muje dakin Dadyn naka."

Ya mike ya kamo hannun ta suka fita. Dakin Dady suka shiga, Dady na zaune sanye da jallabiya ruwan madara a jikin sa.

Hannun sa rike da jarida yaba dubawa. gefen sa kuma fruit ne da lemo a jiye akan table.

Da sallama suka shiga dakin. Amsa musu yayi cikin sakin fuska. Yana cewa,
"Ango ne da kansa."

Kasa Najib yayi da kai, ya zuna a kasa gefen kafar Dady.

Dadyn ma nasiha yayi masa, akan ya rike matar sa lafiya.

Allah sarki Najib har da kuka na barin Mamin sa.

Mami kuwa sai tsiya take masa wai sai kace mace.

Da suka sauka kasa, Su Bara'atu sai da suka sa shi dariya.

Har bakin mota suka rakashi, sannan suka juyo.

Dakin Mami suka je, suka cee sun dawo. Abinci tasa suka zubo suka ciki. Ita ma duk jikin sa a sanyaye.

Sai da ya biya ya siyi kaji da lemoka sannan ya wuce gidan shi.

Yana yin parking zai fita wayar sa tayi kara, yana dubawa yaga Khaleel ne.

Dagawa yayi yana dariya, ya ce,
"Ango kasha Kamshi "

Dariya Khaleel yayi, ya ce,
"Sosai ma, na rigaka girma."

"Ya kake, ya gida da Khadija?"
"Lafiya kalou. Ya Sumaiyya dasu Mami?"

"Mami tana lafiya. Sumaiyya sai yanzu zan ganta."
"To a gaishe ta, sannan dan Allah abi da ita a hankali."

"Kai ni bana sin iskanci fa."
"Hali na sani ai."

"Sai da safe."
"Allah baka hakuri. Sai da safe."

Ya kashe wayar. Gidan ya tsaya kallo gidan da tinda ya fara ginin sa ya tsara yarinyar nan ita zata zauna.

Yau gashi wata ta rigata shiga cikin sa. Ko da yake haka Allah ya tsara.

Addu'a yayi ya tofe harabar gidan. Kofar dakin ya nufa da sallama.

*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *118*

Da sallama ya shiga dakin. shiru yaji wannan yasa yayi tsamanin ko tana cikin daki.

TV ya gani tana yi, kashe ta yaje zai yi, hango ta yayi cikin kujeta, tana kallo hankalin ta kwance.

Fasa kashewa yayi, ya koma tsakiyar dakin ya zauna a kan kujera.

Mikewa tayi daga kwancen da take, kallon ta ya tsaya yi, ba laifi Sumaiyya kyakyawa ce, kuma kwalliyar da tayi ta kara mata kyau.

Ya zaiyi dole yasan yadda zai koyawa kan za, son ta.

Zama tayi, ta gyara zaman rigar jikin ta. Murya a sanyaye tace,
"Ina yini?"

Fuskar sa ya dan saki ya amsa mata, da
"Lafiya lou ya gajiyar biki."

Kasa tayi da kai, ta amsa masa, da
"Lafiya. Ya taka?"

"Lafiya Alhamdulilah."
Sukai shiru.

Can ya ce,
"Dauko plate da kofi."

Kitchen ta mike tayi, ta dauko ba tare da ta dauraye su ba.

Karba yayi, yaji su kamas ba ko dan sanyin ruwa.

Kallon ta yayi, ya ce,
"Baki dauraye ba ai."

Mikewa yayi ya nufi kitchen din da kan sa ya dauraye plate din sannan ya dawo dakin.

Kazar ya bude ya saka a kan plate din sai lemon da ya bude ya zuba mata a cikin cup.

Mika mata yayi, ya koma kan kujera yana canja chanel.

Kallon sa tayi, ta ce,
"Kai baza kaci ba."

Kai ya girgiza, ya ce,
"Naci abinci a gida."

Murya ta dan shagwabe ta ce,
"Dan Allah kazo kaci ko kadan ne."

Ta fada tana mikewa ta nufo shi a gefen sa ta zauna ta mika masa plate din.

Cinyar kaza ya dauka, ya fara ci a hankali. Kallon ta yayi ya ce,
"Bismillah.!"

Dauka ita ma tayi ta fara ci. Kofi ya dauka zai zuba lemo tayi saurin mika masa na hannun ta.

