Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tafi kinyi asara sosai wacce da wuya ki samu kamar ta."

"Ni da kika ce akwai abinda kike son na aminta dashi me ya kawo wannan maganar."

"Sis! Najib nake so ki aminta dashi ya zamo mijin ki.
Dan Allah kada kice A'ah nasan kinsan girman alkawari. Dan Allah ki cika min wannan alkawarin."

Kallon ta Najwa ta tsaya yi. Kai ta gyada mata.

Rasa me zatayi tayi, dan haka kawai sai ta rumgumeta tana kuka.

"Ya zanyi kinsa na dauki alkawari dole nayi kokarin cika shi. Amman ki sani komai ya biyo baya kece sila."

"Ba komai Sis kuma ba abi.da zai biyo baya sai alheri kinji. Nagode."

Wannan yarinyar ita ta katse musu magana ta ce,
"Anty Zahra, ana kira"

Ta nuna mata wajen da yake tsaye a jikin mota. Sanye yake da bakin wando da farar riga me dogon hannu.

"Ina zuwa.!"
Ta dafa Najwa ta mikee.

Karasawa wajen tayi da murmushi akan fuskar ta.

Shi murmushin yake,
"Naga alamar an fara yin nasara ko?"

Murmushi tayi, ta ce,
"Sosai ma!"

"Masha Allah! Nagode!"
"Ba komai."

Kasa kasa yayi da muryar sa ya ce,
"Zan iya gani ta."

Kai ta girgiza masa. Ta ce,
"Ka ganta can."

Ta nuno masa ita da yake ta juya musu baya.
"Amman yanzu baza ta yadda ku hadu ba sai dai nan da kwana biyu. Ga number ta zan baka ka karasa sauran kafin ku hadu."

Murmushi yayi ya ce,
"Nagode."

Wayar sa ya dauki ya amshi Number Zahra da ta Najwa.

Sun jima Zahra na fada masa halaiyar Najwa wanda duk suka dada nasa sin ta da kaunar ta.

Ba abibda ya fado masa sai Summy wacce ba abibda ta iya bare ladabi da biyayya.

Abinda ya dade yana kwadayi sai gashi Allah ya jarabace shi da Sumaiyya.

Ya godewa Allah da ya jure zama da ita. Gashi Nan Allah yaso shi da rahama zai samu wacce yake da burin da kwadayin aura.

Sai gab da magariba ya tafi yana me kara godiya ga Zahra.

Wajen Najwa tayi suka koma daki duk jikin ta a sanyeye.

Zahara ce ke dada mata kwarin gwiwa na yabon halaiyar sa da dabi'un sa.

Da haka har Najwa ta fara samun nutsuwa da shi.


Shi kuwa tib da ya tafi kasa tsaye bare zaune yau gashi ga Najwa.

Ranar kwanan yayi yana sallah. Da asuba kuwa ya kira Khaleel ya fada masa. Haka ma Mami itama da asuba ya kira ta ya shaida mata.

Mami shiru tayi, tana tunanin har yaushe yayi da yake son kara wani auren.

Auren da befi shekara da watanni ba. Haka shima Khaleel ya ke sakawa a cikin ransa.

Da asuba taan tashi, yaji wayar ta na kara dubawa tayi.

Sakon ne wanda aka turo guda biyu dayan tin wajen karge hudun dare ne.

Sako ne akan zallah kaunar da ake mata ta jima tana juta kalaman sannan ta duba dayan da ya ce,

"Ta tashi tayi sallah. Lokacin karfe biyu da rabi."
Ta rasa abinda ya hau kanta har ta kasa tashi yin sallahr da ta saba.

Wani sakon ne ya shigi yana fadin ta tashi tayi sallahar asua.

Mikewa tayi da sauri. Taan tashin Zahra. Bandaki ta shiga ta yi wanka sannan ta tada sallah.

Tana idar wa ta hada musu abin kara da exam din safe ce dasu.

Suna gamawa suka shirya suka wuce hall din exam.

