Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ce,
"Mene ne?"

"Ba komai."
Wajen Najwa ta karasa ta dago ta, hawaye ta gani a idon ta, ta ce,
"Haba Najwa mene abin kukan, ki daina kinji kiyi hakuti kije kema kiyi zaman auren ki. Allah bada sa'a da zamna lafiya kinii. In kina da matsala kina fada min kinji."

Kai ta gyada mata,
"Yauwah ko kefa,"
Ta fada tan goge mata hawayen fuskar ta.

Kamo ta tayi suka sauka kasa, Bangaren Baba sukayi, Mami ta ce,
"Baba Najwa tazo miki sallama."

Baba ta ce,
"Masha Allah. To Najwa Allah bada sa'a ayi hakuri dan aure dan hakuri ne. Allah miki Albarka. Allah bada zaman lafiya."

Mqmi ce ke amsawa da
"Ameen Ameen."

Daga nan ta fito da ita kawayen Mami suka tafi kai ta gidan ta.

Najib na can Hankalin sa gaba daya yana wajen Najwa, sam yau be samu zama da ita ba.

Lallai ya yadda Najwa ta zama farin cikin sa, dan yau wani iri yake ji, haka nan duk kewar ta, ta dame shi.

Allah Allah yake ya gama da Sumaiyya ta tafi yayo gida. Yana gamawa da ita kuma Dady ya kirasa akan yaje.

Zancen tafiyar su Honeymoon ne, amman sai nan da wata biyu, saboda be dde da dawowa ba, ya kamara yaje asibitin su yaga me yake faruwa bayan tafiyar sa.

Ba samu famar komawa gida ba sai bayan magariba lokacin an tafi da Najwa.

Yana zuwa ya fara leken da ya fara, Mami na kallon sa tai masa banza.

Bati naje nai wanka, ya fada yana yin bangaren sa, koda yaje ba Najwa, haka yayi bangaren Baba anan ya samu Baba take fada masa an tagi kai Najwa.

Dadi kashe Najib, a ransa ya ce,
"Amman Mami taki fada masa."

Wannan yasa ya tafi dakin sa, wanka ya shiga sqi da yai alwala sannan ya fito.

Mai ya shafa, ya sja wata farar shadda sabuwa fil, sai hula da ya saka baka haka ma takalmin sa, agogon azurfa ya zira, ya fito.

Tin Mami na kasa take jin tashin kamshin Najib, murmushi kawai tayi.

Yana saukowa ya dukar da kai, ya ce,
"Mami ni zan tafi."

"Allah kiyaye hanya Najib, ka kular min da yarinya ta. Kajo ko?"

"Insha Allahu."
"Allah maka albarka."

"Ameen!"
ya mike ya fita.

A bangaren Najwa sun isa gida lafiya. Part din ta aka bude aka saka ta.

Falon kasa, an masa ado da milk nd purple colour, dakin ya yi kyau ba'ai mata tarkace ba.

Daga kujeru sao kayan kallo da kayan sauti. Haka dagan dakin na kasa aka saka masa tum tum sai karfet suma duk purple kala da adon milk nr. Dayan kuma kayan dakin aka saka gado shima kalar kayan falo ne.

Kitchen din ta an cika mata shi da kayan amfani babu abinda babu. Gefen daining inda shima akai masa ado aka ajiye abubuwan da suka dace da gun.

Haka saman an saka mata brown kujeru masu adon golding kala, daya daga cikin bed room din shima kalar sa ne.

Kayan ne aka saka mata Fararen kaya masu ratsin ja.

Ko ina saida aka saka mata shi kaya. Duk inda ta dusa kamshi da sanyin AC ke tashi. Gidan ba karamin kyau yayi ba.

Bangaren ta ba karamin kyau yayi ba.

A dakin sama suka ajiye ta. Dan kara gyara gidan sukai duk da da rana Mami ta sa an shere an goge sannan suka tafi.

Tana zaune har akai sallah isha'i wannan yasa ta tasji ta daura alwala tai sallah.

Tana kan sallaya tana yin addu'a.

Najib kuwa yana fitowa yaji ana sallah isha'i wannan yasa ya tsaya yayi, daga nan yaje ya siyo.musu abinda zasu ci.