Karba yayi ya sha, ya mika mata ragowa.

Hankalin sa ya mayar akan labaran da ake a BBC.

Sai da taci ta koshi sannan ta ajiye zama ta gyara tana kallon TV din.

Karfe tara ya mike yayi bangaren sa, wanka yayi ya saka jallabiya yayi alwala ya rufo bangaren sa.

A inda ya barta anan ya same ta. Kallon ta yayi, ya ce,
"Kije kiyi wanka da alwala kizo muyi sallah."

"Toh!"
Ta amsa masa, tana mikewa.

Dakin ta, ta nufa tayo wanka, ta daura alwala.

Wata rigar bacci ta saka me fitar da tsiraici.

Jikin ta, ta hade da turarukan da Mama ta bata.

Zama tayi a gefen gado tana latsa wayar ta.

Tana barin falon ya dauke kayan da sukai amfani dasu yakai su kitchen.

Kaya  kallon ya kashe shima ya nufi dakin da ta shiga.

Da Sallama ya shiga dakin, amsa masa tayi tana mikewa.

Kallon ta yayi, take yaji tsigar jikin sa ta tashi, hankalin sa ma haka.

Dauriya yayi, ya ce, ta dauko hijab din ta. Dauko wa tayi ya jasu sallah raka'a biyu.

Yana idar wa, ya dafa kanta ya karanto addu'a.

Sai da ya gama ya mata tambayoyi game da tsarki da ibada ba laifi ta san hukunce hukunce da suke saka wanka da bata tsarki.

Mikewa yayi ya kashe fitilal dakin ya bar dim light kawai.

Kan gado ya nufa, yana cewa,
"Taso kiji."

Mikewa tayi ta zauna a gefen sa.
Kallon ta yayi ya ce,
"Sumaiyya Allah yayi ke ce matata ta farko. Ina fatan kuma Allah ya daurar mana da zaman mu."

"Ameen!" ta amsa kanta a kasa.

"Bazan miki karya ba, ba kuma zan yaudare kiba Sumaiyya, nasan ina son ki saboda damar da kika bani har kika aminta dani kika zamo matata ta. To nagode da wannan damar da kika bani."

Shiru yayi yana nazarin abinda zai fada. Cikin sanyi murya ya ce,
"Amman kiyi hakuri, akwai wata yarinya da nayi alkawarin auren ta. kuma in har na ganta zan cika wannan alkawarin. Dan Allah kiyi hakuri kar ki damu zan yi adalci a tsakanin ku, iya bakin gwargwado."

Wata irin faduwar gaba ce ta doke ta, idon ta tini ya ciko da kwalla.

Hannun ta ya kamo wanda haka ya kara haifar masa da wata matsanaituwar sha'awa.

"Kiyi hakuri, ba fin ki tayi ba ko wani abu. Na riga nayi alkawarin hakan shiyasa. Amman kisani ba abinda zai rabamu dake ki kwantar da hankalin ki."

Kai ta girgiza kawai, kanta ya dago, kwalla ya gani a idon ta, jawo ta jikin sa yayi ya rumgumeta yana lalalshin ta.

Ai kuwa kamar an soketa ta fashe da kuka  sai da ya tabbata ta gama kukan sannan ya dago ta.

Harshen sa ya saka yana lashe hawayen da suke zuba daga idon ta.

Tini jikin ta ya mutu ta kasa magana, shims nan da nan jikin sa ya hau rawa.

Romancing dinta ya fara ba qaqautawa. Tin tana iya jurewa har ta saka masa kuka.

Ina yayi nisa bema san me take yi ba. Bargo kawai yaja ya rufe su.



Najib be bar Sumaiyya ba sai da ya maida ita cikakiyar mace.

Duk rashin jin Summy da bin mazan ta bata yadda ta zubar da mutuncin ta ba.

Dan tana kwadayin kaiwa gidan mijinta ko tasamu kima da daraja a idon sa.

Ai kam Najib yaji dadin yadda ya sameta, hakan kuma ya dada mata matsayi babba a wajen sa.

Da asuba shi ya taimaka mata tayi wanka ya gasa mata jikin ta, sannan sukai sallah.

Sai da ya bata magani sannan suka koma bacci.

Basu suka tashi ba sai karfe Sha biyu.