Karfe sha biyu suka fito a Exam wannan yasa suka shige library anyin karatu.

Acan ma sai da taga sakonnin sa har guda biyu dana barka da safiya dana addu'a Allah basu sa'ar jarbawa.

Murmushi tayi dan addu'ar ta mata.

Be kira ta ba amman dai a ranar ya mata text yafi goma.

Ya kira Zahra yaki ya Najwa take sannan ya ce me suke bukata.

Sam Zahra ta ce basa bukatar komai.

Duk yadda yayi ya kawo musu abu kin yadda tayi.

Lokacin da ya dauka ya koma aiki yayi amman sam yace shi sai yasamu haduwa da Najwa zai koma.

Gobe zasu gama exam din su dan haka, Zahra ta d ya kamata yaxo yau su hadu da Najwa.

Da yake basuyi paper ba yau yasa tin safe suka gama da karatun jarabawar gobe.

Kwallaiya take tsarawa Najwa dake fitowa daga bandaki daure da towel ta tsaya kallon ta.
ta ce,

"Ina kuma zuwa haka? Ko Mustapha ne zai zo?"

Murmushi Zahra tayi, ta ce,
"Kamar kin sani kuma zamu fita yi sauri ki shirya."

Baku ta tabe ta goge jikinta ta shafa mai.

Wani material suka dauka baki da ja, wanda akai musu dinkin doguwar riga me AShape.

Ba karamin kyau dinkin yayi ba. Ita suka saka sai dankunne baki da sarka da abin hannu.

Jajajyen mayafi da takalmi Zahra ta dauko mu.





*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *125*

Zaunar da Najwa tayi zatai mata kwalliya.
"A'ah Sis yimin simple ban son me yawa."

Wannan yasa tai mata jagira kawai sai dan man lebe da ta shafa mata."

Ya salam duk da batai kwalliya ba. Amman ba karamin kyau tayi ba.

Waya aka kira Zahra, dauka tayi, ta ce,
"Gasu ban."

Mayafan suka yafa, suka fita. tin daga nesa ya zubawa Zahra ido.

Najwa kuwa tsaki tayi, ta ce,
"Wallahi Mustapha ya fiya kallo."

Hararar ta Zahra tayi ta ce,
"Dadin ta kayan sa yake kalla."

"Au haka kika ce?"
"A'ah amman ai dadin ta ma bamu san yadda naki zai ba in ya ganki."

"Ba ruwan sa ai."
"Allah Sis irin wadan nan sun fi fitina."

"Ke gidan su. Yayan naki ne fitanan ne."
"A'ah yi hakuri Adda."

"Allah sarki har kin tunon da Basma ta. ina kewar ta wallahi."

Mustapha daya karaso wajen shi ya katse musu maganar da suke yi.

Durkusawa yayi yana cewa,
"Adda ina yini?"

Hararar sa tayi ta ce,
"Dan Allah ku daina mai dani tsohuwa."

"Anki din!"
Zahra ta fada. Duka ta kaima tana dariya.

Gaisawa sukayi, sannan suka matsa gefe suka zauna.

Mota ce, ta danno wajen da suke, kallo suka bi motar da yi banda  Najwa da ke danna wayar ta.

Najib ne ya fito daga motar sanye da  wandon jeans,  sai jar riga idon sa sanye da tabarau me garai garai.

Ba karamin kyau yayi ba, sai tashin kamshi yake.

Zahra ce ta rage murya tana fadawa Mustapha wani abu.

Da sauri Mustapha ya mike ya taro shi suna gaisawa.

Karasowa sukai suka gaisa da Zahra, Najwa ta nuna masa da hannun ta.

Kallon ta ya tsaya yi, da ido baki da hanci. duk ya rasa control din sa dan ya saka daina kallon ta.

Dariya Zahra tayi, ta ce, a ranta.
"Nagodewa Allah naga yadda zatayi da shi. Shima ga kallon nan."

Hannun sa Mustapha ya kama ya kai shi gefen ta.

