Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

monitan aji uku. Ya jinjina kai yace "to me yasa da akayi haka baki zo kin gaya min ko kumako gayawa innarki ta gaya min in yaso ni sai inje makarantar in basu hakuri shi kuma Sadauki inyi masa fada ba?" Na sunkuyar da kaina ina wasa da hannuna ina tambayar kaina me yasa? Ni da abin ya faru ma it never occurred to me cewa in gaya wa inna, in na gaya mata gani nake fada zata yi min ko kuma ma ta dake ni, besides, bana so ayi wa Sadauki fada akan me yasa ya daki wancan yaron.

Yace "to Sadauki ne yace kike buya a sama?" Na gyada kaina, yace "kuma sai shima yake zuwa kuke zama tare a saman?" Na kuma cewa "eh" yace "to me kuke yi a saman?" Nace "games muke yi" yace "wanne irin game?" Nace "ko chess ko lido ko whot ko kuma...." Sai kuma nayi shiru, Yace "ko kuma me? Kinsan dai kinyi min alkawarin zaki gaya min gaskiya ko?" Nace "ko kuma muyi ta labari" yace "wanne irin labari?" Nace "ko ya bani labarin gareji ko makarantar su nima sai in bashi labarin makarantar mu da kawayena" yayi shiru yana jinjina kai sannan yace "to yanzu ina dankalinki da hijab dinki?" Na nuna sama da hannuna, yace "ya akayi kika cire su?" Nace "hijabin cirewa nayi dan kar yayi squeezing, dankwalin kuma bansan ya zame ba" yace "to me yasa kika sauko da gudu dazu, fada kukayi?" Na girgiza kaina sai kuma nayi murmushi ina tuno kalaman sadauki, Baffa ya sake maimaita tambayarsa yana nazarina, nace "na fada mukayi ba, kunyarsa nake ji shine na rufe idona shi kuma yace sai na bude masa yagani" Baffa ya dan bata fuska yace "me yasa kike jin kunyarsa?" Na dan rufe fuskata alamar kunya Nace "cewa yayi I am the only star in his sky" Baffa ya bude baki da mamaki yace "shi Sadaukin?" Na gyada kaina ina murmushi. Ya jima yana kallona sannan yace "to sai wanne wasan kuma kukeyi a saman?" Innocently na daga hannuna nace "shikenan" ya kuma yin shiru yana kallon na, sai kuma ya gyada kai yace "to yanzu kingakinyi wa innarki dani baffan ki laifi, an tura ki islamiyya kinki zuwa, me zaki ce mana?" Na durkusa a gabansa nace "Baffa kayi hakuri" ya kama hannuna yace "na hakura, saura Inna".

A zaune muka sameta, idonta akan tv amma daga gani ba kallon take yi ba, hallonta daya akan Asma'u tana shafa kanta a hankali ita kuma tana bacci. Na rakube daga bakin kofa ina kallonta, Baffa yaje ya zauna akan kujerar da take kusa da ita sannan ya kirawo ni da hannu yace "me kika cewa innarki?" Na durkusa nace "Inna kiyi hakuri, na tuba, bazan kara buya ba inkin kuma tura ni islamiyya" ta watsa min harara tace "kuma ba zaki kara kula Sadauki ba?" Na sunkuyar da kaina nayi shiru. Baffa yace "tashi ki tafi dakin ku ki kwanta" na tashi babu musu na shiga na kwanta, sai kawai naji ina tunanin koya Sadauki yake ji a jikinsa? Dan nasan ba karamin dokuwa yayi a gurin Inna ba.