Gidan ya jufa kai tsaye, gidan da yaga yai wani haske da kyau duk a dalilin sjigar Najwa.

Bangaten Najwa ya nufa kai tsaye, har lokacin tana kan sallaya.

Tinda ya shiga part din ta yaji wani sanyi da dadi na ratsa shi, idp ya lumshe sannan ya bude. Kallon dakin ya ke yana me sha'awar dakin.

Komai na bangaren yai masa kyau. A hankali ya finga hawa stairs din benen har ya kai ga falon sama.

Ba kowa anan ma sai AC da take aiki dakin ya dau sanyi.

Sai da ya bude dakuna biyu sannan ya hange ta akan sallaya.

Da sallama ya shiga dakin. Amsa wa tayi tana mikewa.

Da sauri ya karasa gaban ta ya hade ta da kirjin sa. Ya rumgumeta.

Gefen gado ya zaunar da ita, ya ce,
"Ina yiwa Najwa Barka da zuwa gidan ta. Kuma ina mata albishir ba abinda zai taba raba ta da mijin ta, da gidan nan. Gidan nan mallakin kine, dan haka ki sake kamar yadda kike so."

"Hamma kenan!"
"Baby nah kinyi kyau."

"Kai ma haka."
Kiss ya manna mata a kumatu, ido ta lumshe ta lafe a jikin sa.

"Kinga tashi muyi sallah ta nuna godiya ga Allah,"
Mikewa yayi, ya daga ta.

Bandaki ya nufa da ita ya ce,
"Muje kiyi alwala ko?"

"A'ah! Ina da alwala."
"Toh!"

Ya juyo da ita suka koma kan sallayar dake shinfede a dakin.

Shiya jasu sallah, suna idar wa ya dafa kanta yana yo mata addu'a. Ya dade yana musu addu'ar samun zaman lafiya da zuria daiyiba.

Sai da ya gama sannan ya jata sukai falo, Kaji be ya shigo dasu gasasu, sai farfesun kayan ciki da madarar shanu fresh.

Tare suka ci, suna ci suna wasa da dariya abin su, sai da suka gama ta kwashe ta kai kitchen sannan ta dawo.

Kallo ya kunna, taba shigowa ya nuna mata cinyar sa, alamar ta zo ta zauna.

Tafiya ma canjawa tayi, ta dinga tafi dai dai, tana jijjiga jikin ta.

Ba karamin tadawa Najib hankali tayi ba, a haka ta karasa ta zauna a saman cinyar sa.

Rumgume ta yayi, wayar sa ya zaro dan kira Sumaiyya yaji ya taje gida. Tinda ita bazata iya neman sa ta fada masa ba.

Tana fara ringing ta daga,
"Hello!"

Najwa taji muryar Sumaiyya. Iso ta lumshe ta zame daga jikin sa a hankali tayi cikin dakin ta.

Tana shiga ta wuce bandaki tai wanka ta wanke bakin ta tai alwala.

Turarukan da Mami ta bata su ta murje jikin ta dasu, nan da nan ta hau fitar da wani irin fitinan nen kamshi.

Wata rigar bacci ta dauko pink kala, wacce daga saman ta duk net ne a jiki, iyar ta cinya.

Rigar tai mata kyau, gashin kanta ta daure da ribon. Ba karamin kyau tayi ba sai ta zama kamar 'yar tsana.

Kan gado tayi, tahau tana karanto addu'ar bacci ta tofe duk jikin ta.

Shi kuwa yana falo yana waya da Sumaiyya wacce ta rike shi a waya daga ta ja waccan maganar sai ta ja waccan.

Duk ya kagu yaje ga Najwa yaga halin da take ciki.

Amman taki ta bar shi, sai da kyar ya samu sukai sallama.

Kayan kallon falon ya kashe, sannan yayi cikin dakin sa, wanka yayi yai alwala, san ya saka kayan baccin sa.

Turare ya bade jikin sa dashi. Dakin da Najwa ta shiga ya shiga shima.

Fitilar dakin ya kunna ya hangota can karshen gado a kudundune, murmushi yayi ya kashe fitilar ya nufi kan gadon.

Bargon jikin ta ya yaye, kallon ta ya tsaya yi, baccin ta take hankali kwance.