Kamshin turaren da taji shi yasa ta dagowa da sauri.

Ido ta zaro ta mikewa a razane, kallon sa take da alamun kamar ta sanshi.

Shima hakan kokarin tino inda yasan ta yake.

Kai ya girgiza, tini ai ya dade da sanin ta ko na ganin ta da yake.

Itama kawar da tunanin tayi, a ranta ta ce,
"Kama ce."

Kasa tayi da kai, kallo ya bita dashi.

"Ina yini?"
ta gaisar dashi murya na rawa.

Kallon ta yayi, dan son tino inda ga taba jin muryar nan.

"Lafiya lou Najwa ya karatu."
"Lafiya Alhamdulilah."

Shiru tayi. Kallon ta ya tsaya yi kamar TV.

Kasa sakewa tayi kanta a kasa.
"Najwa Ina fatan kin aminta dani. Najwa ni me son kine, na jima da son ki a raina. Kece farin ciki na."

Duk rashin surutun Najib yau bakin sa yaki rufuwa.

Zuba yake mata bayanai yake a kan duk yadda yake son ta.

Ya kasa yin shiru, Najwa kuwa shiru tayi tana sauraron sa.

Duk yadda tayi tunanin sa yawuce nan.

Gaskiya ya mata, kuma daga maganar sa ma ta fuskanci, ko shi waye.

Da kyar ya barta dan kasa barin ta yayi.

Itama tin bayan rabuwar su, ta fada kogin tunanin sa.

Sun rabu da shi akan gobe zai zo yai musu sallama kafin ya tafi.

Washe gari karfe tara suka shiga jarabawa, inda sha daya har sun fito.

Suna fitowa suka hange sa daga jikin motar sa.

Kasa tayi da kanta, suka karasa gun sa.

Dan durkusawa tayi ta Gaida shi. Amsa wa yayi idon sa kyar akan ta.

Zahra ce, ta ce,
"Har ka fito kenan."

"Eh wallahi, nazo naga Baby na na wuce."
Fuska Najwa ta rufe da tafin hannun ta dan kunya.

"To shikenan ni bari naje, sai munyi waya Allah kiyaye hanya."
"Ameen Zahra Nagode fa "

"Ba komai."
ta fada tana yin gaba

Kallon sa ya komar dashi kan Najwa.
"Baby nah!"

Shiru tayi,
"Toh! ni zan tafi, sai munyi waya."

Muryar ta yajiyo me dadi da sanyi tana masa addu'a.
"To Allah kiyaye hanya Allah kai ka ya dawo da kai  lafiya. Allah tsare."

Kallon ta ya tsaya yi, yana ta amsawa daa
"Ameen Ameen!"

Shiga yayi ta rufe masa kofa tana daga masa hannu.

Sai da taga tafiyar sa, sannan ta nufi hanyar hostel.

Zahra na ganin ta fara yin dariya ta ce,
"Baby ya soyayya."

Duka takai mata, ta ce,
"Bana so."

Kayan su suka hada, suka debo aka saka a motar gidan su.

Lokacin suka tafi gidan Mami har ta hada musu kayan abinci kala kala.

Wanka sukai sannan suka zauna, cin abinci.

Kwanciyya Najwa tayi dan yin bacci. Tinawa tayi da Najib wannan yasa ta dauki wayar ta, ta tura masa sako me dadi.

Yana sauka yaji karar wayar sa, dauka yayi, sakon Najwa ya gani.

Wani murmushi ne ya sauka akan fuskar sa wanda besan lokacin da ya fita ba.

Gidan Mami ya fara sauka dan ya samu abinda zai ci ya huta kuma.

Yana shiga yai wanka sannan ya ci abinci.

Bangaren sa na da ya shiga, ya kwanta bashi ya tashi ba sai yamma.

Lokacin ya kuma ganin wani text din nata.

Mamaki ne ya lullube shi, ganin Sumaiyya da take matar sa ma bata damu dashi haka ba.

In ya tafi in har be kirata ba, to baza ta taba kiran sa ba.

