Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kokarinsa gurin adalci amma Inna gabaki daya ta burkice, ta riga ta sakawa ranta cewa Baffa yafi son Zainabu a kanta dan haka komai sai take ganin kamar zaluntarta yake yi, ko magana sukayi kasa kasa shida Zainabu sai taga kamar gulmarta suke yi, sannan ga rashin haihuwa, dadin dadawa ga dan da Zainabu tazo dashi wanda Baffa ya dauki son duniya ya dora akansa. A bangaren Zainabu kuma, let me tell you about Zainabu, tunda nake a duniya ban taba ganin mutum mai hakuri irin ta ba, irin mutanen nan ne da ko zaka zuba musu kashi aka ba zasu kula kaba sai dai su karkade maka wanda ya taba jikin ka. Dan zan iya cewa idan da akwai hakkin da Inna take dauke dashi a kanta to hakkin Zainabu ne.

Let me tell you about Aliyu. Zuwansu gidan mu Baffa ya chanza masa suna saboda sunan Hardo ne dashi ya ke ce masa Sadauki, Sadauki tun yana jariri kakkarfa ne na gaske dan karfin sa ne ma ya saka Baffa ya saka masa Sadauki. Baki ne, dan kusan kullum ba'ar da Inna take masa kenan "Baƙin munafiki" ko "baƙi mai bakar zuciya". Yana da godon hanci da nannadadden gashi irin na fulani, bayan wadanda kuma bai dauko komai na Umma (Zainabu) ba.

Shekaru suka sake turawa, akayi haife haife da yawa, musamman gidan Alhaji Babba wanda yayi ta aure aure on his quest for samun yaya maza amma in banda second born dinsa yaya Kabir bai kuma samun namiji ba. Goggo na da yakumbo na ma da akayi musu aure daga baya duk suma duk sun haihu, wannan ya kara daga hankalin Inna. Cikin ikon Allah Sadauki yana shekara shidda a duniya Inna ta samu cikina, amma hatta shi kansa baffa bata bari yasan da cikin ba saboda tana ganin kamar Ummah zata cinye abinda yake cikin nata. Sai da ciki ya fito sannan aka gani, Baffa kamar zai zuba ruwa a kasa ya sha saboda murna, yana murna Ummah tana taya shi.

Baffa ya bani labarin cewa ranar haihuwa ta, shi, Ummah da Sadauki ne suka kai Inna asibiti a motar Baffa. Suka zauna suka jira, Ummah tana ta jerawa Inna addu'ar samun saukin nakuda har Allah ya sauke ta lafiya. A lokacin da aka fito dani a zani aka bawa Baffa shi kansa ba zai misalta irin farin cikin da ya samu kansa a ciki ba, ya karbe ni yana nuna wa Ummah wadda take ta goge hawayen taya Baffa murna. Sadauki yazo ya bude fuskata yana kallona, ya shafa fuska ta yana sannan ya gwada hannunsa a jikin fuskar yana ganin banbancin kalar fatar mu, yayi dariya yace "Baffa wannan babyn kyakykyawa ce" Baffa yace "kanwarka ce sadauki. Sunan ta Haleematus Sadiya" Ummah tace "Allah ya raya mana mai sunan Inno" Sadauki yace "to Baffa mai za'ake ce mata?" Baffa ya shafa kansa yace "matarka ce ai, kai Hardo ita Inno, sai ka zaba mata suna da kanka" Sadauki ya yi shiru yana kallon fuska ta yace "Diyam. Diyam zamu ke ce mata Baffa" Ummah tayi dariya tace "to Allah yasa ta zamo mana maganin kishin ruwa" Baffa shima yana dariya yace "ameen". Ummah ta karbe ni saboda Baffa yaje siyan magungunan da aka rubuta, yana tafiya su goggo Fatima suka zo, da sauri yakumbo ta karbe ni daga hannun Ummah tana tofe ni da adduoi, sannan ta juya gurin Ummah tace "kurwarta kur wallahi. Wannan yarinyar tafi karfinki" daga nan suka juya sunayi wa juna barka tare da yaba kyawuna ba tare da sun lura da Sadauki daya hade rai yana ta zabga musu harara.
[1/9, 10:09 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤ DIYAM ❤

By

Maman Maama

Episode Eleven: Family

Daga asibiti gida suka taho gaba-daya. Suna zuwa Alhaji babba da kawu Mamman suka zo, Kawu Mamman yace "zamu tafi da Amina can gidan Alhaji Babba ta zauna tayi wanka a can" Alhaji babba ya kara da cewa "zata zauna a can sai yarinya tayi kwari, daga nan asamu a basu magungunan mayu da kambun baka saboda rigakafi" Baffa dai bai ce komai ba, Ummah kuma ta sunkuyar da kanta tana share hawayenta dan gudun kar Baffa ya gani ransa ya kara baci.

