Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nama wannan yasa nan da nan ta gama ta nade su a foilpaper.

Sauran ta diba tayi falo dasu. A falo ta hage shi a kasa gefen Ummah.

Ummah na waya, har ta juya, ya kira sunan ta.
"Najwa!"

Wannan yasa ta juyo, falon ta karaso kanta a kasa.

Farantin ta ajiye a gefen Ummah, ta durkusa tana gaida shi.

"Ina kwana?"
Shiru taji wannan yasa ta dago tana kallon sa.

Kallon ta shima yake, mikewa tayi ta shige daki.

Sai da ta tabbatar da Ummah ta gama waya sannan ta dawo falo.

A gefen Ummah ta zauna. Kallon ta Ummah tayi, ta ce,
"Najwa je ki, ki samar masa abinda zai ci be karya ba."

Mikewa tayi jiki a sanyaye tana tafiya kamar bata da lafiya.

Shi dai kallon ta yake kawai yana ganin canjin da ta sauya daga jiya da dare zuwa yau.

Kitchen din ta shiga ta dauko dankali ta feraye ta dafa ta kwakwule cikin.

Nama ta nika ta hada da attaruhu da albasa, ta soya sama sama sannan ta cusa a cikin dankalin.

A cikin ruwan kwai ta dinga sakawa tana soyawa.

Tana gamawa ta daura ruwan kunu, motsi taji daga bayan ta. Juyawa tayi.

Ido biyu sukayi dashi, yana kallon ta. Kasa tayi da kanta,



*INDABAWA*

NAJWA*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya online writers*
*Allah kara hada kanmu. Allah kara mana hakuri da juriya*

*Ameen*


Dedicated *Rashida Abdullahi Kardam*
*Aunty Rash*

*Really love's u. May Allah bless you.*
*Ameen*πŸ™πŸ»πŸ˜˜πŸ˜

Page
*136*

*Barrister Halima. Kawata yar uwa. Ina matukar kaunar ki. Nagode sosai da kwarin gwiwar da kike dada bani. Addu'a da kulawa. Nagode sosai. Allah ya bar mu tare ya hadamu a Aljanna.*
*Ameen*

*Really love u*





Kallon ta ya tsaya yi hannun sa harde a kirjin sa.

Kanta ta dauke ta cigaba da aikin da takeyi. Gefen ta ya karasa, yana kallon ta.

"Najwa!"
Ya kira sunan ta.

"Na'am!"
"Najwa lafiya kuwa?"

Shiru tayi, kallon ta yake yi yana jin son ta na daduwa a cikin zuciyar sa.

"Baby ki juyo ki kallen man."
"Hamma ka bari dan Allah baka ga aiki nake yi ba."

Murmushi yayi, ya ce,
"Kawo na taya ki."

Ido tayo waje dasu ta ce,
"Ka iya ne?"

Dariya yayi, ya ce,
"Dai dai kun abubuwa ne ban iya girkawa ba."

Kai kawai ta jinjina. Ta dauko fulas ta juye a ciki.

A babban faranti ta zuba masa duk abinda zai bukata, yana tsaye yana kallon ta.

Komai takeyi cikin nutsuwa da tsabta. Juyowa tayi ta fuskance shi, amman kanta a kasa, ta ce,

"Muje ka karya."
ta juya tayi gaba.

Bayan ta yabi, har suka karasa karamin falo.

Sai da ta zuba masa komai sannan ta mike zata fita.
"Najwa!"

"Na'am!"
Ta fada tana juyowa.

"Zo nan ki zauna."
Ya nuna mata gefen ta.

Komawa tayi ta zauna, Tura mata kayan da ta hada masa yayi.

Idon ta, ta dago tana kallon sa. Kallon ta yayi, idon ta sun kumbura sunyi ja.

Ba komai yake gani ba sai sonsa da kishin sa.

"Baby na me ya same ki."
"Ba komai. Dan Allah kaci abinci tukunna."

"Baby na ke kin karya ne."
"Eh naci."

"Baby na da gaske."
"Eh na sha tea."

