Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuka "dan Allah kuyi hakuri kar ku dake ni, dan Allah" Kawu Isa yace "ba zamu dake ki ba indai kika gaya mana gaskiya. Ina kika je ranar nan?" na cigaba da kuka na "wallahi Kawu na daina bazan sake fita ba". Na dago kai muka hada ido da Inna ta rafka tahumi tana kallona, nayi sauri na sunkuyar da kaina, tace "ba zata fadi inda taje ba fa, amma ni nasan inda taje, ba zai wuce gurin wannan bakin mayen ba" ta juya tana kallon Alhaji Babba tace "rannan ba kace in ya sake zuwa gidan nan sai ka kama shi ba? To shine ita ta tafi gurinsa tunda shi an hana shi zuwa. Wato dalilin da yasa kika nace sai na saka ku islamiyya kenan ko?" Na girgiza kaina da sauri "wallahi Inna ba haka bane ba, ranar nan ne kawai naje kuma bazan sake zuwa ba" Kawu Isa yace "to me kika je yi ranar? Me ya kaiki gurinsa?" Ina sheshsheka ina kuma wasa da fingers dina nace "ce masa nayi kar ya kuma zuwa gidan nan" Alhaji yace "au saboda nace zan saka a kama shi shine kika je kika gaya masa ko? To in nayi niyyar rufe sadauki kaf garin nan akwai wanda ya isa ya hana ni ne? Yanzun ma kuma zan tura har gidan da yake takama dasu din insa akama shi a dan lallasa min shi yadda nan gaba ko kince masa zaki je shi da kansa zai hana ki" Kawu Isa yace "tashi ki tafi" nayi sauri na mike nayi hanyar waje sai Alhaji Babba ya ce "kar ki fita daga gidan nan. Kin gama zuwa islamiyya ai. Zo ki wuce ciki" na juya na bi inda yake nuna min, muka hada ido da Hajiya Babba wadda tun da aka fara maganar bata ce komai ba tana dai bina da kallo kawai.

Kitchen din gidan na shiga, na rakube a jikin kofa na cusa kaina a tsakanin cinyoyi na, me yasa ni bani da sa'a ne? Me yasa duk sanda nayi wani abu sai an kama ni? Karya sam bata karbe ni ba? Sai kuma na kama addu'ar Allah yasa Sadauki ya tafi dan kar Alhaji Babba ya aikata abinda yace.

A palo bayan na tashi inna tace "na rasa yadda zanyi in raba yarinyar nan da wannan nataccen yaron wallahi. Nayi nayi, Allah ma ta gani nayi iya kokarina amma abin ya faskara, ni farko na dauka soyayyar yarinta suke yi, na dauka in suka fara hankali zasu saki hannun juna amma kamar kara tunzura su ake yi" Alhaji Babba yace "wai soyayya suke yi?. Diyam din yanzu harta isa yin saurayi? Shekarar ta nawa?" Inna tace "sha hudu zata yi nan da wata daya" ya gyada kai yace "ta isa kam. Matanen mu na ruga basu kaita ba ma ake musu aure. Kuma wannan tunda har tasan a raba ta da saurayi ita kuma ta dauki hanya ta bishi to lallai ita ma ta isa auren" inna tayi ƙoƙarin kare ni "ya shanye tane fa, babu maganar wanda Diyam takeji sai tasa" Alhaji Babba yace "anyi daya ai, ba za'a sake biyu ba, mu ba zamu kuma hada jinin mu da mayu ba, yadda bakin cikin Manu ya kashe Inno ba zamu bar bakin cikin Diyam ya kashe Hardo ba dan haka kija mata kunne. Babu ita babu shi, in taki kuma duk abinda ya biyo baya ita ta jawo wa kanta".

