Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kara sawa aranta sai me kudi zata aure, dan tasan mahaifinta ba abinda bazai zuba mata ba.

Summy kawai aka bari a gidan kafin abokan ango su zo ta tafi.

Gida Khaleel ya koma, yana shiga dakin Najib, ya tadda shi ya fito daga wanka yana shafa mai.

Da ka kalle shi zaka san bashi da ishashiyar lafiya dan koma a cikin sanyi yake yi.

Karasawa Khaleel yayi yana murmushi, ya ce,
"Sannu Aboki kace, har kaji garau.'

Murmushi shima Najib yayi, ya ce,
"Alhamdulilah. Har ka dawo."

"Eh. Shiryawa nazo nayi mu tafi."
Khaleeel ya fada

Ido daya Najib ya kanne, ya ce,
"Anya kuwa zani."

Fuska Khaleel ya dan marairai ce, ya ce,
"Haba bro ka daure in ka fita ma zaka kara jin karfin jikin ka."

Dariya Najib yayi, ya ce,
"Ai Dole naje ma tinda ba a kwance nake ba."

"Yauwah ko kai fa."
Mikewa yayi, ya shige bandaki.

Shi kuwa Najib ya bude dorowa ya dauko,  kayan da ze saka.

Wata brown din shadda ya dauko, wacce akai maka ado da dark brown din zare.

Sosai yayi kyau, ya saka brown din hula da brown din takalmi. Tabaran sa ya dauka ya saka.

Khaleel na fitowa, shima ya hau shiri cikin irin shigar Najib.sosai sukayi kyau sai kace tagwaye.

"Tashi nu tafi."
Khaleel ya fada

Fuska Najib ya bata, ya ce,
"Ai mayi dai sallah isha ki?"

"Ai lokaci beyi ba, mayi a gidan su Bashir,"
Khaleel ya fada yana mikewa.

Hararar sa Najib yayi,
"Shi ya shirya ne, da zamu tafi."

Ido Khaleel ya zaro. Yace,
"kai kasan, yadda ango ke zumudin wannan ranar kuwa."

Mikewa Najib yayi, ya ce,
"Tayaya zan sani, tinda ni ban taba shiga irin halin ba."

Bayan sa Khaleel yabi yana dariya. Mami sukayiwa sallama sannan suka nufi gidan su Bashir


*INDABAWA*
[2/19, 9:13 PM] Maryam S Indabawa😍😘: *NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHODA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE 109

Kamar kullim suna zaune a kasa Mami da *Najwa* sai Basma dake biyowa *Najwa* karatu ta.

Sai da ta kai aya, sannan ta tsaya, ta kalli *Najwa* ta ce,
"Adda na kara dagewa ko?"

Murmushi *Najwa* tayi, ta ce,
"Sosai ma."

Mami ta ce,
"Ai haka ake so, ayi ta cigaba da karatu."

Murmushi Basma tayi, dan a rayuwar ta tana son taga ta zama kamar yayar ta, komai aka tambaye ta, ta sani iya bakin gwargwado.

Ga sanin hadisi, dan da ka tambaye ta abu zata baka hujja da hadisin Annabi da ya ce kaza da kaza.

Basma na Alfahari da yayar ta. Tana son ta kamar yadda itama, *Najwa* ke son kanwar tata.

Mami ce ta dubi *Najwa* ta ce,
"Najwa yi min bayani akan Alwala.               "*FARILLAN ALWALA*
Farillan alwala guda 7 neh:
• Niyya
• Wanke Fuska
• Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu
• Shafar kai
• Wanke kafafuwa
• Cuccudawa
• Gaggautawa

*SUNNONIN ALWALA*
• Wanke hannaye zuwa wuyan hannu
• Kurkure baki
• Shaka ruwa
• Fyacewa
• Juyo da shafar kai
• Shafar kunnuwa
• Sabunta ruwa agaresu
• Jeranta tsakanin farillah

*MUSTAHABBAN ALWALA*
• Yin bismillah
• Goga asuwaki
• Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye
• Farawa daga goshi
• Jeranta sunnoni
• Qaranta ruwa a nisa gabobi
• Gabatar da dama kafin hau."

