Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar ban ji shi ba sai yace "dama nan da two months ne tafiyar nan tazo, da da amarya ta zan tafi. Ohh ban fada miki ba ko? Nan da wata biyu ne aure na fa" nace "to ka daga tafiyar mana sai anyi bikin? Ohh na manta, ashe bada kudinka zaka yi tafiyar ba da kudin oga ne kuma dole sai abinda oga yace sannan zakayi tunda kudin sa ne. Mtsww i pity you" da naga dai neman magana yake yi sai na tashi na bashi guri saboda ni bana son rigima dashi a gaban Subay'a, amma kuma sai na samu zuciya ta da jin haushin Sadauki na budawa Saghir da yake yi.

Shi ya hada kayan tafiyar sa da kansa, da safe ya turo Subay'a ta kira ni naje na tsaya a bakin kofa yace "rashin kunyar ki, da rashin biyayyar ki shi yasa har yanzu auren mu yaki daidaita, da ace kin kwantar da kai, kin bini yadda nake so da ba karamin jin dadi zakiyi tare da ni ba. Kinga wannan tafiyar ma oga mu biyu ya biya wa, ni dake, yace in tafi da matata saboda wata daya zanyi kar in zauna gwauro a can, kinga da sai muyi tafiyar mu ni da ke da Subay'a but I guess I will have to go alone" ya ajiye kudi a kan mirror "ga kudin cefane nan, kinsan ni ina tsoron Allah dan haka ina kokarin sauke hakkin ki da yake kaina. Ban yafe ba, in kika fita ko da kofar gida ne indai ba abinda ya shafi makarantar Subay'a bane ba, sai kuma rashin lafiya, Allah yana kallonki in kika ci amana ta in bana nan" nayi murmushin takaici kawai, akwai amsoshi da yawa a raina wanda nake so in bashi amma ganin Subay'a yasa nayi shiru har ya dauki jakarsa ya fita yana cewa "gwara mutum ma ya dan bar kasar ya sarara na kwana biyu".

Tafiyar Saghir da kwana biyu Alhaji Babba ya kira ni a waya, I can't remember last sanda ya kira ni. Na dauka na gaishe shi sai naji muryarsa wani iri yace min "Diyam ki zo gida ina nemanki dan Allah" sai naji wani iri da yace min dan Allah, duk da dai Alhaji Babba yayi sanyi sosai tunda yanzu kusan hannu baka hannu kwarya suke zaune a gidan, bashi da komai sai yan abokai da suke taimaka masa da kuma kawu isa shima da yake dan bashi wani abu, duk sana'ar daya kama sai ta rushe, kullum muka je gidan yana ta cewa makiya ne suka sako shi a gaba ni kuwa deep down nasan inda matsalar dukiyar Alhaji Babba take, kudin mune da yaci, dukiyar marayu daya handame ya hada da tasa dukiyar da yasha wahala gurin nema dan haka sai yayi asarar har tasa dukiyar gabaki daya.

Na tambayeshi ko lafiya? Sai yace inzo dai kawai yana nema na. Na shirya ni da Subay'a muka tafi. Bayan mun gaisa da mutanen gida ne muka tafi palonsa na ganshi daga shi sai riga yar shara wadda duk tayi datti. Na durkusa na gaishe shi sai ya dauko wasu takardu ya miko min. Na bude a nutse ina dubawa a dan ilimi na sai na fahimci takarda ce daga kotu ta sammaci, mai kara shine 'Aliyu Usman Kollere" Wanda ake kara kuma "Alhaji Muhammadu Kollere" sai kuma sauran takardu da suka kunshi photocopy na takardar fili belonging to Aliyu Usman Kollere, da kuma takardar garage din Baffa, sannan anyi list na duk abinda yake ciki da kudinsa da kuma estimate na kudin business din gabaki daya, sai kuma akayi jimullar kudin wanda yawansu sai da yasa na kama baki na. Yanzu wannan ne dama kudin da Alhaji Babba yaci na mu? Wannan shine kudin da akace anyi min kayan daki dasu? Amma mai yasa alhajin yake nuna min a yanzu?