Shikenan kamar magana ta wuce, zuwa washegari na shiga harkokina sosai kamar babu abinda ya faru amma cikin raina kuma cikin sallolina ina yiwa Sadauki addu'ar samun nasara, sai inke tambayar kaina ko ya samu mahaifin nasa? Ko wacce irin karba a samu daga danginsa? Hankalina rabi yana tare dani rabi kuma yana gurin Sadauki har ya kwana uku da tafiya. A ranar da daddare aka aiko Alhaji Babba yana kiran Inna, ta dauki hijab dinta ta fita shiru shiru har na gaji da jiranta mukayi shirin bacci ni da Asma'u muka kwanta, amma sai na kasa baccin kuma nayi ta juyi ina jin wata irin muguwar faduwar gaba. Na rasa me yake yi min dadi kawai na tashi na zauna na rafka tagumi sannan sai gata ta shigo, sai kawai naga idonta kamar wadda tayi kuka amma sai ta maze tace "ke kuma me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba?" Nace "bana jin dadi ne kawai Inna. Baffa nake tunowa" sai kuma na fara matsar kwalla, ta dauke kai tace in an tuno mamaci addu'a akeyi masa ba kuka ba" sai ta wuce can karshen gado ta zauna ta jingina kanta da jikin gadon, naso in tambayeta in wani abun yana damunta amma nasan ba lallai ta bani amsa ba dan haka sai nayi shiru na koma na kwanta ina kalllon ceiling, mun jima a haka sannan tace min "Diyam Baffanku ya mutu ya huta, mu da muke duniyar mu mune cikin wahalarta" na runtse idona ina tunanin ma'anar maganar ta ta.

Washegari bayan na tashi da assuba nayi sallah sai na koma baccin safe, cikin bacci na kawai naji muryar mama a dakin na farka ina mamakin me take yi a gidan da sassafe? Sai naji Inna tana cewa "ni wallahi Hafsa kinfi kowa sani, bana son yaron nan sam zuciya ta bata sonsa ballantana har inyi sha'awar ya zama surukina amma duk da haka saghir fa...." Sai kuma suka ga ina kokarin mikewa sukayi shiru. Na tashi na gaishe da Mama, sai naga fuskar Inna still akwai bacin rai idonta kamar batayi bacci sosai ba, sai kawai naji ina son inji maganar da suke yi. Sai na bude toilet na shiga na rufe na kunna pampo kamar zanyi wani abu amma sai na dawo na sakakunne na a jikin keyhole.

Sai naji Mama tana cewa "wannan gajeriyar matar tasa ce zata kissima masa, shi kuma ya hau ya zauna saboda son kansa, amma suma kansu sunsan ai Diyam ba sa'ar auren Saghir ba ce ba, ya ninka ta a shekaru fa, gashi da budadden ido ita kuma fa? Yarinyar da junior waec kawai ta rubuta? Akwai cutuwa sosai a hadin su" Inna tace "babu fa abinda ban gaya masa ba jiyan, sai yaji haushina ma wai ina so in nuna ni na haifi Diyam basu ba, wai ita suke wa gata, wai baza ta taba samun miji irinsa ba, wai gata suke yi mata albarkacin zumunci albarkacin maraicinta" ta danyi tsaki tace "ni da ace Diyam ta fi haka girma ne, da ace misali ta gama makaranta ne wallahi da bani da dumuwa. Ni yanzu abinda nake so kice masa idan kinje shine, ki roke shi a bar yaran su daidaita kafin ta gama makaranta".

Na sulale ma zauna a kasa a jikin kofar. Naji dai suna maganar aure, kuma naji sun ambaci sunana sun kuma ambaci sunan Saghir. To tambaya ta anan itace auren wa za'ayi? Aurena za'ayi ko auren saghir za'ayi? Dan kaina ba zai iya daukan aurena da saghir a sentence daya ba ballantana ƙwaƙwalwa ta ta fahimci cewa aure za'a hada ni da saghir. Na wanke fuskata nayi brush na fito ina murmushin yake, suma duk yaken sukayi min har na zauna na fara breakfast sai na lura duk sun zuba min ido suna kallona. Sai na samu kaina da tattauna abincin amma makogwarona yakasa budewa ballantana in iya hadiyewa.

Muna nan zaune babu mai magana sai ga aike aba kiran Mama inji Alhaji Babba, ta tashi ta tafi muka cigaba da zama ni da Inna sai ga wani aiken wai inna taje itama, tana tafiya na rufe abincin gabana na tashi na kwanta a kan gado trying hard not to think, trying hard not to let my brain assess maganar da naji su Inna suna yi. Ba zan iya tuna adadin mintina ko awannin da suka wuce ba sai ga yarinya an aiko wai inzo inji ana kira na a palon Alhaji, na tashi na saka hijab dina still trying not yo think na fara tafiya blindly zuwa part din Alhaji Babba.

