Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na gyada kaina. Sai kuma ta tambaye mu in mun yafewa Alhaji Babba, nace "ni dama ai ni yace yayi wa kaya da kudin, to in ma ina da ciko na bar masa, wanda ya tara dukiyar ma ya tafi ya barta" Asma'u tace "ni kam in dai har hamma Sadauki zai iya karbar kudin nan to ina son kaso na. Shi da bai taimaka min da komai ba ni ba zan bar masa hakkina ba" na harare ta sai ta daga kafada tace "Inna tace kowa ya fadi ra'ayin sa".

Da daddare tare muka kwana gabaki daya a kan gado daya muna ta hira, Asma'u sai labarin motar Sadauki take yi min "wallahi ban taba ganin mota mai kyau da dadin wannan motar ba. Kai Adda ina ma dai shi kika aura da yanzu a wannan motar za'a ke kaiki unguwa kin huta da dan sahu. Nima in naje gidanki a irinta za'ake kawo ni gida" nayi juyi nace "Asma'u dan Allah ki rabu dani, bashi na aura ba chapter closed" sai kuma nace "motoci fa yake siyarwa. Dole ya hau mota me kyau".

Washegari na shirya, na bar Subay'a anan gidan na tafi gidan Alhaji Babba. Direct part dinsa na tafi tunda yanzu ba sai anyi wa mutum iso ba. Na same shi a zaune yana lazimi, sai da ya shafa sannan ya tambaye ni "Diyam kin same shi? Me yace? Jibi ne fa zamu fara zuwa court" nace "na same shi Alhaji" sai kuma na lissafa masa abinda yace. Ya kama salati, amma wannan yaro anyi asarar haihuwa, yanzu ni tsofai tsofai dani zaice in je in durkusa a gabansa? Sakayyar da zai yiwa rikon da Usman yayi masa kenan? Gwara da Allah yasa bamu bashi aurenki ba Diyam da yanzu da surikin mu zamu shiga Shari'a" ni dai nayi masa sallama na fita ina jinsa yana cigaba da maganganu shi kadai.

A cikin gidan ne zuciyata ta karye. Hajiya Babba ita kanta a jigace take dan yan uwanta sun gaji da taimaka mata. Muka gaisa tace "Diyam baku kyauta mana ba ke da Saghir, yanzu ace tafiya ta same shi amma sai bayan da yayi ta zamuji labari?" Nace "Hajiya ni wallahi bansan be fada muku ba, na dauka duk kun sani" ta girgiza kai tace "ina fa, mu Saghir sai yayi sati ban saka shi a ido na ba sai dai in na kira shi nace ina nemansa. Yanzu idan kunyi waya dan Allah kice masa ya kira ni" nace "to".

Dana shiga dakin Hajiya Yalwati ne na tarar dasu abin tausayi. Aunty amarya dama ta kara mai ta bar yaranta guda uku duk suna gurin Hajiya Yalwati ga sauran yayan da ake bari a gidan duk mata, ga kuma nata yaran dam haka wajan yara goma ne a part dinta, dan abinda manyan ƴaƴanta suke taimakawa dashi da kyar yake ciyar dasu. Ga yara uku sun isa aure sun kuma samu mazaje amma babu halin yi musu auren. Muka gaisa itama tayi min mita "yanzu Diyam shi mijinki ko shinkafa ba zai ke siyowa yana kawowa gidan nan ba?" Ni dai bance komai ba saboda bazanyi alkawarin da nasan ba zan cika ba.

