Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi da shanyayyen barin jiki saboda na kasa adalci? Kina ganin zan iya jera wata dake a zuciyata Halima?" Ta turo baki tace "daɗin baki" yace "au baki na yana da dadi dama? Ai ban sani ba nasan dai naki yana da mugun dadi. Let's taste and find out na waye yafi dadi".

Tafiyar su tazo dai dai da hutun su Subay'a. Dan haka Sadauki yace zasu tafi da ita da Asma'u suyi musu hutu a can kuma su taimaka musu gurin settling a sabon gidan su. Murna gurin Asma'u kamar zata tashi sama dan dadi, Diyam tana kallonta tace "kina murnar zaki je England ne ko kuma kina murnar zaki je gurinsa?" Asma'u tayi saurin yi mata signing akan tayi shiru kar Sadauki yaji. Diyam ta daga murya tace "eh, Bassam da kuke waya dashi Asma'u nace kinga kuwa a can yake karatu, nasan zaku ke haduwa in kinje" Sadauki yayi saurin juyowa daga kallon news yana kallon su yace "Bassam, menene hadin Yar asama da Bassam?" Diyam ta nuna ta tace "gata nan, tayi maka bayani". Asma'u ta fara kame kame tana rarraba ido, ya kalle ta strictly yace "bana son shashanci, idan yana sonki da gaske yazo ya same ni first kafin ya cigaba da neman ki. I know his family, amma shi din zan saka a bincika min halayensa in kuma basu yi min ba kin gama ganin sa kenan. Kinji abinda nace?" da sauri Asma'u ta gyada kai.

Ranar dasu Diyam suka sauka a ranar ne suma su Murjanatu suka zo. Sun taho gabaki dayansu tare da sisters dinta dan su taya su Diyam tarewa a sabon gidan su. Gidan da Diyam taga kamar yayi musu girma dan haka ta saka aka rufe part din matar gida suka zuba kayansu a part din maigida ita da Sadauki. Sai bangaren yara kuma anan Murjanatu zata zauna tare da Judith din da Diyam ta kuma gayyatowa. Daga nan kuma sai gurin ma'aikatan gidan wadanda dama suna nan already, masu kula da tsaftar gidan, masu abinci da masu gadi. A cikin kwana biyu aka gama settling komai, a ranar suna zaune gabaki dayansu matan a palo suna hira sai Sa'adatu take basu labarin abinda Papa ya gaya musu kafin su taho daga Canada, cikin kwaikwayon muryarsa tace "ke Sa'adatu dake Falmata, ku fito da miji ayi muku aure hakanan, tunda naga karatun nan naku ba karewa zaiyi ba" duk suka kwashe da dariyar yadda tayi maganar, Diyam ta harare ta tace "yanzu haka baban nawa yake magana?" Falmata ta bude hannu tace "yanzu fi sabilillahi ni ina naga mijin da zan fitar? Ni ina naga saurayin ma? Samari fa basa kula yayan masu kudi" Murjanatu ta gyara zama tace "basa kula ku dai, ku da kuke musu girman kai, ki zo in koya miki yadda ake jawo hankalin maza" anan Sadauki ya bude kofar bedroom ya fito ya tsaya yana kallon su, duk sunyi tsuru tsuru saboda basu san yana cikin daki ba sai Diyam ce kawai ta sani. Bai ce musu komai ba sai ya dauko wayarsa yayi dialing sannan yace "hello Papa" ya gaishe shi yace "maganar nan da ka yiwa su Sa'adatu, ina ganin a hada harda fanna saboda duk tafi su samari. Okay. Insha Allah. Thank you Papa. Love you too" ya juyo yana kallon fanna yace "ke ma ki fito da naki. Gaba daya guri na zasu fara zuwa First, sai nayi approving sannan zasu je gida" bai sake cewa komai ba ya saka hannayensa a aljihu yayi tafiyar sa.

Murjanatu ta zamo daga kan kujera ta fado kasa tana birgima dramatically, tace "wallahi yau na kuma tabbatar wa yaya Aliyu baya so na" su kuma duk suna tayi mata dariya. Diyam tace "alhamdulillah. Zuciyata fess yau. Karyar tara samari ta kare.

