Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

envelope ya miko min yace "nasan masu ciki da kwadayi. Gashi kya ringa siyan abinda kike so" nayi godiya har zamu tashi sai kyma ya tambaye ni "kuna waya da mijinki kuwa?" Na girgiza masa kai da sauri ina mamakin tambayar, ni da bani da waya kuma banma san number din Saghir ta yaya zamuyi waya dashi? Amma sai na fahimci wani abu, suma kansu basu san inda yake ba so suke suji koni na sani.

A gurguje muka shiga muka gaishe da Inna, sai na ajiye mata kudin da Alhaji Babba ya bani muka tafi.

A ranar da daddare har na kwanta sai naji yunwa, kuma uwani ta riga tayi baccinta dan haka dole na tashi da uban cikina na sauko kasa. Na karanto adduoi na kunna fitilar palo sannan na shiga kitchen na dauko cornflakes na fara hadawa kawai sai jikina ya bani ana kallona. Nayi saurin juyawa na kalli bakin kofa kawai sai idona ya sauka akan Saghir, ya harde hannaye a kirji ya jingina da kofa ya zuba min ido. Cup din hannuna ya zame ya fadi kasa, na ruga a firgice zuwa back door din kitchen din na bude jikina yana karkarwa na fice daga gidan na rufe kofar ta waje, ban tsaya anan bama sai na kara mai sai dana dangane da katangar gidan sannan na tsaya na toshe bakina da hannuna ina numfashi sama sama, na jima ban tsorata ba irin ranar. Sai da hankali na ya dawo jikina sannan na fahimci a inda nake sai kuma wani sabon tsoron ya sake shigata na koma wajen building din da sauri, na leka tagar kitchen sai naga babu kowa, na zagaya ta gaban gidan na leka palo shima babu kowa sannan babu mota wannan yasa na sauke ajjiyar zuciya. Wato mutumin nan har ya fara yi min gizo kenan ko?

Duk da tsoratar da nayi saboda abu irin na mai ciki sai dana karasa hada cornflakes dina sannan na koma sama na sha a daki na wanke bakina nayi addu'a nayi kwanciya ta a raina ina cewa "aniyar Saghir ta koma kansa". Dasafe kamar kullum bayan na gama karatu na da azkar dina na tashi uwani muka fara gyaran gida tare, muna yi muna hirarrakin mu har muka gama da sama muka dauko kasa, dama mun saba indai mukayi wannan saukowar kuma to sai dare zamu sake hawa dan anan kasa muke wuni. Tana cikin mopping ninkuma ina goge tv kawai sai mukaji motsi kamar ana saukowa daga sama, muka kasa kunne a tare sai kuwa muka tabbatar lallai saukowar ake yi dan haka muka fa eeèra rige rigen neman gurin buya sai kawai ga Saghir ya sauko. Yaci kwalliya kamar kullum, sai kamshin turare yake yi, nayi sauri na buya a bayan uwani ina jin tsanarsa tana karuwa a raina. Kallo daya yayi mana daga ni har uwanin ya cigaba da tafiyar sa zai fita daga palon, sai kuma naga ya tsaya ya juyo yana kallona, amma vani yake kallo ba cikin jikina yake kallo, na saka hannayena na rufe cikin dasu, sai ya juyo ya doso inda nake tsaye yazo daf dani ya tsaya, ya kalli cikin yace "meye wannan?" Na tattaro duk sauran rashin kunyar da take tare dani nace "oho, nima bansan menene ba" muka tsaya muna kallon kallo, ya tsare ni da ido ni kuma naki cire nawa idon daga cikin nasa. Uwani tana gefe tace "kyautar Allah ce, kyautar da babu wanda zai baka sai shi. Sai a karba kuma a gode masa" bai kyalleta ba yace min "so this is your plan ko? Wannan shine abinda kika shirya dan ki zauna a gidan nan?" Na girgiza kaina nace "believe me, a zuciyata bayan kiyayyarka babu kiyayyar abinda tafi karfi irin ta abinda yake ciki na, and one day, ranar dana haifesu a ranar zan baka kayanka and then it will be my turn to run away" ya hade rai yace "su?" Na daga gira daya nace "yes, su biyu ne" ya sake kallon cikin sai kuma ya kalleni yace "Allah ya kaimu. Ranar da zaki bani su din" ya juya kamar zai tafi sai kuma ya tsaya ya juyo yace "ohhh, and I didn't run away kamar wani marar gaskiya, tafiya ce ta same ni" sai daya fita daga palon sannan na sauke ajjiyar zuciya saboda tunda ya tsaya kusa dani na rike numfashi na saboda tsoro da kuma kamshin turarensa da yake kokarin sakani amai.

