Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tayaya zan manta da *Najwa* ta."

Murmushi sukayi gaba daya. Mami ta ce,
"Ku tashi muje kuci abinci."

Suka mike, sukayi wajen cin abinci, Dady da Mamin Najib na hira.

Suna gamawa, Dady yace, su taso suje gidan su Ummah, daga nan kuma suka tafi gidan Ammi,Β  mama Amina.




*INDABAWA*

NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


PAGE *81-85*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*



Sai karfe shida su *Najwa* suka dawo daga makaranta.Β  Lokacin Mami Najib da mami suna saman bene a dakin Mami suna hira.

Saman suka hau, suka nufi dakin Mami. Danyi mata sannu da gida.

Sannan sukayi dakin *Najwa*Β Β  dan cire kayan makarantar su.

Suna cirewa, *Najwa* tasa Basma dauko jakar makarantar ta, dan yin homework din ta.

Suna gamawa suka shige sukayi alwala dan yin Sallah magariba.

Mamin suna hira, Basma ta shiga dakin.

Kallon ta Mami Najib, tayi, ta ce,
"Ina *Najwa* ?"

Basma! Ta ce,
"Adda tana daki."

Mami ce ta kalle ta. Ta ce,
"Tashi kije ki kirata."

Basma ta amsa da
"Toh!"

Basma ta fice a guje tayi dakin *Najwa* tana kwada mata kira.

Tare suka dawo da *Najwa* na sanye da hijab din ta har kasa.

Da sallama suka shiga dakin. *Najwa* ta zauna a kasa gefen kafar Mamin Najib.

Fita Mamin *Najwa* tayi dan hada wajen cin abincu.

Mamin Najib ce, ta kalli, *Najwa* ta ce,
" 'yata yanzu ajin ki nawa."

Murmushi *Najwa* tayi, ta ce,
"Mami nayi candy wannan shekarar."

"Masha Allah! Yanzu kuma sai ina?"
"Katsina zan tafi, wajen Anty Hauwa."

"Anty Hauwa ta dauke ki, da na dauke ki ai."
"Amman kafin a fara makaranta zaki kawon ziyara ko."

"Eh! Mami insha Allah!'

Dai dai shigowar Mami da kayan abinci a hannun ta, *Najwa* ce ta mike, ta amsa ta dire a gaban Mami.

Fulas din ta bude, wainar shinkafa ce a ciki, sai miyar agushi da Mami ta saka mata nama.

Sai lemon abarba da kwakwa. Zuba mata *Najwa* tayi sannan ta mike tayi dakin su.

Kur'anin ta, ta dauko, tana muraja'a.


Duk yadda Najib yaso yau yaga yarinyar be samu dama ba, dan basu dawo gida ba sai bayan sallah isha'i duk jikin sa yayi sanyi dan jin sa yake kamar mara lafiya.

Suna shigowa gidan suka zauna a falo, wayar sa ya dauko, ya kira Mami.

"Hello Mami ki fito mu tafi."
Mami dake cin abinci, tace,

"Najib ai ka bari kuci abincu ko?"
"Na koshi ki sauko mu tafi "

"To shikenan gani na."

Ta katse wayar tana kallon Mami. Ta ce,
"Dan naki ya tada darunsa muzo mu tafi."

Mami ta ce,
"Najib kenan har yau yana nan da rigimar sa kenan."

"Gashi nan kuwa kin gani."
"Dan ma Allah yasa, Yaron nawa akwai hankali."

"Daman haka zakice."

Mamin Najib ta mike,Β  tana cewa,
"Bari mu tafi kar muyi dare a waje."

"Dama kwana kukayi."
"Mamin *Najwa* kenan. Muje dai."

Suka fito, Mamin Najib ta ce,
"Ina *Najwah* ne?"

"Tana daki, bari na kirata."
"A'ah barta, bari naje na ganta."

Murmushi Mamin *Najwa* tayi sukayi dakin *Najwa*

Tana zaune tana koyawa Basma karatu suka shiga.

Tsayawa tayi, taba murmushi. Mamin Najib tace,
"Sannu da kokari *Najwa* mu zamu tafi, ga wannan."

