Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata akan a rmabun yasan daga shi har ita baza suji da dadi ba.

Wayar sa ya dauka ya kira ta. Sai da ta kusan tsinkewa ta daga.

"Me kike yi?"
"Ba komai."

"Aah Najwa ban sanki da karya ba."
"Hamma dan Allah ka bari."

"Me zan bari me nayi?"
"Ni zaka bari, kuma ka daina damuwa da halin da nake ciki."

"Tayaya zan barki, bayan kina kuma ko bamuyi aure ba dole muna tare. Tayaya ma kike son na daina damuwa dake. Dan ke zaki iya shine kike son nima na daina...."

"A'ah haba Hamma amman kasan nima na  damu dakai da duk lamuran ka, kasan dai ina son ka ko?"

"Anya? Gaskiya ban tabbatar ba tinda kike neman sani a wani hali."

Kuka ta fashe masa dashi ta ce,
"Basan ya zanyi ba. Ni wallahi ban sani ba."

"In fada miki abinda za kiyi."
"Eh!"

Ta fada da sauri.
"Kicire damuwa aran ki, ki bar ni na saka miki farin ciki a rayuwar ki. Ki bar komai a hannu na."

"Hamma..."
Katse ta yayi ya ce,
"Bana son jin komai. Kije ki kwanta sai da safe."

Ya kashe wayar, kasa kukan ma tayi, ta rasa me yake mata dadi da tunanin da zatayi.

Ji take kamar bata da damuwa, to amman bata san me zaije ya dawo ba.

Har ta dau wayar ta tayi dailing number Zahra sai ta tuna da dare nefa gashi tana tare da mijin ta.

Kashe wayar tayi ta kwanta. Lokaci kan kani bacci ya dauke ta.

Tin Asuba Zahra ta kirata da taga kiran sa.

Dagawa tayi ta ce, ya bari anjima sayi magana.


Summy kuwa ana can an koma gun bukan su, gwarin gwiwa ya kara basu.

A wajen bokan ta jiyo labarin barin kasar da zai yi  da an daura auren.

Wannan yasa ta shirya tayi gidan Mamin Najib da kukan ta.

Mami tayi mamakin ganin ta dan zata ce Sumaiyya befi sau biyu taje gidan ta ba.

A auren da yafi shekara uku. Mami ta amsheta hannu bibiyu sannan ta tambaye ta gida.

Anan ne ta fadhe da kuka. Mami kallan ta tayi hankali a tadhe ta ce,

"Kafiya Sumaiyya, ki kwantar da hankalin, ki fadan duk abinda ke damun ki ni kuma nai miki alkawarin taimaka miki."

Hawayen gulmar ta share ta ce,
"Mami daman Najib ne, yanzu wulakanta ni yake dan zaiyi aure, kina gani shekara nawa dashi yana fice fice sauran kasashen amman be taba zuwa dani ba. Amman ynx tin kan yayi auren yace min da matar zai tafi. Mami yanxu an min adalci kenan."

Kai Mami ta jinjina gaskiya tasan ba ai mata adalci ba.

"Kiyi hakuri, kar ki damu dake zeje ba inda zai tafi da amaryar tasa. Ki kara hakuri akan wulakancin da yake miki kinji."

"To Mami nagode, bari na tafi."
ta mike sukai sallama tayi waje.

Su Talle ta hadu dasu a compound din gidan suna ganin ta suka tuntsire da dariya.

Kallon su tayi, tai kwafa tayi wajen motar ta ta shiga ta fice daga gdn a guje.

A ranta tana murna da abinda Mami ta fada.

Wannan abin ya dan kara kwantar mata da hankali da abinda Anty ta tayi, kuma ta aikata.

Zahra kuwa hankalin ta duk ya tashi game da Najwa.

Wajen karfe bakwai bayan ta gama shirya mijin ta ya tafi aiki ta kira ta.

"Najwa lafiya kuwa?"
"Zahra ina fa lafiya."

"Innalilahi wainna ilahir rajiun! Me ya faru?"
Kuka Najwa ta fashe da shi ta ce,

"Zahra, Najib ashe  mijin Sumaiyya ne."
"Wacce Sumaiyyan."