"Tea kadai?"
Kai ta girgiza, ta ce,
"A'ah da cake."

Shiru kawai yayi, yana kallon ta. Tura masa kayan tayi, ta ce,
"Dan Allah kaci kar yunwa ta maka illa."

Ja yai gaban sa, yana ci yana kallon ta har ya koshi.

Kallon ta ya cigaba dayi ita kuma tana can duniyar tunani.

"Najwa! Najwa! Najwa!!"
Sai da ya kira sunan ta sau uku sannan ta dago.

Kallon sa tayi, ta amsa da
"Na'am!"
Ido ya tsare ta dashi yana kallon ta.

Kasa tayi da kai,
"Najwa dan Allah ki fadan damuwar ki."

Murmushi tayi, ta ce,
"Hamma wallahi, ba komai."

"Kince wallahi fa."
"Eh!"

"To shikenan dan Allah ki daina tunanin kinji."
"To!"

"Amma fa zan ta damuna na rashin sanin abinda ke damun ki."

Murmushi tayi, ta ce,
"Kaina ke ciwo."

"Kinsha Magani? Ta shi muje asibiti."
Murmushi tayi, ta ce,
"Haba Dr daga ciwon kai."

"Eh please tashi muje."
"Yafa daina."

"To amman sai kinsha magani."
"Kayi hakuri man."

"A'ah sai kinsha."
"Toh."

"Tashi muje na dauko miki."
Mikewa tayi sukayi ciki.

Suna shiga ya wuce kitchen ya daukoΒ  mata ruwa da magani.

Tana mamakin yadda Najib yake yi a gidan kamar gidan su.

Sai da tasha, sannan ya ce,
"To ni zan tafi, jirgi na jira na."

Murmushi tayi, ta ce,
"To ina zuwa."

Tayi cikin kitchen, cake da meat pie din ta yi ta debo masa, kawo masa tayi.

Amsa yayi, ya ce,
"Mene wannan?"

"Ba na ka bane, ina zuwa tayi cikin gida."

Bayan ta yabi shima danyiwa Ummah sallama dan sun riga sunyi sallama da Baffah tin safe.

Dakin ta, ta shiga ta dauko, wani turare da Baffa ya bata, mai tsada.

A leda ta saka ta fito falo, yana tsaye a bakin kofa dan ita yake jira.

Kallo Ummah tabita dashi. Karasawa tayi gunsa.

Kai ta daga masa, alamar su tafi. Gaba yayi yana tafiya kamar baya so.

Ita ta bude masa mazaunin sa, sai da ya zauna sannan ta mika masa abubuwan da ta kwaso.

Kallon sa tayi, ya zuba mata ido kamar TV.

Murmushin karfin hali tayi, ta ce,
"Hamma kayan Mami ne dukka ka gaishe ta da Anty na."

Murmushi yayi yana me kara zuba mata idanu.

Murfin motar ta rufe masa, tana me daga masa hannu alamar bye bye.

Ido ya zuba mata ya kasa motsawa. Lallai ba karamin so yakewa Najwa ba.

Ya yadda Najqa ita ce rayuwar sa. Ba Najwa bashi da wani jin dadin rayuwa.

"Hamma!"
Ta kira sunan sa. Tana tafa masa hannun ta.

Firgigit ya kalle ta dan ya tafi duniyar tunani.

"Najwa!"
Ya kira sunan ta a hankali.

Kallon sa tayi ta kasan ido,
"Najwa Wallahi kin tafi da rayuwa ta. Allah dai ya mallaka min ke."

Murmushi tayi ta rufe fuskar ta.

Ido ya lumshe ya bude yana mata murmushi me ma'anoni da dama.

Ido ta zaro, ta girigiza kai.

Kanne mata ido daya yayi, fuskar ta, ta rufe da tafin hannun ta.

"Najwa Tah. Na tafi sai nan da ending month din nan. Zamuyi wa Lil N birthday, sai munyi waya."

Ya tada motar, hannu ta daga masa, tana masa addu'ar Allah kai shi lafiya ya dawo dashi lpy.

Da haka ya fita da kewar junan su.