A palo bayan na wuce Inna tace "shikenan? Shikenan maganar nan ta wuce? Shikenan ba zaka dauki mataki akan yaron nan da yake neman ya lalata maka yarinya ba?" Baffa yace "nayi magana da Diyam, abinda kike tunani ba haka bane ba. Tabbas shi ya hanata zuwa makaranta saboda wai ance za'a dake ta in taje akan laifin da shine ya aikata ba ita ba. Tabbas Sadauki yayi laifi kuma zan zauna inyi magana dashi kamar yadda nayi da Diyam. Zan fahimci inda yake da kuskure in nusar dashi, inda kuma yayi laifi inyi masa fada" hawaye ya zubo daga idon inna tace "shikenan abinda zakayi masa?" Yace "to gaya min me kike so inyi masa?" Tace "ka mayar dashi gidan ubansa tun kafin yalalata mana yarinya ya cuce mu" ya girgiza kansa yace "Sadauki ba zai lalata Diyam ba, in ma hakan ta faru to mune zamu kasance masu laifi fiye dashi. Yanzu in tambayeki? Me yasa da Diyam ta gudo daga makaranta batazo gurinki a matsayin ki na mahaifiyarta ba sai ta tafi gurin Sadauki?" Da sauri inna tace"saboda ya cinye kurwarta bata ganin kan kowa da gashi sai nashi" Baffa ya girgiza kai yace "saboda a gurinsa take ganin zata samu maslaha in ta zo gurinki problem zata karawa kanta. Yarinyar nan dududu shekarunta goma da watanni a duniya, yanzu ne ya kamata ace kin kara jawo ta jikin ki kin koyar da ita lamurran duniya, amma me? Diyam tsoron ki take ji, komai tayi gani takeyi kamar laifi zatayi a gurinki. Yanzu da ace ma lalata tan yakeyi kamar yadda kika yi tunani ta yaya zaki sani? Kince ba kya son taje dakin Zainab, amma ke kin gaza yi mata abinda Zainab din take yi mata har take nacin zuwa dakin nata, wasa da dariya, kulawa, nuna soyayya, wannan shine kadai abinda Diyam take bukata daga gurinki a wannan lokacin. Ke kika haife ta, dan haka in kika sakar mata fuska zakiyi mamakin yadda zata sake dake itama".

Inna ta kalleshi tace "dama na sani, nasan duk yadda zakayi ka juya maganar nan ta koma kamar laifina ce sai kayi, ni kumana riga na sani, nasan cewa kafi son Sadauki akan Diyam, kafi son agola akan yar data fito daga jikin ka, kamar yadda ka fi son zainabu akai na ni uwargidan ka kuma yar uwarka ta jin, kuma uwar yayanka na gaskiyai" Baffa ya mike tsaye yana girgiza kai yace "Diyam ni na haifeta, Sadauki kuma nina rike shi tun yana cikin tsumman sa dan haka dukkan su yaya nane, babu banbanci. Maganar tsakanin ki da Zainab kuma ke kike ganin haka, ke kika saka haka a ranki. Amma ina son ki bude idonki ki kalli gabanki sosai zaki fahimci ke kadai kike fadanki babu wanda yake amsa miki"

Har ya kai bakin kofa tace "ina neman alfarma guda daya a gurinka" ya juyo amma bai ce komai ba, tace "ina son idan har Diyam ta kammala primary a kaita boarding school" yace "Allah ya nuna mana lokacin".

Writing......
[1/14, 8:43 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Sixteen: My Love

Washegari Baffa da kansa ya tisa keyar mu daga ni har Sadauki muka je islamiyya, ya saka muka bada hakuri sannan shima ya bayar, ya kuma ce duk sanda wani abu makamancin wannan ya sake faruwa su sanar dashi shi kuma zai dauki mataki akan mu. A take kuma yayi Asma'u register ya ce kullum tare zamu ke zuwa da ita . Wannan ya kawo karshen gudun islamiyya ta amma kuma ya kawa hauhawar kiyayyar Sadauki a gurin Inna, yanzu yakasance ko gaisheta yayi bata amsawa shi kuma bai fasa gaishetan ba kullum. Takance "shegen naci irin na uwa, kamar tsohon maye".

