Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fa abinda za'a ci a gidan nan" sai ya saka hannu a aljihu ya zaro min yadin aljihun na karkade min ya cigaba da danna wayarsa. Sai na samu kaina da tambayar kaina menene role din Saghir a auren mu? Shi aikinsa kawai shine yayi min ciki? Na shigo ciki na zauna a kan bedside nace "Saghir idan ni da kai da uwani mun zauna da yunwa wannan" na nuna cikina, "bai san babu ba" ya kalli cikin nawa sai ya ajiye wayar yace "to wai me kike so inyi? Ni fa ko kudin man da zan zuba a mota in fita bani dashi, ko so kike a ganni a daidaita sahu ake nuna ni a gari? Ko kuma so kike in ke bin gidajen masu kudi ina cewa allazi wahidi? Ko kuma dako kike so in dauka ko lebura ko kuma aikin mechanic? Na fahimci abinda yasa ya fadi mechanic din, so yaje muyi fada inyi zuciya in rabu dashi amma sai nace "eh, so nake kayi duk abinda ka fada indai zaka samu halak dinka. Wai kai ba kayi karatu bane ba? Ina takardun ka, ka karkade su ka fita kane gurin abokan Alhaji su hada ka da connections din da zama samu aiki. At least if you can't be a good husband try to be a good father".

Bansan ya akayi ba kuma ina daki sai gashi da folder din takardu yace zai je gida ya kaiwa Alhaji, sai kuma yace "in na samo kudi a hannun Hajiya sai in taho mana da wani abun a hanya". Ni dai na rabu dashi a raina ina cewa lallai gata mugun abu. Na tuno Sadauki da rashin zamansa a guri daya, tun yana dan karamin sa Baffa ya nuna masa neman kudi. Sai nayi murmushi ina lissafin irin kudin da Sadauki zai tara in dai ya samu hanya.

Ban kuma tabbatar wa cewa Alhaji Babba ya fada kwata ba sai da muka je gidan few days after that. Mota daya ce a compound din, ita ma kuma daga ganin ta nasan an dade ba'a hau ta ba, komai babu, ni sai naga gidan kamar har wani duhu yayi. Shi kansa ya rame, kayan jikinsa sun tsufa, na gaishe shi ya amsa yana ta yake baki. Muka shiga cikin gida suna ta kallon cikina, Hajiya Babba har da yar min da magana wai da Inna ta hanani komawa bayan ni ina son mijina, ni dai bance mata komai ba. Itama naga dakinta yar aiki daya ce kawai kuma itama na tabbatar yan uwanta ne suka dauko mata. Hajiya Yalwati kam Allah ya taimake ta ƴaƴanta manya su uku sunyi nce sun fara teaching dan haka su suke daukan nauyinta da kannen su. Da zamu tafi su murja suka ce zasu bi mu amma Saghir ya rufe idonsa yace babu wadda zai dauka. Sai da muka dauki hanya ne yake cewa wai nauyi zasu dora masa in suka zo. Sai na tambayi kaina 'ba shine namiji ba, babban wa uba? Bashi ya kamata ya dauki nauyin kannensa ba amma shine mai gudun ciyar dasu na kwana biyu?"

Bayan munje gida yake gaya min "Alhaji ya hada ni da wani abokin sa shi kuma ya hada ni da wani mutum daya bude kamfanin siyar da motoci kwanan nan. Gobe zanje interview kiyi mana addu'a. Idan aikin nan ya fada ko? Hmmmm, ba karamin kudi suke dashi ba a gurin nan kuma kinsan accounting na karanta harkar kudin" ni dai nayi addu'a amma bansa ka rai ba saboda bansa ran zai samu aiki irin haka da wuri ba.

