Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta hada a akwati ta saka da kayan da Mami ta bata, atamfofi ne turmi ashirin da yadika sai kudin gun Dady.

Har lokacin in ta kira wayar sa a kashe take.

Wata zuciyar ta ce,
"Kila yana gun Sumaiyya."

Wanna yasa ta fita falo ta sha tea kawai ta koma saama ta kwanta da tunanin Najib a ran ta.

Wajen karfe goma tana kwance sai gashi ya shigo.

Gun ta ya karaso ya dago ta yana kallon ta.

Kuka ta saka masa, ta ce,
"Hamma ina ka tafi ka barni ina ta neman ka wayar ka ma duk a akashe."

Lallashin ta ya fara, yana cewa,
"Kiyi hakuri Baby na. Aiki ne yai min yawa amman kina rai na."

Jikin ta ta kwace daga gare shi, ta ce,
"Kaje na barwa Aikin kai."

Ta mike zata bar dakin. Da sauri ya kamo ta ya ce,
"Haba dai ai aiki yayi kadan ya same ni. me samu na sai me babban rabo in ba ke ba. Ke kadai zan iya bawa kaina na koma katse komai dan faran ta miki. Kiyi hakuri bazan kuma ba."

Murmushi tayi, ya dungure masa kai. Ta koma ta zauna

Dariya yayi ya ce,
"Baby how did u miss me?"

Baki ta murguda ta ce,
"More than d way u miss me."

Dariya yayi ya ce,
"Anya kuwa?"

"Kana tan tama ne?"
Ido ya dage, alamar tunani.

Be gama abinda yake ba yaji ta ajikin sa tana rikita masa lissafi.

Ta nuna masa yadda tayi missing nashi.

Inda suka fada kan gado suna maida numfashi.

Kan ta ya rufa ya ce,
"Na yadda Baby na tayi missing dina gashi yau zaku tafi da munsha soyayya ko?"

Ido ta damke ta ce,
"Hamma!"

"Menene?"
"A gidan Mami fa muke ko?"

"Yes, and so?"
"Haba da kunya ai."

Dariya ya sheke da ita, ya ce,
"Ina kunyar bayan yanzu kika gama murje ji."

Da sauri ta rufe bakin sa tana kallon sa.

Shima kallon ta yake, sun jima a haka kafin ta fara janye idon ta.

Murmushi yayi, ya ce,
"Baby baki fadan abinda kike bukata ba."

Ido ta zare ta ce,
"Yo ni me zan bukata ba abinda zan bukata sai son ganin ka kullun da son kasancewa a tare da kai."

Kiss yai mata a wuya, ya ce,
"Zan zo na ba da jimawa ba."

Ido ta lumshe. Ya ce,
"Zan turo miki da kaya ki rabawa Dagin Mamin kinji."

"Nagode love Allah kara budi. Allah raba ka da iyayen ka lafiya."

"Ameen Allah kuma ya barmin Najwa ta."
sukai dariya.

Agogo ya kalla ya ce,
"Baby is almost tima fa. Kalli karfe sha biyu."

Mikewa tayi ta ce,
"Bari nai wanka nai sallah ko?"

Shima mikewa yayi ya ce,
"Bari nai wa Matata wanka ko?"

"Eh!"
Ta fada tana dariya a hankali tayi gefen toilet tin kafin ya farga ta fada ta saka key.

Dariya yayi, ya ce,
"Najwa kenan."

Bangaren sa yayi yai wanka ya shirya cikin milk din shadda yai kyau sosai dashi.

Sama ya koma dakin Mami. Najwa ya gani sanye da wani less an masa dinkin riga da zani.

Kayan sun mata kyau, orange less ne a jikin ta sai aon green da milk.

Milk din mayafi da takalmi da jaka ta dauka.

Tana fesa turare ya shigio dakin. Kallon ta ya tsaya yi ba karamin kyau tayi ba.

Rumgume ta ya matsa yayi ya rada mata a kunne,
"Baby kinyi kyau."

Kallon sa tayi ta jikin madubi ta ce,
"Kafi ni yin kyau."

Dariya yayi, ya ce,
"Gaskiya a fasa tafiyar na."

"To ranka ya dde yadda kace haka za'ayi."
"Da gaske?"

"Eh wallahi."
Murmushi yayi ya ce,
"Ai kinsan na ce zaki tin last week ko?"

