Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwance.

Ba abinda take gani a cikin idon ta face so da kaunar ta da suka mamaye shi.

Shima kallon sanin yake mata, amman yana daukar wannan sanin da ganin da yayi mata sune suke sawa yake kallon ya santa.

Idonun ta ba karamin burgeshi suke ba. Manya ne, masu kyau da su. Gasu farare tas dasu.

In ta saka kwalli wani kyau suke karawa da girma.

Yana son mace mai ido sai gashi Allah ya bashi Najwa me idanu abin shawa'a.

Haka nan bakin ta ba karamin son su yake ba. Dan dan karami ne abin sha'awa gasu pink da su  daga ido ma kasan masu laushi ne.

Haka hancin ta dogo ne gashi siriri. Gaban goshin ta kuwa gashi ne kwance luf luf dashi.

Haka jirar ta me kyau da ita a gyare kamar wacce aka yanke ta.

Suna jima suna kallon sunan su. Kuwa na aikawa da dan uwan sa sakon su ta idanun sa.

Najwa ce tayi karfin halin dauke idanu  ta tare da rufe fuskar ta da hannun masu kyau tsirara dasu.

Dariya yayi, ya ce,
"Muje mu zauna in fada miki abinda nace sai mun hadu."

Gaba tayi a ranta tana son tuno da me zai fada mata.

Akan wasu kujeru suka zauna, kallon ta yayi, ya ce,
"Najwa yau baki tambayen Antyn ki ba."

Murmushi tayi, ta ce,
"Ai haduwar mukenan shiyasa. Ya take, ka baro ta da kewar ka. Allah in nice kafata kafar ka."

Wani dadi yaji a ransa. Murmushi yayi ya ce,
"To Allah kaimu lokacin! Abinda nake son fada miki kenan. Ina da mata. Zaki iya aure na haka."

Kai ta girgiza masa ta ce,
"A'ah!"

Ido yayo waje dasu, ya ce,
"Dan Allah Najwa ki taimaka ki soni a haka muyi aure dan  Allah."

Ganin yana neman ya sauka ya durkusa yasa ta ce,
"Da wasa nake maka fa."

Kallon ta yayi dan ya gano da gaske take.
Kai ta daga masa ta ce,
"To mene dan kana da mata. In ban auri me mata ba. Watakila ni a kawo min ita.
Ba yabon kai ba. Allah bana kin kishiya in har zamu zauna lafiya.
Bana ganin aibun ta sam."

kallon ta ya tsaya yi dan ba karamin burge shi tayi ba.

Kuma ya gano gaskiyar abinda take fada ta cikin idon ta.

"Gaskiya Najwa samun kamar ki sai ansha wuya. Allah ya mallaka min ke."

A ran ta, ta amsa da
"Ameen!"

Kallon ta yayi, ya ce,
"Baza kice Ameen!"

Murya ta marai raice, ta ce,
"Haba na fa, fada."

Dariya yayi kawai. Da haka suka dinga hira har Mustapha ya zo shima suka zauna suna tayi.

Sai magariba suka tafi, bayan ya bawa Zahra kayan da ya kawo musu. Da kyar ta amsar musu ta ce, kada ya kuma. Bayan godiya da addu'a da tayi masa.

Dadi yaji dan bai taba bawa Sumaiyya abu tai masa godiya ba.

Haka Najwa da Zahra takai musu itama godiyar tayi masa da jadadda masa dan Allah kada ya kuma.

Shi abin ma har dariya yake bashi sai kace wanda ya kai musu wani abu.

Haka wai kada ya kuma shikan bai ga lokacin da zai daina bata abu ba.

Haka da dare ya aika musu da kayan abinci su idomie lemuka madera bisit.

Ba yadda sukai haka suka karba. Godiya Zahra tayi masa. Najwa kuwa kin kiran sa ma tayi.

Dan ta fada masa kada ya kuma gashi ya kuma.