"Sumaiyya dai da kika sani, 'yar Mama "
"To shine me?"

"Au wai kema haka zakice. Haba Zahra kinsan fa wace Sunaiyya ko?"

"Na sani, amman kuma mene a ciki. Kina son shi yana sonki, to menene da ita zaki zauna ko, kuwa itace mijin ki. K bansan irin halin ki ba. Da kika ce ba lafiya na zata wani abu ne ashe akan Sumaiyya ne. To nidai shawara zan baki in har iyayen ki na son auren nan kuma shima Najib din yana kan bakan shi kada ki soma cewa bakya yi. Wallahi Najwa kika bar Najib da kyar zaki samu wani namijin irin sa. Kinsa dai Najin kinsan halayen sa to ki rike abin ki gam kada ki sake kiyi wasa da damar ki."

"Zahra....."
sauri katse ta zahra tayi, ta ce,
"Kinga Najwa, kefa ba yarinya bace, akan me ma kina son abu dan wani ki bar shi, bayan auren ku ba haramta yayi ba. Kinsan adadin mutanen dake fatan auren nan kuwa. Kinsa farin cikin mutane nawa kuka kara a dalilin auren na. Najwa ki tsaya kiyi karatun ta nutsu kisan abinda kike so. Kina son sa to in kin rabu dashi ya zakiyi. Kinsan kuwa illar kana son abu ka bar shi, komai zai iya faruwa daku na dadi da akasin haka. Wai kinsan ma tin yaushe Najib ke son ki. To bazan fada miki ba amman ki same shi ki tambaye shi  Najib masoyin ki tin kafin yasan ki ko wani abu naki. Najib ya cancanci so daga gareki."

Murya ta sasauta ta ce,
"Kiyi hakuri Najwa duk dan samun farin cikin ki ne, ina son ki ina son farin cikin da kwanciyyar hankalin dan Allah ki kwantar da hankalin ki, ki bashi goyon baya ayi komai a gama."

"Nagode Zahra,"
"Ba godiya a tsakanin mu."

Murmushi tayi. Sukai sallama.

Tana gama waya sai ga kiran Najib nan.

Tana dagawa ya ce,
"Zahra ya kike ya gida."

"Lafiya lou."
"Zahra kinji abinda Najwa zatai mana ko? Najwa sam ta juyan baya, dan Allah ki mata magana."

"Kar ka damu, wallahi yanzu muka gama waya kuma na mata fada da nasiha insha Allahu komai zai dai dai ta."

"Toh Zahra Nagode Nagode."
"Ba konai Hamam ai yiwa kai ne. Nida nasan komai ai ba zan yadda ta bar ka ba. Kaima ya kamata tasan duk wahalar da ka sha aka ta."

"Ba komai. Nagode."
Sukai sallama ta kashw wayar

Najwa kuwa ranar ko falo bata fito, sai dai Mami ta kai mata abinci da magani, daga kwanciya sai kwanciya.

Najib ma be neme tta ba dan ya bar ta ta gama tunanin ta ne.


*INDABAWA*

*NAJWA*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online WRITERS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH DAUKAKAKI YASA KI GAMA DA DUNIYA LAFIYA.*

*REALLY LOVE U ANTY NA*

*THANKS FOR UR LOVE ND SUPPORTING*


*PAGE*
*143*

*Maryam Yusuf* Tnc for ur supporting really love u.*

*Ure so special to me. Tnc for ur care.*


Kwansa uku a kano yaso ya kuma dan yanzu bikin sauran kwana goma sha daya.

A daki ya same ta tana kwance kamar yadda ya zame mata jiki a kwana biyun na.

"Amarya ta."
Ya fada yana leka fuskar ta.

Mikewa tayi zaune, kanta a kasa.
"Ina yini?"

Ta gaida shi,
"Lafiya lou. Ya jikin?"

"Lafiya. Baby na gobe zan tafi kinga abun sai karatowa yake, ya zancen abubuwan da za'ayi. Ko da yake, ga kati nan, komai da abubuwan da za ayi suna jiki."

Ya mika mata wani karamin akwati. Amsa tayi ta ajiye a gefe.