And to me surprise, sai gashi washegari da offer. "I nailed it. Diyam, I got it. Wato managern ne da kansa ya ganni, karamin yaro ne mai babbar harka. Kawai few personal questions yayi min shikenan yace 'you are hired' just like that fa, Diyam you are talking to the financial secretary of Abatcha Motors"
[2/8, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Thirty Eight : Subay'a

Na rike baki ina dariya, ko ba dan Saghir ba ko dan ni kaina da abinda yake cikina nayi murnar wannan aikin. Nace "Masha Allah. Alhamdulillah. Amma fa kayi sa'a, abinda mutane sai su dade suna neman aiki basu samu ba amma kai kaga lokaci daya ka samu" yayi dariya yana zama akan kujera yace "maybe mutanen da kike magana akan su basu san inda ya kamata su nemi aikin ba ko kuma basu dace da aikin ba. Kinsan appearance matters alot a gurin neman aiki, yanzu misali ni, kowa ya ganni yasan na chanchanta da post din dana samu" na zauna ina mamakin bragging irin na Saghir, nace "komai fa a rayuwa yana da lokaci, wadanda basu samu aiki ba lokacin samun su ne baiyi ba, kai kuma daka samu lokacin kane yayi, ita rayuwa....." Ya daga min hannu "don't spoil my mood please. Je ki kawo min ruwa" nayi ajjiyar zuciya na tashi.

Ranar daya fara zuwa office ne bayan ya dawo na tambaye shi "to an baka office? Da fatan sun fara baka aiki kanayi" yace "wanne irin aiki kuma?" Nace "rubuce rubuce mana, ba shine aikin secretaries ba?" Yayi tsaki yace "fin sec fa aka ce miki, ni harkar shiga da fitar kudi a companyn ne kawai part dina, besides, ina da mataimaki so shi zaike handling duk aiyuka" nace "so? Kai menene naka aikin?" Yace "who cares about aiki ne wai, what I care about is the salary kuma zasu ke bani mai kyau shikenan".

Tunda aiki ya samu kuma shikenan Saghir ya koma tsohuwar rayuwar sa, inya fita tun sassafe baya dawowa gida wani lokacin ma har sai nayi bacci. Baya zuwa gida a bige, amma hakan bawai yana nufin ya daina bane ba dan sau da yawa in ina gyaran kayansa nakan ji wannan warin a jiki, sai dai bani da wani kwakwkwaran hujja. Yana ciyar damu, duk da dai considering yadda yake kashewa jikinsa kudi baya yi mana yadda ya kamata amma dai muna cin abinci. Shi kuwa kullum cikin sababbin dinkuna yake yakance "gwara mutum yayi dressing sosai kar a raina masa hankali".

Cikina yana ta girma abinsa, ni kuwa babu komai a raina sai fargaba dan kuwa har yau ban manta da wahalar da nasha a waccan haihuwar ba, gashi wannan cikin duk da cewa daya ne a ciki amma tafi wancan cikin girma, wannan yasa tun cikin yana waya bakwai na tattaro kayana na dawo kasa kusa da uwani kuma kullum ways ta tana kusa dani dan am not looking forward to haihuwa ni kadai irin waccan.

Amma lokacin da muka je scanning tare da Saghir, bayan an gama mun zauna sai doctor yace "am afraid ba zaki haihu da kanki ba, dole za'a yi miki cs ne" duk muka bude baki da mamaki, Saghir yace "ta taba haihuwa fa doctor, twins ma" doctor ya dauko takardar scan din yace "tana da abinda a likitance muke kira da placenta previa. A ka'ida in aka tashi haihuwa ɗa ne a farko sai an haife shi sannan sai mabiyya ta biyo baya. But in her case mabiyyar ce a farko sannan dan, meaning ko da ace ta fara labour to placenta ce zata yi blocking babyn yadda ba zai fito ba so babu yadda za'ayi sai dai ayi delivering through cs" na fara kuka, ni takaicina shine yanzu wai yanka cikina za'ayi a fito da babyn ni Diyam, kai mata munga ta kan mu. Saghir yayi tsaki yace "kuma menene abin kuka a ciki? Ke da ya kamata kiyi murna ma babu ke babu wahalar haihuwa. Sai ni aka bari da wahalar kudi".