Wanka ya kara mata, sannan shima yayi wanka.

Shi da kansa ya shiryata cikin wata ruwan omon atamfa wacce akai mata dinkin riga da siket.

Rigar me kyau irin ta zaman gida dan duk albarkacin kirjin ta a waje suke.

Mami tin karfe bakwai tasa aka kawo musu abinci dan haka suna tashi ya hada musu abinci suka ci.

Sai riritata yake, ba karamin jin dadi haka yayi mata ba.

Dan ranar taga gata, tayi mamaki ashe haka Najib yake.

Shi kuwa wannan kyautar da tayi masa yasa ya ke dada mata haka dan yasan abinda ake wuyar samu a wajen yan matan yanzu kenan.

Wannan abun kuma ya dada masa son ta, da saka masa nutsuwa sai yanzu yaji nutsuwar da ake cewa in anyi aure ana samu.

Ranar shi kansa yayi mamakin yadda yake ta nan nan da Summy ko tafiya baya barin ta tayi, haka nan komai na gida shi yayi yana zaune.

Daga kallo sai sallah. Haka da rana Mami ma ta aiko musu da abinci.

Da dare ma haka. Bayan sunci ya kai ta daki yai mata wanka suka kara hayewa gado dan yin bacci.

Ranar ma be daga mata kafa ba, dan wahalar da tasha har tafi ta jiya duk da yaso ya daga mata kafa ko ta warke daga cikon dake jikin ta.

Amman sam ya kasa dole sai da ya kara kusantar ta.

Summy uwar raki kuwa tai tayi masa kuka.

Da kyar ya lallashita tayi shiru.



*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *119*




Sai da Summy tayi sati biyu sannan Mami ta dana aika musu da girki.

Alokacin Najib kuma yasa ta shirya dan suje gaida Mami.

Ba laifi tayi kwalliya da shiga me kyau. Inda ta saka leshi me dinkin riga da zani sai bababn mayafi da ta daura akan ta.

Da yake ta fadawa Mama zataje gaida Mamin sa.

Mami ta ce ta kai musu turare da atampa Daddy kuma ta kai masa shadda da turaruka ita ma.

Wannan yasa ta diba a leda ta zuba dan kai musu.

Najib ma ya shirya cikin manyan kaya inda ya tuko su a mota har cikin gida.

Tin daga gate ake gaishe su, amman Summy sai dauke kai take yi.

Najib be lura ba dan sam baya son wukanci.

Bangaren Baba suka fara zuwa, ya ce, mata wannan kaka ta ce.

Baba tayi murmushi, suka gaisa da Ita cikin sakin fuska.

Bangaren Mami suka nufa. Mami na zaune ita da su Bara'atu, Bara'atu na yi mata kitso.

Talle na yanke mata farce. Suna hira abin sha'awa da su.

Sallama Najib yayi kafin su shigo. Da gudu Talle ta mike tana fadin
"Ga Yaya, Ga Yaya!"

Murmushi yayi, ya ce,
"Tofa za'a cikan kunne ko?"

"Lah Yaya ni din."
Ganin Summy da tayi yasa, ta ce,
"Lah Ga Antyn mu ga Antyn mu."

Murmushin yake Summy tayi, suka shige cikin dakin.

A kasa suka zauna suka gaida Mami cikin girmamawa.

Su Bara'atu suka gaida Najib shi ma ya jasu da wasa.

Sai Summy da suka gaisar. Mikewa Talle tayi ta kawo musu lemo.

Sama Talle da Bara'atu sukayi,Mami kam ai tambayar Sumaiyya take ko da wata matsala.

Fita yayi ya barta, wannan yasa Mami ta kira mata su Bara'atu dan su taya ta hira.

Ita kuwa wai ta girme su bazata bari su raina ta ba.

Nace ai ba haka ke kawo raini ba.

Tinda suka sauko ta hade rai da yake Mami ta yi can wajen Baba.

Talle kuwa ta dibe ta, ta sata a kwandon shara.
Sai hirar makaranta da suke ita da Bara'atu.

Sai Magriba ya dawo, lokacin tana dakin Mami, dakin Mami ya sameta tana kwance akan gado.

Karasawa yayi gefen ta, kan sa ya daura akan kirjin ta.