Daga zuwa wanka sai da nayi wata hudu a duniya kafin mu dawo gida. Inna ta gaya min cewa a cikin watanni hudun nan duk juma'a sai Baffa ya saka Ummah ta shirya ita da Sadauki sun taho dan su ganni amma ko da sau daya ba'a taba barinsu sun wuce ko da gate din gidan ba. Kuma ko sau daya bata taba gaya wa Baffa cewa ba a barinsu su shiga ba. Sai ranar nan ya dawo daga garage dinsa ya samu Sadauki yana ta kuka shi wajen kanwarsa zaije sai Baffa ya tambaye shi "ba jiya kaje ka ganta ba?" Sadauki ya girgiza kai yace "ai ba'a barmu mun shiga ba, kullum in munje koro mu ake yi ace Alhaji Babba yace kar a barmu mu shiga" to jin haka ne fa sai Baffa ya tafi gidan Alhaji Babba ya samu uwargidansa Hajiya Babba yace "wannan idan auren kuke da niyyar rabawa sai ku fada min in aiko mata takardarta, idan kuma kuna son acigaba da auren to lallai a mayar min da iyalina gidana" jin haka yasa Inna babu shiri ta fara harhada mana kayan mu dan tasan halin Baffa.

Yadda tsarin gidan mu yake shine, ta garage ake shigowa daga nan sai dan karamin fili mai bishiyar umbrella da flowers a sides, sai bandaki a gurin. Daga nan zaka shiga karamar kofa zuwa tsakar gida. A tsakar gida kana shiga kofar palon Inna ne a farko, babbab palo ne da dakuna guda biyu suna facing juna. Dakin Baffa kofar sa tana kallon palon Inna, an yi stairs a kofar dakin Baffa da niyyar yin dakuna a saman dakunan sa, amma kuma ba'a samu damar karasawa ba. Dakunan umma kuma suna daga can ciki saboda daga baya aka sayi fili akayi su aka shigo dasu, suma kuma exactly tsarin na Inna ne. Sai kitchen da toilet a tsakar gida.

Ina so ka fahimci wani abu guda daya. Allah ya dorawa Ummah sona kamar yadda take son mahaifina, soyayya ta gaskiya marar algus a ciki. Tun da muka koma gida sai ya zamana koda yaushe ina gurinta, in dai har Inna zata ajiyeni to kuwa Ummah zata daukeni in ina hannun Inna ne dai ba zata iya cewa ta bata ni ba. Wannan yasa sau da yawa Inna ko aiki zatayi sai ta goya ni tace "bazan ajiyeki ba kar waccan mayyar ta dauka". Hausawa su kance mai da wawa, amma wannan baiyi aiki akan Inna ba, ita idonta ya rufe akan kishin Zainabu.

Sadauki har dakin Inna yake biyo ni, Inna ta kore shi amma yaki tafiya in ta hankada shi sai ya zauna a bakin kofa yayi ta kuka shi a bashi Diyam dinsa. Ni kuma tunsanda na fara gane mutane babu wanda nake murnar ganinsa irin Sadauki. Dana fara rarrafe kuwa daga na tashi zan tsallake Inna tana bacci in tafi dakin Ummah ita kuma ta dauke ni ta bani abinci tayi min wanka da kwalliya ta gyara min dogon gashina ta goya ni, Ummah har kaya tasiya min ta ajiye a dakinta saboda in tayi min wanka ta saka min tunda Inna ba zata bata ba. Ummah macece mai tsafta sosai da kwalliya.
Lokacin dana fara magana kalmar dana fara iyawa itace "Sadauki", sadauki ya bani labarin cewa ban ma iya fadi sosai ba dan "sholoki" nake cewa, shi kuma sai ya sakani a gaba yayi da dora min kamar karatu, "ki ce Sadauki" ni kuma sai ince "Sholoki" a haka a haka har na iya, ranar dana fadi sunansa dai dai yaje ya dauko bankinsa da yake taron kudi a kasan gadon Ummah ya fasa ya tafi bakin asibitin Murtala ya sayo min yar tsanar roba ya kawo min a matsayin gift. Na karba ina murna, yace "to wanne suna zaki saka mata?" Nace "Shubeya" (Subay'a) sunan wata jaririya da aka haifa a makotanmu a lokacin. Tun daga ranar kullum ina rike da shubeya ta, hatta bacci tare da ita nake yi har nayi wayo.

