Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yajewa iyalin sa?"
Anbabi (SAW) Yace, "Eh! se dai yaga, wani abu na najasa shine ze wanke."
Ibn Maja ne ya rawaito.

3. Daga wajen da za'ayi Sallah. Allah mabuwayi da daukaka, Yana cewa,
"Munyi alkawari zuwa ga Annabi. ibrahim, da Annabi Isma'il, dasu tsarkake dakin Allah, dan masu dawafi, da masu ittikafi, da masu ruku'i da sujada.

Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi yaga wani balaraben kauye, yana fitsari a massalaci, sai ya ce da sahabai su kyale shi! Har se da ya gama fitsarin sannan ya ce, a kawo masa ruwa. Sai ya kwara."

*Najwa* ta kalli Mami ta ce,
"Mami daga waje ukun nan ake kawar da Najasa."

Mami ta jinjina kai, dai dai lokacin sukajiyo horn din motar Dady.

Da gudu Basma ta fice, tana cewa,
"Dady oyoyo! Dady Oyoyo!"

Yana ganin ta ya Bude hannu ya daga ta sama.

Dariya take, tana farin cikin dawowar Mahaifin nata.

*Najwa* ce, ta karaso wajen ta ce,
"Dady barka da dawowa."

"Yauwqh Maman ya gida!"
"Lafiya Alhamdulilah. Ya aiki."

Dady yace,
"Alhamdulilah!"

Ta karbi jakar hannun sa tayi wajen Hamma Salim.

Ta ce,
"Hammana kun dawo lafiya?"

Murmua
shi Hamma Salim yayi mata, ya ce,
"Lafiya lou kanwata."

Fuska ta dan hade, ta ce,
"Hamma gashi har ka kusa tafiya, amman ko zama bama yi."

Dariya yayi, ya ce,
"Yau kuma darun ne ya tashi. ai nazata yanzu kin girma."

Murmushi tayi, ta ce,
"Ina maka magana kana kawon wata magana ko?"

Murmushi Hamma Salim yayi, ya ce,
"Yi Hakuri yar uwata, kar ki manta fa sauran shekara daya na gama na dawo gaba daya."

"Shikenan!"
Ta fada dai dai lokacin da suka shiga m Falon gidan.

Mami ta mike, tana musu sannu da zuwa.

Daining sukayi dan yau sunyi dare a waje.

Abinci suka ci sannan kowa yayi dakin sa dan yin bacci.

Kamar ko da yaushe sai da ta saka Basma tayo alwala sannan ta zo ta kwanta tana me ambaton sunan Allah.

Sai da taga ta gama ta fara bacci sannan ta mike tayo wanka ta dauro alwala ta zauna karatun alkur'ani.

Ba ita ta kwanta ba sai karfe sha daya. Inda karfe biyu nayi ta mike tayo alwala tayi sallah. Ta jima tana addu'a sanna ta kuma kan gado. Karfe biyar da rabi ta tashi ta tashi kanwar ta sukai raka'atanil fijir sanna suke sallar asuba.

Zikirin Safiya sukai sanan suka fara, Karatun kur'ani, shida da rabi *Najwa* ta hadawa Basma ruwan wanka, ita kuma tayi kasa ta daura musu abin karin su.

Tana gamawa ta jere sannan ta hadawa Basma nata. Sama ta haye, ta karasa shirya Basma sannan ita ma ta shige ban daki dan yin wanka.




Najib ne zaune a dakin sa, yana tunanin nasa da ya saba.

Karar wayar sa ne ya dawo dashi cikin hayyacin sa, yana dubawa yaga Khaleel ne, dauka yayi. Ya ce,

"Dan Uwa ya akayi ne?"

Khaleel ya ce,
"Eh nace ka dai shirya ko?"

Murmushi yayi, ya ce,
"Eh kai nake jira."

"To gani nan zuwa."
wayar ya ajiye ya mike ya shiga bandakin sa, dan yin wanka.

Ya jima a ban dakin sannan ya fito ya shirya cikin wata milk din shadda wacce akai mata aiki da ruwan kasar zare.

Yar ciki da babbar riga sai ruwan kasar takalmi da hular kan sa ruwan madara da adon ruwan kasa.

Yayi kyau sosai kai kace, shine ango sai tashin kamshi yake, farin tabaron sa ya. Dauka ya saka a idon sa.