Washegari Saghir ya kira wayata. Dama tunda ya tafi kullum sai ya kira sai in bawa Subay'a su gama maganganun su in kashe. Ranar sai yace ta bani zaiyi magana dani. Ina karba ya fara fada "da izinin waye kika fita kika je gidan Alhaji?" Nace "Alhajin ai shi yayi kirana ya hada ni da Allah da Annabi inje in taimaka masa" yace "ke kuma sai kika fita, saboda kina sauri za'a tura ki gurin saurayin ki ko? Ai Alhajin duk ya gaya min abinda yake faruwa, shegen yaro da bai san darajar manya ba wai har zaice zai kar Alhaji kara ya biya shi gadon uwarsa? Yanzu haka kudin wiwin da yake sha ne ya kare shi e yake neman refill" nace "amma Alhaji bai gaya maka lauyoyi ya dauka har guda uku ba? In kudin wiwi yake nema ya siya mana da kudin daya biya lawyers din dashi? In fitsari abinyi ne kaza tayi mana mu gani" yace "kar ki gaya min magana, kinsan dai dan bana gari ne da tuni zan biya shi kudin sa, ko Mr Abatcha na gayawa a take zai bani kudin in bashi" na girgiza kaina ina jinjinawa rashin sani da hausawa suka ce yafi dare duhu. Sai nace "to ko a daga shari'ar ne sai ka dawo sai ka karba a gurin Mr Abatcha ka bawa Sadauki?" Yace "to kudin ma ba Alhaji yace dasu akayi miki kayan daki ba? Ki gayawa Sadaukin haka in yaso in karar ce sai ya kai ki ke ki biya shi" sai na gaya nasa jimlar kudin, nace "ni nafi tunanin bayan kayan daki na har gidan da muke zaune a ciki da kudin aka siya, sannan aka kara jari da sauran. Dan haka dani da kai za'a gamai biyan kudi".

Da daddare lawyer din Sadauki ya kira ni, wai Sadauki yace kar muje court gobe. Inna tace ai dama babu inda zamuje. Washegari suka zauna a court. Sadauki ma baije ba kamar yadda nayi tsammani, lawyers dinsa ne kawai suka je a madadin sa. Suka gabatar da dukkan takardu da kuma dukkan shaidu da suka tabbatar da wanzuwar garejin da kuma filin, sannan suka kawo shaidun cewa an siyar, har wadanda aka siyarwa ne suka zo sukayi testifying da kansu suka kuma fadi kudin da suka siya. Alkali ya nemi Alhaji Babba daya fito da kudi shi kuma ya tabbatar cewa kudi dai babu su kuma bashi da hanyar samun su a yanzu, sai dai yana neman alfarmar a bashi lokaci yake biya a hankali har ya gama. A take lawyers din Sadauki suka gabatar wa court da shaidar cewa Alhaji Babba yana da gida mai number 43 a unguwar sharada, har da estimate na kudin gidan, dan haka suna so Alhaji Babba ya siyar da wannan gidan nasa ya biya wadannan kudade, a take alkali ya amince kuma ya bawa Alhaji Babba kayyadadden lokaci na siyar da gida shi kuma Alhaji Babba sai ya nuna cewa lokacin yayi kadan saboda sai ya samu mai siya, anyi ciniki anyi komai. A take lawyers suka ce Sadauki yace zai siya, ai kuwa alkali ya bada lokaci yace aje a daidaita a kan price.

Ana fitowa daga court kawu isa ya kira Inna ga Alhaji Babba nan hawan jini ya tashi an kaishi asibiti. Haka Inna ta saka mu a gaba muka tafi dubiya ni dai ba'a son raina ba amma dana ganshi sai naji zuciyata ta tsinke. Yana ta kuka shabe shabe da hawaye. "Yanzu ya zanyi in siyar masa da gidana? Gidan dana gina tun auren fari da gumina. In na siyar da gidana a ina zan saka iyalina kuma?" Sai naji tausayinsa,ko babu komai yayan Baffa ne shi uwa daya uba daya. Sannan ga tausayin iyalinsa ina zasu je? They are innocent. Su zan iya rantsewa basu mori ko kwandala a kudin ba.

Na fita na dauki waya ta nayi ta kiran number din Sadauki bata shiga. Ko kuma blocking dina yayi ne oho. Da daddare kawu Isa yazo gurin Inna, wannan shine zuwansa gidan mu na farko tun da su Inna suka dawo. Yace "kudi dai da za'a bawa yaron nan babu su. Dan ni kaina in nace zan fitar da kudin nan to kuwa tabbas zan kassara kasuwanci na. Gida kuma kamar yadda Alhaji ya fada in ya siyar ya kai iyalinsa ina? Dan haka third option shine a kira yaron nan a bashi hakuri, ku zakuyi mana jagora zuwa gurinsa a sasanta maganar nan as a family tunda shima ai kusan family din ne, shekarar sa ashirin a hannun dan uwan mu".

Ni aka saka in kira Sadauki. Na gaya musu ba dauka zaiyi ba amma suka ki dan haka a gabansu na kira kuma taki shiga din. Sai na tura masa text. "Third option. Kazo a baka hakurin da kake so" na tura masa. An jima kadan yayo reply "tomorrow evening. Gidan Baffa" na gayawa kawu Isa abinda yace sannan ya tafi da niyyar gobe zai zo tare da Alhaji Babba.