Uwani ta fara jera min wa'azi. Ba'a yiwa miji haka, namiji shi tarairayarsa akeyi da kalamai masu dadi, hakan shine zai siya miki martaba a idon shi. Nace "shi kuma fa, menene zai siya masa martaba a nawa idon?" Ta bini da kallo kawai ta rasa amsar bani. Na leka ta window ina hangoshi har ya je gate, naga yayi magana da mai gadi sai kuma ya fita daga gidan a kafa. A raina nace "ina motar?".

Bai dawo ba sai dare, ina kitchen ina wanke wanke naji shigowar sa ya haye sama ya shiga dakinsa. Sai ga uwani ta shigo kitchen din tace min "mijinki ya dawo, maza ki zuba abinci ki kai masa" na bita da kallo kamar wadda tayi saɓo. Taga bani da niyya sai ta zuba ta dora a tray tace inje in kai masa. Na dauka kamar gaske na tafi, naje kofar dakinsa na ajiye dai dai bakin kofa a raina ina addu'ar yana fitowa yayi tuntube dashi ya bata kayansa. Sai na shiga daki na na dan zauna kadan dan kar taga na koma da wuri sannan na dawo gurinta.

Haka muka kasance for about a week. Ko magana ta fatar baki bata hadamu kuma kullum d sassafe ya ke fita sannan ya dawo da dare, kuma kullum sai uwani ta saka ni na kai masa abinci ni kuma sai in ajiye a bakin kof inyi tafiya ta, ranar nan naje ina ajiye abincin sai ya bude kofar, na maze nayi kamar wucewa nazo yi shi kuma ya hade rai yace "ke, zonan" na tsaya ina kallonsa yace "ubanwa kike jerawa abinci a bakin kofa kamar dakin bera? Nan an gaya miki gurin ajjiyar abinci ne?" Nayi shiru still ina kallonshi. Yayi tsaki yace "ga tsaurin ido kuwa, anayi mata magana tana tsatstsare mutane da ido. Ki dauka ki shigo dashi ciki nace" na dauka nazo na wuce ta gabansa na shiga, first time dana shiga dakinsa, naga wani table a gefe na dora tray din akai ina lura da irin dattin da dakin yayi, kaya a barbaje har kan gado, takeaway packs sun cika waste basket. Na dauke kaina zan fita ya zauna a bakin gado yace "zuba min abincin" naji raina ya fara baci, wata zuciyar tana gaya min in zuba masa abincin aka in fita da gudu. Na bude na zuba masa shinkafa a plate na dauko miya zan zuba yace "mayar, bana cin shinkafa" na daga kafada na mayar da ita na juye na dauki tray na zanyi gaba yace "menene a wancan bowl din?" Na bata rai nace kwadon zogale ne, ni nayi zanci shine uwani tace in zuba maka wai ko zaka ci" sai naga ya dauke kai yana murmushi, sai kuma ya hade rai ya miko hannu yace "bani" na ajiye tray din na dauki bowl din na mika masa. Charaf ya kama hannuna, na saki bowl din ya fadi akan carpet zogalen ya zube, na fara kokawar kwace hannuna da dukkan karfina amma ko zegau, kuma wai hannu daya fa kawai ya saka ya rike ni. Sai da na gaji da kokawa ta sannan na tsaya ina mayar da numfashi ido cike da hawaye, ya gyara zamansa yace "kin gama kokawar?" Na gyada kaina, yace "good, then listen to me. Am sorry for what I did to you ranar nan. I was drunk" nayi noticing yadda ya fadi drunk din as if it is a normal thing, ya cigaba "bama zan iya tuna details of what happened ba, nasan dai kinyi min rashin kunya kuma ke shine problem dinki baki da kunya, I remember you even threatened me with a knife. But har cikin raina ni banyi niyyar tabaki ba saboda kamar yadda na fada wa Alhaji amma yaki yarda, kinyi min kankanta. Yanzu kin yafe min?" Nayi saurin girgiza kaina, yayi ajjiyar zuciya yace "maybe later. But look on the bright side, babies, har guda biyu. Ni da bansa ran ko daya ba sai gani da guda biyu. Alhaji yace min boys ne ko?" Ban bashi amsa ba sai yayi dariya, the first time da naga yayi dariya, yace "twin boys, in kika haifi twins din nan kin gama biyawa Alhaji bukatar sa ta duniya, you will be his second favorite person bayan ni" ya saki hannuna nayi saurin ja da baya ina goggoge hannun da hijab dina. Yace "Hajiya tace min SC za'ayi miki at 36 weeks ko?" Na dauke kaina nayi hanyar waje yace "how many weeks ne yanzu cikin?" Sai dana bude kofa sannan na juyo nace "oho, ban sani ba, amma ai zaka iya lissafawa saboda kai kafi kowa sanin ranar da akayi cikin" na juya da sauri na fita ina jinsa yana cewa "still with the rashin kunya ko?"