Na murda kofar na shiga da sallama. Duk suka dago kai suna kallona kamar yadda nima nake bin su da kallo. Alhaji Babba, Hajiya Babba, Inna, Kawu Isa da kuma Mama. Na durkusa na gaishe su da muryar da a kunnena naji kamar ba tawa ba. Suka amsa sannan duk suka zuba min ido suna kallona. Alhaji Babba ne yayi magana "Diyam a matsayin mu na iyayenki wadanda baki da wadanda suka fimu kaf duniyar nan mun yanke shawara a kanki. Zamu hada auren zumunci tsakanin ki da yayanki Saghir".

"Dama an jima da bani shawarar cewa babban abinda zai saka Saghir ya zauna a guri daya ya nutsu shine in na samu kyakykyawar yarinya na aura masa, tun a lokacin Diyam ce ta fado min a raina na kuma kuduri aniyar hada su aure in ta isa auren, to kuma yanzu ganin har ta fara iya bin saurayi zuwa gidansu na fahimci ta isa auren a yanzu, dan haka za'ayi yanzu. Diyam zaki cigaba da karatu kamar yadda mahaifiyar ki ta bukata, amma ba zaki koma makarantar kwana ba, za'a saka ki a day ki karasa secondary, in kin gama in mijinki ya yarda sai ki cigaba in bai yarda ba kuma shikenan. Bamu saka rana ba tukunna, na kira shi Saghir din nace masa lallai ya hawo jirgi yazo ya gobe ina nemansa, in yazo sai muji tsare tsarensa sai mu samu saka lokacin. Shikenan abinda zan ce miki Diyam, tashi ki tafi".

Na tashi kamar yadda yace, amma sai kafafuwana suka lankwashe na fadi a gurin, Inna da Mama suka yo kaina a tare amma kafin su karaso na sake mikewa na kama hanyar na fice. Bansan ya akayi nazo ba kawai sai gani na nayi a dakin inna, na durkusa a gaban gado gabaki dayan jikina yana karkarwa kamar ana kada mazari amma idona babu hawaye, lallai wani tashin hankalin yaji gaban kuka. Baffa naji ya fado min arai, na tuna maganar sa sanda yake mana fada ni da sadauki "waye kuke tunanin zaiyi muku aure yanzu? Ba dai ni babanku ba" ashe haka maraici yake? Ashe haka rashin gata yake?

A gefe na naga handbag din Mama, na dauka da sauri na bincike da dauko wayarta, babu tsoro ko kadan a raina nayi dialing number din da Sadauki ya bani.

Ring biyu ya dauka, muryarsa as clear as yana gabana a tsaye wannan yasa na samu relief na san at least lafiyar sa kalau. Yayi sallama amma ni sai na kasa magana saboda karkarwar da baki na yake yi, sai kuma kuka ya kwace min. Na fara rera wa ba kakkautawa nan take ya rikice "Diyam?? Ya Salam Diyam kiyi min magana menene? Me ya faru Diyam? Please talk to me" shima kamar zaiyi kukan, na tsagaita nace "Sadauki ka taimaka min, Sadauki aure za'ayi min wai" yayi shiru kamar baiji ba sannan yace "what?!!!" Nace "yanzu suka kira ni suka gaya min, aure zasu yi min Sadauki, wai hamma Saghir zasu aura min" yace da sauri "su? Su waye su? Diyam kar kiyi min wannan wasan bana so" na lissafa masa duk wadanda suke gurin sanda akayi maganar nace "da gaske suke Sadauki, wallahi da gaske suke, Sadauki mutuwa zanyi ka taimaka min". Yace cikin muryar da ban taba jin yayi magana da irinta ba "Diyam listen to me, zan ajiye duk abinda nake yi zan taho kano gobe and I promise you I will not let anything bad happens to you".

Kofa ta bude inna da Mama suka shigo fuskarsu babu yabo babu fallasa, sai kuma suka tsaya suna kallona da waya a hannu ina kuka. Na sauke wayar daga kunne na ina ji a raina bana jin wani tsoro kuma, wanne punishment za'a yi min wanda yafi wannan da aka riga akayi min?
[1/25, 11:53 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Twenty Six : Forever and Ever

Alherin Allah ya kai gun masoya na a duk inda kuke. Ina gani, ina karantawa kuma ina godiya da duk comments dinku, it kept me going.