Ciki ta koma zuciyar ta ba dadi. Dakin ta tashige ta kwanta.

Bacci ne ya dauke ta sai karf? biyu ta farka.

Sallah tayi,Β  tayo falo inda Ummah take, zama sukai suna hira sai bayan sallah la'asar ta dauko wayar ta.

Sakon sa ta gani, dauka tayi, ta tura masa sakon ya gajiyar hanya.



*****-******
Sumaiyya kuwa tin bayan tafiyar Najib suka shirya ita da kawar ta suka nufi gun boka.

Sunje da bukatar kar ya auri Najwa, sai dai bokan ya basu tabbbacin auren nan ba me iya raba shi. Sai dai su bari, in anyi saga abinda zasu iya.

Sumaiyya bata ji dadi ba, wannan yasaΒ  daga nann suka kuma yin wani wajen.

Sunje gu yafi Biyar amman duk maganar daya ce, taurin kan Summy yasa suka kara ninkawa har nigar.

Shima ya duba yaga abin bazai taba lalacewa ba amman ya ce su bashi kudi zai yi aiki.

Ba karamin dadi Summy taji ba. Daga nan sukayo gida ran ta fari kal.

A kalla sai da sukai sati guda a nigar. Sannan suka dawo, kwanan ta uku da dawowa Najib ya dira.

Duk da ya fada mata zuwan sa amman ba abinda ta shirya masa.

A gidam Mami ma ya dira ya bata kayan da Najwa ta bashi ya kawo mata.

Cake da meat pie ta dibar masa tana shiwa Najwa albarka.

Wanka yayi yaci abinci sannan ya kira Najwa, sannu tayi masa kawai tace yaje gun matar sa.

Da zai kima wayar ta kashe gaba daya.

Murmushi kawai yayi, a ransa yana kara yabawa hali irin na Najwa.



*INDABAWA*

NAJWA*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya online writers*
*Allah kara hada kanmu. Allah kara mana hakuri da juriya*

*Ameen*


Dedicated *Rashida Abdullahi Kardam*
*Aunty Rash*

*Really love's u. May Allah bless you.*
*Ameen*πŸ™πŸ»πŸ˜˜πŸ˜

Page
*137*
*Anty Bilkisu Yakub. Marubuciyar Sarah ko Aidah.*
*Ummu Mohammad*

*Allah ya raya mana Muhammad ya bar mu tare. Ameen.*
Nagode sosai.


Sai magariba yaje gida, yar mulkin na zaune a falo tana cin fruit.

Ko kallon sa batayi murnushi yayi, ya karasa kusa da ita.

Kai taΒ  dauke, kallon ta yayi ya saki murmushi.
"Uwar gida sarautar mata, ya kike na same ku lafiya."

Banza tayi dashi, murmushi yayi ya tashi ya bar dakin.

Ita fushin da biyu ya dadu, ga aure da zai yi. Gashi wannan tafiyar baya kiran ta kamar yadda ya saba.

A da zai kirata da safe da rana da dare, amman wannan karan in ya kira da safe shikenan.

Kallo tabishi dashi. Ya kara kyau da gogewa.

Najib abin burgewa ne, sannan abin so ga kowa. Ba karamin kewar sa take ba. Gashi kuma taga alamar yau shima bazai dau raini ba.

Tsaki tayi ta mike tayi cikin daki.

Ji tayi bazata iya jurewa ba dan ganin san da tayi ba karamin kara tada mata da hankali yayi ba.

A daki ma juyi kawai take dan marar ta ba karamin daurewa tayi ba.

Da kyar tta samu bacci ya dauke ta. Da asubar fari ta kuma tashi da wata matasananciyar sha'awa.

Har ta nufi bangaren Najib kuma ta tuna da shawarar kawayen ta da suke bata.

Akan bin sa da take yi.
Tsaki tayi ta juyo ta dawo, daki ta koma.

Wayar ta, ta dauka ta kira kawar ta Bebilo, dake ita a Abuja take.

Bebilo cikakkiyar yar lesbian ce, dauka tayi, tana tambayar ta lafiya.