Tun daga ranar ya dan fara kulani, misali in zai fita zai neme ni yace min ya fita, in ya dawo kuma uwani zata saka lallai in kai masa abinci. A lokacin ne nake lura cewa most of the times a buge yake dawowa gida, ni kuma dana ji wannan warin a tare dashi zan gudu. Duk lokacin zuwa asibiti na, Mama ce take zuwa da kanta ta dauke ni muje bata taba fashi ba, kullum kuma tana gaya min "dan lafiyar ki nake yin wannan abin Diyam ba wai dan yayan cikin ki ba, in an haife su dole zan so su saboda jikoki nane amma a yanzu lafiyar ki tafi su muhimmanci". Alhaji Babba kuwa lokuta da dama da kansa yake zuwa har gida wai yazo ganina ya duba lafiya ta, Hajiya kuma kullum tana cikin aiko min da kayayyakin kwalama wai duk cikin nuna kulawa ne, ni kuwa nasan bani suke yiwa ba abin cikina suke yiwa. Sai na samu kaina da tunanin inba sa'a naci ba yadda suka lalata Saghir haka zasuyi wa duk abinda zan haifa, ni kuwa I can't even begin to imagine myself as a mother of yaya masu halayyar Saghir har guda biyu. A haka har cikina ya kai 32 weeks, and that's when it happens.

Ranar wata laraba, Saghir ya dawo kamar yadda ya saba dawowa ni kuma na zuba abinci na kai masa kamar kullum. Ina shiga dakin naji wannan familiar warin dan haka na tabbatar yau ma a bugensa yake. Na ganshi a kwance daga shi sai singlet da gajeren wando yayi dai dai akan gado, na lallaba na ajiye abincin na juya zan fita kenan sai ganinsa nayi a gaba na yana kallona kasa kasa fuskarsa da murmushi, sannan cikin irin voice din da bazan manta ba yace "wai ke kullum sai ki shigo min daki kina wani lallabawa a tsorace kamar dakin dodo, ko ni dodo ne?" Ban bashi amsa ba na chanja hanya sai naji ya damko hannuna ta cikin hijab dina ya dawo dani baya, na fara kokarin ture shi nace "don't touch me" ya maimaita cikin kwaikwayon muryata "don't touch me, shikenan dai kullum don't touch me sai kace wani abin tabawar ne a jikin nata, bayan bata da komai haka aka kawo ta gidan nan, kirjin ma sai dana mammatso su sannan suka fito" naji hawaye yana bin fuskata, na ture shi na bude kofa da sauri na fita palo amma kafin inyi nisa ya kuma kamo hijab dina da karfi ya finciko ni baya, naji bayana ya amsa da karfi na saki kara. Ya zare hijab din yana cewa "ke dai kiyi ta yawo da wannan dogon abin, ke ko zafi ba kya ji?" Na sakar masa hijab din na durkusa a kasa saboda bayana da naji ya kasa mikewa straight, Sai kuma idonsa ya sauka kan dogon gashina da ya zubo har saman bayana ya bude ido yace "well well well, what do we have here. I always have a thing for mata masu dogon gashi" sai ya nannade hannunsa a cikin gashina ya dago ni tsaye da gashin, naji tamkar fatar kan gabaki daya yake cirewa, ba shiri na saki bayana dana rike na kama kaina na saki kara. Ban kuma jin abinda yake cewa ba saboda azaba sai jin muryar uwani nayi tana cewa "Saghir baka da hankali? Ka sake ta mana, baka ganin halin da take ciki?" Sai kuma ya sake ni, uwani tayi saurin rike ni muka bishi da kallo ya tafi dakinsa yana harhada hanya.