Mami ta gyada kai, ta xe,
"To indan na manta da wata farilla daga cikin alwalar fa?"

*Najwa* ta ce,
"Idan kika tuno sai ki aikata ta da abunda ke bayanta. Idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun."

Mami ta jinjina kai, ta ce,
"Idan kuma na bar sunna fa?"

*Najwa* ta gyara zama ta ce,
"Sai ki aikata ta ita kadai baza ki sake sallah ba."

Mami ta sake yo mata wata tambayar,
"Idan kuma na mance lam'a fa?"

*Najwa* ta ce,
"sai ki wanke ta ita kadai da niyya, in kuma har yayi sallah bayan faruwar hakan toh sai ya sake ta."

"Indan na tuna da kurkurar baki ko shaqa ruwa bayan na rigaya na fara wanke fuska fa?

"to baza ki dawo gare su ba har sai kin  gama alwalar ki. Sannan ki aikata su."

Mami ta ce,
"In ban da alwala zan iya sallah?"

*Najwa* ta girgiza kai, ta ce,
"A'ah Bai halatta ga wanda bashi da alwala yayi sallah, koh dawafi, koh ya taba al qur'ani koda acikin gafakarsa neh, bada hannunsa ba saidai idan *juzu'i* neh ga mai neman ilimi acikin sa."

"Idan nayi salllah ba tare da nayi alwala ba kuma ina sane mene hukunci na.?"

"Mami Wanda yayi sallah da gangan ba tare da alwala ba toh shi kafiri neh. Allah ya ki ya she mu."

"Ameen! Meye da meye suke katya alwala."
*ABUBUWA MASU WARWARE ALWALA*
Sun kasu biyu:-
*_Karrai da Sababai_*

*Karrai sune:*
• Fitsari
• Bayan gida
• War rihu (tusa)
• Maziyyi
• Wadiyyi

                          *Sababai sune:*
• Bacci mai nauyi
• Suma
• Farfadiya
• Marisa
• Maye
• Hauka
• Sumbata
• Shafar mace, idan anyi da niyyar jindadi ko kuma ya samu jindadin babu nufi
• Shafar azzakarinsa da cikin hannu ko da cikin 'yan yatsu duk ta warware."

Mami ta kara kallin ta. Ta ce,
"Idan nayi kokwanto acikin samuwar kari me zanyi?"

"Mamai Alwala ta wajaba agareshi, sai ya sake alwala.
saidai in mai yawan waswasi neh, to babu komai agareshi."

"Idan na shafi mijina  sai maziyyi ya fiton! Bayan ina da alwala kuma sallah zanyi me zanyi?"

Kai *Najwa* ta sunkuyar sannan ta ce,
"Kiyi tsarki ki sake alwala kiyi sallah ki. Ba sai kinyi wanka ba."

Mami ta kalle ta, sannan ta ce,
"Menene ma Maziyyi?"

°Mami shi maziyyi wani ruwa ne da yake fitowa lokacin 'yar sha'awa karama, ta yin tunani koh kallo koh yin wanin wannan."

"Tsarki gida nawa ya kasu."
"Tsarki kashi 2 neh:-
°Tsarkin kari
°Tsarkin dau'da"

"Dame ake tsarkake su?"
"Dukkan su basa inganta sai daruwa mai tsarki, mai tsarkakewa shine: wanda kamarsa bata jirkita ba, ko dandanon sa, ko qamshinsa, da abunda yake rarrabe shi marinjayi. Babu laifi da kasar gishiri da kasar kanwa da makamancinsa."

"Masha Allah, ti kamar ina da ruwaa cikin kayon tanki, digon fitsari ya diga mene matsayin ruwan."