Satin su Sa'adatu daya suka koma. Su kuma su Asma'u sai da sukayi wata daya sai da hutun su ya kare sannan suka koma gida. Washegarin da suka tafi ne da assuba Diyam tana karatun Alkur'ani akan sallaya sai ga Sadauki ya dawo daga masjid. Ya zauna akan gado yana kallonta har ta idar sannan ta mike ta hawo kan gadon ta kwanta tana lulluba yace "ni fa har yanzu banga tazo ba" bata kalle shi ba tace "wacece zata zo? Bakuwa zaka yi?" Ya yaye rufar yace "yau ba zaki yi baccin nan ba sai kin gaya min akwai ko babu" ta fara yi masa shagwaba "ni me zan gaya maka. Ni babu abinda zan gaya maka" ya cire rigar da yaje masjid da ita yayi astriding dinta yace "ko ki gaya min ta lallami da lumana ko kuma ki gaya min in kinji wuya" ta fara dariya, ya sakar mata nauyinsa shima yana dariya, tayi kokarin ture shi ta kasa sai ya rike hannayenta duk biyun da hannunsa daya, yace "akwai ko babu?" Tace "to ni yanzu me kake so ince maka" yace "cewa zaki yi 'sadauki kayi min ciki" ta kwace hannunta da sauri ta rufe fuskarta tace "la ila, wai kai baka jin kunya ne?" Yana dariya yace "ina ji mana, ina jin kunyar mutane amma bana jin kunyar matata" tace "ni dai bazan iya fada ba" yace "to kinga, in akwai ki gyada kanki, in babu ki girgiza kanki" tayi shiru, yace "akwai ko babu?" Ta bude ido tana kwallon sa ta miko masa hannu tace "kawo tukuici" yace "say it, duk abinda kike so, anything" ta rufe hannun tace "in ka kawo tukuici sai kazo a gaya maka" yace "a bani bashi zan biya" ta turo baki "har yau fa baka biya ni bashin kaza ta ba kuma kake neman a kara maka wani bashin?" Ya dafe kai "wannan kaza, wannan kaza. Yanzu duk kajin gidan nan amma ban biya ba?" Tace "waccan special ce" ya mike yana saka rigarsa. "Zan siyo miki kaza yanzu, zan kuma kawo miki tukuicin ki".

Sai daya loda rigunan sanyi a jikinsa saboda sanyin da ake yi a waje, gashi kuma gari bai ko gama wayewa ba amma haka ya fita, da kyar ya samu kazar saboda duk eateries din kusa dasu basu fito ba sai da ya shiga cikin gari sosai sannan ya samu, ya siyo mata chocolates duk wadanda yasan tana so leda guda sannan ya dawo gida.

A gado ya same ta har lokacin ta lulluba tana baccinta. Ya zauna a gaban gadon ya bude ledar gasassun kajin ya yanko cinya daya ya bude fuskarta ya kai naman kusada fuskata, ta motsa idonta sannan ta bude idon cikin nauyin bacci tana kallon naman sai kuma ta kai hannu da sauri zata karba sai ya janye yace "kwadayayyiya. In kina so sai kin fada min abinda nake son ji, akwai ko babu?" Ta tashi zaune ta leko tana kallon naman kajin daya bude ya cika dakin da kamshi ga kuma chocolates din daya zube a kasa suma. Sai ta kalleshi ta gyada kai da sauri ta koma ta kwanta ta rufe fuskarta.

Wannan ciki na Diyam ya sha gata, gayu da soyayya a gurin sabon shiga Sadauki. Rigimar da tayi tunanin zasu yi akan komawarta school basu yi ba sai yanzu akan zuwa school da ciki. "Idan kuma kika fara rashin lafiya a can fa? Ko kuma in kina son ki kwanta ki huta babu gurin kwanciya? In zaki yi amai fa? Ko kuma kina sauri kin makara ki gurde ki fadi" tana dariya tace "baban baby kenan" yace "babies, kar ki rage min daraja mana" tace "okay Baban babies. Wannan cikin fa ba me laulayi bane ba, dame laulayi ne da ni da kaina zan nemi hutu. Ka barni in cigaba da zuwa please kaga yafi inyi ta zama a gida ko?" Amma fir Sadauki yaki, sai yayi enrolling dinta a online classes yadda zata zauna a gida tayi connecting da class dinsu online, duk abinda suke yi ko suke cewa tana ji kuma tana gani a screen din computer dinta, za kuma ta iya yin question a amsa mata, in bata kusa kuma zata iya saving lecture din sanda take free ta bude ta gani. Sai Murjanatu ta koma ita kadai take tafiya school sai Judith, dan ma dai ta samu at last ta koyi driving an kuma bata mota tana zuwa da ita.