Kuka ta fashe mata dashi, tana fadin,
"Bebilo Najib wani sabon iskanci ya shigon dashi, wai ya dawo amman ko ya neman."

Tsaki Bebilo tayi, ta ce,
"To shine me?"

"Haba Bebilo, kinsan kwanan sa goma sha uku ai dole nayi kewar sa."

Wani tsakin ta kuma ja, ta ce,
"Shiyasa nifa na ce bazan yi aure ba ko rayuwa da mazan nan. Sun fiya gadara ko dan sun ga anan son su ne oho. Malama ki bar wannan mijin naki kizo ayi harka, Allah kika hadu da manyan mata sai kin raina ko wane na miji."

"A'ah Babilo, ki daina fadin haka ni bazan iya ba. Yanzu ya zanyi."

Tsaki taja ta kashe wayar ta.Β  Wayar Sumny ta tsaya kallo, kiran ta ta kyma yi.

"Haba Bebilo, ki ban shawara man."

"Shawara daya ce, ki ajiye Najib a gefe kizo mu shiga harka."

Shiru Summy tayi, tana nazarin abin da Bebilo ta fada mata.

"Kinga mayi magana anjima kije kiyi tunani."
Ta kashe wayar.

Kan gado ta fada, tana juyi, aranta kuma tana cewa baza ta tsaya Najib yai mata illa ba.

A ranta take magana
"Haka kawai, gashi da jaraba sai yaje ya tsufar dani, gashi zai yo aure ya samin hawan jini dan kishi. To bazan iya ba gara na san nayi. Dan ma yaga ina biye masa ne."

Tsaki tayi ta gyara kwanciyyar ta. Bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba, batai sallah asuba ba sai karfe biyun rana.

Lokacin har Najib ya fice a gidan.

Wanka tayi ta shirya ta sha lemo kawai. Dan bata jin zata iya cin abinci.

Maman ta ce ta fado mata dan rabon da ta kira ta, ta manta, gashi ko zancen auren bata fada mata ba.

Tana dauka, a gaishe ta a gajar ce,
"Mama, daman wai Najib ne zai yi aure shine nace, Mama ya zan yi."

Ran Mama in yayi dubu ya baci, tana mamakin hali irin na Summy, kwata kwata taki ta canja.

Magana ta fara cikin bacin rai.
"Sumaiyya ni dai ban san irin halin ki ba. To dan zai yi aure shine me? Me za kiyi kuwa ban da ki rike mijin ki da abokiyar zaman ki...."

"Mama..."
ta kira sunan ta, katse ta mama tayi daga abinda zata fada.

"Yi min shiru, Sumaiyya vazaki fadan komai ba. Nasan halin ki, nasan ki bakya son tsabta, da rashin girki. Wallahi Sumaiyya kiji tsorin Allah ki sani Allah na ganin ki, ki san me kike yi."

"Mama dan Allah ni me nake yi. Tsabta da girki kuma Mama akwai masu aiki fa."

"Kinji ko. Waya fada miki kowa ke son girkin me aiki in ba ke din ba."

"Mama ni dai abar wannan batun, dan Allah ba wata mafita."

"Sumaiyya mafitar me zaki nema guna. Mafita daya ce, kina addu'a in wannan abun alkhairi ne Allah ya tabbatar dashi, ya baku zaman lafiya. Shine kadai mafitar da na sani."

"Mama...."
"Bana son jin komai. Ni dai ga abainda na fada miki nan. *In kin ji to. In kuwa ba ki jiba shikenan. Duniya ce, girma gare ta.* "

Mama ta kashe wayar, baki Summy ta tabe, ta kira Wata kawar tata.

"Kuna ina ne?"
"Gamu nan zuwa gidan naki."

"Yauwah sai kunzo."

Minti kadan sai gasu nan sun shigo, duk cikin su ba me shigar kirki. Ke daga ido ma zaka san ba yaran kirki bane.

"Lafiya kuwa?"
Daya daga cikiΒ  su ta tambaye ta.