Ta mika mata wata katuwar bakar leda.

Hannu biyu *Najwa*Β  Tasa ta amsa, tana godiya. Mikewa tayi da niyyar rakata.

Amman tace tayi zaman ta, komawa tayi ta zauna tana musu addu'ar komawa gida lafiya.

Mamin Najib ta tafi da son yarinyar dan *Najwa* abar burgewa ce ga kowa saboda hankalin ta da nutsuwar ta

Suna sauka Najib ya mike, Mami ce tayi kitchen, ta dauko masa abincin da ta zuba masa a basket.

Ta foto, ta mika masa, ta ce,
"Gashi in kaje gida kaci abinci, tinda kaki ka zauna kaci."

Najib ya ce,
"Mami ba haka bane."

"Toh! Ba komai."

Tare suka fito har Salim dan sai da suka ga tafiyar su sannan suka koma cikin gida.

Tin a mota Mami, ta gane Najib din nata ba dai dai yake ba. Batai masa magana ba har sai da sukaje gida, suka zauna. Ta ce,

"Son lafiya kuwa?"
Murmushin karfin hali yayi. Sannan yace.

"Momy ba komai."
Kallon sa tayi cikin mamaki. Ta ce,

"Wai me yake damun kane yanzu, naga baka da abokin shawara sai ni amman yanzu kana son kadaina fada min damuwar ka."

"Mami ba haka bane bana son kema ki shiga cikin damuwar ne."
Ya fada cikin sanyin murya.

"Amman kasan ai dole na shiga damuwa. Dan ko ta kallon ka nasan akwai abinda ke damun ka. Kuma in ka fadamin zan taya ka da addu'a."

"Haka ne Mami, akan Yarinyar nan ne wallahi, har yanzu ba nasara ban ganta ba dazu, gashi munyi dare dazu har sun tashi. Gashi gobe alhamis. Ga lokacin tafiyar mu na karatowa."

Murmushi Mami tayi duk dan ta karfafa masa gwiwa. Ta ce,
"Son ka kwantar da hankalin ka. Insha Allahu zaka ganta. in ma baka ganta ba ni na gano maka wata ma."

Murmushi yayi. ya ce,
"Wace Mami."

"Yar wajenka mana *Najwa* mana "
"Mami *Najwa* kuma."

"Eh ita, wai yaushe rabonka da *Najwa* ma tukkunna."

Murmushi yayi, sannan yace,
"Mami tin bayan dawowata befi sau biyu muka hadu ba! Shekaru biyar baya."

Kai Mami ta jinjina. ta ce,
"Lalai to baka ga yadda *Najwa* ta koma ba. Sak irin yarinyar da kake son aura. Dan *Najwa* akwai ilimi hankali, nutsuwa, ai dai kasan ko wace Mamin *Najwa* kuma kasan irin tarbiyyar da yake baku."

"Gaskiya ne Mami amman ni *Najwa* a kanwa na dauke ta."

"To shikenan Allah nuna maka waccen din."
"Ameen!"

"Tashi kaci abinci. Dan Mamin *Najwa* kamar tasan zamuzo tayi abinda kake so."

"Mami me ta dafa mana."
"Duba kaga."

Da sauri ya janyo fulas din, ya bude. Wata ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idon sa ya sauka kan masar da tayi.

Murmushin fuskar sane ya dadu, sannan ya zuba yace, Mami tazo suci.

Ta koshi tace masa, haka ya ci abincin duk ransa ba dadi duk yadda ya kai da son masa kadan yaci ya mike.




*INDABAWA*

NAJWA*


By *Maryam S Indabawa*
*MANS*


*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻



DEDICATED TO *ANTY RASH KARDAM*

Page *86-90*

Kayan Kwalliya Mamin Najib ta kaiwa Najwa da su turaruka masi tsada da kamshi.

Basma ce ta shiga dakin *Najwa* ta ce,
"Adda karatu kike yi."

"Eh Basma.ο»Ώο»Ώ yauwah Basma biyo min karashen karin ku na yau."
"Wanne Adda."

"Na tauhid."
"To Addah

"Su su'al:- Limaza kalakallahu?
Tambaya:- saboda me Allah ya halice ka.?

