Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka ba."

"Yauwah sannu My Baby yanzu ki tashi kije kiyi sallah kinji."
"Angama Ranka ya dade. Sai ka dawo Allah bada sa'ar aiki."
"Ameen!"

Ta kashe wayar.

Tana idarwa ta shige kitchen frief rice tayi, sai hadin karbeji, da lemon ginger.

Wanka tayi ta canja shiga cikin riga da siket yan kanti.

Hula ta saka akan ta, ta kara share bangaren ta. Sannan ta koma falo ta kunna kallo.

Tana zaune har akai sallah la'asar ta mike tayo sallah.

Cikin ta taji ya fara kiran yunwah wannan yasa ta zubo abinci, tana zaune tana juya abinci sai ga Najib nan ya shigo da sallama.

Amsawa tayi ta mike ta taryo shi. Sannu da  zuwa tai masa, sannan ta kawo masa lemon ginger ya sha.

Abincin gaban ta ya kalla ya ce,
"Baby dan wannan abincin zaki ci?"

Abincin ya janyo, ya ringa bata har ta koshi, fulas yaje kitchen ya zubo, ya zauna yaci ya koshi ya kora da lmon ginger din shi.

Yana gamawa, ya kalle ta, ya ce,
"Me kike bukata, zanje gidan Mami."

Murmushi tayi, ta ce,
"Ka gaishe min da su, kacewa Baba dan Allah ta baka abin jiyan naan ka kawon."

"Angama Baby na sai. Na dawo."
Ya fita yayi bangaren Sumaiyya. Bangaren da ko shara be samu ba.

Tana zaune tana chat ya shigo, ko kallo be ishe ta ba, bare ta amsa sallama.

Waje ya samu ya zauna, kallon ta yayi kawai.

Ya jima zaune a falon kafin ya mike ya fita, yai gidan Mami.

Sai da ya fara fadawa Baba sakon Najwa sannan ya shiga bangaren Mami.

Baba kuwa nan da nan ta mike ta dafa ramar ta daka kulli.





*INDABAWA*

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*160*

*Godiya me tarin yawa ga masoya littafin nan. Nagode Allah bar kauna.*





Sai karfen tara ya baro gidan Mami bayan ya amsowa Najwa kwadon ramar.

Yana zuwa gida yai mata knocking ta fito ta amsa yayi bangaren Sumaiyya.

Tana zaune a falo, kamar yadda ya fita ya bar ta.

Yanzu ma ko kallo bata ishe shi ba, Haka ya karaci zaman sa ya mike, yayo wanka ya saka kayan baccin sa.

Fita yayi, ya yi bangaren Najwa. Najwa na zaune tayi dai dai da ita daga ita sai ves da wani wandi three quater.

Kanta ba dan kwalli tayi parking nashi, gaban ta farantin rama ne, har guda biyu.

Daya take ci, dayan ta rufe shi, sai maltina da ta dauko zata sha.

Yana shigowa ta kalle shi da murmushi akan fuskar sa,
"Baby na ni ina tawa."

"Taho muci."
Mikewa yayi ya zauna suna ci.

Sai da taji tayi nak, sannan ta mike ta shiga kitchen din ta, lemon kwali ta dauko masa sai snacks din da tayi dazu.

A faranti ta kawo musu, meat pie kawai ta ci ta dauke hannun ta.

Najib kuwa tinda ya fara ci ya kasa daina ci duk da cikin sa a cike yake.

Tinawa da yai ba lallai ne ya samu break gobe ba yasa, ya ce, ta ajiye masa sauran gobe zai amsa in zai je office.

Kwashe kayan wajen tayi, daya plate din zogalen ta saka a friji dan kada ya lalace, komai ta maida shi inda yake.

Falo ta koma, kallon ta yayi, ya mikar da ita, ya ce,
"Muje nai miki wanka dare yayi."

"Toh!"
Dauka ta yayi, sukai sama.

Sai da yai mata wanka sannan ya shirya ta cikin kayan baccin ta.

Kan gado ya kai ta, ya kwantar da ita. Kallon ta yayi ya ce,
"Baby mun tsara yadda kwanan girkin ku zai kasan ce. Kwana bibiyu ne, sannan da safe da rana da dare duk zan na shiga dakin 'wacce bata da girki dan naga halin da take ciki. Yayi."