Uwani ta kama ni ta kaini dakina tana yi min sannu. Na durkusa a kasa inajin kaina kamar zai tsage da baya na shima ya rike. Sai naga ta dauko wayarta tana waya amma bana jin me take cewa na dai ji ta ambaci sunana da sunan Saghir. Daga nan baccin azaba ya dauke ni. Sanda na farka cikin dare ni kadai ce a dakin a kwance a kan gado, wani irin mugun ciwon baya ne ya tashe ni nakasa mikewa ma tsaye ballantana in fito in nemi taimakon wani, haka nayi ta murkususu ni kadai akan gado ina karanto duk adduoin da suka zo bakina. Ban samu bacci ba sai da aka fara kiraye kirayen sallah.

Sai da gari ya fara haske sannan na lallaba na tashi nayi sallah, nayi azkar sannan na kuma kwanciya akan sallayar na sake komawa wani baccin. Lokacin dana sake farkawa sai naji ciwon kan ya lafa sosai sai bayan ne har yanzu amma shima ba kamar cikin dare ba. Na fito na duba agogo naga 20:32, nasan already Saghir ya fita dan haka na sauko kasa gurin uwani. A zaune na same ta da jakar kayanta a gabanta ga mayafinta a kusa da ita. Na tsaya ina kallon ta nace "wannan kayan kuma fa? Wanki zaki bayar?" Tace min "zauna Diyam" na zauna a kusa da ita tace "dazu da sassafe mijinki ya shigo nan, yazo ya same ni ya kare min zagi tas wai ni munafuka ce na hada shi da mahaifiyarsa. Yace min in fita in bar masa gidan sa kar ya dawo ya same ni" na mike tsaye zan fara masifa "lallai ma Saghir din nan, yanzu ke din zai yiwa wannan rashin kunyar?" Tace "ni dai abinda nasan nayi shine jiya da naga yana neman halaka ki na kira uwarsa, ni kuma abinda yasa na kira ta shine naga halin da kike ciki wai ko za'a zo a kaiki asibiti ko kuma a turo ma'aikaciyar lafiya ta duba ki, ni bansan me ta kira shi tace masa ba shine yazo yayi min wannan diban albarkar" nace "kira hajiyan to sai mu gaya mata abinda yayi, ita zata san abinda zata yi akai" tace "hmmm. Ai yana fita ita din na kirawo, tunda tun farko ai ita ce tace inzo in zauna din, amma dana gaya mata abinda yace sai cewa tayi in tafi can gidan kawai tunda yace baya son zama na anan din. Tace zata samo wata ta turo miki take kula dake" naji raina ya kara baci, hawaye yana bin fuskata nace "wannan wacce irin rayuwa ce, yanzu ace mutum babu yadda za'ayi yayi abu ba daidai ba a gyara masa sai ya zama laifi. Yanzu jiyan da ace ba kyanan Allah ne kadai yasan abinda zaiyi min. Ni ba zan zauna ba uwani, kina tafiya nima binki zanyi, bazan zan zauna ya kashe ni ba" uwani tace "a'a, ba zaki bini ba Diyam, ina tafiya dake cewa za'ayi nazo na kashe miki aure. Ni dai yanzu in naje zan gayawa mahaifiyar ki halin da kike ciki, itace take da hakkin zuwa ta tafi dake".