Ja jawabi:- Kalakani li'ibadatihi
Amsa:- Ya halice mu ne dan mu bauta masa."

"Masha Allah."
"Adda dan Allah ki kara min kafin ki mana kari."

"To
Su'al: Tambaya

Kaifa ta abudullaha? : tayaya kake bautawa ubanhijin ka?

jawab: amsa
A'abuduhu, kama amara,: ina bauta masa kamar yadda ya umarce mu.

Wakama amara rasulillhi
Kuma kamar yadda Manzon Allah ya umar ce mu.""

"Ina nabiya ki biya."
Haka suka dinga yi har sai da Basma ta iya.

Mami dake tsaye a bakin kofa tace,
"Toh *Najwa* Mecece Najasa?"

"Mami a cikin fikihul miyasar, malamin yana cewa,

"Najasa:- Fitsarin mutum, da bayan gidan sa, da wadihi, da maziyu, da jinin haila, da na nifasi, da yawun kare, da fitsarin abinda aka haramta cin sa, da kashin sa, da matattaun dabobi na kan kasa, me jini. sune najasa.

Sannan Fitsari bayan gida, waziyi da wadihi, sune abubuwan da in kayi su ko ka same su sai ka sake alwala. Su ake kira da karamin hadasi.

Janaba, da haida, nifasi kuma sune wadan da in ka same su sai kayi wankan tsarki. Su ake kira da babban hadasi."

"Menene janaba?"
Mami ta tambaye ta, bayan ta gama jawabin.

"Mami Janaba:- wata abace nau'i biyu.
1- fitar mani dan wata sha'awa da ta samu mutun a cikin bacci ko ido biyu. Shine janaba

2- ko kuma haduwar fatu guda biyu (haduwar farjin mace da na miji) idan an samu haka ko mutun be fitar da komai ba wanka ya wajaba a gareshi wannan ita ce janaba."

" *Najwa* da akwai, banbancin tsakanin fitsarin yaro karami da babba?"

"Eh! Da akwai, fitsarin yaro karami yayafi ya isar masa.Β  Sabanin na babba (Malam me fikihu ne yafada.) Wannan yana nufin fitsarin yar karami in aka yayafa ruwa ya isa. Na babba kuma sai an wanke."

"Na mata fa?"
"Mami Malam me fikihu miyasir yana cewa, ita mace ko da takasan ce ana shayar da ita tayi fitsati sai an wanke shi.
Manzon Allah (SAW) Yace, " Fitsarin yaro karami yayyafi ya isar masa. Fitsarin yarinya karama a wanke shi."
Turmizi ne ya rawaito shi."

"Shin Mani najasa ce."
"A'ah Mami. Mani ba najasa bace. Dan akwai wani lokacin da Nana Aisha in ta samu mani a tufafin Manzon Allah (SWA)Β  Take kankare shi da farcen ta, kuma yasaka kayan yaje yayi sallah. wannan yana nuna kenan Mani ba najasa bane.

Sannan Nana Aisha tace, akwai lokacin kuma da zata sa ruwa dan kawar dashi, kuma ko be bushe ba, Ma'aiki (SWA) Yana sakawa yayi Sallah dasu.

Mami in har da Najasa ce, sai Manzon Allah ya tabbatar da an wanke su.

Akwai hadisin da Manzon Allah (SWA). An karbo daga Jabir dan Samrata. Yace,
"Wani mutun ya tambayi Manzon Allah (SWA) shin zan iya sallah da tufafin da najewa iyali na.
Sai Manzon Allah (SWA) yace,
"Eh sai dai in yaga wani abu a jikin sa. Sai ya wanke." Ibn maja ne ya rawaito shi.

Fadin malamai da yawa wasu sunce mani ba najasa bace, wasu kuma sunce najasa ce. Allah shine mafiyin sanin gaskiya."

Salim ne ya karaso dakin. Yace,
"Mami wallahi kun bar mu da yunwah."

"Ayyah kuyi hakuri ban san kun sauka kasa bane. Gamu nan."

Salim ya ce,
"Mami ai sai nasa ku a gaba. In ba haka ba nasa baza ku taso ba."