"Mami, Malamin mu ya ce, ruwan yana da kyan sa, saboda abibda ya zuba a ciki, be jirgkita kaman nin sa ba.'

"To kamar muna da rijiya, sai ruwan cikin ta ya zama ruwan kasa, wato ya koma ja. Shin zan iya alwala dashi."

"Eh Mami!"
"Menene dalilin fadar haka."

"Mami da farki, ruwan a gaka yazo bamu muka bata ba, kuma ruwan me kyau ne, tin da daga sama ya sauka, ya shiga cikin kasa, kasa kuma ta fito da shi. Kuma Mamai Kasa ba najasa bace, da zamu kiyin amfani da ruwan."

"Idan najasa ta fito fili me za'ayi."
"Sai a wanke gurin,"

"idan kuma  fantsama tayi fa?"
"sai a wanke tufar gabadaya."

"Idan nayi kkokwanto acikin samuwar najasa fa?"
"sai yayi yayyafi da ruwa ajikin sa."

"Idan kuma na tuna da najasa inaa cikin sallah fa?"
"sai ya yanke sallar, saidai idan yaji tsoron fitar lokaci."

"Idan nayi sallah da ita ina mai mantuwa fa sai na tuna bayan nayi sallama."
"to ya sake sallah idan da lokaci."

"Idan na kasance ina da janaba, gashi lokacin fitar sallah ya kusa, gashi ina da lalurar da in na taba ruwa zan iya kwanciya rashin lafiya, yaya zanyi."

"Mami taimama zakiyi, in ya samu ruwan dumi ya tsarkake jikin sa.
"Saboda me kika ce haka *Najwa* "

"Mami akwai wani lokacin sahabai, da wani sun fita yaki, da asuba an tashi za'ayi sallah, sai yake tamnayar sahanai shin ze iya yin taimama, duk da yana da janaba, saboda ya kasance, yana da lalura wacce in ya taba ruwa zai iya kwanciya ciwo.
Sai sahabai suka ce, A'ah sai dai yayi wanka.
Haka wannan sahabin yayi wanka, wanka da ya zamo shine ajalin sa, ko da suka dawi gida Manzin Allah (SWA) ya tambayi wannan bawan Allahn sai suka fada masa abinda ya faru.
Sai Annabi Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi yace, kun kashe shi. Saboda abinda yaxo ya tambaye ku, dai dai ne kuka hana shi aikatawa. To kinga ya hallarta kenan."

" *Najwa* yaya ake taimama?"
"Mami, zaka samu waje me tsarki, a kasa, kayi niyya, sannan ka buga tafukan hanayen ka biyu akasa.
sai ka dago su ka kade dutsun da ya diba da baki, ko ka bugi hannaye.
Zaka shafe fuskar ka kamar yadda ake alwala sannan ya shafe hannayen ka, iya yatsun ka zuwa kan wajen da ya kai gaba da zata sada ka da hannu.

Shikenan an gama taimama."


"Masha Allah *Najwah* Allah kara ilimi."
Dady ya fada yana saukowa daga bene.

Kai ta dukar kasa. Mami tace
"Ameen!"

"Ku tashi muje aci abinci."
Suka.mike suka nufi wajen cin abincin.




Suna zuwa gidan su Bashir har ya shirya sukawai yake jira. Daukar sa sukayi suka shige wani store sukayi masa siyyayar kayan abinci da kayan motsa baki.

Karfe takwas da rabi suka isa gidan nashi.

Gidan sai tashin kamshin yake, fuskar sa, ta kasa daina fitar da murmushi.

Baki Najib ya tabe, yace,
"Yanzu zaka samu nutsuwa ko?"

Bashir ya ce,
"Sosai ma."

Khaleel yayi dariya ya ce,
"Ka gwada auren kai ma ka gani."

"Allah ya kawo lokacin."
Najib ya fada.

