Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gyara inda na bata a kujerar ta, sai kuma ta zaunar dani ta sake yi min bitar wankan tsarki da sauran abubuwa da suke shafi haila, ta kama kunnena tace "babu wasa da maza daga yanzu, babu wasa da Sadauki" nayi kyar kara sannan ta cika min kunne na. A lokacin Sadauki ya shigo yace "ya naji ana ambatar sunana?" Sai kuma ya kalli irin zaman da mukayi yace "hirar me kuke yi ne haka?" Na tabe baki zan saka masa kuka ya juya yace "na fita, in tayi tsami zanji".

Sai da muka gama maganganun duk da zamuyi da Ummah sannan tace min in tashi inje in gayawa Inna. Na zaro ido nace "Inna? Ni bazan iya gaya mata ba" tayi dariya tace "ai kuwa sai kin gaya mata. In baki gaya mata ba ke da ba'a gida kike zaune ba ta yaya zata sani?" Nace "dan Allah Ummah kije ki gaya mata" tarike baki tace "ni? Babu ruwana, ke zaki gaya mata da bakin ki" naji duk hankalina ya tashi, sai tace "bara in baki shawara. Kinga, yanzu ki tafi dakin ta, ki saka pad a jikin pant ki ajiye akan gado inda tana shigowa zata gani. Da kinji ta taho sai kiyi sauri ki shiga toilet ki buya".

Haka nayi kuwa, na ajiye akan gado sai da naji ta taba kofa sai nayi sauri na shige toilet. Na jima aciki,a tunani na ta fita sai na fito ai kuwa sai gata azaune a kan gado ta tasa pant dina a gaba, nayi sauri zan koma toilet tace "ke! Zo nan" na dawo ina karkarwar jiki na tsaya. Ta nuna pant din tace "wannan na waye?" A hankali nace "nawa ne" sai kuma tayi shiru tana kallona sannan tace "yaushe kika fara?" Nace "dazu" sai ta zaunar dani itama ta dora daga inda Ummah ta tsaya a nasiha da bayanan sabon yanayin dana samu kaina a ciki. Sai data gama sannan tace "saura kuma in sake ganin kun rike hannu ke da wancan bakin munafikin".

Muna gab da komawa hutu exam din su Sadauki ta fito. Alhamdulillah, ya samu nasara sosai. Duk da dai ba distinction ya samu ba amma ya samu credits a duk subjects din daya kamata. Mukayi murna sosai. Sai da jamb ta fito sannan murnar mu ta koma ciki, yayi kokari nan ma, sai dai bai samu points din ake bukata ba a mechanical engineering wanda shine abinda yake so ya karanta. Ranar haka ya wuni ransa babu dadi, ni kuma harda kuka na zauna inayi masa, Ummah kuwa dariya tayi tace "wa kuka taba ganin ya samu abinda yake so lokaci daya? Kuje jami'ar ku tambayi daliban kuji wadansu da yadda suka samu admission din. Ko kuma ku samu mutumin daya ke da daukaka ya baku labarin yadda ya samu daukakar tasa. Babu wani abu mai kyau da ake samun sa cikin sauki".

Baffa yana duba takardar yace "babu komai Sadauki, kar ka damu, akwai next year ai insha Allah sai ka sake gwadawa. In the meantime kuma zan nema maka computer school kayi diploma kafin ka sake jamb din".

Ayi hakuri da wannan.
One love 😘❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Eighteen: Saghir

Assalamu alaikum masoya littafin Diyam. Kafin mu cigaba zan danyi wani jan hankali a game da masu cewa in bar labarin da muke akai yanzu in koma gurin Bassam da Diyam. Ina so ku fahimci wani abu, shi littafin nan gabaki dayansa labarin rayuwar Diyam ne da irin wahalhalun da tasha har ta kai stage din data hadu da Bassam, wanda kusan shine karshen labarin. Na fara ta can ne saboda ina so ku samu glimpse of yadda rayuwa ta juya mata saboda in kara increasing curiosity dinku.

PLEASE stop asking me to summarize and get back to labarin Bassam. This story is not about Bassam but about Diyam.