Kai ta sunkuyar ta ce,
"Duk yadda kuka tsara yayi."

"To Allah miki albarka."
Da "Ameen!"
Ta amsa.

Sai da yai mata addu'a sannan ya rufe ta da bargo. Kissing nata yayi sannan ya mike.

Fitilar dakin ya kashe, ya fita, ido ta lumshe tana jin kewar Najib.

Tasan Bacci barawo ne zai dauke ta, inda ta saba kwana a jikin Najib yana ririta ta, yau gata daga ita sai fulalluka. Duk wanda taja dan taji dadi amman sam babu.

Da kyar tai bacci, wanda zazzabi ya tashe ta cikin dare.

Rasa yadda zatayi tayi. Gata ba gwanar shan magani ba. Haka ta gama rawar jiki har bacci ya dauke  ta.

Gefen asuba ta tashi, alwala tayi dai dai lokacin da Najib ya kirata.

Dauka tayi muryar ta a sanyaye, ta ce,
"Hamma na tashi."

"Najwa lafiya naji muryar ki haka ."
"Lafiya lou baccin da na tashi ne."

Yaji tane kawai, ba dan ya yadda ba. sallah ta tashi tayi, tana kan sallaya har karfe bakwai.

Da kyar ta tashi tai gyara bangaren. Dankali ta soyawa Najib sai farfesun da tayi jiya ta dumama masa.

Motar sa takai, hade da snacks din da yace ta ajiye masa.

Ruwan zafi ta shiga ta gasa jikin sa dashi. Tana fitowa tai shirya cikin wata farar atamfa me adon baki.

Riga da siket ne, sawa tayi, ba tare da tayiwa jikin ta komai ba ta koma kan gado ta kwanta.

Najib na shigowa bangaren Kamshi ya doki hancin sa. Kitchen ya duba yaga bata nan.

Sama ya hau, ba kowa a falo, dakin baccin ta ya shiga ya ganta kwance akan gado.

Karasawa yayi, ya dago ta, tana ganin sa ta mike, ta gaisar dashi.

Amsawa yayi yana mata kallon tuhuma.
"Najwa lafiya kike kuwa?"

"Hamma lafiya nake, me ka gani na gajine kawai."
"Sannu kin gaji ko? Bari zan na tayaki, kinji."
Ido ta lumshe kawai.

"Me kike bukata?"
Kai ta girgiza masa ta ce,
"Bana bukatar komai sai dai ka kular mana da kan ka. Allah bada sa'a Allah kai ka ya dawo dakai lafiya."

"Ameen! Baby na, na gode."
Ya mike, mikewa itama tayi, kallon ta yayi, ya ce,
"A'ah ki zauna."

"Nidai A'ah tafiyar ka kawai zan gani."
Murmushi yayi, ya ce,

"Muje toh!"
Hannun su sakale da na juna suka fito.

Suna fitowa yaga Sumaiyya a compound din su.

Duk da daga bakin kofar dakin ta, ta tsaya sai da taga a yadda suka shigo.

Dariyar mugunta tayi, ta karasa gun Najib da yake dagawa Najwa hannu, kamo shi tayi tana kwanciyya a jikin sa.

Mamaki ya tsaya yi, jansa take amman duk hankalin sa baya jikin sa.

A jikin mota ta jingina shi, ta wani danna masa kirjin ta.

Bakin sa ta fara lallba dan masa kiss da sauri Najwa ta shige ciki.

Zuciyar ta na bugawa, lallai Najib ita zai wa haka a gaban ta ai sa bari in sun kebe.

Tsaki tayi tai sama, ta kwanta, bacci ne ya dauke ta.

Karfe daya ta tashi, alwala tayi tai sallah.

Ba abinda taci, dan haka jikin ta duk ba karfi, ga abinda Sumaiyya tai a gaban ta, shi kuma ya biye mata.

Koda yake ai matar sa ce, Mtsxxx

Tsaki ta kuma yi, yau ko text batai masa ba bare waya.