Sumaiyya duk abinda take so, Najib na mata shi. Kudi kuwa kamar me kullun zai dire mata.

Abunda yake hada shi da Sumaiyya shine rashin son yin aiki. Bazata taba gyara waje ba.

Haka nan bata son kitso, jikin ta dai zatai wanka sau da a rana, tai kwalliya amman kanta ba ya samun gyara sai ta gadama zataje saloon a tsefe a wanke a sake wani.

Sai rashin girki sam bazata masa girki ba. Duk yadda yake da son abinci amman baya samu dan in ya dawo sai dai ya samu abu me sauki ya dafa ya ci.

Bangaren sa kuwa zai iya cewa bata shiga sau biyar ba. Bare taga ya baci ta gyara masa ma.

Ga rashin kula, wai taga yayi dare ko yai tafiya ta kira sam babu wannan.

Sai dai in tana neman wani abu ne. Abin na damun sa.

Gashi wai safiyya tayi ta gaishe shi ya dawo daga aiki a tarbe shi ko ai masa sannu da zuwa duk bazai samu ba.

Be taba ganin ta da Alkur'ani ba bare yaji tana karatawa.

Shi da yake son mace me addini sai gashi Allah ya hada shi da Sumaiyya.

To ya godewa Allah kuma a koda yaushe yana mata addu'ar shiriya.

Har a isilamiyya ya saka ta amman bazai ce ta taba zuwa ba.

Ga rashin Sallah akan lokaci. Gashi bata son zuwa gaida su Mami. In yace yazo suje sai ta kawo wani abun.

*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *126*

Sai da yai wanka yai sallah sannan ya kira Najwa.

Dagawa tayi cikin sallama da murya me dadi.

Amsawa yayi yana saukar da ajiyar zuciya.

"Hamma kaje lafiya?"
Sunan da ta kira shi dashi ne ya tuno masa da Najwa kanwar sa.

Murmushi yayi, ya ce,
"Lafiya lou Alhamdulilah ya kuka je gida kuma."

"Lafiya lou wallahi. Amman dai kaci abinci ko?"

Murmushin jin dadi yayi na kular da take dashi.
"Ban ci ba yanzu dai. Zanje madam ta bani."

Shiru tayi, a ranta kuma ta ce,
"Madam kuma ba Mama ba."

A fili kuwa murmushi tayi, ta ce,
"Ka gaishe min da ita."

Mamaki amsar ta, da ta bashi yayi, ya ce,
"Bakya kishi nane?"

Murnushi tayi, ta ce,
"Kishin ka shine naso abinda kake so. Ko so kake na tada maka da hankali."

Kai ya jinjina, a ransa ya ce,
"Alhamdulilah wannan ita ce matar aure ta rufin asiri."

"Haka ne Najwa in na dawo mayi magana."
"To shikenan sai anjima ka gaida su Mami da kowa."

"Zasu ji insha Allahu."
Mikewa yayi ya fita falo ransa cike da farin ciki.

Mami ya sama zaune a falo.

Gefen ta ya zauna ya ce,
"Mami Najwa na gaishe ki."

"Ina amsawa a ina ka ganta."
Murmushi yayi, ya ce,

"Mami yarinyar da nace miki na gani."
Kai ta girgiza ta ce,

"Najib wai aure kake son ka kara."
Murmushi yayi ya ce,

"Mami kin san dai Najwa na fara so kuma har yau tana raina."

"Haka ne Najib nima ina son ta tinda kana sonta. Kuma tin ban ganta ba naji sonta ya shige ni. Allah yasa albarka a ciki."

"Ameen Mami na."
Ya rumgumeta yana jijiga ta.

Su Talle ne suka shigo, Talle ta ce,
"Haba Yaya sakar mana Mamin mu kar ka balla mana ita."

Harara ta yayi ya ce,
"Zo kuji labari me dadi."

Talle uwar yan son labari ta karaso wajen da sauri, ta  ce,
"Bani mu sha."