Shekara tazo ta wuce. Lokacin na cika shekaru goma sha uku shi kuma sadauki yana sha tara. A cikin ta babu abinda ya ragu sai ma karuwa da abubuwa suke yi a tsakani na da Sadauki, musamman yanzu da yake jin sa ya kara zama saurayi tunda gashi har ya kammala diplomar sa a computer science. Ya sake zana jamb, kuma wannan karon yaci abinda ake bukata din, sai dai kuma cikowar dalibai masu neman admission da kuma rashin hanya yasa ya gaza samun admission din, Baffa yaji takaicin wannan abin dan yana ganin hakan kamar gazawa ne daga bangarensa a matsayinsa na uba.

Ni kuma a bangare na, na kammala jss2 lokacin ina da shekara goma sha uku amma ina nan jiya i yau, babu abinda na kara a girman jiki sai dan tsaho da kuma hankali. A lokacin kam zan iya cewa duk wanda yake tare damu ni da Sadauki yasan something is going on, including Baffa, Ummah da Inna. Baffa baice komai ba, haka ma ummah, basu taba encouraging din mu ko discouraging din mu ba. Babban problem din, kamar yadda duk muka yi tsammani shine daga gurin Inna dan sosai take nuna kiyayyar ta ga tarayya ta da Sadauki.

Hutun da muka zo na third term din jss2, ina shiga palon Ummah hannuna rike da Asma'u da take ta murnar gani na, na tarar da akwati a ajjiye a kofar palo. Bayan na gaisheta nace "Inna wannan kayan fa?" Ta hade rai tace "naki ne, hutu zaki tafi" naji zuciyata ta buga nace "hutu Inna? Ban gama ganin ku ba fa ina zan tafi hutu kuma?" Ta harare ni tace "gidan Alhaji Babba zaki tafi, in muna son ganin ki mu zamu zo mu ganki" nayi ajjiyar zuciya a boye, dan dai sharada? Nasan Sadauki ko da adungure zai je ya ganni. Kwana na daya a gida na tafi sharada. Ni da Rumaisa ne zamu je muyi hutu a can yayin da Inna ta yi mana rakiya. Rumaisa tana ta murna saboda ita kam tana son zuwa gidan Alhaji Babba. Ni kuma ina yake saboda kar Inna ta harbo jirgina na plans din da mukayi da Sadauki.

Now, let's talk about Alhaji Babba da family dinsa.

Kamar yadda na fada Alhaji Babba shine babban yayan su Baffa, shi ya fara zuwa Kano neman kudi kuma a lokacin yafi dukkansu dukiya, dama baffan mu ne baya. Allah ya jarrabi Alhaji Babba da mugun son yaya maza sai kuma ya hana shi su, wannan yasa ya kasance mai aure aure duk a tunanin sa da burinsa hakan zai saka ya samu cikar muradinsa. Matarsa ta farko yar uwa ce daga Kollere, ya daya ta haifa masa Adda Zubaida, daga nan bata sake haihuwa ba sai ya auri Hajiya Babba wadda tashin farko ta haifa masa muradinsa na ɗa namiji wanda muke kira da hamma Saghir. Hajiya Babba jinin sarautar kano ce, hamshakiyar macece mai mulki da izza wadda hatta kishiyoyinta inka gansu a gabanta zaka iya dauka cewa yaranta ne. Bayan shi ta sake haihuwar mata biyu, Aysha da Salma. Daga Hajiya Babba kuma sai Hajiya Yalwati wadda tafi duk sauran matan yawan yaya kuma wannan shine kadai abinda yake zaune da ita a gidan. Hajiya Yalwati kawar Inna ta ce dan haka duk sanda muka je gidan a dakinta muke zama, kuma nima saboda babbar kawata a gidan, Murja, yar Hajiya Yalwati ce dan haka nima na zama yar dakinta. That plus daga ni har Inna babu wanda yake iya jurar mulkin Hajiya Babba. Sauran vacant space din guda daya kuma na mai rabo ne, wannan ta shiga wannan ta fita.

