Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min. Ya Allah tafiyar nan da Saghir yayi Allah kasa yayi hatsarin mota ya mutu kar ya dawo. Ya Allah ka hada shi da yan fashi a hanya su sabauta shi kamar yadda ya sabauta ni. Ya Allah ka saka ginin gidan da zai sauka ya fado masa cikin dare ya tarwatsa shi kamar yadda ya tarwatsa rayuwata".

Ina nan kwance matar tazo, ina jinta suka gaisa da Adda zubaida da Uwani. Sannan ta zauna kusa dani tace "amarya" na bude ido na kalleta na rufe, tace "kar ki zama raguwa mana. Tashi tsaye mu gani" nayi saurin girgiza kaina sai ta kama kafafuwana tayi bending dinsu, nayi kara saboda jin cinyoyi na nayi kamar wadda nayi frog jump, ta bude rigata tana dubawa tace "babu tear, the place is just sore kuma akwai bruises" ta rufe rigar tace "zanyi mata allurar da zata rage mata pain sannan zan rubuta muku magani ku siyo mata. Sai take amfani da ruwan dumi sosai" Adda tayi mats godiya sai ta juyo tana kallona tace "ina angon? Yazo ya mayar dani gida" ita as a joke ta fada ni kuma kalmar angon ma bata min rai tayi. Har zata fita ta juyo ta sake kallona tace "amma yarinyar nan tayi kankanta da aure wallahi Zubaida. Wai dama har yanzu fulani kuna irin wannan auren?" Ban dai ji amsar da Adda ta bata ba suka fita.

Ranar har dare Adda Zubaida tana guri na, kuma ta saka ni na shiga ruwan zafi sosai sannan kuma ta dafa min abinci mai kyau ta matsamin na ci. Sai kuma ta saka ni nayi tafiya wadda sanda ina yi ji nayi kafafuwana kamar ba'a jikina suke ba. Uwani ce ta zauna ta kwana a gurina washegari sai ga kayanta Alhaji Babba ya saka a aiko mata dasu yace ta zauna a gurina har sai Saghir ya dawo daga tafiyar da yayi. Sai da nayi kwana uku a sama ina jinyar kaina sannan na iya saukowa kasa, ina saukowa daga bene idona ya sauka akan katon hotonsa ya sha shadda army green wadda ta kara haska farar fatarsa, ya turo hular nan gaban goshi fuskarsa dauke da murmushi, sai a lokacin nayi tunanin kamar ban taba ganin murmushin sa ba. Na taka naje har gaban hoton na tsaya ina kare masa kallo sai kuma na saka hannu na ciro hoton na sauke shi kasa sannan na juya shi ya koma kallon bango.

Jikina ya warke, amma tabon zuciyata yana nan kuma banajin zai warke har abada. Saghir kuma kullum zuciyata kara tsananta tsanarsa take yi. Ko mai irin sunansa baba son inji an ambata ballantana shi. Babu sallar da zanyi ba tare da nayi addu'ar neman sakayya tsakani na dashi da duk wanda ya aura min shi ba. Kullum kuma da fargabar dawowarsa nake kwana da ita naje tashi. Ko wani kwakwkwaran motsi uwani tayi sai na firgita ballantana in naji an taba gate. Muna da kayan abinci wadanda aka kawo da sunan kayan gara, kudi kuma duk karshen sati Alhaji yana aiko mana dashi shi dai kawai burinsa in zauna a gidan. Uwani tana tare dani, kuma duk weekend su murja ko su Rumaisa sukan zo su kwanar min biyu, wannan sosai yakan rage min kewa amma a zahiri a zuciyata kuwa empty nake jin heart dina.

Kwanaki suka wuce haka satittika, sai watanni suka biyo baya har nayi wata uku a gidan Saghir amma babu shi babu alamar sa. A ranar da na cika wata ukun ne Hajiya Babba tace mu shirya muje gida mu kwana biyu. Da wuri driver yazo ya dauke mu muka tafi. Tun daga bakin gate na lura da yadda gidan ya chanja, ma'aikata sun ragu, motoci ma haka, gidan kuma yayi datti flowers sun mutu.

