Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zasu zo suga jikin."

Kai kadai Najib ya daga ya zuba wani uban tagumi.

Kansa Mami ta shafa ta ce,
"Ka dauki hakuri kaji."

Kai ya gyada ya ce,
"Ina kokarin Mami."

"To Allah dada hakuri ya bata lafiya."
Shifa rasa me ma zaiwa Najwa yake. Yanzu baida abinda zai taimaki Najwa da shi. Sai addu'a.

Sumaiyya kuwa tana can ta shiga wata harkar gidan ta cika da kawayen ta su tayin shakiyanci suke yi.

Wani barin na zuciyar ta na tambayar ko Najwa ta mutu ko tana raye.

Ko kiran Najin batai ba taki lafiya ko ba lafiya ba.

Ta fi sawa a aranta Najwa ta mutu tinda taga bata ga Najib ba.

Ai kuwa in hakan ta faru ita me zatayi, wani lokacin tsoro na kamata sai dai in tatuna in Najwa ta mutu ba wanda zai fadi wanda ya shiga part din ta ma.
wannan na kwantar mata da hankali.

Duk abinda take jikin ta a sanyaye take yin sa.

Daan tsoro yafi yawa a cikin zuciyar ta.

Ni abinda yafi bani mamaki shine bata fargabar Najwa ta mutu zunubi akan ta.

Duniya ta baci inda har mutum yake neman kashe dan uwan sa akan abinda be kai ya kawo ba.

Ansan dole kowa yana da kishi to akwai kishi na tsarin addinin musulunci.

A yadda na fahimci kishi shine kuna gasar wajen faranta ran me gidan ku.

Allah ka kare mu daga sharin shaidan da zuciya. Ameen.



Sai yamma sannan su Ummah da Baffah suka zo tare da Hamma Salim dan Mami ta ce bazata iya zuwa ba.

Mami akwai kunya da kara, duk yadda take son ganin Najwa amman hakura tayi sai addu'a da take binta da ita.

Basma kuwa kuka take kamar ranta zai fita bama da Mami ta ce bazata je ba.

Tofi Baffah ya dinga yiwa Najwa, a gidan Mami suka kwana.

kwanan Najwa biyar bata motsi sai Numfashi.

A na shidan ne, da Yamma ba kowa a dakin daga Najib da ya kwantar da kai a gefen gadon ido sa jajir.

Baya samun bacci bare cin abinci, Numfashin ta ne ya fara kokawa da sauri ya mike kasa taimaka mata yayi wannan yasa ya danna bell din dakinsa dan kiran taimakon gaggawa.

Da sauri likitoci suka yo kan ta, sun jima akan ta, dan sai da suka dauki fin awa biyu.

Najib kuwa ya kasa tsaye bare zaune, hawaye ne ke tsiyayya ta idon sa kawai.

Mami sai lallashin sa take. Sai da sukai awa biyu sannan suka fito daga dakin.

Najib ne ya tari Farouk ya ce,
"Farouk ya jikin?"

Dafa shi Farouk yayi ya girgiza kai ya ce,
"Sai dai kayi hakuri."

"What?"
Rumgume shi yayi, yana bubuga bayan sa, ya ce,
"Kullu Nafsin za'ikatul mauti."

Gun Mami yayi, ya ce,
"Mami zo kiji me Farouk ya fada."

Janyo Mami yayi, suka yo gun farouk da ya tsaya kamar dutse.

Kamoshi Faruok yayi, dan yaga baya cikin hayyacin sa, rumgume shi yayi yana shafar bayan sa, tini ya fara  sulalewa daga jikin Farouk.

Da sauri Farouk ya dago shi yana kiran sauran likitocin dan bashi taimakon gaggawa.

Mami kuwa da su Bara'atu Kuka kawai suke yi.

Bame lallashin kowa, Dady ne ya shigo asibitin ganin suna kuka yake tambayar lafiya.

Baba ita tayi karfin halin shaida masa halin da ake ciki.

"Innalillahi wainna illahir rajiun."
haka Dady yayi ta fada tana rike da kan sa.

Sun jima a tsaye duk sun rasa abinda zasuyi.

Dady ne yayi karfin cewa,
"Kuyi hakuri, haka Allah ya rubuta. Allah ya jikan Najwa. Bari naje a dauke ta aje a shirya ta. A kaita gidan ta na gaskiya."