Kai ta gyada. ya ce,

"To bazan karya alkawari ba."

Juyowa tayi ta kalle shi ta rumgume shi tana dariya. Shima hugging nata back yayi.

Kofar dakin suka ji ana tabawa wanna yasa Najwa tai saurin sakin sa.

Bara'atu ce ta shigo da sallama ta ce,
"Mami ta ce, ta fito, kuma ta bada kayan ta ta saukar mata dasu."

Akwatin ta Najib ya nuna mata ta dauka ta sauka kasa.

Janyo ta yayi jikin sa, ya ce
"Bari naji dumin jikin Baby na."

Lafewa tayi ajikin sa. Kafin daga karshe ta mike kallon sa, tayi ta ce
"Muje kar Mami ta gaji da jira."

Tai gaba hannun ta ya janyo ya ce,
"Ban gaji da kallon ki ba."

"Hamma Allah na fasa tafiyar nan ma tafi tare."

Baki ya rike ya ce,
"Kinga muje in ba so kike mami ta zane ni ba."

Dariya tayi suka sauka kasa. Mami ta na zaune akan kujera na jiran Najwa.

Najwa na saukowa tayi gefen ta, biyo ta Najib yayi.

Kai ta dago ta harare shi. Dariya yayi, ya ce,
"Mami matata zatai tafiya mene dan na makale mata."

Wayyo kasa bude Najwa ta shiga haka Najwa taji dan kunya.

Kasa kawai ta kuma yi da Kan ta. fulon dake kan kujera Mami ta dauka ta jiafa masa.

Ta ce,
"Ni matsa ka ban waje."

Dariya yayi bayan yai saurin barin gun.

Kallon ta ta maida kan Najwa ta ce,
"Najwa rabu da wannan yaron kinji."

Ta kamo hannun ta suka fita daga dakin bangaren Baba sukaje mata sallama kafin su fito su shiga mota.

Gidan baya ya budewa Mami ta shiga ya budewa Najwa gidan gaba ta shiga.

Sai da ya kai su airport, har aka kira su sannan Najwa ta samu damar satar kallon sa.

Ita yake kalla kamar TV shima abimda yake son ya gani idanun ta.

Ai kuwa tana dago kan ta, ya matsa gun ta,
"Baby na Allah tsare sai na zo."
Ya fada yana kamo hannun ta.

Satar kallon Mami tayi taga hankalin ta baya kan su.

Wannan yasa ta kara rike hannun. Juyowa Mami tayi ta ce,
"Son kada ka yanke hukuncin da ba dai dai ba. Kayi hakuri."

Kai ya gyda mata, ya ce,
"Allah kiyaye hanya."

"Ameen!"
Ta Maida kallon ta ga Najwa da bata gane maganar da sukai ba.

"Najwa muje."
ta fada tana yin gaba.

Hannu ta daga masa tabi bayan Mami.

Janyo ta yayi, ya hada ta da kirjin ta. Ido ta zaro ta ce,
"Hamma......."

Da sauri ya hade bakin su. Lafiyayen kiss ya bata sannan ya sake ta.

Ta tafi tana dago masa hannu jikin ta a sanyaye.

Sai da yaga tashin su sannan ya koma gida.

Yana zuwa ya wuce bangaren sa ya dauko takardar da ya rubuta ya fito ya aika driver ya kaiwa Sumaiyya tare da kudi.

Dakin sa ya koma ya kwanta yana jin ya yar da kwallon mangoro ya huta da kuda.

Sai da Najwa tai masa waya sun sauka sannan ya samu ya kwanta bacci.


Sumaiyya kuwa zata fita kenan aka kai mata sakon amsa tayi ta saka a mota ta fita

Sai da ta gams gararin ta da dare ta dawo gida zata shiga sannan ta tuna da sakon da Najib ya aiko mata dazu.

Envelope din ta dauka tayi cikin gida.

Tana shiga ta baje a falo kudi ne suka zubo tini ta hau murna.

Amman kuma tana mamkin me yasa be mata transfer ba.

Takardar ta bude ta fara karantawa. Ido ta zaro tana goge gumi.

bata taba shiga tashin hankali irin na yanzu ba.

Ta jima zaune ta rasa abinyi ranar a falo ta kwana dan ko kwakawarn motsi bata yi.


Najwa kuwa suna sauka Hamma Salim yazo, yazo dauke su.