Duk kiran da yayi kin dauka tayi sai da ya hada ta da  Mustapha da Zahra.

Su suka shawo kanta. Godiya tayi masa tana kuma me kara jan hankalin sa da kada ya kuma.

"Wai me yasa kike fadan haka?"
Ya tambaye ta.

"Ni bana son mu daura maka nauyi. Kuma in a gida akaji fada za ayi mana. Dan Allah ka daina kashe kudin ka akan mu."

Gaskiya halayen Najwa na burge shi, dan da wasu ne karba zasu yi tayi.

Banda roko da yan matan yanzu suke wai ace saurayi shi zai na maka komai.

Ai wadan nan abubuwan su suke jawo wa yan mata su baci.

Wannan ta ce, saurayin ta ya mata abu. In ya mata dan Allah wata ba dan Allah zai mata ba.

Ko ta wacce hanya ce zatabi dan ganin an mata shi.

A koda yaushe yana godewa Allah da kuma kara addu'ar Allah mallaka masa Najwa.

Dan yasan  ya'yan sa zasu samu tarbiya da nagarta.

Yana tuna kullum sukai waya sai ta tambayi ina Mami ko ta ce a gaishe ta.

Abinda Summaiya bata taba yi ba, bare ta ce zataje.

In ya ce ma tazo suje sai ta kawo wani abu duk son da Mami ke  mata amman ita ta wufantar.

Abubuwa da yawa na  dada masa son Najwa.

Kullun sai yazo da yamma har lesson yake musu.

Haka in yana Abuja ta whatsapp ma yake musu ko ya koya musu assignment.

Ana haka har suka gama level three suka tafi hutu.

Duk yadda yaso yazo cikin hutun hana shi tayi ta ce ya kula da Antyn ta da aiki.

Yaso yazo ta nuna bacin ran ta wannan yasa ya hakura.

Tasan in har yazo sai yayi sati biyu ko uku.

To matar sa fa, da aikin sa. Ai zasu shiga hakkin ta.

Shi ita nauyi take ji ace wani yazo gunta.


*Bayan shekara daya*

Abubuwa da yawa sun gudana. A ciki har da kara shakiwa tsakankn Najib da Najwa.

Wanda duk wata sai yaje ya ganta duk da basu taba haduwa a gida ba.

Su Najwa har an kammala makaranta sun fita service.

Inda aka saka ranar bikin Zahra wata biyu da fara seevice din su.

Wannan yasa Najwa ta ce, sai ta kammala service din ta zata koma gida gaba daya.

Su Mami da Dady duk sunzo graduation din su dasu Hamma Salim.

Da first class suka fito, Najib be samu damar zuwa ba saboda baya kasar.

Ba karamin rashin jin dadi sukai ba. Ranar da zasiyi dinner din su a ranar ya dawo dan haka katsina ya sauka.

Ranar kawai ya samu hallartar bikin kammala karatun su.

Sun sha hotuna inda ya basu kyaututuka masu yawa dan har waya ya sauya musu.

Lokacin dai dole suka amsa suna masa godiya.

Washe gari ya koma Abuja.


Sumaiyya kuwa ba abinda ya canja sai gaba da abubuwa suka karayi.

Dan kazantar ta ta kuma yin gaba.

Ta kuma samun ciki wanda Najib be san da shi ba ma ta zubar da shi.

Kawaye sai kara rudar ta suke bata yin abu dan kanta sai kawaye.

Gata kullum bani bani. Najib kuwa sai addu'a yake mata.



*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*129*





Lokacin bikin Zahra yazo, Amman Wannan karan ma Najib baya kasar.

Najwa ba karamin jin haushi tayi, inda ya ce, in ya dawo zasu karayin wani reception din nasu.

Ba yadda ta iya sai dai hutuna da vedio da take tura masa.

Amman gaskiya yayi missing dan kyan da Najwa tayi kwayi tsammanin ita ce amarya.