Wayar ma ta kashe gaba daya. Najib kuwa yana can yana ta zumudi dan yau da dare Najwa zata amshi girki.

Najib na shiga mota yaga basket din Najwa a ciki,
"Allah sarki My Naj, Allah miki albarka."

A office da kayan ciki yai break haka ma da rana da su yayi lunch.
Ya nemeta amman wayar a kashe.

Duk kiran wayar da yai mata wayar a kashe yana mamakin me yasa wayar ta take a kashe bayan yasan ba rashin charge bane.

Waya ya kira me gadi akan ya duba yaga Najwa na nan lafiya.

Mai gadi yaje ya tabbatar ya shaida masa. Murmushi yayi ya ce,
"Najwa yau rigima ake ji kenan."

Ita kuwa tana tashi ta fara gyara sai kace wacce ta dade bata gyara gidan ba.

Ko ina sai da ta kal kaleshi, ta goge komai kyelli yake.

Turare ta turare bangaren ta dashi. Nan da nan gidan ya hau fitar da wani kamshi me dadi.

Kitchen ta shiga ta daura tuwon shinkafa miyar agushi, wacce taji naman kasuwa suka dahu lugub dasu.

Zobo ta hada masa ta wanda yaji kayan kamshi, a friji ta saka.

Kafin magariba ta gama duk abinda zatayi ta jere kayan a falo.

Kitchen din ta gyare yai tsaf dashi, sama ta haye dan yin wanka, tin kafin ayi magariba take wanka har aka kira tana bandaki.

Ita ce wanke can kwakule can, sai da ta durje jikin ta sannan ta fito.

Zama tayi a gaban mudubi, ta tsara kwalliya sosai.

Wani less ta dauko, dark blue wanda akai masa ado da goldin kala.

Abinda ka da dare sai fitila tini ya hau sheki yana walwali.

Dauri tayi me kyau ta saka sarkar da ya bata kyau.

Duk da bata jin dadi haka be hanata kin yi komai da gayara jikin ta ba.

Cikin ta kuwa sai kuka yake yana jin yunwa, amman bata sha'awar cin komai.

Falo ta koma, bayan tayi Sallah isha'i.

Najib ma sai da yayi sallah isha'i ya dawo gidan.

A ran Najwa ta ce,
"Wato da yake girki nane shine be dawo da wuri ba."

Kallo ta kunna dan ya dauke mata kewa. A ranta kuma tana mamakin abinda ke faruwa.

Wata zuciyar ta ce,
"Mene na mamaki bayan tare kika gansu ita ya fara so kafin ke, kema a koda yaushe yaga wacce tai masa aurar ta zaiyi."

Tini kirjin ta ya buga, cikin ta ya haustine dan tsoro.

Najib kuwa yana dawowa yaje bangaren Sumaiyya dan yai mata sallama.

Abin Mamaki wai sai ga Sumaiyya na bawa Najib labari abinda bata masa, haka ta dinga jan sa da hira har karfe tara.

Agogon hannun sa ya duba ya ce,
"Kai Sumaiyya kinga dare yayi, bari naje gun Najwa."

Ya mike, tsaki tayi, tayi cikin dakin ta.

Tunani take tayaya zata bawa Najwa maganin nan ne dan Najwa ba karamin tsaya mata tayi ba.

Najib kuwa da sarsarfa ya karasa bangaren Najwa.

Najwa na zaune ta rasa me ke mata dadi, budo kofar sa tajiyo, juyowa ta kirkiri murmushin karya, dan be kai zuciya ba.

Mikewa tayi a hankali, cikin tafiyar ta me daukar hankalin sa ta karasa wajen sa.

Rumgomo shi tayi, kamar yadda ta saba, ta ce,
"Sannu da zuwa Hamma na."

Ta janyo hannun sa ta zaunar akan kujera. Ruwa me sanyi ta dauko a firij ta tsiyaya masa ta bashi.

Amsa yayi ya kurba, sanyi ya ratsa zuviyar sa.

Safar kafar sa ta durkusa tana cire masa, sannan ta cire takalmin kafar sa.

Rigar saman  jikin sa ta cire. Duk abin nan da take sam taki yadda su hada ido.

