Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matar kenan" yace "eh, a can gida ne. A Maiduguri ne" sai naji wainar dana ci duk ta tattaro ta dawo makogwaro na, da sauri na mike na shiga toilet sai da na amayo duk wainar da naci.
[2/19, 5:19 PM] +234 818 247 0922: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Seven : The Messages

Sai dana gama sannan na zauna akan toilet seat na dafe kaina, ina jin jiri yana juyani duk da cewa a zaune nake. Nayi iyakacin kokari na gurin ganin cewa ban yi tunanin maganar da Sadauki ya fada a palo ba sannan na mike na wanke bakina da fuskata na fita, ina tunanin ya riga ya tafi amma ina fita sai na ganshi a tsaye yana kallona yace "ba kya jin dadi ashe? Allah ya sawake" na sunkuyar da kaina ciki ciki nace "ameen" sannan na wuce shi zan shiga cikin daki Inna tace "ba kiji Sadauki yana miki sannu ba? Shine kika wuce ba zaki amsa shi ba?" Na juyo nace "Inna nace masa ameen, ameen, ameen summa ameen,me kuma yake so ince masa" sai kawai yayi murmushi ya juya ya fita, inna kuma ta rufe ni da fada Mama tana taya ta, na zauna kawai nayi tagumi da hannu bibbiyu ina jinsu har suka gama sannan na zame na kwanta a gurin ina jin jikina kamar mai zazzaɓi har Mama tayi mana sallama ta tafi.

Kwana biyun haka na kare su babu lafiya sosai, na so inki komawa saboda bana jin dadi amma Inna ta matsa Saghir ma kuma yace in ma zan zauna sai dai ya dauki Subay'a saboda makaranta ni kuma bana jin zan iya barin ta tare da Fauziyya dan nasan ba kunya ce ta ishe ta ba. Dan haka dole na shirya Saghir yazo muka tafi. A hanya ya kalleni yace "kin kara kiba, baki da lafiya amma kinyi kiba kin kara fari. What's the secret?" Na bata rai nace "what secret kuma?" Yayi murmushi "wai cewa nayi ko Subay'a ce zata yi kani? It is about time, tayi girma da yawa" na juya kai ina kallon titi" I missed my period wannan watan, a lokacin bikin nan ya kamata inyi kuma banyi ba but that doesn't mean anything tunda dama ina missing sometimes. Ina ganinsa yayi packing a bakery suka shiga shida Subay'a suka lodo kayan ciye ciye sannan muka tafi.

A toilet da zan shiga wanka na tsaya ina kallon kaina a mirror, da gaske nayi girma na ciko ta koina musamman hips, abinda da bani dasu sai yanzu suke zuwa kuma. A raina nace "sai yanzu makerin budurci ya tuna dani" after I lost mine long time ago.

Na fito daga wanka kenan ina shiryawa text ya shigo wayata. Na daga sai naga number din Sadauki, a raina nace "really? Ko dai batan kai yayi?" Sai kawai na ajiye wayar nayi shiryawa ta. Saghir ya shigo da magunguna a leda ya bani yana taba wuyana yace "gobe asibiti ya kamata muje in zazzabin nan bai tafi ba, test nake so ayi miki ma dan ni jikina yana bani ciki ne" nace "no fa ba wani ciki" amma a raina sai naji ina son ma ace cikin ne, I was really in need of love, kuma ina ganin haihuwa zata taimaka min sosai" na kwanta na dauki wayata yace "za'a fara karatun ko? Bana hana ba?" Nace "to me zanyi? Babu wani abin yi sai dai mutum yayi bacci ya tashi ya gyara gida yayi girki ya kuma komawa tayi bacci" ya danyi shiru yana kallona kamar mai tunani sai yace "kina son komawa school?" Nayi saurin kallonsa, ban taba tambaya ba saboda banyi tunanin zai bari ba amma raina yana so, ina son in zama abinda baffana ya ke kwadayi, nace "da gaske?" Ya daga kafada yace "why not? In dai zai faranta miki that's what I will do" sai na kama tsalle ina murna shi kuma yana dariya sannan ya jawo ni yace "so? Me zaki karanta?" Nayi shiru ina tunani. Na tuna wani visiting da Sadauk yaje min school shida wani abokinsa and we talked about carrier, a lokaci nace musu bani da choice sai Sadauki yace later in life zan fahimci role din daya kamata inyi playing a rayuwa, but yet still, bani da choice a raina.

