Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai mala'ikan mutuwar zai zo ya hada dani. Mama ce tafito ta ganni a gurin, sai ta dauko tabarma ta shimfida mana muka zauna ta jani zuwa cinyarta na kwanta. Anan mukayi sallar magrib, sai ga yaya ladi ta fito tazo inda nake ta shafa kaina tace "sannu Halima, Allah yaji kansu yayi musu rahama, shi kuma Aliyu Allah ya bashi lafiya" na dago kai da sauri na ina kallonta sai naji tace wa Mama "zan koma asibiti inga halin da yake ciki" Mama tace "to Allah ya jishe mu alkhairi" nace da Mama "waye a abibitin?" Tace "Sadauki mana" naji wani abu mai nauyi daya tokare tun daga zuciyata zuwa makogwarona ya janye, numfashi na ya fara fita da sauri nace "Sadauki? Ba tare suka mutu ba? Na dauka ko an kai gawarsa wani gurin" ta rike hannuna tace "Sadauki bai mutu ba ya samu buguwa ne a kansa shi yasa doctors sukayi sedating dinsa. Baffanku kuma tun kafin a kawo su asibiti ya cika, Ummah kuma tashin hankali ne ya saka ta yanke jiki ta fadi, jininta yayi mugun hawan da cikin yan mintina ta mutu" naji wani abu yana sauka daga kai na zuwa kafafuwana. Sadauki is alive. Then there is hope for me.

A daren ranar banyi bacci ba, muna kwance ina rungume da Asma'u da take ta jera ajjiyar zuciya saboda kukan da tasha, sai da naga ta samu bacci mai nauyi sannan na zame jikina na fita palo, Inna na gani zaune akan sallaya ta rufe fuskarta da hannayenta tana kuka a hankali, sai na wuce ta na shiga toilet nayo alwala nafito nima na tayar da Sallah, yau shine daren Baffa da Ummah na farko a kabarinsu kuma nasan suna bukatar adduoin mu sosai. Har na idar da sallolina Inna tana kuka, sai na kwanta akan sallayar na dora kaina akan cinyoyinta sannan nima na samu kuka yazo min.

Washegari yan Kollere suka zo, gida ya cika taf ana ta karbar yan gaisuwa amma babu wanda naji ya kuma maganar halin da Sadauki yake ciki, yaya ladi ma kuma ban kuma ganinta ba duk kuwa da cewa jama'ar Ummah suna ta zuwa gaisuwa suma. Inna dai kam tayi kuka kamar idonta zai fita kowa yashigo gidan sai ya tausaya "uwargidan sace kuma uwar yayansa". Sai dare na ajiye tsorona na tambayi Inna "Inna ya jikin Sadauki kuwa?" Ta kalle ni ta dauke kai, "ban sani ba" ta fada tare da cigaba da jan carbin ta.

Ranar da akayi sadakar uku ranar munga mutane, dan ko ranar mutuwar gidan baiyi wannan cikar ba, ranar yaya ladi tazo akayi adduoi da ita, sai da aka gama ta tashi zata tafi na bita a baya nace "yaya ladi ya jikin Sadauki?" Ta juyo ta kalleni tace "da sauki Halima, jikinsa da sauki" sai ta juya tayi tafiyarta. Alhaji Babba ya shigo bayan an gaishe shi yace "Amina zamu saka a gyara muku guri a can gidana, idan anyi bakwai sai ku koma can ku zauna ke da yara saboda nan din ba zaku ji dadin zama ba ku kadai. Allah ya ji kansa" akace ameen sannan akayi masa godiya ya tashi ya tafi.
Zuwa yamma I have taken all I can, ji nake nima kamar nawa jinin zai hau irin na ummah nima in mutu, an gama adduoin kuma an mayar da gidan kamar gidan biki sai ciye ciye ake da hira da dariya. Na shiga dakin inna na bude jakar ta na dauki kudi na saka hijab dina na fixe ba tare da kowa ya lura ba. Adaidai na hau direct na tafi asibitin malam, naje har emergency room nayi sa'a kuma visiting hours ne dan haka na tambayi nurses Aliyu Usman Kollere nake nema sai suka ce inje aminity room 3. Da sauri na na tafi, zuciya ta tana jin kamar zata kara sauri tayi gaba ta riga ni shiga dakin.