Shi kuwa kallon ta kawai yake yana mamakin me yake damun shi.

Sama tayi da kayan hannun ta, sai da ta ajiye sannan ta hada masa ruwan wanka.

Saukowa tayi daga bene ta kamo hannun sa, ta ce,
"Tashi muje kai wanka."

Binta ya dinga yi kamar jela har suka karasa saman, suna shiga dakin sa ta cire masa rigar jikin sa, bandaki ta tura shi ta rufo masa kofa.

Kayan baccin sa ta dauko masa, ta feshe su da turare sannan ta fita daga dakin.
Kasa ta sauka ta debo masa duk kayan abincin da ta shirya masa.

Tana hawa sai gashi ya fito, fuskar sa wasai, dan ya samu irin kulawar da yake so.

Kallon Najwa yayi yana son ya fara gano mene matsalar ta kafin yasan ta inda zai faro.

Tana ganin shi, ta kamo hannun sa ta zaunar dashi.

Tuwon shinkafa ta zuba masa, malmala biyu sai miya, gaban sa ta tura masa.

Zobo ta zuba masa, ta tura gaban shi, ja yayi yana ci yana satar kallon ta.

Yana gamawa ta kara masa nan ma ya tashi da ita.

Zata kara masa ya rike hannun ta, ya ce,
"Cikina zai fashe ai."

Hannun ta, ta janye ta kwashe kwanun kan zata sauka dashi, mikewa yayi ya amshi kayan ya dawo da ita.

Ajiye kayan yayi a gefe ya jata jikin sa, Zafi yaji jikin ta.

Kallon ta yayi cikin ido, wannan yasa ta lumshe ido ta.

Tana son Najib dan haka dole tai kishin sa.
Magana Najib ya fara cikin Sanyi.

"Haba My Naj me nayi ake fushi dani, dan Allah ayi hakuri asasauta min mana."

Wani abune ya tokare mata kirji, ta ce,
"Lallai be ma san me yai min ba."

Kuka ta fashe dashi kawai.
"Ya Salam! haba Baby nah, fada min me nai miki kinji."

Mikewa tayi daga jikin sa tayi cikin daki, da sauri ya bi bayan ta.

Tana fadawa kan gado yana shigowa, baya ya rufa mata ya dago ta.

Rumgume ta yayi yana lallashin ta har tayi shiru.
"Naji nai miki laifi amman Wallahi ban san me nai miki ba. Ki daure ki fadan laifina a gare ki."

Banza tayi dashi, sai da kyar ya shawo kansa ta ce, zata fada masa.
"Ina jin ki to."

Hawayen idon ta, ta goge ta ce,
"Hamma abinda kukai dazu a gabana man, Hamma ai kwa bari ba agaban ido na ba ko? Daman nasan kafi son ta ba sai ka nuna min na.
Ita da take farkon soyayyar ka, ni kuwa fa.
Amman ai kwa bari in bana gu kuyi kome zakuyi ko?
Kuma shine ka dawo kaje kai zaman ka ko?"

Tinda ta fara maganar ya gane kishine ke damunta, dariya ce ta so kama shi yadda take maganar cikin shagwaba tana buntsiro baki.

"Haba Baby nah, shine akan wannan kika batan kwalliya ta, kika hanani kallon idanun ki masu kyau bare na samu karfi a jikina."



*INDABAWA*

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

?? *HAJOW* ??
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*161*

*Salma Khaleed*
Tnc for ur love. I really appreciate



Jikin sa ya janyo ta, ya ce,
"Duk laifi nane da ban fada miki tin yaushe na fara son ki ba. Sai da Zahra ta ce na fada miki amman naki. Nasan da na fada miki da duk haka baza ta faru ba."