Nace "me kake ganin ya kamata?" Yace "anything. Nasan ku mata da son harkar health, zaki iya yin nursing ko midwifery. In ma kuma medicine din kike so sai inyi wa Mr Abatcha magana ya hada ni da wani a samo miki admission" na ture shi ina jin raina ya baci nace "forget Mr Abatcha din nan" yace "why? Shi ya bani wannan shawarar ma fa, ya tambaye ni kina makaranta nace a'a sai yace ya kamata in saka ki. Kinga ai he will be willing to help" na girgiza kaina nace "na fasa karatun" sai kawai ya tsaya yana kallona da mamaki.

Sai da zan kwanta na bude message din Sadauki "ya jikin? Allah ya kara afuwa ameen" nayi tsaki na ajiye wayar na kwanta, sai kuma na tashi na sake karantawa sai kawai na kashe wayar na jawo drawer na saka ta nayi kwanciya ta.

Da safe muna breakfast gabaki dayan mu har Fauziyya, ya ajiye ledar drugs din daya siyo min jiya yace "kina gama cin abinci zaki sha magani, dan naga ashe jiya baki sha ba kwata kwata" nace " in tambaye ka mana Please" ya ajiye spoon din hannunsa yace "ina jin ki" nace "ya sunan ogan ku na office" ya bata rai yace "Mr Abatcha mana" na girgiza kai nace "sunan shi na gaskiya nake nufi. Like sunan da yake rubuta wa in an bukaci sunansa" ya danyi tunani yace "Engineer Aliyu Umar Abatcha" na gyada kai nace "ohh okay" yace "me yasa kika tambaya?" Nace "a bikin nan ne naji ana zancen wani, I tot shine ashe bashi bane ba" yayi murmushi ya fara praising Mr Abatcha "yana da kirki sosai, na girme shi amma mi gaskiya he is my role model. He is very smart and intelligent. Kuma yana sona. Kunga yadda yake korar mutane kuwa duk wanda yaga wasa yake yi ba aiki ba yanzu zai tura maka quiry amma ni ko sau daya bai taba bani ba. Diyam kin tuna sanda ya tura ni Germany? Sai da naje na fahimci ya tura ni ne kawai dan in huta ashe already ya riga yayi sighing contract din. Sai dan workshop dana ringa zuwa kawai" na girgiza kaina a raina nace 'ya tura ka ne dan ya samu damar zuba kaji a gidan ku'.

Munje asibiti anyi min pt and it came back positive. Sai naji dadi, maybe wannan haihuwar ta zamo min silar gyaruwar lamura na. Saghir kam doki har a gaban Fauziyya, ya bawa Subay'a labarin zata yi sister ko brother ita ma tayi ta murna. And yana fita sai gashi da sabuwar waya, yace "wannan tsohuwar wayar taki dai ya kamata ki ajiye ta haka" na karba nayi masa godiya sai kuma ya tambaye ni in akwai abinda nake so. Na zauna kusa dashi nace "so nake kayi wa su Murja aure" ya bata rai, nace "Please, auren suke so wallahi kuma Alhaji bashi da halin yi musu to waye zaiyi musu in ba kai ba? Su ba karatu ba, su ba aure ba me kake tunanin xasu yi?" Yana kallona yace "sai in kinyi min alkawarin kema zaki koma school" nace "sai in kayi min alkawarin zaka daina shan giya" ya daga kafada "na daina fa" na tsare shi da ido sai yace "na kusa dainawa. Seriously na kwana biyu rabo na da ita" nace "mata fa?" Yace "na daina wannan tunda na kara aure ai" sai kuma ya jawo ni yace "tell me, kishi kike yi?" Nace "Saghir ko bana sonka, kai mijina ne, kuma uban yayana, ba zan so kuma yayana su tashi suga babansu da wadannan halayyar ba". Yayi murmushi yace "am getting there".

And two days after that. Ina ta aiyukan gyaran gidana, da yake ni ban damu ba ko aikina ne ko na Fauziyya ni in dai na tashi zan gyara gida saboda bana son kazanta, it irritates me, ina mopping kasa Saghir ya leko ta stairs yace min "ina tsohuwar wayar kine? Naga har yau baki kunna sabuwar ba" nace "tana bedside drawer ta" na cigaba da aikina.