Alayi fixing date, a week to my edd sai dai da sharadin in naji nakuda kafin lokacin muyi sauri mu tafi. Na dage kullum da addu'a, na kuma gayawa su inna suma suka tayani da addu'a har Allah ya nuna mana lokacin. Mama ce tazo gidan muka tafi tare, dama Inna tunda nayi aure bata taba zuwa gida na ba. Tun a day to aikin mukaje suka bamu gado muka kwana a can, sukayi duk gwaje gwajen da zasuyi sannan washegari sai ga Hajiya Yalwati tazo daga gidan Alhaji Babba, har aka zo aka gama shirya ni babu Saghir babu labarin sa. Naji duk jikina yayi sanyi. Anzo ance lokaci yayi na dauko waya ta and I found myself dialing number din Sadauki, hoping to hear his voice just once more amma naji a kashe na kashe wayar na ajiye feeling so lonely kanar ni kadai ce a duniyar. Mama da Hajiya Yalwati suna ta lallashina suna min addu'a a haka aka shiga dani.

Aikin mai bacci akayi min saboda jini na yaki karbar na ido biyun. Dan haka duk abinda akayi ban sani ba har aka gama aka fito dani dakin hutawa. Anan ne na dan farka kadan naga Inna a zaune kusa dani ta rike hannuna, gefe kuma Mama da baby a hannun ta "Sadauki" na fada cikin bacci, "inna ki kira Sadauki kice yazo ya duba ni" sai na kuma komawa bacci. Sanda na sake farkawa doctor na gani da nurse a kaina, suka yi min sannu daga nan na sake komawa.

Sanda nayi final farkawa kuma babu kowa a dakin sai ni kadai, na bude idona ina ta kalle kalle ina jin kaina yana ciwo sai na hango Saghir a can kusa da window da alama waya yakeyi. Irin yadda naga yana bada respect ga wanda suke wayar yasa ni son sanin ko wanene saboda ban taba ganin yana magana irin haka ba. Sai daya gama sannan ya juyo, muka hada ido yayi murmushi ya nuna wayar yace "my boss. Ya kira yaji ya jikin ki saboda na fada masa za'ayi miki aiki. Yana da kirki sosai. Can you believe he paid for everything hadda karin kudin ragon suna?" Na rufe idona na dauke kai ina jin haushinsa har cikin raina, wato abinda zai fara fadamin kenan bayan an yanka ni an fito da jaririn daya saka a ciki?

Sai yazo ya dafa kafada ta "am sorry banzo ba tun jiya, I am not good at all this emotional stuff ne shi yasa nayi zamana a gida kawai" sai kuma ya juya ya tafi gurin crib din baby ya dauko yana murmushi, na yi kokarin tashi amma na kasa nace "kawo min, menene?" Yayi dariya "au baki ganta ba? Baby girl ce, so beautiful like her mother" this is the first time daya kirani beautiful. Ya karaso ya sunkuyo yana nuna min ita, and he was right, she is so beautiful but tafi kama dashi because she looked just like twins dina, just ta fisu girma sosai.

Nayi murmushi ina jin attraction so much like wanda naji akan twins. Na daga hannu na shafa kanta ina murmushi, yace "inye, Diyam an zama uwa, sai ki daina yi min rashin kunya in ba haka ba zan saka take rama min" ya jima yana ta surutun sa shi kadai sannan ya mayar da babyn cikin crib dinta ya dauko waya yayi ta daukan ta pictures sannan yazo yayi kissing dina a goshi ya fita.

Four days nayi a asibitin. I was so in love with my daughter naji tamkar na samu another reason to live. Sau daya Saghir ya dawo ya tambayi Inna ko akwai abinda muke bukata, ya dauki daughter dinsa sannan yayi min sannu ya fita, and that was all, ko abinci ba'a taba kawo mana daga gidan Alhaji Babba ba. Wannan yasa ranar da aka sallame mu muka wuce gidan Inna, shi ogan ma baisan an sallame mu ba sai daya kira ni naki dauka sannan ya kira uwani tace ai an sallame mu sai kuma gashi a gidan Inna, wai ai ba'a gaya masa zan zo gida ba, ya gama rashin kunyar sa ya fita. Inna tana ta mitar abin, a raina nace "zabin ki ne dai". Tunda Hajiya Babba taje ta dubani a asibiti bata kuma zuwa ba, shima Alhaji Babba ko leke sai yace ace min baya jin dadi ni kuwa nasan dan mace na haifa ne da namiji ne da ko da rarrafe sai yazo.