Take ya kara haskawa ya kuma wani kwarjini.

Masha Allah Najib ba dai kyau ba. Duk inda kyau yake, yakai dan cikaken namiji ne me kamala da kwarji.

Yana shirin zama sai ga shigowar Khallel nan. Kallon sa ya tsayayi, ya ce,
"Abokina ka yi kyau, kar fa kafi ango yin kyau "

Harara sa Najib yayi, ya ce,
"To zage ni."

Dariya Khaleel yayi, ya ce,
"Malam bamu da lokaci kalli fa har mun makara abin karfe takwas yanzu karfe tara. Kuma kasan no african time."

Najib ya ce,
"Bro ai kai ka makarar damu. Dan a shirye ka ganni. Malam shige muje."

Suka fice, Najib na tsokanar sa, kyan ta, Khadija taga kwalliyar sa.

Dakin Mami suka je suka mata sallama sannan suka fice a motar Najib


Summy ana gefe anci kwalliya cikin wani golding din material sai maroon din head da ta saka. Tayi kyau sosai, an zubo da gashi ta gadon baya.

Wajen ya cika da manyan yan mata da samari daga wannan tace tafi wannan sai wacan tace tafi wacan.

Amman Summy na data daga cikin yan matan da sukafi kowa kyau a wajen.

Dan Samari da yawa sai kai mata hari suke amman sam ko kallo basu isheta ta ba,

Amarya da Ango kuwa suna wajen da aka tanadar musu a zaune, sunyi kyau, cikin wani farin material me adon baki! Shi kuma Angon yasa bakar shadda.

Ba karamin kyau suka yi ba.

A hanya ma suna tafiya suna hira abin su, har suka karasa Wajen bikin.


*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


*By Maryam S Indabawa*
*MANS*

Page 106


Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Aunty Rash*





Khaleel ne yake tsokanar Najib! Cewa yau fa sai ya samo masa budurwa

Dariya Najib yayi kawai dan yasan Khaleel tinda ya daura niyyar samo masa dan fitar dashi daga damuwar da yake se ya samo masa.

"Kayi shiru?"

Najib ya kalle shi. Ya ce,
"Me kake son nace,"

Khaleel ya kalle shi, ya ce,
"Kana son kace ka aminci "

"To ya zanyi ai dole na amince dan nasan halin ka."
Hannun sa ya dauke daga kan motar ya tafa su.

Ya ce,
"Ina son ka dan uwana."

Murmushi Najib yayi, ya ce,
"Wannan a jinin mu yake "

Khaleel ya dage gira ta ce,
"Tabbas."

Dai dai lokacin suka isa wajen. Ya fito sun tafiyi a tare, suka nufi hall din.

Hall din ya cika da hadaddun yan mata da samari. Amman shigar su Najib sai kallo ya koma sama. Dan daga mazan har matan duk sai da suka yaba da Najib.

Duk da shi ba fari bane, amman kyakywa ne, kasancewar sa bafulatanu. Haka maka Khaleel kyakyawa ne, amman shi fari ne.

Tafiya yake cikin iska da takama, har suka isa inda aka tanadar musu.

Yan mata da yawa ya dauke hankalin su, a ciki harda Summy wacce tsabar girman kanta duk yadda taji ana maganar gayen bata dago ta kalle shi, sai danna watar ta da ta cigaba dayi.

Suna Zama, Khaleel ya fara zuba ido dan ganin, ta inda ze samowa abokin nasa matar aure.

Cikin kalle kallen sa, idon sa ya fada kan Summy dake can gefe, tana ta basarwa, ga maza se zuwa suke amman ko kallo basu ishe ta ba.

Wanna yasa yaji yarinyar ta kwanta masa. MC ne ya fara jawabi cewa manyan abokan ango sun zo, dan haka ana musu barka da zuwa

Sannan yana son ganin ango da amarya a fili. Kai Najib ya dago yana kallon abokin sa Bashir.

Yayi kyau murmushi ya aika masa dashi. Sanna suka fito tsakiyar fili.

Anan ne MC yace, wannan fili na Manyan Aboka nan ango ne, Khaleel da dan uwan sa Najib.

Murmushi Khaleel tayi, ya ce,
"Tashi muje,"

Hararar sa Najib yayi, ya ce,
"Wannan filin zanje, ai ta kallon na sai kace TV."