Wannan maganar ita ta kara rikita su Bara'atu. Wai da gaske dai Najwa ta mutu.

Kuka suka kara fashewa dashi.

Anan aka kira waya aka shaidawa su Mamin Najwa da Dadyn ta.

A can Kano ma duk mutuwar Najwa ta karade ko ina kowa kukan rasuwar Najwa yake.

Basma kuwa ai itama sume musu tayi da kuka.

Mami kuwa sai addu'a take yi, tana Allah yai wa Najwa Rahama. Kukan ma ta kasa.




*Allah ka jikan dukkan musulmai. Allah ka kyautata namu zuwan, Allah kasa muyi kyakyawan karshe.*

*Ameen!*


*Allah ka jikan mahaifan mu, yan uwa abokan arziki alummar annabi mohd (SAW)
*Ameen!*

*MS Indabawa*

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*165*





Magariba da tayi ne yasa ba a tafi kai Najwa ba.

An ajiye ta a dakin Mami, inda dakin yake a ciki da yan uwan Mamin ta, da yan uwan Dadyn ta.

Duk addu'a suke mata, Najwa na kwance cikin sitirar ta.

Kuka kuwa gidan duk a rikice yake. Mamin Najwa sam bata zo ba.

Ta ce,
"Da zuwana da ba zuwana duk daya ne, addu'a ce dai kuma bakina bazai taba daina yiwa Najwa addu'ar samun Rahama ba."

Mami dake gefen Najwa ta zuba mata ido taga kamar likafanin na motsi,

Bude fuskar Najwa tayi, ji tayi, tana cewa,
"Hamma! Hamma!"

da sauri Mami ta kalli jama'ar dakin tana cewa,
"Najwa bata mutu ba."

Da sauri jama'ar dakin suka yo kan ta, Kuje ku kira min driver.

Mami ta fada tana dauko wani katon hijab.

Najwa ta sakawa sannan ta kira Dady da kansa yazo ya dauke ta suka yi asibiti.

Suna zuwa aka amshe ta aka yi office din Najib inda ake duba ta.

Ruwa suka jona mata, Dr Farouk kuwa sai Hamdala yake ga Allah da yasa Najwa bata mutu ba.

Cikin ikon Allah wajen karfe Dayan dare sai ga Najwa ta bude ido, Mami ta gani zaune a gefen ta.

Mami ta kalla, ta ce,
"Mami, ina Hamma?"

"Sannu Najwa, sannu kin tashi?"
Ta danna bell da sauri Dr Farouk ya shigo, dudubata yayi, ya ce,
"Alhamdulilah! a samu a gasa mata jiki sai a bata ruwan zafi ta sha."

Mami da kanta ta hada mata ruwan wanka, wanda Najwa kasa tafiya ma tayi sai a kujera aka daurata aka kai ta ban daki.

Mami da kanta ta gasa mata jiki, suka fito ta canja mata kaya sannan Dady ya tayata daura ta akan gado.

Duk abinda Likita ya ce ai mata sukai masa.

Sai dai duk yadda ta motsa jikin ta sai ta ce,
"Wash!"

Mami sai sannu take mata, ai dole jiki yai ciwo ace kana kwance kwana da kwanaki.

Mami tausayin Najwa take dan har hawaye sai da ta zubar mata.

Najwa ta rame sosai, tayi haske idon ta duk sun zurma.

Allura aka karai min na koma bacci.

Da safe ina tashi Mami ta karai min wanka ta gasa min jiki, Dr Farouk ne ya bata wani magani ta shafa min a jiki na.

Ruwan Zafi kadai ake bani tin daren jiya.

Ganin har lokacin Hamma Najib be zo ba yasa Najwa mamakin ina yake, ko tsoron ta yake ji ne?

Kasa daurewa Nayi na kalli agogon office din, karfe Takwas da rabi, amman har yanzu ba Hamma wanda duk jama'ar da suka zo ta'aziyya ta kowa yazo yai min sannu.

Har su Mami nah duk sun kira suna min sannu, Basma kuwa ai sai murna Addu'ar ta bata mutu ba.

Ina kwance ina tunanin Hamma, abin na damuna na rashin ganin sa.

Ni dai kasa Daurewa nayi, nace,
"Mami ina Hamma ne, ko baya nan ne?"