Ji yayi kamar yayi tsuntsuwa ya dawo to ba yadda zaiyi karatun yake dadawa, na wata takwas inda yanzu wata daya ya ci.

Gashi gab da bikin ya tafi. Duk dai abinda zata bukata sai da ya dire mata. Dan wani lokacin sai dai kawai taji alert ta account din ta.

Mamin sa ma taje bikin haka Dadyn sa amman shi besan bikin Zahra suka je Katsina ba.

Anyi biki lafiya an gama lafiya inda aka kai amarya gidan ta kato me kyau da shi.

Ba abinda babu a cikin gidan nan. Tare suka cigaba da bautar kasar su da Najwa.


*Bayan wata biyar*

Su Najwa an kammala service inda tana ta shirye shiryen tafiya gida.

Su Momy kuwa duk basuji dadin tafiyar da zatayi ba.

Ana ya gobe zata tafi a gidan Zahra ta kwana kuka kuwa akarasa me rarrashin wani.

A haka a gida ma daga Najwa har Kannen Zahra kuka suke.

Da haka suka rakata. Sai da sukaga tafiyar ta sannan suka dawo gida da kewar ta.

A gida kuwa ai dan party Hamma Salim da Basma suka hada mata.

Da murna suka tare ta. Dan  Dady ko fita beyi ba.

Wanka kawai tayi, akai mata kwalliya ta shirya cikin wani material baki, jikin sa duk stones ne kala kala.

Sosai tayi kayi, yan uwa da abokan arziki duk sun zo.

Inda Najwa ta samu kyatutuka masu yawa, ansha hotuna an ci an sha.

Inda sai dare ma aka tattafi.

Su Baffah da Ummah duk sun zo.

Sai isha'i tayi, sama tayi wanka tayi sallah.

Kan gadon ta, ta fada ta kwance wayar ta janyo taganta airplane mode.

Ido ta bude dan tasan Najib ya kirata be samu ba.

Cireta tayi, ta shiga hotuna tana son ganin wanda sukai ita da Mami, Dady, Hamma Salim da Basma.

Amman sam babu, wannan yasa tayi tuna ashe me camera da aka dauko ne ya dauke su.

Wayar ce tayi kara sakonni ne suka shigo.

Kafin ta bude kiran sa ta shigo,
"Baby na ina kika shiga wayar ki a kashe."

"Ayyah kayi hakuri, ban ma sani ba sai yanzu da na dauko ta."

"Ina kika je to."
"Wallahi Hamma nane ya hada min party, baka gani ba, har dasu Baffah duk sun zo fa. Kowa na nan ban da kai."

Ta karashe maganar cikin shagwaba,
"Sorry Baby na. Kema kinsan jiya naso na dawo amman ban samu dama ba. Gashi yau ma haka. Kiyi hakuri insha Allahu gobe zan sauka."

"Allah yasa."
"Ameen!"

"Amman fa sai mun kara yi a Katsina,"
"Haba dai, A'ah."

"Ina ruwan ki, da su Basma zamu yi abin mu."
Dariya tayi, ta ce,
"Ayi lafiya."

"Yauwah!"
"To yaushe zaka zo kano?"

"Bazan zo ba!"
"Saboda me?"
ta fada da muryar kuka."

"Oo Baby na yanzu ta zama shagwababiya fa,"

"Ni dai ga abinda na tambaye ka nan."
"To shikenan daina kukan."

"Na daina."
"Tayaya kike zaton zan ki zuwa wajen ki haka kawai. Ni da nake son na kasance tare dake a koda yaushe."

"Uhm!"
"Baki yadda ba kenan!"

"Ni bance ba."
Ta fada muryar ta kamar zata fashe da kuka.

"To shikenan bari na fada miki dalili na."
"Ina ji."

Dariya yayi, ya kwaikayi muryar ta, ya ce,
"Ina ji."

"Allah dan kaga ina son ji shine kake jamin rai ko?"