Na gama naje na wanke mop, na dawo ina saka turaren wuta Fauziyya ta sauko ta kunna tv ta kwanta tana kallo. Sai Saghir ya sauko da wayata a hannunsa, I looked at his face and I felt something knot in my stomach. Ya nuna min wayar "waye wannan?" Fauziyya ta mike zaune tana kallon mu. Message na gani a jikin wayar "ya jikin? Allah ya kara afuwa ameen" na girgiza kaina nace "duba ni ake yi, what's there?" Sai yayi scrolling sama, tun message din farko.

"Third option. Kazo a baka hakurin da kake so"
"tomorrow evening. Gidan Baffa"
"ina yiwa Asma'u godiyar kyautar da aka yi mata. Allah ya kara arziki mai albarka"
"You are welcome".

Na daga kafada, ni banga abin tayar da hankali a cikin maganganun mu ba. Ya sake cewa "waye wannan Diyam? Sadauki ne ko? Amana ta kike ci ko Diyam? Wato abinda yasa kike guduna saboda kina samu a wani wajen ko? I always tot, yarinyar nan sai kace dutse, ashe kina da tap din da kike karbar rabonki a gurinsa".

Na zaro ido "wanne irin magana kake yi? How can You even accuse me of that. Menene a cikin messages din nan da zasu saka har ka fadi haka? Yes, munyi magana sanda suke case da Alhaji Babba kuma yayi wa Asma'u kyauta na yi mata godiya. Menene a ciki?" Yace "to uban wanene ya gaya masa baki da lafiya har yake duba ki?" Nace "a gida ya same ni yaje gaida Inna yaga bani da lafiya. I don't even know me yasa nake defending kaina. Dan kana yin abu sai ka dauka kowa ma yi yake yi?".

A girgiza kai idonsa jawur yace "am going to trace him. Am going to enter his number into my phone and call him. In na gano inda yake kuma wallahi sai na daure shi. Sai yasan matata ya taba" ya juya da sauri zai koma sama sai nayi saurin rike rigarsa "Saghir ka tsaya ka saurare ni. Wallahi ba abinda kake tunani bane ba" ya juyo a fusace ya sauke min mari a fuskata, kafin inyi wani abu ya sake sauke min wani a same side. Na rine fuskata ina jin jini yana bin hancina, ganina yayi dusu dusu. Amma still na rike rigarsa i a girgiza masa kaina, ta gefen idona na hango Fauziyya tana dariya, sai ya warce rigarsa ya hankada ni da karfi na fadi, unluckily sai cikina ya bugu da kafar bene, na mirgina gefe ina rike marata da hannun bibbiyu shi kuma yayi sama da sauri ba tare daya kalli inda nake ba.

Na sake kokarin mikewa amma marata ta rike kam sai da kyar na daddafa stairs na mike, tunani na daya shine in Saghir yayi dialing number din Sadauki a wayarsa zaiga Mr Abatcha. And that can destroy Sadauki's reputation a gurin aikinsa. Na juya na kalli Fauziyya da take zaune tana kallo na da murmushi a fuskarta nace "get up from my chair. Munafuka"

Sai na kama bene ina tafiya a hankali nabi Saghir a baya. Ina hawa sama yana fitowa daga dakinsa hannayensa da waya ta da kuma tashi. Nace "ka saurare ni Saghir" bai ce komai ba ya fara daddanna wayar sa. A lokacin mara ta tayi wata irin murdawar da sai da na kai kan guiwowina na runtse idona, sai ji nayi yace

"Mr Abatcha? Menene hadin Sadauki da Mr Abatcha?"
[2/19, 8:38 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Eight: When The Going Gets Tough

Bature yace "when the going gets tough, only the tough gets going" hakane?
It is either you get tough ko kuma kana ji kana gani a tafi a barka.

"Mr Abatcha? Menene hadin Sadauki da Mr Abatcha?" Na dafa bango na mike ina kallonsa kawai. Babu abinda zance masa a yanzu, dama kokari na shine inyi preventing dinsa from finding out kuma ya riga yayi. So magana ta kare kuma.