Tana shiga gida Basma ta dane ta tana murnar zuwan ta.

Mamin Najwa kuwa sai Mami taiwa sannu da zuwa.

Amman fa duk hankalin ta na kan Najwa ta rame.

A gidan Mami ta ci abincI dan sai da ta huta sannan Hamam Salim ya kai ta gidan su.

Sai bayan fitar Mami ne, Najwa ta samu yima Mami magana.




*MS Indabawa*

NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*168*


*Nagaida ku duk writers ina mika sakon gaisuwa ta tare da jinkinar ban girma. Allah ubangiji ya kare mun ku daga sharrun mutum da aljan da duk abin ki. Allah kara basira. Allah kara hada kan mu.*
*Ameen*

Ina kaunar ku gaba daya.


*kuyi hakiri na jina da kukai shiru kwana biyu.*

*Hakan ya samune na zama na bana samun yi. Amman ayi hakuri.*

Kara gaisawa sukai Mami na tambayar ta ya jikin ta ya su Sumaiyya da me gidan.

Mami dai sai nan nan take da Najwa, Dan ba karamin dadi taji da ta ganta ba.


Haka nan Basma kamar ta goya Najwaa take ji.

Bamma salim ma yana dawowa daga kai. mami yazo ya saka Najwa a gaba wai tayi kiba shi da yake ya ganta da bata da lafiyar.

Ana fadawa Dadyy Najwa ta dawo ya baro office yazo ganin Najwan sa

Kowa yayi murna da zuwan Najwa. Inda aka debi. Kayan ta a kai dakin ta na da.

Mami da kanta ta hada mata ruwan wanka.

Bayan ta fito ne Najib ya kira suka sha hira abin su.




A bangaren Sumaiyya kuwa safiyya nayi ta kwashi kayan ta ta hada ta tafi tasha ta hau mota sai kano.

Ko da ta isa kano gidan su Antyn ta ta wuce, Antyn tasai zuga ta take akan ta bar wani Najib ta shigo gari kawai.

Sai da ta gama ziga ta sannan sukai gidan Mama.

Mama na zaune suka shiga kallon su ta tsaya yi taga daga ina suke tare.

Zama sukai sumaiyya ta mikawa mama takardar hannun ta.

Budewa mama tayi, ta zaro ido tana salati.

Ta ce,
"Yanzu abinda kikai kenan Sumaiyya. kin kaso auren kin dawo. Mene. Najib baya mana amman kika ki zama. Allah ya shirya ki sai kizo mu zauna tare ai."

Mikewa sukai ita da Anty sukai dakin Sumaiyya na da.

Da farko Sumaiyya taso ta sa damuwa aran ta sai daga karshe Anty ta hure mata kunna.

Inda tin kafin ta gama idda suke fita yawon su.

Lokaci kankani Summaiyya tai yi kudi da mota.

Duk yadda Mama zatai mata fada sai ta ce, ai a gidan su Antyn ta suke.

Daga karshe can ta koma da zama. shi kuma baban ta murna yake ta koma gidan Mahaifiyar sa da zama

Mama dai addu'a take mata dan sam ita bata son mu'amalar ta da Amtyn ta.

Najwa kuwa duk tabi kannen Mami da yayan ta da matan yayen ta tai musu alheri kowa da abinda zata kai masa duk da suna da rufin asirin su.

Har wajen Maman Sumaiyya sai da taje tai mata alheri.

Taje wajen su Ummah, inda ummah ta kara gyara jikar ta kamar me.

Najib kuwa yana can yana musu shirye shiryen tafiyar su.

Yau ya dawo da wuri dan ya gama da komai. Yana shigowa Dady ya kira sa.

Dagawa yayi suka gaisa, Dady ya ce,
"Son ina Sumaiyya ne?"

Kai Najib ya sosa ya ce,
"Dady na sake ta."

"What?"
Dady ya fada cikin tashin hankali.

"Dady kayi hakuri, wallahi Sumaiyya tafi karfi na, Dady na. Gaba ni zata so ta kashe ba wani ba. Dady kayi hakuri ka gafar ce ni."

"Ba komai Allah maka albarka. Amman ka daina saurin yanke hukunci."

"To Dady. Gobe ma zan tafi Kano ta can zamu tashi."

"To shikenan Allah kiyaye hanya ka gaishe min da Najwan."