Diyam babu abinda take yi sai dai taci ta sha ta kwanta tayi bacci sannan ta kula da mijinta, wanda sun rasa gane a cikinsu waye yafi kula da danuwansa. Kullum tamkar kara wa musu kaunar junansu ake yi. A lokacin ne kuma ya bayyana mata abinda yake shiryawa. "Branch nake so in bude na Abatcha Motors anan kasar, kinga sai inke siyan motocin daga nan ina aikawa dasu Nigeria kuwa zanke siyarwa anan din ma. Tunda muka zo nake processing abin amma saboda kasancewar ni ba dan kasa bane ba sai na kasa samun permit na bude Company, but alhamdulillah yanzu na samu" ya dauko takardar ya nuna mata, ta karba tana karantawa yace "har na sayi fili ma, yanzu zan fara gina gurin tukunna sai in dauki ma'aikata insha Allah" ta rungume shi cikin jin dadi tace "congratulations darling. Allah ya cigaba dayi maka jagora mijina" ya zagayo da ita gabansa yace "ameen. Yanzu problem din shine, bana son harkar bude wannan branch din ta saka ni in kasa saka ido akan wancan, though lafiya lau komai yake tafiya a can din but I need an assistant, someone that I can trust" tayi shiru tana tunani sai tace "Alhaji Bukar bashi da ya'ya? Kayi masa magana mana ya hada ka da mafi aminci a cikin yayansa kaga shima zaiji dadin ka karrama shi" yayi murmushi mai kyau sannan yayi kissing forehead dinta yace "that is one of the reasons I love you, saboda kina da tunani mai kyau. You know what? Kema na baki aiki" ta bata rai tace "wanne aiki kuma bayan wanda already nake dashi?, na matarka?" Yace "you are now my special advisor" tace "duk ka dai part of my job ne as your wife".

Koda yaushe Diyam tana lissafin Saghir a ranta, amma bata taba yiwa Sadauki maganar ba saboda bata son taba masa zuciya, duk kuma sanda suka yi waya da Subay'a sai tayi mata maganar sa, duk da cewa Inna tana yawan kaita ta ganshi. Shima Sadauki bai taba yiwa Diyam maganar Saghir din ba amma shima Subay'a bata barshi gurin tambaya ba.

A lokacin dasu Diyam suka kammala second semester dinsu a lokacin cikinta yana da watanni biyar, a lokacin kuma Sadauki har ya kammala ginin sabon branch din Abatcha Motors. Cikin Diyam ya dan fito kadan amma baiyi girma sosai ba, abinda ya fito sosai shine kyawunta, dan sanda suka fito daga jirgi a malam Aminu Kano international airport ita da Sadauki hannayensu rike dana juna, duk wanda ya kalle su sai ya sake kalla. Gidan Inna suka fara zuwa, a can suka ci abinci suka huta Diyam tana ta jin kunyar cikin jikinta, anan Sadauki ya barta sai dare yazo ya dauke ta duk da tayi ta rokonsa ya barta ta kwana biyu a nan. Yace "ina garin zaki kwana gida? Ki bari in nayi tafiya sai kiyi zauna ko kwana nawa ne kiyi musu".