Dariya Khaleel yayi, ya ce,
"Wai meyasa kwanan nan duk ka canja. Yau ka fara shiga cikin mutane ne. Dan Allah ka tashi kar mu bashi kunya."

Ba yadda Najib ya iya haka ya mike, suka shiga fili hoto aka farayi musu, sanna suka fara wa Bashir da amaryar sa likin yan dubu dubu.

Suna gamawa suka koma wajen su, akai serving nasum lemo kadai Najib Ya sha.

Kawayen Amarya akayi kira, dan nuna mata kara suma, Summy da wata Aisha aka kira, inda suma sukai musu nasu likin.

Kan Najib a kasa, dan ji yake duk ba a sake ba, dan gani yake da ya ga yan matan nan zata iya masa gizo yazo yana jin kunya.

"Bro kaga wata yarinya da nayi maka kamu."

Kai ka dai Najib ya jinjina.
"Bro Wallahi da gani zatayi maka. Dan baka ga yadda maza ke neman ta kula su ba amman taki."
Dago kai Najib yayi ya kalle shi. Ya ce
"Ni dai na baka wuka da nama."

Dariya suma yi.
Khaleel ya ce,
"Nagode!"

"Dame?"
Najib ya tambaya

"Da ka bani dama."
"Kaji ka. nike da godiya ai."

Suna zaune, har karfe goma tayi, agogon hannun sa Najib ya duba, ya kalli Khaleel ya ce,
"Dare fa!"

"Nagani, yarinyar nake son ta tashi ta fita "
"Yanzu har sai ta tashi zamu tafi."

"Haba man Najib."
"Naji. Amman bari naje mota in ka ga fitar ta ka taho, dan hayaniyarΒ  tayi min yawa "

Ya fada yana mikewa. Wajen Ango yaje, ya duka gefen sa. Dai dai lokacin da Summy ta dago kan ta kenan.

Ya Salam!
Ta anbata a zuciyar ta dan gani tayi ya wuce inda taji ana yabar sa. Kasa dauke idon ta tayi daga kansa.

Tana kissimawa dama wanna mijin tane, da ta huta dan daga gani hutu da jin dadi. Hadi da ilimi sun zauna.

Magana yake masa
"Friend kayi hakuri zan dan fita hayaniyar nan ta fara sa min ciwon ka."

Bashir yace,
"Ba komai. Allah sauwake."

"Ameen! Ya fada, ya kalli Hauwa, amarya yace,
"amarya sai gobe in munzo."

Kasa tayi smda kanta. Tace,
"To nagode!"

Ya sauka ya cigaba da tafiya sa cikin takun kasaitar sa.

Summy kusa sandarewa tayi, dan yadda yake magana ma avin kallo ne ga takun sa na jan hankali da birgewa.

Take taji duk yadda ta dauki kanta ta raina, dan ta gefen ta ya wuce amman be san ma da wata hallita Ita a wajen ba."

Yana fita ya shiga mota ya kwantar da kujerar ya kanta akai. Tunanin yarinyar ya tafi.

Tin bayan fitar sa daga wajen taji duk wajen ya isheta, mikewa tayi, ta fice, ganin haka yasa Khaleel zuwa yayi wa Bashir Sallama.

Yana fita kuwa ya hange ta zata shiga motar ta, da sauri ya karasa wajen ta.

"Sannu yan Mata!'
Khaleel ya fada yana murmushi

Murmushi ita mata, ta amsa masa da yauwah.

"Dan Allah in baza ki damu ba number ki nake so."

Kallon sa tayi, ta ce,
"Number kuma!"

Murmushi yayi, ya ce,
"Eh ita kar ki Damu ba wani abu bane."

Kamar bazata bayar ba kuma sai ta bayar. Sukai sallama ta shiga motar ta, shima ya tafi wajen Najib suka tafi gida.

Tin a hanya ya fara tsara mata kalaman da zata amince da abokin sa, tare da tura mata hoton sa.

lokacin Summy bata Online, dan haka ya bar mata sakkon in ta hau ta gani.

Ranar a gidan su Najib ya kwana.

Summy na zuwa gida bayan ta gama komai ta hau Online, message din Khaleel ne suka shigo ta bude tafara karantawa.

Da farko abin dariya ya bata, ganin wai bashi ne ke son ta ba yake ta tsara ta, haka, bata kara gigicewa ba sai da taga hoton Najib sannan ta mike zaune.