Ya zuba min ido, "magana nake miki Diyam? Sadauki kike texting ko Mr Abatcha" kallon da nake masa yasa ya tsaya shima yana kallona and then the realization hits him. I saw lokacin da yanayin fuskarsa gaba-daya ya chanza, ya saki wayoyin duk guda biyun suka zube a kasa. His whole world came crashing down on him.

"Mr Abatcha? Mr Abatcha shine Sadauki? When? How?" Ya saka hannayensa duk biyun acikin kansa ya fara zagaya palon da sauri har wani gumi ne yake karyo masa. Idonsa ya ciko da kwalla. Ya taho da sauri ya tsaya a gaba na "you? You were playing me all these years? All these years kina tare dashi dama? My God!" Ya sake dora hannu aka jikinsa har rawa yake sai ya dafa kujera yana mayar da numfashi. Ya jima a haka sannan ya juyo yana kallona sannan yace "ke kika saka shi ya bani aiki ko? I remember ke kika ce inje in nemi aiki. Ke kika saka ya dauke ni without even looking at my credentials saboda ku kasance tare ko? Saboda kuyi controlling dina ko? Is that it?" Na girgiza kai kawai amma kafin inyi magana yace "kar kice min komai, ko inzo in babballaki anan. My God, wannan wanne irin cin amana ne, hatta sunan da zan sakawa yata shi ya zaba min" sai ya fara dukan kansa da hannunsa yana cewa "wawa, dolo, soko, dakiki".

Sai kuma ya zauna akan kujera ya dafe kansa da hannayensa yana girgiza kai. Yace "wato tare kukayi planning din abinda aka yiwa Alhaji ko? Shi yasa ya tura ni tafiya a lokacin. Da aka gayamin sharadan daya saka sai da nayi tunanin me yasa a ciki bai ce in sake ki ya aura ba, ashe baya bukatar wannan tunda already yana tare da ke".

Kamar wuka haka maganganun Saghir suke huda ni. Wannan accusations din yana daya daga cikin abinda na kasa mantawa har yau. Komai zan gaya masa ba zai fahimta ba, amma duk da haka zan gaya masa ruwansa ne kuma in ya dauka in kuma bai dauka ba matsalar sa. I was beyond caring a lokacin.

Nace "sanda Sadauki ya dauke ka aiki bansan shi bane ba, bai taba contacting dina ba, I had no idea yana ina ma har sai ranar da kuka shirya masa party, a ranar nasan shine oganka. Bansan dalilin sa na daukan ka aiki ba, zata iya yiwuwa ya dauke kane kamar kowa, wannan shi yasa ban gaya maka ba tunda ina ganin fadin bashi da amfani. Bamu taba magana ni da Sadauki ba in banda sanda Alhaji ya tura ni gurinsa, a lokacin ma yayi shutting dina out dan haka babu maganar da muka yi sai wadda takaini. Bamu taba waya da Sadauki ba. Texts din da ka gani sune a tsakanin mu. Wannan shine gaskiyar magana" na juya zan bar gurin naji kafafuwana sun rike tun daga cinyoyi na zuwa marata suna min wata irin suka. Nace "Saghir?" Bai amsa ba sai cewa yayi "karki gaya min karyar banza. Wallahi bai isa ba. Baku isa ba daga ke har shi kuyi min wannan cin mutuncin. Sai na nuna masa dukiyar sa ta banza ce wallahi sai ya raina kansa. I will destroy him ko zan rasa raina wallahi." Sai ya shiga daki ya dauko key din mota, zai wuce ni na rike rigarsa nace "Saghir bani da lafiya" ya kwace rigarsa yace "zaki warke ne ma, munafuka" ya fice ya barni without another look at my side.

Na daga rigata naga jini yana bin kafata a dai dai lokacin dana ji tashin motarsa. And I realized something, na rasa cikin jikina kamar yadda na rasa twins dina. And there and then na yanke shawara, na gama auren Saghir.

