Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da tarbiyya, yana son macen da ta iya girki. Kuma duk nasa,n bamu da matsala ta gun insha Alalhu."

Kai ta gyada. A ranta kuwa cewa take,
"Girki dai da sauki, tsafta kuma ai baza arasa masu aiki ba."

A fili kuwa sai murmushi da take yi.
Kallon ta Khaleel yayi, ya ce,
"Toh Sumaiyya gashi inji abokina ya ce, kiyi hakuri ba yawa."

Shiru tayi, sannan tace,
"Har da wahala, toh nagode."

Murmushi yayi sannan ya mike,
"To ni zan tafi, sai munyi waya."

"To shikenan nagode ka gaishe shi."
"Zai ji, zai ma kira ki."

Suka fito sai da ta kai shi har jikin motar sa sanna ta juyo.

Gida ta shige aran ta kuma tana tunanin Najib da tsare tsaren sa, da irin halaiyar sa me kyau da burgewa.

Dakin ta, ta shige, ta zazzage kayan rafar yan dubu daya ne suka fado. Dauka tayi tana murna.

Kayan ciki ta dinga dagawa, duk kaya ne masu kyau da tsada.

Cikin leda ta mayar sannan tayi dakin Mama.

"Mama! Mama! kinga kayan da aka kawon."
Ta fada yana juye su akan gado.

Kallo Mama ta bita dashi, tana daga kayan, sannan ta ce,
"Kuma kika karba."

"Mama to yabani me zan ce."
"Ke baki da hankalin ce masa ya bar su,in kuna bashi zaki aura ba, daga haduwar ku."

Marairai cewa Summy tayi, ta ce,
"Kiyi hakuri Mama zan mayar musu."

"Ai kin riga kin karba. Dan Allah Sumaiyya ki rage son abin duniya kina boye kwadayi ki akan abin mutane."

"Ki yi hakuri Mama bazan kara ba, Yanzun ma ban so karba ba."
"Shikenan Amman kin ji dai abinda na fada ko?"

"Eh Mama."
"Tashi kije, ki ajiye kayan kada a dinka."

"To!"
Ta fada tana debe kayan ta fita daga daki.

A dakin ta kuma mita take wai Mama bata waye ba. Abata abu amman wai baza ta dinka ba. Kuma ta maida hannun kyauta baya.

Tsaki tayi sanna ta debe kayan ta saka a cikin durowar ta. Kudin kuma ta saka su a cikin jaka, idan anjima zata tasaka a account din ta.

Wayar ta, ta dauka ta fara duba hotu nan sa, kalla take tana murmushi.

Da haka bacci ya dauke ta, wanda duk mafarken Najib ta dinga yi.


Najib kuwa suna suka har drivern su yazo yana jiran su.

Motar suka shige sai gida. Suna zuwa gida ya hau hada kayan sa, da yamma zasu tashi

Suna zuwa gida masu aikin sai murnar dawo war Mami suke. Dan ba karamin kewar su sukayi ba na kwana biyun nan da basa nan ba.

Baba kuwa sai nan nan take dasu Najib da Mami ko da taji tafiya zai kara yi, sai taji ba dadi. Amman dayake abin karin nasara ne sai ta taya shi da addu'a.

Daga wajen Baba daki ya tafi, Yana hada kayan sa, yana gamawa ya fice ya tafi asibitin sa, abubuwan da zai amfani dasu ya kwaso ya koma gida

Yana komawa yayi wanka, yayi sallah yaci abinci. Zama sukai a falo suna hira da Mami, mami na kara masa fada da ya ji tsoron Allah a duk inda yake. Ka.

"Najib kaji tsoron Allah a duk inda kake, ka sani duk abinda kake Allah na ganin ka, ka ji tsoron sa kaji tsoron haduwar ka dashi. Kai kaga bama nan kayi abinda ba dai dai ba. Ka tsare imanin ka. Kayi riko da addinin ka."

"Mami insha Allahu bazan taba aikata abinda ya haranta ko ya sabawa addini na ba. Mami amman sai kun cigaba da min addu'a akan Allah ya tsare ni dan ba wayo na ko dabara ta ne zai sa hakan ba."