Da farko ta zata idon take mata gizo sai da ta mutsika su sannan taga dai da gaske ne,

Wani uban tsalle ta dukka tana dariyar samun nassara.

Kin maida masada reply tayi dan tana son ta dan ja ajin ta.

Shikuwa Khaleel ya kagu safiya tayi ya hau Online, yaga reply din da zata turo

Wanna yasa tin asuba ya hau, sai dai me ta hau taga komai amman ba reply.

Rasa yadda ze yi yayi, kamar ya kira yaga kuma asuba ce. Dan haka ya ringa Allah Allah safiyya tayi ya kira ta.

Shidai Najib sai kallon Khaleel yake ganin bin-bini ya duba waya ko zega tayo reply.

Shi Najib ma abin har dariya ya fara bashi.



*INDABAWA*

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *Maryam S Indabawa*
*MANS*


PAGE *107*





Ita kuwa Summy ranar bata tashi daga bacci ba sai karfe dayan rana. Sallah ma sai alokacin tayi.

Wanka tayo sannan ta shiga kitchen dan samun abinda zata ci. Dankali da kwai akayi musu sai kunun gyada. Diba tayi ta shige daki ko gaishe da iyayen ta bata yi ba.

Sai da ta cika cikin ta sannan ta dauko wayar ta. Hoton Najib ne akan wayar dan tana kallon hoton bacci ya dauke ta bata sami ba.

Wani murmushi ta saki tina mafarkin da tayi da shi. Data ta kunna ta hau online, tana duba messages.

Tana zuwa kan Khaleel taga messages nashi wajen guda ashirin. Dariya tayi ta bude, duk rokan ta yake da ta amince.

Ita kuma sai jin dadi take, ta kasa tunanin me ya hana shi wanda yake son ta yi mata haka. Ita dai kawai hankalin ta yayi wajen Najib din ke saka shi.

Sai da ta ja aji sannan tayi masa reply da.
"Haba Khaleel daga ganin sarkin fawa sai miya tayi dadi. Ban san ko shi waye ba haka nima ban san sa ba."

Turawa tayi ta sauka dan tasan yana ganin sakon ze dawo mata da amsa

Waya ta dinga yi da samarin ta wanda ta dauki wajen awa daya ko me suke fada oho.

Khaleel kuwa sosai ya shiga damuwa na rashin ganin bata hau online ba har dayan rana.

Kai kace shi ke son ta. Amman wannan abin duk abokin sa yake yiwa.

Shi kuwa Najib ba abinda ya dame shi sai na yarinyar da ya gani ta daga masa hankaki.

Wanan shi ake kira, son maso wani. Ita Summy ta macewa Najib shi kuma yana son wacce bata son yanayi ba.

Karfe daya suka tafi massalaci sukai sallah suna fito wa. Khaleel ya dauki waya ya duba amman har lokacin bata hau ba.

Sai da suka je gida suka ci abinci sannan ya kara dubawa sai a lokacin yaga sakon da ta turo masa.

Duk da sakon ba abinda yake nema ya sanar masa ba amman yaji dadi ganin ta dai hau har ta bashi amsa.

"Sumaiyyah ki yadda dani da kuma aboki na, abokin na mutum kirki ne, yan mata dayawa na son sa ba dan kyan sa ba kawai dan hankalin sa da ilimin sa both (dukka) yana da dadin mu'amala. Be kula yan mata, dan be son yaudara kuma a Shirye muke ko da kince mu fito."

Ya tura mata haka.
A kunne ta bar datar ta, dan jiran jin sakon sa. Yana shigowa ta fara ganin sa a notification din ta. Kin budewa tayi dan ta ja aji. Duk da zuciyar ta, ta kwadai tu da taga me ya rubuto mata.

Sai da ta bada minti goma baya sannan ta hau ta bude sakon. Murmushi tayi, ta ce,
"Nasan da haka dan daga gannin sa ma ya wuce duk tunanin me tunani."

Ta fada tana tura musu da sakon.
"Naji Khaleel amman kuma kasan ni wace da har zaku soni, kasan yaya nake, kasani ko ina da wanda nake so."

Khaleel kin sauka yayi tinda ya tura mata sakon ta kawai yake jira ta maido masa. Ko da sakon ya shigo ya duba sai ya kara nutsuwa da yarinyar.