Rigar jikin ta tayi kyau, itama ba karamin kyau tayi masa ba.

Ya jima yana kallon ta kafin daga bisani ya kai hannun sa kan kirjin ta.

Shafata yayi a hankali, sam bata farka ba. Bakin ta yai kai mata sumba.

Haka ya dinga daga ya taba can sai ya tabo can, har sai da ta farka.

Dan cikin bacci ta dinga jin wani yanayi na shigar ta wannan yasa ta bude ido.

Najib ta gani, ido ta lumshe, janta yai jikin sa, ya fara romancing nata.

**********************************************----------------------------------------------------------------------++++++++++++++++++++++++++++++++++

Baza mu iya fassara a wane hali Najib ya tsinci kan sa ba don be san a wace duniya yake ba. Wannan yarinya haka 'yar albarka, me cikakkiyar ni'ima lallai Najwa ta ciri tuta.

Ya jima yana mamakin irin ni'imar da Najwa ke da ita, lallai ta ciri tuta ta dagawa sauran mata tuta shi dai be ga wanda ya isa ya raba shi da Najwan shi ba in ba mutuwa ba.

Sha shagwabar Najwa wanda ta kara masa tsantsar sonta da begenta.


*INDABAWA*

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*155*

*Zainab Suleiman (Zetty) Maman Hanan*
Allah kara basira da zakin hannu. Na jinjina miki Allah ya raya Hanan ya karawa Mama tafiya.
*Ameen!*

So much love u.




Da asuba ya tashi yai wanka yayi sallah ya zuba wa Najwa ido, tana ta shakar baccin ta. Sonta da kaunar ta ya kara ninkuwa a zuciyar sa.

Hannun sa ya dauka yana shafa fuskarta ta dan bude idon ta da suka kumbura sukai jajir dasu.

Murmushi yayi mata ya ce,
"Najwa tashi kiyi sallah kinga gari ya waye."

Marairai ce masa fuska tayi kamar zatai kuka, ta ce,
"Hamma!"

Da sauri ya tari nunfashin ta ya ce,
"Yi hakuri Baby na, Hamma ne ko? Rabu dashi ba ruwan mu dashi."

Ya dungure kan sa zai kuma kenan ta rike hannun nasa. Tana masa wani irin kallo.

"To yi hakuri, tashi muje."
Kai ta gyada masa sai dai ta kasa tashi.

Da kansa ya dauke ta ya kai ta bandaki. ruwa ya hada mata me zafi ta gasa jikin ta, shi ya daura mata alwala ya fito da ita ya saka mata wata doguwar riga, ya kai ta kan sallaya.

Tana idar da sallah ta kwanta a wajen, da sauri ya isa gare ta,  ya dago ta ya rumgume ta a jikin sa.

Kallon ta yayi cikin so da kauna, ya ce,
"Nagode miki Najwa, Allah miki Albarka Allah ya bamu zuri'a ta gari."

Kanta ta kwantar a kirjin sa tana lumshe idanun ta, da suka kumbura saboda kuka.

Gado ya dauke ta suka hau, a jikin sa tayi bacci yana jijjiga ta kamar wata yarinya, shi kuwa ya kasa baccin ma sai kallon fuskar ta da yake yi yana sa mata albarka.

Sai karfe sha biyun rana suka tashi shi yai mata wanka ya tsane mata jikin ta sannan ya shafe mata jikin ta da mayukan ta.

Hoda ma shi ya shafa mata da man lebe kwalli ne kawai ta saka da kanta.

Wani milk din less ne wanda akai masa ado da purple colour ya dauko mata wanda akai masa dinkin riga da siket.

Dinkin ba karamin kyau yayi ba. Rigar ta zauna a jikin ta sosai haka siket din eight pieces ne, ya zauna shima a jikin ta.

Ba karamin kyau tayi ba, shi ya fesa mata turare ya gyara mata kai, bayan ya busar mata gashin ta, yai mata parking da ribon.

Be daura mata dankwalli ba dan yana son kallon gashin ta a haka.

Sai da ya gama da ita tsab sannan ya nufi bandaki dan yin wanka.

