Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mayafinta tace "bara in fita in je gidan da kaina" har ta kai bakin kofa kuma sai ta juyo "babu komai idan na tafi na barta ita kadai?" Nurse din tace "babu komai, allurar baccin ma zan sake yi mata. Amma kiyi sauri, in babu kudin ma ki samo maza wadanda za'a iya dauka a jikin su" Inna ta sake kallo na sannan ta fita da sauri. Nurse din tazo kaina tana zuko allura tace "ki godewa Allah yarinya, you are very lucky" tana yi min allurar na tambayeta "ina babies din dana haifa?" Ta girgiza kai tace "ban sani ba gaskiya, ke kadai aka kawo ki nan tun cikin daren jiya" daga nan bacci ya dauke ni ina wandering ina babies dina?.

Sanda ma kuma farkawa Inna na gani tana waya tana kuka "wallahi Hafsa babu ko dari a hannuna a yanzu, gashi suna ta tsorata ni da yana yin jikin nata. Naje gidan babu wanda ma na samu duk sun tafi asibiti gurin Alhaji" naji kamar kaina ya kara nauyi,nayi kokarin daga hannuna naji shi kamar ba a jikina yake ba, eyelids dina ma kansu sunyi nauyi. Na sake cewa "Inna" ta ajiye wayar da take yi ta taho gurina da sauri ta rike hannuna "sannu Diyam, Allah zai dube mu kinji? Allah zai dubi maraicinki ya bamu yadda zamuyi".

Kamar amsa maganar ta sai ga wani doctor sun shigo shida nurse, hannunta dauke da ledojin jini guda biyu tazo da sauri ta fara kokarin dauka min. Inna ta mike "jini? A ina aka samu jini" kana jin muryar ta zaka fahimci wani relief a ciki. Doctor ya juyo yana kallonta yace "ba ke kika kirawo wani dan uwanku ba?" Tayi saurin girgiza kai, "ni ban kira kowa ba, ban samu kowa ba da naje gidan" doctor yace "but baki dade da fita ba wani yazo yace dan uwanku ne, mun dauka ke kika turo shi, yace a debi jininsa, kuma muna aunawa muka ga yayi matching, shi leda ukun ma yaso bayarwa mu muka ce kar ya zama affected shi kuma. Ya biya dukkan bills dinku na gado da kudin magunguna duk mun rubuta masa ya biya har da kari wai ko wani abin zai taso" Inna ta koma ta zauna akan kujera "to waye wannan kuwa?"
Nurse din tace "Halima Usman Kollere dai yace yana nema. Ya shigo nan ma ya tarar tana bacci sai ya fita". Inna ta rasa bakin magana.

Nurse ta gama daura min jinin ta juya suka gama rubuce rubuce ita da doctor sannan suka fita yayin da Inna ta zauna tana ta jera addu'a zuwa ga savior dina. "Allah ya bashi abinda yake so duniya da lahira. Yadda ya bude mu Allah ka bude shi shida zuri'arsa, Allah ya biya shi da gidan aljanna" na gyara kwanciya ta ina kallon window, dare ne, meaning na kwana na wuni kenan da haihuwa. Ina 'ya'ya na?

Washegari sanda na farka naji muryar Mama suna magana da Inna, sai kuma hayaniyar su Asma'u da Muhsina. Na bude ido ina kwallon su, they looked like twins, ina twins dina? A tare suka taho gurina suna rige rigen rije hannuna, nayi musu murmushi ina shafa kawunansu, Mama ta taso itama "sannu Diyam, ya jikin naki?" Nayi gyaran murya nace "da sauki Mama" tayi murmushi tace "naji dadin yadda na ganki, da duk hankali na ya tashi, ai mun auna arziki sosai" Inna tace "gashi kinga har ta fara sabewa, amma jiyan nan duk a kunbure take. Wannan mutumin Allah ya biya shi da aljanna" Mama tace "ni nafi tunanin irin masu bin asibitin nan ne suna taimaka wa mutane, maybe ya tarar ana zancenta shine ya nuna kamar dan uwane, tunda dai kinga yanuwan duk mun tambaya sunce basu bane ba". Ni dai ina jinsu ina jiran inji sunyi hirar jarirai na amma shiru. Tare suka kamani suka tashe ni tsaye, na tashi da kyar ina cije lebe, sannan Mama ta hada min ruwan zafi sosai ta kaini toilet da kanta ta gasa min jikina ta kuma saka na shiga ciki. Muna fitowa take ce da Inna "ashe bata karu ba" inna tace "eh fa, haka nurse tace min. To ai yaran ne baki gansu ba yan kanana dasu, ni ko a bakwaini ban taba ganin masu kankantar wadannan ba" Mama tace "Allah sarki. Allah yasa masu ceton ta ne" gabana ya fadi, na juya ina kallon Mama sai naga duk jikinta yayi sanyi, na saki cup din tean data miko min na rufe fuskata da hannayena. Tayi sauri tazo ta rungume ni a jikinta tana jijjiga ni kamar yarinya "kiyi hakuri Diyam, Allahn da ya baki su shi zai baki wadansu. Kuma yayi alƙawarin aljanna ga duk iyayen da ya karbi ran yayansu suka yi hakuri" na kifa kaina a kafadarta nayi ta kuka, sai naji duk ciwon jikin da naje ji ya barni dan wanda nake ji a raina yafi na jikin ciwo. Sai naji muryar da naji jiya ta cewa ban mutu ba ta koma, naji tamkar rayuwa bata da amfani a gare ni. Na rufe idona ina tuno their cute little faces.