Murmushi *Najwa* tayi, ta ce,
"Mami tashi muje an bar Dady da yunwah."

Ta fada tana kama hannun Mamin tata. Mikewa tayi suka sauka kasa dan cin abinci.




*-*-*-*-*-*-*-*
Karfe goman dare.

Cikin sanda take shiga cikin gidan nasu. Muryar Mama taji tana cewa.
"Zo nan."

A firgice ta juya tayi wajen Maman tata. Mama ta ce,
"Sumaiyya wai me kike yi haka ne, yanzu karfe nawa?"

Shiru Sumaiyya tayi. Mama ta cigaba da magana
"Ace kina mace ki kai karfe goman dare a waje wannan ai ba mutunvin ki bane. Ba wani dalili sai na yawo da har zaki kai karfe goman dre a waje."

Sumaiyya baki da turo gaba ta ce,
"Mama kiyi hakuri."

Mama ta girgiza kai, ta ce,
"Sumaiyya ki canja hali ki sani ke mace ce, yan da kyu kina yin tsafta da sanin abinda kike. Amman ke kullim yawo shine a gaban ki dn kinga Abban ku na kyale ki ko. Tashi ki bani waje."
Daki tayi tana mita.

Dakin ta Sumaiyya ta shiga, kaca kaca da shi, daga ledar biskit sai ta alawa, sai kwalon lemo.

A haka ba tare da ta kawar da komai ba, ta hau kan gadon da ba gyara ba komai ta kwanta.

Tunanin irin shigar da zatayi a bikin da zasu yi take dan tasan Bashir babban mutum ne ko zata samu itama mijin aure.

Sumaiyya bata da buri sai na tayi samari wadan da zasu na kashe mata kudi. Samarin ta yawa ne dasu haka nan kuma, kowa tatsar sa take, amman ba duk da haka bata barin ayi wani abu da ita.

Sai dai shigar banza, da son kudi. Sumaiyya ba abinda ta iya. Dan ko gyaran daki ma bata iya ba bare yin girki.

Kan ta sai yayi wata a kitse bata tsefe ba, ko zata tsefe sai dai taje saloon a tsefe a wanka mata wani lokacin sai yayi wata zata wanke.

Kaya kuwa duk da tana da masu wanki amman kafin ta dauka ta bayar a wanke aiki ne a wajen ta.

Sai dai tai tayin sabon dinki. wannan halin sumaiyyan na damun ta maman ta.

Duk yadda taso tasata a hanya abin yafi karfin ta. wannan yasa ta hana masu musu aiki gyara mata daki a ganin ta zata na gyara wa amman ina ba ruwan ta haka take rayuwa a dakin duk datti da kura.

Addu'a kuwa Mama bata fasa ba na kan Allah ya shirya mata yarinyar ta.

Ga wani girman kai da Allah ya daura mata. Dan ko ya'yan yan uwan Mama duk bata son su ko magana bata hadasu. Ko dan Allah ya rufa musu aisri ne ko mene ne oho.

Duk fadan da Mama zatayi sai tace ai ba sa'anin ta bane yaran da ta basu shekara wajen bakwai tayaya zatayi mu'amala dasu.




*INDABAWA*

NAJWA*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻



PAGE *91-95*

.DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*



Yanzu abin har ya zaman masa jiki dan sai dai bai kwanta bacci ba amman mafarkan ta zai tayi. Yaga sunyi aure ko ya gansu a tare dai.

Najib ya rame saboda ba shi da kwanciyar hanakali. Burin sa kawai yagan ta kullum cikin bulayi yake amman sam bai kara gani ko me kama da ita bane.

Mami ma duk hankalin ta ya tashi dan gani yadda yaron nata ya koma, abin tausayi.

Yau Tin safe Khaleel ya je gidan su Najib dan ranar juma'a za ayi dinner abokin su, kuma ranar asabar daurin aure da kai amarya.

wannan yasa yazo dan yaji Najib din shiru kwana biyu.

A dakin Mami ya zauna, bayan zun gaisa yake tambayar ta Najib. Tace masa yana dakin sa.