Shima yana fitowa ya shirya cikin milk din wando da riga yan kanti, ba karamin kyau sukai ba. in ka gansu sai kayi zaton gasar fitar da me kyau zasu.

Duk kan su sai tashin kamshi suke, kamar wandan da sukai barin turare.

Najwa kuwa na jikin Najib tana zuba masa shagwaba, shi kuwa ya gigice sai lallashin ta yake yi.

Falo ya dauke ta suka yi, Abincin da Mami ta aiko musu dashi ya dauko.

Lafiyayen abinci me rai da lafiya ta hada musu.

Sai da suka ci suka koshi sannan ya dauke ta, suka haye kan kujera.

Tausa ya dinga yiwa Najwa har bacci ya dauke ta bata sani ba.

Jikin ta yaji da zafi har lokacin wannan yasa yai waya asibiti aka kawo masa abinda yasan zai bukata.

A ciki da allura da magunguna. Tana kwance ta farka, kallon sa ta tsaya yi dan ya zuba mata ido ya lula duniyar tunani.

A hankali ta mike, ta kamo hannun sa da ya zuba taguni ta ce,
"Hamma lafiya?"

Murmushi ya sakar mata ya ce,
"Baby na, jikin ki zafi, bari na baki magani kinji."

Ba abinda Najwa ta tsana kamar magani da allura, fuska ta marairaice, ta ce,
"Haba Dai ai zan warware,"

Be kalle ta ba ya janyo first aid box din da aka kawo masa, allura taga yana hadawa, ai tini cikin ta ya duri ruwa.

Kallon ta yayi, ta ce,
"Hamma dan Allah kada kai min allura, bana so."

Ajiyewa yayi ya janyo ta jikin sa, ya rumgume ta, a hankali ya dinga shafa jikin ta har ta lumshe ido, a hankali ya janye Siket din jikin ta.

Allurar ya dauka, ya soka mata, wata wahalalliyar kara ta saki, rumgume ta ya kara yi, yana lallashin ta.

"Yi hakuri my soul mate, shine kadai abinda zan iya miki, sannu kinji."

Kanta ya dinga shafawa a hankali, ya ce,
"Najwa kin shayar dani da abinda ban taba zato ba abinda banyi tsammani ba,  Najwa Allah miki albarka, Ubangiji ya albarka ce, Allah karawa Dady da Mami lafiya da nisan kwana. Hakika ina alfahari dake kina da gurbi babba a cikin zuciya. Ba zan taba iya rayuwa babu ke ba Najwa. Allah miki albarka."

Ido Najwa ta lumshe kawai, Albarka tin daren jiya take shan ta yafi a kirga.

Bacci ne ya kuma dauke ta, daukar ta yayi, ya kai ta dakin ta,  kallon ta ya tsaya yo yana mamakin yadda ya same ta da yadda yaji ta. Najwa ta daban ce, lallai ya kuma yadda da Najwa ta daban ce.

Ya jima yana kallon ta kafin daga karshe ya tashi ya fita.

Shi da kansa ya gyara gidan ya kunna turaren wuta sannan ya koma dakin da take, ya zuba mata ido kamar TV.

Yana zaune, har akai sallah azahar, wannan yasa ya tafi massalaci daga can Dady ya kira sa, ba dan yaso ba ya tafi ya bar Najwa.

Najwa kuwa bata tashi farkawa ba sai karfe uku Najwa ta farka.

Tana farkawa tai sallah, sannan fitowa ta nufi kitchen, abinci ta daura musu, miyar kaji tayi, sai shinkafa da ta zuba mata kayan lambu a ciki. Sai farfesun kayan ciki da tayi. Zubo ta hada wanda ta zuba masa kokonba a ciki.

Sai da ta gama komai ta jere shi a daining sannan ta nufi Bandaki dan yin wanka.

Wanka tayi ta sake tsantsara kwalliya. Cikin riga da siket na atamfa, ta dasa daurin ta ta saka dankunne da sarka da abin hannu.

Sosai ta fito a amaryar ta dama ga lalle kafa da hannu.

Gidan ta kara turarewa tai sallah la'asar sannan ta koma falo ta zauna.

Sai karfe biyar sannan Najib ya dawo, lokacin tana dakin ta.