Sai da suka samu na tsagaita da kukan sannan suka saka ni a gaba na basu duk labarin abinda ya faru. Gabaki daya suka dauki salati. Inna tace "amma dai Saghir ya cika makaryaci, cewa fa yayi ita ce ta shiga daki ta rufe kofa sai daya ji shiru ya balla kofar ya shiga ya same ta a haka" na matso hawayen idona nace "wallahi karya yake yi. Shi ya kashe min yara na. Ta sanadiyyar shaye shayensa suka rasa rayuwarsu, bazan taba yafe masa ba wallahi". Mama tace "duniya ce Diyam, ki barshi da duniya ta ishe shi darasi shi da iyayen nasa dukka. Tun yanzu ba gashi nan sun fara gani ba" Nace "me ya faru?" Mama tace "ai daya gama mayen nasa ya farka ya ganku shine ya dauko ku babies din ko cibiya ba'a yanke ba ya taho daku gida a gigice, a nan aka jere wa Alhaji Babba su a gabansa innarki kuma Saghir din ya dauko ta tare dake ya kawo ku nan, dan wulakanci kuma babu wanda yayi kara ya biyo ku su ta yayan da suka riga suka mutu suke yi. Sai gashi Saghir yana kawo ku nan aka kira shi wai kuma gobara ta tashi a kantin kwari, shagunan Alhaji Babba gabaki daya sun kone kurmus babu abinda aka fitar, yanzu dai Alhaji ya yanke jiki ya fadi, hawan jini ya tashi, har yanzu yana asibiti unconscious".

Na karbi tean da Inna ta sake hado min na kurba ina jin zafinsa yana kona min bakina. A raina sai nayi wani tunanin irin hikimar ubangiji da take cikin haihuwar wadannan yaran, sannan kuma na saka a raina cewa mutuwar su tamkar wata sabuwar jarabawa ce a gareni, kuma nayi niyyar yin iyakacin kokarina wajen cinta. Twins dina sunzo sun tafi, ko picture dinsu bani dashi sai wanda nayi saving a memory na, kuma bazan taba mantawa dasu ba har in tafi inda suka tafi.

Kwana na biyar a asibitin na warware sai abinda ba'a rasa ba, sai dai something is bothering me deep inside sai dai na kasa magana a kansa. Ina zaune ina cin abincin da Inna ta zuba min ne ina tunanin yadda rayuwata take, kaddara upon kaddara haka take samu na and I wondered wacce kaddarar ce kuma next.
[2/4, 11:21 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman maama