Hamma Saghir shine da daya tilo da Allah ya bawa Alhaji Babba, dan haka zama bayyana cewa dan gata ne bata lokaci ne. An haife shi tun kafin Baffa na yasan zai auri Inna ballantana a haife ni, dan a lissafi ya bani shekaru goma sha shida da watanni. A kullum idan naji mata suna lissafa siffofin mijin da suke so su aura sai inga kamar lissafin kamannin hamma Saghir suke yi, fari, dogo, kyakykyawa, mai saje, marar son surutu, mai kudi, mai class blablabla. Hamma Saghir is all that and more. Labari ya zo min cewa makarantar da hamma Saghir yayi ma kanta daban take da ta sauran yaran gidan dan Alhaji Babba cewa yayi "a samo min makarantar da yayan masu kudi suke zuwa a garin nan, ita zan saka Saghiru" a haka yayi primary da secondary dinsa, sannan aka saka shi a buk yayi degree a economics ya fita da pass. Alhaji Babba yace "ba wani abu, dama an saka ka a makarantar ne saboda ka samu ilimin juya dukiya ba wai dan ka nemi aiki da takardun ka ba". Sai kuma Alhaji Babba yayi masa irin abinda Hardo yayi masa shima. Ya debi dukiya msi yawa ya bashi yace "tafi ka nemi arzikin ka" Saghir ya gyara zama yace "China zan tafi Alhaji, tunda can ne cibiyar kasuwanci ta duniya a yanzu. In naje sai in nemi Company in saka hannun jari a ciki. Maybe kafin shekara sai kaga nazo na bude nawa Companyn"

Haka ya shirya aljihu fal kudi ya tafi China, daga nan ba'a kara jin labarinsa ba har sai da ya shekara uku sannan sai gashi ya dawo daga shi sai jakar kayan sa yace "yan damfara na hadu dasu Alhaji, gaba daya kudina sun salwanta da kyar na tsira da kudin jirgi na dawo gida" Alhaji Babba yace "kasuwanci ya gaji haka dama, yau riba gobe faduwa hakan kuma ba zai saka mu karaya ba" sai ya debi wadandu kudaden ya kuma bashi, shi kuma ya karba yace "Dubai zan tafi wannan karon inke saro kaya ina aikowa dasu gurinku kuna siyar min". Wannan karon ma tunda ya tafi ba amo ba labari ko waya babu, amma sai iyayen suke boyewa kullum suna nuna kamar yanayi musu waya "abubuwa ne suka yi masa yawa amma yace yana gab da zuwa gida". Yazo gidan kuwa bayan shekara biyu, sai dai wannan karon ko akwatin kayansa bai dawo dashi ba ballantana kudi "Dubai bata karbe ni ba Alhaji. Kudi na gabaki daya sun salwanta ba bu abinda ya rage a hannu na" Alhaji Babba yace "kasuwanci bai karbe ka ba Saghiru. Dole sai mun zauna munyi maka adduoin neman sa'a sosai. Kuma ina kyautata zaton akwai nasara sosai a rayuwar ka shiyasa kake samun tangarda" Hajiya tace "musamman ma shi da yake da tarin makiya, gaskiya kam sai an hada da addu'a".

Bayan an gama rarraba wa malamai kudi sunyi adduoi, sai kuma Alhaji yace "gwara ka zauna a kasar nan saboda muke ganin abinda kake yi muna kuma baka shawara" amma sai Saghir yace "gaskiya Alhaji ko zan zauna a kasar nan to ba'a Kano ba, saboda anan an saka min ido dayawa". Haka rayuwa ta cigaba masa, yau yana wannan garin gobe yana wancan duk da sunan neman kudi, in kudin hannunsa sun kare ya dawo Kano ya karbi wadansu ya kara mai.

Tunda nake bazan iya cewa ga ranar da hamma Saghir yazo gidan mu ya gaishe da Baffa wanda yake kanin babansa ba ballantana Inna da take cousin din babansa kuma matar kanin babansa. Ni kaina ganin da nayi masa a duniya a lokacin bashi da yawa sai dai a jikin katon hoton sa dake kafe a main palon gidan.

A ranar da muka je gidan, kamar yadda muka saba, part din Hajiya yalwati muka fara zuwa muka ajiye kayayyakin mu muka huta sannan muka fita muka zagaya muka gaishe da sauran matan gidan. Bayan mun dawo palon Hajiya Yalwati ne Inna take tsokanar Murja "Murja ya na ganki a daki ne yau kamar matar kulle? Tunda muka zo gidan nan banga kin fita ko babban palo ba?" Hajiya Yalwati tace "uhmm ina zata fita taje, boss din su yana gidan? Tun safe nace musu suyi zamansu a daki kar wadda ta fita in ba haka ba sai kiga an dawo da kumburarriyar fuska ya kama su ya mara, komai akayi ai shi laifi ne a wajensa, magana ma mai karfi in sunyi cewa zaiyi sun hana shi bacci duk ya hada su yayi musu duka. Kuma ban isa inyi magana ba" Inna tace "wai Saghir kike nufi? Yazo garin kenan. Oh ni yaushe rabon da inga Saghir?" Kamar da hadin baki kuwa sai gashi ya shigo palon. Ya dafa kujera daga tsaye yace "Hajiya barka da gida" Hajiya Yalwati tayi yake tace "Barka kadai Saghir, anzo lafiya" yace shortly "lafiya lau" sai ya juya zai fita, Hajiya Yalwati tace "ga gwoggonka fa, gwoggo Aminan baffa Usman" ya dan juyo yana shafa kai yace "lah gwoggo ai ban lura ba. Ya gida? Ya Baffa?" Inna tayi murmushi tace "lafiya lau Saghir, ya kasuwa? Allah yayi jagora" yace "ameen" sannan ya fice ba tare daya ko kalli inda muke zaune ni da Rumaisa muna kokarin gaishe shi ba.