Fitowar ta kennan yana karasa shigowa falon, da dan gudun ta, ta karasa gare shi, tana fadin,
"Oyoyo My Honey."

Wani dadi yaji abinda be taba samu ba kenan ya dawo gida a nuna anji dadin dawowar tashi.

Hugging nata yayi, shima ya ce,
"Sannu Baby nah "

Ya dago da fuskar ta yana kallon yadda tayi kwalliya kamar ka sace ta ka gudu.

Kiss yai mata a saman idon ta, da wuhan ta. Sannan suka karasa falo.

"Sannu da Zuwa Honey."
"Yauwah Baby na."

Mikewa tayi ta bude firij ta dauko masa lemo me sanyi ta taho ta kofi ta kawo masa.

Lemon ya kurba yaji wani sanyi har cikin zuciyar sa, ya ce,
"Najwa ina son ki, tinda na fita kina rai na, na kasa sake wa, ga wayata na manta ta a gida bare na kira naji ya Baby na take ya jikin ya warware."

Kai ta daga masa cikin jin nauyi da kunya, ya janyo ta jikin ta ya ce,
"Yesterday you call Mami, today are u going to call Dady."

Dan dukan wasa ta kai masa a kirji tana son mikewa, riko ta yayi ya ce,
"Oh you won't call Dady ko, ko Hamma Salim za'a kira min."

Kukan shagwaba ta saka mishi,
"Ayyah Sorry! Sorry Baby nah."

Ya rumgume ta sosai yana shafa bayan ta nagode Najwa, Allah miki albarka yadda kika kyautata min Allah ya kyautaya miki."

Hannu ya saka a cikin aljihu, ya dauko wani dan karamin akwati, mika mata yayi,
"Najwa ban san dame zan saka miki ba, sai dai nai tai miki addu'a Allah albarka ce ki ya albarkaci zuri'ar ki."

Budewa Najwa tayi, wani dan kunne da Sarka na gold ne a ciki wanda daga kallo kasan makuden kudi sunyi kuka wajen  siyan shi.

Key din mota ya kara fito dashi ya ce,
"Ga mukullin motar ki nan, ta Sumaiyya ma na waje. Allah miki albarka."

Murmushin kan fuskar tane ya dadu, inda tai saurin hade bakin su gu daya tana aika masa da sakkonni kala kala.

Sun jima a haka kafin ta dago, ta ce,
"Hamma ban san me zan ce ba. Nagode nagode Allah kara budi Allah ya karawa su Mami lafiya da nisan kwana. Allah ya dafa maka."

Bakin su ya kara hadewa dan yasan in Najwa ce baza ta gaji da masa addu'a ba.

"Haka ma nagode. kiyi shiru ai kaina nayiwa."

Lallai sai yanzu yasan yayi aure, da Allah ya hada shi da kyakyawar Yarinya me hankali da nutsuwa hadi da tarbiyya.

Yasan haduwar sa da Sumaiyya Kaddara ce, kuma jarrabta ce, ko dan son da ya nuna nason samun macen kawarai ne Allah ya hada shi da Sumaiyya. To Alhamdulilah Ala kulli halin. Ya gode Allah kuma yana kara gode masa.

Suna wajen cin abinci ma sai santi yake zuba mata yana nuna mata yaji dadin abincin.

Suna gamawa suka koma falon kasa, suna kallo tana makale da jikin sa.

Wayar ta, ta dauka ta kira Mamin Najib, kyautar da yai mata ta fada mata, sosai Mami ta taya ta murna.

Inda suna gamawa ta kira Mamin ta itama tai tai musu addu'a da sa musu albarka.

Ummah Najwa ta kira, Ummah na dagawa ta yi sallama.
"Ummah na"

"A'ah amare kune ya kike ya gidan ashe kin tare ina Najib din."

"Ummah gashi "
Ta mika mishi wayar sai fa suka gaisa ya tsokane ta sannan ya bawa Najwa wayar.

Ana ta fada mata kyautar da yai mata ita Ummah albarka ta dinga sa masa tare da addu'ar zamamn lafita

Duk wayar nan da suke Najwa na jikin sa a makale.