A ranta tace,
"Wallahi Najib ka fiya jaraba."

A fili kuma, hannun ta, ga daura akan sa, tana shafa masa a hankali,
"Sannu da zuwa."

Fuskantar ta yayi, ya ce,
"Yauwah yau nayi kewar ki wallahi."

"Nima haka. Ina kaje ne?"
"Naje duba Abokina ne."

"Nazata gun yarinyar kaje ai."
Murmushi yayi ya ce,
"Kishi ko?"

Shiru tayi dan ta lura maganar yarinyar nasa shi nishadi da farin ciki.

Kofar sukaji ana tabawa alamar za'a shigo da sauri ya daga ta.

Mami ce, ta shigo, kofi ta mikawa Summy tace,
"Karbi ki shaye ku taso muje gun Dady."

"Mami ni fa?"
Hararar sa tayi.

Murmshi yayi, ya ce,
"Ni daman na sani Mami daina sona zzakiyi."

"Wai kai baza ka girma ba ko?"
Mikewa yayi, ya ce,

"Nima bari naje wajen Dady na."

Yayi waje. Sai da Summy ta shanye, sannan suka tafi dakin Dady.

Dady da fara'ar sa ya tare ta suka gaisa cikin so da kaunar sirikar tasa.

Sai da zasu tafi ta dauko kayan da ta kawo musu sosai Su Mami sukai farin ciki.

Dady ma kudi me yawa ya bata. Mami kuma ta hada mata kayan girki ta raka su har bakin kofa.

Sai karfe tara suka koma gida. Wanka ya yi mata sannan shima yayi wanka.

Summy na mamakin ganin Najib be gajiya da sakawa jikin sa Ruwa.

Ita kam har ta fara gajiya a rana ace ayi wanka sau uku sau hudu gaskiya da gajiya.

Dake Najib na gida shi ya dinga musu girki Summy kam ba abinda take yi.

Sai da yayi wata da aure sannan ya koma wajen aikin sa.

Ranar da zai koma aiki duk da ya fada mata lokacin da zai fita amman sam bata tashi ta hada masa break ba.

Haka ya tafi dan sai da ya shirya ma ya tashe ta. Kudi ya bar mata duk da yasan ba abinda zata nema.

Ko a office sai karfe daya sannan ya sha tea dan be fiya son cin abincin waje ba.

Har karfe uku yana jiran ganin kiran ta amman sam ko flashing be gani ba.

Ta kuwa tana gida tana ta bacci dan sai karfe biyu ta tashi, da kyar ta iya gyara gadon da suka kwana.

Shara kuwa cewa tayi dakunan basuyi datti ba.

Wanka ma da kyar tayi ta shirya cikin doguwar rigar material me kyau da ita.

Batayi kwalliya a fuskar ta ba.

Kitchen taje tana tunanin me zata ci. Cornflask ta hada ta sha.

Falo ta koma ta kunna kallo tana daga kwance.


Sai da yayi la'asar sannan ya kira ta. Dagawa tayi.

Shiya fara magan, da tambayar ta ya gidan.

Sam batayi kokarin jin ya wajen aikin sa ba, ko ya gajiya ba.

Haka suka gama waya ba tare da ta tambaye sa ba.

Sai magariba ya dawo gida da gajiya a tare dashi.

Tin yamma take kwance har magariba dan ko sallah ta kasa tashi tayi.

Karar shigowar motar sa tajiyo. Amman sai kara gyara kwanciyga da tayi.

Da Sallama wacce ta zame masa wajibi ya shigo dakin.

Tana daga kwancen ta amsa masa da
"Wa'alaikum salam!"

Karasawa dakin yayi, ya zauna a gefen ta. Gefen fuskar ta ya shafa ya ce,
"Ya gidan?"

"Lafiya Sannu da dawowa."
"Yauwah."

Ya fada yana yin mika dan ya gaji. Dakin ta ya mike ya shiga.

Kallon dakin yayi, da yadda aka gyara gadon kamar ba'a gyara ba ya gani.

Ban daki ya shiga shima ko wanki be gani ba.

Komai ya gyara sannan ya shiga ya gasa jikin sa da ruwan zafi ya fito yayi alwala ya tafi massalaci.

Sai isha'i ya dawo tana zaune a inda ya barta tin dawowar sa.