"A'ah a'ah yanzu zan fada miki."
Kukan karya ta fashe masa dashi,

"Yi hakuri, dalilina shine, bazan zo gidan ku ba, sai an san dani koma nace sai an bani ke."

Dariya tayi, ta ce,
"Da gaske?"

"Da gaske nake dan haka ki fadawa Dady, ya bada number wanda zamuje gun sa.
Kinsan da ta waje na ne da tini kin ahekara biyu a gida na.
To kince sai kin gama karatun ki. yanzu kuma ai kin gama ko?"

"Ni zan ma iya fadan ne?"
"To shikenan kar ki iya. Allah wannan kunyar taki karfa ta cuce ni."

Dariya tayi, kawai,
"Allah gobe nake son ki bani dan kafin na dawo na bawa Dady,  jibi suje."

"Ba bincike?"
"Baki yadda dani ba?"

"A'ah! Na yadda da kai."
"To ni na yadda dake ba sai an min bincike ba. Amman ke in munzo sai ayi ko?"

"Nifa bance ba."
"To me kika ce?"

"Sai na turo maka da number dai."
"Shikenan kinci abinci?"

"Yanzu zan ci."
"To kije kici ki dawo muyi wata magana."

"Toh!"
Ta fada, ta mike tana kashe wayar.

Dakin Mami ta shiga, Mami na zaune tana cin Nama.

Zama tayi itama taci ta sha lemo sannan tayi dakin Hamma Salim.

Yana zaune yana waya da Budurwar sa. Yana ganin ta ya bata suka gaisa sannan sukai sallama.

Kasa tayi da kai tana wasa da yatsun ta.

Kallon ta yayi yana dariya ya ce,
"Wai ke har yau kin ki daina jin kunya ta ko?
Nifa yayan kine in baki tambayen abu ba wa zaki tambaya."

Shiru tayi, kallon ta ya kuma yi, ya ce,
"Fadi mana kinji."

Ya kamo hannun ta. A hankali ta ce,
"Yaya daman wanda yake so nane ya ce, na fadawa Dady ya basu Number wanda zasuje gun su dan neman aure na."

Ta fada tana rufe fuskar ta. Dariya ya kwalkwale da ita.

Ya ce,
"Yanzu Najwa akan wannan kike jin kunya ta. Kada ki manta fa ni wanki ne, mene abin jin kunya anan."

Bata bude fuskar ta, ta mike, ta yi hanyar waje, ta ce,
"Hamma dan Allah ka fada masa dan gobe da safe yake spn number."

Ta fita a guje, Mami da Dady da suke Falo, suka bita da kallo.

Salim ne ya fito daga dakin sa yana dariya.

Gefen Dady ya zauna, Dady ya ce,
"Lafiya dai ko?"

Dariya yayi, ya ce,
"Dady kasan Najwa da kunya ai.  Sai kace akan ta aka fara bafulatana."

Dariya Dady, yayi, ya ce,
"Ai kunya ado ce."

"Haka ne Dady."
Mami ta ce,
"Kunyar me take ji to?"

Zama ya gyara, ya ce,
"Ta zo ta fada min ne, wanda suke soyayya dashi, yana son ya turo, shine suke so  address da number wanda zasuje gun sa."

Dariya Dady da Mami sukai, suka ce,
"Najwa kenan."

Dady ya ce,
"Abuja zasuje, sai ka bada Number Abban naku."

"To shikenan!"
Ya mike yayi dakin Najwa.

Najwa na kwance akan gado tana waya da Najib ya shigo dakin mikewa tayi da sauri ta kashe wayar.


*INDABAWA*

NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*

*AMEEN*

PAGE
*130*

*Hadiza Saban tnc for love. Nima ina son ki. Allah bar zumunci da kauna. Ameen.*

Really appreciate wit ur care.



Zama yayi a gefen ta, yana kallon ta,
"Shine kika kashe da ki bani mu gaisa."