Akwai ranar da bazan manta ba duk da kankantata. Ina wasa da Shubeya a tsakar gida Ummah kuma tana wanki Inna tana kitchen tana girki. Wata yarinyar makota ta shigo tace min "Diyam wai babyn waye wannan?" Ta nuna Shubeya, nace "yata ce, yata ce ni da mijina Sadauki". Ai kuwa sai ga Inna da saurinta ta fito daga kitchen tace min "me kika ce Diyam?" Na sake maimaita mata tunda ni a lokacin bansan ma ma'anar kalmar miji ba, nan take inna ta ciro bulala a bishiyar tsakar gidan mu ta daga skirt dina ta ringa tsula min a kafafuwana ina ihu tana cewa "zaki kara cewa Sadauki mijinki?" Ummah ta ajiye wankin hannunta ta rugo da gudu takwace ni daga hannun Inna ta shige dani dakinta ta rufe kofa. Inna ta ringa bugun kofar amma taki budewa sai ma dauka na da tayi ta kaini toilet ta wanke min kafafuna da suka tashi suka yi rudu rudu, ta shafa min vaseline ta kwantar dani akan gadonta tare da Shubeya ta.

A waje kuma bayan Inna ta gaji da bugun kofa sai ta dauki waya ta kira gidan Alhaji Babba cewa ga Ummah nan ta dauke ni ta shige dani daki ta rufe kofa ita bata san me take yi min ba. Nan da nan sai ga gwoggona da nake cewa Aunty Fatima wadda akayi dace taje gidan a lokacin, da Adda Zubaida babbar 'yar Alhaji babba wadda a lokacin take zawarci, da wadansu da suke yammata a lokacin suka zo gidan mu suka yi ta bugun kofar Ummah, ai kuwa tana budewa suka rufe ta da duka Inna kuma ta shige ciki ta dauko ni tana duba lafiya ta, a lokacin Baffa ya shigo rike da hannun Sadauki daya dauko daga makaranta, yana shigowa yaga abinda ya faru ya nemi ba'asi kowa ya bashi side din story dinsa, a take zuciya ta ciyo shi ya rubuta wa Inna takarda saki daya, ya kuma karbe ni daga hannun ta ya mika wa Ummah ni.

Wannan yana daya daga cikin abubuwan da har yau Inna ta kasa mantawa a rayuwar gidan mu. A lokacin sai da Hardo da kansa yazo har kano ya sasanta maganar sannan Baffa ya mayar da ita amma da sharadin kar wanda ya kuma daga hannu ya dakar masa mata. Bayan wannan Inna ta rage tsangwamar Ummah sosai sai dai ba za'a taba kiran zamansu da zaman lafiya ba.

Shekara ta biyar a duniya Inna ta haifi kanwata, Asma'u, tun daga nan kuma shikenan babu wata haihuwar. Sadauki bashi da kokari a makaranta, dan yana daga yan karshe karshe a position a ajinsu, amma kuma Allah ya bashi fasaha a kan kere-ƙere. Wannan yasa kullum daga ya dawo daga school zai shirya yabi Baffa zuwa gareji, kafin wani lokaci Sadauki yasan kan mota sosai dan zai iya kunce inji ya mayar ya hada, duk minor gyaran da aka kawo wa Baffa sadauki ne yake yi kuma ya gyaru sosai. Ina iya tuna lokacin da Baffa yake cewa "Sadauki da ace ni mai kudi ne da kasar waje zan kaika kayi karatu, tunda karatun kasarmu duk theory ne kai kuma kafi gane practical".