This page is dedicated to duk wadda za'ayiwa ko kuma aka taba yiwa auren dole.
This page is dedicated to duk saurayin da aka raba shi da budurwarsa ba tare da wani cikakken dalili ba.
This page is dedicated to duk iyayen da suke da ra'ayin yiwa yayansu auren dole. Ina fatan wannan labarin zai saka ku chanza ra'ayin ku.
Ku fahimce ni sosai, auren dole nake nufi bawai auren haɗi ba, akwai banbanci tsakanin arranged marriage da kuma forced marriage.
Mama ta shigo ta karbi wayar daga hannuna tayi cutting kiran. Bata ce min komai ba ta saka wayar a jakarta ta harhada sauran kayanta ta rataya jakarta. Inna tace "ba dai tafiya zaki yi ba" Mama tace "tafiya zanyi, ni ba zan iya kallon wannan kayan takaicin ba, Allah ya bamu alkhairi". Ta juya da sauri ta bar dakin. Inna tayi ajjiyar zuciya dan ta fahimci Mama fushi tayi akan magana ta, tazo ta zauna a bakin gado daga gefena tace "shi kika kira ko? Diyam taurin kanki ne yake jawo miki koma menene akeyi miki. Ke ba kya jin magana ta, da ace tun farko da na hanaki kulashi kin daina ai da bata kai ga haka ba" tayi shiru tana sauraron kuka na, sannan tayi tsaki tace "nima zuciyata ba son hadin nan naki da saghir tace ba kawai dai dan babu yadda zanyi ne, ba wai saghir din ne bana so ba a'a auren ki ne yanzu bana so, duk da dai kamar yadda Alhaji ya fada ana yiwa wadanda basu kaiki bana aure kuma su zauna amma nasan da babanki yana nan da bazai miki aure yanzu ba. To ni wannan shine damuwata. Amma in kika duba ta wani bangaren fa zaki ga gata akayi miki, Saghir yafi wancan yaron da kike ta naci komai, yafishi kudi ya fishi kyau ya fishi asali ya fishi shekaru ya fishi hankali ya fishi wayewa sannan uwa uba gashi dan uwanki. To me kike nema kuma bayan duk wannan" a hankali cikin dasashshiyar murya nace mata "bana son shi Inna. Bana son Saghir Sadauki nake so, bana son aure yanzu karatu nake so. Inna ki taimaka min kar kuyi min auren dole" sai na dora kaina akan cinyarta na cigaba da rera kuka, ta dora hannunta a kaina tana shafawa, a hankali tace "gata akeyi miki Diyam, yanzu ba zaki gane ba sai nan gaba".

Kafin azahar zazzaɓi mai zafi ya rufe ni, ko palo ban kuma lekawa ba ina kwance daki a kudundune ina karkarwa. Ina jin yan gidan suna ta zuwa dubani kuma nasan da yawa daga cikinsu tsegumi ne yake kawo su. Ina jin Hajiya Yalwati ta shigo itama suna ta magana da Inna "amma dai Amina in kika yarda da wannan hadin kun zalinci yarinyar nan wallahi. Saghir in ana so ya shiryu ai gagarumar mace wadda taga jiya taga yau za'a samo a hada shi da ita ba yar mitsitsiyar Diyam din nan ba, ya zata yi dashi?" Inna tace "to wai Yalwati ya kuke so inyi ne da raina ne? Nima fa ba son abin nan nake yi ba amma ya zanyi? Yanzu zan iya cewa da Alhaji Babba ba zai aurawa Diyam Saghir ba? Duk duniya tana da wadanda suka fisu ne ko kuma ni duk duniya ina da wadanda suka fisu ne? Hakuri kawai zatayi nima kuma inyi hakurin sai mu hadu muyi tayi musu addu'a. Duk wannan koke koken nata daga anyi auren fa shikenan. Yara nawa ne akayi musu auren irin haka kuma gasu nan har sun hayayyafa sunyi zaman su" Hajiya Yalwati tace "to ba dole suyi zamansu ba tunda sun hayayyafa? Amma kije ki tambayesu kiji idan har yau abin baya musu ciwo a ransu. Kije ki tambayesu kiji irin wahalar da suka sha kafin su hakura din. To wannan fa wai ina yi miki magana ne akan in mace bata son miji aka aura mata shi to ina ga in shi din ma baya sonta? Kar ki manta Saghir fa bashi yace yana son Diyam ba. Kinsan kuwa ciwon auren wanda baya sonka? Kinsan kuwa irin bakin cikin da zai ta kunsa maka?"