"Zata ji."
Suka fara hira daga ban sukai sallama.

Kwanan su Najwa shida Najib ya dira, Hamma Salim ne ya dauko shi, wannan yasa yayo gida dashi.

Najwa bata san da zuwan sa ba tana kitchen tana yin gulisuwa.
Fitowar da zatai sai ganin shi tayi yana shigo wa.

Yana ganin ta ya bude mata hannu da gudun ta ta tafi ta fada jikin sa.

"Sannu da zuwa Hamma."
"Yauwah Baby na."

Jin shigowar Salim yasa ta sake shi, ta ce,
"Mu shiga ciki."

Kitchen ta shiga ta dauko masa lemo da abinci ta zo ta zuna masa.

Kallon ta kawai yake ta dawo da jikin ta tayi kyau.

Sai da ya fara ci sannan Mami ta sauko suka gaisa.

Yana gamawa ya yi gidan su Ummah daga nan yayi wajen Mami.

*Agur guje*

Kwanan sa Biyar da zuwa suka daga. Su Najwa anyi yawon shakatawa sun sha soyayya ita da Najib.

Sun huta, sun ji dadi sun jiyar da juna dadi.

Rayuwa ta musu dadi sosai.
Sun kuma tabbatar wa da son junan su.

Basa da damuwar komai sai ta faran tawa junan su.

Suna kiran gida inda anan sukaji an sa ranar bikin Hamma Salim.

Fitowar su daga wanka kenan Najib yana shafa mata mai, kallon ta ya tsaya yi.

Iska ta hura masa, ta ce,
"Hamma lafiya?"

"Baby kin kara kyau, kinyi haske, kinga nan."

Ya nuna mata kirji, ya ce,
"Sun kara girma da kyau suna jan hankali na a duk sanda na gan su."

Zaro shi tayi, ta mika masa, ta ce,
"Ungo sha."

Wani yar yaji, na yadda tayi masa magana.

Janyo ta yayi suka rufa da bargo.

Sai da sukaje kasa biyar sannan suka wuce kasa me tsarki.

Kaya kuwa duk garin da sukaje sai Najib ya jidowa Najwa.

Watan su bakwai suka dawo, ta katsina suka sauka.

Gidan Mami, Mami sai murna take tayi nan da su tayi can dasu.

A ranar Najwa taje gidan Zahra, lokacin har Fauwaz ya kara girma.

Dan har ya fara tafiya. Kwanan su hudu suka tafi Kano.

Gidan su Ummah suka fara zuwa, inda Ummah sai nan nan take dasu.

Sai yamma suka tafi gidan su Najwa dan Najib ya ce a ranar zasu tafi Abuja.

Tafiyar dai batayi ba dan sai da suka kwana biyar a kano sannan suka daga.

Kowa Najwa tai masa tsara ta basu kayan su.

Gidan Mami suka dira suna sauka, Kowa yazo ya rungume Najwa yana mata sannu da zuwa.

Suna shiga falon Mami. Mami ta tawo da saurin ta ta rumgume Najwa.

Najwa na shakar kamshin turaren Mami taji juya na dibar ta, daga haka sai tashin zuciya.

Da sauri ta fita daga dakin tayi wajen famfo dake compound din gidan tana shara amai.

Najib ne ke rike da ita, tafi minti goma tana abu daya.

Sai da ya lafa mata sannan ta wanke mata baki, ya dago ta.

Mami ce ta komota, kara shakar turaren da tayi ne, yasa ta kara yin wani aman.

Najwa ta galabai ta dan sai da takai ba abinda take amayar wa sai kakarin.

Sai da ya wanke mata baki sannan sukai bangaren Mami tana maida haki.

Su Bara'atu sai sannu suke mata. Mami ce ta kalli Najib ta ce,
"Son daman bata da lafiya ne?"

"A"ah Mami lafiyar ta kalou."
Mami ta kalle ta ta ce,
"Sannu 'yata."

Cikin lokaci kadan kuma ta dawo dai dai dan har abinci suka ci suka koshi.

Da dare suna zaune a falo Mami da Dady sai Najib da Najwa dake kasa a zaune.

Mami ta ce,
"Son amman anan dai Najwa zatai min kwana biyu ko?"

Shiru yayi, wannan yasa ta kalli Najwa ta ce,
"Najwa zaki kwana ko?"