Kamar amsar tambaya ta sai naji yace "Diyam kinga abinda tsohon saurayin ki zaiyi min ko? Yaron da Usuman ya rike kamar shi ya haifeshi kinga sakayyar da zaiyi mana ko? Wai ya kaini kara wai naci dukiyar marayu to dukiyar ta ubansa ce? Ina ruwansa? Kudin nan ba aure nayi miki dasu ba? Ai na gaya wa Amina tun a lokacin kuma ra amince. Takamarsa shine da kason uwarsa a ciki shine yake so yayi min tonon silili" ni dai na ajiye takardun ina kallonsa har ya gama fadan sa sannan kuma sai yace "an ce min in na saka kika yi masa magana zai iya ya janye wannan maganar" na gyada kai, so that's it. Wannan shine dalilin da yasa aka shigar dani maganar. Nace "ni Alhaji bansan inda Sadauki yake ba ballantana inyi masa magana, kuma ma ba lallai ne ya saurare ni ba. Amma shi ne ya kawo takardun?" Yace "ina fa? Babu wanda yasan inda yake fa, lauyoyi ya dauka har guda uku, su suka shigar da karar alkali kuma ya aiko min da sammaci" ba gyada kaina, wato basu san waye Sadauki a yanzu ba. Nace "to ni Alhaji in zanyi masa ma maganar ai bansan inda zan same shi ba" yace "Amina ma tace bata san inda yake ba. Kuma ko number dinsa babu a jikin takardar sai ta lauyoyinsa" na dauki takardar ina kara dubawa sai naga numbobin, na dauki daya a waya ta nace "idan na same shi me zance masa?" Ya gyara zama yace "ki gaya masa ni ba matsiyaci bane ba, kaddara ce ta sauka a kaina da kuma makiya da suka sako ni a gaba wannan ne yasa a yanzu bani da kudin da zan bashi, amma kice masa yayi hakuri muyi aggrement zanke biyansa a hankali a tsakanin mu ba sai munje kotu ba" nace "shikenan Alhaji, zanyi kokarin ganin yadda za'ayi a fahimci juna" yayi ta saka min albarka sannan yace "ashe mijinki yayi tafiya? Sai da aka kawo takardar nan jiya na neme shi sannan naji ma wai baya kasar".

Na fito ina ta mamakin halin Saghir. Sai kuma na koma lissafin wannan lamari. Me Sadauki yake after? Na tabbatar ba kudin yake so ba dan yafi karfin wannan kudin a yanzu. Sai kuma na fahimci wannan shine dalilinsa na tura Saghir kasar waje saboda baya so yayi blowing cover dinsa ta matsayin ogan Saghir, duk da dai yadda ya shirya kai karar ba lallai ne ma a ganshi ba dan lauyoyinsa sun isa su wakilce shi amma me yake bukata?

Sai dana koma gida sannan na kira number din lawyer din. Ya dauka na gaishe shi ya amsa sama sama sai nace dan Allah ina son magana da client dinsa Aliyu Usman Kollere, yace "what for? Bana bada contact din client dina gaskiya" nace "na fahimta, but please ka gaya masa in ya tuna Halima Usman Kollere to tana son magana dashi" ya amsa zai fadi sakona sannan ya katse wayar. Jira jira har dare babu amsa, haka nayi ta duba waya ina karo volume wai dan kar a kira banji ba.

Sai safe around ten sannan kiran ya shigo, lawyer din ne dai yace "yace menene? Ki gaya min sakon sai in gaya masa" na runtse idona ina jin duniyar ma duk tayi min zafi nace "shikenan. Tell him nace dashi nake son magana ba da kai ba in bashi da guts din da zai saurare ni shi kenan na rike magana ta" na kashe watar ina jin zafin Sadauki a raina. Wato bama yason magana dani, baya son gani ba, ya manta dani yake nufi ko me? Ya manta alakar mu? Ya manta alkawarin mu? He said he will love me forever yanzu har forever din tayi? Amma sai wata zuciyar take tuna min da matsayi na na matar wani, wata zuciyar tana so in yi wa Sadauki uzuri na kin saurata ta da yayi, na gudu na da yake yi.