Nayi kokarin motsawa daga gurin na kasa. Ina so in taimaki kaina kuma ina son in warning Sadauki dan ban san me Saghir zaiyi ba daya fita amma na kasa zuwa ina waya ta take yashe a kofar dakin Saghir. Kafafuwana tamkar sun daina aiki haka nake jinsu sai jini ne yake biyo su zuwa kan tiles. Option dina daya, Fauziyya. Na fara kiranta da dan abinda ya sauwaka daga murya ta. "Fauziyya, Fauziyya" amma shiru, ban tabbatar ta jini ba ko a'a saboda nasan kallo takeyi. Na jima a haka sannan na jiyo hawowarta sama. Tana shigowa palon ta tsaya tana kallo na yadda na hada gumi ga busashshen jini a hancina ga kuma jinin da yake kwance a kasa na sai ta saki purse din hannunta ta taho da sauri "Halima? Me ya same ki haka?" Cikina kawai na iya na nuna mata, ta kama ni ta kwantar a gurin sannan ta koma ta dauko jakarta data yar ta dauko wayarta ta fara kira. Jikina ya bani Saghir take kira sai kuwa mukaji wayar tasa tana kara a kusa da tawa. Ta ajiye wayar tace min "ina ya tafi?" Kaina kawai na girgiza mata, sai tace "ko miscarriage kike yi ne? Ko asibiti zamu je?" Na gyada mata kai sai ta kama ni zuwa toilet dina, ta taimaka min na wanke jiki na amma fa jini zuba yake dan pad ma ba zata rike shiba sai face towel ta bani na saka muka tafi. She half carried my down the stairs sannan ta saka mai gadi ya samo mana abin hawa muka tafi asibiti. Wannan yasa ba zan taba mantawa da Fauziyya ba.

Bayan fitar Saghir daga gidansa ya shiga motarsa ransa a mugun bace, bai taba jin bacin rai irin na ranar ba danji yake kamar ya hada ni da Sadauki ya saka mana wuta mu kone. Sai kawai ya bude aljihun motarsa ya dauko wata tsohuwar ajjiyar sa da kullum in ya dauko zai sha sai ya tuna yayi wa Diyam alkawarin ya daina sha. But yau Diyam din ce da kanta ta bata masa dan haka with vengeance ya shanye kwalbar gabaki dayan ta sannan ya kunna motar ya fita daga gidan ya tunkari kamfanin Abatcha Motors.

Sadauki yana cikin meeting da ma'aikatan sa, meeting din da ba'a ko gayyaci Saghir ba sai assistant dinsa. Sadauki yana tsaka da yin bayanin sababbin dokokin da yake kafawa saboda ma'aikatan da suke incompetent da irin hukuncin da za'a ke dauka akan duk mai karya doka sai ga Saghir ya banko kofa ya shigo, duk suka juya suna kallonsa ya taho yana tangadi ya nuna Sadauki yace "munafiki. Allah ya tona asirin ka yau" gaba-daya gurin suka mike, wasu daga ciki suka mike suka yo kan Saghir amma sai Sadauki ya dakatar dasu da hannu yace "ku rabu dashi" ya gyara zama ya kalli Saghir yace "menene yake tafe da kai?" Saghir ya nuna Sadauki yana kallon mutanen gurin yace

"wannan da kuke gani is not who he is saying he is. Ba sunan shi Abatcha ba sunan shi Sadauki kuma Sadauki shine Mr Abatcha kuma shine saurayin Diyam kuma Diyam kullum sai ta fadi sunan Sadauki ashe shine Mr Abatcha. Shine kuma ya bani aiki sannan ya saka wa yata suna ya siya mata ragon suna. Yazo kuma ya kai Alhaji kara ya karbi rabin gidan sa yayi gidan gona. Sai yau na ga message din sa a wayarta sannan na gane ashe shine"

Wani a gurin yace "do you understand cewa baka making sense kwata kwata?" Sauran mutanen suka kwashe da dariya. Sadauki yayi ajjiyar zuciya ya nuna Saghir yace "Ladies and gentlemen, this is an example of one of the effects of shaye shaye" sai ya kalli security yace "get him out of my sight".

A asibiti akayi confirming fitar cikina. Amma suka ce bai gama fita ba. Sai suka bani wani tablet suka ce zai fitar da sauran. Muna can lokacin tashin su Subay'a daga school yayi, Fauziyya ta koma gida ta dauko ta ta kai makotan mu sannan ta dawo gurina.