A kwance na same shi da drip a hannunsa daga alamar har yanzu allurar baccin akeyi masa, fuskarsa da dan fada kuma tayi haske, kansa a nade da bandage. Babu kowa a dakin sai shi kadai. Na karasa ciki inajin wani irin tausayinsa yana saukar min, na zauna a gefen gadon na kamo hannunsa nayi intertwining fingers din mu. Ya dan bata rai sai kuma yayi blinking ya bude jajayen idonsa yana kallona, ya kakalo murmushi mai nuna yana jin ciwon yinsa yace "you are here" na gyada kai nace "am here" yace "waye ya dauko ki daga school?" nace "Abban su Rumaisa" yace "good" mukayi shiru kuma can sai yace "ya jikin Baffa?" Gabana naji ya fadi na zuba masa ido, wato bai ma san abinda yake faruwa ba? Ya sake cewa "yaya ladi tace min ya samu karaya ne shine aka kai shi asibitin kashi. Shine kuma duk kuka tafi gurinsa ko?" Ya sake kirkiro murmushi "dama nasan Ummah tafi son Baffa akaina shine ta tafi jinyarsa ta barni, in kin koma ki gaya mata nayi fushi, nima tawa matar tazo ta ganni" na cije lebena ina danne kukan da yake so ya kwace min, sai yace "don't cry please, everything will be alright"

Na gyada kaina nace "yes Sadauki, everything will be alright. Ka koma kayi baccinka" ya lumshe ido yana kara rike fingers dina a cikin nasa. Mun jima a haka ina kallon fuskarsa ina jin wani irin yanayi yana kara shiga ta a kansa, nayi kokarin zare hannuna daga nasa sai ya kara rikewa a hankali cikin bacci yace "don't leave me please, stay with me please" sai ya dora hannayenmu akan kirjinsa sannan ya dora daya hannun ya sake rike wa.

A haka yaya ladi ta shigo ta same mu, ta tsaya tana kallon mu sannan ta girgiza kanta tace "an mutu an bar muku gadon wahala".
[1/21, 10:27 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Twenty Two : Birthday Gift

Abinda na tarar a gidan mu dana koma banji dadinsa ba, harkoki kawai ake yi ana wadaka da abinci, wato shi wanda akayiwa mutuwa shi kadai ta shafa ko? Shi kadai yasan me yake ji? Wato mutuwa ba zata zamo izna ga sauran mutane su nutsu su daina biyewa duniya ba? An bubbude koina har palon Baffa mutane ne a ciki, bedroom dinsa ne kawai a rufe.

Dakin mu na wuce da niyyar in kwanta inji da abinda yake damuna amma sai na tarar da yammata ne fal a dakin, suna ta dauke dauken hotuna da kallon videos a waya suna kyalkyatar dariya. Ko magana banyi musu ba na fito da shiga part din Ummah, babu kowa anan kofar palon ma a saye take dan haka na tura na shiga na mayar na rufe. Direct dakin Sadauki na tafi na bude na shiga. Dan karami ne dai dai size din dakin mu ni da Asma'u, katifa ce kawai a dakin sai wardrobe, standing fan, sai kuma tarkacen takardu a gefe. Sai hoto guda daya a jikin bango. Na tsaya a gaban hoton ina kallonsa kamar yau na fara ganinsa, Ummah ce da Baffa a zaune akan kujera, sai Sadauki a durkushe a gaban baffa sai ni kuma akan cinyar Ummah da shubeya a hannu na.

Na tuna sanda aka dauki hoton da wata sallah ne lokacin Inna tana da cikin Asma'u, babu yadda Baffa baiyi ba ita ba akan tazo ayi hoton taki tace sai dai yaje mu dauka daga ita sai shi sai ni. Shi kuma yaki. Na zauna a gaban hoton ina jin kewarsu tana kara mamaye ni, ina jin kamar inyi rewinding din rayuwar mu ta dawo baya in cigaba da ganin su, in cigaba da ganin Sadauki a gidan mu. Inna tuna cewa Sadauki bai san anyi mutuwar nan ba sai inji zuciya ta duk ta narke, bansan yadda zai dauke ta ba, ina gudun kar wani abun ya same shi shima. In na tuna yanzu bashi da kowa a duniya sai inji kamar in tashi in koma asibitin in zauna a wurinsa. Hope dina daya shine na yaya ladi zata kaishi gurin mahaifinsa tunda nasan dole zata san waye shi, in ma bata sani ba shi wanda ya hada auren ai zai sani. Amma kuma in nayi wannan lissafin sai inji zuciya ta ta kara tsinkewa saboda tunanin rabuwa da Sadauki. Kuma what if shi uban baya bukatarsa? What if shine yakori Ummah da jariri yace baya so?

