Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na tashi na shiga dakin Mama zan mata sallama tace "da daren nan" sai na sunkuyar da kaina nace "Sadauki ne yazo zamu tafi tare" tace "kuma babu gaisuwa? Ki ce masa ya shigo mana" na dauki waya na kira na gaya masa yace "ke ba'a sirri dake? Ban taba zuwa na gaishe ta ba sai kuma in zo in fitar mata da ƴa? Ni kunyar ta nake ji" nace "to ai in bance kai ne ba ba zata barni ba cewa zata yi dare yayi" a dolen sa ya shigo, yana ta sunkuyar da kai yana shafa keya, and I asked myself "wai me yasa maza in suna jin kunya suke shafa keyar su?".

Bayan ya fita nayi wa Mama sallama na bishi a baya. A cikin mota na same shi a zaune a seat din driver. Sai ya bude min kofar gaba yayi min alamar in shigo da hannunsa. Na shiga na rufo kofar sai ya juyo yana kallo na, na sunkuyar da kaina kasa ina feeling uncomfortable. Motar naga kamar tayi mana kadan, space din tsakanin mu yayi kadan, ga motar ta cika da kamshinsa mai shiga har cikin ruhi. Sannan kuma gashi yana min murmushi.

Naji kamar in bude motar in fice. Bai kunna motar ba ya juyo yana kallona Yace "wai ke duk fushin ne haka? Me zanyi ne wai ayi min murmushi ko guda daya ne" sai na kara bata rai na turo baki yace "okay rashin kunyar tana nan ashe kenan. Na dauka an barwa Subay'a" sai ya tayar da motar muka bar gidan.

A hanya yace "kinsa naji kunyar Mama fa, banzo na gaishe ta ba sai da nazo zance" na kalle shi nace "zance? Gurin wa kaje zancen? A kano muke fa ba'a Maiduguri ba" ya dan bata rai kamar mai tunani sai kuma yayi dariya yace "ohhh okay, yanzu na gane wannan fushin na menene. Ai na gaya mata zan zo gurinki dama kuma tace in gaishe ki" nace "kar ma kayi tunanin da nake tunanin kana yi. It is not what you are thinking" yace "yes it is. Hausawa sunyi karin magana suka ce kishi kumallon mata, amma ke naki kishin aman gaskiya yake saka ki. Daga jin muna magana da Inna sai ki kama amai?" Na gane maganar da yake yi nayi saurin cewa "ba fa abinda kake tunani bane ba, bani da lafiya dama a lokacin. To ni ina ma ruwa na da aurenka" yace "okay idan rashin lafiya ta saki amai ita ce kuma ta saka daga nayi miki sannu kika rufe ni da fada?" Nace "kaga nifa bana son ake juya min magana ta" yace "shikenan, an daina" muka cigaba da tafiya sannan yace "na bata labarin ki. I told her ina son aurenki first and she agreed" ya fada yana kallona, nayi kamar ban jishi ba ina jin bacin raina yana karuwa, amma sai ya sake cewa "tana sonki sosai. Tace zata zo Nigeria karshen week din nan purposely saboda ta ganki" na saka hannuna na toshe kunnuwa na ina jin zaman motar duk ya ishe ni. Nace "stop the car" yace "why?" Nace "ko dai ka daina wannan maganar ko kuma ka tsayar da motar nan in fita in karasa a kafa" sai ya kama dariya yace "an daina your highness".

Muna zuwa gida nayi masa godiya, kafin in bude kofar ya kira suna na "Diyam" na juyo ina kallonsa yace "Please in na kira ki ki dauka kinji. Say whatever you want to say in kin dauka din but please kar ki ƙi dauka".

Ranar na jima banyi bacci ba ina juyi. Feeling a familiar warmth a cikin zuriya ta wanda a da naje tunanin ko ba gushe yanzu baya nan. Zuciyata da ƙwaƙwalwa ta suka cigaba da battle dinsa ni kuma na zama confused dan bansan wanne daga cikin su zan bi ba. My heart was telling me in kira Sadauki a waya, in bude masa zuciyata in gaya masa irin zurfin da soyayyar sa tayi a ruhina, while my mind was asking me to hold on, reminding me cewa ba lallai ne in Sadauki ya samu abinda yake so ni kuma ya bani abinda nake so ba.