Yai shiru ya cigaba da magana,
"abu daya zan fada miki dayan in kinaso sai dai kiji a gun wani.
Najwa nafi shekara Biyar da fara sonki, tin daga wata rana da naganni kin dawo daga isilamiyya lokacin ban san ke wace ba.
Wallahi Najwa daga kallon ki sonki ya shige ni, dan yadda kike tafiya ma nasan ke din ta daban ce, a lokacin kina rike da hannun Basma. Abinda yasa har na ganki shine an tashe ku daga isilamiyya sai aka tsaida mu dan tsalakar da yan makrantar ku.
Kuma wani ikon Allah tin da na fito nake jin wani nishadi da na rasa na menene. Abinda nasan na gani kece gaskiya Najwa nasha wahala kafin Allah ya nuna min ke.
Kullum sai na shiga gari neman ki, sau biyu na ganki da wata rana da kuka je shopping a shoprite, shima kafin na biyo ku kin bace min."

Matse ta ya karayi, ya ce,
"Wani abun mamaki shine sai gaki na naganki a katsina shima kuma kika bace min abinda yasa na dinga bibiyar katsina kenan har ranar da na ganku na biyo ku.
Mami ita na fara fadawa lokacin da na ganki, a lokacin bansan mene so ba, ita ta fara fada min ai son ki nake."

"Mamaki na dinga ganin daga kallon ki na fada tarkon son ki, bayan akwai lokacin da Mami ta ce, naje na neme ki na nuna kimin yarinta ashe akan ki nake shan wahala ban sani ba.
Ashe yaran ma sunfi wasu manyan sosai, dan ni aguna kin fiye min manyan nan mene bana samu a gunki, jin dadi kwanciyyar hankali da nutsuwa duk ina samu.
Najwa na rantse miki da Allah kice farkon wacce na fara so kinji na rantse.
Sumaiyya, Khaleel shi ya samo min ita dan yaga ya kamata nai aure, baki ga wahalar da yasha ba wannan yasa na amshi tayin sa a wajen Sumaiyya. In baki yadda ba ki tambayi Kahleel."

"Sam ban taba son Sumaiyya ba hasali ma zaman hakuri nake da ita, Sumaiyya....."
Bakin sa Najwa ta rufe da hannun ta, tana girgiza mai kai.

"Kin yadda dani, wallahi Najwa son ki ya wahalar dani. Sai yanzu nagane me yasa ya wahalar dani ashe dan zanyi babban samu ne.
Kinsan ana cewa ba a samun abu me daraja cikin sauki. To na yadda da wannan maganar ko ta kan ki ce."

"Najwa kece farin cikin rai na! Kece komai nawa. Ina sonki fiye da yadda nake son kai na. Wannan yasa na kusan zarewa lokacin da kika ce baki aure na. Yanzu kuwa kika juya baya ai nasan mutuwa zanyi kawai. Dan Allah ki rufan asiri ki janye fushin nan da kike dani, wallahi Najwa da sonki na ke rayuwa, son ki ya zama jinin jikina. Tin kafin na samu na gana dake son ki ya zama jiniin jikina.
Ina kaunar ki. Ina kaunar ki kece farin ciki na......"

Bakin su ta hade gu daya kawai, duk da rashin kwarin jikin ta haka be sa tayi sanya wajen farantawa mijin ta ba.

Sun jiyar da junan su kishirwar da suka yi kwana biyu basa tare.

Najib ya nunawa Najwa matsayin ta a gunsa, inda ba karamin Mamki abin ya bata ba.

Najib ya samu abunda yake so, Najwa ta bashi, kulawa ta kyautata masa ta kwantar masa da kishin da ta isheshi na kwana ki biyu.

Lallai Najib ya dada bawa Najwa wani matsayin da sai yanzu ya kara ganin banbancin su da Sumaiyya.

Da Asuba suna sallah suka koma bacci dan ba karamin Gajiyar da Najwa yayi ba.

Karfe bakwai ta mike da kyar ta shiga kitchen, Bread ta gasa masa, sai wainar kwai da ta soya masa taji tumatur da albasa.

Komai ta shirya a falo, sannan ta hau gyaran bangaren nata.

Duk girman bangaren ta cikin awa daya takan iya gyare shi yai tsaf. To daman ba wani datti yayi ba. ban daki ta shiga danyin wanka.

Shima yana shafa wajen kwanciyyar su yaji ba Najwa ya mike ya shiga dayan dakin.

Bandakin ciki ya shige shima yai wanka.

Najwa na fitowa ta gyara dakin, sannan ta hau shiri.