Around 12 wani kiran ya shigo wayata, saida zuciyata ta buga ganin sabuwar number, sai na samu kaina da rike wayar amma na kasa amsawa har ta kusa katsewa sannan na dauka a hankali na kai kunnena idona a rufe nayi sallama, shiru at first, sannan yace "kina son magana dani, ina jinki" muryar Sadauki, as clear as ever. Na hadiye abinda yaki tafiya a makogwaro na sannan nayi kokarin nima in yi irin nasa nace "maganar Alhaji Babba, yana son ayi negotiation. Can you do that?" Ya danyi shiru sannan yace "come to my office tomorrow morning, you know where it is" daga nan ya katse. Sai na zauna da waya a hannu ina mamakin wai da Sadauki nayi magana yanzu, but it sounded as if da wani stranger nayi maganar.

Ranar bana jin nayi baccin awa daya. Da assuba na tashi nayi wanka nayi sallah sai kuma na zauna ina kallon agogo yana ta lakaki yaki yin sauri balle gari ya gama wayewa. Na tashi Subay'a na shirya ta sannan nima na shirya tana ta tambayata inda zanje, na bata breakfast nima na hada tea na kurba amma sai ya tsaya a makogwarona yakasa wucewa. A haka har lokacin kaita school yayi, na kaita sai kuma nayi tunanin is too early inje office din Sadauki dan haka na dawo gida na cigaba da kallon agogo har saida ten tayi sannan na fita. Ina gayawa mai adaidaita Abatcha Motors sai yace "okay companyn motocin nan ko?" Sai da muka isa gurin sannan na kare wa building din kallo, so all of this is owned by Sadauki, how? Na shiga trying not to act like yar kauye, shi kansa building din anyi shine da shape din mota, haka round about din da yake tsakiyar gurin shima siffar mota ce dashi. Sadauki and cars bansan wacce irin soyayya ce a tsakanin su ba. Ina shiga reception din sai na tuno da ranar da akayi party, nayi tunanin ko wasu zasu gane ni? Amma kuma ranar babu haske sosai dan haka ba lallai bane su gane fuskata. Naje desk din receptionist, kafin inyi magana tace "Halima?" Na amsa mata sai ta dauki waya tayi magana a ciki sannan ta nuna min bene tace in hau, na hau na tarar da wata tana jira na sai ta bude min wata kofa tace in shiga, na shiga na tarar da wata mata da name tunanin secretary ce, kyakykyawar gaske gata ta sha make up sai kamshi take zubawa, ta yi min murmushi sai kawai naji ina jin haushinta ba tare da ta yi min laifin komai ba, ta wuce gaba sai naga kamar tana sane take murguda min bombom ta bude min wata kofa da card din hannunta na shiga sannan ta rufe.