Washegari. Inna har dayiwa Sadauki girki tana ta gyaran gida ni dai ina kallonta kawai. Su Alhaji Babba ne suka fara zuwa, sai a lokacin ma yasan akwai yan haya a gidan mu. Suka zauna nan palo aka bawa Alhaji pillow ya dan kashingida saboda babu lfy. Sai after 5 Sadauki ya shigo gidan. Shi kadai, babu wani abu a jikinsa da zai nuna cewa shi mai kudi ne dan shirt da wando ne kawai a jikinsa ko agogo babu a hannunsa. Sai naga ya koma min wancan Sadaukin da na sani ba wai Mr Abatcha ba, kuma ganinsa a cikin gidan mu sai yayi adding to that feeling.

Yana shigowa palon muka hada ido sai ya dauke kai, fuskarsa babu walwala ko ta cikin cokali sai kawai naji gabana ya fadi. Ya gaishe da Inna ta amsa, the first time da naji Inna ta amsa gaisuwar Sadauki. Sai ya samu guri ya zauna yana kallon Alhaji Babba yace "ina jin ka," kawu Isa yace "dama cewa mukayi a kira ka muyi magana. Ayi hakuri a bar maganar nan ta wuce" sai yace "ba kai zaka bada hakurin ba ai" Alhaji Babba ya tashi daga kwanciyar da yayi ya matso gaban Sadauki yace "ka duba darajar rikon da Usman yayi maka, da kuma darajar yanuwantakar da take tsakanin mu ka bar maganar nan. In na baka gidana iyalina kuma ina zan kaisu? Ka duba halin da nake ciki na karayar arziki data same ni ka yafe min kudin nan. Banyi dai dai ba na sani, na aikata maka laifuffuka na sani, amma na hada ka da Allah kayi hakuri ka bar maganar nan" sai naji zuciyata ta karye, hawaye ya fara bin fuskata amma dana kalli Sadauki sai naga kamar da dutse ake magana. Sai ya mike tsaye yana kallon Alhaji Babba yace "na yafe maka kudin gadon Ummah. Amma kudin fili na ban yafe ba dan haka zan aiko a yankar min wani part na gidan ka a maimakon fili na, dama ina da sha'awar yin kiwon kaji sai inyi a gurin".

Na mike da sauri ina kallonsa cikin mamaki. Can his heart really be this dry? Bai jira sauran magana ba yayi hanyar waje na bishi da sauri ma sha gabansa nace "this is not you Sadauki. Ba kai bane wannan. Kai kace minzaka yafe masa in ya durkusa a gabanka ya roke ka and he did just that" ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallona yace "ni ba haka na ce miki ba. Cewa nayi in ya durkusa ya roke ni gafara in naki yi masa a lokacin ne zai fahimci irin yadda naji. So, nayi kokari ma ai, na yafe masa rabi saura rabi".

Na dafe kirjina nace "are you this heartless Sadauki?" Yana kallona with straight face yace "do you blame me? Yes, I am heartless because they took away my heart. You are my heart remember?" Sai ya juya ya fice ya barni a tsaye.
[2/15, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Four : Sweet Sixteen

Nabi bayansa da kallo ina jin kamar ya ciro tawa zuciyar ne ya tafi da ita. My chest felt empty kamar babu komai a cikinsa, ji nake kamar in bishi a baya da gudu in rungume shi kamar yadda naje yi sanda ina karama, ina son ya rungume ni nima kamar yadda ya taba yi min a gidan Alhaji Babba, but I couldn't saboda akwai wata igiya data ke rataye a wuya na, igiyar auren Saghir.

Bazan iya komawa palon ba saboda duk bana son kallon fuskokin su. Yes, Alhaji Babba ya cuce ni iyakacin karshen cuta amma kuma still yayan Baffa na ne, kuma va'a taba chanjawa tuwo suna, komai suka yi bazan taba cewa su ba iyayena bane ba. And there is wani satisfaction da ake samu a cikin forgiveness, wannan satisfaction din shi nake yi wa Sadauki kwadayin samu.