A karshen term din muka rubuta jarabawar common entrance. A lokacin shi kuma Sadauki ya rubuta jarabawar shiga ss3, qualifying exam, kuma dukkanin mu munyi nasara. Naci makarantar day science ta nan garin kano. Ina karbowa na taho gida da murnata na kuma yi sa'a Baffa yana gida, suna palon sa shida Sadauki suna lissafe lissfen da suka shafi gareji. Na durkusa na gaishe shi sannan namika masa takardar, ya karba ya karanta yana murmushi yace "very good Inno. Kinyi kokari sosai Allah yasa albarka a cikin karatun ki" nace "ameen Baffa" yace "sai dai ba day science zaki tafi ba, nayi magana da wani abokina wanda yake malami ne makarantar kwana ta yammata dake garin Taura a jahar Jigawa, yace in kaiki zasuyi miki interview in kinci sai a kaiki can" na taba rai cike da confusion nace "taura? Gari ne haka din? Makarantar kwana?" Sai na juya na kalli Sadauki wanda shima Baffa yake kallo yace "Baffa boarding fa kace, Diyam? Baffa Diyam bata da girma manyan dalibai zasu ke cin zalinta kuma...." Sai ya hadiye sauran maganar saboda kallon da Baffa yayi masa, Baffa ya miko min takardar yace "ki kaiwa innarki ta adana miki, gobe da safe ki shirya zamuje kiyi interview din" na karba jikina a sanyaye na wuce dakin inna. Na kai mata ta bude tana gani fuskarta da murmushi duk kuwa da cewa ba wai sanin abinda aka rubuta tayi ba. Na zauna a kusa da ita nace "Inna naci day science, makarantar su Rumaisa" ta ninke takardar ta ajiye tace "Rumaisa ai jeka ka dawo take yi, ke kuma makarantar kwana zakiyi" na fara hawaye nace "Inna Baffa yace wai gobe za'a kaini a gwada ni, inna ni bana son zuwa dan Allah kiyi masa magana kar a kaini" tana kallona tace "saboda me?" Na rike hannunta nace "bana son barin gida Inna bana son rabuwa daku" sai ta zame hannunta daga nawa tace "ko dai bakya son rabuwa Sadauki? Ni kuma saboda shime nake son akaiki makarantar kwanan ko hankalina ya kwanta, kuma idan ba kya ganinsa a hankali zaki manta dashi. Kafin Allah ya taimake mu ya tattara ya koma gidan ubansa" jin haka yasa na fahimci bani da hope a gurin Inna, ba zata rokar min Baffa ya fasa kaini boarding ba.

Dakin Ummah na tafi ina sharar kwalla, ta rike ni tana tambayata, "Diyam lafiya? Wani abu ne yake yi miki ciwo?" Na zauna ina kara sautin kukana nace "Ummah wai boarding za'a kaini inji Baffa, dan Allah Ummah ki bawa Baffa hakuri" tayi ajjiyar zuciya tace "Diyam, ai ba laifi kikayi masa ba ballantana in bashi hakuri, zai kaiki boarding ne saboda yana ganin hakan shi yafi dacewa dake" nace "to ni yanzu Ummah me zanyi? Me zanyi ya fasa kaini?" Tana shafa kaina tace "kiyi addu'a, kiyi fatan Allah ya sa hakan shi yafi miki alkhairi"

Washegari tun da assuba Baffa ya leko yace min in tashi in shirya, karfe takwas na safe muka dauki hanyar Taura, Sadauki ne yake jan motar sai Baffa a gaba ni kuma ina baya ni kadai, wannan yasa na kwanta wai ko za iya bacci amma bacci yaki zuwa ina ta jero duk addu'ar da tazo bakina akan Allah yasa kar inci interview din nan. Su Baffa ma ba sosai suke hira ba sai jefi jefi, shima kuma duk akan harkar garejin su ne. Karfe goma saura muka isa makarantar, aka bude mana gate muka shiga har bakin staff room sannan Baffa ya kira number din abokin nasa wanda shine vice principal a lokacin, inanan dai a kwance yazo, naji suna gaisawa da Baffa sannan Sadauki ya gaishe shi, sai ya bude kofar baya yana kallo na yace "manu wannan kawai bar mana ita za'ayi anan, a aiko mata da kayayyakin ta" Baffa yace "shi kenan kuwa kaga mun huta da sake dawowa" ina jin haka na kifa kaina a jikin kujera na fara rera kuka, Sadauki ya juyo yana kallona yace "wasa suke yi miki fa, ke baki san wasa ba? Ya za'ayi a kawo ki makaranta a lokacin hutu" sai kuma na tuna ashe hutu akeyi, na fara goge hawayena ina cewa "Sadauki bana son makarantar nan" yace "kiyi shiru kar Baffa yaji yayi miki fada" daga waje naji abokin Baffa yana kira na, na fita ina goge hawayena da hijab dina. Staffroom babu malamai sosai saboda ana hutu, office din principal muka shiga, na gaisheta a darare ta kalle ni daga sama zuwa kasa sannan tace "too young" vice ya matsa kusa da ita ta fara yi mata bayanin cewa karamin jiki ne dani amma eleven years nake a lokacin, ya nuna mata birth certificate dina da sauran takardu. Ta gyada kai sannan ta bani wata exam question paper tace in zauna in amsa. Na zauna ina dubawa, obj ce, dan haka nayi ta cike shiririta ta wata question din ma ko karantawa banayi wai ni a lallai so nake in fadi. Ina gamawa na bata na fito raina fes saboda nasan nayi messing up. Baffa ya mike yana kallon vice yace "to ya akayi? I hope taci?" Vice yayi dariya yace "ai ba'ayi marking ba, amma abinda ta rubuta a paper doesn't matter, tunda ina gurin ai babu wani abu, maybe ma ni za'a bawa in yi mata marking. Kawai da lokacin kawo yara yayi ka shirya ta ka kawo ta. Ya dan daki kaina cikin wasa yace "kaga manyan yan boarding" naji kamar in rufe shi da duka dan haushi.