Washegari da safe bayan na dawo daga islamiyya ya kirani, daga alama a office yake "kinci abinci? Me kika ci?" Nace "kosai Asma'u ta soya mana" yace "yan gayu. Ni kuma kinga yunwa nake ji babu wanda ya damu yace Sadauki ga abinci" nace "Sadauki ko Mr Abatcha?" Yayi dariya yace "all the same" nace "ni banga same ba. Sadaukin dana sani is different from this rich Mr Abatcha" yace "really? To fada min menene bambancin" nace "da farko dai Sadauki baya taba yin abinda zai bata ran Ummah ko Baffa. Ita kuwa Ummah a cikin masu hakuri ma ita daban Allah yayi ta, bata taba fada ballantana har ta kasa yafewa wadanda suka bata mata. Na tabbatar kuma zata so ace yayanta, ni da kai, munyi koyi da ita, ko da bamu zama irin ta ba sai mu kwatanta ko yaya ne"

Ya jima shiru sannan yace "she was a good woman. The best. Bata bata wa kowa, in mutum ya bata mata ma sai tayi kamar bata gani ba duk kuwa da cewa ta gani ɗin. Har gida har daki za'a zo aci mutuncin ta ba tare data yi laifin komai ba and she will always looked at me and said "kar kayi magana, kar kace komai" and I will keep quiet. Amma ranar data mutu kinsan me Alhaji Babba yace? Cewa yayi ba za'a shigar da gawarta gidan mijinta ba as if she were some kind of trash" na goge hawayen daya taru a idona ina tuno wa da abinda ya faru a ranar data chanja gabaki dayan rayuwata.

Nace "sai menene kuma? Hakan ai bai rage ta da komai ba a wajen ubangijin ta, kuma muna saka mata ran cewa yanzu tana gurin da yafi gidan nan kyau da daraja. Kuma nasan da ace zata kalle ka a yanzu zata ce "kar kayi magana, kar kace komai" saboda tana son ka zama mai hakuri mai yafiya irin wanda Allah yake so, Annabi kuma yake alfahari dasu" yace "nasan abinda kike so ki ce, so kike yi kice in yafe musu gabaki dayan su, amma abinda kika manta shine, su fa basu yi nadama ba har yau. Yes, Alhaji ya bani hakuri ranar nan amma daga ni har ke har shi munsan cewa tuban muzuru yayi, na saka shine a corner babu yadda zaiyi shi yasa ya bani hakuri amma a lokacin da yana da dama da ina juya bayana zai daɓa min wuka"

Nace "na sani, amma wannan shi da ubangijin sa, ni da kai na damu ba dasu ba, zuciyarka nake fatan gyarawa and maybe a kokarin haka kaga tasu itama ta gyaru. Kasan abinda na fahimta? Babu abinda yafi saukarwa da mutum nadama irin idan wanda akayi wa sharri yayi sakayya da alkhairi. Take Inna as an example. Ba karamar nadama ce Inna tayi ba kuma a yanzu babu wanda take kaunar farantawa sama da kai" ya ajiye numfashi yace "kina so in yafe musu?" Nace "yes, amma badan ni zaka yafe ba. Dan Allah zaka yafe. Take your time and think over it. Kai da kanka zaka yanke shawarar yin abinda ya dace". Sai ya chanja maganar "yanzu ya za'ayi a kawo min kosan nan zuwa office?"

Kamar wasa few days bayan nan da daddare ina shirin kwanciya ya kira ni "me kike shirya wa bakuwar ki ne?" Nace "wacce bakuwar kuma?" Yace "kin manta nace akwai wadda zata zi gurinki?" Naji duk nishadin dana ke ji ya kau, nayi shiru yace "gobe zata sauka. Jirgin safe. Ni ina da meeting about that time. Ki shirya sai in turo miki da mota kije ki dauko ra a airport" nace "ni kuma? To ni da bansan ta ba ta yaya zan gane ta?" Yace "ki saka bakar doguwar riga ita kuma zata saka milk. You will know her when you see her" na hadiye abinda ya tsaya a kirjina nace "ya sunanta?" Yace "Murjanatu".