Sai na juya na tafi gurin Maman Iman duk da dai ita kuma surutu ne da ita ni kuma a lokacin bana son magana. So nake inyi shiru inyi jinyar zuciya ta. Dan haka ina zuwa sai nace mata bana jin dadi ne ina so zan kwanta, sai kuwa ta bude min dakin yaranta, dakin mu ni da Asma'u a da. Na shiga na kwanta, but sai dakin ya cigaba da dawo min da memories din da. Sadauki's memories, na sake gwada kiran wayarsa still bata shiga. Dai na kifa kaina a pillow na fara kuka. It really hurt to love someone so deep while you are married to another, another din kuma wanda ba ka so.

Sai da akayi magrib Maman Iman ta shigo ta tashe ni in yi sallah. Ayi alwala nayi sallah sannan na koma part din Inna, ina shiga na tarar sun tafi, Inna ta bini da kallo tace "kuka kikayi ko?" Na girgiza mata kai amma sai hawaye suka fito. Tace "me yasa kika masa magana dazu? Ba nace miki ki fita daga maganar ba? Tunda ke kince kin yafe shi ki barsa ya karbi abinsa. Na gaya musu nace Asma'u ma tace bata bari ba".

Ranar sunday, da safe muna shirye shiryen komawa gida ni da Subay'a kamar daga sama sai jin sallamar Sadauki nayi a tsakar gida. Na dakata da folding kayan da nake yi naji Inna tana amsa masa da yake tana tsakar gida ni ina palo, naji ya gaishe ta ta amsa tana tayi masa sannu da zuwa tace ya shigo palo, yana daga labule muka hada ido sai yayi sauri ya saki labulen ya koma yana cewa "basai na shiga ba Inna, dama zan dan shiga dakin Ummah ne" sai Inna ta kira saka mayafinta da kanta ta shiga gurin Maman iman ta gaya mata za'a wuce, saboda sai an bi ta nan za'a karasa dakin Ummah. Subay'a dake kusa dani ta tashi ta leka tsakar gida, sai naji yace mata "Subis, come here" sai ta makale a bayan kofa taki fita, yace "ba zaki zo ba? Dan kin ganni baki babanki kuma fari ko?" Sai inna ta dawo ta tarar dasu tayi dariya tace "Subay'a kizo ki gaishe da babanki mana?" Subay'a ta tura baki tace "ba baba na bane ba" inna tace "ji fitsararriya?" Yayi dariya yace "gado tayi ai" sai Asma'u ta shigo, tana ganinsa ta kama murna tana gaishe shi, yace "yar asama yammata" a raina nace "wato yana iya yiwa kowa magana faran faran, ni ce dai na koma aljana a gurin sa".

Asma'u ce ta raka shi ya bude dakin Ummah ya shiga, sannan ta dawo. Inna ta shigo tana kallona tace "kina jin Sadauki ba zaki fita ki gaishe shi ba?" Nace "baya son ganina inna. ganina a dakin ne fa yasa ya fasa shigowa". Inna tayi shiru kawai bata ce min komai ba ni kuwa zafin da nake ji a raina yasa na dauki kayan na koma cikin daki, amma sai na kasa cigaba da gyarawa na kwanta kawai. Ina kwancen ya dawo, ya leko yayi wa Inna sallama sai ta ce yazo tana son magana dashi. Ya shigo palon ya zauna tace "Sadauki. Ni dai kam bansan wanne kalamai wanda yayi laifi irin wanda nayi maka zai yi amfani dashi gurin rokon gafarar wanda yayi wa lafin ba. Na cutar da kai Sadauki iyakacin cutarwa kuma duk a bisa son zuciyata ba wai dan kayi min wani laifi ba. Amma a karshe sai ya kasance ni din dai nice a wahale. In kace ma ba zaka yafe min ba Sadauki bazan ji haushi ba saboda na cancanci koma menene zakayi min. Amma abinda na sani shine nayi nadama, Sadauki dan Allah...." Sai ya dakatar da ita yace "Inna na yafe miki ai, da ban yafe miki ba Inna ba zaki ganni a dakin nan ba. Maganar ta wuce tsakanin mu har abada" sai Inna ta kama yi masa godiya, har ya sake mikewa zai fita sai ta kira Asma'u, sai kawai zuciyata ta raya min in leka su, naje ta jikin labule ina lekawa sai naga ta kamo hannun Asma'u ta saka a cikin na Sadauki tace