Yana zaune a bayan katon table din gaban sa, as majestic as ever, bai ko dago kai ya kalle ni ba yaci gaba da rubutu a takardar gabansa ni kuma ina tsaye sai daya gama sannan ya dago fuskarsa blank yace "welcome Madam, have a seat please" naji kamar in juya in fita daga office din, nayi nadamar dana sani banzo ba amma ina bukatar amsa, ina bukatar ji daga bakinsa cewa ya manta da first twenty years of his life. Na zauna a kan cussion chairs din da suke jere a office din. Ya mike tsaye, sai naga ya kara cika min ido da kwarjini da girma baki daya ya zagayo ya zauna a kujerar gaban table dinsa sannan yace "kince Alhaji Muhammadu ya turo ki akan wani negotiation, ina jinki" naji wani sabon bacin rai, ni na ma manta abinda ya kawo ni kenan, sai kawai hawate ya fara bin fuskata. Nace "abinda zaka ce ma kenan? Irin karbar da zakayi min kenan? Sadauki nice fa Diyam, how can you even......call me Madam?" Sai ya mike tsaye ya juya bayansa ya saka hannu a aljihu yace "menene sakon da Alhaji yace ki fada min?" Sai na mike na nufi kofa da sauri ina goge hawayen fuskata, bai ce min komai ba har naje na kama kokawa da kofa amma taki budewa, na juyo ina kallonsa sannan yace "ba'a fita daga office dina sai nayi wa mutum izni" sai na dawo da baya da sauri na dauki wasu magazines na motoci na jefa masa, na debo tarkacen files din kan table dinsa suma na yi ta dukansa dasu har takardun suka tarwatse a gurin amma ko motsawa baiyi ba, na durkusa a tsakiyar gurin na kama kuka sai ya dawo ya zauna akan kujera yace "menene sakon da zaki gaya min?" Sai dana gama kukana sannan na tashi na zauna na goge fuskata nace "why? Sadauki why? Me yasa kame treating dina haka?" Yace "ya kike tsammanin zanyi treating mayar employee na?" Nace "shikenan? Matsayina kenan? Matar employee dinka? Me yasa ka dauke shi aiki ma? A ina ka sami wannan kudin kuma? I need answers Sadauki, I need to talk to Sadauki not this Mr Abatcha" yace "zaki samu answers dinki in due time. Now me Alhaji Babba yace?" Na goge hawayena nace "nasan kasan bashi da kudi yanzu, bashi da kudin biyanka ko da kuwa kotun koli zaka kaishi, dan haka I think you are just wasting your time" yace "really? To tunda bashi da kudin biya na fili na da gadona sai ya shirya zuwa prison for it. Kullum takamarsa kenan, kullum maganar sa itace zai saka a rufe ni, lokacin yana da kudi ni kuma bani dashi. Ki je kiyi masa albishir da cewa the table have turned, yanzu nine zan rufe shi" na bude ido ina kallonsa nace "you don't really mean that, me zakayi da kudin? Me zakayi da filin Sadauki look at this" na fada ina nuna office din nasa "zaka iya siyan hundreds of wannan filin, kafi karfinsa yanzu" yace "Baffa ne ya siya min remember? I was suppose to build us a house a kan filin nan, gidan mu ni da ke da yayan mu remember?" Sai kuma ya mike ta sake juya bayansa yana kallon window. Mun jima a gaka sannan nace "kayi tunanin abinda Baffa zai so, Alhaji Babba yayansa ne uwa daya uba daya ba zai so ya ganku a court dakai dashi ba, ba zai so yaga ka rufe masa dan uwansa akan kudi ba" ya juyo yana kallona yace "kamar yadda ba zai so a cire ki daga makaranta exactly 40 days bayan rasuwar sa ayi miki aure ba, kamar yadda ba zai zo a siyar da abinda ya kwashe rayuwarsa yana building abar iyalinsa da hamma ba" sai yakuma juya wa sannan yace "kamar yadda ba zai so a raba mu ba" na runtse idona ina jin wound fin zuciyata yana dawowa sabo, kewar Baffa na tana lullube ni, mun jima haka sannan yace "tell Alhaji Babba nace yana da options guda biyu, na daya shine ya bar mana gidansa da yake ciki tunda shi kadai ne yanzu abinda ya rage masa, na biyu kuma shine ya tafi prison for the rest of abinda ya rage na rayuwarsa"

Na mike tsaye, "Sadauki, ubangiji ma yana son rama sharri da alkhairi, kamar yadda kayi wa inna, dan Allah ka bar maganar nan, Allah ma daya halicce mu muna yi masa laifi kullum amma idan muka durkusa muka roke shi gafara sai ya yafe mana" ya juyo yana kallona, his eyes shining, yace "then tell him yana da third option, yazo ya durkusa ya roke ni gafara, ya saka gwuiyoyinsa a kasa ya roke ni in yafe masa kamar yadda na saka guiwowina a kasa na roke shi ya bani aurenki ya hana ni, ya durkusa kamar yadda na durkusa na roke shi kar ya aura miki that monster he calls a son amma duk da haka ya aura miki shi. Yes, I want him to cry and beg kamar yadda nayi in yaso in naki hakura duk da yayi haka sai yaji shima irin yadda naji".

Sadauki yayi tsauri da yawa ko? Lol

Not edited
[2/14, 10:05 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Three : Heartless
Raina ya kara baci, ina mamakin anya kuwa wannan Sadauki nane? Sadaukin da na sani will never do that amma kuma sai nayi wani tunani. Yes, Sadauki yana da kirki da kyawun hali sosai amma bashi da yafiya, musamman idan akan abinda ya shafe ni ne Sadauki bai taba daga kafa ba ko da kuwa waye ya taba nin indai ba Inna ko Baffa ba, na tuno ranar daya doka wa yaya Mukhtar ball aka a gaban Inna. Sadauki bashi da tsoro ko kadan tun a lokacin da bashi da komai ma, ballantana kuma yanzu da yake da masu garin.