"Kai Hamma."
Tayi kasa da kai.

"A ina yake ne?"
"A Abuja."

"Wane aikin yake?"
ya kuma tambayar ta.
"Likiti ne?"

"Yaushe kuka hadu?"
Kallon sa tayi,

"Eh! Mana ni dana yi budurwa ke nake fadawa kuma komai sai na fada miki. Kinga kuwa ke tinda baza ki fada min ba sai nai ta tambaya ko?"

Murmushi tayi, ta ce,
"Hamma ka bari ai zaka san shi ne?"

Murmushi yayi, ya ce,
"To shikenan! Dady ya ce, ki  bada Number Dadyn Abuja, da Number wayar sa."

"To nagode!"
Dariya yayi, ya ce,
"Sai da safe to."

Ya fita. wayar ta kashe dan kada Najib ya kirata. Dan kunyar sa ma take ji.


Najib tin kafin ya dawo ya sanar da Dadyn sa komai, ya fada masa gobe da safe zai turo Number dan ya fadawa Dadyn Kano ya sani.

Dariya Dady kawai yayi, ya ce,
"Sai ya turo."




Washe gari da safe ta tura masa, be duba ba kawai shima ya tura mata.

Dady na ganin sakon da daya turo yayi dariya, ya cewa Mami.
"Wallahi Najib ya mai dani kakan sa dai."

"Me yayi?"
"Wai ya ce, zai turon Number da Address din gidan yarinyar da zai aura shine ya turo number ta da address din gidan nan."

Dariya Mami tayi dan indai Najib ne haka yake shi kowa ma kakan sa ne.

Wannan tafiyar ma kaya sosai ya jidowa Najwa banda na lefe da ya kara hadowa.

Allah Allah yake ya dawo yaji labari a wajen Dady game da gidan su Najwa.

Sumaiyya likafa tacigaba dan kawayen ta sai suyi kwananki a gidan ta bama da Najib baya nan.

Yanzu a kalla ta zubar da ciki yafi biyar tin Najib na damuwa da rashin haihuwar har ya fauwalawa Allah.

Dan yasan ana samun irin haka.

Gashi 'dan Khaleel Najiib har ya shekara biyu da wattanni.

Yaro ne kyakyawa dashi, ga kuzari.

Zaman Khaleel da matar sa zama ne me tsafta.

Dan Khadija akwai iya girki ga tsafta ga ladabi da biyayya.

Sunje Abuja dan su hada su kawance da Summaiyya amman sam sai wani shan kamshi take.

Wannan yasa Khadijan itama ta janye jikin ta.

Duk abokan Najib nason su hada matan su da matar sa amman Sumaiyya bata bada fuska.

Wannan yasa duk suma suke janye jikin su sai dai suyi zumunci da Najib din kawai.

Tin abin na damun Najib har yazo ya hakura ma.

Yana dawowa ya nufi gidan sa. Ko ina a gyare yake dan yasa su Talle su gyara masa.

Har girki sukai masa. Abinci yaci, yai wanka sukai sha waya da Najwa. kwanciya yayi, dan yana son ya dan huta.

Be farka ba, sai karfe sha dayan dare abin ba karamin mamaki ya bashi ba.

Sallah isha'i yayi, ya koma bacci ba dan yaso ba dan so yayi ya je gun Dady yaji ya sukayi da mahaifan Najwa.

Sumaiyya kuwa duk da tasan Najib ya dawo amman bata neme shi ba.

Har dare tana zuba idon shigowar sa amman taji shiru,

Da kamar taje, sai kuma ta fasa wai dan kar ya raina ta.

Duk da a bukace take dashi. Kawayen ta sun hure mata kunne kan kar ta kuma yadda ta zauna a Nigeria bama yanzu da ya fada mata ya samu wani aiki da zaiyi na shekara daya.

Dan haka tasa a ran ta wannan karan itama sai ta fita daga kasar nan.