Ranar nan ya dawo daga makaranta na tafi da guduna na rungume shi ina masa oyoyo, ya ciro alawar da ya siyo min da kudin taran sa, wadda yasan in dai ya shigo babu ita to sai nayi masa rigima, na karba nace "Nagode Sadauki" ya kamo kunnena yace "daga yau hamma Sadauki suna na" na gyada kai ina murza kunnen da yaja, Ummah ta harare shi tace "sai son girma kamar gwambo, ga kuma mugunta" ni dai na wuce dakin Inna da sauri na kai mata sweet din nace ta bude min. Ta karba tana tambayata "waye ya baki?" Nace "hamma Sadauki ne" ta kamo kunnena da sauri tana daga muryarta yadda Ummah zata ji daga waje tace "hamma wa? A gidan uban wa ya zama hammanki? Babu hadin danga da garafuni kar in kara jin kince masa hamma" na saka kuka saboda zafin da kunnen yake min nace "na daina Inna" ta sake ni na fita da gudu gurin Ummah ina share hawaye na, ta dauke ni ta dora akan cinyarta ta bude min alawar tana rarrashina. Daga ranar ban kuma cewa Sadauki hamma ba shima kuma bai kuma cewa in gaya masa ba

Shekarar da aka saka ni primary Sadauki ya shiga secondary, dan haka a lokacin Baffa ya siya masa keke yake zuwa akai. Ni kuma Baffa ne da kansa yake kaini a motarsa tunda makarantar mu babu nisa kafin ya fita amma ranar nan sai na saka rigima nace ni a keken Sadauki zan ke tafiya, nan take Sadauki yace "Baffa ka barta, kaga hanya daya ne sai in ajiyeta in an taso kuma in biya in dauke ta" Inna tace "kaji mugunta, salon kake kayar da ita a hanya kullum? In banda mugunta ga motar ubanta sai ace ta hau keke? To ba zata hau din ba" na makale kafafa ina kakalo hawaye, Baffa ya tsaya yana kallon Inna saboda yaji zafin maganar ta amma saboda muna gurin sai kawai yace "bishi ku tafi, Allah ya kiyaye hanya" Ummah tace "ka bi a hankali, kar kaje kana wannan rawar kan naka ka jefa ta a kwata" ni kuwa sai tsalle da murna, ya dora ni a gaban sa ya saka na rike kan keken sannan ya taka keken muka tafi. Muna barin layin mu na saki kan keken na fara kokarin mikewa tsaye, ya rike ni da hannu daya yace "ki zauna Diyam, zaki fadi fa" na ture hannunsa "ka tsaya kaga abinda zamuyi, irin na titanic, nice rose kaine jack" na mike na bubbude hannayena, ai kuwa kafin yayi managa na zame zan fadi, garin rikeni shima ya biyo ni sai gamu a kasa a kan kwalta, guiwowina duk sun daddauje goshina ma haka. Na dage kuwa tun karfina na ringa zunduma ihu, yayi rarrashin duniyar nan naki inyi shiru, haka ya dauko ni da hannu daya ya jawo keken da daya hannun muka taho gida.

A bakin gate muka tarar da Baffa yana shirin fita. Yana ganin mu ya taho da saurin sa ya karbe ni a hannun Sadauki ya dora ni a saman mota yana duba ciwon da naji. Tun kafin Sadauki ya bada labarin abin da ya faru sai ga Inna ta jiyo kuka na ta fito da sauri tana cewa "ai dama sai da na fada, yaron nan babu komai a zuciyarsa sai zallah mugunta, gashi nan yaje ya jefar min da yarinyar ya cuce ni" Baffa ya juya kanta shima da nasa fadan sukayi tayi, basu san sanda Ummah ta fito ta dauke ni ta wankemin ciwon da naji ba ta chanza min kaya sai ji sukayi tace "baban Diyam ko zaka kaita chemist a duba ciwon sosai?" Baffa ya juyo yana kallonta yace "Allah yayi miki albarka Zainab" tayi murmushi tace "ameen, Nagode". Sannan ta cewa Sadauki "kaima sai ka bisu a duba hannunka" sai a lokacin duk muka lura cewa shima yaji ciwo a hannunsa yana ta jini, yayi saurin nuna jarumta ta hanyar cewa "babu komai" amma Baffa ya tilasta masa sai da ya bimu.

Na jima da wannan tabon a goshina, duk wanda ya tambaye ni sai ince "Sadauki ne ya kayar dani a keke".

Writing......
[1/10, 9:56 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Twelve: My Brother, My Friend.