Nace "abinda kake so kenan? Abinda kake after kenan? Revenge?" Ya girgiza kai "this is not revenge, this is justice" nace "wanne justice din ne kuma wanda yafi wanda Allah ya riga yayi? Shin in kayi haka Sadauki ka gode wa Allah kenan? Kaga kuwa halin da Alhaji Babba yake ciki a yanzu? Ka kuma duba kaga halin da kai kake ciki a yanzu, kai kanka ka fada, the table have turned, menene kuma saura? Shin in ka yafe wa Alhaji Babba mai zai ragu daga jikin ka? Sai ma daraja da hakan zai kara maka a gurin ubangiji. Yanzu in ya siyar da gidansa ina zai kai iyalinsa?" ya bar inda yake tsaye ya zagawa gurin kujerar sa ya zauna yace "sai su dawo gidan ku ku zauna tare, ai naga kuna da bene, sai su zauna a sama ku kuma a kasa" na saki baki ina kallonsa sai ya danna wani button a jikin table din sai naga kofar dana shigo ta bude, ya kalle ni yace "goodbye, Diyam" na tsaya kawai ina kallonsa ina girgiza kai, I can't believe Sadauki yayi tauri har haka, sai na je na tsaya a gaban table dinsa nace "I don't like this Mr Abatcha da nake gani a gabana, I want my Sadauki back, I want my brother back" sai na juya da sauri na bar office din.

Ina jin matar nan ta waje tana yi min magana amma ban ma fahimci abinda tace ba ni dai na gyada mata kai kawai na fita da sauri. Da saurin kuma na karasa wajen gate na tari abin hawa na shiga muka tafi. Sai da muka bar gurin sannan na saki kukan da nake rikewa, ma dauka hawaye ne kadai nake yi bansan ya fito fili ba sai da naji drivern yace "yammata kiyi hakuri, komai na duniya mai wucewa ne watarana sai kiga kamar ba'ayi ba" a goge hawaye na ina jinjina maganar sa, watarana zanga kamar ba'ayi ba? Yaushe?

Sai dana je gida sannan nayi realizing wani abu guda daya, ni da na tafi gurin Sadauki da niyyar samun answers amma ban samu ko daya ba sai karin tambayoyi da na debo wa kaina. Na sani Alhaji Babba ya zalunce ni kuma ya zalunci Sadauki kuma har cikin raina ban damu ba in wani abin ya same shi a saboda abinda yayi, abinda na damu dashi shine Sadauki, I don't like this person he as turned to bana son wannan hanyar da yake tafiya a kai. Ni da zai aje duk wannan kudin nasa ya koma former Sadaukin da na sani da sai nafi jin dadi.

Na biya na dauko Subay'a sannan muka karasa gida. Muna zuwa na shiga daki na hada mana kayan mu ni da ita a akwati na chanza mata kaya muka fito. Mai gadi yace tafiya zakuyi ne haka Hajiya?" Nace "cikin gari zamu shiga baba iliya, sai Sunday zamu dawo" ya taro mana abin hawa ya saka mana kayan mu muka tafi Subay'a tana ta murna.