A cikin hutun na harda ciwo nayi. Inna da Baffa kuma duk sunsan abinda yake damuna amma babu wanda yabi ta kaina, sai ma shirye shirye da suke yi. Aka dinkamin uniform, aka siyamin manyan trollies dina guda biyu daya ta kayan sawa daya ta kayan abinci. Vice ya rubutowa Baffa duk abinda ake bukata Baffa kuma ya bawa Sadauki yaje ya siyo min. Akan haka sai da akai rigima da Baffa da inna tace ina ruwan Sadauki da siyayyar makaranta ta? Amma Baffa bai fasa bashi ba. Idan Baffa ya bashi list din sai ya zauna ya kakkara wasu abubuwa yace ai duk zan bukace su, sai da Baffa yace "Sadauki ya isa haka in ba so kake ka talautani akan Diyam ba, muma ai muna bukatar kudi a gidan".

Ranar da zan tafi, tun da na tashi nake yan koke koke na amma Inna ko ta kaina bata bi ba tace "kya yi kya gama. Gata akeyi miki ke baki sani ba". Sai ga Ummah tazo da kanta da kaya cikin leda, da cincin a cikin wani dan karamin plastic container mai murfi tace "Diyam gashi ki tafi dasu makaranta, ki rike addinin ki kinji? Kuma kar kike wasa da cikin ki ki tabbatar kina cin abinci akan kari, duk abinda kika ga ya kusa karewa ki saka ayo waya gida a fada" na karba ina share hawayena nace "to Ummah na gode" Inna ko daga kai bata yi ta kalleta ba.

Sadauki da Baffa ne suka kaini, tun daga gate nake kuka har muka shiga ciki aka gama cike ciken takardu, malamai suna ta tsokana ta wai daga gani na sabun shiga ce. Sadauki ya durkusa a gaba na yana share min hawayena yace "zaki yi ciwon kai na gaya miki. Ki daina kukan nan haka" na rike hannunsa nace "ni karka tafi ka barni" ya kakalo murmushi yace cikin wasa "ai babu hostel din maza" sai kuma yayi dariya shi kadai ba tare dana taya shi ba. Yace "zanke zuwa ina ganin ki. I promise. Amma sai kin daina kuka in ba haka ba bazan ke zuwa ba" na langwabar da kai nace "ai kukan ne yake zuwa da kansa" yace "to kiyi, amma kadan". Ina kallonshi yana ta delaying shiga mota da zasu tafi, har sai da vice ya tisa keyata zuwa class sannan na jiyo tashin motar su. Ina zuwa nayi kawa Jidda, itama yau aka kawo ta tana ta kuka sai class master din mu yace mu zauna a seat daya kuma daga yau mun zama kawaye tunda mune masu kuka a aji.

Duk yadda na dauka rayuwar makaranta zata zo min ba haka tazo ba. Kafin inyi sati na warware sosai ina harkokina, nayi suna a ajinmu saboda kokarina da kuma surutuna. A hostel kuma nayi suna saboda kankantata da kyau na. Seniors suna sona sosai, wadansu su kance ina musu kama da baby doll saboda yar karamace ni babu tsaho babu kiba, gani fara tas kamar babu jini a jikina sai uban gashi mai tsaho da santsi wanda baya kitsuwa sai da kyar. Daga wannan senior din ta dauke ni tace kanwarta ce ni sai waccan ta dauka, ayi tabani kayan dadi ina ci, in an tare yan makara dani sai ace "wannan in aka dake ta ma ai sai a balla ta, tashi ki tafi, karki sake makara" dutse kuwa sai da aka samo wanda yafi komai sauki, sharar verandah sannan aka bani.