Zama yayi a gefen ta ya ce,
"Wash!"

Kallon sa tayi, ta ce,
"Sannu."

"Yauwah!'
Ya amsa mata da.

Daining ya kalla ya ce,
"Me kika dafa ne?"

Fuska ta marairai ce, ta ce,
"Wallahi yau bana jin dadi shiyasa banyi girki ba."

Kallon ta yayi da mamaki akan fuskae sa. Abinda be taba ganin Mami sa tayi ba.
Duk rashin lafiya sai ta samar musu abinda zasu ci.

Kawar da abin yayi ya ce,
"Me yake damun ki?"

"Wallahi tin safe nake jin zazzabi da kasala ga tashi amai da nake ji."

Kallon ta yayi ya ce, "yaushe kika fara ji  hakan"

"Yau ne."
Daukar ta yayi yakaita  har toilet yasa tayi fitsari.

Test yayi mata yana dubawa ya fara hamdala dan abin da yake tunani shine ya samu.

Kallon sa tayi, ta ce,
"Lafiya?"




*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *120*



Kallon sa tayi ta ce,
"Lafiya?"

Juyowa yayi ya rumgume ta, ya ce,
"Ki godewa Allah Sumaiyya ciki ne dake."

Ido ta zaro waje tana mamkin wai ciki ne da ita.

Kallon sa tayi, ta ce,
"Ci... me?"

"Ciki man."
Ya fada.

"Wallahi ki godewa Allah. Allah na son mu da yai mana wanann kyautar."

Fuska ta bata ta ce,
"Kai yanzu cikin nan kake so."

Kallon ta yayi ya ce,
"Ke bakya so ne.

Kan gado kawai tayi ta zauna a gefe.
karasawa yayi gefen ta.

Kallon sa tayi ta ce,
Kaga ni yanzu yunwa nake ji."

Mikewa yayi da sauri ya ce
"me kike so?"

"Shawarma zaka siyon."
Mukullin ya zara ya fita da sauri.

Tagumi ta buga aranta tana cewa daga yin aure ban huta ba sai ciki.

"Ai wallahi sai na zubar."
Ta fada a fili.

"To ai shi kuma naga yana so."
Wata zuciyar ta ce,

"Yo ke bakya so."
Tagumin ta sauke lokacin da ta tuna kawar ta, Fatisha.

Wayar ta, ta dauka ta kira ta. Dauka tayi muryar ta a cikin wani yanayi.

Summy ta ce,
"Allah shirya ki, ki daure kiyi aure. Ko ke huta da bin maza."

Fatisha najin haka ta gane Summy ce dan ita ke mata irin wannan tsiyar.

"Amarya!"
Ta fada daga can bangaren.

"Fatish ya kike?"
"Lafiya kin ci amarci. Kinji abinda muke ji ko?"

Dariya Summy tayi,
"Kinga ni tukkuna fada min maganin da kika sha da kika zubar da cikin ki."

Dariya Fatish ya bushe da ita. Ta ce,
"Me zakiyi dashi ke da kika same shi ta hanyar Allah."

"Ke dan Allah ni dai fadan. Ban gama hutawa ba sai wani ciki."

"Kuma fa haka ne, bari zan turo miki da sunan nashi."
"To nagode sai anjima."

Ta kashe wayar ta ta.

A ranta kuma tana cewa,
"Bama zan fada masa ba bare ya hanani. Dan naga alamun yana son cikin nan."

Kwanciya tayi akan gado tana jiran dawowar sa.

Sai da ya siyo mata shawarma sannan ya dawo gida.

Tana kwance ya tashe ta. Sai da yai mata wankan da bata so sannan ya saka mata kayan bacci ya zaunar da ita ya ciyar da ita.

Sai da ta koshi ya bar ta. Lalashin ta ya dinga yi.

Washe gari ma beje aiki ba shi ya zauna ya kula da ita, ya gyara musu gidan.

Ita kuwa so take ya fita ko ta samu ta fita ko ta aika me gadi.

Najib be fita ba sai da yaga jikin nata yayi kwari sannan ya koma aiki.

Ranar kuwa murna kamar me. Sunan maganin ta bawa me gadi tare da kudi ya siyo mata.

Ba bata lokaci ya kawo mata maganin.

Amsa tayi tana tunanin yadda zatayi kar ya gane tasha wani abun.