Dai dai nan suka isa falon da su Hauwa, suke zaune, ita da Summy da wata kawar ta Nafisa.



*INDABAWA*
[2/19, 9:13 PM] Maryam S Indabawa😍😘: *NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHODA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE 110




Sam Nqjib be kalli yan matan dake wajen ba, gefe ya samu ya zauna.

Ita kuwa Summy sai satar kallon sa take, dan sai taga a fili ma yafi kyau, jiya kuma da ta ganshi ko dan ba kamar yau da ba jama'a bane.

Amman ya gama tafiya da imanin ta. Sai wani dauke kai take, wai ita bata ganshi ba, shi kuwa gogan naka be san ma tanayi ba.

Addu'a sukai musu tare da yan nasihohi sannan suka mike dan tafiya.

Mota daya suka taho da ita, dan haka, suka dauki Summy da Nafisa a baya, shi Najib ya karbi tukin Khaleel ba gefen su.

Nafisa yar unguwar su Hauwa ce, dan haka suna zuwa ta sauka, Summy ma fita tayi dan daukar motar ta.

Khaleel kallon Najib yayi, ya ce,
"Bro ga Summy can kaje ka kaita da motar ta sai na biyo bayan ku."

Tsaki Najib yayi, ya ce, a ransa,
"Ashe kuwa baza ta gida ba."

Tuno yadda Khaleel yasha wuya akan ta. Yasa, ya ce,
"Ka biyo mu da motar ta, tazo ta shigo nan."

Murmushi Khaleel yayi, ya ce,
"Yauwah dan Uwa."

Bin bayan ta yayi, ya fada mata yadda sukayi. Ba musu tabi bayan sa, ya bude mata gidan gaba.

Khaleel ne yazo yayi gaba yana nuna masa hanyar, Kala be ce mata ba hasali ma baze ce ga kalar yarinyar ba dan kansa na kan titi kawai.

Summy kuwa tana jiran jin maganar sa. Amman taji shiru wannan yasa ta kuma dukar da kanta.

Wata kwana da zasu sha ne, yasa idon sa kallon gefen da take.

Kan ta a kasa, sannan ta yane kan ta da mayafi. Wannan abin da ya gani shi ya sa yaji ta dan burge shi.

Har suka isa kofar gida su be ce da ita kala ba. Sai da zata fita ne, ya ce,
"Nagode."

Kusan Sumewa Summy tayi jin muryar sa me dadi da zakin.

Kallon sa tayi amman sai taga wayar sa ke dannawa.

"Sai da safe."
Ta fada tana fita.

"Allah tashe mu lafiya."
Ya kuma bata amsa ba tare da ya kalle ta ba.

Murmushi tayi, tayi cikin gida inda Har Khaleel ya mata parking motar ta.

Kallon sa tayi, ta ce,
"Nagode fa."

Ido ya fito dashi waje, ya ce,
"Muke da godiya."

Kalon sa tayi ta girgiza kai. Shima kallon ta yayi, ya ce, fadi kar ki mutu.

Dariya tayi, ta ce,
"Bama zan mutu ba dan ban fada ba."

"Naji amman dai fada min."

Kallon sa tayi, ta ce,
"Abokin nan naka tsoron kallon mata yake ne."

Dariya yayi ya ce,
"Me kika gani?"

Numfashi taja, ta ce,
"Sai dai yayi magana amman sam ko kallo na beyi ba."

Murmushi yayi yace,
"Be taba soyayya bane, shiyasa yake jin haka."

Ido ta fito da su waje, aran ta kuma tana cewa,
"Duk haduwar gayen nan amman be taba soyayya ba. Wow amman na samu bagas."

Murmuahi tayi ta ce,
"To Nagode sai da safe."

"Allah tashe mu lafiya sai munyi waya."
Ya fada tana daga mata hannu.