Fuska ya bata ya ce,
Haba Baby na, dauko ki gani man."

Daukowa tayi ta bude kati nan ne wajen kala hudu ko wanne a wajen sa a ajiye, na dauri  auren ya ban banta da sauran dan ya fisu girma, fari ne an masa rubutu da ruwan omon. Za ayi daurin aure a sharada gdn Baffah, ranar lahadi.
Sai na yinin su ranar asabar, sai dinner Ranar juma'a,
Sai budar kai, ranar Alhamis kamu kuma ranar laraba.

Kallon sa tayi, ta ce,
"Hamma abubuwan sunyi waya fa."

"A gun ki ba da bakya son auren."
"Hamma ba haka bane."

"To yaya ne?"
Ya katse ta.

"Yi hakuri."
"Baki min komai ba."

Shiru tayi, kallon ta yayi ya ce, jibi za'a kawo miki kayan da zaki saka zan turo miki da duk shigar kayan da zaki a waya.

"Nagode!"
"Kinsa me?"

"A'ah, aikin da zanje nayi a England ya fito, ranar daurin aure suke son zuwa na kinga tare zamu tafi."

Kai ta girgiza ta ce,
"Aah Hamma kar ka so ma, ni dai ka bar ni a nan kawai har kaje ka dawo."

Kallon ta yayi ya ce,
"To ni ban amince ba."

"Kayi hakuri."
Shiru yayi dan da har ya dau zafi. Najwa na kara burgeshi da bada hakurin nan. Kafin kace tayi laifi ma zata baka hakuri a wuce wajen.

"Shikenan zan turo miki da kudin gyaran jiki da kayan ado kinji."

Kai ta gyaada masa kawai.
"Baby yaushe rabon da naga murmushin ki."

Kwalla ce ta ciko mata ido, tuna irin soyayyar da suke sha da in dai suna tare bata son su rabu, sannan fuskar ta bata taba rabuwa da murmushi.

Ita kanta tasan bata kyauta masa amman bata san yada zatayi bane.

Murmushi yayi, ya ce,
"Zaki shigo hannu ne."

Mikewa yayi ya ce,
"Ki fito muje gidan su Ummah na fadawa Mami tace ki shirya."

Fita yayi. Kanta ta kifa akan gado tana matsar kwalla.

Mikewa tayi ta saka wata bakar doguwar riga ba karamin kyau tayi ba.

Fuskar ta, ta daurayo ta zo ta shafa hoda. Turare kawai ta fesa ta fita.

A falo ta same shi, shida Mami, kallon ta yayi ya ce, ki kwason katin na goma goma zamu biya mukai wa Khadija.

Komawa tayi ta debo masa

Sallama sukai wa Mami suka fita. Mami kanta sai da suka burge ta. Dan ba karamin dace da juna sukai ba. Shi ya bude mata motar ta shiga.

Gidan su Ummah suka fara zuwa, Ummah da Baffah na zaune.

Ummah na gano su, ta fara fadin.
"Kaga amarya da ango, kaga har wani sheki sukai."

Najib sai dariya yake, Najwa kuwa kan ta na kasa.

Gefen su Umma suka zauna, Najwa ta gaida Ummah. Kanta a kasa.

Baffah ta gaishe, yana sa musu albarka.
"Allah muku Albarka, Allah ya bada zuri'a daiyiba ya kade fitina."

Najib ne me amsawa da
"Ameen! Ameen"

Najwa kuwa kanta a kasa, sai da ya gama sa musu albarka, Sannan ya ce,
"Amman dai yanzu komai ya dai dai ta ko?"

Najib ne, ya ce,
"Eh Baffah gamu ma tare."

"Masha Allah ana cigaba da hakuri da juna. In anyi auren ma haka za'a nayi. Sai hakuri."

"Insha Allahu, Baffah baza kuji komai daga gare mu ba."
"Allah yasa."

"Ameen!"
Daki Ummah ta ja, Najwa, zaunar da ita tayi, ta na bata sirikan aure. Tin Najwa najin kunyar Ummah har taga abin ba na kare bane.