"A'ah yana nan, shima yana cikin asibitin nan be da lafiya, amman yanzu Dady ya ce, min ya farka, ki kwantar da hankalin ki da sauki."

Hankalina ji nayi ya kara tashi da a kwance nake da sauri na mike zaune, zaman kasa yi min yayi na mike da sauri.

Ai kuwa nayi gaba zan fadi saboda rashin kwarin jiki na.

Da sauri Mami ta riko ni, ta ce,
"Ina zaki?"

"Mami gun Hamma zani."
Zaunar da ni Mami tayi, ta ce,
"Kiyi hakuri, anjima kaje kinji."

Dan dole na hakura, kwanciyya nayi amman duk hankalina baya jikina.

Karfe uku ina kwance naji an budo kofar dakin Juyowa nayi.

Hamma na gani da sauri ya shigo. Mikewa nayi zaune da sauri.

Sai da yazo gaban gadon ya durkusa, hannun sa ya kai, kan wuya na, ya taba fuskata, ya juyar da ita gefe, ya kuma juyar da ita gefe.

Wani murmushi ya saka, rumgumeni yayi a jikin sa, ya dago ni ya kuma mayar dani.

Sai da yai haka sau uku sannan ya kamo hannuna, ya kai dan yatsana bakin sa.

Cizar hannun yayi, wata kara na saki da sauri ya zare hannun yana dariya. Nima dariyar nayi.

Kan gadon ya hau ya zauna, ya janyo ni jikin sa ya rumgume ni.

Saukar danshi naji a bayana wannan yasa na dago da sauri.

Haawaye na gani a idon Hamma Najib,
"Haba Hamma mene abin kuka?"

"Najwa hankalina ya tashi sosai, kwakwalwata ta samu rudani da kin mutu da bansan ya zanyi da rai na ba. Da bansan ina zan shiga ba. Da bansan ya...."

"Haba Hamma, kamar ba musulmi ba, zaka dinga ringa wannan maganar, baka san Allah na jarabar bawa yaga ya zai yi ba.
Ka kuma san Allah me rahama da jinkai da ya baka ni, da ya dauke ni, haka Allah zai mayar maka da wacce tafi ni, hamma kana mika komai ga Allah dan zai iya jarabar ka yaga yadda zakayi."

Yatsan sa ya saka ya rufe min baki, ya ce,
"Najwa nasan da wannan kuma ina kokari, amman ki tayani da murna da godewa Allah da ya bar min ke."

Ya fada hawaye na zubowa daga idon sa.

Magana ya cigaba dayi,
"Bazan iya kwatan ta miki halin da na shiga ba da baki da lafiya, haka nan bazan iya kwatan ta miki halin da na shiga ba da aka ce min kin mutu. Cikin kan kannin lokaci na koma wani iri...."

Mami ce ta shigo dakin da sallama. Da sauri Najwa ta janye jikin ta daga na Najib.

Basket ne a hannun ta, mikawa Najib tayi, ta ce,
"Ka bata abincin ta ci."

Kai ya gyada mata, fita tayi. Kallon sa ya maida kan Najwa wacce take shafa cikin ta.

Tinda ta farka bata ji motsin da ya sabai mata ba. Ko lafiya?

Tausaya mata yayi, ya ce,
"Baby na. Komai ya samu ga bawa mukadari ne, kuma haka Allah ya kaddarar ta mana."

"Haka ne Honey. Me ya faru?"
Hawayen idon sa ya goge ya ce,
"Baby mun rasa Babyn mu."

"Innalillahi wainna illahir rajiun!"
Ta fada a cikin zuciyar ta.

Shiru tayi, kallon ta yayi ya jawo ta jikin sa, yana lallashin ta dan yasan kukan zuci take duk dan kar ta tayar masa da hankali.

Najwa bata taba kara sanin tana son Cikin jikin ba sai yanzu da ta rasa shi.

Tabbas kamar ya sani kukan zuci take dan sai ajiyar zuciya take saukewa.

Sun jima a haka kafin ta daina.

Zaunar da ita yayi ya zubo mata abincin da Mami tayo mata.

Dankali ne da hanta ta dafo mata, sai farfesun kayan ciki.

Kadan ta iya ci dan cikin ta a cunkushe yake.