Ina ji ina gani uwani ta dauki jakarta ta fita, na raka ta har bakin gate ina hawaye tayi sallama da mai gadi wanda har sun saba dashi sosai, na tsaya ina kallonta har tayi nisa sannan na dawo cikin gida na rufe kofa. Na kwanta akan kujera ina tunanin wannan wacce irin kaddara ce ta hau kaina, wacce irin tarbiyya Saghir zai yiwa yayan mu bayan shi kansa ba tarbiyyar ce dashi ba? Ina nan kwance dai har yunwa ta kamani na tashi na shiga kitchen sai na tarar ashe uwani ta ajiye min dumamen tuwon jiya dan tasan ina so. Na dauko na dawo palo na zauna ina ci kawai naji ciwon bayan ya dawo and this time yafi na dare karfi. Yayi ya lafa ya sake dawowa kamar bayana zai rabu da jikina. A haka azahar ta same ni, la'asar ma tazo, sai dari ya fara duhu. A lokacin ciwon bayan ya hade har da cikina da mara ta. Na lallaba na koma sama ina tunanin wannan wanne irin ciwo ne haka tunda ni dai cikina ai bai isa haihuwa ba ballantana inyi tunanin ko nakuda ce. Bayan nayi sallar magrib ne kuma sai na kasa kofa tashi daga kan sallaya ta saboda azabar ciwo, ban taba addu'ar ganin Saghir ba sai a wannan rana na ringa addu'ar Allah yasa ya dawo da wuri ya kaini asibiti, wannan wanne irin ciwo ne haka? Ga yunwa dan tun tuwon safe ban kuma cin komai ba, ga babu waya a hannuna ballantana in kira in nemi taimako.

Shiru shiru babu Saghir babu labarin sa tun ina duba agogo har na daina. Sai kuma kamar daga sama naji tsayuwar motarsa, na daddafa da kyar na mike amma ina tsayuwa sai naji kamar an bude famfo ruwa yana fita ta kasana, nace na shiga uku ni Diyam fitsari nake a tsaye ko me?

Tun daga yanayin yadda yayi packing nasan cewa yau ma ba kalau yake ba, ina jin motsin shigowar sa palo sannan naji ya hawo sama, sai dai banji ya bude dakinsa ba. Na jima ina tattaro karfina sannan na fara bin bango na fita daga dakin. A palon sama na same shi, ya cire rigarsa ya jefar a gefe, ya kure ac ya kwanta a kan carpet. Da rarrafe na karasa inda yake nayi masa magana "Saghir, Saghir" shiru, na dan jijjiga shi, nan ma babu alamar motsi a tare dashi. Da daga hannunsa naji ya saki. Banbancinsa da gawa shine kawai shi yana numfashi. Na fara kuka "hamma Saghir ka taimaka min zan mutu, wayyo Sadauki" amma da wani ciwon ya sake tahowa sai na nemi kukan na rasa. Lallai wani abin yafi gaban kuka.

Na tuna da maigadi a waje dan haka nayi kokarin ganin ko zan iya zuwa gurinsa ya samo min taimako, duk da cewa ba makota ne damu ba. Amma tashi ya gagare ni, kamar kafafuwana sun daina aiki. Na durkusa na kankame kujera yayinda wani irin nishi wanda bazan iya rikewa ba tazo min, ina ji har dan jaririn ya fito daga jikina, na sauke wani numfashi jikina sharkaf da gumi duk da acn da take palon. Na saka hannu na dauko shi, the smallest most cutest baby dana taba gani a rayuwata. Komai nasa irin na babansa ne except dan karamin ɗagaggen bakin sa da yake irin nawa, nayi murmushi ina jin sonsa for the first time yana huda zuciyata. But baya kuka, baya numfashi, aren't babies suppose to cry in aka haife su? Na jijjiga shi, "wake up little soldier" shiru, na dora bakina akan nasa ina hura masa iska irin yadda naga anayi a film amma shiru, na saka fingers dina guda biyu ina danna masa little kirjinsa shima shiru.

Wani ciwon ne ya sake dawo min, babu shiri na jawo rigar Saghir da ya ajiye na dora babyn akai na koma fagen fama har na haifi dan uwansa. Na dauko shi shima ina kallon fuskarsa, kamarsu daya da dan uwansa kamar an tsaga kara. Na dan jijjiga shi da dan saurin karfin daya rage min sai naga yayi motsi ya danyi kuka kadan sai kuma yayi shiru. Na ajiye shi kusa da dan uwansa ina feeling very dizzy, a lokacin ne na lura da jinin da yake malala akan tiles din palon. Na koma na kwanta kusa dasu a ina kallonsu. And it occurred to me that karshen rayuwata kenan, sai naji dadi saboda ina ganin nayi shahada na samu kyakykyawan karshe, my only regret a lokacin shine mutuwa without seeing Sadauki again.