"Najwa a aure babu jin kunya, ba wai kunya ba a'ah kunya wajen farantawa me gida, bama ke da kike da kishiya sai kin mike tsaye wajen gyara kan ki, ki karanci duk abinda ya fiso a tare  da ke, da wanda yafi so kina masa."

Ummah ta ce,
"Bari kiji na fada miki Najwa babu Namijin da yafi karfin mace sai dai in bata san yadda zatayi mu'alama dashi ba.

Mace 'yar ce me baiwa, ke mace, Ubangiji Allah ya bata wata baiwa da daraja ta musamman mace ita ce rufin asirin 'da namiji, abinda zakiyi ki kara karkato da hankalin da namiji kanki shine, biyayya ki bishi sau da kafa kiyi masa biyayya ki kula dashi kamar yaro dan goye.
Duk abinda kika san yana so kifi shi so, haka nan duk abinda kika san baya so kifishi 'ki."

"Sai *Hakuri,* ki zamo mai hakuri da kamun kai, ki zamo me hankali da nutsuwa ki zamo mai tatausan lafazi ga mijin ki.
Kiyi hakuri da abun da ya kawo ya baki kada ki zamo me hangen na sama dake rinka kallon na kasa dake ako da yaushe."

"Sai *biyayya,* biyayya ta zamo jigon zaman auren ki, Najwa yana yi bari na bari, idan ya dawo daga wajen neman abinci, ki taryo shi kina sannu da zuwa megida kina goge masa gumi, ki zaunar da shi kan kujera ki cire masa kayan jikin sa, wato ki rage masa kayan dake jikin sa kamar takalmi, in court ce ki cire masa ta sama, in babbar riga ce ki cire masa, kiyi hanzarin kawo masa ruwa me sanyi ko lemi, ya zamo kin shayar dashi.
   Ki hada masa ruwan wanka ki kai shi yayi, ko ki taya shi koma kuyi tare, ki bashi ko saka masa kaya mara sa nauyi, wanda zai sake a cikin su, ki rike hannun sa, ko ki fada jikin sa ki jashi gurin cin abinci. Ki zuba masa ki tura gaban sa yana ci kina  kara masa wani a haka se yaci da yawa ba tare da ya sani ba. Kar ki damu da sai kinci ke dai burin ki, ki ga megidan ki ya saki jiki ya ci abincinki ya koshi."

"To ya megida ze rinka cin abincin ki yana koshi, dole ne ki gyaragirkin ki kisan irin kalar abinci megidanki yafi so,
Kada ki yuwa  mijin ki girki daya saboda sauri gudura kiyi masa abinda ki kasan ransa yafi so."

"Akwai kalolin girke girke na hausa na gargajiya na turawa na larabawa ke har da nasara kai. Najwa ina son ki kasan ce wacce mijin ta ba ya iya cin abinci a wani waje duk in da yaje ba ze ci komai ba har sai ya dawo yaci girkin ki. Ko tafiya ze yi wata kasar sai dai ya tafi akan dole in ba halin tafiya da ke,"

Sai *Tsabta* nasan kina da ita na kuma tabbatar, ki kara dage dantse, ki kasan ce mai gyara gidan ki, ki tsaftace shi ko, da yaushe falonki ya kasance cikin gyara ki turare shi da turaran wuta me dadin kamshi.
  Dakunan ki da na megidanki dan Allah k rika tsabtace su da kanki kada ki bari 'yar aiki ko yaron gida su gyara miki, dakin miji wannan kamar kin bayyanar da sirrin ku ne, ki gyara dakin mijin ki ko ina ki kade ki share ki goge, ki turare su, su rinka fitar da dadin kamshi wanda zai na kwantar da hankali, ban dakin ki na masa turare ya kasance kullum shi ma ciki kamshi, Kananun abubuwan sa, irin su shimi, gajeran wando, hankici ke zakina wanke masa. Ki goge ki sa musu turare ki adana su."


*INDABAWA*

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page

*144*

*Ummu imsal* nagode da kulawar ki nagode Allah bar zumunci.

Masoya littafin *Najwa* na gode da son da kuke min.