A main palo muka samu Hajiya Babba, har da mikewar ta tsaye ta tarye mu da fara'a "sannunku da zuwa uwani" ta jawo ni jikinta zata rungume ni sai na zame na durkusa na gaisheta, ta amsa da fara'ar ta ni kuma na mike na nufi dakin inna ta ina jin missing dinta a raina, ina jin Hajiya Babba tana cewa "Masha Allah, lallai Diyam, wannan girma haka kamar ana hura ki?"

Ina shiga na tarar da Inna tana ta murnar zuwa na itama. Na je na rungume ta tana ta dariya ta dan tura ni baya tace "Diyam kinyi girma haka? Alhamdulillah, naji dadin ganin ki sosai. Ni ina nan ina ta fargabar halin da kike ciki gashi Saghir ance yayi tafiya kasar waje business ya rike shi" na zauna akan gado ina rungume da Asma'u ina dariya. Ta zauna gefe na tana ta yi min tambayoyi game da halin da nake ciki ni kuma ina bata amsa a takaice. Tace "naso inyi miki girki tunda aka ce zaku zo, nasan kina son tuwo amma kinsan bana girki a gidan nan" na kalle ta sai na lura da yadda ta fada tayi baki bakinta duk ya bushe. Nace "inna ku ya kuke ciki? Lafiya dai ko?" Tace "hmm, lafiya lau" nayi shiru dai ina kallonta dan na fahimci ba karshen maganar ba kenan. Sai nace "Inna an saka Asma'u a makaranta kuwa?" Tace "eh an saka ta" sai ta sake shiru, ta jima kuma sannan tace "na jima inata faman bi akan zancen makarantar yarinyar nan, da kyar na samu aka saka ta amma wai ga makarantar da sauran yaran gidannan suke yi sai aka dauke ta aka saka a makarantar gwamnati. Tana kallon yaran zasu shiga mota a tafi dasu makaranta ita kuma sai dai ta tafi a kafa, har kuka sai da tayi min wai ita makarantar su siyama take so amma haka ba bata hakuri saboda babu yadda zanyi"

Naji zuciyata tana zafi nace "to Inna ke ki saka ta ata kudin mana? Ina kudin da ake samu a garejin baffa duk wannan watannin ayi amfani dashi mana a saka Asma'u a makaranta mai kyau" tace "hmmm. Diyam kenan. Wanne gareji kuma kike magana? Tun a lokacin bikin ki nayi wa Alhaji maganar gare jin kinsan me yace min?" Na girgiza kaina tace "yace garejin shi aka siyar akayi miki kayan daki" na bude baki ina kallon ta nace "garejin? Da duk motocin da suke ciki?" Eh kawai tace, na sunkuyar da kaina sannan nace "filin Sadauki fa? An bashi kayansa?" A can kasa ta amsa tace "har dashi ya sayar".

Na tashi na shiga toilet na hada kaina da kofa, rabona da in kira sunan Sadauki tun ranar da aka kaini gidan Saghir amma ni kadai na san me nake ji a zuciyata, I missed him so badly dan tunda nazo duniya ban taba yin wannan dadewar ba tare dana ganshi ba yanzu kuma ambatar sunansa ya tayar min da mikin dake cikin zuciyata. Na tuna ranar da yaje school gurina da murnarsa yake bani labarin Baffa ya saya masa fili, kuma da kudinsa daya tara masa ya siya masa his hard earned money amma wai Alhaji Babba ya siyar. Ban roki Allah sakayya bama saboda nasan tabbas zai yi maybe slowly but surely.

Bayan na dawo dakin ne uwani ta shigo suka gaisa da Inna ta kuma kawo min mangwaro na dana siya a hanya. Inna ta karba tana cewa "wannan mangwaron Diyam ai bai nuna ba aka baku shi" na karba na fara sha ina cewa "yafi dadi ai" sai ta tsaya tana kallona sannan ta juya ta kalli uwani tana girgiza kai sai naga uwani ta gyada mata kai, sai kuma suka juyo suna kallona a tare ina ta rasgar danyen mangwaro. A raina nace "su kuma wadannan menene naga suna magana da ka kamar kurame?".