Episode Thirty Five : A Glimpse

Yan uwa da yawa sunzo sun duba ni kuma sunyi min gaisuwar twins dina. Aunty Fatima tazo har sau biyu ita da yaranta, Adda zubaida tazo itama, sai daga baya sai ga kawu Isa nan yazo shida iyalinsa, sai a lokacin yake tambayar inna nawa ne kudin asibitin? Tace masa kawai an biya shikenan sai ya bar maganar ba tare da yaji yadda aka yi aka biya din ba ko kuma waye ya biya ba.
Da dare sai ga Hajiya Babba ita da wannan sister din tata, amma babu Saghir babu alamarsa, su inna suka karbe su babu yabo babu fallasa sannan suka tambayesu jikin Alhaji. Sunce yana asibiti har lokacin amma yana samun sauki sosai. Suka kawo min maltina da fruits. Na gaishe su sai Hajiya Babba tace "Diyam, banji dadin abinda kika yi ba ko kadan wallahi, kinga abinda ya jawo ko? Garin kiyayyar Saghir an kusa a rasa rayuka har hudu" Mama da dama kamar jira take yi tace "me Diyam din tayi" Hajiya Babba tace "innarta bata gaya miki ba? Saboda bata son Saghir bata son haihuwa dashi shine ta shiga daki ta rufe kanta wai gwara ta mutu ita da yayan baki daya, gashi nan yanzu yaran da basu ji ba ba su gani ba sun rasa ransu, ga kakansu can kuma rai a hannun Allah. Dan ma Saghir mai taurin zuciya ne da har dashi zamu hada muyi jinya" naji raina yana min zafi, hawaye masu zafi suka kawo a idona, na yunkura zanyi magana Inna ta dakatar dani tace "kar kice komai" ta juya gurin Hajiya Babba tace "wannan magana ce da Saghir ya fada, ita kuma Diyam ba haka ta gaya mana ba tace a gaban Saghir ta haife yara guda biyu yana sheka uban bacci, babu irin tashin da bata yi masa ba amma ko motsawa baiyi ba" sai sukayi dariya duk su biyun, yar uwar Hajiya tace "kuma yanzu ku da hankalin ku sai kuka yadda da wannan maganar? Wanne irin bacci ne mutum zaiyi har a haihu a gabansa bai san anayi ba?" Mama tace "baccin wadanda suka sha suka bugu mana? Wadannan kam aiko yanka su zakayi sai dai su farka su gansu a lahira" sai kuma suka daina dariyar, Hajiya Babba tace "Hafsa? Wacce irin mummunar magana ce kike jifan dan dan'uwanki da ita?" Inna tace "ba mummunar magana bace ba, gaskiyar magana kenan. Saghir shayeshaye yake yi, kuma wannan shayeshayen shi yayi sanadiyar mutuwar wadannan yaran. Wannan shine gaskiyar magana" Hajiya Babba ta juyo kaina, fuskarta babu annuri ta nuna ni tace "Diyam sakayyar soyayyar mu gare ki kenan? Sharrin da zaki yiwa dan uwanki kenan?" Na girgiza kai na nace "ba sharri bane Hajiya, in baku yarda da magana ta ba ku je gidan ku bincika, ku duba dakinsa na tabbatar ba zaku rasa kayan maye ba, ku duba motarsa ba zaku rasa kwalbar giya ba, in still baku yarda ba ku tambayi uwani ta baku labarin yadda ta kwace ni rannan a hannunsa wanda shine dalilin fara nakuda ta ba tare da lokacin haihuwa yayi ba, in still baku yarda ba ku tambayi mai gadin gidan, ai yana ganin dawowarsa gida kullum a buge yake shigowa" sai suka hada baki suna tafa hannaye suna salati "kuji yarinyar nan yar karama da ita amma ta iya shirya magana irin wannan? Ku kuma iyayen ta kuka hau kai kuka zauna dan kun zama butulu ko? Duk kun manta irin alkhairin da Alhaji yayi muku amma shine yanzu saboda abinda ya same shi har zaku juya masa baya ku dorawa tilon dansa sharrin shayeshaye? Dan kunga Alhaji iftila'i ya fada masa shine zaku juya mana baya?"

Sai ta kama kuka yar uwarta tana rarrashinta. Mama da Inna duk suka tsaya suka saki baki suna kallonta. Sannan Mama tace "Hajiya saratu in kika ce haka baki kyauta mana ba, da Diyam da Saghir duk yayan mu ne amma dole a cikin su in wani ya kauce hanya zamu fada dan gyaransa ba wai dan bata masa suna ba. Bincike ya kamata ayi kamar yadda Diyam tace, wanda duk aka samu da laifi a cikin su sai ayi masa fada dan ya gyara laifukan sa" sai suka tashi cikin fushi suka fice daga dakin. Mama tazo ta zauna kusa dani ta goge min hawayen fuskata tace "kiyi hakuri Diyam, in dai shayeshaye halin Saghir ne wata rana zai yi ne a gaban jama'a yadda babu wanda zai musa". Ni kam zuciyata zafi take yi min, an jima ba'ayi min abinda ya kona min rai kamar wannan ba, ya Saghir zai kala min wannan sharrin? How can they accused me of killing my own babies?