"Ina fa lafiya? Najib ya karo rashin mutun ci. Jiya fa ko saurarata bai yi ba."

Ta zuba tagumi, Salima, ta kalle ta, ta tabe baki, ta ce,

"To shine me? Shine kika daga hankali haka. malama dole fa Najib ya rainaki, irin wannan nuna masa so da kika yi, ba dole ba. Malama ki rabu dashi yaje yayi duk abinda zaiyi mana. Kima ki shiga duniya."

Habiba ce, ta ce,
"Uhmm shiyasa ni wallahi ba maza a harka ta. Dan baza su cucen ba haka kawai. Duk abinda zan samu a gun su, a gun yar uwa ta ma zan samu."

Bebilo, dake shigowa ta ce,
"Wallahi kuwa. Namiji bazai samana hawan jini ba."

Sumaiyya kuwa ba abimda take sai tagumi da ta zuba tana bin su da kallo.

"Malama ki tsaya kiyi tunanin ta nutsu, in ba haka ba, sai kin tsofe kin bar mu."

"Dije! Dije!"
Habiba ta kwalawa me aikin Sumaiyya kira.

Amsawa tayi ta karaso a guje, kallon ta tayi a yamuste, ta ce,
"Kije ki samon abinda zan ci."

"Toh!"
Ta amsa mata ta mike tayi kitchen da sauri.

Suna zaune suna ta bata gurguwar shawara har Dije ta kawo musu abinci.

Jallof din tafita ne, sai farfesun kayan ciki.

Kamshin kawai Sumaiyya tasha, ta mike tayi dakin a guje.

Bandaki ta shiga tana kwara amai. Sai da ta gama, sannan tayi gun calender.

kirji ta dafe, ganin lokacin period din ta ya wuce.

Falo tayi, ta zauna shabar,
"Lafiya?"

Suka hada baki suna tambayar ta.
"Ku tashi muje asibiti ina jin ciki ne dani fa."

"Shine sai munje asibiti, Habiba muje mu siyo mata maganin nan."
suka fice.

Sai lallaba ta suke, har su Habiba suka kawo mata maganin ta sha.

Bacci ne ya dauke ta, inda ko minti goma batayi ba ta farka saboda marar ta da taji tana murda mata.

Ba karamin wahala tasha ba, dan sai da suka kira wani likitan su ya duba ta.


Najib kuwa ko a office suna can makale da juna suna ta hirar su abin sha'awa, dan bayan mjnti kadan zai kira ta.

A ranar da abinda ta bawa Mami yayi break yana ta shi mata albarka.


Najwa kuwa Ummah ta ce, baza ta koma gida ba, nan zata zauna mata kwana biyu.





*INDABAWA*

NAJWA*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya online writers*
*Allah kara hada kanmu. Allah kara mana hakuri da juriya*

*Ameen*


Dedicated *Rashida Abdullahi Kardam*
*Aunty Rash*

*Really love's u. May Allah bless you.*
*Ameen*πŸ™πŸ»πŸ˜˜πŸ˜

Page
*138*

*Khadija Sallehu. Marubuciyar nida Abba nah.*
na gaishe ki jinjina gare ki. Allah kara basira da daukakka.




Cikin ikon Allah, har Najib na kokarin zuwa Birthday din Lil N da za'ayi na shekara uku.

Yaso suzo da Summy amman ta ce, ita bazata je ba.

Dan yanzu shi da summy abin har mamaki yake bashi dan ko ya neme ta bata yadda bare har ya samu nutsuwa.

Haka ya shirya da farin cikin xuwa ganin masoyiyar sa.

Bama tasan da xuwan sa ba sai fitowa tayi falo kawai ya ganshi yana ci abinci.

Komawa daki tayi da saurin tin kafin ya ganta. Nan kuwa bata san ya ganta ba.

Sai da Umma tayi sama ne, ya mike ya nufi dakin.

Tana kwance a kan gado ta lumshe idanun ta ya shiga.

Ko bude kofar ma bataji sanda aka yi ba tana can tunani.

Kallon ta ya tsaya yi, yana daukar ta a hoto. Motsi taji a kuda da ita wannan yasa ta bude idon ta.