Murmushi yayi ya tabo Najib.
"Aboki yarinyar nan fa ta hau."

Baki Najib ya tabe, ya ce,
"Ai naga alama tin da naga kana ta wani danne danne."

"Allah zakayi farin ciki da zabi na, bari nasa ta turo min pics nata."
Khaleel ya fda.

Ko kallon sa Najib beyi ba, bare yasa ran samun amsar sa.

Wayar sa ya dauka ya fara yi mata magana.
"Sumaiyya daga ganin ki ma nasa kina da hankali da tarbiyya, batun ko kina da wanda kike so kuna banga alama ba, dan nasan kema zaki so samun miji kamar Najib. dan na tabbata yafi wanda kike so in da akwai ma. Dan Allah ki yadda da mu.Β  Ba da yaudara muka zo ba."

Ko da Sumaiyya taga sakon dariya tayi, ta ce,
"Allah sarki ai nagama samun miji insha Allahu."

Wata ziciyar kuma ta ce,
"To in kuma bashi da kudi fa."

Dayar zuciyar ta ce,
"Ai daga gani ma yana da kudi. Ke ni ko ban da kudi ina son sa haka."

Ta fada tana sauka daga whatsapp din nata.

Shiru shiru yaga Reply amman shiru, wannann yasa ya kira Number ta, sai da tayi ringing sau biyu sannan ta daga.

"Ranki ya dade kar a gaji damu."
Ya fada cikin sanyin murya.

Murmushi tayi, ta ce,
"Ba komai. Ya kake?"

Dadin amsar da ta bashi yasa ya saki murmushi shima ya ce,
"Lafiya Alhamdulilah. Ya kika je gida."

"Lafiya!"
Ta fada a sharen nan.

Murya ya dan gyara ya ce,
"Amman yau zaki zo kai amarya ko?"

Summy ta ce,
"Wallahi, saboda Hauwa ta takura min se nazo."

"Ai kam ya kamata kizo, zan zo gida na dauke ki."

Dadi taji a ranta, amman a fili ta ce,
"A'ah nagode zan zo kawai."

"To shikenan. Anjima mayi magana ki huta lafiya."

Suna gamawa ta daka tsalle tana murnar babban kamun da tayi.

Shi kuwa Najib kallon Khaleel kawai yake, yana kara jin son sa a ran sa.

Khaleel da baya kule kule amman yau shi ake garawa duk da bashi ke so ba.

Dariya ya sheke da ita yana cewa.
"Bro ai ko, babyn taka bata wahalar da kai haka ba."

Harara sa Khaleel yayi, ya ce,
"Eh saboda naga ana wahalar da kai, shiyasa na dauke maka wannan wahalar kar abin yai maka yawa."

Fuska Najib ya dan hade, ya ce,
"Kai Ware!"

Dariya Khaleel yayi, ya ce,
"Naji."





*Najwa* ce zaune gefen Mami, rike da littafin fikihu tana duba shi. Ajiye shi tayi, Mami ta kalleta, ta ce,
"Ya dai?"

*Najwa* ta kalle ta, ta ce,
"Mami na gaji ne."

"Sannu toh, In miki tambaya daya man."

Gyara zama *Najwa* tayi, ta ce,
"Ina ji Mami!"

Mami ta fuskan ci, *Najwa* ta ce,
"Dame ake kawar da Najasa?"

*Najwa* ta ce,
"Mami ana kawar da Najasa da *ruwa* me kyau, Ubangiji madaukakin sarki, ya ce,
"Lalai mun saukar muku da ruwa daga sama, mai tsarki."
Tsarki da ruwa shi ake kira da Istinja'a

Ana kawar da najasa Da *kasa,* dan kawar da abinda ya makale na najasa, na jikin tufafin mata, ko takalmi, ko taimama.
An karbo hadisi daga Humadatu, Allah kara mata yadda,Β  ta ce,
"Ni na tambayi Ummu salama, matar Annabi tsira da amincin Allah sukara tabbata a gareshi.Β  Ta ce,

"Ni na kasance mace mai dagayen tufafi, kuma ina tafiya ta wajen Najasa, Sai Ummu salama ta ce,
"Manzon Allah tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya ce, "Abinda yake bayan sa an tsarkake shi."
Abu dauda ya rawaito shi

Wannan yana nufin abinda ta tako na najasa in tabi ta kan kasa to kasar ta tsarkake shi.