Not edited. Sorry for the typos.[3/4, 8:20 PM] +234 703 589 5826: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episodes Fifty Nine & Sixty : The Answers

Da safe na gayawa Inna sakon Sadauki. Tace "to fa! Sai kije ki dauko ta din. Anan zata sauka ne ko kuma a wani gurin daban?" Nace "nima ban sani ba inna" sai tace "to ki kira shi ki tambayeshi mana, in nan zata sauka ai gwara mu sani dan ayi mata abinci ko?" Na kasa kiransa saboda ji nayi duk haushinsa nake ji, sai na tura masa text "a nan zata sauka?" Sai da na fito daga wanka naga reply dinsa, "bakuwar ki ce ba tawa ba. Besides, ni gwauro ne bani da gurin da zan sauke ta".

Karfe goma da rabi yace min jirgin su zai sauka. Karfe goma driver yazo yana jirana. Asma'u tana school Subay'a ma haka, dan haka dole na shirya ni kadai na fita ina ta bace bacen rai. Sai 10:30 muka je airport din a raina ina cewa 'in sun sauka ma ta jira, da waye ya gayyace ta zuwa wajena?" Sai kuma nayi rashin sa'a jirginsu yayi delay dan haka sai da muka jira ma sannan suka sauka. Ina tsaye da bakar rigata da ya umarce ni in saka idona akan kofa ina ganin masu fitowa, mostly turawa ne maza da mata, sai few blacks suma kuma yawanci maza ne sai kuma wasu family da suka fito tare. Sannan na hango ta ta taho, tun daga nema na ganeta saboda kalar rigar jikinta. Waya a makale a kunnenta tana magana tana murmushin da yake bayyana hakoranta, naji kirjina ya buga da karfi a lokacin da zuciyata ta ayyana min wanda suke wayar dashi.

Ta fito waje sosai tana dan dube dube, idonta ya sauka a kaina sai naga ta sake fadada murmushin ta ta katse kiran sannan ta taho inda nake. I was suppose to like nima in tafi inda take sai mu hadu a hanya amma sai nayi tsayuwata pretending as if ban gane taba har ta karaso gaba na tana murmushi tace "Diyam?" Sai kuma na kirkiro murmushi nayi mata ina studying dinta. Baka ce, mai matsakaicin jiki kyakykyawar gaske and every part of her was screaming "I am rich" dan kallo daya zaka yi mata kasan cewa bata san wata kalma wai ita wahala ba. And something caught my attention, kalar skin dinta, manyan fararen idanuwanta, shape din fuskarta da kuma yanayin murmushin ta irin na Sadauki ne. Na tambayi kaina "are they related? Ko hadin gida za'ayi musu?"

Na kirkiro murmushi nace "Murjanatu?" Sai tayi dariya, ta saka phone dinta a cikin karamar jakar da take rataye a kafadarta sannan sai kawai naga ta rungume ni, ta sake ni tana kara kallona tace "wow, you are even more beautiful in person than yadda aka kwatanta min ke" na danyi dariya ina tunanin tsaurin ido na Sadauki da zai zauna yayi wa budurwarsa description dina. Nace "welcome to kano, fatan dai baki sha wahala sosai ba" ta yarfe hannu tace "zafi, haka kullum in muka je Maiduguri nake fama. Kamar ace an ciro mutum daga cikin freezer ne an saka shi a cikin oven. Na kan tambayi Adama, wai haka kaji sukeji in ana gasa su? irin frozen chicken din nan kuma a saka su a oven" nayi dariya a raina ina cewa wannan surutu ne da ita.

Drivern da muka zo dashi ya zo ya fara jan akwatin ta ni kuma sai na mika hannu da niyyar in karbi jakar hannunta amma sai taki bani tace "rufa min asiri, so kike yaya ya gasa ni kamar gyada?" Na maimaita kalmar yaya a raina. So they are related da gaske.

Muna tafiya veil din kanta ya fado kafadarta ya bayyana gyararren gashin kanta, but sai naga bata damu data gyara ba har sai da ni da kaina na gyara mata. She just thank me casually muka cigaba da tafiya.

A hanya muka dan taba hira, duk da dai da yawa daga hirar ita takeyi, a lokacin take gaya min cewa wannan ne zuwan ta kano na farko "in munzo Nigeria gida muke zuwa, Maiduguri, sai Abuja sometimes, mun dai taba zuwa Kaduna once" jin haka sai na fara yi mata bayanin guraren da muke wucewa a hanya, and she looked very interested.