Wata dabara ce ta fado mata. Dan haka ta balli maganin  ta sha ta shiga ban daki.

Sai da ta fara jin cikin ta na juyawa sannan ta dauki waya ta kirashi murya a raunane tana fadin
"cikin ta cikin ta."

Rikicewa yayi, ya taho gida da sauri, kafin ya karaso har cikin ya zube.

Abinda take so kenan  da hanzari ya karaso ya daha ta, danshi ya ji yana dubawa yaga jiki na zuba.

"Inalilahi waina'illahir rajiun!"
yai ta nanatawa abin tausayi har da hawayen sa.

Sai da ya gyara mata jikin ta ya gyara dakin sannan ya bata magani tasha  yai mata allurar bacci dan ta samu hutu.

Zama yayi ya dafe kai. A ransa kuwa yana godewa Allah dan shine abin godiya ga duk abinda ya samu bawa.


Alhamdulilah su Najwa an gama level two, dan gashi har suna shirye shiryen zuwa kano.

Najwa sai murna take, tin asuba tayi wanka ta shirya.

Suna gama karyawa ta dauko akwatin ta. su Momy kuwa sai tsiya suke mata.

Dady da kansa ya kaisu har kano, inda Basma ta rumgume yayar ya.

Zuwan da sukai sai da Mami tasa taje duk gidan yan uwa da abokan azurki.

Inda Mamin Najib na samun labarin zuwan ta. Tasaka a kai ta tai mata kwana biyu.

Najib na office yana aiki, wayar sa tayi kara. Dubawa yayi yaga abokin sa ne.

Murmushi yayi ya ce,
"Dan uwa."

"Na'am ya kake ya Madam."
"Tana lafiya. Kasan munyi bari."

"Ya salam! Allah kawo yan biyu nan gaba."
"Ameen!"

Kasan me?"
"A'ah!"

"Khadija ita kuma ta samo maka takwara insha Allah!"
"Da gaske?"

"Eh!"
"Allah sarki. Allah sauke ta lafiya. Allah ya kare mana ita. Ai mata sannu."

"Zata ji. Yaushe zaka zo?"
"Zan je katsina a cikin satin nan daga nan zan biyo insha Allah."

"Allah kai mu."
"Ameen!"

Sukai sallama. Zaman Summy da Najib zama ne me dadi sai dai yan kalubalan da Najib yaje samu na rashin tsafta da rashin son masa girki.

Wannan abin na damun sa duk da wani lokacin sai ya koma daga aiki ga gaji sannan yayi girki.

Shi tausayin ta yake ji, bama da yaga tayi barin nan gashi itama ta damu har ta fishi damuwa ma.

Wannan yasa yake kara daga mata kafa. Amman kuma ai yanzu ta warware dan tayi wata guda dayin barin amman abun duk sai a hankali.

Yau ma ya dawo a gajiye ya zauna, ba abinda yake bukata sai abinci dan tin tean safe ne a cikin sa.

Summy ce ta fito daga daki da riga da wando a jikin ta.

Sai juya kugun ta take. Kamo ta yayi ta fado jikin sa.

Numfashi ya saka me karfi ya ce,
"Sumaiyya yunwa nake ji."

"Gashi ban yi girki ba."
Kallon ta yayi, ya ce,
"Wai menene matsar ne?"

"Tame fa?"
Ta tambaye shi.

Fuska ya bata ya kalle ta.
"Dan Allah haka Mama takewa Abban ki. In ya dawo daga aiki ba abinci."

"Tab Maman. A'ah Mama sai tayiwa Abba girki wajen kala biyar ma."

Murmushi yayi, ya ce,
"Me yasa bakya min."

"Wallahi aiki gidan nan kemin yawa shiyasa. Yauwah daman nace dan Allah kasa a kawon yan aiki mana."

Wani kallo ya wurga mata, wanda sai da ta tsorata.
"Meye aikin ki da baza ki iya ba sai an kawo miki yar aiki. In zaki mike kiyi ki mike in ba haka ba zan gyara miki zama."

Mikar da ita yayi, ya ce,
"Kije ki dafa min abinci dan yunwa nake ji."

Tinda take da Najib wajen wata uku bata taba ganin bacin ran sa ba sai yau.

Da sauri ta

Please Login or Register in order to submit comment