Ficewa yayi ya nufi wajen Najib yana  mamakin magan da yayi wa Summy, lalai Summy ai ta godewa Allah ma da tasamu ya mata magana.

Dan shi sam a rayuwar sa baya kula mata in be san su ba. Wannan ma yasan dashi ya samo masa ita ne.

Yana shiga motar ya ce,
"Yah bro tayi."

Murmushi Najib yayi, ya ce,
"Tinda ta maka ai shikenan. Ni ba dole ku samon kamar wacce nake so ba."

Hararar sa Khaleel yayi, ya ce,
"Ai daman kai ba a iya maka. Ina jin yar shekara goma zaka aura ko."

Duka Najib ya kai masa. Sanna ya
tada motar suka nufi gida.

"Please biya dani ta zoo road zan sha fura."
Khaleel ya fada

"Kaji shi sai kace bafulatani. Ka bar mu, mu fulani muce zamu sha furar mana."

"Yo zama da kai, yasa nima na zama ba fulatanin."
Dariya sukayi sannan suka dau hanya.



*Najwa* ce zaune gefen Mami. Kanta akan ciyar ta, tana tsefe mata kalbar kanta wacce take kwance har gadon bayan ta.

Mami ta fuskan ta, ta ce,
"Mami yau tinda ba Isilamiyya zamu je shoperite zamiyo siyaya."

Mami ta ce,
"To *Najwa* Allah kai mu anjiman."

"Mami, Mamin Hamma Najib ta ce, kan na tafi Katsina naje mata."

"To ba matsala,  Allah nuna mana. Sauran wata uku ai tafiyar taki."

*Najwa* ta ce,
"Yaushe Hamma Salim ze koma ne?"

"Cikin satin nan ze tafi ya ce, dan har sun fara karatu."

"Allah Sarki Hamma, Allah basu sa'a."

"Ameen"
Mami ta fada.

"Ni yan Ajina ma nake tausaywa in na tafi. Wallahi ba dadi Mami."

"Sai hakuri ai ci gaban kune har su."

"Haka ne. Allah shige mana gaba."
"Ameen!"

"Mami ai dazu Zahra ma ta kirani, wai har an samar mana hostel da zamu zauna."

"Masha Allah. Zahara ai sai murna zuwan ki take."

Dariya *Najwa* tayi,
"Mami, wai cewa tayi na tafi tin yanzu kinji ta fa."

"Uhmm kunfi kusa ai."
"Oh Mami haka zakice."

"Me zance miki toh."


Basma na dawo wa, tayi wanka, suka ci abinci sannan suka shirya dan fita siyayya

Doguwar bakar riga ta saka me adon ja a jiki. Sai jan mayafi da ta nade knta dashi, parking din da tayi ya taso ya karawa rolling din da tayi kyau.

Jan cover shoe ta saka da wata jar jaka ta rataya ta a kafadar ta.

Sosai tayi kyau duk da batayi kwalliya a fuskar ta ba, daga hoda sai kwalli wanda ya karawa idon ta kyau da girma. Sai man lebe da ta shafa wanda ya karawa bakin nata kyau da laushi.

Basma ma, shigar bakar rigar tayi ta saka dan karamin hijab.

Tare suka fito hannun su rike da na juna.

Mami sukai wa sallama sanna suka fita harbar gida.

Drivern su da yasan da fitar yana tsaye yana jiran fitowar su.

Suna fitowa suka gaida shi cikin girmamawa sanna tmsuka gaida Baba Me gadi.

Mota suka shige suka tafi, suna hira abin sha'awa.

Yana dire su suka shiga, siyaya suka shiga sunayi, wanda duk rabi kaya zaki ne, da na sanyi *Najwa* ta debo, ita kuwa Basma story book ta kwaso da kayan rubutun makaranta.

Sanye yake da Bakin wando sai jar riga da jan takakmi idon sa sanye da tabaro.

Zaune yake a harabar gidan su shi kadai. Kamar an tsikare shi ya mike ya shiga motar sa.