Har muka koma gida gurin magrib Saghir bai dawo ba. Na sha tablet din sannan na kwanta, Subay'a tana ta jera min sannu. Na sake trying number din Sadauki bata shiga, duk da dai nasan koma menene zai faru ya riga ya faru. Na kwanta ina ta jiran shigowar Saghir amma shiru har bacci ya dauke ni banji ya shigo gidan ba. Cikin dare wani azababben ciwon mara ya tashe ni, ji nayi kamar raina zai fita gashi daga ni sai Subay'a a daki. Jini guda guda haka ya rinka fita daga jikina. Ban yi bacci ba sai da aka fara kiraye kirayen sallah.

Cikin bacci naji Fauziyya ta shigo dakin tana tashin Subay'a, sai kuma tace min "Daddy fa bai kwana gidan nan ba. Ga wayarsa kuma tana nan. Na kira Kabiru kuma yace basa tare. Ko zaki kira gidan Alhaji kiji ko yana can?" Nace mata to kawai, amma ba wanda na kira. Ita ta shirya Subay'a ta mika ta school sannan ta dawo ta kawo min tea.

Zuwa 12 na dan warware, sai dai weakness sannan kana kallona zaka ga nayi pale saboda ba karamin jini na zubar ba. Na tashi nayi wanka, na fito na shirya sai na tsaya ina kallon kaina a mirror. Na dora hannuna akan marata ina tabbatar wa kaina cewa it is gone. It is dead before it even begins living. It is going to be the last thing da zanyi loosing a sanadiyar auren Saghir. Ina saka kaya na sai na jawo akwati na fara zuba kayana dana Subay'a. Ina cikin zubawa Fauziyya ta shigo, yanayin ta kamar a rude tace "Halima, kizo inji Kabiru" ta fita na saka hijab dina na bita a baya. Yana tsaye a bakin kofa ya kalle mu yace "Saghir yana station tun jiya. Bansan me ya faru ba amma ance security din gurin aikinsa ne suka kama shi suka damka shi a hannun police. Ban san menene charges din ba. Nayi kokarin yin bail dinsa sun hana ni, sunce order ce direct from the commissioner of police cewa kar a bayar da bail dinsa".

Fauziyya ta zame ta zauna. Ni kuma sai na juya nayi hanyar sama. Kabir yace "Diyam ki kira gida ki fada. Maybe Alhaji yana da wani a sama wanda zai saka a fito dashi" na gyada masa kai kawai na wuce. Ina zuwa daki na karasa hada kayana na fito na wuce Fauziyya a palo ta zabga tagumi na je na dauko Subay'a na dawo na sake wuceta. Na shirya Subay'a sannan muka sauko tare da akwatin kayan mu. Fauziyya ta tashi tsaye tana kallon mu tace "ina zuwa haka?" Nace "gida" bata kuma cewa komai ba har muka fita. Mai gadi yayi min sannu da jiki sannan ya taya mu da kaya muka tari abin hawa muka tafi.

Inna tana ganina da akwati tace "lafiya" na ajiye kayan hannu na sannan na gaishe ta, bata amsa ba tace "lfy nace? Lafiya na ganki da tsakar ranar nan da akwati?" Na sunkuyar da kaina nace "Inna na gama auren Saghir" ta saka salati, "shi Saghir din ne ya turo ki gida ko kuma ke kika yi ra'ayin kin gama aurensa kika taho gida? Dama igiyar auren a hannun ki take?" Na girgiza kai nace "Inna Saghir fa...." Tace "Saghir me? Saghir din yanzu ai bana da bane ba. Kika zauna da wancan Saghir din ma ballantana wannan da kowa ya tabbatar ya chanja. Dama tun randa Sadauki yazo nan da maganar aurensa naga yadda kikayi nasan in ba sa'a akayi ba sai kin fito da wata maganar kuma" naji hawaye ya fara bin fuskata, nace "Inna ba a kan Sadauki na taho gida ba, tsakani na da Saghir ne, ni ba zan koma gidan sa ba Inna. Dan Allah karki mayar dani" tace "ina Saghir din?" Na share hawaye na nace "yana police station" ta sake wani salatin "me ya faru? Me yake yi a can?" Nace "Sadauki ne ya rufe shi." Ta mike tace "kuma kika ce ba'a kan Sadauki bane ba. kira min Sadauki yanzu yanzun nan" nace "na baro

Please Login or Register in order to submit comment