Tana ganin shi ta zaro ido, murmushi ya sakar mata.

Mikewa tayi da sauri ta ce,
"Hamma mu koma falo."

Tayi hanyar fita. Hannun ta ya kamo. Juyowa tayi, cikin tsoro da faduwar gaba.

"Hamma ba kyau fa. Ka sakeni mu koma falo."

ido daya ya kanne ya ce,
"Mene in mun zauna anan?"

Kai ta girgiza ta ce,
"Hamma ai baiΒ  dace ba mu kebe dagani sai kai. Dan Allah ka taho mu fita."

Kallon ta ya tsaya yi, shi dariya ma take bashi. Idon ta ya ciko da kwalla, daga gani kuma a tsorace ta ke.

Hannun nata ya saka, ya ce,
"Muje!"

Da dauri tayi gaba kamar zata fadi. Sai da suka isa falo ta sauke wata ajiyar zuciya, wacce sai da yaji saukar ta.

Kallon ta yayi, kasa tayi da kanta. Ta durkusa, ya ce,
"Ina yini Hamma ya hanya?"

Murmushi yayi ya ce,
"Lafiya Alhamdulilah."

"Yasu Mami da Anty na."
"Suna lafiya suna gaishe ki."

Ido ta rufe, kallon ta yayi ya ce,
"Na samu Baby na lafiya."

Kai kadai ta daga masa.
kallon sa tayi ta ce,

"Amman shine baka fadan kana hanya ba. Bayan dazu ma munyi waya."

Ido daya ya kanne ya ce,
"Surprise ne."

Murmushi tayi, kallon ta yayi, ya ce,
"Gobe birthday din Lil namesake fa."

Murmushi tayi ta ce,
"Mommyn sa ta kirani take fada min ai."

"Yauwah kinga dai ki je ki kwana ko?
Ido ta zaro ta ce,

"Kwana kuma."
Dariya yayi, ya kura mata ido. Kasa tayi da idanun ta Ya ce,

"Tsokana nake. Idon ki nake son kawai naga kin bude su. Kuma nasan hakan bazai faru ba sai na kawo abin mamaki. Ina son idanun ki Najwa suna burgeni. Suna sani nishadi."

Numfashi kawai Najwa ta sauke. Tana mamaki Najib sosai.

"Baby!"
ya kirata.

"Ina kaunar ki. Bantana son wani abu kamar ki ba. Kice macen da na taba so kece farin ciki na. Allah mallaka min ke."

A ranta ta amsa da
"Ameen!"

"Baby kice Ameen man."
"Hamma ai ba sai kaji ba. Dan kace ban da kunya ko."

"A'ah a'ah zanyi farin ciki kika ce hakan."
"Hamma kenan ina mana addu'a toh."

"Da gaske."
"Eh man."

"Nagode."
Ummah ce ta fito suka zauna suna hira abin su.

Ranar da wuri ya tafi dan yana son yayi arrangement din wajen da zasuyi partyn.

Washe gari da safe ya aikawa da Najwa kayan da zata saka da gift din da zata bawa Lil N.

Wata Orange din doguwar riga ce, wacce akai mata ado da bakin stones. Na karamin kyau tayi ba. Bakin mayafi ne da ita.

Wani bakin cover shoe da jaka ya hado mata dasu.

Kayan da ya hadowa Lil N kuma wasu English wears ne masu kyau. Kala biyar sai sweet da kayan wasa.

Ummah da kanta tasa aka zo akayiwa Najwa kwalliya sosai tayi kyau.

Karfe hudu ya karaso gidan saiΒ  da yayi sallah ma sannan ya shiga gida.

Najwa na dakin ta a kwance lokacin be samu kowa a falo badan haka dakin Ummah ya shiga.

Tana zaune akan sallaya, tana ja carbi a gefen ta ya zauna yana gaishe ta.

Amsawa tayi fuskar ta asake tana cewa.
"Har kazo?"

"Wallahi Ummah."
"To tana daki. Kaje ku tafi."