Yana fita Inna ta juya tana kallon Hajiya Yalwati tace "kai masha Allah. Saghir ya zama babban mutum sosai" Hajiya Yalwati ta tabe baki tace "eh fa. Yo mutumin da yake kokarin cika shekara talatin a duniya ai kuwa dole a kira shi da babba. Ni in dai gatan gaskiya kuke yi masa ma aure ya kamata kuyi masa maybe ko ya haifa muku jika namiji" Inna tayi dariya tana tafa hannu, Hajiya Yalwati tace"a'a to bai isa auren bane ba? Ko dai kuyi masa aure wallahi ko kuma ya dauko muku abin kunya dan duk abinda yake aikatawa a garuruwan da yake zuwa muna sane, in munyi magana kuma ace hassada muke yi masa" Inna ta watso mana harara ni da Rumaisa, sum sum muka tashi muka basu guri dan munsan ma'anar hararar.

Muna fita Rumaisa tace "zo mu tafi palon Hajiya Babba" na makale "ke ni bana son zuwa gurinta tayi ta mulka mutane tana kallonsu sama sama" ta kuma jan hannu na "dalla can kizo muje, wani abu zan nuna miki". Muka je muka sameta a dan karamin palonta tana kishingide yar aikinta tana yi mata tausa. Muka sake gaisheta sannan muka zauna a gefe muna kallon tv. Muna zaune ya shigo, yana shigowa na kama hannun Rumaisa da niyyar ta tashi mu basu guri amma sai ta rada min "ki bari muyi kallo" na koma na zauna na zubawa tv ido. Ya zarce gaban Hajiya ya zauna. Tace "kaje duk ka gaishe su?" Ya yamutsa fuska yace "naje" sai kuma yace "Alhaji har yanzu bai fito bane?" Tace "na gaya maka ai baya jin dadi ya kwanta. Wani abu kake bukata?" Yana shafa kai yace "dama kudi nake nema, akwai wasu kayana da aka kawo min daga porthercout shine nake so inje in karbo" tace "kaje drawer ta ka gani ko zasu ishe ka" ya mike zai tafi Rumaisa tayi sauri ta gaishe shi, ya dan bata rai yana kallon ta sannan ya amsa, wannan yasa nima na gaishe shi, ya amsa a ciki ciki irin irritatingly dinnan. Hajiya tace "ba ka gane Diyam ba" ya juyo ya kalle ni yana yamutsa fuska yace "bangane taba. Yar uwar mu ce?" Hajiya ta danyi dariya tace "Diyam fa, babbar yar baffan ka Usman" ya danyi shiru sannan yace "ohh, that little baby da akayi jegon ta anan? Wannan mai cika mana gida da kuka?" Hajiya tayi dariya tace "ita fa" ya dan karkata kai yana kare min kallo sannan yace "sam ban gane ta ba. Bata kama da iyayenta" Hajiya tace "ai kuwa Diyam kamar su daya da innar ta, dan karamin jikin ne dai ta dauko na babanta" ya sake kallo na yace "no Hajiya, gwoggo Amina ai kyakykyawar bafulatana ce, wannan kuma sai naga tana min kama da bararoji" gaba dayan mu sakin baki mukayi muna kallon sa har hajiyan, tace "bararoji kuma Saghir? Diyam kuwa ai kowa yana yaba kyanta" ya sake kallona sannan ta tabe baki yace "still, ni ban gani ba".