Not edited
[1/31, 9:21 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman maama

Episode Thirty One : The Broken Heart

Inna ta saka na zagaya na gaishe da mutanen gidan, kuma kowa naje sai ta yi comment akan girman da nayi, ni kuma sam banga wani girma da nayi ba na dai san cewa kirjina ya kara cika amma bayan shi ban kara komai ba. Ina dawowa dakin inna na tarar an aiko min da abinci kala kala daga gurin Hajiya Babba, inna tace "da yake surukar ta tazo shine ta aiko mata da abinci, amma mu yaushe rabon da muga kwano daga dakinta" ni dai bance komai ba na fara bubbuda flasks din zaben abinda zanci, na samu wani farfesun kaji na ja gefe na fara ci. Ina cikin ci Hajiya Yalwati ta shigo, ta kalli lodin abincin tace "hmmm. Ana cewa babu kudi bayan kudin suna can a inda aka ajiye su" Inna tayi dariya tace "ke kam ba kya rabo da bakar magana".

A dakin Inna na wuni, sai da yamma ta tura ni inje in gaida Alhaji, kuma in shiga gidan Kawu Isa suma in gaishe su. Sai a lokacin na fahimci cewa ashe Alhaji Babba bashi da lafiya yana kwance. Ina dawowa sai ga sako dafa Hajiya Babba wai inje an gyara min daki a gurinta inje in sauka a can. Naki zuwa nace ace mata na gode amma a gurin Inna zan zauna, sai nayi sa'a kuma innar bata matsamin in tafi din ba.

Da daddare Inna take gaya min cewa gobe ne zata fita daga takaba, ashe shine dalilin da yasa aka dauko ni. Sai na tambayeta "Mama zata zo goben?" Inna tace "inajin zata zo, wani abun ne?" Nace "dama wata tambaya nake so inyi mata" ta zauna a kusa dani tace "tambayar me fa?" Sai na fara jujjuya hannuna ina feeling uncomfortable, ni ban saba irin wannan maganar da Inna ba dama Ummah ce da sauki. Sai data sake tambayata sannan nace "so na ke inji, wai dama in mutum yayi aure sai ya daina period? Dama matan aure basayi?" Sai ta tashi ta bude wardrobe kamar mai dauko wani abu, ta jingina kanta da kofar tace "yaushe rabon da kiyi?" Nace "tun kafin.....tun kafin biki" tace "wata uku kenan ko?" Na ce "eh" tace "matan aure sunayi Diyam, sai dai in matar aure tana da ciki ne bata yi" naji kaina ya kulle nace "ciki?" Sai kawai ta juyo tana kallo na, na dan yi shiru ina tunanin kalmar ciki sai kuma lokaci daya naji tamkar an ciro zuciyata an buga ta da kasa ta tarwatse. Nayi saurin rike kirjina na zamo daga kan gadon na fado kasa, a hankali na fara kiran innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Inna ta taho da sauri ta rike ni tana kokarin daga ni amma na dunkule a guri daya danji nake yi tamkar idan na mike zuciyata zata fado daga kirjina. Amma hawaye yaki zuwa idona, kalmar ciki ce kawai take yawo a kaina, wai ciki nake dashi ni Diyam kuma cikin ma wai na Saghir wannan wacce irin jarabawa ce, wannan wacce irin rayuwa ce. Har yanzu banyi accepting Saghir a matsayin miji na ba ballantana kuma in karbe shi a matsayin uban yayana. Inna ta rike ni tana cewa "haba Diyam, menene hakan kuma daga maganar ciki? Ciki yar kyautar Allah ne in aka same shi murna ya kamata ayi a kuma godewa Allah" sai na kifa kaina a jikinta ina jan numfashi da kyar. Na rufe ido na ina tunano fuskar Sadauki. Wannan cikin tamkar yayi sealing aurena da Saghir ne, tamkar ya tabbatar da rabuwa ta da Sadauki kenan.

Ranar yadda naga rana haka naga dare. Ina jin ko lokacin da aka daura min aure da Saghir ban shiga irin wannan tashin hankalin ba. Sai bayan nayi salllah asuba sannan nayi bacci dan haka har mutane suka fara zuwa yiwa Inna gaisuwa da kuma taya ta murnar fita daga takaba ban tashi ba, dagabaya ma dana farka sai na yi kwanciya ta har saida naji muryar Mama sannan na tashi na gaisheta. Ta bini da kallo kamar mai accessing dina, wannan yasa na koma na kwanta na lulluba dan ji nake yi kamar duk wanda ya ganni yana iya hango cikin jikina.