Suna gamawa cikin ta ya hau ciwo nan da nan Najib ya rikice.

Dr Farouk ya kira, dubata yayi ya ce tasha magani ba wani abu bane, rashin cin abincin da batayi ne kwana biyu shiyasa. Amman a hankali zata daina ciwon in ta ci abinci.

Shifa Najib yana mantawa dashi likita ne, dan indai abu ya samu Najwa rikicewa yake ya manta da komai da komai.

Sai da ta Sha maganin sannan cikin ya lafa mata.

Bacci ne ya sauke ta. Kwanan su Uku suka Koma gida.

Gidan Mami suka koma dan Mami sam taki ta bar mishi Najwa dan har yanzu bata gama warwarewa ba.

Haka ya hakura, kayan da Mami tasa ya dauko a gida shi ya tuna masa da Sumaiyya ma.

Yana shiga gidan yaga shigar ta part din ta ita da wasu kawayen ta.

Bangaren Najwa yayi ya debo mata kayan sawar ta.

Har zai wuce ya ce, bari ya leka gun Sumaiyya.

Zai shiga kenan yaji shewar su, suna cewa,
"Ashe kin rabu da Alakakai."

Suka kara kwashewa da dariya. Be san da wa suke ba kawai ya juya ya bar wajen.

Gidan Mami ya koma, dakin Mami ya shiga dai dai fitowar Najwa daga wanka kenan.

Karasawa yayi ya kamo ta, ya zaunar da ita a gefen gado.

Shi ya shirya ta, sannan ya saka mata kaya.

Kwanciyya tayi dan bacci take ji. Shima gadon ya hau zai kwanta.

Da sauri ta Najwa ta mike, kallon ta yayi ya ce,
"Menene cikin ne?"

Kai ta girgiza ta ce,
"Allah ka tashi ka fita salam Mami tazo ta ganmu tare."

Kallon ta ya tsaya ya ce,
"To shine me?"

"Haba Hamma kai fa baka da kunya ko?"
Baki ya bude yana kallon ta.

Ya ce,
"Nine banda kunya ko?"

Kai ta girgiza,
"A'ah zan nuna miki bani da kunya ne a gaban Mami."

"A'ah Hamma ayi hakuri."
"Naki."

"Shikenan."
Ta fada tana mikewa.

Janyo ta yayi ta fada jikin sa,
"Yi hakuri man."

Shiru tayi tana kokarin tashi daga jikin sa.

Tausa ya farai mata, tausar da rabin ta tsokana ce.

Tini jikin ta yai sanyi tai shiru tana amsar sako da yake aika mata.

Jin shirin yai yawa yasa ya leka fuskar ta.

Idon ta a lumshe, sai murmushi take.

Cakul kuli yai mata ai kuwa da sauri ta mike tana dariya.

"Haba Honey Bacci fa nake yi."
"Na sani amman akwai abinda nake so muyi magana akai."

Mikewa tayi zaune, ta ce,
"Ina ji."



*MS Indabawa*

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*166*





"Ina ji."
ta fada tana gyara zaman ta.

"Najwa kar ii boye min komai a abinda zan tambaye ki. Dan Allah ki fadan gaskiya."

Gane abinda zai tambaye ta, yasa ta kwanta, ta ce,
"Kaga anjima mayi maganar bacci kaji."

Daga ta yayi, ya kalle ta. Fuska ta marairaice masa.

"Shikenan!"
Ya fada yana kwantar da ita, jijjiga ta yake yana matsa mata jiki har tayi bacci.

Ya jima a dakin yana kallan ta, tabbas Najwa ta gane abinda yake son tambayar ta. Kuma yasan indai Najwa ce to bazata taba fada masa abinda zai tambaye ta ba.

Ta ina zai fara tunanin inda zai gano wanda yai mata wannan abun.

Ya  jima a dakin. kafin ya mike ya fita.

Gida ya koma dan debo wasu takardu, bangaren Najwa yaje yana zaune a falo yana tunanin abinda ya faru.

Kai ya daga ya daura akan jikin kujera kamar ance ya kalli sama, yaga CCTV camera da akan saka masa

Da sauri ya mike har yana tuntube ya shige bangaren sa

Dakin da ya zuba computer da kayan karatun sa ya shiga.