Washegari da safe Hajiya Yalwati tazo itama, tayi ta bawa inna hakuri wai abubuwa ne suka sha kanta ga Alhaji a kwance ga yara ga gida babu kudi. Sai Inna ta bata labarin yadda mukayi dasu Hajiya Babba jiya, sai tace "dalla rabu dasu, waye baisan Saghir yana shaye shaye ba? Amma su kullum sai su ke nuna kamar ba'a sani ba. Yanzu shima uban da ace lafiyar sa kalau kuna gaya masa zai musa". Da daddare muna zaune Inna tana ta mitar cewa tunda muka zo asibitin Saghir bai ko kira waya ya tambayi jikina ba, bai bada ko kwandala ta magani ba bai kuma nemi yaji inda muka sami kudin maganin ba. Tace "wannan wanne irin aure ne?" Na dauke kaina dan bani da amsar da zan bata. Bayan mun kwanta na yi mata tambayar da take raina. "Inna Sadauki kuwa ko yasan bani da lafiya? Yanzu shi ko duba ni ba zai zo yayi ba ballantana yayi min gaisuwar wadannan yaran? In babu aure tsakanin mu ai akwai shakuwa ko? Shi din tamkar yaya yake a gare ni" sai tayi shiru kamar bata jini ba, sai can tace "Diyam bansan inda Sadauki yake ba. Yaya ladi ma da naje nemanta gidan Alhaji Bukar ance min ta tashi kuma basu gaya min inda ta koma ba" na mike zaune nace "nemanta kikaje yi inna?" Tace "eh, naje nemanta da niyyar in bata gadon zainabu na gidan ku kamar yadda kika bani shawara amma ban same ta ba. Bansan ya zanyi ba yanzu". Nayi ajjiyar zuciya kawai ina wondering what happened? Ina Sadauki? Ko yana bornon? Ya samu admission din kuwa ko bai samu ba? Is he doing well? Na lumshe idona ina hangen fuskarsa a cikin kaina.

Washegari bayan an gama duk tests din da za'a yi suka sallamemu, muna shirin tafiya sai ga mutanen gidan Alhaji Babba nan sunzo, har da saghir, a lokacin ne suka fada mana an sallami Alhajin shima jiya, Hajiya Babba tana ta wani yayyatsina tana bata fuska, shi ogan ma a bakin kofa ya tsaya ya gaishe da Inna sannan yace min "sannu" na tattara shi na bawa iska ajjiyarsa. Budar bakin Hajiya sai cewa tayi "amma Diyam gidan ta za'a mayar da ita ba ko?" Inna ta tsaya tana kallon ta tace "ban gane ba" Hajiya tace "ina ganin abinda yafi shine ta zauna a gidanta, sai a tura wata matar haka take kula da ita kafin jikinta yayi kwari saboda kinga shi Saghir kinga babu dadi a barshi shi kadai a gida ba mace" Inna tace "haka ne" sai ta yafa mayafinta ta kama hannuna muka mike, ranta ya baci sosai. Tace "shi Saghir din yasan yana da matar amma tunda ta kwanta kwana bakwai bai waiwayo inda take ba? Shi Saghir din shin anyi masa fada akan abinda tace yanayi ko kuwa haka za'a kuma daukanta a mayar masa in yaso ya karasa kashe ta? Ina son Diyam fa nima ba wai bana sonta bane ba, ina kawaici ne kawai saboda karfin zumuncin da nake hangowa a tsakanin mu amma kuma kunsan wallahi da mahaifinta yana da rai ko soma maganar nan ma ba za'ayi ba ballantana ayi ta" Aunty amarya tace "haba Amina, yanzu kiri kiri a gaban mu kike nuna Diyam taki ce ba tamu gabaki daya ba, yanzu zumuncin har yakai haka tabarbarewa?" Na juya ina kallon Saghir har yanzu yana tsaye da hannayensa a cikin aljihunsa yana bin kowa dai dai da kallo, naji a raina ni kam ko inna ta yarda da komawa ta gidansa ni ba zan koma ba, gwara in shiga duniya yafi min sauki. Na zame hannuna daga na inna na fice daga dakin.