"To Ummah sai mun dawo. Ina tsohon mijin ki."
Dakuwa tayi masa ya fita yana dariya.

Dakin da Najwa take ya shiga a hankali. Ta kuyawa kofa baya wannan yasa bata ga shigowar sa ba.

Kallon ta ya tsaya yi, duk da ta baya ya ganta amman yasan ba karamin kyau tayi ba.

"Baby nah!"
Ya fada cikin rada.

Juyowa tayi da sauri, Ya salam. Ai kasa ko motsi yayi.

Kallon ta ya tsaya yi ta baki da hanci ban da ido.

Kallon sa ta tsaya yi shima ba karamin kyau yayi ba. Ya saka bakin wando da orange din riga.

Sai bakin sandal dake kafar sa da agogo baki. In ka kalle shi ka rantse bakin balarabe.

Kamar yadda yake shima a wajen sa. dan Najwa ba karamin kyau tayi masa ba. Kai bakace yar Nigeria bace.

A ransa kuwa sai tasbkhi yake da Allah da ya bashi Najwa.

Ya jima yana kallon ta duk ta tsargu, mikewa tayi ta yafa mayafin ta. Duk yana bin ta da ido.

"Hamma!"
Ta kira sunan sa a shagwabe.

Tsigar jikin sa yaji ta tashi, wannan yasa yai saurin fita daga dakin.

Falo ya kuma ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.

Bayan sa tabi, gefen sa ta zauna tana gaisar dashi.

Idon sa dake lumshe ya bude. Lokaci daya sun kada sunyi jajir dasu.

To mutum ne me neman kuka aka jefe shi da kashin akuyoyi.

Dan a bukace yake gashi yazo ya tadawa kan sa da wahala.

"Hamma lafiya?"
Kallon ta ya tsaya yi kawai.

"Hamma lafiya kai min magana man."
Murmushin karfin hali yayi mata.Β  Ya ce,

"Kawon ruwam sanyi please. In kuna da lemon tsami ki hado min dashi kinji."

Kai ta gyada tayi kitchen ta kawo masa.

Ruwan ya sha, sai lemon tsamin da ya sha shima. Lokaci daya ya fara fiyar da wata zufa.

Daga haka ma bacci ne ya dauke shi. Wanda befi na minti talatin ba.

Har lokacin Najwa na zaune tana kallon sa.

Yana tashi ya kalle ta ya sakar mata murmushi.
"Hamma baka da lafiya ne?"

Dai dai sakowar Ummah daga benr kenan.

Kallon su tayi ta ce,
"A'ah baku tafi ba."

"Yanzu zamu tafi."
Ya fada yana mikewa.

"Tashi muje."
Ya fada yana kallon Najwa.

"Toh!"
Ta mike tanawa Ummah sallama sai sun dawo.

Suka fita.



*Indabawa*

NAJWA*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online WRITERS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH DAUKAKAKI YASA KI GAMA DA DUNIYA LAFIYA.*

*REALLY LOVE U ANTY NA*

*THANKS FOR UR LOVE ND SUPPORTING*


*PAGE*
*139*

*Maman Ihsan. Nagode da kulawar ki. Nagpde Allah bar zumunci.


Shi ya bude mata mota ta shiga. Sai da suka hau titi sannan ta kalle shi, ta ce,
"Hamma"

Kallon ta yayi, ya amsa da
"Na'am Baby."

"Hamma dan Allah baka da lafiya ne?"
Murmushi yayi, ya ce,

"Lafiya ta lou."
"Hamma dan Allah ka fadan gaskiya. Hankalina bazai kwanta ba in har baka fadan ba."

"Kar ki damu. Wata yar matsala ce kadan."
"Hamma matsala kadan fa kace, abinda duk naga ka fita a haiyyacin ka."

"Bari anjima zan fada miki."
"Toh!"

"A ina za'ayi ne."
"A cikin Shoprite ne."

Tayi shiru bata kara magana ba. Sai shi da yake bata labari.

Har suka karasa ya fito ya bude mata mazaunin ta.

Fitowa tayi, suka jera. Gaskiya ba karamin dacewa sukai da juna ba.