Connecting yayi ya sako abinda ya faru tin daga saka camerar tin daga dakin Sumaiyya.

Da lokacin da ta sha maganin ta na karshe da maganar cire mahaifar ta, da lokacin da ta balli magani ta fita daga bangaren ta, har ya zuwa yau da yagansu da kawayen ta.

Shige da ficen ta duk sai da ya gani, lookacin da baya gidan bata fiya awa biyu a gidan bama.

Ta bangaren Najwa kuwa yana ganin yadda take gudanar da gyaran gida da su karatun alkura'ani.

Duk yana gani wani abin in tayi yayi dariya wani kuma ya kasa magana ma.

Bama in tana zaben kayan da zata saka masa, sai tasa kaya kala nawa kafin ta zabi wanda take so.

Haka wajen kwalliya, in ta gama ta juya can ta juya can ita kadai dai.

Najwa na burge shi matuka. Zuwan Sumaiyya bangaren Najwa ya gani nan da nan ya maida hankalin sa kan naurar.

Tambayar ta abinci da tashin Najwa, daukar Maltinar Najwa da zuva mata wasu kwayoyi duk ya gani.

Hana ta sha da tafiyar ta.
"Innalillahi wainna illahir rajiun."

Kawai Najib yake fada, be taba kawo wa aransa Sumaiyya zata iya abinda ta aikata ba.

Wani iri yanayi ya dinga ji, fadar bacin ran da ya lullube shima bata baki ne.

Rasa me zaiyi yayi, mikewa yayi da sauri, yai waje. Zai shiga bangaren Sumaiyya kenan Dady ya kirasa.

Dauka yayi yana futar da wani irin numfashi.

Dady najin haka ya ce,
"Son lafiya?"

Bai tsaya jin amsar sa ba yace,
"Kaga ka zo yanzun nan ina jiran ka."

Yasan Halin Najib ya tabbata rai aka bata masa in ba haka yayi ba bazai zo ba.

Bangaren Sumaiyya ya kalla ya juya ya shiga mota ya bar gida.

Da gudun tsiya ya bar gida. Ko da zai shiga gidan daga driving dinshi Dady yasan ba lafiya.

Ya jima bega Najib a cikin irin wannan bacin rai, zai iya cewa tin yana yaro amman yanxu me akayi har ransa ya baci haka.

A hankali ya fito daga motar ya nufi gun Dady dake zaune a cikin wata rumfa zaune akan wata kujera. cikin Rumfar ya nufa ya zauna kansa a kasa.

Ruwan sanyi dady ya mika masa, amsa yayi ya sha. Kara masa yayi amsa yayi ya dada sha.

"Najib!"
Dady ya kira sa.

Dagowa yayi ya kalle sa da idon sa jajir ba tare da sun amsa ba.

"Kayi hakuri ka fawalawa Allah komai, Kana ambaton  Allah zaka samu sauki a cikin ran ka."

Kai kawai ya gyada masa, a ransa yana ta addu'a.

A hankali a hankali, ya fara jin sauki a cikin zuciyar sa.

Gumi ne ya hau karyo masa alamar ya gama sauka kenan.

Duk abinda ke faruwa Dady na kallon sa.

Sai da ya nutsu sannan Dady ya ce,
"Son me yake faruwa ne?"

Kuka ya fashe da shi da sauri Dady Ya mike yayi gefen sa.

Kansa yake shafawa yana lallashin sa har ya samu yai shiru.

"Haba Son ka rage sa abu a zuciya komai na duniyar nan dan hakuri ne, fada min me akai maka?"

"Dady Sumaiyya bata kyauta mana ba. Dady ashe Sumaiyya ita ce sanadiyar rashin lafiyar Najwa."

Nan dai ya fada masa ta yadda abin ya faru.

Kai kawai Dady yake girgizawa, Mikewa Najib yayi yai cikin gida.

Bangaren sa kawai ya nufa ya dauko Paper yayi rubutu ya ajiye, kwanciya yayi ya rasa me ke masa dadi.

Tab lallai, ya yadda Sumaiyya ta wuce duk inda take tunani.

Bama a abinda ya gani irin kawayen da take kulawa da abubuwan da suke masa a gida.

Gaskiya har ga Allah kamkamin gidan ma yake ji.

A cikin gidan sa ake masha'a ayi shaye shaye.