"Eh!"
Ta fada tana gyada kai.

Kallon Najib tayi da ya zurawa Najwa ido.

Dady ne, ya ce,
"A'ah Najwa gidan ta zata tafi, ai an gama komai ko?"

Da sauri Najib ya daga kai, ya ce,
"Eh Dady daman sallama zamuyi muku."

"To shikenan ku tashi ku tafi Allah yayi albarka ya bada zaman lafiya."
"Ameen!"

Najib ya amsa. Mikewa mami tayi tana kama hannun Najwa.

Dakin Mami suka shiga, nan ta bata kayayaki tai mata bayanin su.

Daga nan sukai bangaren Baba sukai mata sallama.

Tin a hanya taga sun dauke hanyar gida, wani waje ya je ya siyo musu gasaaun nama da lemuka.

Daga nan suka kara dauke wata hanya ita dai tana zaune tana kallon sa.

Wani katon gida suka shiga me kyau dan daga nesa kai ka zata zane ne. Dan kyau da tsarin sa.

Ko kuma kayi zaton ba a kasar kake ba.

Kallon Najib tayi, ta ce,
"Ina ne nan?"

Murmushi yayi ya ce,
"Gidan ki."

Ya bude kofa ya fita. Tana zaune har ya bude mata ita ma ta fita.

Bata kara tabbatarwa da gidan nashi bane sai da suka shiga falon gidan.

Wani katon pics din sune manne a dakin. Ba karamin kyau sukai ba.

Kallon dakin ta tsayi yi, dakin ba karamin kyau yayi ba.

An saka masa pursher pink din kujeru sai adon black a jiki.

Katon falo ne dan su kansu kujerun sun fi set daya a dakin.

Hannun ta ya kama ya fara nuna mata cikin dakunan. A kasa dakin bacci biyu ne, da falo biyu.

Duk an cika su da kaya. Haka sama babban falo ne, sai kofofi guda hudu.

Kofa farko, falo ne da bed room hade da ban daki, dayan ma haka sai daya da aka zuba masa set din gado na yara dayan muka normal daki ne.

Duk gidan an kawata shi yayi kyau haka nan kitchen an cika shi da kayan amfani.

Gidan dai masha Allahu yayi kyau sai tashin kamshi da sanyin AC ke ratsa gidan.

Sama suka shiga kowa ya shige dakin sa. Wanka Najwa tayi ta canja kaya zuwa kayan bacci.

Doguwar riga ce, yar karama iya cinya, ta murje jikin ta da mai me saka kamshi a jiki.

Sai wani turare da ta shafa, tana gaban madubi tana parking din kan ta ya shigo.

Ribom din hannun ta ya amsa, ya ce,
"Yau adon sa nake so a haka"

Ya fada yana Barbaza gashin. Juyowa tayi ta rumgume shi.

Hugging nata yayi, ya ce,
"Baby nah bana taba gajiya dake. Ina kaunar ki."

Murmushi tayi. Gefen gado ya matsa da ita ya zaunar sannan ya fita.

Be jima ba ya dawo rike da Faranti da kofina a hannu sai leda.

Juye musu naman yayi ya sauko da Najwa ya zaunar akan cinyar sa, a baki y dinga bata tana ci yana ci har suka koshi.

Suna gamawa suka fita da kayan sannan suka dawo suka wanke baki suka haye gado suna kashe junan su da soyayya me tsayawa a rai.








*INDABAWA*

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*



*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page *169*
*END*


*Nagode nagode da soyayyar ku gareni. Allah barmu tare masoyana Ameen*






washe gari da safe kamar yadda ta saba kafin Najib ya tashi ta kimtsa, ta gyara gidan ta hada musu break.

Kwalliya ta tsara me kyau. Wacce tasan zata rikita shi.

Sai tashin kamshi take, ta dade a gaban mudunbi tana juui ta kalli can ta kalli can.

Kan gado ta hau inda ta kwantar da kan ta akan kirjin sa, tana shafa kirjin sa, tare da dan hura masa iska a cikin kunnen sa.

A hankali ya bude idon sa, kallon ta yayi, yana murmushi.

Kiss tai masa akan goshin sa, ta ce,
"Love ka tashi kar ka makara ko?"

Agogon dakin ya kalla ya ce,
"Wai! Har karfe sha biyu."

Kai ta gyada masa. Da sauri ya mike ya fada ban daki.