Kai ya dungure mata ya mike ya ce,
"Na ki din."

"Dan Allah Yaya!"
"To Najwa na gaishe ku."

"Yaya Yaushe kaga Najwan?"
"Ke ba wannan Najwan ba."

Dariya tayi, ta ce,
"Wacce toh?"

"Matar da zan aura."
"Dan Allah fa?"

Ta fada da karfi. Bangaren sa yayi yana cewa,
"Tambayi Mami kisha labari."

Kallon Mami tayi, ta ce,
"Wai Mami yaushe Yaya Najib ya fara soyayya?"

Dariya mami tayi ta basu labarin haduwar sa da Najwa tin daga farko har haduwar da sukayi yanxu.

Mamaki suka dinga yi, dan sun  san ba ruwan shi, da kula mata da har  zai karo aure.

Talle kuwa murna take tana addu'a Allah yasa ba irin halin Sumaiyya ne da ita ba.

Ga girman kai, ga rowa kullum fuska a hade kamar wacce aka ce ga mutuwar ta.

Shiryawa yayi ya fito yai wa Mami sallama kan gobe da safe zai zo gun Dady.

Yana zuwa gida yar mulki na can ita da kawaye sai shewa suke yi.

Be ma shiga bangaren nata ba yayi bangaren sa ya kwanta.


Sai bayan isha'i da ya dawo yaje bangaren ta. Kaca kaca da shi Me aikin su na gyara wajen

Gaishe shi tayi ya shige ciki. Dakin Sumaiyya ya shiga da sallama.

Tana zaune akan gado sai waya take amsawa. Zama yayi a gefen ta.

Kallon sa tayi ta cigaba da amsa wayar da takeyi.

Kai ya girgiza ya mike ya fita, ace ta ganshi ai in ba da iyayen ta take waya ba ko waye ya kamata ta kashe yai masa sannu da zuwa.

Kallo ya kunna yana yi, lemo ya shiga kitchen ya dauka yana sha.

Har karfe tara bata fito ba. wayar sa ya dauka ya kira Najwa.

Suna falo gaba dayan suna hira kiran sa ya shigo.

Dago da ido tayi tana kallon Momy  da Zahra.

Mikewa tayi, tayi cikin Daki da sauri. kallo Momy ta bita dashi.

Zahra kuwa ta kwalkwale da dariya. Kallon ta Momy tayi ta ce,
"Lafiya?"

"Momy Najwan ce kamar mara gaskiya."
"To mene?"

"Bata saba bane?"
"Da me fa?"

"Soyayya mana Momy."
Murmushi tayi, ta ce,
"Allah sarki Najwa wa ya janyo hankalin ta."

Dariya Zara tayi, ta bawa Mami labarin duk abinda ya faru.

Najwa na shiga daki, ta kwanta akan gado,
Sallama tayi, cikin sanyin murya.

"Assalamu Alaikum!"
"Wa'alaikum Salam Gimbiyya sarautar mata."

"Ina yini Hamma?"
Shiru ya kuma yi, ya amsa da
"Lafiya lou Sarauniyar mata."

Murmushi tayi ta ce,
"Ya gajiya?"

"Lafiya Gajiya ta tafi."
"Sannu toh!"

"Yauwah Baby nah. Mene labari."
"Labari na gunka. Ina Anty na ka baro ta da daren nan kana waya."

Murmushi yayi ya tuno ko haduwa ma da ita basuyi ba.
"Kar ki damu tasan dake ai."

"Da ni kuma?"
Ta tambaya tana nuna kanta.

"Eh man!"
"Kamar ya toh?"

"Abar maganar shima zan fada miki."
"To kaje wajen Anty kaga dare yayi."

"Kin gaji dani ko?"
"Ni na isa. Kar dai a shiga lokacin ta ne, kaga yau ka koma."

"Haka ne, to sai Safe."
"Allah tashe mu lafiya."

"Ameen Nagode."
Suka kashe wayar. Text ya tura mata, kafi  ya mike ya shiga dakin.