Yana mamaki dan duk kyautar da Yakewa Sumaiyya baya taba fada a gida ba bare ai musu addu'a ko su nuna jin dadi

Kara rumgune Najwa yayi dan shi yasan me yake ji kawai a tattare da ita.


Sai da aka kira sallah magariba sannan ya shiga ya watsa ruwa ya nufi massalaci.

A lokacin tai sallah ta samu damar daura musu abincin dare.

Jallof taliya ta dafa wacce ta saka mata dankalin da naman kaza, lemon kwakwa ta markada musu.

Tana gamawa tai wanka, ta shirya cikin wata farar ves me red stones sai jan wando, dogo.

Kanta tayiwa parking da red ribon ba karamin kyau tayi ba. Karamar barima ja ta saka a kunnen ta.

Sallah tayi, shima sai da yayi sallah isha'i sannan ya dawo gidan.

A falo ta same shi, yana zaune, a hankali ta karaso gunshi, cikin tafiyar nan da tasan tana daukar hankalin sa.

Kallo ya bita dashi sai kace dolo, ya janyo ta jikin sa ya ce,
"Kinyi kyau Baby na."

Murmushi tayi ta ce,
"Barka da dawo wa. Ya ibada."

"Alhamdulilah."
Mikewa tayi ta sauka kasa, a babban faranti ta jero fulas din abincin da ta girka musu.

Tana shigo ya tashi ya amsa, yana cewa,
"Sannu da kokari."

A ransa ya ce,
"Ashe dai shima zai samu kula kamar yadda Mami kewa Dadyn sa."

Gaskiya ya gode Allah da ya samu Najwa.

Tayi yunkurin zuba musu ya janyo ta ya zaunar da ita, ya ce,
"A'ah ai ni zannyi kin gaji da yawa."

Yana bude fulasa din wani kamshi, ya dpki hancin sa ya zuba musu abimcin yana hadiyar yawu.

Suna fara cin abincin ya fara santi yana lumshe ido. Yana ci yana shan lemon kwakwar.

Sai da yayi nak,  sannan ya kalle ta ya ce,
"Najwa wai kinyi makarantar koyan girki ne."

Dariya tayi ta ce,
"Kaine malamin amman."

Dariya yayi ya ce,
"Lallai kuwa."

Kayan ta kwashe takai kitchen sannan ta dawo, a saman cinyar sa ya daura ta.


*INDABAWA*

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*157*




*Basira Sabo* jinjina gareki. Allah kara basira da zakin hannu.
*Ameen!"

Nagaishe ki.






Wai ina Sumaiyya ne.

Tinda Sumaiyya ta isa Kano take neman Antyn ta wacce bata gari, duk neman da tai mata a waya bata same ta ba.

Bata tashi samu  ta ba sai da tai sati biyu a kano sannan a lokacin Antyn ta ta ce, ai bata kasar amman zata dawo nan da sati biyu duk abinda ya kamata

Sosai Sumaiyya tai murna. Kullum kafar ta a waje yawo kamar ba matar aure ba.

Duk fadan da Mama take bata ji, kawayen ta kuwa duk sun kara junewa.

Dan har hotel rake binsu, ita bata ganin aibun su ma yanzu.

Abu daya shi ya fi damun ta shine ta raba Najib da Najwa.

Bata da buri da ya wuce wannan dan ita ce daga gun wancan malamin sai gun waccan malamin.

Kowa da abinda zai fada mata ba gaibu dan da akwai wanda ya ce, kafin ta koma auren zai mutu.

Amman komai aka fada mata shiru baya faruwa.

Duk ta daga hankalin ta, ta rame tayi baki, bata samun kwanciyar hankali.

Mama kuwa ba abinda take sai addu'a da take mata.

Sam bata kiran sa, sai dai in ya kira ta.

Duk kudin da ya bata sun kare a bin malamai, wannan yasa tai sa Najib ya kara turo mata kudi.

Be tambaye ta abinda zatai da su ba kawai ya tura mata.

Amman suma cikin sati  sai da ta gigita su.

Kawar ta daya ke mata fada ta nuna mata ta daina abinda take sannan ta bar Najib da Najwa.

Amman sam taki ji abinda yasa ta daina zuwa gun Hauwan ma kenan.