Yana fitowa ya tsaya a gaban madubi yana kintsa wa.

Kallon sa tayi, ta ce,
"Hamma ina Anty nah."

"Wace Antyn ki?"
Kallon sa tayi da mamaki ta ce.

"Anty Sumaiyya man."
Wani murmushi ya saki ya ce,

"Tana gidan su,"
Shiru tayi kafin ta ce,

"Yaushe taje?"
Shiru yai mata.

Wannan yasa ta canja salon maganar, ta ce,
"Hamma dazu Khadija, ta ce,  min sun dawo kwanan nan zasu zo."

"Oh haba?"
Kai ta daga masaa.

Kaya ya saka, ya koma gaban madubi ya dauki wani turare yana fesawa.

Tinda, ta fara jin kamshin turaren taji kanta na juyawa.

A hankali ta koma ta kwanta akan gado. Sai da ya gama sannan ya juyo ya kalle ta.

Murmushi yayi, ya yi gun gadon, yana zuwa ya dago ta, dai dai fara shara aman ta a jikin sa.

Tana kokarin tashi ya riketa har ta gama sannan ya dauke ta suka shige ban daki.

Sai da yai mata wanka, sannan ya yi shima.

Yana fitowa ya shirya ta suka sauka kasa ya bata abinci. Ya dauke ta suka tafi asibiti.

Gwajin farko da akayi aka tabbatar tana dauke da juna biyu.

Murna gun Najib kamar me, dan rasa abinda zai yi yayi.

Daga nan ya wuce da ita store ya dinga jikar kayan Babies.

Najwa dai sai dariya take masa. Daga haka suka tafi gida.

kamar waccen cikin dai Najwa ta sha fama da laulayi dan wannan har yafi na wancan.

Ranan suna zaune a harabar gidan sai ga su Khaleel nan. da gudu Najwa taje ta tare ta.

Khadija na da yara biyu da lil N da Iman.

Ciki suka koma Najwa ta kawo musu lemo da abinci.

Ranar a gidan suka kwana, sun sha hira kamar me?

Kwanan su biyu suka daga bayan sunje gidan Mami sun yinar mata.



Sumaiyya kuwa likafa taci dan ita da Anty karuwanci yai gaba abinda bata tin tana budurwa ba shi yanzu take.

Dan fitar ta wajen uku bayan rasuwar auren ta, ta zama babbar yarinya da ba kowa take kulawa ba

Duk ranar da taje gun Maama sai tai mata fada amman kamar bayi ake ba.

Mama ba abinda take sai addu'a da tashin dare kan Allah ya shirya mata sumaiyya.

Har azumi Mama take da sadaka.

Kamar ko da yaushe wannan karan an gayace su partyn wani group nasu na karuwai wanda zasuyi a wudil.

Tin kafin lokacin suke shirye shiryen abinda zai faru.

Dinki sukai wanda daga gani kasan ba yayan mutunci ne zasu saka ba.

Sun shirya komai inda suka dau mota ita da Antyn ta suka hau titin Wudil

A dai dai gada suka tafka hasari inda daga nan aka dauke su aka kaisu Asibitin murtala duk kan su a jinya ce.

Kowa baya cikin hayyacin su wannan yasa aka yashar dasu kafin yan uwan su suzo.

Duk wayar su ba number gida ko daya sai ta abokan shashancin su.

Su kuma duk wanda aka kira baya gari sai wanda suna can shargoliyar su, basuga kiran ba.

A haka suka kwana wanda Sumaiyya ta karye a kafa, Antyn ta kuma ta karye a cinya da hannu.

Duk ba a duba su ba, har saida Wani dan unguwar su Sumaiyya yazo ya gansu sannan ya sanar da Mama.

Mama da hanzari ta nufo asibitin tana kuka. Zuwan ta shiyasa aka duba su.

Akai musu treament din ciwo kan su, inda suka tafi dasu gidan dan a daura su,

Alhamdulilah anyi dauri lafiya sai dai yanzu ba damar yawo suna zaune a gida,

Mama ita ta dinga dawainiyya da su.

Antyn ta da ta karfe a cinya tafiyar ta ta canja sai wani gwalatsewa take.

Ita kuwa Sumaiyya sai dingishi take da jan kafa.

Badai wanda zai kalle su ya ce, sune matan nan masu adabar jama'a.