Har lokacin waya take, kallon ta yayi, ya girgiza kai ya ce,

"Sai da safe."
Hannu kawai ta daga masa.

Dakin sa yayi yana tunanin hali irin na Sumaiyya ace mijin ka ya dawo daga tafiya amman ba wani sannu da zuwa bare kula da shi.

Sai Najwa ta fado masa, wacce ji yadda take kula dashi da tambayar halin da yake ciki.

Da wannan tunanin yayi bacci da mafarken Najwan sa.

Najwa kuwa na kashe wayar ta canja kaya ta hau kan gado tana me tunanin Najib.

Bata taba tunanin haka soyayya take ba, tayi mamakin ta da tai saurin aminta da Najib.

Itama da tunanin sa tayi bacci.

Da asuba yana tashi yai wanka ya tafi massalaci.

Bai dawo ba sai karfe shida da rabi.

Wanka ya kuma ya shirya cikin Kananun kaya, dakin Sumaiyya yayi, tana  kwance ko tashi sallah batayi ba.

Kudi ya ajiye mata ya juya fita. gidan Mami ya tafi.

Mami da Dady na kan daining. Mami na hada masa break.

Karasawa wajen yayi, yana gaisar da su Mami, amsawa sukai, sannan ya zauna.

A ransa kuwa yana kara jinjinawa Mami da yadda take kula da Dady.

Abincin shima ya hada ya ci, sai da yaci ya koshi sannan suka koma falo.

Kara gaisawa sukai, suka tattauna akan asibitin su, sannan ya tashi ya tafi aiki.

Yana shiga office yaga sakon Najwa na barka da safiyya.

Murmushi yayi ya kira wayar ta.
Dagawa tayi da sallama tana gaushe shi.

"Baby na kin tashi lafiya?"
Murmushin jin kunya tayi ta amsa da
"Lafiya Alhamdulilah."

"Ya aikin?"
"Aiki yanzu muka fito."

"To Allah ya taimaka. sai anjima kar na tsayar da kai."
"Najwa!"

Ya kira sunan ya cikin wata irin murya.
"Na'am!"

"Najwa ban gama jin muryar ki ba. Ita ce kadai zata dada min kuzari."

Fuska ta rufe kamar tana ganin shi ta ce,
"Kai Hamma."

"Zan kwari kai nane. Ni wallahi ban gaji da jin muryar Baby na ba."

"To aiki fa."
"Kar ki damu sai goma zan fara ganin masa lafiya."

"Hmm to ni me zance?"
"Komai kika fada zai faranta min."

"Allah bansan abinda zan fada ba."
"To shikenan ce ne kina so na."

Ido tayo waje dasu, ta ce,
"Me?"

"Eh! Kinji."
"In na fada zakaji dadi."

"Dadin ma da zanji ai bazai misaltu ba."
"To shikenan. Rufe idon ka."

Dariya yayi ya ce,
"Ta wayar ma kunya kije ji."

Shiru tayi, dan itama idon nata a rufe yake.
"To shikenan Na rufe."

"Ina kaunar ka. Ina son ka. Bye ayi aiki lafiya."
Ta katse wayar.

Bude idon sa yayi yana dariya. Ya girgiza kai, yana me jin farin ciki a ransa.



*INDABAWA*

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *127*


Soyayya tsakanin Najib da Najwa tayi nisa inda a tsakanin su ba wanda yake boyewa dan uwan sa halin da yake ciki.

Sosai Najwa ta saba da shi, son sa kuma ya shige ta sosai.

Abinda ya hana Najwa  soyayya tin farko shine.

Najwa bata iya soyayya ba. In ta tashi sa mutum a ran ta gab  aaa daya take son shi. Haka nan in bata so bata taba iya nuna masa tana son sa.

Wannan yasa take tsoron soyayya dan bata san wanda ke son ta tsakani da Allah ba.

Duk yadda Najib ya so, yaje Katsina hana shi tayi dan ya ce,
"Aikin sa da kula da Antyn fa."