Da muka je gida ina kallonta ina jiran inga tayi wa gidan mu wani kallo haka, ko kuma in an bata abinci inji tayi wani comment marar kyau amma sai naga sam babu abinda ya dame ta, she is the most down to earth person I have ever met. Ta zauna ta harde kafa tana ta cin tarin abincin da Inna ta jera mata tana kuma yiwa Inna hira. Sai tace "ina 'yar Asama? Kullum sai an bamu labarin Yar Asama da Diyam, Diyam this Diyam that. Ko kaya muka saka sai yace "ku kun mayar da kanku turawa, kuyi ta saka kananan kaya, why can't you dress like Diyam?" Ta fada tana kwaikwayon yadda Sadauki yake maganar sa.

Na kai mata kayanta dakina sannan na hada mata ruwan wanka a toilet nace tayi wanka ta huta. Bata tashi ba sai da Asma'u ta dawo daga school, ina jin Inna tana yi mata bayanin bakuwar da akayi sai kuwa naga ta tura baki tana kunkuni, Inna tayi mata warning kar ta sake tayi mata wata magana marar dadi.

Na shiga daki na tarar ta tashi daga bacci tana sallah, na zauna ina jira har ta idar sannan na tambayeta ko da akwai abinda take so. Kafin ta bani amsa Asma'u ta shigo tace "nazo gaishe da matar yayana" sai naga Murjanatu ta kalle ni sai ta cigaba da nineke abin sallah. Asma'u ta sake cewa "matar yaya barka da zuwa" sai Murjanatu ta kalle ni tace "ana miki magana" nace "ke take gaisarwa fa" sai tace "matar yaya naji tace, wanne yayan?" Na gyara zamana ina so inyi confirming suspicio dina Nace "Sadauki mana" ta dan bata fuska tace "waye Sadauki?" Na sunkuyar da kai nace "Aliyu, mu anan Sadauki muke ce masa" cikin mamaki tace "yaya Aliyu? Nice matar tasa kuma?" Nace "well, not legally yet, yace dai an bashi ke an kusa biki" sai ta zauna a bakin gado ta dafe kanta tana dariya tana kallona tace "tsokanar ki yake, he is my brother, my half brother, baban mu daya".

Har dare Murjanatu tana ta tsokana ta. Ina jinsu suna waya da Sadauki tana bashi labari suna dariya sai na harare ta daga ita har wayar tata, ina jinta ta gaya masa wai ina hararar ta sai naga ta saito ni da wayar kamar zata min hoto sai na rufe fuskata ita kuma tayi ta min hotuna a haka.

Sosai Murjanatu ta sake a gidan mu, nan take muka kulla kawance mai kyau a tsakanin mu. Tana ta yimin hirar gidan su, Papa, Mama, Adama, Sa'adatu, Yani. Amma ban taba yi mata tambaya a kansu ba, na saka a raina cewa Sadauki ne ya kamata ya bani labarin su. Na fahimci kuma tana tsoron Sadauki, duk da kuwa na kanga suna yin waya suyi hira amma kamar bata taba ketare maganar sa, bata yi masa musu, kuma tana bani girma sosai saboda shi.

Ranar nan bayan Murjanatu ta kwana uku da zuwa muna waya dashi tace gobe mu shirya gabaki daya zai zo mu fita yawo "mu zagaya da Fanna taga garin Kano" nace "Fanna?" Yace "yes, Murjanatu. We call her that a gida".

Ina gaya musu sai murna, nan da nan Asma'u ta fara making list na guraren da zamuje, aka fara ware kayan da za'a saka da irin kwalliyar da za'ayi. Murjanatu ta kalleni ina yi musu dariya tace "gobe sai na yi miki kwalliya. Asma'u zata rike min ke in kinki tsayawa".