Yan uwan shasahnci su kuwa ba wanda ya wai waye su.

Tin daga wannan suka shiryu suka koma ga Allah.

Sumaiyya tayi nadama sosai inda ta yi aure ta auri wani mai rufin asiri ta zauna lafiya.

Itama Antyn ta ta komai gidan uban ya'yan ta.



*Seven month*

Najwa ta haifi yan biyu duk maza, inda aka saka wa Baban Abubakar suke kiran sa da Nashat, Ahmad kuma suke kiran sa da Nashit.

A gida tayi wankan arbain anan taje gidan Mama ta gaishe ta.

Anan ne suka hadu da Sumaiyya take neman yafoyar ta akan abinda tai mata.

Najwa da bata san me tai mata ba. Shiru tayi ita dai.

Har ta roketa ta bawa Najib hkuri. Ba komai Najwa ta ce, bayan ta dauko kudi ta bata da atamfofi.

Sumaiyya da ta tsani Najwa kamar me, sai gashi yanzu Najwa ta kere mata.

Komai nata abin sha'awa ga yara. Gashi itaa tayi aure ko haihuwa batai ba.

Sai bayan arba'in ta dawo.

Ya'ya basu hana Najwa kula da mijin ta ba haka nan basu sa ta ganda ba.

Tsakanin Najwa da Najib kuwa sai zaman lafiya da ya duwar soyayya.

Bayan shekara uku Najwa ta haifi Babyn ta kyakyawa wacce aka sa mata sunan Kakar Najwa wato sunan Najwan.

Amina inda suke kiran ta da Meenal.

Najib ya kara girma da cikar haiba samun ya'ya da mata me son sa da kyautata masa.

Bai da damuwar komai ai burin farantawa iyalin sa.


*Shekara biyar*

Hamma Salim yayi aure har da ya'ya uku.

Haka nan su Bara'atu da Talle duk sunyi aure suna da ya'ya bibiyu.

Basma yan mata yanzu zatayi aure.

Najwa kuwa yayan ta hudu, bayan Meenal ta kuma haifar Namiji inda aka saka masa sunan Baffah.

Rayuwa tayi dadi ta ko ina basu da damuwar komai sai zumunci da suke yi a tsakanin su.




*Alhamdulillahi rabbil alamin*

Anan na kawo karshen wannan littafi, nawa. *Najwa* kuskuren dake ciki Allah ka yafemin, abinda na rubuta daidai kuma Allah kabani ladan, nagode nice taku har kullum *Maryam Suleiman Indabawa*

kuzama cikin aminci, semun hadu cikin sabon book dina me suna *............*

Sakon gaisuwa da ban girma ga Mahaifana.

My sweet Mum Allah kara maki lafiya da duk musulmai baki daya, *Momy nah a komai kece Fari tnc for ur love nd supporting*

Allah kara miki Nisan kwana yasa ki gama lafiya Ameen.

Mahaifina Allah jikan ka yai maka rahama yasa ka huta.

Daga ke sai Yar uwa ta. Rayuwa ta *Nusaiba Suleiman Indabawa. Autar Dady*
kema kina son Littafin nan *Najwa* nagode sosai Sis. Allah barmu tare ya kara mana son juna Ameen*

Kina ina Autar Momy. Autar mu. *Hauwa'u Yasmeen*
Sonki daban yake a zuciya ta. Really love u Autah.

*Anty nah. Allah yaja da ranki. Allah dada daukaka da basira. Gaisuwar ki daban ce, ba kowa ba ce, fa ce, *Rashida Abdullahi Kardam*

Ina kaunar ki sosai. na kuma sadaukar da littafin nan xuwa gare ki.

My kawar fada, my sister ke my everything *Nusaiba S Indabawa*

Da kuma my best frnd, my kawar shawara
*Hauwa kamilu Zimit*
Allah ya albarkaci rayuwar ki ya kare ki daga sharrin mutum da aljan, ya baki ya'ya masu albarka. Ya kara daukon soyayya tsakanin ki da *Yaya Bashir*
*Ameen*


Na gaishe da ku dukkan *marubuta littafin hausa Nobel* Allah kara basira da zakin hannu.

*Sis Bilkisu Yakub* nagode da kaunar ki Allah bar zumunci ya raya *Muhammad* Ameen

Our the great *Barrister* Allah kara basira da

Please Login or Register in order to submit comment