A week after that, ya dawo daga office sai taga mood dinsa ba shi da kyau, tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya zauna akan kujera tare da lunshe idonsa. Ta zauna a hannun kujerar tana shafa fuskarsa tace "wanka ko abinci?" Ya dan bude ido ya kalleta yace "bara in dan huta tukunna" sai ta sauka ta durkusa a gabansa ta cire masa takalmi ta hada da briefcase dinsa ta kai sama ta dawo ta sake zama a gabansa ta cire masa safar kafa ta dora kafafun a kan cinyarta tana mammatsa masa ita, tana jan yatsun kafar. Ya dan janye kafar yana cewa "ke! Chakulkuli fa kike min" ta sake jawo kafar tace "tausa fa nake yi maka, haka ake chakulkulin?" Sai tayi masa chakulkulin gaskiya a tafin kafarsa, Yayi dariya yana tashi zaune sosai ya janye kafarsa, sai ta mike tayi kneel down tana murmushi ta faki idonsa ta saka hannunta cikin rigarsa tayi masa chakulkuli tana cewa "gana gaskiyar nan nayi maka to" ya kama dariya har da zamowa kasa ya jawo ta suka fadi tare, sai shima ya yi mata yana cewa "sai na rama wallahi" ta kama kyalkyata dariya tace "wayyo zan mutu, ka bari wallahi, chakulkuli fa kanin mutuwa ne" ya sake ta ta janye daga jikinsa tana dariya, yace "kinci sa'a bake kadai bace ba" ta murguda masa baki sannan ta dawo kusa da fuskarsa tace "wanne mai tsautsayin ne ya taba min lion dina" ya danyi tsaki yace "mutane, yanayin rayuwa, cin amana. Babu abinda wasu mutanen ba zasuyi saboda kudi ba. Babu wanda ba zasu ci amana ba akan kudi. I don't know mai mutanen mu suka mayar da kudi, abinda zaka iya samu yau gobe ka rasa, abinda zakayi bayani a lahira dalla dallar yadda akayi ka samu" tace "me ya faru?" Yace "Saghir zai fito next week insha Allah" taji dadi har cikin ranta amma sai ta boye ta danyi murmushi tace "alhamdulillah. An samu Kabir din kenan?".

Yace "tun kafin ku koma school ake neman Kabir an kasa kama shi, iyayensa sunki bada hadin kai dan haka ba'a san sanda yake shigowa gari ba ballantana sanda yake fita, nayi nayi abu ya gagara, daga baya ma sai na samu labarin wai ya kwashe iyalansa daga kano sun koma kaduna da zama baki daya. I told Ahmad amma sai yace ba zai iya kama shi a kaduna ba saboda kaduna ba a ikonsa take ba, in dai zai kama shi a can sai yana da arrest motive da zai nuna wa commissioner of police na kaduna, kuma a lokacin babu wani motive na kama kabir tunda zargi kawai akeyi babu shaida. Sai nayi tunani a kan wani abu, Nayi tunanin yadda son kudi ya kai Saghir inda yake a yanzu, na kuma tuna yadda son kudi ya saka abokinsa yayi framing dinsa, sai na tuna maganar hausawa da suke cewa sai hali yazo daya ake abota, da kuma maganar bature da yace birds of the same feathers flock together, sai na saka aka bincika min wanene next friend dinsu su biyun, sai aka hada ni da wani Bashir, kin sanshi?" Diyam ta gyada kai, yace "ranar da muka zo gari na kira shi nace ya same ni a office dina, and he came, na gaya masa abinda Kabir yayi wa Saghir ba kuma nemi ya taimaka mana mu kama Kabir din, farko sai yaki, but then as I expected sai ya fara bargaining, ya fadi kudin da yake so in bashi in ina so ya fada mana sanda Kabir zai shigo gari da kuma inda za'a same shi. I told him in yana so in bashi kudi sai dai yayi making Kabir yayi confessing cewa shi yayi framing Saghir and he agreed. I gave him some money. Yau sai gashi ya dawo, can You believe ge got Kabir drunk ya ringa yi masa questions yana amsawa shi kuma yana recording? It hurts me cewa duniya tayi lalacewar da friend zai iya yiwa friend dinsa haka, but considering abinda shima kabir din yayi sai naga yayi deserving shima ayi betraying dinsa"

"Nayi submitting record din to Ahmad, yanzu zasu iya shiga har Kaduna su kama kabir, and Saghir is coming out latest next week".

Not edited. Ayi hakuri da typos.❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Seventy Eight and Nine : Finale

Sai da Diyam ta gama da Sadauki sannan ta zauna ta kira Inna ta gaya mata labarin zancen fitowar Saghir. Inna tayi murna sosai tace "Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah yasa karshen wahalar sa kenan shi kuma Sadauki Allah ya saka masa da alkhairi" Diyam tace "ameen Inna" tace "bari in kira gidan Alhaji Babba inyi masu albishir". A ranar zance ya zagaya family, zuwa washegari yab uwa suka fara kiran Diyam suna confirming "da gaske Saghir zai fito?".

Ranar da aka kama Kabir kuwa Hajiya Babba har gidan Diyam ta zo tayi mata godiya ita da sister dinta, hawaye fal idonta, tana ta bata hakuri dan gane da rashin kyautawar da suka yi mata a baya. Diyam ta cika su da abin arziki kuma ta nuna musu babu komai ai yiwa kai ne. Sun so ganin Sadauki suyi masa godiya amma yaki fitowa yace ace musu babu komai.