Not edited
[2/3, 9:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Thirty Four : My Savior 2

Bansani ba ko bacci nayi ko kuma suma nayi, amma cikin either baccin ko suman ne nayi mafarki ina tsaye a cikin cincirindon mutane hannayena biyu a rike da babies dina, hawaye yana fita a idona ina kwalla kiran neman taimako amma kowa yana ta harkokin gabansa babu wanda yako kallo inda nake, can sai ga Sadauki yana kutso kai ta cikin mutanen yana tahowa inda nake amma yawan mutanen da suke gurin ya saka yakasa karasowa sai ya tsaya daga nesa yana miko min hannu, kawai sai na zubar da babies din hannuna na kama hannunsa amma ina kamawa sai ya bace ya barni ni kadai a tsakiyar mutane. Na kwalla masa kira "Sadauki! Sadauki!! Sadauki!!!" Amma bai dawo ba.

Ji nayi ana rirrike ni ana ƙoƙarin kwantar dani yayinda ni kuma nake ta yunkuri ina kiran Sadauki. Na bude idona naga nurses suna tura ni akan gadon marasa lafiya, ga Inna tana biye dasu a baya zani a hannu har suka tura ni wani daki suka rufe kofa, sai kuma naji shigar allura a hannu na, daga nan na koma baccin ko suman ne ban sani ba.

Sanda na kuma farkawa I was feeling much better, dan a hankali na bude idona na sauke su akan ledar ruwan da take sakale a jikin karfe sannan nabi tube din da ya taho daga kasanta da kallo har zuwa inda ruwan yake shiga jikina. Na fara karewa dakin kallo ina kokarin recalling abinda ya kawo ni nan. Idona ya sauka akan Inna da take zaune rashe rashe a dandaryar kasa duk kuwa da cewa akwai kujera a dakin. Kuka take da iyakacin karfinta, sai na tambayi kaina "kukan me take yi?". Abinda na fara tunawa shine kyakykyawar fuskar jarirai na, sai naji wani relief yazo min cewa ban mutu ba at least zan sake ganin su, zan dauko su in rungume su a jikina. Sai naji xewa yanzu na sami wani source of happiness din bayan Sadauki.

Nace "Inna" sai naga ta juyo da sauri gurina tana share hawayenta da gyalenta, tazo ta zauna a kusa dani ta rike hannuna wanda babu ruwan a jiki "sannu Diyam" na gyada mata kai kawai, zuciyata tana so ta tambayeta ina jarirai na amma sai baki na ya kasa furtawa. Ta tambaye ni "menene yake miki ciwo yanzu?" Na rasa me zance mata saboda duk ilahirin jikina ciwo yake yi tun daga kaina har yan yatsun kafata. Na tuna irin wahalar da nasha dan ko a mafarki ban taba tsammanin haka haihuwa take da azaba ba, na tuna mafarki na, sai naji ina jin haushin Sadauki me yasa ya rabu dani in the first place, mai yasa duk sanda nake bukatar sa nake samun bayanan?

Inna ta tashi da sauri ta fita, sai gasu sun dawo tare da wata nurse da tazo tana yi min sannu sannan ta auna bp na ta duba idona da hannuna tace da Inna "har yanzu mijin nata bai zo dawo ba? Yarinyar nan fa in ba'a kara mata jini ba za'a iya rasata, gashi har ta fara kumbura. It is a miracle ma da take a raye wallahi" Inna ta karkata kai "nayi ta kiransa wayar bata shiga wallahi, nayi ta kiran mahaifiyarsa ita ma bata dauka ba, yanzu babu wani abu da za'a iya yi mata kafin kanwata tazo? Tayi tafiya zuwa Abuja ne amma tace min yanzu zasu taho ita da mijinta" nurse din ta girgiza kai tace "gaskiya babu wani abu da zan iya yi mata ni dai, jinin nan dai shi za'a kara mata kamar leda uku first sannan kuma muga yadda za'ayi" Inna ta gyara

Please Login or Register in order to submit comment