Ba yadda ya iya, sai dai kullim cikin waya suke.

Momy kuwa har mamakin Najwa take, Dan ma Najwa akwai kunya bata taba yin waya a gaban ta.

Mami kan ta, tasan da batun Najib haka shima yasan ta dan suna gaisawa a waya.

Batun Sumaiyya kuwa yayi gaba dan in har ba ita take bukatar sa ba bata sauraron sa.

Shi kuwa ba ruwan sa duk nauyin ta dake kansa yana sauke mata.

Dan kullum Mami da Dady cikin masa fadan rike iyali yake.

Wannan yasa ko zai mata wani sai ya fasa.


Cikin ikon Allah su Najwa an koma makaranta, Sun koma second semester level three.

Satin da suka koma kuwa ya dira a katsina ba tare da ya fada mata ba.

Dan ya kasa jure rashin ganin ta.
Da yamma sun fito daga lectures sa kawai ganin sa sukai.

Mamaki dauke a fuskar su suke kallon sa.

Zahra kuwa sai cewa, tayi,
"Daman kin san da zuwan sa ne?"

"Ina fa?"
Suka karasa gun sa.

Har kasa suka durkusa suma gaida shi.

Amsawa yayi yana me kafe Najwa da idanu.

Dan ta kara kyau ta kara haske. Da ido tai masa alama da Zahra.

Murmushi yayi, ya ce,
"Zahra me kike bawa Baby na ta kara kyau haka."

Dariya Zahra tayi, ta ce,
"Ai ta dan rame ma dan kaji."

"Dan Allah fa. Gaskiya ne Allah yayiwa Dady da Momy albarka da kula min da Baby na da suke "

Dariya Zahra tayi, ta ce,
"Ameen!"

"Tashi mu koma can."
Najwa ta fada tana kallon sa.

Kallon ta yayi shima, wannan yasa tayi kasa da kai da sauri.

Gaba tayi suka biyo bayan ta. Zama sukai Zahra, tayi hostel.

Kallon ta yayi, ya ce,
"Baby na kasa jurewa sauka ta kenann."

Ido ta zare, ta ce,
"Sannu amman baka huta ba. Kaci abinci ba."

"Najwa ganin ki shine gaba da su. Na ganki na ji dadi sosai."

Murmushi tayi, ta ce,
"Sannu to, ya gajiya."

"Gajiya ta ganki ta gudu."
"Da gaske."

"Eh man. Sannu toh. Yau naga me maka tausa, ka baro Antyna a can."

Murmshi kawai yayi, aransa kuwa ya ce,
"Sumaiyya bata tabai masa tausa ba."

"Bari na kawo maka lemo."
"A'ah nagode!"

Fuska ta bata, murmushi yayi, ya ce,
"To shikenan daukon."

Daki tayi kallo ya bita dashi, gaskiya Najwa ba dai Diri ba tubarkallah.

Daki ta shiga, ta tadda har Momy ta kai musu abinci.

Budewa tayi taga fried rice ne da kaji.
Dibar masa tayi, ta daukar masa lemo da cokali.

Ta zuba a basket. Ta fita dashi. Yana zauna yana kallon ta har ta karaso.

"Sannu!"
"Yauwah Sannu! Ga shi nan kaje gida kacci ka huta kaji."

Murya ya shagwabe, ya ce,
"Uhmm uhmm ni ban gaji da kallon Baby na ba."

"Haba Hamma nah. Kayi hakuri man. Kaje ka huta  bazan taba jin dadi ba in har baka je ka huta ba."

"Yi hakuri Baby na. Na tafi sai anjima in na dawo."
Ya mike har baki mota ta rakashi ta mika masa basket din.

Amsa yayi yana mata godiya. Fuska ta hade ta ce,
"Mene na godiyar?"

"Gashi nan."
"Ni bana so. In kayiwa kanka abu kana godiya ne?"

"A'ah!'
"To kuma."

Murmushi yayi, ya ce,
"Haka ne. Na tafi."