Ranar da Saghir zai fito, Friday kenan, a ranar Sadauki yace da Diyam ta shirya tare zasu je. Daga gidan su gidan Inna suka fara zuwa suka dauki Subay'a sannan sannan suka tafi prison din. Suka yi packing a tsallake, Sadauki yace musu su zauna a mota ya shiga shi kadai. Bayan ya tafi Subay'a tace "Mommy nan prison ce ai" Diyam tace "eh" "inda Daddy na yake" "eh" "to Mommy mu shiga mana muhe mu ganshi" "a'a ba shiga zamuyi ba Subay'a" "to Mommy mai uncle ya shiga zaiyi a ciki?" Sai kuma ta bude ido ta ja numfashi tace "zuwa yayi ya fito dashi, dama ya gaya min zai fito dashi, Mommy ki bude min kofa inje gurin su" Diyam ta rike hannunta, sai kuma tayi murmushi tace "Subay'a uncle zuwa yayi ya fito da Daddy, amma kiyi zamanki a mota tunda uncle bai ce ki fito ba, yanzu zaki gansu sun fito tare". Subay'a ta hakura bata fita daga mota ba amma kuma bata zauna ba, in ta leka ta waccan window din sai ta dawo ta leka ta wannan, in kuma taga motsi a bakin kofar gurin sai ta fara tsalle sai taga basu bane ba. Daga baya data gaji sai ta kwanta a backseat tana kuka wai sunki fitowa.

At last sai gasu sun fito. Sadauki ne fara fitowa tare da wadansu mutum biyu wadanda Diyam ta gane a matsayin lawyers dinsa. Sai kuma Saghir ya fito tare da wani wanda ya tsaya yana ta yi masa bayanai har su Sadauki suka karaso mota. Mutanen suka yi masa sallama suka tafi sannan wancan ma yayi wa Saghir sallama ya tafi.

Diyam ta zauna tana kallon shi ta cikin motar. Yayi baki sosai, ya kuma rame sosai, amma wannan kyawun yana nan sai dai babu gayun, kuma shekaru sun fito sosai a fuskarsa harda strings of furfura a gashin sa. Ta gane kayan jikinsa, sune kayan da yake sanye dasu ranar da aka kamashi a airport, she can remember yadda ya fito daga arrivals cikin yana taku dai dai yana jin duniya duk a tafin kafarsa ga kyakykyawar Fauziyya a gefensa but yanzu da ta kalle shi bata ga komai daga cikin characters din wancan Saghir din ba. He looked calm and very different.

Sadauki ne yayi knocking a tagar da Subay'a take, ta dago tana kallonsa sai yace "Subis ga Daddy nan" ta mike da sauri ta kalli kofar prison din, tana hangoshi sai ta kama kokawa da handle din motar sai Diyam ta bude mata central lock tana dariya. Ai kuwa nan take ta bude ta fice daga motar a guje, Diyam ma ta bude ta fito tana cewa "careful Subay'a akwai titi fa". Daga tsallake Saghir ya hango fitowar ta, ya kuma lura da yadda tayo kan titi da gudu dan haka sai shima ya taho da sauri gurin ta zuciyarsa tana bugawa. A tsakiyar titi suka hadu, ya daga ta sama amma sai ya kasa juyi da ita ya sauke ta yana haki yace "kinyi girma Subay'a, Daddy kuma bashi da karfi" sai ta rungume ƙafafuwan sa tana murmushi.

Ya kamo hannunta suka karasa tsallako titin zuwa inda su Diyam suke a tsaye. Unintentionally hannun Diyam ya sauka akan cikinta tana kallon Saghir, sai taga ya kalli cikin sai kuma tayi sauri ta dauke hannun tana sunkuyar da kanta. Yayi murmushin takaici Yace "amarya" sai ta gaishe shi ya amsa yace "a sake min godiya gurin Mr Abatcha. Na goge sosai Allah ya bar zumunci" ta gyada kai a hankali tace ameen tana kallon Sadauki wanda yake ta danne danne a waya kamar baya jin me suke cewa. Sai ta kalli Saghir tace "congratulations. Allah ya kiyaye gaba" daga haka ta bude mota ta koma ciki. Sadauki ya dago kansa yana kallon Saghir ya nuna masa mota yace "Bismillah, sai mu ajiye ka a gida ko?" Sai Saghir ya kalli Diyam, ya hadiye wani daci a ransa ya girgiza kai yace "no, thank you. Kar in takura muku maybe akwai inda zaku je. Bara in hau napep kawai" Sadauki ya daga kafada kawai, sai ya tare masa napep din ya kuma biya kudi sannan ya yi wa mai adaidaitan kwatancen sabon gidan Alhaji Babba, tunda Saghir din bai sani ba.