Yayi mamakin yadda Najib bayaΒ  daki Mami kuma na dakin ta, dan ko da yaushe Najib na makale da Mami sai da kyar yake barin gefen ta.

Dakin ya shiga, yayi tsamamanin ma wanka yake shi yasa ya bar Mami ita kadai. amman sai ya ganshi a zaune, ya zubawa taga ido.

Salama yayi tafi sau uku amman Najib be san ana yi ba. Cikin dakin Khaleel ya shiga.

Sai da ya dafa shi sannan yasan ya shigo cikin dakin.

Juyowa yayi a Firgice. yana kallon sa. Murmushin yake ya saki. Ya ce,
"Dan uwa kai ne."

Kallon sa Khaleel ya tsaya yi, "Najib lafiyar ka kuwa."

Mikewa yayi ya kamo hannun sa. "Lafiya kalou me ka gani."

"Naje dakin Mami naga baka can, abinda ko da yaushe kana gefen Mamin ka, gashi nazo na same ka kana tunani abinda ban saba gani daga gareka ba, gashi duk naga ka rame."

"Khaleel kenan, wanka nazo nayi shi yasa baka sameni a dakin Mami ba, tunani kuma yanzu ya fado min shine nake yi, rama kuma ban dan jin dadi ne."

Khaleel ya zuba masa ido. Sannan yayi wani murmushi. Ya xe,
"Najib wanene ni a gunka."

Najib ya dube shi, "Me ya kawo wannan tambayar."

Khaleel ya girgiza kai. Ya ce,
"Malam ban amsa ta."

Najib yayi murmushi ya ce,
"Kai bababn abokina ne kuma na dauke ka a matsayin dan uwa na."

"Indai haka ne. To Dan Allah ka fadan damuwar ka, kasan nasan komai game da kai. To ban yadda da abinda ka fada min ba yanzu."

Zama yayi a kan gado ya dafe kansa. "Dan Uwa wallahi bana son ina tuno abin ne."

"Dan Allah daure ka fada min ko zan iya taimaka maka. In bazan iya ba nasaka a addu'a."

Numfashi yaja,Β  "Bro kasan matsala ta. ta farko, ina da bukatar aure, dan wallahi har magani ya kusan fara kin karbata,"

"Wannan me sauki ne, ka samo mata a cikin masu sonka."

Najib ya dan bata fuska ya ce,
"Kai ma kasan irin matan da nake so ai. Duk masu sona babu irin su."

"Zan tayaka nema wannan. Sai kuma me?'

"Kasan me ya kara dawon da wancan abin kuwa?"

Khaleel ya girgiza kai ya ce
"A'ah!".

Nan ya kwashe gamuwar sa da yarinyar nan da irin rashin kwanciyar hankalin da yake shiga.

HannunΒ  Khaleel ya kamo. Yace
"Bro, yawan mafarken da nake da ita shi ya kara kawon sabuwar sha'awar aure. Wallahi."

"Innalillahi wa'inali lahir rajiun. Bro Allah kawo mana dauki, Amman duk da haka zamu cigaba da neman ta, amman baza mu zauna haka ba, gara ka fara aure dan matsalar nan taka ta ragu."

"Anya zan iya kuwa inba wannan yarinyar ba."
"Bro kar fa dai ko gamo kayi."

Duka ya kai masa.Β 
"Wane gamo, mutun ce,"

"Toh Allah yasa."

Harara sa yayi, sannan yace,
"Ameen."

Dariya Khaleel yayi,ya ce,
"da kar kace Ameen din man."

"Yasu Momy da Yasmeen."
"Suna lafiya."

"Ina Anty, Suraiyya kuwa, wallahi na dade bamu yi waya ba."
"Tana nan basu dade da dawowa daga Makkah ba."

"Ina sudais din ta kuwa ya girma ko."
"Sosai ma kuwa."

"Insha Allahu kafin mu koma zan je na gaida ta."
"Allah yasa. Tinda kai yanzu mace ta dauke mana kai sai lokacin tunanin ta kake dashi baka da lokacin mu."

"Wa ya fada muku."
Sukayi dariya.

"Kai wajen Bashir zamu fa."
"Me zamuyi."