A bakin gate din asibitin na tsaya ina sharar hawaye, sai ga Inna da saurinta ta rike ni, "Diyam ya akayi kika fito ke kadai? Ina zaki je?" Na sunkuyar da kaina bance mata komai ba. Muna tsaye a waje suka fito, Saghir shi kadai ne a motarsa sai Hajiya tace ya dauke mu, nasan a lokacin da inna tana da kudi da ba zamu shiga motar Saghir ba amma dai haka muka shiga muka zauna a baya mu biyu, yana ta wani bata rai irin shi ba haka yaso din nan ba.

Ina zama na kwantar da kaina na lumshe idanuwana ina tunanin ta inda zan fara neman Sadauki, I just want to see him koda bance masa komai ba. Naji ya tayar da motar, sai naji Inna tace "Yakasai zaka kai mu" nayi saurin bude ido na ina kallonta, a raina nace 'finally' Finally Inna ta yi breaking out of her shell zata yi flying, to kawai yace mata ya dauki hanyar gidan mu. Naji mun tsaya na kuma bude idona sai naga traffic light ce ta tsayar damu a gefen asibitin, na dan sauke glass din windown da nake saboda in sha iska tunda babu ac, kamar daga sama naji kamar an ambaci sunana da muryar da ba zan taba mantawa ba, nayi saurin dago kai amma sai naga su inna kamar basu ji kiran ba, and then I smelled him, wani unique smell wanda daga gurinsa kawai nake jin sa, nayi saurin kallon window na and there he was, Sadauki, yana tsaye da hannayensa cikin aljihunsa yana kallona da budaddun idanunsa. Yayi loosing weight sai naga kamar ya kara tsaho, fuskarsa da kansa suna bukatar aski. Na zauna kawai ina kallonsa as the time froze and my heart stopped. He just stood there looking at me, sai kuma na kwalla masa kira "Sadauki!!" Inna ta juyo a tsorace ta riko ni tana tambayata lafiya, na juyo na kalleta sannan na juya da niyyar nuna mata sadaukin dana gani but ge was gone, as if yayi vanishing.

Kuka nake iyakacin karfina ina kiran sunan Sadauki yayinda Inna ta rike ni take tofa min addu'a, Saghir kuma yana bala'i duk da bana jin abinda yake cewa nasan akan kiran sunan Sadauki da nake yi ne ni kuma ban daina ba.

Manage this please
[2/6, 10:06 PM] +234 818 247 0922: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Thirty Six: Mother's Tears

Har muka je gida ina kuka na, though na daina yi da karfi sai ajjiyar zuciya nake yi. Ina jin Saghir yana cewa "wannan Sadauki dama naji ance dangin mayu ne, tunda kin kwallafa shi a ranki ba dole yake yi miki gizo ba? In kuma da gaske shi din kika gani Allah ya bashi sa'ar yi miki magana in nuna masa shi karamin dan iska ne" daga ni har inna ba wanda ya kula shi wanda hakan ya bani mamaki dan nasan inna bata wuce tayi in dai akan zagin Sadauki ne. A raina nace "kaji Saghir din nan da son a sani gaida uwar saurayi a kasuwa".

A kofar gidan mu yayi packing muka fito, na tsaya ina kallon gidan da yake holding so much memories, good memories, Inna ta dauko key a jakarta ta bude gidan ni kuma na dauko mana jakar mu zan wuce ciki naji Saghir yana cewa "anan zan barku ne naga kuna daukan kaya?" Ban kula shi ba sai Inna tace "eh" daga haka itama bata kara komai ba muka shiga cikin gidan.

Na tsaya a tsakar gida na jingina da bishiya ina karewa gidan kallo, ko ina yayi datti dukun dukun. Inna ta bude dakin ta ta shiga sai ta dauko key din dakin baffa shima tazo ta bude. Cikin dakunan basu yi datti sosai ba. Na zauna akan kujera ina tambayarta "Inna anan zamu zauna ko? Ba zamu koma gidan Alhaji Babba ba ko?" Eh kawai tace min sai ta dauki kayan shara ta tafi ta fara share dakin baffa. Na taso na biyo ta zan taya ta tace "ke da baki da lfy kiyi zamanki kawai" amma sai naki, tana share yana ni kuma ina karkade kurar kan furnitures, a haka muka gama gara cikin daki da palon sa, muka wanke toilet dinsa na palo sannan sai gasu Mama sunzo ita da yammatan ta da yake ranar weekend ne babu school, su suka karasa aikin tsakar gida da kitchen da garage. Dakunan umma kuma aka rufo su muka zauna a palon Baffa muka ci abincin da Mama ta taho mana dashi sannan Mama da Inna suka fita su kace zasu je gidan Alhaji Babba.