Saghir yace da Subay'a "zaki bini gidan Alhaji?" Ga mamakin su sai ta kalli su Diyam ta kuma kallonsa sannan ta girgiza kai tace "no, Aunty Asma'u tace yau Uncle Bassam zai zo, kuma na bashi sakon abubuwan da zai taho min dasu in zai zo, ka ga kar yazo bai same ni ba" Sadauki ya bude ido yace "Subis akwai zarar magana sai kace wata babba" Saghir yayi murmushi yana kallon inda Diyam take yace "gado tayi ai". Har adaidaitan zai ja sai Subay'a tace "Daddy zan kawo maka ziyara gidan ka".

In silence suka bar gurin kowa yana lissafe lissafe a zuciyarsa. Sai can sannan Sadauki yace "ba zan bashi aiki ba kamar yadda kika bukata. Bana son drama, nafi sonsa a nesa damu" bata ce komai ba, ya cigaba "amma zanyi masa komari ya samu kudin sa na gurin Kabir" Diyam tayi sauri ta kalle shi tace "kudin ka dai, ai kudinka ne" ya girgiza kai yace "nayi signing takarda cewa na bar masa kudina daya dauka, so legally yanzu kudin sa ne ba nawa ba. I have already talk to my lawyers, za'a siyar da kadarorin Kabir maybe za'a samu part of kudin amma nasan ba za'a samu gaba daya ba" Diyam taji dadi sosai a ranta tana yabawa kyawun zuciyar Sadauki, kamar yadda ya taba fada mata shi fire ne da ice, duk da wadda kazo dashi za'a tarye ka.

Tayi masa godiya sosai sannan yace "kin san wani abu? Ni da Saghir are alot alike" ta bude ido dan ita bata ga hadin su ba bayan kasancewar su musulmai kuma half fulani tace "ta yaya?" Yace "kinga ni da shi duk only sons ne a gurin iyayen mu. Kuma iyayen mu suna son mu sosai sannan sun nuna mana soyayya in their own different ways. Duk kanin mu iyayen mu sun bamu kudi, the only difference is yadda muka yi da kudin da suka bamu. Sannan kuma duk muna sonki" ya fada yana kallon ta, tayi saurin girgiza kanta tace "he doesn't" yace "he does. I saw it in his eyes yanzu da yana kallon ki"

Tayi saurin kawar da maganar ta hanyar cewa "kuma duk ku biyun kuna da kanwa mai suna Murja" yayi dariya yace "ni kanwa ta Murjanatu sunan ta ba Murja ba, kuma ni nafi shi son kanwa ta" tace "ita kuma duk duniya gani take yi kafi kowa kinta" and they laughed together.

*************************

Saghir ya juyo yana kallon Subay'a, yana kallo Sadauki ya kama hannunta ya bude mata kofa ta shiga mota sannan shi kuma ya zagaya ya zauna kusa da pregnant Diyam. Yayi sauri ya rintse idonsa tare da dafe kansa yana jin hawaye yana zuwa idonsa. Bai dauka har yanzu Diyam tana da gurbi a zuciyarsa irin haka ba, ya dauka ba zaiji komai ba inya ganta musamman saboda kokarin da mr Abatcha yayi masa, amma ita zuciya bata da linzami dole ya ja baya dasu ya daina ganinsu, ko kuma abinda yaji din yana da alaka da yadda Diyam din ta zama? Irin kyawu da cikar halittar da tayi? Wai hakan na nufin da ace ya kula da ita tsahon shekarun da suka yi a tare da irin haka zata zama kuma maybe da zata so shi? Lallai gaskiyar hausawa da suka ce tun ranar gini tun ranar zane, shi kuwa nasan ginin ya bushe dole sai dai ya hakura da zanen ko kuma ta sake sabon gini, sabon ginin

Please Login or Register in order to submit comment