"Diyam, ba zaki cigaba da cin abincin nan ba sai nazo ko?" Na daga kai ina kallon Inna da take zazzare min ido cike da barazana. Na debi shinkafa a chokali na kai bakina ina taunata da kyar saboda koshin da cikina yayi ji nake kamar zanyi amai. Na shawabe fuska "Inna wallahi na koshi, nasha tea, naci bread, naci kwai, bazan iya cin shinkafa ba kuma amai zanyi" tace "kiyi aman, sai ki zo ki cigaba da ci" na kalli kofa da sauri saboda motsin mutum dana gani, ta gefen labule na hango Sadauki sanye da uniform dinsa, muna hada ido yayi min alamar in taho da hannunsa, na ture abincin na sunkuci jakata zan fita Inna ta fizgoni ta dangwarar akan kujera tace "in kika fita daga dakin nan sai na yanke kafafuwanki" ta harari kofa tace "bakin munafuki, babu inda zakuje tare" ta kara dangwara min kwanon shinkafa a cinyata.

Muryar Baffa na jiyo a tsakar gida "kai kai kai, Sadauki wai baku tafi ba har yanzu? Ai kun makara, ina Diyam din?" Nayi saurin ajiye kwanon amma hararar da Inna ta jeho min yasa na dauka na cigaba da rikewa. Baffa ya leko yace "ke Diyam, ki fito ku tafi mana kin makarar dashi zaki sa a dake shi" Inna tayi charaf tace "ya tafi kawai kar a hukunta shi a makarantar su. Diyam bata gama karyawa ba" na ajiye kwanon nace "na gama Baffa, tun dazu na gama Inna ce ta hanani fitowa" na zagaya ta gefenta na fice daga dakin da sauri na rungume sadauki shi kuma ya dauke ni ya dora akan kekensa muka tafi.

Haka mukayi ta fama kullum ba fashi, kullum sai inna tayi ƙoƙarin hanani bin Sadauki ni kuma sai na nace na bishi. Shi zai kaini har class dinmu yaga na shiga sannan ya tafi tasa makarantar. A lokacin dana kara girma kuma sai ya daina dorani a keken sai dai mu tafi a kafa yana jan kekensa a hannu har sai ya kaini sannan shi kuma ya hau ya tafi tasa. Haka islamiyya ma tare za muje, in asma'u ta biyo ni sai in korata ince tabi yaran makotanmu. Sadauki shine yayana, shine abokina, shine kawata, shine abokin shawarata, duk da cewa a lokacin akwai yarinta sosai dan haka duk shawarar ta shirme ce, shima kuma tunda ba wani girmata yayi sosai ba haka zai bani amsar shiririta.

Duk kawayena, na boko dana islamiyya sun san Sadauki, wadda bata sanshi a fuska ba kuwa to tabbas tasan sunansa saboda da wahala in muna hira in iya hada sentence guda ba tare da sunan sadauki ya fito a ciki ba. Duk kuwa sanda wani a ajin mu ko ajin gaba damu yaci zalina ko na tsokani wani ya dake ni to tabbas sai jikinsa ya gaya masa in ya shiga hannun Sadauki, wannan yasa ake shayin tabani ko a yaran unguwa sai dai in na tsokani yaro yayi hakuri dan dole dan sun san cewa sadauki ƙashi daya ne dashi.

Bashi da surutu sam, he is a good listener rather than a talker, ko a gida in dai kaji yana hira to dani ne, ko da Baffa, amma ko Ummah basu cika zama suyi doguwar hira ba. Yana da zuciya da fada in an taba shi ko an taba ni, amma ni din ko daga min murya baya iyayi balle yayi min fada. Kuma duk zuciyar Sadauki, bai taba daga kai ya kalli Inna in tana gayawa Ummah magana ba, sai dai ka gani a fuskarsa cewa ransa ya baci amma ba zai mayar mata ba. Yana da kazar kazar sosai kuma baya zama guri daya, in har baya makaranta to yana gareji in kuma baya can to yana gida yana aiyuka, zai share gidan mu tas ya gyara wa Baffa dakinsa ya wanke masa mota. Watarana nace masa "Sadauki kai baka gajiya ne? Ka kwanta ka huta mana" Sai yace "wa kika taba gani yayi achieving wani abu a kwance? In kana son wani abu you have to work hard to earn it".