Inna ta dauke kanta gefe tana jin kamar bakar magana ce Hajiya Yalwati take gaya mata. Ita kuwa ita tasan bakin cikin auren wanda baya sonka don har yau tana iya tuno farkon aurenta da Baffa ko kallo bata ishe shi ba, sai gabanta ya fadi data tuno Saghir, idan har Baffa daya tashi ya kuma yi karatu a kauye yayi mata wulakanci saboda baya sonta to ina kuma ga Saghir din da ya gama bude idonsa a kasashen turawa?

Da yamma Aunty Fatima autar su Baffa tazo, ita ta tashe ni zaune tana taba jikina tace "Amina anya kuwa wannan yarinyar ba za'a kaita asibiti ba, jikin ta yayi zafi da yawa fa?" Hmmm shine kawai abinda inna tace tana jan charbi, Aunty Fatima ta bani magani na sha na koma na kwanta tana cewa "wallahi baki ji irin dadin da naji ba dazu da Alhaji Babba ya kira ni take gaya min wannan labarin, kai amma Allah ya sanya alkhairi shi kenan munyi abinmu tuwo na maina. Dama tunda Hamma Manu ya rasu yaran nan Diyam da Asma'u suke raina ina ta tunanin su kinga yanzu shikenan, in akayi auren dai ta dauki kanwarta suje can suyi zamansu kema kin huta, duk inda zai tafi yawon nasa ba sai ya saka matarsa a gaba su tafi tare ba? Itama ma a hakan zata waye din ai" a raina nace kaji wata kuma, ita wayewa ce damuwarta.

Washegari da safe jikina ya danyi sauki sai wani matsanancin ciwon kai da nake ji. Inna ta saka na tashi da kyar ina shan kunun gyadar da Hajiya Babba ta aiko min dashi wai taji ance naki cin abinci. Ina cikin sha aka budo kofar dakin kamar za'a balla ta, duk muka tsorata muka daga kai sai idona ya sauka akan Hamma Saghir da yake haki kamar wanda yayi tseren gudu, Inna tana yake tace "a'a Saghir saukar yaushe?" Ya dauke idonshi daga kanta ba tare daya amsa mata ba ya kalle ni cikin ido yace "dan ubanki, tun wuri kije ki gaya musu cewa ba kya sona tun kafin a makala min ke ki zokina nadama" ban dauke idona daga kansa ba har ya juya ya fice ya bar mana kofa a bude, na sauke kaina kasa na ajiye kunun hannuna, ina jin Inna ta tashi da sauri ta fita tana salati. A hankali naji wata irin tsana, tsanar da ban taba tunanin it is possible ba tana shiga zuciyata a game da Saghir, abinda ya fada bashi yafi bata min raiba akan ambaton ubana da yayi.

Na jawo pillow na kwanta sama sama ina jiyo hayaniya a palo, naji Inna tana tsara musu abinda Saghir yace, muryarta har kakkaryewa takeyi kamar zata yi kuka, sai kuma naji Alhaji Babba yana magana shima amma bana fahimtar me yake cewa sai can naji yace "kai ka haife mu ko mu muka haife ka? To sai an aura maka ita din in yaso in an kaita gidan naka ka kasheta kakawo mana gawarta".

Na runtse idona na jawo wani pillown na dora a kaina na toshe kunnuwana.

Da yamma Mama ta sake dawowa gidan. Inna ta tsara mata abinda dazu ya faru da Saghir. Mama tace "to dama ni abinda ya kawo ni shine in gaya miki in anjima Sadauki zai zo, ya sake kiran layi na yace min zasu zo shida dan uwan mahaifinsa da kuma Alhaji Bukar na garin nan. Abinda nake so ince miki shine dan Allah idan sunzo kema ki fito ki nuna cewa ba kya son hadin Diyam da Saghir, ki karbi Sadauki sau daya dai a rayuwarki ko dan yarki" Inna ta fara girgiza kai "na gaya miki Hafsa, kin sani kuma bana son yaron nan bana kaunarsa" Mama ta fara daukan zafi "Yanzu kinfi son ki hada Diyam da mutumin daya kalli cikin idonki ya gaya miki baya kaunar yarki akan wanda yake binki kamar zai lashi takalmin ki saboda ki bashi yarki? Wacce irin zuciya ce dake Adda?" Amma inna sai ta cigaba da girgiza kanta kawai.