Da safe da ya tashi, yayi wanka sannan ya nufi bangaren Sumaiyya tana gado tana bacci.

Sanye take da wani dan mini siket da halfves a jikin ta.

Bacci take hankali kwance abin ta. Tinda ya daura idon sa akan ta yaji duk ya rasa control din sa.

Kan gadon ya nufa gadan gadan. Romancing nata ya fara yi da zafi zafi, cikin bacci taji shi, martani ta fara mayar masa dan itama tayi kewar sa da yawa.


Sai da suka jiyar da junan su sannan ya bar ta.

Shi yai mata wanka dan ba karamin wahala da sha a hannun sa ba.

Tare suka karya, suna cikin karyawa ne ya dube ta. Ya ce,
"Sumaiyya ki shirya muje mu gaida su Dady man."

Kai ta kawar gefe, ta ce,
"Gaskiya Najib bazan iya ba, dan wallahi a gajiye nake."

Kallon ta yayi kawai ya dauke kai. Sai da suka gama yayi bangaren sa ya canja kaya ya fita tsarabar yan gidan ya saka a mota.

Yana zuwa bangaren Baba ya wuce, ana zaune a falon ta, ya shiga da sallama.

Amsawa tayi, tana cewa,
"Murya wa nake ji kamar dan kirki nan."

"Baba nine."
"Lalale lalale sannu da zuwa Najibullah."

Ya shiga ya zauna suka gaisa suna hira su Bara'atu suka shigo.

Hirar ce ta kuma ballewa, ya jima a wajen su, ya bawa kowa tsarabar sa. sannan yayi bangaren Mami.

Tama zaune a falon kasa, suna waya da Mamin Najwa.

Ya shigo da sallama, amsawa tayi, ta ce,
"Kin ganshi ma."

Mika masa wayar tayi ya kalli screen din sannan ya kara a kunnen sa.

Gaisawa sukai ya tambayi su Salim da Najwa sannan ya mikawa Mami waya.

Sai da suka gama sannan suka gaisa.
Kallan ta yayi, ya ce,
"Mami ina Dady ne?"

"Dady ya fita amman yanzu zai dawo."

Be ji dadi ba amman ya zaiyi zaman jiran sa ta zauna yi.

Suma zaune Mami tayi kitchen, binta yayi, tare sukai girkin.

Can ya kalle ta, ya ce,
"Yauwah Mami, Dady be fada miki batun zuwa gidan su Najwa ba."

Kallon sa tayi, fuska dauke da alamar tambaya.

"Mami jiya fa na turo masa Number da Address din wajen wanda zasuje."

"Be min maganar ba. Ka bari in ya dawo ka tambaye shi."

Suka koma falo. Har akai Sallah Azahar Dady be dawo ba.

Yana Falo Dady ya shigo, mikewa yayi ya amshi jakar hannun sa sukai sama.

Sai da suka gaisa ya sauko dan yasan sai yayi wanka zai saiko kasa.

Mota yaje ya dauki kayan da ya kawo musu.

Yana zaune yana kallo Dady ya sauko. Abinci sukaje suka ci sannan suka koma falo.

Shi dai Najib ya kagu yaji bayani gun Dady amman Dady ya masa shiru.

Ganin shirun yayi yawa yasa ya ce,
"Dady wai ya batun sakon da na turo maka jiya?"

Kallon Sa Dady yayi ya ce,
"Ni banga wani sako ba."

Ido ya ware ya ce,
"Ya Salam! Dady baka ga sakon ba."

"Eh ban gani ba."
Wayar sa ya dauko a aljihu, ya duba sakon. Yaga yayi masa forwarding fa.

"Dady kaga."
Ya mika masa wayar.

Amsa Dady yayi ya kalli sakon, kallon Najib yayi ya ce,
"Wai ni kakan kane Son."

Kallon Dady yayi fuska da alamar tambaya, ya ce,
"Me kuma nayi Dady?"