Another character added. Saghir. Tell me your feelings about him[1/18, 9:45 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Nineteen: Inna

Haka ya shige daki ya bar mu da budadden baki. Na kamo hannun Rumaisa muka fito da sauri.muna fitowa nace "what? Lallai ma mutumin nan" Rumaisa tana murmushi tace "ya hadu ko? Shi yasa nace miki kizo muje mu ganshi" nace "au wai kina nufin saboda mu ganshi kikajawo ni dakin nan? Meye abin kallo a gurinsa? Wai dan wulakanci nice bararoji" Rumaisa tayi dariya tace "au wai haushi kikaji? Ke baki san wasa ba? Wasa fa yake miki dallacan" na bata rai nace "it doesn't look like wasa yake min, har cikin ransa abinda yake nufi kenan" Rumaisa ta bagarar da maganar tace "to ya kika ganshi? Ya hadu ko?" Na tabe baki nace "ko kusa da haduwa baije ba" tace "ko dai don idonki ya rufe, Sadauki ya tare gaba ya tare baya" nayi murmushi ina jin sanyi a raina nace "yanzu kika kamo hanya yar gari" ta bani hannu muka tafa. Rumaisa ita kadai ce wadda nake zama muyi hirar Sadauki sosai da ita, tasan komai akan yadda muke ji a zukatan mu. Muka samu guri muka zauna, na bata labarin tsarin da mukayi da sadauki na cewa zai ke zuwa zance gurina a matsayin saurayina. Ta rike baki tana zaro ido tace "Diyam? Ba kwajin tsoro? Ba kya jin tsoron a kama ku?" Nace "relax. Kinsan dai gidan nan akwai yammata da yawa ko? Kuma duk suna fita zance so babu wanda zai gane, he will be just one saurayi among others, kuma I will make sure duk wanda yasan fuskarsa bai ganshi ba, ballantana kadan ne a gidan nan suka sanshi".

Ranar da Sadauki ya fara zuwa gurina a ranar na bashi labarin encounter dina da hamma Saghir. Ya bata rai yace "kar ki sake shiga harkar sa, duk hanyar da kika san yana bi ma karki kara bi ta gurin ballantana ya sake gaya miki wata maganar banzan". Duk sanda yazo zai gaya min next time da zai sake zuwa, dan haka ni nake fita da kaina in shigo dashi. A gefen dakin mai gadi muke zama, wanda yau da gobe sai muka zama very friendly dashi. Duk ranar da Sadauki yace min zaizo bai taba sabawa ba, koya wuce time din da yace zaizo to kuwa yan minutes kadai zai kara saboda traffic. A wannan lokacin na kara fahimtar cika alkawarin Sadauki, in dai yace zai yi abu to kuwa tabbas zaiyi din sai dai in wani abu ya faru beyond his ability.

Tun ranar da hamma Saghir yace min bararoji bamu kuma haduwa ba, nabi shawarar Sadauki dan haka ko muryarsa naji a guri to bana shiga, inkuwa tsautsayi ya biyo dani ta hanyar da yake to zanyi saurin chanza hanya. Rumaisa ce mai nacin zuwa gurinsa wai burge ta yake yi. Sai ranar nan bayan nayi ten days a gidan, muna tafiya da Rumaisa zata rakani in shigo da Sadauki sai muka hango Saghir a can packing lot, yasha farin voile sai kyalli yake yi kuma daga inda muke muna jin kamshin turarensa sannan muna jin muryarsa yana ta sirfawa baba audu zagi akan wai bai wanke masa motar daya saka shi ba, dan tsohon Allah sai hakuri yake bayarwa kansa a kasa amma kamar kara zuga saghir yake yi "tsabar iskanci da rashin mutunci wajan awa guda kenan nace ka wanke min mota ta amma saboda ban isa ba shi yasa kaki wankewa ko?" Baba Audu yace "kayi hakuri yallabai, Alhaji ne ya saka ni in gyara masa gurin da yake shan iska yana so ya fito anjima" yace "dalla yi min shiru, wallahi in kayi wasa kafin in koma porthercout sai kabar gidan nan. Ka kiyaye ni wallahi" dan dattijo ya durkusa yana ta bada hakuri. Ban san lokacin da naja wani uban tsaki ba, Rumaisa tayi saurin toshe min baki ta jani bayan flowers "rufa ma kanki asiri Diyam. Tsaki? Hamma Saghir? Wallahi in yaji ki zai balla ki" nace "ai kuwa daya gane cewa shayi ma ruwa ne" ta girgiza kanta tace "Sadauki ne dai takamar ki ba wani ba, amma kiyi tunani, do you really want to get him involved with hamma Saghir?" Na juya ina kallonsa, tabbas Sadauki na is very brave and fearless, amma saghir is not his match dan at least ya bashi shekaru goma, ga kudi ga kuma gata. Dan haka hada shi rigima da Sadauki will be like putting Sadauki in trouble. Na ja bakina nayi shiru sannan muka zagaye ta bayan sa muka fita daga gidan.