Ni kuma jin maganar Mama sai naji hankalina gaba-daya ya koma kan Sadauki. Sadauki zaizo da gaske? Kuma tare da dan uwan babansa? Kenan ya ga babansa da gaske. Amma kuma har zuciya ta ina tsoron yadda zata kasance tsakanin su da Alhaji Babba.

Muna nan zaune kuwa sai ga kira a wayar Mama, ta amsa sai ta tashi tana saka hijab dinta tace "sun zo, bara inje" amma inna bata motsa ba, ni dai ina zaune ina jin jira, irin jiran da akuya take yi lokacin da aka kaita mayanka. Har wani daci daci nake ji a bakina.

Abinda ya faru a waje kuma shine; Mama ce da kanta ta shigo da Sadauki tare da wani mutum da zuka zo tare daga Maiduguri. Babban mutum ne sosai kuma kana ganinsa kaga babarbare harda tsagun su a fuskarsa. Sai kuma Alhaji Bukar wanda shine asalin wanda ya aurar da Zainabu. Suka shigo tayi musu iso har palon Alhaji Babba ba tare dashi Alhaji Babban yasan ko su waye ba ballantana abinda yake tafe dasu. Sai da yaga Sadauki sannan balli ya fara tashi yace a fitar masa dashi daga gidan sa. Mama ta roka dan Allah a tsaya a saurare su tunda dai suka taho kafa da kafa tun daga Maiduguri ai sun chanchanci a saurare su. Mutumin da hausa bata ishe shi sosai ba sai yana hadawa da turanci ya fara bayanin cewa mahaifin Sadauki ne ya turo shi yayi representing dinsa saboda shi baya kusa, gurin nemawa Sadauki auren Diyam kamar yadda shi Sadaukin ya nema. Nan take Alhaji Babba ya basu short ansa da cewa "ba za'a bashi dinba, kuma Diyam mun riga munyi mata miji. Na gama baku amsa ku tashi ku bar min gidana tun kafin in kira muku yan sanda" Alhaji Bukar yace "shikenan dai? Shikenan maganar 'yan sanda dai?" Alhaji Babba yace "ai gida na kuka shigo, dan haka duk abinda nace kunyi min ya zauna kenan" Alhaji Bukar yace "ai kai abinda baka sani ba shine, in kai baka rufe mu ba mu sai mu tufe ka kuma muga wanda zai tsaya maka ya fito da kai" Alhaji Babba yace "anji din, aure dai ba za'a bayar ba in kaji haushi kamar yadda kayiwa zainabu aure dan munki yarda Manu ya aureta to shima Sadauki ka daura masa aure gobe mu gani" Alhaji Bukar yace "tabbas nayi wa zainabu aure, aure kuma wanda manu baiyi irinsa ba, amma kuma da amincewar ta ba wai tilasta mata nayi ba kamar yadda kake da niyyar tilastawa marainiyar Allah ta auri lalataccen danka. Wallahi indai kayi mata wannan auren sai Allah ya kamaka da hakkinta tun a duniya ba sai kunje lahira ba". Ya mike tare da dayan mutumin daya ke ta mamaki yana tambayarsa dama haka mutanen suke? Anan kuma Aliyu ya girma?

Amma Sadauki sai yaki tashi daga inda yake a durkushe. Sai ya rarrafa gaban Alhaji Babba yace "Alhaji dan Allah, nasan nine ba kwaso na yarda kuma ba zaku aura min Diyam ba amma dan Allah, dan Allah Alhaji kar kuyi mata aure, in dai saboda nine to na hakura na janye neman aurenta please ku barta tayi karatunta, ku barta ta girma ta zabi wani da kanta" Alhaji Babba ya dauke kansa, Sadauki ya sake cewa "in kuma lallai sai kunyi mata aure please not Saghir, ga Mukhtar nan" ya fada yana nuna Mama, "ku aura mata Mukhtar indai har sai kunyi mata auren yanzu but please banda Saghir".

Alhaji Babba ya mike "kai a matsayin ka na waye zaka gaya mana wanda zamu aura mata da wanda ba zamu aura mata ba? To albishirin ka, Saghir din zamu aura mata kuma rana ita yau za'a daura auren idan kaji haushi kaje ka fada rijiya ka mutu".

Ina daki a kwance, na bude idona a hankali ina kallon dakin na lura Inna bata nan. Sai na tashi zaune haka kawai naji ina son in fita waje. Na

Please Login or Register in order to submit comment