Kwalliya tayi sannan ta, saka riga yar karama sai wandon jeans, Kanta kuwa ta gyara shi ta faka shi a tsakiyar kanta.

Sai turare da ta bade jikin ta dashi, tana ta futar da kamshi me dadi.

Ta fito ta sauka kasa ta dauko farantin da ta jere musu break din a kai.

Tana ajiyewa ya biyo ta bayan ta ya rumgume ta.

Ya ce,
"Baby na kin tashi sannu!"

Dan gaskiya a yadda ya gajiyar da ita beyi zaton zata iya hada musu break ba.

Wannan yasa yake kara sarawa Najwa dan jaruma ce, akwai karfin hali.

"Allah miki Albarka Najwa, inda kika faranta min rai Allah kema ya faranta miki.
Wallahi Baby na duk sanda na kalle ki sai naji farin ciki a duk sassan jikina. Duk sanda na kalle sai nayi nishadi, bare ki rabeni ai banda abinda zan ce.
Baby nah kin siyen zuciya ta. Ina kaunar ki da yawa."

Ya cikata ya koma daki, wani karamin akwati ya dauko na zoben gold ne da awarwaro wanda a kalla kudin sa ya kai naira dubu dari uku da wani abu.

Lokacin da ta kai masa abinci ne ya biya ta wani shago ya ganshi ya siyo mata.

Tana zaune gaban break din su tana jiran sa sai gashi ya fito daga daki.

Hannun ta ya kama ya saka mata zoben da abin hannun.

Ido ta ware tana kallon su, ta ce,
"Honey!"

Yatsa ya daura akan leben sa, alamar tayi shiru kawai.

Hannun ya dago ya ce,
"Masha Allah! Baby kinga yadda yai miki kyau."

Ita dai Najwa kallon su ta tsaya yi kawai, hannun nata ya sumbata.

Kallon ta yake, inda ta kai bakin ta cikin nasa ta gigita shi da wani kiss don har sai da suka baje akan kujera.

Ta dago tana dariya, tea ta hada masa, cikin jin dadi da nishadi take ciyar dashi.

Suna gama ya ce, shi zai bata, cawa tayi ta koshi amman ya ce, bata isa ba.

Dan haka ya hada mata tea ya fara bata, kurba daya tayi da gudu ta shige ban daki.

Bayan ta yafi, inda ta dinga kelaya amai kamar zara zubar da kayan cikin ta dan ba abinda ta ci.

Shi kuwa duka ya gigice yana rike da ita, sai sannu yake mata.

Tafi minti goma tana abu daya, kakari kawai take yi. Sannan ta samu ya lafa mata.

Baki ya wanke mata ya dauke ta ya kai ta kan gado.

Bandakin ya gyara ya dawo gun ta,
"Sannu Baby daman baki da lafiya ne?"

Ya fada kamar zai fashe da kuka.

Hannun sa ta kamo ta ce,
"Kada ka damu kawai dai dan zazzabi da nayi kwana biyu ne, sai kuma naga bana son cin abinci."

"Ayya sannu,!"
Ya mike yana dauko mata doguwar riga a dorowa.

Kafin ya karaso ta kuma mikewa da sauri ta shige bandaki, nan ma wahalar ta sha dan ba komai a cikin ta.

Sai da ya kara gyara mata jiki sannan ya dauko riga zai saka mata.

Kamshin da taji rigar nayi yasa taji juwa na daukar ta.

Kasa ta zube ta zauna tana girgiza masa kai.

A wahala ta ce, ya canjo mata wata rigar da sauri ya koma ya dauko mata.

Itama sa shi tayi ya canjo. Daga baya dai sai sabuwa aka dauko mata a cikin akwati dan ta ce duk kamshi turaren suke mata.

Daukar ta yayi gaba daya yayi cikin mota da ita.

Sannan ya tada motar suka tafi asibitin sa.

Suna zuwa ya shiga cikin office dinshi ya juna mata ruwa.

Jinin ta ya dauka ya tafi lab ya bayar ai mata text.

Office ya koma ya sata a gaba tana bacci duk ta fada.

Ta kara haske, kirjin ta ya dada tashi.
Waya ya zaro ya kira Mami ya ce, Najwa ce ba lafiya.