Sai three days to resumption date din mu sannan Baffa yazo da kansa ya daukeni zuwa gida. Matan gidan sun hada min goma ta arziki wai tsarabar boarding. Amma ni sai naji duk boarding din ta fara isata amma inaji inagani haka aka daukeni aka mayar dani. Sanda muka dawo next holiday shima ina zuwa na tarar da kaya na a ajiye, ban damu ba na shiga harkokina ina tunanin ai sharada ba nisa amma sai naga inna tana hada nasu kayan ita da Asma'u tace "Kollere zamu tafi, mun kwana biyu bamu je mun gaishe su ba musamman yan uwana da muke uba daya nan take naji bakin cikin duniya ya ishe ni amma haka Baffa ya debe mu a mota gabaki daya har su Ummah muka tafi, naji dama dama saboda ganin da Sadauki ne, amma bayan munje mun kwana daya a gidan Hardo da sabuwar matarsa sai naga su Baffa suna shirin komawa suna ta sallama da mutane, na bishi soro da gudu na rungume shi ina kuka nace "Baffa dan Allah zan biku mu koma tare" ya rike fuskata yace "kiyi hakuri uwata, ba tare daku zamu koma ba ku zaku zauna ku zagaya yan uwan innarku na gurin babanta" ai kuwa a take na kara wani kukan dan ni in akwai abinda bana so a lokacin to zama a Kollere ne. Suka tafi, Baffa da Ummah da Sadauki, suka barmu ni da Asma'u mun rike juna muna kuka, Inna ta tabe baki tace "sai suje ai suci uwar da zasu ci a gidan".

Mune daga wannan gida mu koma wancan mu kwana anan mu tashi anan muna ta ziyarar yan uwa har sai da muka yi sati biyu, Asma'u ta dan ware amma niko alamar warewa banyi ba, ranar da muka cika sati biyu Baffa yazo daukarmu ashe wai yayi wa inna waya akan mu shirya zaizo mu tafi ita kuma taki. Yana zuwa ta lissafa masa sauran gidajen da bamu je ba shi kuma yace baisan magana ba, "Diyam makaranta zata koma nan da sati daya, kamata yayi taje gida ta huta tukunna" Inna tace "wanne hutu zatayi a gidan? Taje dai gida mayun gidan su cigaba da lasheta" Baffa ya gyada kai yace "in har mayun gidan basu cinyeta ba a tsahon wadannan shekarun, to kuwa ke a garin wannan yawon naku zaki kaita gurin mayun" nan take sai rigima, inna tace ai Baffa yace yan'uwanta mayu ne. Hardo ya goya mata baya yace "to in bata kaisu sunga yan'uwanta yanzu ba sai yaushe?" Wannan yasa Baffa ya shiga motarsa yayi tafiyar sa, yace duk sanda muka gama yawon ma taho a motar haya.

Bamu koma ba sai two days to komawa ta makaranta, dan haka a gurguje na shirya shima kuma dan na samu Ummah ta fara harhada min wasu kayan kafin inzo. Dan haka wannan hutun ni da Sadauki sai gani da ido.

A hutun second term ne Baffa ya buga kafarsa yace babu inda zanje hutu, shima yana so ya zauna dani. Nan take rikici ya balle a gidan mu, Inna ta fito da abinda yake zuciyarta na kiyayyar ta a dangane da dangantaka ta da Sadauki, tace "sai dai bayan raina wallahi, wannan yarinyar indai ni na haife ta ba zata auri wannan yaron ba" Baffa yace "saboda me? Menene dalilinki na cewa haka?" Tace "Saboda bana sonsa, na tsane shi tamkar yadda na tsani uwarsa kuma bazan taba yarda in hada jini na da nasu ba" Baffa yace "to shikenan dalilin naki? Kishi ne kawai dalilin naki? To kuma in Allah ya riga ya rubuta akwai aure a tsakanin su fa? Fada min ya zakiyi?" Tace "sai in sallama ta, in dai ta aure shi to babu ni babu ita har abada sai dai ta nemi wata uwar

Please Login or Register in order to submit comment