Ina kwance Mama ta shigo tace "Diyam taso ki raka ni unguwa" da sauri na mike ina straightening hijab dina dan ba karamin gajiya nayi da gidan da duk mutanen da ke cikinsa ba. Muna shiga muka shiga motar da tazo da ita, Mukhtar yana ja muka tafi sai na gan mu munzo wani asibiti, naji gabana ya fadi ina tuna ranar da aka kaini asibiti naga gawar Baffa, ranar da rayuwata ta tarwatse. Na tambayeta "Mama waye bashi da lafiya?" Tace "ba kowa, ke na kawo kiga likita" sai na sunkuyar da kaina a raina ina cewa Inna ta gaya mata kenan. Da yake asibitin kudi ne dan haka muna zuwa aka dauki jini na for a confirmation test, mu ka zauna jira sai kuma aka kira mu dakin likita, muka shiga suka gaisa da Mama sannan nima na gaishe shi ya dauko result din yana kallona yace "Halima Usman Kollere?" Na gyada masa kai, yace "how old are you?" Nace "14" sai naji kalmar 14 din tana burning a kirjina. Ya girgiza kai yana kallon Mama yace "how comes? Yarki ce?" Ta gyada kai tace "yar yaya tace, mahaifinta ya rasu shine yan uwansa suka aurar da ita ga dansu" ya girgiza kai yana kallona sannan yace "well, she is pregnant. Zamuyi scanning dai muga wata nawa ne sannan muga in ya shiga yadda ya kamata, za kuma mu duba lafiyar mahaifarta in zata iya daukar nauyin cikin" nayi sauri dago kai ina kallon doctor din, da rawar murya nace "doctor please ka cire cikin nan bana so" Mama tace "kul Diyam, kar in sake jin kince ba kyason abinda yake cikin ki. Allah ne fa ya baki ajjiya, ba naki bane ba na Allah ne kuma shi kadai zai karbi kayansa a lokacin da yake ganin ya dace".

Muka je na kwanta akan gado Mama tana rike da hannuna da yake rawa saboda tsoro. Doctor ya zuba min wani abu mai sanyi a mara ta sannan ya fara goga wata roba akai yana kallon screen din gabansa, can sai naji yace "wow wow." Ya juyo yana kallon Mama yace "we are having twins here".

Bayan an gama scanning din mun koma mun zauna yace "gaskiyar magana yarinyar nan tayi kankanta, bayan rashin shekaru gashi kuma tana da kankantar jiki, she can carry the pregnancy but I strongly suggest that kar a barta tayi labor, musamman tunda she is carrying multiple a shawarce da ta kai around 36 weeks ku kawo ta a cire babies din saboda lafiyar ta" Mama ta gyada kai da sauri tace "insha Allah doctor hakan za'ayi" ya tura mu mukayi sauran tests sannan ya rubuta mana drugs ya sallame mu.

Hankalina idan yayi dubu to duk ya tashi, dan tunda doctor yace twins ne bankara magana ba dan in nayi ma inajin muryar ba zata fita ba. Wato ba daya ba, ƴaƴan Saghir guda biyu ne a cikina. Har muka zo gida bance komai ba ina dai jin Mama tana tayi min bayanai da yadda zan kula da kaina da abincin da ya dace in ke ci, ni dai na jingina jsina da kofar mota kawai na rufe idona.

Muna packing su Salma suna fitowa ita da Aysha zasu tafi gidajen su, bana son magana dan haka ko kallon su banyi ba nazo zan wuce ta kusa dasu Salma tace "oh su Diyam manya, kamar ba itace nan take ta koke koke ba wai bata son auren hamma amma gata nan harda ciki. Ni ko zanso inga yadda akayi cikin nan". Sai suka kyalkyale da dariya. Har na taka step zan shiga palo sai na tsaya ina juya kai, it is hardly a gaya min magana inyi shiru and this is not going to be the first time. Na juya na sha gabanta nace "yes bana son yayanki kuma har duniya ta nade ba zan so shi ba ko da kuwa zan haifa masa duk mutanen da suke duniyar nan. Ni ma kuma zanso ace kinga yadda akayi wannan cikin dan a lokacin ne zaki tabbatar cewa yayanku is nothing but a monster, a big for nothing monster". Mama tazo da sauri ta jani muka wuce, amma naji dadi a raina.