"na hana ka auren Diyam a lokacin da kiyayyar ka ta rufe min ido, amma yanzu ga Asma'u na baka, duk abinda yayi Diyam shi yayi Asma'u har kamanninsu iri daya ne, ina fatan zaka karba kuma wannan zai wanke maka zuciyarka"

Na juya ina dafe kirjina kamar mai kokarin gana zuciyata fadowa kasa. Idanuwana kamar zasu baro mazauninsu ina girgiza kaina a hankali ina cewa "no, no, no" amma sai naga Sadauki yayi murmushi, sai ya cire hannun Asma'u daga nasa ya mayar wa da inna yace "Inna na gode da wannan babbar kyauta da kika yi min, kuma da gaske wannan kyautar ta wanke min zuciyata sosai amma kiyi hakuri bazan iya karba ba. Zuciyata Diyam take so ba kamannin Diyam ko asalinta ba, in na karbi Asma'u banyi mata adalci ba saboda zan tilasta mata zama dani alhalin zuciyata bata tare da ita. Kiyi hakuri idan ban kyauta miki ba amma hakan shine zaifi mana alkhairi a gani na".

Na saki labulen na zauna a gurin ina juya lamarin a kaina. He refused Asma'u, sweet teenage Asma'u, yana claiming that his heart belongs to me, how can that be? Bayan ni kuma I belong to someone else?

Sai yamma muka koma gida, daga nan kuma muka cigaba da lonely rayuwar mu nida Subay'a. Duk da ina kokarin ganin na rage tunanin Sadauki amma kullum tamkar kara min shi akeyi.

Two weeks after that akazo aka raba gidan Alhaji Babba. Aka ja katanga tun daga part dinsa har zuwa bakin gate, sai ya kasance part din nasa da filin compound din dayake gaban part din har zuwa dakin maigadi da gate din gidan duk na sadauki ne. Main house din kuma da sauran abinda ya rage na compound shi kuma na Alhaji Babba, amma ko gate basu dashi dan haka sai katanga suka fasa ake shiga gidan, ko kudin da za'a sayi kofa a saka babu.

Ba'ayi sati dayin haka ba dakunan Alhaji Babba suka zama dakunan kaji, Sadauki ya cika katon palon Alhaji da kuma two bedrooms dinsa da kajin gidan gona, broilers da layers. Compound din kuma akayi katuwar rumfa aka zuba raguna da tinkiyoyi, dakin maigadi kuma ya saka masu kular masa dasu.

Alhaji Babba kuma ya koma cikin gida, dakin da Inna ta zauna nan ya dawo da zama. Washegarin da aka zuba dabbobin da sassafe murja ta kira ni "Diyam wallahi yau bamuyi bacci ba a gidan nan. Yadda muka ga rana haka muka ga dare wallahi, ragunan nan tun magrib suka fara koke koke har garin Allah ya waye sannan kuma kaji suka dauki nasu suma. Ni dai gidan ki zan taho in taya ki zama kafin hamma ya dawo ya kore ni" nace ta taho babu komai. Sai kuma naji babu dadi a raina. Murya, Hajiya Yalwati da sauran yayan Alhaji Babba basuyi wa Sadauki komai ba amma har dasu ake paying. Isn't Sadauki taking this too far? Bayan gudun daukan alhakin wanda baiji ba bai kuma gani ba?

Da dare Sadauki yaje gidan mu. Ya gaishe da Inna sai yace da Asma'u. "Yar Asama kina son gidan gona?" Tace "gidan gona kuma hamma?" Sai ya ajiye mata takardu yace "gashi nan na baki kyauta. Duk karshen wata za'ake kayo miki kudin da aka samu a ciki" Asma'u sai murna da tsalle, yayinda Inna ta saki baki ta kasa magana.

Yana tafiya Asma'u ta kira ni tana son bani labari amma maganar ta kasa fitowa dan murna. Nace "kinga ki nutsu ki fada min, me ya faru?" Tace "hamma Sadauki ya bani kyautar gidan gonar sa da yayi a gidan Alhaji Babba" cikin mamaki nace "what?" Sai ta mikawa Inna tayi min confirming maganar. Har da sunan ta da komai a jikin takardun.