"Innalillahi wainnaillahir raijun"
Haka yai ta nanatawa har ya samu sauki bacci ya dauke shi.

Sai magariba ya tashi yai wanka ya wuce massalaci.

Najib be dawo gidan ba sai tara saura. Najwa kuwa tana can tana zuba idon ganin sa amman shiru.

Tana kwance a dakin Mami tayi shigar bacci ya shigo dakin.

Da sauri ta mike dan tin daga muryar sa ta gane ba lafiya.

Karasowa yayi cikin dakin, kallon sa ta tsaya yi, kafin ta kamo hannun sa, ta ce,
"Honey lafiya me yake faru?"

Jikin sa kawai ya jata ya rumgume ta, sun jima a haka kafin ya sake ta.

"Hamma kayi hakuri, ka daina sa abu aran ka abi yazo ya samu lafiyar ka. Kana barin komai ga Allah kadai Addu'a ce taka. Dan Allah ka daina barin bacin rai na tasiri a cikin zuciyar ka. Allah yasa bani na batawa mijin rai ba."

Janyo ta ya karayi jikin sa, ya ce,
"Matan Albarka irin ki basa batawa mijin su rai, kullum burin su fara ta musu. Kuyi hakuri daga yau na daina saka damuwa arai na. Ina dake nasan ban da sauran damuwa. Ina kaunar ki Najwa."

Ya hade bakin su, wani abu Najwa taji yana yawo a jikin ta dan ta jima rabon ta da wannan abin tin da ta tashi a ciwo.

Duk kulawa Najib yaba bata amman be fiya kissing nata ba dan ya ce,
"Kiss na saurin tada shi,"

Ma'ana da yayi kissing mutun baya iya controlling feeling din sa.

Shi kuma tausayawa Najwa yake dan yasan dauriya kawau take.

Yanzun ma, sai da ya fara fita a hayyacin sa yaji jikin Najwa zafi. Wannan yasa ya barta ba dan yaso ba.

Sai rumgume ta da yayi yana saukar da ajiyar zuciya. Ranar a dakin Mami ya kwana.

Tin Asuba Najwa ta koreshi dan ta ce, Mami bazata zo ta gansu tare ba.

Da safe kamar yadda Mami ta saba da kanta ta kawowa Najwa kayan karin ta.

Lokacin ta fito daga wanka, tana ganin Mami ta karasa gaban ta ta amshi kayan hannun ta.

Dire su tayi, ta durkusa, tana gaishe da ita.

"Ina lafiya Najwa ya jikin naki?"

"Mami jikina ya warware Alahmdulilah."

"To Alhamdulilah haka nake so. Daman na gama hada miki komai na ce, tinda Mamin ki na mana fulatanci ya kamata ke kije ta ganki tinda ita ta kasa saboda kunya."

Kan Najwa a kasa amman zuciyar ta kamar takarda zata je taga Mamin ta.

"Anjima za a gama miki komai dan haka nan da gobe sai mutafi ko?"

Murmushi tayi, ta ce,
"Nagode Mami."

"Ba komai, ki fadi duk abinda kike bukata sai ayi kafin goben."

"Mami bana bukatar komai."
"A'ah dai ki fada dai,"

Shiru Najwa tayi, sanin halin Najwa yasa Mami cewa,
"Shikenan bari naje."

Ta mike ta fita. Tana fita Najib ya shigo dakin, tana ganin sa ta hau gyara hijab din jikin ta dan daga ita sai towel.

Zamewa tayi daga kan gadon da take zaune ta ce,
"Hamma ina kwana?"

Kai ya make alamar be amsa ba, hannu ya bude mata.

Mikewa tayi a hankali ta fada jikin sa.

Ya ce,
"Ko kefa, wannan nake bukata tukkuna."

"Ina kwana?"
"Baby na lafiya, kinsan kwana a tare dake ya fi komai saka min kwanciyar hankali."

Sakin sa tayi, tayi gaba mudubi tana daukar mai zata shafa.

Da sauri ya amshi man hannun ta, ya lakata yana murzawa a hannun ta kafin ya yaye mata hijab ya murza mata a cinyar ta.

Tsigar jikin ta ce, ta tashi ido kawai ta lumshe har ya gama shafa mata man.

Shi da kansa ya dauko mata kayan da zata saka.