Bayan sun tafi ne Rumaisa take tambayata "Diyam, bani labarin yadda haihuwa take, naji Mama tana cewa kinyi kokari kin haifi yara biyu ke kadai babu taimako, ya kika ji?" Na girgiza kaina kawai, ni kadai nasan yadda naji, babu wanda zai gane kuma yadda naji din sai wanda ya tsinci kansa a irin hakin dana tsinki kaina. Ba kuma nayi wa Rumaisa fatan shiga halin da na tsinci kaina.

Sai bayan magrib su Inna suka dawo, sun debo duk kayan Inna da na Asma'u, amma duk naga rayukansu a bace suke daga dukkan alamu ba rabuwar arziki akayi ba. Asma'u ta shigo tana ta tsallen murnar dawowa gida, tace "Adda ina son gidan nan wallahi, nafi son muyi zaman mu anan dani dake da inna".

Washegari muka yi breakfast da yan kudaden da Mama ta bamu da zata tafi, bayan nan kuma sai Inna ta fita can sai gata ta dawo da dillaliya, suka shiga dakinta suna ta cinikin kaya ni dai ban bisu ba, daga baya matar ta fita sai gata ta dawo da maza suna ta jidon kayan dakin inna. Set din gadonta, set din kujerunta, kayan kallon ta kai hatta labulayenta sai da aka fita dasu. Katifar dakin mu ce kawai aka kawo nan dakin Baffa sai sauran tarkace kuma ta saka almajirai suka tattara ta zuba su a dakin soro. Sai aka share dakin kuma aka rufe shi. Naje na leka dakin Ummah ta taga naga yana nan yadda yake ko kayanta ba'a kwashe ba. Da daddare naga Inna ta zauna tana ta lissafin kudi.

Kafin sati ya zagayo mun samu tenants a gidan mu, sai akayi yar karamar katanga a tsakanin mu for privacy. Mata da miji ne da kananan yayansu guda biyu Iman da Saudat, da zasu tare sai sukayi fenti suka hada harda gurin mu suka yi mana. Matar mai kirki, irin masu son shiga mutanen nan ce dan tun da suka zo data gama abinda taje yi zata zagayo gurin mu muyi ta hira, in mijin ya siyo wa yayansa wani abu kuwa sai kiga ta dibo ta bawa Asma'u.

Kudin kayan da inna ta siyar, sai ga Mama tazo ta dauke ta suka fita sai gasu sun dawo da lodin kaya, tun daga kan shinkafa har zuwa ashana, sabulan wanka dana wanki kala kala, har da biscuits da sweets da bobo na yara, ta saka aka buga mata runfa daga gefe ta jibge kayan ni na dauka kayan amfanin mune har ina lissafin watannin da zamuyi muna amfani dasu sai naji ta tura Asma'u duk makotan mu ta gaya musu tana siyar da kaya. Kwanon shinkafa kanon fulawa, har gwangwani daya in kana so zata auna maka, manja man gyada barkono babu abinda Inna bata siyarwa. Ta mayar da Asma'u kuma former school dinta, da yake tsohuwar dalibar suce ba'a siya mata form da uniform ba kawai books aka siya mata sai kudin makaranta wanda a take Inna ta biya, Asma'u tana ta murna. Sai naji dadi dana bata wannan shawarar, na kuma ji dadi data dauka.

A bangare na kuwa tunda muka koma gida kullum sai wata makociyar mu ta shigo tayi min wankan jego, wankan runhu take yi min inyi ta kuka wai zafi amma ni kaina nasan inajin dadin wankan. Sosai na warware na dawo haiyacina karfina ya dawo jikina. Inna kullum tana diban kudi ta siyo min nama ta dafa minmai romo ta saka in chinye in shanye romon, ga tuwo zatayi min da dare da safe ta dumama min. Har addu'a nake Allah kar ya kawo karshen wannan zaman nawa. Amma ina....

Tunda muka zo gida babu wanda ya kara bibiyar mu a cikin yan uwanmu, Saghir ko mai kama dashi ban gani ba, hatta aunty Fatima bata

Please Login or Register in order to submit comment