*Wanda basu samu sanarwa ta akan shirun da kukaji kwana biyu ba. Ina bada hakuri, wani abune ya tsaidani kuma kafin faruwar hakan sai da na fada.*

*nagode da kulawar ku a gareni nagode Allah bar kauna.*


*Sannan ina cigitar kawata Ummu Affan*





"Gyran jikin ki loko da sako, na jikinki ki wanke shi ki gyare shi ko ina ya kasance yana daddadan kamshi yanda in mijin ki ya kusance ki ze sheki kamshin jikin ki yayi nishadi.
in da safe ne kiyi hanzarin tashi ki hada masa break ki shiga wanka, ki saka kananun kaya.
Najwa nasan ki da kunya to anan waje nake son wannan kunyar ta tafi, dan wadan nan abubuwan su zasu kara ninka sonki a ransa. Ya zamo bai da abin so da kalla sai ke.

Ki shirya cikin kananun kaya masu kyau idan kin gama shiryawa kije ki tashe shi, ba a tashin miji da hayaniya ko surutu, ko kina jijjiga shi, idan megida yana bacci kuma lokacin aiki yayi zaki dan kwanta a jikin sa, ki rinka shafa fuskar sa, ki na jan hancinsa ki rinka, hura masa kunne a hankali zaki ga ya tashi cikin nutsuwa,

Indan ya shiga wanka ki taya shi, yana fitoea ki goge masa jiki ki dauko masa kayan da zai saka,
ki ataimaka masa wajen gyara shi shafar mai da tazar kai.
in ya gama kije ki ciyar dashi, in zai tafi dauki jakar sa ki raka shi har wajen mota, kina masa yan magan ganun kauna.

Ki masa abinda ko yaje office zai na Allah Allah a tashi yazo wajen ki, in ya tafi ya dauko lokacin da kika san ya isa ki kira shi kijibya hanya.

Haka nan bayan awanni ki kira kiji ya office, ki masa kalamai masu dadi wanda zasu sa ya kara shiga cikin nutsuwa yayi abinda yaje yi.

Kafin ya dawo kisan kin gama komai na girki da gyaran gidan ki. Ki turare gidan da turaren wuta yai kamshin me rikidar da zuciya tare da kasa nishadi da bukata.

Kici kalliya, kamar me shirin zuwa fati, idan ya dawo kiyi masa kyakyawar kulawa, ta musamman.

Tin a gun oyoyo zaki na aikia masa da sakon ni kauna da salon so.

In kuwa ba da wuri zai dawo ba, ki aika masa da abincu dan kada ya zauna yunwa ta illata shi.

Ki masa abinda zai ci ya koshi dan ya samu kuzarib yin aiki.

In dare yayi, ki masa abu mara nauyi, sannan akwai hirar dare ake dan tsokano sha'awa, ki rinka yi masa hirar da zai dinga dariya tana sa shi nishadi a zuciya ta kuma dinga in gizi shi ga sha'awar ki.

Lokacib kwanciyya zaki saka tsadadiyar kwalliya, kisa tigar bacci me kyau, da daukar hankali.

Ki saki jikin ki da mijin ki bashi kulawa sosai kada ki gaji da bukatar sa, ki kyale shi har sai ya gamsu don kansa.

Ina kara jaddada miki kada ki ce zaki sa kunya a wajen kwanciyar ku da wajen faran ta masa. Kada ki kwanta masa kamar ruwa ki san irin nauikan wasanni da sali nasa nishadi da za ki kirkiro masa ki rinka yimasa dob gamsar dashi kada ki gaji. Kar kina mitar ya dame ki, kp ya fiya ta kura ko kin gaji ko baya barin ki ki huta.

Nuna irin wannan na bata ran megida yaji baya bukatar ki.

"Najwa dauko waccan littafin ki rubuta wa dan nan sirikan. Dan basa illa sai dai kara ni'ima da suke. In kuwa har me gidan ki ya dandabe ki bashi ba kara jin dadin wata."

Mikewa Nakwa tayi ta dauko littafin da biro,

Magana Ummah ta fara,
"ki samu kayan marmarin ki, ki markade ki zuba musu madara ki sha.wannan na kara lafiya a jiki ga kara ni'ima.