Hararar sa yayi, ya ce,
"Kalli sakon da ka turon tukkun."

Wayar ya amsa ya duba sakon, ido ya zaro, ya ce,
"Dady ai Number ka ce da address dinka."



*INDABAWA*

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*131*


*Hajiya Nafisa. Our lovelly Anty. U are like Mother to us. Really love u. Tnx for ur Care. May Allah bless you.*
Ure  so special to me. Tnc for ur love.

*Allah ya barki da mijin ki ya yara Ya'yan ki, Allah kara miki lafiya da nisan kwana.*

*So much love Anty na.*

*Allah kara hade kan mu, dukkan marubuta.*
*Ameen*


Kallon sa Dady kawai yayi, tunani Najib ya tsaya yi.

Number Najwa ya kira bugu daya ta daga, kafin tayi magana ya ce,
"Wai Number wa kika turon ne?"

Shiru tayi, ta ce,
"Wacce Number?"

"Number da Address da kika turon jiya."
"Oh na Uncle dina ne."

"Uncle din ki?"
"Eh! Menene?"

"A'ah babu komai zan kira ki anjima."
Ya kashe wayar kan sa ya dafe.

Kara kiran ta yayi, dagawa tayi,
"Please dan karai.min resending kinji."

"Toh!"
Ta katse wayar. Ta tura masa.

Number Dadyn ce dai, wayar Dady ce tayi kara,

Dubawa yayi yaga dan uwan sa ne, dagawa yayi, da sallama.

"Assalamu Alaikum!"
A can bangaren ne aka amsa masa da.

"Wa'alaikum Salam Dan uwa."
"Na'am dan uwa ya gida ya iyalai."

"Lafiya Alhamdulilah!"
Najib mikewa yayi ya hau sama dakin Mami ya shiga.

Mami na zaune ta kalle shi, gani tayi ya canja lokaci guda.
"Lafiya Najib?"

Kan gadon ta ya fada yana fitar da wani irin numfashi, dafashi tayi, ta ce,
"Najib lafiya?"

Zai yi magana Dady ya shigo kallo  su ya tsaya yi.
"Mami na kasa ganewa ne?"

"Me ka kasa ganewa?"
"Mami ta kuma turon Address din da Number duk na Dady ne wallahi."

"Toh!"
Mami ta fada tana Kallon Dady da sai murmushi yake yi.

"Dady kana jifa."
"Naji Mamin Najib, kinsan wa Najib yake so ne?"

"A'ah!"
Ta fada tana zukuwa taji wacce yake so.

"Najwan kice fa?"
"Najwa ta."

"Eh Najwan Ahmad."
Ido ta zaro, ta ce,
"Da gaske?"

Murnushi yayi, ya ce,
"Yanzu Ahmad ya kira ni yake fada min Najwa an fito amman ya bada Number ta da addrss dina. Kinga kuwa ai ita ce."

Najib dake kwance tini ya mike da sauri yana kallon Dady.
"Dan Allah Dady da gaske."

Ya fashe da Dariya, Dady ya rumgume yana murnar da farin ciki.

Mami kuwa kallon sa ta tsaya yi, a ranta ta ce,
"Allah ya amsa addu'ar ta da ta su Baffah kenan. Ba ahada su ba sun hada kan su."

Najib ne ya kalli Mami, ya  ce,
"Mami tunanin me kike?"

Murnushi tayi, kawai ta zauna a gefen su.
"Wai kar dai kace daman baka san Najwa ba yarinyar da rainon ka ce,"

Dariya yayi ya ce,
"Mami kibar wannan zancen, wallahi abin ma abin kunya."

"Wallahi kuwa. Ace mutum da kanwar sa be san ta ba."

"Na santa man, kinsan tin da na bar kasar bana ganin ta ko nazo."
"Allah ya kyauta."

Fita Najib yayi, bangaren su Baba yana basu Labari.