Anan dakin bacci mai nauyi ya dauke ni saboda kwana ukun nan duk bana samun bacci mai nauyi. Na jima ina yin baccin sai naji magana kamar a tsakiyar kaina ance "Diyam? Uban me kike yi anan?" Na tashi zaune ina mitstsika ido amma na kasa bude idona saboda fitilar da aka haske ni da ita. Aunty Fatima tazo ta kama ni muka mike "tun dazu ake ta neman ki, babu inda ba muje ba duk hankali ya tashi mun dauka an sace ki ne" nace "kuyi hakuri, bansan bacci ya dauke ni ba, hayaniya ce ta yi yawa acan ni kuma ina so in zauna ni kadai" sai kuma sukaji tausayina, amma inna sai da tace "kuma ki rasa inda zaki je ki kwanta sai nan dakin? Ba gwara ki tafi makota ba?".

Sai da aka sake kwana biyu sannan na kuma samun dama na tafi dubo Sadauki, wannan karon tare da Rumaisa muka tafi kuma sai da na saka tayi min alƙawarin ba zata gaya wa kowa ba. A zaune muka tarar dashi yaya ladi tana ta fama dashi akan yaci abinci. Tun a fuskarsa na gane yaji dadin zuwana sosai. Yace "kun taho da waya? Ina son in kira Ummah, ina so kuma inji ya jikin Baffa" na girgiza masa kai nace "bani da waya ai ka sani, kuma bansan zaka bukata ba shi yasa ban karbo wata na taho da ita ba" ya jingina kansa a jikin gado yana runtse idonsa yace "a gurin da muka yi accident aka dauke min waya ta, ita kuma wannan tsohuwar wai tata ta lalace" na jawo kujera na zauna ina karbar kwanon abincin daga hannun yaya ladi nace "duk suna lfy Sadauki, ummah cema tace inzo in duba mata kai. Kasan ba zata iya barin Baffa ba Musamman yanzu da bashi da lfy" ya gyada kai yana murmushi yace "ji nake yi kawai ina so in ganta" ina kallon Rumaisa ta tashi ta fice daga dakin. Na zuba masa tuwon alkama miyar danyar kubewar da yaya ladi tayo masa na zauna ina bashi a baki, ba musu yake karba idanuwansa a kaina ko kiftawa baya yi har sai da ya cinye wanda na zuba masa tas, yaya ladi tace "oh, tun safe nake fama da shi akan yaci abinci yaki ci, shifa yace inyi masa tuwon amma shima ya bar ni da abina, amma da yake ke kece gashi nan ai ya cinye tas" ya juya yana kallonta yace "baki iya tarairayar miji ba ne shi yasa" da alama so yake suyi wasa irin yadda suka saba amma sai ta kasa mayar masa, sai ta hau tattara kayan gurin ta fita dasu.

Na saka tissue ina goge masa bakinsa sai ya rike hannun yana kallona cikin ido yace "kin rame, kinyi duhu, idonki sun kumbura" na kirkiro murmushi nace "ka manta daga makaranta na dawo, kuma exams muka gama bama samun isashshen bacci" ya saki hannuna yace "fada min gaskiya, ya jikin Baffa, is it bad? A ina ya karye?" Na kasa kallon idonsa nace "a hannu ne kuma da sauki" yace "hannu kuma? I thought kafa ce ma saboda shi yake driving" na dago ina kallonsa da mamaki dan nasan Baffa hardly drives in dai da Sadauki a motar. Nace "me ya faru?" Ya sunkuyar da kai yace "rami muka daka sai taya ta fashe, daga nan motar ta fara a dungure akan titi, sai data daki wata bishiya sannan ta tsaya" na gyada kaina ina rike hawaye na.

Muna komawa gida muka tarar da inna a tsakar gida tana alwalar magrib tace "daga ina kuke?" Rumaisa tace "makota muka shiga". Shikenan bata kara ce mana komai ba.