Sunyi kyau kowa ya gansu zai tsammanin ango da amarya ne.

Suna shiga Khadija tazo ta kamo Najwa. Murmushi Najwa ta saki suna gaisawa.

Khaleel ne ya karaso gun shima suka gaisa.
"Dady da Mummy kufa ake jira kawai."

Khaleel ya fada musu, Dariya Najib yake ya ce,
"Muje toh."

Lil N na hango Najwa ya taho a guje yana cewa,
"Mummy na. Mummy nah."

Kayan hannun ta, ta mikewa Khadiya ta rumgumoshi.

"Mummy na ina yini?"
Ta amsa da
"Lafiya."

"Happy Birthday boy na."
"Tnx u Mummy nah."

Hannun ta ya kamo suka karasa cikin wajen.

Tare suka yanka cake ya saka wa Dadyn sa da Najib. Sannan yasawa Najwa da Mamin sa.

Sun sha hotuna inda yara sukai rawa. An ci ansha an bawa yara gift din kayan wasa.

Shima ya samu kyaututtuka. Sai magariba suka tafi gida gaba dayan su.

A can ma wani partyn ne su biyar sukayi shi.

Duk inda Najwa tayi Najib yana haska ta da waya yana mata vedio.

Banda hotunan da ya sukayi da wanda ya dinga daukar ta.

A nan ne ya bawa Lil N mukkulin wani katon store daya bude masa.

Khaleel da Khadija sunyi murna sai godiya suke haka ma Najwa.

Daga nan store din sukaje. Katon store ne wanda aka zuba masa kaya komai akwai a cikin sa.

Daga nan gida sukai. Su Najib ma suka yi hanyar gida.

Tin a hanya, take tambayar sa ya fada mata abinda yace zai fada mata.

Haka ya ce sai sunje gida wai duk dan ta manta ne fa.

Ai kuwa suna zuwa gida ta ce,
"Hamma baka fada min ba."

Kallon ta yayi, ya ce,
"Kawai auren ki nake son yi, kuma time din da akasa yayi yawa gaskiya zan fadawa Dady wani satin ayi komai a gama."

Ido ta zaro ta ce,
"Hamma wani satin fa kace."

"Eh Najwa. Ko a yau nace ai ba komai bane. Nasan kowa a shirye yake lokaci kawai ake jira."

"A'ah Hamma ka dai bari. Dukka fa sauran four weeks."

"Kinji fa. Har four weeks wallahi bazan iya ba. In na daga dayawa in sa two weeks bazan iya ba. Najwa ina bukatar ki."

Numfashi kawai ta sauke, tace,
"To Hamma sai da safe ko?"

Kallon ta ya tsaya yi.
"Najwa bakya bukata tane."

"Hamma nidai a bar maganar nan. Duk yadda Dady yace, haka za'ayi."

Murmushi yayi, ya ce,
"Sai da safe to.'

A ransa kuma yace, washe gari zaije wajen Dady yace shidai ayi abinda za'ayi a huta."

Sai da ya daina hango ta sannan ya shiga mota ya bar wajen.


Washe gari kuwa wajen Dadyn Najwa yaje ya same akan batun a rage lokacin bikin.

Dady ya amince inda yace zaiyi wa Dadyn sa magana dasu Abbah.

A ranar Najib yaso ya je gida dan yasan a week din za'a kawo lefe.

ranar yaje ya fadawa Najwa batun komawar sa. Ya fada mata kuma ta shirya insha Allahu na da sati biyu za'ayi biki.

Wannan tafiyar har Airport ta rakashi suna jin kewar rabuwa da juna su.

Yana dira a Abuja, ya wuce gidan su. Mami da Dady na zaune a falo.

Bayan ya gaishe su ne ya kawo zancen matso da auren.

Mami ce ta hau fada.
"Haba Najib akan me zaka ce a matso dashi, ka bari abi komai a sannu, kana so suyi abubuwa a gagggawa ne. Nidai in dai zaka bi ta tawa ka bar shi mene nan da

Please Login or Register in order to submit comment