Amma fa wannan ko da second daya baisa na cire Sadauki daga raina ba, kullum dashi nake kwana dashi kuma nake tashi. Wani lokaci sai im zauna inyi ta rubuta masa letters ins bashi labarin rayuwar makaranta ta, in zana flowers a jiki da hoton heart da arrow da sunansa a jiki "Aliyu Haidar". Rannan jidda ta gani ta dauka tana karantawa tace "wanene Aliyu?" Nayi murmushi nace mata "saurayi na ne".

Sai da nayi wata daya sannan rannan muna class aka aiko inzo anzo min visiting. Na mike da sauri ina murna a raina ina kwadayin Allah yasa tare da Sadauki aka zo. Ina fitowa aka nuna min bayan staffroom akace inje can. Na tafi da sauri na, banga motar gidan mu ba amma sai na hango Sadauki shi kadai a tsaye ya jingina da daya daga cikin bishiyoyin gurin. Na kwasa da gudu, ya juyo yana kallona yana dariya amma da yaga da gaske jikinsa na nufa sai ya dakatar dani da hannunsa daya sannan ya girgiza min dan yatsa. Na bata rai na turo baki na juya baya nace "ni fushi ma nakeyi da kai" ya zagayo ta gabana kyakykyawan murmushi kwance a kyakykyawar fuskarsa yace "me kuma nayi? Allah sarki Aliyu bawan Allah" na rike kugu nace "ai kasan laifin ka" ya kama kunnensa yace "na tuba, duk da bansan me nayi ba" na nuna shi da dan yatsana nace "ba cewa kayi zaka ke zuwa ina ganin ka ba? Amma shine tunda aka kawo ni ba ka taba zuwa ba?" Yace "aiya, Halima wata daya ne fa kadai" nace "eh, ai duk sati nake so kazo" yayi dariya yace "duk sati ai suma kansu makarantar ba zasu bari ba" ya kama hannuna muka zauna a daya daga cikin benches din dake gurin yace "kinga, visiting card guda uku suka bamu, suna nufin sau uku aka yarda azo ganin ki. In na ce zanke zuwa duk sati ai ko wata ba zakiyi ba cards dinki zasu kare. Kuma kinga su Inna ma si zasu so suxo su ganki ko?" Na danyi murmushi naji ina missing Inna nace "ya suke? Ya Baffa da Asma'u?" Yace "duk suna lafiya, basu san dai na taho ba sai Baffa kadai. Ke kuma fa? Ya makarantar? Ba'a cin zalinki ko?" Ya kama hannuna yana checking ko yayi kaushi ko kanta yace "ba'a saka ki labour? Noma da shara mai yawa?" Na gyara zamana ina wasa da hannuna na bashi labarin duk irin yadda nake enjoying makarantar, yace "wato it sometimes pays to be smallish ko?" Muka yi dariya. Sai kuma ya bani labarin tasa makarantar, yanzu sun shiga ss3, ya fada min an bashi prefect, yace "guess me aka bani" na karkatar da kai ina kallon murmushin fuskarsa nace "labour prefect" yayi dariya yace "you are a smart one, aren't you?" Nace "to kar dai kake cin zalin yayan mutane" ya daga hannu sama yace "ba zalin wanda zanci, kar alhakin su yasa aci min zalin matata" sai kuma naji kunya na rufe ido.

Mun jima muna hira, jin mu muke kamar masu yawo a saman gajimare har sai da aka zo ake ce masa time up sannan muka fara sallama, rai ya fara baci kuma. Yace "hope kayan abincin ki basu kare ba" na gyada kai kawai ina goge hawaye, yace "okay, to bara in koma da sweets din dana zo miki dasu tunda kuka zakiyi" nayi sauri na jawo ledar gabansa na turo baki ina kunkuni. Na bude naga kayan alawa, chocolate da biscuits ne kawai a ciki. Ya miko min kudi yace "inji Baffa, yace ki fada in kina son wani abu" na girgiza kai, yace "to kiyi min dariya mana in gani. Kuma ko sammin sweets din ba zaki yi ba?" na bude ledar na dauko chocolate guda daya na bare na bashi nace "gashi nan, ladan ganin ido"

Share your thoughts akan soyayyar Diyam da Sadauki. Do you think tana dorewa?
[1/15, 8:20 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Seventeen : PS: I Love You