Washegari bayan nayi sallah na kwanta akan kujera amma ba bacci nake yi ba, na rufe idona ne kawai saboda bana son kowa yayi min magana a lokacin. Ina ji akayi ta hidimar abinci sannan aka fito palo aka baje kowa yana ci ana ta hira, cikin hirar naji Inna tana bawa yan uwanta da suka zo daga Kollere labari:

"Wallahi in gaya muku, daga zuwanta da yaron nan ya dauki son duniya ya dora akansa, komai Sadauki komai Sadauki, ni na dauka ko rashin haihuwa ne ya saka haka amma sai gashi bayan na haifa masa yaya har biyu amma sadaukin nan dai ya fiye masa duk su biyun. To in ba asiri ko maita ba me zai jawo haka? A ce agolan da aka haifa a wani gidan koma a wani titin ne oho, tunda babu wanda yasan ubansa amma ace yafi yayanda mutum ya haifa da cikin sa? Ai shari'a tsakani na da zainabu sai a lahira za'a karasa ta. Tun yaron nan yana dan mitsitsinsa aka fara bashi mota a gidan nan, kullum 'sadauki zo ka kaini guri kaza, Sadauki zo muje guri kaza' nayi magana amma a banza tunda dama ni ba jin magana ta yake yi ba. Shine ranar nan yace "Sadauki zoka kaini Taura mu dauko Diyam' to gashi nan bai kaishi taura ba ya kaishi lahira" naji kaina ya sara, ina so in tashi in gaya mata cewa ba Sadauki ne yake driving a ranar ba amma nasan ba yarda zata yi kuma zata tambayeni wa ya gaya min.

Wata ta tambayeta "to ina yaron yake yanzu?" Tace "yana asibiti yana karbar magani, kinsan irinsu bada wuri suke mutuwa ba" sai na tashi tsam na wuce su na shiga daki. I can't take sunan sadauki da sunan mutuwa a sentence daya, not now da nake ganin ya samu sauki sosai. Not now da nake ganin nafi bukatar safiye da koyaushe.

Washegari akayi sadakar bakwai. Jama'a sun taru sosai bangaren Baffa da na Ummah, ga kuma makota da abokan arziki. Yaya ladi ma da sassafe tazo ta bude dakin Ummah inda mutanen su suka zauna. Ana gama yin adduoi aka yi sadaka sai kuma kowa ya fara watsewa, har yan Kollere ma duk sun gama shirin su ana gama wa suka yi sallama suka dauki hanya. Muma kuma sai Inna ta fara hada mana kaya amma ni sai na koma na zauna a tsakar gida na takure a guri daya ina sheshshekar kuka. Yanzu shikenan barin gidan mu zamuyi? Gidan da aka haife mu muka tashi a ciki, me yada zamu barshi mu koma gidan wasu mu zauna a karo? Bayan muna da rufin asirin mu. Ina kallo aka fara fita da kayan mu ana zubawa a motar da Alhaji Babba ya aiko da ita.

A lokacin ne kuma ya shigo. Kansa still a nade da bandage hannunsa kuma sanye da carnula. Ya tsaya yana rike da kofa for support idanuwansa a kaina, na mike nima ina kallonsa ina hango tsantsar tashin hankali a idonsa. Ko ba'a gaya min ba nasan ya sani. "Ina Ummah?" Ya tambaye ni da wata irin murya, sai na fara sheshshekar kuka na kasa ce masa komai. A lokacin ne Inna ta fito da wani akwati a hannunta ta ajiye tana kallonsa tace "sun sallamo ka kenan, dama yanzu nake tunanin yadda za'ayi a fitar maka da kayanka zamu rufe gida" ya kalleta kawai sannan ya sake mayar da dubansa kaina yana kallon yadda nake kuka babu sauti, hawaye wani na korar wani. Sai ga yaya ladi ta shigo afujajan, tana ganin shi ta sauke ajjiyar zuciya "yanzu shine ka fito daga asibitin ka taho nan Aliyu?" Kallo daya yayi mata sai ta saka kuka itama.