Zagaye garin yake kawai sai gashi a kofar Ado bayero mall. Har ya gifta kuma yace bari ya shiga yaga ko da abinda ze siya. Parking yayi ya fito ya tsaya daga can gefe.



*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHODA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE 111


Dai dai lokacin da su *Najwa* suka gama biyan kudin su kenan. suka fito rike da ledojin su,.

Karba drivern yayi ya saka musu a mota sanna suka shiga ciki. Kamar ance yayi gate din fita ya nufi can yana amsa waya.

Lokaccin *Najwa* ta dago tana murmushi tana kallon hanya. motar ya tsaya kallo se kace wanda aka ce, ga yarinyar aciki ya hange ta, tana ta zuba murmushi.

Sandarewa yayi a wajen, ya rasa me zeyi. Sai daga baya ya nufi motar sa da sauri, ya bi bayan su.

Amman ina yana fita yaneme su rasa. Kai ya dukar kasa. Hawaye na zubar masa a idon sa.

"To wai ma me ya hanashi tsaida motar har ta tafi."

Ya jima a wajen dan anna yayi sallar magariba ya nufi gida duk jikin sa a sanyaye.


Su Najwa na zuwa gida suka zube kayan da suka yi. Kayan zakin ta ta kwashe zuba a firjin dakin ta.


Wacce Mami.

Mami suna ta na gaskiya Maryam, 'ya ga Maalm Isah da matar sa Hafsat.

Malam Isah babbsn malami ne dan garin maidiguri kasuwan ci ne ya kawo su kano har ya zama kamar dan garin.

'Yayan sa hudu suka haifa. Ado shine babba, yana da ya'ya shida, Amina itace babba wacce take da ya'ya uku, Summaiyya itace babba sai, Khaleel da kanwar ta Nusaiba.
Sai, Maryam, da Aminu, Huwaila, da  isah. duk sunyi aure kuma kowa yana da rufin asiri.
yana aiki a ma'aikatar tafiya.

Sai Ahmad wanda yake da ya'ya biyar, kamfani yake, dashi. Marzuk, Adnan, Shuaib, Sani, Halifa.

Sai Mami wacce ya'yan ta, Uku. Salim, *Najwa* Basma.

Sai Hauwa, wacce ke da ya'ya biyar, tana aure a katsina. Zahra itace babba sa'ar *Najwa* sai, Jabir, Hamza, Haidar, Abbasa sai auta Khairat.

Mami ta tashi cikin tarbiyya da kula. Ta samu ilimi na addini da boko.

Yanzu haka Anty Hauwa, ta nemi Dadyn *Najwa* da ya bata *Najwa* tayi karatu acan.

Dady ya amince dan duk sun zama daya.

Summaiya (Summy) ta kasance jika wajen Mami. Dan Baban Maman, Summy shine babba wan su Mami.

Suna da zumunci sai Summy da bata kaunar yan uwan ta, sam bata son zumunci bari *Najwa* da sam jinin su be hadu ba.

Dan ko magana bata yiwa *Najwa* Duk yadda Maman ta ke mata fada sam bata dauka.

In taga *Najwa* kamar taga mutuwar ta ne, ko dan taga kowa nason tane, kuma tana da ilimi da farin jini.

*Najwa* yar gata ce, daga dangin Mami har na Dady kowa son ta yake, dan akwai ta da hakuri da hankali da nutsuwa.

Kakannin ta na son ta, itama tana son yan uwan ta.

Sai dai bata fiya shiga yan uwa ba saboda harkar makaranta, sam *Najwa* bata son fashin makaranta. Kullun tana makaranta.

Kowa son ta yake da alfahari da samun ta a matsayin 'ya ko jika. *Najwa* bata da son hayaniya akwai ta da hakuri da riko da addini.

Miskila ce, dan sai ta yini a gidan bata ce komai ba.