"Ki samu  danyan kwai guda daya ki fasa shi ki juye dan karamin abu, ki sami ganyrn shayi ki tsoma shi a ruwan kwan. In ya dan jiku sai ki kicire. Ki matse shi akan kwan sai kisa cokali ki kada shi. Har sai ya tsinke, kinga yana yauki. Ki shanye shi gaba daya.

Indab kikasha ko kamas kike sai kib ji danshi a jikin ki udan kuna mijin ki ya kusance ki sai yaji banbancinki giye da kullun dan yana kara ni'ima da kara dandano.

Ki samu kwanki ki fasa ki zuba masa isashiyar albasa ki soya shi yai ruwa ruwa. Yana kara ni'ima da dandano.

Abinda zai tsayar miki da nonon shi.
Ki sami farar shinkafa ki dake ta luku luku ki sami sewar burgu shima ki dake shi luku luku ki tankade su ki sami busashiyar aya ki dake ta luki li tankade sai ki hade su waje daya ki sami nono, kirdirmo me kyau ki rinka damawa kina sha sai kinyi mamakin girman nononki kuma ya tsaya yaki zuvewa.

Kayan kara ni'ima
ki samu kankana,
coxumber,
tumatur,
mazarkwai la
Madara
Dabino
Kanunfari.

Zaki yanka kankana duka harda ya'yan ta ma cocomber haka ki yanka tumatur ki cire ya'yan dabino ki markade su gu daya, kisaka mazarkwailar ki ta narke ku zuba zuma da madara. Kina yawan shan sa

Abarba
Ayaba
Gwanda
Kankana
Zuma
madara

Ki markade su zama ruwa kisa zuma da madara ki rinka sha da asuna sannan ki samu zogale dafafr ki hada da albasa da kawai kiyi kwadon sa da alayahhu da tumatur sai kici shima.

Dankalin tirawa a dafa a bari yasha oska ko damashi da madara shanu sai a zuna zuma a yini asha.Jikin ki bazia na zubewa ba.

Kina jika kanunfari shi kadai ki rinka sha yana ska kamshin gaba ma shi kadai.

Kina yawan shafa man hulba da zaitun a gaban ki.

Kina amfani da miski bayan kin gama al'ada, yana saka kamshin gaba.

Kina yawan tsarki da ruwan dumi, kina yawan shan fruit kina yawan amfani da miski.

"Bana son kina gamje gamjen maguman matan nan dan wasu na da illa bama na cushe cushen nan. Kinji ko."

Kai kawai Najwa ta gyada mata dan ta kasa dagowa ta kalle ta ma.

Kina yawan cin aya da dafafiyar gyada, dasu zuma.

Sai humra da zan koya miki wacce da kanki zaki hada abar ki gangariya ce, kayan zaki bayar a siyo miki koda bakya garin nan ne. Dan suna nan na jima da miki su dan jikowa kawai suke yanzu.

Kina hada lalle cokali biyu, ki hada da kwai hishir da kurkur. Ki hadr su ki kwaba, kafin ki kwanta kisaka yayi kintina ki wanke da ruwan dumi.

Ki hada bawan kawai, gishiri, sabulh  ghana da sabulun salo lalla, kina wankq dashi jikin ki zai dada santsi.

Ki samu ayana da lemon tsami, mafara cpcumber, kwai. Ki hada ki sga a jikin ki yayi awa daya kiyi wanka.

Man tafin kafa. Ki samu man shani da man kwakwa da man ridi da alayyadi da zaitun. Ki hade eu gu daya zaki kanta ki shafa ki wanke da ruwan dumi,

Kina goge fuskar ki da bawan kan kana.

Ki gada lemon tsami da zuma kina shafawa afuskar ki na tsawon minti talatin.

"Najwa duk wata matsalar ki kada ki sake ki fadawa kowa. Ki dage da addu'a a duk abinda ya shige miki duhu, in kina da katsalar da sai iin fada ki fada min insha Allah zan baki shawara da abinda zakiyi."