Muna shiga gida naga Inna duk tayi wani jeme jeme da ita, bayan mun gaishe ta ta kalli akwatin kayan mu tace "da fatan ba yaji kika yo ba Diyam" na girgiza kaina nace "yayi tafiya ne Inna, shine muka zo gida muyi dan kwana biyu" ta gyada kai tace "duk da haka ina fatan da amincewarsa kika taho gidan. Nasan ba kya son Saghir, kin fada kin kara fada cewa ba kya son sa kuma har yau nasan ba kya son nasa din. Amma kuma rashin son nasa da ba kya yi ba zai cire shi daga matsayin mijinki ba. Ni nasan kiyayya Diyam nasan illolinta, tun zamanin yammatanci na na dora wa zuciyata kiyayyar Zainab kawai saboda baffanku yana sonta ni kuma ina sonsa. Kiyayyar ta karu lokacin da aka aura masa ni ina matsayin matarsa amma kullum sai ya tuna min cewa dole aka aura masa ni, sai ya gaya min cewa ga wadda zuciyarsa take so. Na kara kin ta kuma lokacin daya aure ta ya kawo ta gidan nan duk kuwa da cewa tayi aure ta fito amma bai rage soyayyar ta ba daga zuciyarsa. Sai ma ya dauki wani son daban ya dora akan agolan da tazo dashi har a gurina nake ganin kamar yafi sonsa akan ku yayan da na haifa masa. Sai ni kuma na tsani yaron ba tare daya yi min komai ba. Har yau ni bazan iya fadar wani abu na rashin kyautawa ko rashin kunya da Sadauki ya taba yi min ba. Na tsane shine kawai saboda na tsani uwarsa. A gaban Sadauki zan gaggayawa Zainab magana amma baya kulani saboda ta hana shi tace babu ruwansa da tsakanin mu. Amma haka na cigaba da rura wutan kiyayyar sa a zuciya ta yadda har mutuwar ita kanta wadda ta haife shi da wanda ya kawo su gidan bata wanke kinsa a raina ba a karshe ina ji ina gani na saka rayuwar yata ta cikina a wahala kawai saboda in bakanta masa" sai ta rufe fuskarta ta kama kuka "Diyam ki gafarta min abinda nayi miki,ni na haife ki amma na tauye miki hakkin ki na bawa azzalumai damar zaluntarki" sai na tashi daga gabanta na koma kusa da ita na dora kaina a kafadarta na fara kuka. Ta saka hannu tana shafa kaina tace "nayi nadama, nadama mai tsanani. Maganar baffanku ta tabbata, yan uwanmu sun watsar damu a titi Sadauki yazo ya dauke mu. Ohh duniya. Duk wanda bai godewa rahamar Allah ba to kuwa tabbas zai godewa azabtar sa. Diyam nayi nadama a lokacin da nadama bata da amfani. Wallahi da ace igiyar auren ki a hannuna take Diyam da tun haihuwar ki ta farko zan gutsire auren gwara ki dawo gida ki zauna a gaba na akan auren Saghir. Amma na kai ki na baro ki. Babu abinda zanyi sai dai in nemi gafarar ki" na rungume ta nace "Inna kinfi karfin haka ai, ni dama ban rike ki a zuciyata ba ballantana ki nemi gafara ta. Wanda zaki nemi gafara shine Sadauki. Shi kika fi zalunta ba ni ba" tace " to ni Diyam ina zanga Sadauki? Tunda ya kawo mu nan ya ajiye mu bai dawo ba. A lokacin na gaya masa ina son magana dashi sai yace min zai dawo amma tun lokacin nake zuba idon ganin sa sai dai shiru babu shi babu labarin sa".

Sai na bata labari. Na bata labarin asalin ko wanene Sadauki a yanzu sannan kuma na gaya mata yadda mukayi da Alhaji Babba da kuma irin amsar da Sadaukin ya bayar. Na karashe da "yanzu dai Sadauki yace Alhaji Babba yana da dama uku. Ko dai ya bamu gidan da yake ciki a maimakon kudin mu, ko yayi jail time, ko kuma yaje gaban Sadauki ya durkusa yana kuka ya roke shi gafara a bisa dukkan abinda yayi masa" Inna ta rike baki ta kasa magana. Nayi shiru ina kallon ta ina jiran ta inda zata fara jero tsinuwa ga Sadauki amma sai naji tace "to, kudin nan dai namu ne gabaki daya, ni dai abinda yake hakkina a cikin kudin nan na yafe wa Alhaji Babba tare da fatan Allah zai dubi niyya ta nima ya yafe min wasu daga cikin laifuffuka na. Amma a cikin ku ban tilastawa kowa ta yafe nata ba, duk wadda taga bata yafe ba sai ta bawa Sadauki goyon baya gurin karbo muku abin ku. Shima kuma Diyam kar ki kuma kokarin hanashi karbar hakkinsa, in ma zubarwa zaiyi ai nasa ne ko? Da basu san kina da amfani ba sai yanzu? Babu ruwan ki, ki fita daga harkar"

Please Login or Register in order to submit comment