*Najwa* fara ce, doguwa, bata da kiba, tana da idanu tana da dogon hanci, bakin ta karami.

Kanta gashi ne, mai tsayi da yawa, sai gefen fuskar ta da ya lulube da gashi a kwance.

Daka ganta, kasan bafulatana ce usuli.

Sai isha'i ya shiga gida. Yana zuwa gida ya kwanta akan kujera dake falon.

Ido ya lumshe, yana tunanin abin da ya faru na rashin samun damar ganin ta. Gashi jibi yake son su tafi saboda yana son da sun koma zai yi tafiya

Ya jima kwance akan kujerar Mami ta sauko kasa.

Kallon sa ta tsaya yi, sannan ta samu gefen sa ta zauna.

Kansa ta shafa, ta ce,
"Najib lafiya?"

Ido ya bude wanda suke jajir dasu, murmushi ya dan kwakwalo, ya ce,
"Mami yau ma na ganta, amman ban samu damar mata magana ba."

Kallon sa tayi, ta ce,
"Garin yaya?"

"Mami kafin na karasa har sun bace min."

Kai Mami ta girgiza ta ce,
"Haba Najib kabi komai a hankali, insha Allahu koman daren dadewa zaka hadh da yarinyar kuma rabon ka ce insha Allah. Ji yadda ka koma duk ka rame, kana son hankali na yana tashi ne. In naganka a haka."

Hawayen idon sa ya goge ya rumgume Mami, ya ce,
"Mami kiyi hakuri, nima ban son damuwar nan da nake ciki. Insha Allahu bazan kuma saka damuwar ba. Ki cigaba da yin addu'a."

"Toh Najib, Allah ya kawo maka dauki. Tashi kaje kaci abinci. Gobe zamu jewa su Umma sallama."

"Toh Mami!"
ya fada Yana mikewa.

Sallamar Khaleel ita ta tsayar dashi. Kallon sa yayi, ya ce,
"Sannu da zuwa."

Ya fada yana yin saman bene da gudu. Yana dariya

Murmushi Mami tayi ta ce,
"Ya maka laifi kenan."

Dariya Khaleel yayi, ya ce,
"Mami kenan ni da Najib sai Allah."

"Shiyasa nake sa muku ido ai."
Dariya yayi, sannan suka gaisa.

Sama ya nufa.

Najib na hawa sama ya cire kayan sa ya shige ban daki.

Khaleel na shiga ya samu waje ya zauna, laptop din sa ya janyo ya fara danne danne.

Yana zaune Najib ya fito rike da tawul yana goge jikinsa.

Kallon sa Khaleel yayi, ya dauke kai ya cigaba da danne danne sa.

Gefen sa Najib ya zaune, ya ce,
"Haba Bro menene?"

Kai ya dauke, ya cigaba da danne, dannen sa.

Hannun sa ya riko ya ce,
"Wallahi bana son fushi nana naka."

"A hakan ne baka son fushi na. Bayan kai kasa nake yi. Yarinya na je na gama shawo kan ta da kyar amman na baka number ta ko kira ba kayi ba, gashi jibi zaku tafi ko son zuwa kayi baka yi."
Khaleel ya fada cikin fada da bacin rai.

Tin da ya fara maganar Najib yayi kasa da kansa. Shima yasan be kyau ta ba, amman ya zai yi, ya kasa saka yarinyar aran sa ne, duk da ko hoto ta da ya bashi be kalla ba.

Kai ya dago ya kalli! Fuskar sa da alamar ban hakuri.
"Dan Allah kayi hakuri ban 'ki kira dan na bata maka rai ba, kawai na kasa sakin jiki da ita ne, amman insha Allahu zan kira ta, sannan gobe zan samu lokaci sai muje."

"Kaje dai!"
Khaleel ya fada yana dauke kai daga kallon abokin nasa, dan yasan da wuya ya iya sakin jiki kamar yadda yake son yayi.