Nan da nan Mami ta taho asibiti dai dai lokacin da aka kawo text din ta.

Tana kwance tana bacci bata san Mami tazo ba.

Yana amsar text din ya tsaya ya kasa motsi.

Wani sanyi da farin ciki suka ratsa zuciyar sa, shi kuwa me zaiyi sujjada kawai yayi yana me godewa Allah.

Kallon sa Mami tayi, da sauri ya fada jikin Mami yana cewa,
"Mami na zama Father, ki kuma kin zama grandMa."

Ido ta bude tana kallon sa takardar hannun sa ta amsa ta gani ai nan da nan ita ma ta fara hamdala.

Cikin su ka rasa wa yafi wani murnar samun cikin nan.

Khaleel ya fara sanar wa Khaleel ya taya shi da murna daga nan sai Salim.

Sai su Talle, cikin mintina kadan kowa ya gama sanin Najwa na da ciki banda ita dake kwance tana baccin wahala.

Sai karfe daya ta tashi, ba laifi taji dadin jikin ta sai dai rashin dadi na rashin cin abinci.

Tana mikewa Mami ta mike tana taimaka mata ta gyara mata zama.

"Sannu Najwa Allah baki lafiya."
"Ameen! Mami yaushe kika zo."

"Tin dazu."
Dai dai shigowar Najib tare da Bara'atu.

Da sauri ya karaso wajen ta yana tambayar me yake damun ta me takeji?

Ita dai kasa tai da kai ko ya manta Mami na gun ne.

Kallon Mami yayi ya ce,
"Mami bata ci komai ba."

Mami ta ce,
"Najwa me kike so a dafa miki?"

"Mami kwadan zogalen Baba nake so."
"Sai kuma me?"

"Sai faten dankali da wake."
"To shikenan, bari naje yanzu zan dawo."

Mami ta mike ta fita. Bara'atu ce ta matso tana mata sannu.

Mikewa tayi dayin sallah, sai jiri da sauri Najib ya kamata ya kai ta bandaki.

Tai alwala ya dawo da ita. A zaune tayi sallah dan da ta tashi jiri ne ke kwasar ta.

Kan gado ya maida ita, yana hado mata tea. Ya saka mata madara da yawa.

Yana kawo mata ta hau yin kakarin amai da sauri ya matsar dashi.

Mami bata dade ba sai gata nan da faten dankali da kwadon zogale.

Kwandon ta fara ci dan ko faten bata gani ba.

Magani Najib ya bata tasha da kyar sai allura da yai mata.

Bacci ne ya kara tashin ta inda karfe hudu saura ta tashi da yunwa.

Tana farkawa ta kalli Najib ta ce,
"Hamma yunwah!"

Da sauri ya dauki mata wannan faten dankalin da wake da hanta da alaiyahu.

Shi ya dinga bata inda tana gamawa ta ce, masa Maltina take so.

A firij ya dauko mata ta sha, tana jikin sa a kwance bacci ya dauke ta.

Har Mami ta shigo be ajiye ta ba. Najwa ta bude ido taga Mami, zata gyara kwanciyya taji ta ajikin Najib.

"Wayoo Allah!"
Kunya kashe Najwa.

Ido ta damke, ta kasa motsawa. Mami ce ta ce,
"Najib ka kwantar da ita naga tana motsi."

"Mami kada ta tashi kuma."
"A hankali zaks kwantar da ita."

Yana kwantar da ita ya mike danyin alwala yai sallah.




*INDABAWA*

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*162*

*Teemah*
*Tnc for ur prayer*
*I really appreciate*





Sai magariba suka koma gida dan har Mami sai da suka rakasu.

Bara'atu ta bar mata dan tana taya ta aiki.

Duk rashin lafiyar da Najwa keyi, be hana ta bawa Najib kulawa ba dan sai shi da yake hana ta.

Lallabawa tare da gatan ta ta kuwa sai abinda yai gaba.

Sosai take samun kulawa daga Mami zuwa ga Najib.

Kwado kuwa kullum sai an mata, haka nan Faten wake sai na Mami kawai take

Please Login or Register in order to submit comment