"Kina kula da mijin ki da halin da ya sauya aciki. Ki rike addu'a domin Addu'a makamin mumuni ce. Ki mike tsaye akab mijin ki, kina masa addu'a in yayi bacci kin farka ki kara tofe ki da addu'a

Haka in zai ci abinci kina tofa masa addu' a ciki kar kiyi sanya da addu'a dan itace gatan ki."

'Sannan ?annan kunyar dan Allah asan lokacin yin ta kada ta cutar da me gidan namu ya dawo guna. Ki daure kina rage ta a fannin kula dashi.

Ga wannan addu'ar kinayi aduk lokacin da zakici wani abu, duk abibda ke ji mara kyau Allah zai kare kivsaga sharrin sa.

Kina karanta *Li'ilafi* kafa daya ki tofa a abinci da za kici ko shi zai ci maganin sihiri da ake tsoron sa ko anyi bazai samaka ba insha Allahu.

A duk inda zaku hadu da abokiyar zaman ki, kina ambaton sunan Alalh tare da karanta *li'ilafi kafa 14* kariya ce daga haduea da abokan gaba.

"Inq baki wannan abubiwan ne dan naji furucin da Antyn Sumaiyya ta fada ne. Dan haka Ki dage da addu'a Najwa."

"Haka nan aduk lokacin da zaki fuskan ce ta, ki karanta wanna adfu'ar
" *Allahumma inna mwj'qluka finsgurihim wana uzunika mib shururihim* "

"Ki dage da rokan Allah akab duk al amuran ki. Sai da sukai sallah sannan suka fita falo.


*INDABAWA*

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*145*


Wannan shafin naka ne, *UMAR DALHA* Allah bar zumunci.
*Ameen*




*Shafi daya zan na kawo muku, saboda ina busy kwana biyu.*

*Nagode*




Sai la'asar sakali suka bar gidan umma, bayan ta gama wayar wa da jikar tata kanta. Najwa duk sai wani nauyin ta ta dada ji.

Haka nan Najib shima kamar yasan abinda akai amman wai kunyar sa take ji.

"Ummah me kuka tattauna ne ni babu ni"
Najib ya tambayi Ummah da suka rako su shiga mota.

"Kaji ka kai muka san me kuka tattauna da zaka tambaye mu."
Ummah ta bashi amsa.

"A'ah mu ba abinda muka tattauna."
Abbah ya fada.

"Ashe dai daya muke da kai."
Ummah ta fada

Dariya sukai suka shige mota. Suna dagawa kakan nin nasu hannu.

Sai da suke tafiyar muntina ba wanda yayi wa dan uwan sa magana. Kallon ta yayi, ya ce,
"Me Ummah ta fada miki ne naga duk kin canja."

Baki ta murguda mashi ta ce,
"Bakaji me Ummahn ta fada ba kenan."

Kallon ta yayi ya ce,
"Eyye ni kike murgudawa baki, lallai yarinya, wato rashin kunya Ummah ta koya miki ko?"

Bakin ta ta rufe da sauri dan ita bata san ma ta murguda masa bakin ba.

"Zaki sani ne."
Yayi dariya ciki ciki.

Ita dai shiru tayi tana nazarin magan ganun Ummah, "gaskiya abin da nauyi wallahi. Amman ya zanyi zan gwada naga yadda abin zai kaya."

Ajiyar zuciya ta sauke, da dauri Najib ya kalle ta, ya ce, "Lafiya?"

Murmushin son kare kai tayi, ta ce, "lafiya lou."

Kallon ta ya tsaya yi, ya ce, "Gaskiya Najwa keda Ummah baku da gaskiya ban yadda da wannan ajiyar zuciyar ba. Dan fada min kinji."

Ya miko mata kunnen sa, matsowa tayi kamar wacce zata fada miki. Murmushin mugunta tayi, tana kai bakin ta bakin kunnen ta sakar masa kara a kunnen.

Da sauri ya janye kunnen sa yana kallon ta, dariya ta saki, tana masa gwalo.

Girgiza kai yayi, ya ce, "zan rama ne."

"Haba Hammanah kayi hakiri." Kafada ya makale, ya ce, "Naki wayon."

"Please man." Kallon ta yayi yana mamakin canjawar ta, rabon da ta sake tai masa

Please Login or Register in order to submit comment