"Ba komai Najib addu'a kullum muna yi, dan Addu'ar iyaye ga ya'ya ba karamar aba bace, kasan Allah yace addu'oi biyu idan har mutum yayi ba a juyar masa dasu, da addu'ar iyaye ga 'ya'yan, da addu'ar wanda aka zalumta."
Kaga kuwa dole mu dage wajen nema muka Lahira me kyau. Dan in har kaji tsorn Allah to komai ya dai dai ta."

"Nagode Mami! Allah ya saka musu da gidan Aljanna."
"Ameen Najib."

Karfe biyar suka daga, yana me kewar barin Mamin sa.

Wanda tafiyar in da bata zama dole ba bazai je ba. To wani course zai kara karantowa na wata biyar, wannan yasa dole sai ya tafi ya bar Mamin sa.

Dan Mami ita ta samo masa karatun tayi masa komai akai.

*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHODA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *114*


Summy kuwa tana can tana zuba ido taga kiran sa amman shiru kake ji.

Bayan kwana biyu ta shirya ta tafi gidan amarya Hauwa.

Hauwa ba karamin jin dadin zuwan ta tayi ba.

Nan ta tare ta da kayan motsa baki da abincicika.

Summy kuwa wannan abin ba karamin burgeta yayi ba, hakan ya kara mata kwadayin auren mutum me kudi.

Sun sha hira, inda anan take bata labarin Najib da yadda suke ciki.

Hauwa ta jinjina kawai wai da Najib yace yana son Summy dan tasan halin sa sosai.

"Summy Kuma Najib din ne yace yana sonki."
Ta fada cikin mamaki.

"Eh shine, menene?"
Summy ta fada.

"A'ah babu komai. Summy in kika samu Najin kin huta, amma ina mamakin yadda ya ce yana son ki bayan shi baya kula yan mata."

"Haka ne Hauwa, Khaleel ya fadan komai, yanzun ma ya kasa sakewa dani sosai."

"Sai kinyi hakuri, sannnan sai kin canja hali da Najib akwai shi da son girki da tsabta."

Hararar Hauwa tayi ta ce,
"Ni ban da su ko?"

"A'ah nufina ki kara dagewa kisan wanda zaki aura. Dan nason ki da son jiki."

Haka suka dinga hira Hauwa na yiwa Summy nasiha.

kafin magariba ta mike ta ce zata tafi. Ba karamin mamaki abin ya bawa Hauwa ba dan tasan kawar ta,, bata fita in ba dare ba dan tana cewa da dare anfi yin babbar harka.

"Kallon fa?"
Summy ta tambayi Hauwa

Murmushi hauwa tayi ta ce,
"Summy kin canja fa."

Dariya Sumaiyya tayi ta ce,
"Dame fa?"

"Da na san ki da son fitar dare saboda ki samu saurayi, kuma kin fi jin ddi a lokacin amman yanzu kince zaki tafi ko da inda zaki biya ne."

Murmushi Summy tayi ta girgiza kai. Ta ce,
"Hauwa wallahi aure nake bukata ne yanzu, kuma na samu a hannu me zan tsaya kulawa a mayaudaran mazan nan. Yan sukai su baro ka."

Baki Hauwa ta saka tana kallon Summaiya cike da mamaki. Yadda take fado wadan nan magan ganun.

"Kuma yanzu Mama tana fadan kaiwa dare."
Sumaiyya ta fada.

"Gaskiya ne gara mubi iyayen mu, dan in sukace A'ah, ka 'kiji to zakayi gamu da ba dai dai ba."

"Wallahi kuwa!'
Sumaiyya ta fada tana mikewa."

"Ina zuwa."
Hauwa ta fada tana shiga dakin baccin su.

Minti kadannta fito rike da leda a hannun ta, hannu Sumaiyya ta kamo tana damka mata, tare da jan ta waje.

Drivern gidan ta kira dan ya mika Sumaiyya gida.

Godiya Sumaiyya tayi mata sanna sukai sallama ta shiga mota yaja suka tafi.


Kamar ko da yaushe Mami ce zaune sai Najwa da Basma dake gefen ta.

Duk lokacin dasu Najwa suke zauna da Mami mami bata barin lokacin ya kare a banza.