"Malam gobe fa yan mata zasuyi kamu."
"Ni nazan je wani kamu ba."

"Amman toh saboda me."
"Mata zasuyi yawa."

Driya Khaleel yayi, ya ce,
"Toh tsoron mata kuma ka fara."

"Haba dai. A'ah saboda tsaro dai."
"Kaji dashi dai. Kasan jibi dinner, gata daurin aure da kai amarya."

"Allah kaimu."
"Ameen! Tashi muje."

Najib ya mike, ya ce,
"To!"

Khaleel ma mikewa yayi
Dakin Mami sukayi.

Mami na gani su tayi murmushi. Ta ce,
"Son Ina kuma zuwa."

Khaleel ya ce,
"Zamu wajen Bashir ne."

"Sai kun dawo. Ku gaida Momyn sa."
"Zataji."

Suka fice. Tana me jin dadin ganin canjawar yaron nata. Wannan yasa take kara son Khaleel dan aboki ne na gari.

Dan taaan shi ya yi sanadin sanya yaron nata cikin farin ciki.




Summy ce zaune wajen me lalle, ana cire mata lalen da akayi mata,
Lallen yayi kyau sai kace a kafar aka hallice su tare.

Summy ba dai kyau ba, fara ce, tana da idanu sai hanci wanda yake a dan bude daga karshe.

Tana da kirar jiki me kyau, bata da tsayi, kuma jikin ta in yasamu hutu kara budewa zeyi.

Mikewa tayi ta bawa me lalle kudin sannan ta tafi saloon dan ai mata kitso.

Tana zuba zubby me mata kitso ta farai mata kirari. Tana cewa,

"Kaga hajjaju, manyan mata matar manya, matar me kyau da kudi, Allah ja da ranki, Allah yasa wannan kitson ya kawo mana miji har gida."

Ido take jutawa tana wani jijiga jikin ta.
"Ameen Zubby ya kuke ya gidan?

"Lafiya."
"Kina da attachment dai ko?"

"Eh akwai, guda nawa za ayi miki dashi."
"Kananu nake so. To ranki ya dade."

Ta bude kanta, da niyyar tsefewa. Ta ganshi a tsefe ta ce,
"A'ah Summy ya naga yau har kin tsefe kan nakki."

"Oh kedai bari, wallahi Mama ce jiya ta zaunar dani na tsefe shi."

"Toh Mama da kanta."
"Kedai bari, ita ta wanken shima."

"Mama na ji da ke."
"Tab baki san da azabar da ta wanke min bane."

"Jin fatar kaina nake kamar an tsatsaga min. Dan dirje min tayi sosai."

"Sannu."
"Yauwah. Kuma fa wai kar a samin gashi tace, ni da zamiyi biki ai dole sai an min kari."

Zubby ta ce,
"Ah gaskiya kuwa."
Suna kitso suna hira. Zuvby na kara tunzura ta.




*INDABAWA*

NAJWA*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

PAGE *96-100*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTU RASH KARDAM*



Kamar ko da yaushe, sun dawo daga makaranta tare da kanwar ta, hannun su rike da na juna.

Kanta a kasa take tafiya dan ta tsani kallo. Duk da ta saka Nikaf.

Basma ta take tayi mata surutu. Hannun ta, ta rike.

Shiru Basma tayi. Sai da suka shiga cikin gidan su sannan ta kalle ta.

Ta ce,
"Haba Basma sai kace ba mace ba. Mace fa an santa da yanga da jan aji. Amman muna tafiya kina ta surutu."

Kallon ta Basma ta tsaya yi. Basma tana son Yayar ta, kuma tana burgeta kome nata a tsare da hankali take yin sa.

Idon ta *Najwa* ta hure da bakin ta.

"Tunanin me kike ina miki magana?"

Murmushi Basma tayi, sannan ta ce,
"Wallahi Adda kina burge ni."

Murmushi itama *Najwa* tayi, ta ce,
"Shige muje daga ciki."

Suka shige bayan sun gaida Baba Me gadi.

Mami kamar kullum na zaune akan sallaya tana lazumi.

*Najwa* ce ta fara mata sannu da gida sannan Basma da ta haye kan kafar ta.