Ba wanda yakai su bara'atu murna.

Dady ne ya kalli Mami ya ce,
"Kinga ikon Allah ko? Allah ya amsa addu'ar Baffah da Ummah."

"Abinda na gama tunani kenan. Kaga Baffah akan haka har makka yaje yayi addu'a ashe Allah ya hada su bama mu sani ba. Alhamdulillah ai ni zanyiwa Ummah wannan albishir din."

Ta fada ta nayin dariya Dady ma dariyar yayi, ya ce,
"Uwar Amarya!"

"Wallahi kuwa tuwo na mai na. Kai Alhamdulilah ai kowa yayi kwadayin samun Najwa wallahi."

Dady ya ce,
"Mun gama magana ma, zanje na fadawa su Baffah wata biyu masu zuwa za'ayi komai a gama."

"Toh Allah yasa ayi da mu."
Dady ya amsa da
"Ameen!"

Najib kuwa tin lokacin ya fara shirin zuwa Kano.

Sunyi waya da Najwa be fada mata komai ba sai lokacin da zai zo.

Tin da ya fada mata ta fara shirye shiryen zuwan sa.

Girke girken da zatai masa, da kayan da zata sa duk sai da ta tanade su.

Tana son fadawa Mamin ta tana jin kunya.

Suna zaune a falo, ita da Salim ta ce,
"Hamman Jibi fa zai zo."

Kallon ta yayi, ya ce,
"Waye?"

"Shi man."
"Najwa kenan wallahi kin fiya kunya. Yanzu sunan nashi ma baza ki iya fada ba."

Shiru tayi, kai ya girgiza ya ce,
"Kin fadawa Dady da Mami ne?"

"Hamma wallahi bazan iya ba."
Dariya yayi, ya ce,

"To ya kenan?"
"Ka fadawa musu."

"To shikenan. Kinsan kuwa nan da wata biyu za ayi komai a gama."

Mikewa tayi daki da gudu, dariya yayi, ya nufi dakin Mamin su.

Zama yayi, ya ce,
"Mami 'yar ki dai ta mayar dani dan aike."

"Me kuma ta kuma aiko ka."
"Wai zai zo, shine ta kasa fada."

"Allah sarki Najwa. To menene? Yaushe zai karaso?"
"Jibi ne."

"To Allah kaimu zan fadawa Dadyn naku."
Duk abin nan da ake su Mami ba su san wa yake neman auren Najwa ba.

Mami, ta kalli Salim ta ce,
"Kasan har an kai sadaki da komai. Laife kawai zasu kawo."

"Ikon Allah Abin da zafi zafi haka."
"Wallahi."

"Allah sanya alheri ya kore duk wata fitina."
"Ameen Ya Allah."

Najib ma ya fadawa su Mami, ranar zuwan sa Kano, kuma yasan da an gama komai, daurin aure kawai ya rage da kai laife.

Sumaiyya ya sama ya fada mata duk halin da ake ciki, da zancen auren sa.

Ji tayi kamar tayi bindiga, kudi ya zube mata masu yawa tare da sabuwar mota ban da laife da ya jido mata ita.

Amman duk wannan abin basu burgeta ba. A ranta ta dauki alwashi sai taga bayan matar nan tasa.

A haka ya tafi ya bar ta, zuciyar ta kamar ta fashe dan bakin ciki.

Yana tafiya, ta kira kawar ta Jamila.
"Jamsy!"

"Na'am Summy lafiya kuwa?"
"Ina fa lafiya. Najib ne zai kara aure fa?"

"Aure kuma ana zaune lafiya."
"Kedai bari yanzu mene abin yi."

"Ki kwantar da hankalin ki. Zan shigo akwai wani malamin na anan nigar in nazo sai muje."

"Yauwah jamsy nagode sai kinzo. Dan Allah ki shigo da wuri dan abin yafi saurin

Please Login or Register in order to submit comment