Sai ta san tambayoyin da tayi musu dan daduwar su. yanzu ma haka ce ta faru.

Najwa ta kalla ta ce,
"Najwa, kiyi min bayani game da sallah baki dayan ta da farillan ta mustahabai da sauran su"

"To Mami
FARILLAN SALLAH sun kasu ne gida 2:
1. Sharuddan Sallah
2. Rukunan Sallah

Kuma akwai bambanci tsakanin Sharadi da kuma Rukuni. Sharadi ana samunsane kafin a shiga cikin ibada, shi kuma Rukuni ana samunsane a cikin ibadar, kuma dole sai kowanne yasamu sannan ibada take cika.

SHARUDDAN SALLAH
1. Muslunci
2. Hankali
3. Balaga
4. Tsarkin kari
5. Tsarkin dauda
6. Shigowar lokacin sallah
7. Suturce al-aura
8. Fuskantar alqibla.

Kuma gabadayan Malamai sun yi IJAMA'I akansu, sai dai Malamai sun yi sabani akan cewa shin NIYYA da KABBARAR-HARAMA su ma sharadi ne ko kuma ba SHARADI ba ne?

RUKUNAN SALLAH
1.Tsayuwa
2. Ruku'i
3. Sujjada
4. Zaman karshe.
5. Daidaituwa acikin Ruku'i
6. Zaman da'akeyi tsakanin sujjada guda 2
7. Tahiyar karshe
8. Salati ga Annabi(ﷺ)
9. Sallama.

*FARILLAN SALLAH*
1. Niyya
2. Kabbarar harama
3. Tsayuwa dominta
4. Karatun fatiha
5. Tsayuwa dominsa
6. Ruku'i
7. Dagowa daga ruku'i
8. Sujjada
9. Dagowa daga sujjada
10. Jeranta tsakanin farillai
11. Nutsuwa
12. Daidaituwa
13. Sallama
14. Zaman karshe wanda za'ayi sallama acikinsa
15. Kulla niyyar koyi da liman,*

*SUNNONIN SALLAH*
1. Karatun Sura
2. Boye karatu
3. Bayyana karatu
4. Kowacce kabbara in banda ta farko
5. Sami'Allahu liman hamidahu
6. Zaman tahiya na farko
7. Karin addu'a a zaman tahiya na 2
8. Sanya sutura a gaban mai sallah

Saidai kuma Malamai sun yi sabani dangane da zaman tahiya, akwai Malaman da suka ce zaman tahiya dukansa farilla ne, to amma mafi rinjayen Malamai sun tafi ne akan cewa zaman tahiya na farko SUNNA NE, amma zama na biyu FARILLA NE.

*ABUBUWAN DAKE BATA SALLAH*
1. Rashin yin niyya
2. Yin dariya a cikin Sallah
3. Wasa mai yawa a.

"Masha Allah! Najwa nasan kin sani. Sai dai ina son na kara gwada basirar ki. Bama yanzu da kike daukar kananun yara karatu ya kamata kina sanar dasu dukan wadan nan."

"Mami Nagode, dan wani abun da kin tambayen anan na baki amsa, sai kiga washe gari an min tambaya, ina jin dadin gwajin da kike min. Dan in ban san abu ba kina dada tada ni."

"Ba komai *Najwah* kema ina son ki kula da ilimin ya'yan ki bama na addini dan neman dace duniya da lahira."

"Insha Allahu Mami."
"Yauwah Dadyn ki ya ce, jibi zakije Abuja da kin dawo sai tafiya."

Kai tayi kasa da shi, Ta ce,
"Allah ya kai mu."

"Ameen!"




*INDABAWA*

NAJWA*

🌐 *HAJOW* 🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE. *115*


Najib kuwa wayar sa ma a gida ya manta ta bare har ya kira Summy, Number Momy kawai ya rike sai ta Khaleel.

To amman bazai kira Khaleel yanzu ba dan yasan zai kawo masa maganar Summy shi kuma baya so.

Yana sauka ya turawa Mami ya sauka lafiya yanzu haka yana ta harka akan abinda yaje yi.

Fatan Alkhairi Mami ta kuma yi masa tare da kara fada masa yaji tsoron Allah.