Na kira shi da niyyar yi masa godiya amma shiru wayar bata shiga kamar kullum. Nayi tsaki na yar da wayar feeling very frustrated sai kuma na dawo na sake dauka na tura masa message "ina yiwa Asma'u godiyar kyautar da aka yi mata. Allah ya kara arziki mai albarka" na tura sannan na zauna rike da wayar a hannu ina jiran reply. Can sai gashi ya shigo. Three words

"You are welcome".

Nayi tsaki ina jin haushin sa, amma bansan dalilin da yasa nake jin haushin nasa ba.

Bayawa ko? Sorry, busy weekend
[2/16, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Five: Fauziyya

Murja tazo gidan muka zauna tare da ita, da yake ta gama makaranta kuma tun tuni ana ta zaune gida ba'a cigaba da karatu ba, ita tafi son tayi aure ma. Tace "wallahi Diyam na gaji, na gaji da zaman gidan nan wallahi. Gafa samarin nan ina dasu, kuma duk wanda nacewa ya turo a cikin su wallahi fitowa zaiyi amma Alhaji shiru har yanzu yaki yace wani abu, kuma maganar sa daya wai wasu kudi yake jira su zo kuma duk munsan babu wasu kudin da zasu zo fa. Ni so nake in bawa umman mu shawara duk ace da samarin mu su fito, in yaso kowa kudin auren ta da kuma kudin sadakin ta sai a hada ayi mata kayan daki yadda ya sawwaka kawai. Ai ba sai an kashe mana kudi ba mu auren mu ke so kawai" na jinjina maganar nace "amma biki fa? Gara fa?" Tace "wannan kuma mijin ki zaki yiwa magana dan Allah ya rage matsolancin sa yayi mana. Kudin yadin da yake sawa a jikin sa kadai ya isa ayi abincin biki da shi" nayi dariya nace "kai murja, hadda sharri kuma?" Tace "wallahi ba sharri bane ba kayan da yake sakawa ko sanda Alhaji yana da kudi baya saka irin su. Amma ya bar alhajin da yar shara".

Sanda Saghir yaji labarin abinda Sadauki yayi a gidan su ya kira ni ya zazzage min bala'i. Bance masa komai ba har ya gama sannan nace "ni dai bani na kar zomon ba, ni ratayar ma ba'a bani ba, ka bari in ka dawo sai kaje ka neme shi kayi masa masifar, but I doubt in zaka samu ganin sa dan kasan manyan mutane ba kowa suke bari ya gansu ba" ina fadar haka na kashe, yayi ta kira naki dauka dan nasan cigaba zamuyi daga inda muka tsaya.

Tun ana gobe zai dawo yakira yagaya min "ke yanzu ko dan I miss You din nan ma baki iya gayawa mijin ki ba. Kinga ni kuma har da tsaraba na siyo miki. Ina fatan dai kin tana de ni saboda da kishin ruwan ki zan dawo" sai naji ma abin ya bani dariya nace "duk wanda ka gama samu anan bai ishe ka ba? Mai zakayi da yar mitsitsiyar Diyam?" Bai musa ba yace "naki special ne. Da gaske nayi missing dinki fa" sai na kashe kawai. A raina ina jin inama yayi zamansa a can kar ya dawo?

Banyi niyyar yi masa komai na dawowa ba amma dai sai na daure nayi masa girki, wainar shinkafa na miyar taushe da taji tantakwashi. Na hada masa lemom kankana. Sanda zasu taso ya kira wai zai turo friend dinsa ya kaimu airport ni da Subay'a mu taro shi, nace ni aiki nake yi sai dai suje da Subay'a. Na shirya ta kuwa suka tafi, nima nayi wanka na shafa mai kamar kullum na saka normal kayana na gida nayi kwanciya ta a kan gado.

Ina jinsu suka zo, kawai naji wani bacin rai ya sauko min nayi tsaki na gyara kwanciya ta. An jima kadan Subay'a ta shigo tana ta tsalle. Mommy ki zo Daddy ya dawo, ya siyo min kaya da jirgi da mota" nace "kice kin gode, sannan kice masa ga abinci nan a dining" ta fita na koma nayi kwanciya ta. Sai gasu nan sun dawo tare, na tashi zaune ina kallonsa shima yana kallona, ya kara fari har da kumatu yayi alamar ya huta sosai, yace "shikenan? Babu oyoyo mijin ki yayi tafiya for two months amma ko dan welcome back hug ba zai samu ba?" Nace

Please Login or Register in order to submit comment