Ya zauna yana amsa, bayan sit ya juya ya dauko, wata leda.

Mika mata yayi, kallon sa tayi, tayi murmushi ta juya ba tare da ta juyo ba ta ce,
"Sai anjima ka tafi a hankali. Ka kula da kanka."

Dariya kawai yayi ganin abinda tayi. Sai da yaga tafiyar ta sannan ya tada motar ya tafi.

Da yamma wajen karfe biyar ya dawo makarantar, Najwa na kwance kiran sa ya shigo.

Mikewa tayi tana kallon Zahra wacce tayi kamar bacci take yi.

Da sallama ta daga wayar
"Assalamu Alaikum!"

Murmushi ya sauke tare  da wata ajiyar zuciya kafin ya amsa sallamar.

Dan muryar ta ba karamin sa masa kasala take yi ba.

"Wa'alaikum salam ya ma'abociyar kyau da hankali da nutsuwa."

Murmushi tayi, ta ce,
"Hamma zaka fara ko?"

"Me zan fara in ba fadar gaskiya ba."
Kwafa tayi, tayi shiru kawai.

"Yi hakuri sarauniyar Matan duniya me kyau da aji."
"Allah bana so."

"Haba Najwa tayaya ni kuwa zan ki fadan abinda yake gaskiya ne."
"Ni ba wani nan."

"To karya nayi."
Ya fada yaba danna dariyar da tazo masa.

Ido ta zaro, ta  daura hannu akan bakin ta ta ce,
"Ni na isa nace haka. Kayi hakuri."

"Baki min komai ba Princess. Ya kike ya gajiyar makaranta."

"A'ah ni ya kamata na tambaye ka haka ai. Ya gajiya hanya."

"A'ah ina waje kizo kigani tana nan ko ta gudu."
Dariya tayi, ta ce,

"Da gaske kazo?"
"Zo ki gani."

"Shikenan gani nan."
Ta mike, Hijab ta dauka ta saka. Sai turare me sanyin kamshi da ta shafa a jikin ta.

Zahra ta kalla, ta daka, sannan ta ce,
"Hamma yazo, zanje ko zaki zo muje ne."

Ido Zahra ta bude ta ce,
"Nima Mustapha na hanya yanzu."

Ido Najwa ta bude, ta girgiza kai kawai ta fita.

Tin daga nesa ya zuba mata ido. ita kuwa kanta a kasa ta kasa dagowa ta kalle shi.

Sanye yake da farin wando, sai jar riga me dogon hannu.

Sai tashin kamshi yake, hannun sa makale da agogon fata fari, takalmin kafar sa sandal ne me kyau shima fari.

Sai da ta karasa sannan tai masa sallama.

Amsawa yayi yana kara zuba mata idanun sa masu kyau.

Durkusawa tayi ta gaishe dashi.

Abinda yake kara burgeshi da ita kenan. Ba dai ta gaishe shi a tsaye ba.

Yarinyar akwai ta biyayya da ladabi.
Amsawa yayi yana kallon ta. So yake ta dago da idon ta amman sam taki kallon sa.

"Wayoo ido na!"
Ya fada yana kallon ta.

Ai kuwa da sauri ta dago kanta tana kallon idon nasa.

Kallon juna suke, duk sun kasa kawar da idanun su.


*INDABAWA*

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*128*


"Wayoo ido na!"
Ya fada yana kallon ta.

Ai kuwa da sauri ta dago kanta tana kallon idon nasa.

Kallon juna suke, duk sun kasa kawar da idanun su.

A ran Najwa ta ce,
"Tabbas nasan wannan fuskar da idon,"

Ita ganin kamar su ma takeyi ta wani fannin  haske kadai zata nuna masa.

Allah me iko, Gaskiya Najib kyakyawa ne, dan dai shi baki ne kawai. Amman bakin nasa me kyau ne.

Ga ido da hanci, ga bakin sa dan karami dashi, haka gashin kansa ma me kyau dashi a

Please Login or Register in order to submit comment