Manzon Allah (SAW) ya ce, "idan dayan ku ya tako najaa a takalmin sa, hakika kasa mai tsarki ce a garshi."
Wato kasar ta tsarkake abinda ya kwaso.

A wata ruwayar kuma, idan dayan ku yaga najasa ko datti a takalmin sa, ya goge shi a kasa, shine ya bubuga su da kasa.

Annabi tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi ya ce,
"Yaga wani mutum janaba ta same shi, kuna babu ruwa sai ya ce, tafi kayi tsarki da kasa hakika ita ta isar naka
(Wato yaje yayi taimana. Amman ko yayi indai ya samu ruwa sai yayi wanka.)

Sai da *dutse* ko abibda zai tsayar masa, sunna ce amfani da da su. In mutun zai kawar da najasa da shi ya kasance wutiri wato uku, biyar, bakwai, tara, sha daya haka dai.
amman daga uku suwa sama dai.


An haramta yib tsarki da kashi ko kashin dabba, da dukan nin abinda aka haramta.

To Mami da wadan nan ake kawar da najasa.

*Masha Allah Allah kara ilimi."
"Ameen Mami na."

*INDABAWA*
[2/19, 9:13 PM] Maryam S Indabawa😍😘: *NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


By *Maryam S Indabawa*
*MANS*


PAGE *108*



Zaune take sai kwalkwale kwalkwal take, daga ta shafa wanan sai ta shafa wanca.

Tayi kyau sosai, tana sanye da wata jar atamfa me adon yellow da baki, an mata dinkin doguwar riga, ta yafa ruwan daurawar mayafi da takalmi da jaka. Sai tashi kamshi take.

Summy kenan yar yanmata me ji da kyau da kwalliya. Fitowa tayi daga dakin ta tayi dakin Mama.

Mama na zaune da kur'ani a hannun ta tana karantawa, ta shiga, gefen ta, ta zauna.

Kallon ta Mama tayi ta dauke kai, Summy ta ce,
"Mama zan tafi."

Mama ta kuma kallon ta, ta ce,
"Da zakina wannan shigar ai da kinfi zama kamilalla, ba shigar banza ba."

"Mama ai na daina."
Summy ta fada

"Allah yasa."
Mama ta fada

"Sai kin dawo."
Sumaiyya ta amsa, da toh.

Motar Dadyn ta dauka, ta nufi Unguwar su Hauwa.

Tana zuwa har an shirya amarya motar daukar ta kawai ake jira.

Zama Summy tayi a gefen ta, ta dan daga alkebar da aka rufe mata fuska da ita.

Hawaye taga ta na zubar wa. Baki ta tabe, ta ce,
"Haba Hauwa, mene abin kukan bayan wajen wanda kike so zaki je, sai kace ba ke kika zabe shi ba dan ya zama abokin rayuwar ki "

Wata Khadija kawar su ce, ta ce,
"Summy kukan rabuwa da gida take."

Summy ta ce,
"sai kace wacce zata mutu ko wani abu, abinda nan da yan kwana zata iya zuwa ganin gida. Dan Allah ki daina kukan nan kar ki bata kwalliyar ki man."

Ta janyo ta jikin ta tana lalashin ta tare da kwamtar mata da hankali. Da nuna mata wanda ta aura kuma yana son ta, ga jin dadin da zataje ta shiga

Ita dai Hauwa, bata ce komai ba sai hawayen da ke zuba a idon ta.


Khaleel ne yake ta fama shirin zuwa kai amarya, kallon Najib yayi, ya ganshi kwance akan gado idon sa lumshe.

Murmushi yayi, ya ce,
"Haba Guy ka tashi ka shirya mutafi."

Ido Najib ya bude wadan da sukaii jajawur dashi, ya kalli Khaleel.

Da sauri Khaleel ya matso kusa da shi, yana tambayar sa "lafiya?"

Mikewa yayi zaune, sanna yace,
"Bazan iya zuwa ba, anjima in naji dama dama ma raka shi, shima dan kar yaji haushi nane. Ya zabe mu bamu je ba."

Kai Khaleel ya girgiza, ya ce,
"Sannu to kasha magani."

Kai ya girgiza alamar A'ah.
"Bari na kawo maka."