Na dauka wasa suke sai washegarin na fito daga wanka sai gasu da make up kit, nace bana so amma haka suka tilasta min suka yi min kwalliya. Na dauko abaya ta na saka sai Murjanatu ta tsaya tana kallo na tace "wannan rigar is too loose, bai fitar da duk abinda ya kamata ya fitar ba bayan kuma akwai abin" sai ta dauko wani belt a kayanta ta daura min, na kalli kaina a mirror naga yadda hips dina suka fito sosai, ni kaina bansan ina dasu har haka ba, sai na girgiza kaina nace "bazan iya fita haka ba. Mutane zasu ke kallona fa" sai ta dan dake ni a kafada tace "dalla in sun kalle kin sai me kuma? Ke wallahi halin ku daya da yaya Aliyu yanzu zaku fara wa'azi" nayi dariya kawai amma na hakura ne kawai dan bana so in gwale ta amma ni nasan bazan iya sakewa ba sam.

Muna gamawa yazo, muka fita ni dai ina ta rabe rabe a bayansu. Muna fita muka hango motarsa duk da bama ganinsa but I felt his eyes on me sai na kara buya a bayan Murjanatu ina jin kamar zan gurde in fadi har muka karaso inda yake, Murjanatu ta bude min kofar gaba tace "entere" nayi murmushi na shiga ina jin still idanuwansa a kaina amma na kasa kallon side din da yake, sai naji yayi gyaran murya yace da Murjanatu "koma ciki ki samo mata hijab" sai ta kama bubbuga kafa a kasa kamar mai shirin kuka sai yayi mata tsawa "are you still there?" Da sauri ta koma cikin gida.

Nayi kasa da idona ina wasa da fingers dina, still feeling his eyes on me. Sai yace "kinyi kyau sosai Halima. But I can't let people see you like this. Ina da kishi da yawa I might end up fasa wa wani hanci akan hanya. In son samu nane ma bayan hijab har nikab zaki saka ki rufe fuskarki" tunda ya fara magana nake murmushi, ina jin feeling mai dadi a raina cewa nima ina da value. Sai na tuno da ranar da Saghir yake fito min da gashina "let's show them abinda matansu basu dashi".

Ta kawo min hijab din na saka ya saka hannu ya gyara min fuskar hijab din sannan yace "that's much better" sai kuma ya leka waje yace da Asma'u da Murjanatu "duk wadda bata shigo ba zamu tafi mu barta" da sauri suka bude baya suka shigo suna dariya.

Yawo mukayi sosai a garin kano, har gidan sarki sai da muka je muka shiga ta kofar gudu muka fito ta kofar arewa muka ga grand central mosque. Muka je gidan mesium muka je gidan makama da gidan mutan da. Muka hau badala, muka hau dutsen dala da gwauron dutse. Muka je har government house muka yi zagaye a ciki muka fito sannan muka tafi Abatcha Motors.

Murjanatu tace "yau dai finally zanga wannan precious Abatcha Motors din da yake rike yayana a Nigeria. Ko da yake ban sani ba ko ba shi kadai bane yake rike shi ba" ta fada tana mintsini na ta baya. Na juya na harare ta shi kuma yana mana dariya muka shiga building din.

Da yake weekend ne duk babu ma'aikata sai security kamar zasu ci mutum. Muna zuwa suka taso kamar zasu durkusa mana ni dai duk sai naji inajin nauyin su. Ya saka su bude ko'ina a gurin sannan yace dasu Murjanatu su zagaya duk inda suke so mu kuma sai ya saka aka kawo mana kujeru gaban wani fountain muka zauna.

Sannan ya dauko waya yayi kira, da alama abinci yayi mana order. Sai kuma yace min "ranar nan, you asked me some questions. Are you ready for the answers?" Na tuno tambayoyin da nayi masa farkon zuwa na office dinsa. Sai nace "eh. Ina son sani please". Yace "okay. Let's start from the beginning".

"Tun farko na san cewa Alhaji Bukar ne ya hada auren Ummah da mahaifina, amma bamu taba maganar dashi ba saboda ganin kamar umman bata so".