Na tafi a hankali har inda yake tsaye na rike hannayensa a nawa, sai kuma na dora kaina a kirjinsa a hankali nace "Sadauki Ummah ta tafi ta barmu, Baffa ma ya tafi ya barmu, sun mutu Sadauki ba zamu sake ganin su ba. Mu dasu sai dai muyi musu addu'a kuma sai kuma a lahira in munje muma"

Baice min komai ba bai kuma yi magana ba amma ina jiyo yadda zuciyarsa take bugawa kamar zata bar jikinsa, ya saka hannu ya ture ni daga jikinsa ya fara tafiya kamar zai tafi dakin Ummah sai kuma ya juyo, yayi kamar zai fadi na tafi zan rike shi sai ya dakatar dani da hannu daya daya hannun kuma ya dafe kirjinsa dashi. Ya dan jima a haka sannan ya sake straightening ya doshi hanyar waje, da sauri ni da yaya ladi muka rufa masa baya muna kiransa amma sai Ummah ta damko rigata a dawo dani baya "in kika bar gidan nan sai na kakkarya ki" ta harari waje "muma duk marayun ne, mun rasa iyayen mu kuma mun hakura".

Sai daga baya na fahimci ashe wasu kawayen Ummah ne suka je duba shi a asibiti shine suka yi masa gaisuwa, basu san cewa bai sani ba, shine ya gudo daga asibitin ya taho gida dan ya tabbatar. Ni dai a bangare na zan iya cewa tunda akayi rasuwar nan banyi kuka mai yawa irin na ranar nan ba dan a tsakar gida na zauna nayi tayin abu na, ina kukan tausayin kaina ina kuma kukan tausayin Sadauki. Menene makomar mu ? Menene makomar soyayyar mu? Babu wanda ya kula ni sai Asma'u da take makale dani tana taya ni kukan itama.

Can naji Inna tana cewa "su kenan kayan sun kare, in muna bukatar wani abu ko Diyam sai tazo ta daukar mana tunda babu nisa" Mama tazo ta tashe mu ni da Asma'u "ku daina kuka kunji? Ai ba barin gidan kuka yi ba gaba-daya zaku dawo in innar ku ta gama takaba" na gyada mata kai kawai. Muna ji muna kallo aka tisa keyar mu zuwa waje aka rufe gidan, a raina ina tunanin kayan Sadauki fa? Kayan Ummah fa? Ai bamu kadai muke da gidan ba tunda dai a tunani na Ummah tana da gado dan haka Sadauki ma yana da gado kenan.

Ina shiga mota kamar ance in kalli side sai na hangoshi a tsaye a jikin bishiyar da take opposite gidan mu, hannayensa a rungume a kirjinsa, idanunsa a cikin nawa. Nayi kamar zan fita sai Inna ta tura ni ciki ta shigo ta rufe kofa. Driver kuma ya tayar da mota muka tafi. Na juya waiwaya baya ina hangoshi ya matso tsakiyar layin mu yana kallon motar mu har muka sha kwana na daina ganinsa. Na juyo idona ya sauka akan dashboard din motar, agogo na kalla,time 3:15 date 25th August and it occurred to me cewa yau ne ranar Birthday dinsa, a yau ya cika shekaru ashirin cif a duniya. So young and so alone. Sai na rufe fuskata da hannayena ina sake wani sabon kukan.[1/22, 11:13 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤ DIYAM ❤

By

Maman Maama

Episode Twenty Three : Shared Strength

Assalamu alaikum wa rahmatullah

Ina neman afuwar wadanda littafin Diyam ya saka kuka a kwana biyun nan, ina rubutu ne dan in faranta muku badan in bakanta muku ba. Amma ina so ku sani ita rayuwa is full of ups and downs dole sai ansha wuya sannan za'a sha dadi. Ina so duk sanda kuke karatu ku saka a ranku cewa kirkirarren labari ne, non of this happened in real life duk da cewa zai iya faruwan. But labarin Diyam kirkirarren labari ne.

Daki ne aka bamu a gidan Alhaji Babba, dakin a babban palon gidan yake. Ciki daya ne da banɗaki mai dauke da gado da wardrobe a ciki, asalin dakin an yi shine saboda baki in sunzo daga Kollere anan suke dauka amma sauran matan gidan kowa in tayi baki to part dinta suke tafiya. Muna zuwa matan gidan duk suka firfito harda Hajiya Babba da kanta, aka zauna a palo ana ta kara yiwa juna gaisuwa da kuma jajanta abinda ya faru sannan aka saka yan aiki suka kara gyara mana dakin aka kai mana kayan mu can sai kuma kowa ya watse ya bar mu mu kadai.