Khaleel ya fada yana mikewa, hannun sa Najib ya kamo, ya ce,
"Tahon da lemon tsami a kitchen dan Allah."

Yayi maganar da kyar. Mikewa Khaleel yayi ya nufi kitchen ya dauko masa lemon tsamin, da wani magani, tare da ruwan sanyi

Amsa yayi yasha maganin sannan ya dauki, lemon tsamin ya fara sha, cikin kan kanin lokaci ya fara fitar da zufa sai wanda yake a cikin rana me zafi, duk da dakin akwai AC.

Marar sa ya rike yana juyi akan gadon. Wanda yafi minti ashirin yana fama da ciwon ganin haka yasa, Khaleel tafi daga dakin.

Motar sa ya nufa ya nufi wani chemist a unguwar ya amso masa allurar bacci ko ze sami sauki, tinda yasha maganin a banza.

Yana zuwa ya hada ta, yayi masa, nan da nan bacci ya dauke shi. Yana fitar da wani irin numfashi me karfi.

Zama Khaleel yayi a gefen sa, yana goge masa gumi da ya tsarsafo a kan goshin sa, ya jima yana kallon abokin nasa, yana tausaya masa halin da yake ciki.

Can ya suke wata nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya fara fitar da numfashin nasa a hankali a hanakali.

Bargon gefen sa ya rufa masa, sannan ya shafi kansa. Lokaci daya har ya fada.

Dan dole ze fita ya bar abokin nasa, kuma dan fitar ma samun, saukin abokin nasa ne, shiyasa ze fita amman da ba abinda ze fitar dashi.

Fita yayi ya nufi dakin Mami, Mami na zaune akan kujera tana kallo ya shiga dakin da sallama.

Amsa masa tayi cikin sakin fuska, gefen kafar ta ya zauna, ya ce,
"Mami zan fita amman yanzu zan dawo, dan zamuje raka ango anjima."

"To sai ka dawo. Ina Najib dan shi yake."
Mami ta tambaya.

"Bacci yake."
"Ok toh sai ka dawo."

"Toh" ya amsa mata da. Ya mike ya fita.

Daga nan gidan su Bashir ya nufa, a can suka hadu da abokan Bashir da zasu je dibar amarya.

Suna zuwa ba wacce Khaleel ke son gani sai Summy, ganin be ganta ba, yasa ya kira Number ta, sai da tayi ringing na biyu sannan ta dauka.

"Assalamu Alaikum Ranki ya dade. Kuna ina ne."

"Wa'alaikum salma. Ina gidan su Hauwa."
Ta bashi amsa.

"To dan Allah ki fito na kai ki, ko na samu lokaci kafin ki tafi."

Dariya tayi, ta ce,
"Kayi Hakuri na zo da mota ma."

"Haba Summy dan Allah ki yi hakuri ki ajiye ta na kai ki, na dawo da ke. Dan Allah."
Ya fada muryar sa a marairai ce.

"To shikena gani nan zuwa."
Ta fada tana kashe wayar.

Hauwa aka zo aka fitar da ita, Summy na gefen ta. Sai da ta shigar da ita motar Khaleel sanna ta koma gidan gaba ta zauna.

Kallon ta yayi, yayi, murmushi, tabbas yasan indai Najib yaga Summy dole ma ya sota, dan karshe ce, ga kyau, ga hankali.

Kai ta, ta sunkuyar kasa, ta kara gaishe, ya amsa mata.

A ranta, kuma tana tambayar ina Najib din shi kuma. Shiru tayi dan kar yaga ko ta damu dashi har haka.

"Summy mutum na gida ba lafiya, be san ma na taho ba,Β  da sai ya makale min ya biyo ni ya ganki."

Gaban ta taji ya fadi, jin ance bashi da lafiya, dakewa tayi, ta ce,
"Allah sarki Allah bashi lafiya."

"Ameen mun gode."
Murmushi kawai tayi masa.

Can Rijiyar zaki suka nufa, Gidan Hauwa katon gaske ne, flat ne, amman ya hadu dan dakunan bacci ma kan su guda hudu ne, da falo guda biyar, da daining dinta guda biyu, dana cikin kitchen dana babban falo.

Gidan Hauwa ba karaminΒ  rikita Summy yayi, ba dan ji ta dingayi dama na ta ne.

Sosai

Please Login or Register in order to submit comment