Summy kam kullum Khaleel zai kira haka nan zai turo mata da kati. Amman ita tafi son taga Najib ya kira ta

Duk harkar shirmen ta, ta daina, sai dai halin ta na son jiki da rashin son gyara da har yanzu yake nan.

Samari kuwa duk ta watsar dasu. Yanzu kawai jiran kiran Najib take da dawo war sa ayi abinda za'ayi.



Dady da kansa ya kai Najwa Har Abuja lokacin Dadyn Najib ya dawo bai kwana ba a ranar ya juya da yake tafiyar jirgi ce.

Su Mami kuwa ba karamin murnar zuwan ta sukai ba, Mami sai nan nan take da ita.

Daki dake kusa v
danata ta kai ta, sannan ta kai mata abinci da kanta.

Wanka tasa tayo sannan ta kwanta dan ta huta.

Kwanciya kawai tayi dan ta kasa baccin ma.

Zaman da Najwa tayi a Abuja sosai ta huta dan sam ba abinda take yi.

Kullun Mami ta dauke ta, ta kai ya yawo ko shopping ahaka tayi har tayi sati biyu sanna ta fara shirin komawa.

Kullum sai sunyi waya da Najib, lokacin da tafiyar ta tazo sosai Mami ta hada mata kaya banda na kwalliya ga sutura.

Dady da Mami da kan su suka kai ta kano. a gida kuwa sai kewar ta ake yi bama Basma.

Dawowar ta da sati biyu ta daga katsina, gidan Anty Hauwa kanwar Mamin ta.

A can ma sai murna zuwan ta ake bama Zahra. Daki daya aka bata wanda aka zuba mata komai a ciki.

Komai an gama musu dan karatu kawai suka fara. Kullum a kai su a dauko su.

A haka har suka yi rabi a semister karatun su. Kullum sai sunyi waya da gida da Hamma Salim.

Sai da lokacin Jarabawa yazo sannan suka koma hostel da zama. A hostel din ma Kullum sai momy ta aika musu da abinci.

A haka har suka kammala first semestern su. A katsina tayi zaman ta. Dan Mami ta ce kada tana yawan zirga zirga akan titi.

Duk wata sai Mami ta aiko musu da dinki da fashion ta ce ana zuwa makaranta dasu. Haka duk wata Abban mahaifin Zahra sai ya basu kudi sun shiga kaswani da store kowa yayi siyayyar abinda yake so.

Haka nan Dadyn Najwa shima duk wata zai turawa Zahar da Najwa kudi a account din su.

Najwa najin dadin zaman ta a katsina kowa son ta yake.


Najib sai da yayi wata biyu be kira abokin sa ba shima duk dan kada ya kawo masa maganar Sumaiyya ne.

Ganin bazai iya jure rashin kiran abokin nasa va yasa, ya dauki waya ya kira shi.

Gaisawa sukayi kamar ba komai, Najib ne ya ce,
"Bro daman number Summy nake son ka turo min."

Wata dariyar rainin hankali Khaleel yayi, ya ce,
"Wacce haka?"

"Dan Allah kayi hakuri wallahi abubjwa ne sukai min yawa kuma na manto wayata a gida shi yasa ko Mami da kyar na tuno number ta yanzu haka ma ita ta turon taka."

Murmushi me sauti Khaleel yayi ya ce.
"Ka daina karya ba halin ka bane. ba komai zan turo maka ita yanzu kasan yadda zaka ce mata "

"A'ah dan Allah kada kayi min haka. Ka dan tsara ta yadda zata yadda da abinda zan ce mata."
"Oho maka ni ba ruwana."
Ya katse kiran.

Number ya tura masa yana dariya. Yana tura masa ya kashe wayar gaba daya dan yasan in ba haka yayi ba bazai barshi ba. Sai ya dame shi da ya kira Sumaiyyan shima.

Nan kuwa besan ya riga ya fada mata ceewa Najib ya manta wayar sa shiyasa ko gida be nema va. Amman da ya kira gida yasan zai neme shi ya bashi number ta.

Wanann yasa sam hankalin ta be tashi ba akan rashin kiran da be mata ba.