Kallon ta *Najwa* tayi. Ta ce,
"Basma kedai bakya girma tashi muje ki cire kaya kiuo alwala."

"Toh."
Basma ta fada tana mikewa.

Bayan *Najwa* tayi da tayi bene.




Zaune yake gefen Mami yana aiki cikin laptop dinsa.

Sanye yake da dogon wando, baki, sai farar riga me dogon hannu, idon sa sanye da gilashi. Sai tashin kamshi yake. Ke kace unguwa zashi ko wajen budurwa.

Mami ce ta mika masa lemin da ta tsiyaya masa a kofi.

Karba yayi ya sha. Sannan ya ce,
"Mami gobe ne fa mothers even din Mamin Bashir."

"Ban manta ba. Allah kaimu. Zaka kaini ai."

"Momyn Khaleel ma zata je fa."

"Ah toh ai da sai ka. Kaimu gaba daya ko."

Kallon Mami yayi,Β  "Kinsan kuwa ranan ta zo."

"Yaushe?"
"Ranar da mukaje gidan su Abbah."

"Amman ban ji dadi ba. Gashi ni ban je mata ba."

"Ran juma'a na kai ki ki wuni, tinda sai Monday zamu tafi."

"Allah kai mu, ranar asabar zanje gidan, Ummah, lahadi naje wajen su Mamah."

"Ummah kuwa ta ce, naje tayi min dambu."

Fuska Mami ta bata, "Najib ka kiyaye ni fa da sa min iyaye aiki wallahi."

Dariya yayi, ya ce,
"Haba Hajiyata. Ina wani aikin yake."

Fuskar ta a hade dai. "Baka ji ko?"

Dariya ya kuma yi. Ya ce,
"Yi hakuri da wasa nake, yimin zata bayar ayi."

Murmushi tayi, "Wai Najib ka mai dani kakar ka ne ko?"

Ido daya ya kanne, ya ce,
"Toh ya zanyi tinda kin hanani jan kakan nin nawa."

Murmushi tayi ta dauki remote tana canja channel.

Shirun da suka samu, yasa ya lula tunanin Yarinyar da ta hanashi sukuni. Wacce kullum sai yayi mafarkin ta.

Kullum tana cikin ran sa. Be da buri da ya wuce ya ganta. Ajiyar zuviya ya sauke. Sannan ya cigana da aikin sa.

A ransa yana mamamkin yadda Allah yasaka masa son wacce be santa ba daga kallo.

Lalle ya kuma jin tsoro da kara gaskata lamarin Ubangiji.

Parking mota yaji ana yi. Labulen dakw gefen sa ya daga. Murmushi ya saki. Yana mikewa.

"Mami gasu ango nan."

Itama Murmushin tayi, dai dai lokacin da suka shigo dakin tare da Khaleel kenan.

"Mami ina yini?"
Bashir ya fada yana dukawa har kasa.

Cikin fara'a maami ta amsa masa,
"Lafiya lou yasu Monyn taka."

"Murmushi yayi, ya ce,
"Suna lafiya."

Khaleel ne ya koma kusa da ita, ya ce,
"Mami ina yini?"

"Lafiya lou Khaleel. Yasu Momy taka."
Ta amsa masa,

"Suna.nan kalou."
"Ashe ranan tazo ba ma nan."

"Wallahi Mami."
"Wallahi kaga yaron nan sai yanzu yake fada min ma."

kitchen taje ta sa Jummala ta kawo musu lemo da abin tabawa.

Sannan ita kuma tayi bayan gida.

Jummala ce ta kawo musu lemo, da nama da meat pie a gefe.

Najib ne ya tashi ya zuba musu lemon a kofi, sannan ya kuma ya zauna.

Kallon Bashir. Ya ce,
"Ango Ango."

Gira Bashur ya dage masa, ya ce,
"Kai dai bari na kusa shiga sahun manya na barku abaya."

Khaleel ne yayi dariya, ya ce,
"Mu dai barshi."

Hararar sa Najib yayi, "Mene a ciki to."

"Ai kam da komai a ciki. Malam zamu samu nutsuwa mu kara hankali fa."