A tsakiyar term su inna suka zo min visiting suma. Sadauki ne ya tuko su amma babu Baffa kuma babu Ummah sai Asma'u Mama da su Rumaisa. Nace "ayyah, Inna da kun sani kun taho da Ummah, nayi missing dinta" babu wanda yace dani ci kanki a cikin su. Ranar nayi murna har na rasa inda zan saka kaina, su kuma suna ta yimin dariya. Suka zo da abinci kula kula muka hadu muka ci tare ana ta hira, amma Sadauki tunda muka gaisa ya koma mota, sai da muka gama cin abincin sannan na zuba na kai masa, ina mika masa kuwa inna ta kira ni in dawo haka na taho bamuyi magana ba. Sai da zasu tafi ya dauko bakar leda ya miko min yace inji Ummah, garin karba naji ya saka min takarda a hannu na sai nayi sauri na saka ta cikin aljihuna, yayi murmushi kawai ya daga min hannu suka tafi.

Bayan na koma hostel ina jejjera kayan dasu Inna suka kawo min, na duba ledar da sadauki ya bani naga dambun nama ne da yaji attaruhu da tafarnuwa, just the way I liked it. Nayi murmushi na dauko takardar daya bani na bude ina karantawa.

My dearest star.
Am sorry ba mu sami damar magana ba, but ganin kina lafiya kadai ya ishe ni farin ciki. Ga dambun nama nan inji Ummah tana gaishe ki.
PS
I love you.

Na dora takardar a kirjina ina jin wani iri. Na sani cewa akwai wani abu a tsakani na da Sadauki amma bai taba furtawa direct ba sai yau. And it feels great. A hankali nace "I love You too Aliyu".

Haka rayuwa ta cigaba da kasance wa, har cikin ikon Allah muka shiga third term na js1, a lokacin shi kuma Sadauki suke zana ssce dinsu. Kullum in naga yan ss3 dinmu suna exam sai inta yiwa Sadauki addu'a, Allah ga Sadauki nan, Allah ka bashi sa'ar exam din nan. Wannan term din gaba daya baizo min visiting ba. Sai ranar da mukayi hutu suka zo daukana shida Baffa, ko dan ma kwana biyu ban ganshi ba? Sai naga ya kara girma ya kara kyau.

Naje na shige gaban mota na barshi da daukan kaya yana sakawa a booth, Baffa kuma ya tafi zaiyi signing dina out. Na dauko powder da lipstick ina shafawa wai duk kyalliyar zuwa gidan ne, sai kawai naji kamar ana kallona, nayi sauri na kalli mirror muka hada ido dashi, ya tsaya da jaka a hannunsa kawai ya zuba min ido ta mirror, muna hada ido sai kuma kunya ta kamashi yayi saurin dauke kai kunya a rubuce a fuskarsa. Dariya kawai nayi wai namiji da kunya.

A cikin hutun ne muna gida na fara period. Ranar ina kwance a dakin Ummah ina tashi kawai naji danshi a kasana, na saka hannu na shafa kawai sai naga jini a hannu na, na kalli Ummah naga itama ni take kallo. A lokacin Sadauki yayi sallama nayi sauri na koma na zauna ina boye hannu na a baya na, ya tsaya daga bakin kofa yana kallona yace "ke kuma lafiya kike rarraba ido kamar bera a buta?" Ummah tace "ina ruwan ka da ita, tsabar sa ido me kazo yi ma gida a yanzu?" Ya shigo yana cewa "babu aiki a garejin, shine nazo gida in huta. Diyam tashi ki bani abinci" na kwabe fuska kamar zanyi kuka Ummah tace tana nuna masa kofa "tashi ka fita" yace "Allah ya baku hakuri, daga tambaya?" Sai ya mike ya fita yana waige na.

Yana fita Ummah tace "tashi in gani" na mike, tace "kin san menene?" Na gyada mata kai. Tabbas nasan jinin haila da hukunce hukuncen sa tun a islamiyya, na kuma kara sani a kansa a makarantar boarding. Akwai yan ajin mu da suke yi, kuma seniors din mu ma sunayi dan sukan aike ni wajen wata matron in siyo musu pad, amma ban taba tsammanin zaizo gare ni ba ni Diyam, at least not now, ni ban shirya girma ba gaskiya. Ummah ta saka ni naje drawers dinta na dauko wasu undies data siyamin da niyyar in zan koma makaranta zata bani, ta saka na dauko pad itama a dakinta takoya min yadda ake sakawa sannan tace min inje toilet in gyara kaina. Ina dawowa na tarar

Please Login or Register in order to submit comment