"Ina kara baka hakuri dan uwa, kasan bazan iya va ni kadai. Ka taimakan nasan kai me sona ne da har kake son cire ni daga cikin damuwa."
Najib ya fada yana kama hannun sa.

Damke hannun sa Khaleel yayi, ya ce,
"To shikenan amman dan Allah kana kula da ita."

"Insha Allahu. Nagode!"
"Mene na godiya mun zama daya fa."

Ido daya ya kanne ya dage gira. Jallabiya ya saka sannan ya feshe jikin sa da kamshi.

Kallon Khalleel yayi, ya ce,
"Tashi muje muci abinci."

Mikewa Khaleel yayi, yayi gaba Najib yabi bayan sa.


*INDABAWA*

NAJWA*

🌐 *HAJOW* 🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHODA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *113*


Yana zuwa gida ya kira Summy. Dagawa tayi cikin farin ciki dan tana tunanin yau zasu je mata.

Shi ya fara mata sallama. Sannan ta amsa masa, cikin sanyin murya.

"Sumaiyya ya kike yasu Mama."
"Duk suna lafiya."

"Masha Allah. Daman zan fada miki anjima da yamma zan kawo miki sako inji Najib, dan an masa waya ana neman sa awajen aiki, a yau ma zai bar kasar."

Ji tayi kirjin ta ya buga. Mazewa tayi ta ce,
"Allah sarki ba komai. Allah ya bada sa'a."

"Ameen Nagode. Sai anjiman"
Sukayi sallama.

Tana ajiye wayar ta saka kuka, Ita da tayi niyyar rikita shi da adon da zata masa, amman wai bama ya garin, kuma kasar zata bari.

Ita kuma haka Allah ya daura mata son wanda be san yadda soyayya take ba.

Nikam nace son wacce ba ta ita yake ba dai.

Kamar yadda sukayi da yamma ta shirya tsab. Cikin Riga da zani na atamfa.

Sai babba mayafi da ta yane jikin ta dashi, duk wanda ya kalle ta yasan tana cikin damuwa.

Dan Mama ma sai da ta tambaye ta abinda ke damun ta.

Wajen karfe hudu da rabi Khaleel ya kira ya shaida mata ya zo.

Dakin baki tasa aka kai shi, lemo ta aika masa dashi, sannan ta je ta fadawa Mama ana kiran ta a waje.

Ganin ta da shiga mai kyau yasa Mama bata damar zuwa.

Da sallama ta shiga dakin kanta a kasa, amsawa yayi, cikin sakin fuska, yace,

"Sannu da zuwa, Matar mu insha Allahu."
A ranta ta amsa da Ameen.

Can daga gefen sa ta zauna kan ra akasa.
"Ina yini?"

Murmushi kwance a fuskar ta, ta gaidashi.

"Lafiya lou Summaiyya ya gidan ya su Mama."
"Lafiya lou suke."

"Sumaiyya ina kara baki hakuri akan abinda ya faru, wallahi baki damuwar da ya shiga ba da be samu zuwa gun ki."

Wani sanyi taji a ranta jin ya damu da ita. Kai ta girgiza. Ta ce,
"Ayyah ba komai ai."

"Yauwah Nagode. Gaskiya nan indai Najib ya zauna tare dake zai kauna ce ki fiye da yadda yake kaunar ki yanzu haka."

Kai tayi kasa dashi alamar jin kunya. A raina nace sai kace ba Summy ba, wai har da su jin kunya abinda ba halin ta bane.

Hira suka dan taba duk akan Najib ne, yana mata bayanin Najib da abinda yake so, da yadda ya taso da wajen aikin sa da yan uwan sa dake garin nan.

Duk abinda yasan ya kanata ta sani akan Najib sai da ya fada mata su.

Sannan ya daura da,
"Najib nason mace me addini da ilimi, yaba son mace mai tsabta,

Please Login or Register in order to submit comment