Nina fara tashi na shiga dakin da aka bamu ina kare masa kallo, babu laifi yana da girma kuma da toilet a ciki amma kuma it doesn't change the fact that aro aka bamu, aron kuma da nia ganina bama bukata. Na tuna yawan dakunan da suke gidan mu, Inna daki biyu da palo, Ummah daki biyu da palo sannan ga dakin Baffa ciki da palo ga kuma dakin waje, amma wai duk mun ajiye su mun dawo daki daya mun zauna da sunan taimako, taimakon me? In taimaka mana za'ayi ni a ganina ai food stuff ya kamata ake kai mana can gidan mu kamar monthly haka ko duk sanda aka samu dama, ko ake bamu kudi muna siyan abin bukatun mu da kan mu amma ba gurin zama muke bukata ba. Kuma ko kudin ne ma ni aganina zamu iya kula da kan mu ba sai mun dogara da kowa na. Yes, Baffa ya mutu amma bai bar mu fakirai ba, ya bar garejin sa da yake running for over twenty years, zamu iya cigaba da running kayan mu da kan mu, Sadauki can do that tunda yasan komai dashi ake komai kuma duk costomers din Baffa sun san shi.

Ni a ganina da mun yi zaman mu a gidan mu mun dora Sadauki akan komai kuma nasam as hard working and dedicated as he is zai iya yin komai. Ya cigaba da zamansa a gidan for security tunda za'a ce ba zamu zauna mu kadai babu namiji ba, in ma kuma Inna bata son zamansa a cikin gidan tana ganin ba muharramin mu bane ba zai iya zama a dakin waje ai, kuma yadda yake da kwarjini din nan babu wanda zai kawo mana raini a unguwa. Sadauki yana da gado a gidan da garejin, so it will be a mutual relationship wanda ni nake ganin mu zamu fi benefitting akan sadauki.

Ina ta tunanina har Inna ta shigo tana ta jera mana kayan mu a wardrobe din dakin, Asma'u tana tayata tana kuma mitar cewa wardrobe din tayi mana kadan sai dai mu bar wasu kayan a cikin akwati. Bayan sun gama na tashi na sake goggoge dakin na wanke toilet na jera mana toiletries dinmu da kuma kayan shafe shafen mu, sannan nayo wanka da alwala nazo nayi sallah tare da jera adduoin neman nasara akan Inna in samu ta saurare ni ta kuma yadda da shawara ta.

Da dare sai ga kwanukan abinci nan daga duk matan gidan kowa ta zubo ta aiko mana dashi, Inna ta karba tayi godiya amma daga ni har ita ba wani cin kirki mukayi ba Asma'u ce ta danci da yawa. A lokacin da muke cin abinci ne naga chance dina na magana da ita dan haka na zayyane mata duk tunani na da plans dina na kara da cewa "inna in mukayi hakan kamar mun dogara da kan mu kenan, ba ruwan mu da abinda za'a bamu da abinda ba za'a bamu ba. Duk wanda ya ke ganin zai taimaka mana saboda zumunci sai yaje har gidan mu ya taimaka mana in ma ba'ayi mana ba bamu da damuwa tunda muna da abin hannun mu. Inna dan Allah ki duba maganar nan".

Tunda na fara ta ajiye spoon dinta tana kallona har na gama sannan ta fara girgiza kai tana kallona tace "yayi daidai Diyam, ya kamata a jinjina wa wannan tsarin naki. Amma bara in tambayeki, sanda kike yin wannan tsarin mune a ranki ni da Asma'u ko kuma bakin yaron can? Iye? Wato bakin cikin ki shine mun taho nan gidan an raba ki da shi shine kike so mu koma saboda ku cigaba daga inda kuka tsaya ko? Kuma ke yanzu a tunanin ki duk duniya in rasa wanda zan dauki ragamar rayuwata ni da yayana in bawa sai wannan yaron? Bani da yan uwane? Ko shi mahaifinku bashi da yan uwan da zasu kular masa da sana'arsa su kuma kular masa da iyalinsa? Ai ina sane na karbi shawarar Alhaji Babba ta cewa mu dawo gidan sa mu zauna saboda in raba

Please Login or Register in order to submit comment