Dariya Najib yayi, ya ce,
"Da baka da nutsuwa da hankali ne."

Murmushi Khaleel yayi, ya ce,
"Malam ba irin wacce kake tsammani ba ce."

Bashir ya ce,
"Yauwah aboki fada masa dai."

Dariya Najib yayi, ya ce,
"Malamai bana son iska ci kuma."

"Ina jin fa Najib be da lafiya ne."
Bashit ya fada da tsokana.

Dariya Khaleel ya sheke da ita.
"Tab wannan ai duk nan ya fimu lafiya in dai ta wannan fannin ne, na fada maka yanzu magani ma yana son daina karbar sa."

Folon dake gefen sa ya dauka ya cilla masa.

Karewa yayi yana dariya ya ce,
"Karya nayi ne?"

"Wallahi Bro sai nayi maganin ka."

Driya Bashir yayi, ya ce,
"Toh ko sai mun nemo masa mata ne."

Dariya Khaleel yayi! Ya ce,
"Ai shi macen da yake nema daban ce."

Bashir, ya ce,
"Ka fadan wace iri ya yake so. sai mu samo masa."

Najib ya rufe laptop din gaban sa, ya ce,
"Malamai bana so. Kasan kai ma na samu ai."

Driya Khaleel yayi, kawai. Ya ce,
"Ku tashi muje."

"Ina zamu,"
Najib ya tambaya.

"In munje ka gani."
Khaleel ya fada masa.

"Nifa banson yawo."
Najib ya fada

"Tinda Allah ya hadaka damu ai sai kayi hakuri."
Khaleel ya fada yana mikewa.

Shi dai Bashir dariya kawai yake., dan Najib da Khaleel na matukaw burge shi.

Bayan gida suka nufa inda Mami ke zaune.

Sallama sukai mata sannan suka fice.


*INDABAWA*

NAJWA*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*





DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

PAGE *101-105*.

Suna gama shirin su bayan sunyi sallar magariba suka, sauka kasa. Mami zaune akan sallaya tana jan carbi, suka karasa gefen ta.

*Najwa* ta ce,
"Mami sannu da gida ya aiki?"

Mami ta dubi *Najwa* cikin fuska me nuna so da kulawa tace,
"Lafiya *Najwa* ya karatun?"

"Alhamdulilah!"
"Allah taimaka."

"Ameen Mami."

*Najwa* ce ta kalli Basma ta ce,
"Basma Fara kawon haddar ki."

"To Adda!"
Basma ta fada tana gyaran muryar ta, karatun ta fara cikin kwarewa da fitar da ko wacce harafi da hakkin sa. Suratul Nisa'i take kawo mata hadda.

Sai da ta kawo mata shafi uku sannan ta tsaya.

Mami ta dubi Basma ta ce,
"Masha Allah Basma, kamar bake kika karanta ba. Allah kara basira"

"Ameen Mamai!"
Suka hada baki suka fada

" *Najwa* a ko da yaushe zaki ga nafi miki magana akan fikihu, ba kome yasa nake miki ba sai dan inganta rayuwar ki, dan sai da tsarki da ibada rayuwa rake yiyuwa. Kuma haka nan ibada bata yiyuwa sai da tsarki da ilimin fikihu."

*Najwa* tayi kasa da kai, ta ce,
"Haka ne Mami. Shi daman fikihu ai ilimin rayuwa ne. Duk abubuwan mu na yau da kullum na ibada yanaΒ  cikin sa. Allah abamu sani akan sa da kuma amfani dashi."

"Ameen! Shin daga ina ake kawar da Najasa?"
Mami ta tambayi *Najwa*

"Ana kawar da Najasa daga waje 3,
1. Daga jiki, Allah madaukakin sarki yana cewa, "in kun kasance masu janaba kuyu tsarka."

2. Daga Jikin Tufafi. Allah Mabuwayi da daukaka yace, "Tufafin ka, ka tsarkake shi."
Akwai hadisin da aka rawaito daga Subarata Allah kara masa yadda, ya ce, "Wani mutum ya tambayi. Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi, ya ce,
"Shin ze iya sallah da tufafin da

Please Login or Register in order to submit comment