Amman kwana biyun nan Maman ta, ta matsa kan ta fito da miji abinda ya fara damun ta kenan.

Gashi yanzu ba wanda take kulawa duk ta zubar da samarin ta ganin ta samu Najib.

Kwance take tana tunanin sa, taji karar wayar ta. Dauka tayi jiki a sanyaye.

Sabuwar number ta gani kuma bata kasar ba. Bata kawo shine ba dan haka ta kara a kunne ta. Tare da cewa
"Hello."

Tsaki yayi a cikin ransa dan shi ya tsani wannan dabi'ar ta hello kafin kayi sallama.

Sallama yayi mata cikin muryar sa me dadi.

Mikewa taayi daga kwancen da take da sauri. Dan sau dayan da taji muryar sa ko ina ne baza ta taba mantawa da muryar ba.

Muryar da ita kadai ma gizo take mata. Nutsuwar ta, ta dai dai ta, ta amsa masa da
"Wa'alaikum salam "

Shiru sukayi gaba dayan su. Ita ce tayi karfin fara magana da gaishe shi.

Amsa mata yayi, rasa abin fadi yayi. Da kyar ya daure ya ce,
"Kinji ni shiru ko?"

"Lah ba komai ai, Khaleel ya fada min ka manta wayar ka ne. Ya kake ya aikin?"

"Lafiya lou Alhamdulilah "
"Masha Allah daman kira nayi mu gaisa zan kira anjima."

Ya katse wayar. Wayar yabi da kallo yana mamakin wai shine yake magana da wata a nufin saurayin ta

To ya zaiyi auren shine kadai samun saukin sa. Dole yayi tinda Allah yasa be ga wacce yake so din ba.

Summy kuwa dadi kashe ta murnar da take ciki sam baza ta musaltu ba.

Ta rasa wane irin farin ciki zatayi da ya kirata.



Cikin ikon Allah har su Najwah sun shiga level two karatun su Alhamdulilah basu da matsalar komai dan karatun suke sosai.

Kuma result din su me kyau ne. Tin zuwan Najwa katsina bata taba zuwa gida ba.

Amman wannan karan Momy ta ce zasu tafi ita da Zahrah.

Murna gun Najwa bazata misalti ba dan tana son zuwa gida

Lokacin da Hamma Salim yayi graduation duk yan gida sunje amman ita karatu ya hana ta zuwam.

Hamma Salim da kansa yaje har katsina yayi mata kwana ki sannan ya koma gida ba karamin jin dadin zuwan sa tayi ba.

Ko a makaranta su Najwa abin sha'awa ne sam basu da kawaye sai dai classmate da suke yin zumunci a karatu.

Saurayi kuwa sam basa kulawa bama Najwa da an mata magana zata ce tana da mijin.

Gara ita Zahra tana da wanda zata aura ma dan gidan abokin baban ta ne


*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *116*

Momy har tayi fadan amman Sam Najwa bata iya tsayawa da kowa.

Mutum daya ne ya na ce mata shine dan gidan kawar Momy duk rashin kulawar da take masa amman sam shi ya kasa hakura da ita.

Tin da ta bashi hakuri tare da hada shi da Allah akan ya tabu da ita yaki. Yasa ko ya zo bata zuwa bare ya ganta.



Ba laifi yana dan kiran ta su gaisa ya tambayi su Mama daga haka ba abinda yake daduwa.

Haka nan duk wata yana aikiwa Khaleel da kudi tayi amfani dasu.

Mama ceta, ta kurawa Sumaiyya kan ta fito da miji wannan yasa ta fadawa Khaleel dan ita yana jin nauyin Najib.

Khaleel ya kira Najib ya fada masa komai. Ba komai ya ce masa akan zai fadawa Dadyn sa ayi komai da an dawo ayi bikin.

Ba karamin dadi Khaleel yaji ba inda suka shirya zasu bikin su gaba daya.

Dady Najib ya fara ya fada masa, komai Dady yayi ji dadi da farin ciki bama Mami da ta fara hada lefe tin lokacin da ta samu labari.

Kafin ya dawo aka saka rana wata biyar. inda da ya dawo za'a sha shagalin biki.

Aiki aka dauke shi a can na shekara abinda ya hanashi dawowa kenan.