Dan wai da taje zata fara gaya mata Allah yace Annabi ya ce. Ita kuma abinda ta tsana kenan.

Yau tana zaune a gida sai kawai tajoyi sallamar Anty kaltum.

Da sauri ta mike ta taro ta ta a murnar dawowar ta

Mama bata nan dan haka a falo suka zauna.

Anty Kaltum ta ce,
"Sumaiyya ya na ganki haka duk kin rame sai kace ba Summy gaye ba."

"Uhmm kedai bari Anty. Dan Allah ji yadda kika kara haske da kiba har wani ja kike. Mene sirrin ne."

"Sirrin zawarci. Ba abinda yafi zawarci dadi yarinya. Kinga da Alhj lukuman fa muka dawo  jiya. Kudi sai dai na diba abinci sai wanda zanci mota sai wacce nake son haka. Ba ruwana da bacin rai bare nasa damuwa a rai na."

Kallo ta Sumaiyya take, ta ce,
"Anty wai ya zamuyi ne da wannan shegiyar Najwan. Anty kinga inda Najwa ta koma kuwa."

"Kinga ki kwantar da hankalin ki, kafin na dawo na kira wani malamina dake madobi, mu yake jira kawai  tashi muje."

Mayafin ta  dauko kawai suka fita.
Basu zarce ko ina ba sai madobi. Sun isa lafiya, sun yiwa malamin bayanin komai.

Inda ya buga kasa ya dago ya kalle su, ya kuma bugawa ya kalle su, can ya ce,
"Kaltum maganar gaskiya, wannan abin bazai taba rabuwa ba. Ba yadda zamuyi dan Allah ne ya hada su, kuma shi ne zai iya raba su, nidai na dubo duk hanya da zanyi naga na rabasu amman babu. Shawara daya kuyi hakuri kawai."

Ran Sumaiyya kamar me dan bakin ciki. Antyn ta ce,
"Shikenan mun gide."
Suka mike suka bar wajen sa.

"Anty kina ganin haka zamu zauna mu zuba musu ido kenan."
Sumaiyya ta fada

"Ke wa ya fada miki. Ai nan takai muka nufa ki kwantar da hankalin ki kinji."
Murmushi Sumaiyya tayi, ta ce,

"Shiyasa nake kara sonki Anty nah."
can ma da sukaje ba sa'a sunje gu yafi biyar ana shidan ne ya basu wani magani ta sakawa Najwa a bin shan ta insha Allahu zata mutu gaba daya ma.

Ta tafi gida da murna, tinda ta koma ta fara shirin tafiya.

Watan daya ta shirya tafiya.

***************
Najwa da Najib kuwa soyayya tayi gaba kowa yana kokarin farantawa ran da uwan sa.

In kaga Najib da Najwa sai kai tsammanin sun fi shekara nawa da aure dan shakuwa.

Yau kamar ko yaushe suna zaune ita da Najib, kan ta na kan cinyar sa.

Shafa gashin kanta yake idon sa a lumshe, can ta zame kanta ta bude idon ta, ta ce,
"Hamma dan Allah ina son zuwa na gaida Mami."

Kallon ta yayi ya ce,
"Najwa yaushe kika baro gidan Mamin?"

Fuska ta marairaice, ta ce,
"Haba Honey, month fa, please kaji."

Ajiyar zuciya ya sauke, a duk lokacin da Najwa tayi masa shagwaba ba karamin karya masa lago take ba, dan Haka ya ce,
"Shikenan ki bari gobe na kai ki."

Rumgume shi tayi, ta ce,
"Nagode Hamma na."

Mamaki yake yadda take murnar zuwa gun Mami banda Sumaiyya da in ya ce tazo suje zata kawo masa uzuri.

To wajen Mahaifiyar ta ma bata fiya zuwa ba bare tashi. Lallai yanzu yasan yayi dacen aure da yarinya ta gari.

Tin daren ranar take shirya abubuwan da zata kaiwa mami.

Yana fita massalaci, ta hau kwabin cake, me inibi ta kwaba tayi baking nashi.

Sai meat pie da ta kwaba shima, ta zuba masa nikaken nama.

Kaji ta debo a firij, guda biyar ta yayanka ta dora akan wuta,

Please Login or Register in order to submit comment