Ranar nan, a lokacin ina primary 5, ina da shekaru goma da yan watanni sadauki kuma yana sha shida. Anti Hafsa, wadda muke kira da Mama tazo gidan mu, suna ta hira da Inna ni kuma ina kwance sun dauka bacci nake yi naji Mama tace "ni Addah kullum sai inga kamar kara ramewa kike yi, har yanzu kin ƙi ki kwantar da hankalinki kiyi ƙiba kema" Inna tace "hmmm Hafsa ina hankalina zai kwanta ne bayan wannan mayyar ta sakani a gaba, ita da wannan baƙin dan nata sun hana zuciyata hutawa sam" Mama tayi dariya tana riƙe baki tace "kai Addah, daga ni har ke fa mun sani cewa bafa mayyar bace da gaske, muna sane muke takewa kawai dan mu bata mata rai amma da mayyar ce da ba tini ta cinye ki ba ko ta cinye yayanki? musamman tunda ita bata haihu anan gidan ba?" Inna tace "to ai yanzu gashi danta ya chinye kurwar Diyam ko? kamar yadda ita kuma ta chinye ta baban Diyam, na rasa yadda zanyi da yarinyar nan, nayi fadan nayi nasihar nayi dukan amma abun ya faskara, gashi da shegen naci kamar jinin mayu, bana son mu'amalar yarinyar nan da yaron nan wallahi kullum gani nake kamar zai cutar da ita, kullum in suna tare sai inyi ta fargaba" Mama ta sake dariya tace "bafa mayen bane kin sani kuma. Yara ne, ki barsu suyi wasansu mana, ki kwantar da hankalinki kiyi tayi mata addu'a" Inna tace "idan ba maye bane ta bangaren uwarsa waye yasan waye shi ta bangaren ubansa? Ni fa tunda matar nan tazo gidan nan da yaron nan ban taba jin ko da sau daya ta ambaci mahaifinsa ko wani dangin mahaifinsa ba, ban taba ganin an kaishi dangin ubansa hutu ba. Ni ba dan makota sun tabbatar mun an daura mata aure anan bayan layi ba da sai ince anya ba shege bane ba? To ko ma dai ba shegen bane ba akwai wani mummunan abun da suke boyewa a game da mahaifinsa. Shi kuma babansu ko na tambayeshi cewa yake ina ruwana? Wai ai Allah ma ya hana mutum ya shiga abinda babu ruwansa" Mama tace "to yanzu menene abin yi?" Inna tace "yanzu ni dai so nake ki tambayi baban Diyam tunda wannan satin zasuyi hutu dan Allah ya baki ita da Asma'u duk ki tafi dasu gurin ki suyi hutunsu a can kona samu zuciya ta ta huta kafin su dawo". Mama tace "au yanzu akan agolan kike so ki raba yara da gidan ubansu? To Allah ya sa ya bani din dan kinsan halin mijin naki ba wanda yake gane kansa sai zainabu abu, Allah yasa ma kar yace sai dai in hada har sadaukin in tafi dasu tare" ta fada tana tsokanar Inna, Inna tace "Allah ya kiyaye. Allah ya tsari gatari da saran shuka. Insha Allah ko kofar gidanki ba zai sani ba ballantana ya ga ciki". Ni dai ina kwance ina jinsu, amma sai naji duk raina ya baci saboda babu abinda na tsana irin a kaini wani gidan, saboda bana so a raba ni da Sadauki.

Bayan ta tafi da daddare ina dakin Ummah muna cin abinci a plate daya dani da ita da sadauki. Tana ta loda min nama a gabana wai inci inyi girma in kamo Sadauki. Shi kuma yana ta min dariyar yadda na dage bil hakki nake cin abinci wai kamo shi zanyi duk kuwa da cewa a lokacin ya kusan yin biyu na a girma tunda ni bani da garun jiki shi kuma girma ne dashi. Nace da Ummah "Ummah menene agola?" Tayi shiru tana kallona bata ce komai ba, na cigaba "Inna naji ita da Mama suna cewa wai Sadauki agola ne, sannan kuma maye ne" Inna ta ajiye chokalin hannunta, Sadauki ya kamo hannuna yace "Diyam, agola shine yaron da aka haifa sai iyayensa suka rabu sai uwarsa tayi wani auren ta tafi dashi, mijinta kuma ya rike shi kamar dansa. Kamar ni kenan yadda Baffa ya rike ni amma ba shine ya haife ni ba" nace "to kuma da gaske kai maye ne?" yayi dariya yace "sosai ma kuwa. Yanzu ma sai in cinye ki" ya fada yana yi min chakulkuli ni kuma ina kyalkyala dariya nace "wayyo na tuba kar ka chinye ni" hararar da Ummah ta zabga masa ne yasa ya sakeni muna cigaba da dariyar mu sannan Ummah ta kalle ni seriously tace "Diyam, idan kinji innar ki tana hira da wani, ko cikin yan uwanku ko

Please Login or Register in order to submit comment