Najib yana can duk abinda ya gani na mata sai ya siyo ba Sumaiyya yake siyowa ba. Illa Yarinyar da ta zame masa jinin jikin sa. Yarinyar da be san ta ba. Sai gani sau biyu da yayi mata.

Cikin ikon Allah har ya kammala abinda ya kai ya fara shirye shiryen dawowa.

Mami ba karamin murnar dawowar sa tayi ba  dan ya kara kyau da girma ya zama cikaken namiji me kamala

Ranar da ya dawo ranar aka kai lefen sa gida Su summy. Summy kuwa murna kamar tayi me.

Khaleel yazo suka shirya abubuwan da za'a yi dan sati biyu aka saka za'ayi bikin sa.

Kati suke kaiwa wanna yasa ba zama tinda ya dawo dan ma abokan nasu daya ne

Wannan yasa suka raba wanan yayi can wancan yayi can.

Katsina ya tafi dan kaiwa abokin mahaifinsa, kati wato mahaifin Zahra.

Yaje lafiya inda Momy ta tarbe shi hannu bibiyu, ya ci ya sha. Duk yadda suka so ya kwana ki yayi. Dan ya ce akwai inada zai je a ranar ma.

Sallama yayi musu ya fita, gidan wani abokinsa ya nufa dan kai masa kati tare da yi wa matar sa barka ta haihu.

Har ya nufi hayar gidan ya tuna be siyo musu komai ha. Wanna yasa ya juyar da motar sa ya nufi. Green House dan siyawa Baby kaya.

Yau Dady ya basu kudi wannan yasa tin safe da suka fita har yamma basu dawo ba dan daga kasuwa suka tafi Can green house dan siyar wasu kaya da zasuyi.

Sun gama siyayar su sun fito, suna cikin mota za'a tayar kenan ya karaso gun a motar  sa.

Ajiye motar sa yayi ya fito ya nufi cikin wajen kiran sa akayi yana juyawa yaga wani abokin sa da sukayi karatu tare komawa yayi suna gaisawa kamar ance ya kalli gefen sa ya hango ta a cikin mota kallon ta ya tsaya yi dan ya tabbatar  da ko ita ce.

ido ya mutsuke ya kara kallon su lokacin da suka hau kan titi. Kafin yayi wani yunkuri har sun bacewa ganin sa.

Dafa shi abokin nasa yayi ya ce
"Tafiya?"

Kai ya gyada ya ce,
"Wallahi wata yarinya da nake nema ce ta kuma har sun tafi."

"Ko dai da ita za ayi ne."
Murmushi yayi ya bude motar sa ya dauko masa kati ga katin bikina nan.

Sukai sallama ya shiga yayi siyayyar da zai yi ya fito.

Ya dade yana mamaki dan yana tunanin ko idon sa ne amman me zai kawo yarinyar nan garin.

Da wannan ne ya samu hankalin sa ya dan kwanta.

Dan sai ya dinga tunanin ko gizo idon sa ke masa.

Amman yagi alkawarin zai zi ya neme ta.

A ranar ya wuce kano be koma abuja ba har aka daura aure.
Mami taso Najwa  tazo amman lokacin sun fara jarabawar second semester wannan yasa duk yan uwa sai tambayar ta suke. Duk da daman bata saba shiga cikin su ba.

Basuyi wani event ba sai a Abuja da suka hada dinner.

Summy ko kukan barin gida ha tayi ba.

Tin karfe biyu suka tafi kai amarya, inda da magariba aka tafi yin dinner.

Zan iya cewa tin da ya dawo sau daya suka hadu sai ranar dinner Khaleel.

Amman Summy bata kawo komai a ranta ba. Shi kuwa duk abin nan hankalin sa ya tafi kan Yarinyar da yake yawan gani.

Gidan Najib katon guda ne wanda masu ginin ma daga waje aka dauko su.

Gida ne wanda ya tsari dashi abin sha'awa.

An zuba wa summy kayan alfarma da kyau a bangaren ta.

Bangaren sa kuwa shi ya zuba duk abinda yake bukata sai dayan site din da yake a rufe.

Dakin bacci uku ne sai falo guda biyu da kitchen da ban daki a bangaren summy.