Mu da muka zo da niyyar kwana biyu sai da mukayi sati. A cikin satin na fahimci abubuwa da yawa, na farko shine arzikin Alhaji Babba ya ragu sosai, dan naji ana cewa yanzu shagunan sa na kantin kwari ne kadai suke functioning. Abu na biyu Inna tana cikin damuwa game da negligence da take fuskanta a gidan, babu wanda yake daukan abinsa ya bata dan zumunci sai dai idan ta roka, hatta sabulun wanka da wanki sai ta roka za'a bata.

Da safiyar ranar da zamu tafi Inna ta dauko wasu kudi ta bude hannu na ta saka min, nace "kudin menene wannan?" Tace "kudin sadakin kine" na kalli kudin ina jujjuya sannan nace "me zanyi dasu?" Sai tayi murmushi tace "ki sayi wani abu dasu, duk abinda kike so" a hankali nace "ni babu abinda nake so Inna, ni yanzu babu abinda nake tunanin zai saka ni farin ciki, Sadauki shine farin ciki na kuma a yanzu bana jin zan kuma ganinsa har abada" sai na bude hannunta na saka mata kudin nace "ki karbi wannan kudin inna dan Allah ki dauki Asma'u ku bar gidan nan. Ki koms gida ki samo masu rabon gado su fitar wa da Ummah gadonta a gidan mu ki danka a hannun yaya ladi ko Sadauki. Misali in aka fitar masu da dakunan Ummah sai su fitar da kofa daban. Dakunan ki kuma zaki iya saka yan haya a ciki ke kuma sai ki zauna a dakunan Baffa. Kinga kudin hayar zaki iya wani abu dashi sannan kuma zaki samu security yafi ki zauna ke kadai. Kudin nan kuma dubu hamsin sai ki kama sana'a dasu, idan ba zasu isa ba sai ki siyar da kayan dakin ki ko na dakin Baffa ki kara. A yanzu abinda zai sani farin ciki inna shine in ganku a farin ciki" sai naga hawaye yana fita daga idonta, tayi sauri ta goge tace "Diyam. Ni a tunani na abinda nayi miki shine dai dai, amma na rasa me yasa na kasa jin farin ciki a zuciya ta" sai ta dawo min da kudin hannuna tace "bazan karbi sadakin ki ba Diyam. Ki ajiye su, wata rana zasu yi miki amfani" nace "to Inna zaki tafi din?" Nan ma sai ta girgiza kai tace "ba zaki gane ba Diyam".

Sai nayi shiru ina kallonta, sai nayi realizing wani abu, ba wai gidan Alhaji Babba ne bata son bari ba but she is not strong enough to stand on her own, tana bukatar shoulder da zata jingina da ita. Na tuna cewa a kauye aka haife ta a can kuma ta girma ba tare da tayi karatun boko ba, sannan aka aura mata Baffa ya raho da ita kano ya ajiye ta a gida. Tunda na taso ban taba ganin inna da kawa ba, babu wanda ta sani sai Mama da Aunty Hafsa sune kawayenta, in dai Inna ta fita unguwa to in ba gidan su ba to gidan Alhaji Babba ko kawu Isa, gaba daya rayuwarta tayi revolving ne around them. Wannan ne ya kara banbanta ta da Ummah tunda ita Ummah tayi karatu a hannun Alhaji Bukar dan haka ta waye sosai tayi kawaye. Wannan yasa yanzu it will be hard for Inna ta tsaya da kafafuwanta, ko kuma tayi challenging Alhaji Babba. Maybe nan gaba.