"Sunan mahaifina Alhaji Umar Mustapha Abatcha" nayi saurin cewa "Alhaji Umar Mustapha dai wanda muke jin labarin sa?" Ya gyada kai yace "shifa. Family din Mustapha Abatcha family ne da yayi suna ba'a Maiduguri ba kadai har ma da sauran Nigeriya. Suna da kudi tun asalinsu but kudin Umar Mustapha daban ne dana sauran. Tun yana saurayi ya mallaki kudin da shi kansa mahaifinsa a lokacin bashi da su. Harkar man fetur yakeyi yi, tun yana yin gidajen man fetur a gari gari har ta kai shi ga fara siyan rijiyoyin man fetur din gabaki ɗaya. Bashi da lokacin aure, dan haka ya jima baiyi ba, wannan yasa yan'uwansa, musamman da yake duk yan uba yake dasu dan shi kadai ne a gurin mahaifiyarsa, suka sako shi a gaba, suna saka ran in ya mutu suci kudi. A lokacin ne Alhaji Bukar, tsohon amininsa da sukayi secondary school tare yayi masa tayin auren bafulatanar yarinya Zainab. Shi kuma sai ya karba yana ganin tunda ba auren soyayya bane ba ba zata ke demanding time dinsa ba. Ta gaya masa labarin wanda take so aka raba su and he was sympathetic, yana nuna mata kulawa sosai ita kuma ta kwantar da hankalin ta sukayi zamansu lafiya a nan family house dinsu dake Maiduguri. A haka har ta samu ciki. A lokacin ne kuna ya fara business da Canada yana exporting crude oil daga Nigeria zuwa Canada wanda har yanzu shine sana'arsa, a yanzu yana daya daga cikin manyan dealers na crude oil a kasar Canada.

Tunda zainabu ta samu ciki shikenan kuma sai al'amurra suka cabe mata, gashi lokacin baya zama a kasar ita kuma taji duk duniya babu inda ta tsana irin gidan aurenta, babu wanda bata son gani kamar mijinta, babu kuma abinda take son rabuwa dashi irin cikin jikinta. Ta zama kamar mahaukaciya, sai ta fita da gudu sai an bita ana kamota ana dawo da ita gida, wani lokacin kuma sai ta zauna tayi ta dukan cikin wai sai ta kashe abinda yake ciki. Alhaji Umar yana zuwa ya ganta a wannan halin yasan asiri ne dan haka ya hada malamai aka zauna addu'a da magungunan karya sihiri akayi tayi mata, in abun ya lafa kwana biyu sai ya dawo. Ta sha wahala sosai. Ranar nan cikin dare suna bacci ta tashi tafita ko dan kwali babu ta kama doguwar katangar gidan da aka zagaye da waya da kwalabe amma a haka ta haura ta var gidan cikin jinin ciwuwwukan da taji, Alhaji Umar yana tashi yaga bata nan ya fito yayi ta nema babu wanda ya ganta sai ya dauki mota ya fita hankali a tashe. Cikin ikon Allah sai ya samo ta tana ta tafiya kamar zautacciya a kamata da kyar ya saka a mota daga nan sai airport. A can ya samu yayi mata adduoin ta dawo hankalinta ya sako ta a jirgi ta taho Kano ya kira Alhaji Bukar ya gaya masa, shi kuma sai ya koma ya nuna cewa bai same ta ba. Akayi ta nema har da cigiya a gidajen radio daga baya aka hakura.

Ita kuma ta dawo gurin yaya ladi ta zauna a kano. Har ta samu lafiya sosai aka tabbatar duk sihirin dake jikinta ya fita. Anan ta haife ni, Alhaji Umar yazo da kansa yayi min huduba da suna Aliyu "saboda ka zama jarumi ya sa na saka maka Aliyu" daga nan sai ya datse igiyar aurensa da zainabu, ya kuma roki Alhaji Bukar cewa ya nemo wannan wanda take so din yayi kokarin hada su aure, bayan an samo Baffa kuma Alhaji Umar da kansa ya bashi amana ta. "Dan Allah ka rike shi tamkar kai ka haife shi. Ɗa na kowa ne ai, wata kila ma kai zaiyiwa rana bani ba. Ni dai kawai ina son shi da mahaifiyarsa su kasance safe". Through all those years da nake gurin Baffa ashe duk Alhaji Umar yana biye da rayuwata, kuma yace ko da sau daya Baffa bai taba neman wani taimako daga gare shi ba.

To bayan rasuwar Umma da Baffa, bayan na koma gidan Alhaji Bukar, sai yake gaya min cewa ya gaya wa mahaifina zancen rasuwar, amma baya kasar a lokacin yasan da zaizo gaisuwa ma amma yace a gayamin in saka rana da kaina

Please Login or Register in order to submit comment