An shirya mata wajen nata sosai. Inda daga gun dinner aka kai ta dakin ta.

Tare da yan uwan ta suka kwana dan sai gobe zasu tafi.

Wasje gari da safe Mami ta aika musu da abincin da tayo musu ba abinda ba a aiko musu ba.

Haka nan duk wanda yazo sai da aka bashi kudi da turnin atamfa  banda kayan rabo na biki da aka hada musu.

Suna gamawa suka fara shirin tafiya. Inda Mamin Najwa da ta kwana a gida mami tazo ta yiwa Summy fada kan ta kula da mijin ta.

Yan uwan ta duk suka tafi, Mami ce ta aika mata da Bara'atu da Talle dan su tayata zama kafin anjima Najib ya tafi.

Tunda mutanen da suka kawo ta suka tafi ba abinda tayi ko dan karkade karkaden nan batayi ba.

Sai kwanciyya ma da tayi, ko da su Talle su kaje gidan duk sallamar da  suke bata amsa musu ba saboda baccin da take yi.

Gidan suka kara share mata tare da goge shi tas suka turareshi sai tashin kamshi yake.

Abincun ranar da Mami ta basu su kawo suka jere mata a dining sannab suka zauna suna kallo.

Sam bazaka taba kallon su kace masu aiki bane dan kyawawa ne ga tsafta ga ado. dan Mami duk wata sai ta kaisu siyayya tare da kaisu gyaran kai.

Wannan ya kara dada fito musu da kyan su. In ka kalle su sai ka  zaci ya'yan wani attajiri ne.

Ga makaranta da suke yanzu haka suna SS2 makarantar da suke ita kanta sai ya'yan wane da wane.

Najib shi ya sa su dan yanajin yaran kamar kannen sa dan yana son kakarsu ya dauke ta kamar kakarsa.

Ya horar da yara da tsafta kamar yadda Mami ta horar dashi.

Haka nan ya koya musu jan aji da nutsuwa dan ya tsani mutumin da be da nutsuwa.

Duk abinda ya daura su akai sun dauke wannan yasa suke burge su

Samari dayawa na kawo musu hari,  amman sam basa kula su. Dan ko a abokan Najib din ma akwai masu son su da yawa.

Sai da yace su bari su gama secondary tukunna.


*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *117*


Summy bata tashi ba sai la'asar alwala tayi, tayi sallah azahar da la'asar, falo ta fito.

Ganin dakin tayi tsaf da shi ga kamshi dake tashi.

Murmushi tayi ta kare masa kallo, daining ta nufa inda taga an jere kulolon abinci.

Can ta nufa ta zauna ta ci ta koshi sannan ta mike tayi falon babbn falo.

Ba ta dauke kayan da taci abinci ba.
Kallon mamaki nake mata dan ban taba ganin amarya haka ba.

Ace ki tashi daga bacci baki gyara wajen da kika kwanta ba bare sake wanka ki fito haka.

Sannan kizo kici abinci, ki tashi kibar wajen ba gyara.


Wani kamshi taji yana tashi na daban falon tayi ta zauna tana yin kallo.

Motsi take jiyowa a kitchen tare  da kamshi girki.

Mikewa tayi ta nufi kitchen din. Yan mata ta gani suna girki kallon su ta tsaya yi.

Su kuwa da suna can aiki kuma ba sallama tayi ba yasa bama su san da zuwan ta ba.

Aikin su suke suna hira abin sha'awa dasu.

Bara'atu ce ta juyo, Kallon Summy tayi, ta ce,
"Ina yini Antyn mu?"

Baki ta ya mutsa ta ce,
"Lafiya!"

Ta juya zata fita. Kallon ta talle tayi ita ma ta tabe baki ta saki tsaki.

Juyowa Summy tayi ta kalle ta, kallon ta itama tayi ido cikin ido ta tsame hannun ta daga aikin da take.

"Bara'atu in kingama ki fito mu tafi ina waje."
Talle ta fada mata.

Kallon ta Bara'atu tayi, ta ce,
"Bafa mu gama ba."

Ko kallon ta batayi ba, tayi hanyar waje tana tambayar

Please Login or Register in order to submit comment