Sai da suka gama sannan ya zaunar da ita akan kafet din dake tsakiyar dakin ya fara hada musu break.

Duk abin nan da yake tana kallon sa, shi ya gama hadawa ya fara bata a baki har ta koshi sannan shina ya ci.

Kanta ta kwantar akan cinyar sa, shafa kan yake idon ta a lumshe.

"Baby nah!"
Ya kira sunan ta a hankali.

"Na'am!"
Ta amsa tana dago kanta  ta fuskan ce shi.

Kiss ya manna mata akan leben ta, ya ce,
"Baby nah kiji Mami wai gobe zaku tafi kano ko?"

"Eh haka ta fada min. Menene?"
Numfashi yaja, ya ce,
"Baby nah bana son nayi nesa dake, ganin ki a tare dani shi ke dada min kuzari."

Fuskar sa ta shafa, ta ce,
"In har baka son naje na hakura da zuwan."

Kai ya girgiza ya ce,
"A'ah bazan taba kin abinda nima kike so ba. Amman ki sani nasan sai na biyo ku."

Murmushi tayi, ta ce,
"Me zai hana mu tafi tare."

"No akwai wani abu da zan gama shiryawa ne, so nake da mun dawo mu tafi cin amarcin mu ko?"

Fuska ta rufe da tafin hannun ta, dariya Yayi ya kai bakin sa za ciji hannun.

Da sauri ta janye tana dariyar ita ma. Sun jima a tare kafin ya mike zai fita. Ita ma Mikewa tayi, ta ce, zata gun su Baba.

Tare suka fita hannun su rike da na junan su.

Zasu fita kenan Mami ta sauko daga sama.

"Najib!"
ta kira sunan sa.

Juyowa yayi, ya amsa da
"Na'am!"

Da sauri Najwa ta zame hannun ta tayi waje.





*MS Indabawa*

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page *167*







Cikin falon ya koma yana kallon Mami.
"Kazo Dadyn ka na son ganin ka."

Ta juya, bayan ta yabi. Dady ma zaune a dakin sa Najib ya shiga.

A gefen sa ya zauna, ya dukar da kai ya ce,
"Dady gani."

Kallon sa Dady yayi ya ce,
"Me kayiwa Sumaiyya jiya?"

Dagowa yayi ya kalli Dady, sannan yai kasa da kai, ya ce,
"Bam mata komai ba."

"To shikenan kar kai mata komai ka barta da Allah."
Kai Najib ya girgiza ya ce,

"Dady ba irin su Sumaiyya ake bari da Allah ba, Dady niyyar kisa fa tayi, tayaya zan cigaba da zama da ita na tabbata wata rana ni zata so kashewa. Ko ya'ya na."

Mikewa yayi ya sauka, ya bar mahaifin nashi.

Wajen ginin da yasa a ke masa ya nufa ya ce, yana son a tada ginin a gama nan ba dadewa ba.

Shifa sam bazai iya cigaba da zama a gidan can ba.

Najwa kuwa tana zuwa gun Baba suka zauna hira ita da Su Bara'atu.

Anan ta yini dan sunyi dan malele ta zauna suka ci suka koshi.

Sai la'asar ta koma bangaren Mami. Mami ce zaune kadai a falo.

Gefen ta ta zaune wajen kafufun ta.,   ta ce,
"Mami sannu!"

"Yauwah Najwa."
Kallo suke babu wanda ya kuma magana a cikinsu.

Can Mami ta ce,
"Najwa komai ya zama ready gobe sai gaban Mami ko?"

Fuska ta rufe tana gyada kai,
"to ga kaya can a daki inji Dady ya ce, ki bawa wanda kika ga ya cancan ta, sannan ga dubu dari can ya ce, inda abinda zakiyi da su."

"To Mami nagode Allah saka da alheri Allah dara girma da arziki."
"Ameen Najwa Allah miki albarka ya baki zuri'a ta gari."

Tashi tayi da sauri ta abar dakin, Mami kuwa murmushi tayi.

Najwa dai har tai bacci ranar bata ga Najib ba. Kuma ta kira wayar sa duk a kashe. Da kyar ta iya bacci.

Washe gari kamar yadda ta saaba komai haka ta kimsa, kayan da Najib ya debo mata su

Please Login or Register in order to submit comment