A ranar da muka koma gida ni da uwani sai naji gidan yayi min wani iri, kuma nasan hakan yana da dangantaka da sanin da nayi cewa ina da ciki, twins, cikin Saghir. Da dare sai na bude balcony din da yake hade da palon sama. Na tsaya na lunshe idona ina jin dadin iskar da take kadawa, na bude idona naga sky ta cika da stars ga wata ya zama full. A hankali nace "Sadauki where are you?" Sai na tuno abinda ya taba fadamin "You Are The Only Star In My Sky" na shafa marata ina tunanin babies din da suke ciki amma sam banji wata soyayya tasu a raina ba. I can give anything to have them taken away from me. Da Sadauki na shirya haihuwa, dashi na shirya rayuwar aure. Da Sadauki nayi wannan plan din, dashi na shirya zanyi rayuwar aure har in samu ciki har in haifa mana ya'ya. Mace mukayi fatan zamu samu daga farko sai mu saka mata subay'a sunan yar tsana ta, daga nan sai mu haifi namiji mu saka masa sunan Baffa mu kira shi da Junior.......... Ya Allah take my life please, ya Allah end my suffering please. Sai na rike railers din gurin na durkusa ina kuka a hankali. The first tears da nayi shading tun first night dina a gidan.
[2/2, 8:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Thirty Two and Three : The Lost Treasure 1 & 2

Sai da nayi kuka na mai isa ta sannan na tashi daga gurin na dawo palo, sai naji zuciyata tayi min dadi dan at least na dan samu relief na zafin da take yi min. Na zauna a kujera ina karewa kayan gurin kallo, kayan da aka ce an siya min with my father's life time earnings. Sai na tuno da yadda kullum Baffa da Sadauki suke fita tun safe suna aiki a gareji basa dawowa sai magrib basu da weekend basu da public holidays kullum cikin aiki suke. Na hango yadda Sadauki yake dawowa a gajiye kayansa duk bakin mai ya bata su inyi tayi masa dariya. Na tuna sanda yake bani labarin filinsa "anan zan gina mana gidan mu ni dake Diyam". Na lunshe idona a hankali nace "Allah ya isa".

Washegari su Rumaisa suka zo, a lokacin ne suke gaya min cewa anyi hutun first term, sai na samu kaina da tambayar kaina 'ko yaushe za'a saka ni a makarantar da akayi min alkawari? Nasan in nayi magana ma yanzu cewa za'ayi ga ciki kuma wacce makaranta zan shiga sai dai in bari sai na haihu.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar min cikin kunci da bacin rai, ga kuma laulayi daya sauko min a lokaci daya, bani da damar inci abinci sai na amayar dashi. Baba son kamshi kwata kwata kona turare ko na sabulu, ga kadaici. Inda Allah ya taimake ni ina tare da uwani wadda take taimaka min sosai dan kusan duk aiyukan gidan ita take yi, sannan tayi min girkin duk abinda nace inaso, wani lokacin kuma ina gama ci zan shiga toilet in amayar dashi gaba daya sannan in dawo ince mata wani nakeso daban. Uwani tana daga cikin mutanen da bazan taba manta alkairin su ba.

Ciki na yana wata biyar, amma in ka ganshi zaka dauka yayi bakwai saboda girma. Lokacin kuma laulayi na yayi sauki sosai. Sannan kuma a lokacin ne muka sake komawa scanning ga mamaki na muna hanya sai ga wayar Alhaji Babba yana cewa da Mama wai a duba masa sex din babies din. Ina jin Mama tana mita "shi Alhaji Babba wai har yanzu ba zai dauki ishara akan wannan son yaya mazan nasa ba? Shin Saghir ba zai zamar masa darasi ba?" Ni dai bance komai ba amma a zuciya ta ina ta addu'a "Allah kasa mata ne, ya Allah kasa mata ne" amma muna zuwa doctor ya duba ya kalleni yace "congratulations, you are having twin boys" na runtse idona, it is official, bani da sa'a a rayuwa ta. Sai kuma nayi sauri nayi istigfari akan sabon da nayi.

Tun a asibitin Mama ta kira Alhaji Babba tayi masa albishir, ai kuwa daga nan direct gidansa yace a kawo ni ya ganni. Muna zuwa muka wuce part dinsa muka same shi zaune a palo shida Hajiya Babba muka gaishe su, yace "Diyam ba dan bani da isassun kuda de ba da kasar waje zan fita dake ki haihu a can. Amma yanzu ma ina saka ran wasu kudade, indai sun samu kafin lokacin haihuwar ki to duk kasar da kike so nan za'a kaiki ki haihu" Hajiya Babba tana ta washe baki tayi min godiya ni kuwa ko ci kanka bance masa ba. Sai ya dauko wasu kudi a

Please Login or Register in order to submit comment