Kullum in ana kallon yarinyar nan sai na tuno Sadauki, lissafin mu ni da shi shine mu haifi girl mu saka mata Subay'a, to ga girl din kuma na samu amma bata Sadauki ba, gashi ko sunanta ban sani ba duk da nasan yayi mata huduba gaya min ne kawai baiyi ba. Sai ranar suna da safe ya kirani "anyi radin suna a gidan Alhaji. An saka mata Saratu" sunan Hajiya Babba. Na runtse idona ina jin haushin sunan, nace "Allah ya raya, zamu sami wani sunan da zamu ke gaya mata" yace "already na riga na samu, Subay'a" na maimaita cikin mamaki "Subay'a?" Yace "yes, ko ba kya so?" Nace "no, ina so, a ina ka sami sunan?" Yace "my boss called, ya nemi alfarmar duk sunan da aka sawa baby a ce mata Subay'a, and I see no harm in honouring his wish. Besides, shi ya sayi ragon suna" ya karashe maganar yana dariya. Na kashe wayar ina mamakin me yasa boss dinsa zai ce a gaya wa babyn mu Subay'a? Inna ta tambayeni suna nace mata sunan Hajiya Babba ne za'a ke ce mata Subay'a, ta maimaita sunan tana kallona.

An dan taru a gidan sunan babu laifi, duk da cewa yan'uwa ne kadai kuma yanuwana da nasa duk daya ne, sannan ni ba kawaye ba ba makota ba, sai makotan mu na nan gidan da suka shishshigo mana. Abincin suna ma Saghir baiyi ba, cewa yayi ai ba shi yace in taho gida ba dan haka wanda ya kawo ni gidan sai yayi abincin sunan. Ragon sunan ma a gidan Alhaji Babba aka yanka aka soya aka kuma raba sai namu rabon aka kawo mana a kwano. Bayan suna Mama tazo ta dauke ni muka je asibiti, ni na dauka wani check up za'ayi min sai naga an saka min wani abu mai kamar allura a dantsen hannuna ashe abin family planning ne aka saka min na shekara biyar.

Satina biyu a gida Saghir yazo yace ai na warke haka, in shirya in koma. Haka ina kuka ina komai na hada kayana dana Subay'a, Allah ma yaso Asma'u tana hutu nace tazo mu tafi, itama kuma tana shiga mota yace da iznin wa zan tafi da ita? And that kept me wondering if I don't have a say in my own marriage. Shin miji shi kadai ne mai making every decision, ita mace bata da nata ra'ayin? Ko kuma ita mace bata da zuciya ne a kirjinta?

Bayan komawar mu gida ne nayi realizing something, Saghir's weakness lies in his daughter. Yana son Subay'a sosai da sosai dan zan iya cewa yana sonta fiye da komai a duniya. Kullum tana hannunsa sai dai in baya gida ko kuma in zanyi feeding dinta. A lokacin ne kuma aka fara daukan sabon session na makaranta, a lokacin yan set din mu zasu shiga ss3. Nayi wa Saghir maganar komawa ta school sai cewa yayi "ita kuma Subay'a fa? Yaya kike so ayi da ita? Sai dai ki bari sai wani session din kafin nan tayi kwari" sai ya kara da cewa "in kuma kafin nan kin kuma samun wani cikin shikenan" ban mayar masa da magana ba saboda bai san zancen implant dina ba, haka na hakura da zancen makaranta dan babu yadda zanyi, in nace zan kai kara ma bayan sa za'a bi ace in bari yarinya ta tayi kwari.

A lokacin ne kuma yake sanar dani cewa ogansa zai tafi kasar waje karatu "he will be managing the company from there, kin san komai yanzu an mayar dashi computerized ballantana manyan harkoki irin na wadannan mutanen" nayi kamar ban ji shi ba dan ni har na gaji da maganar ogan nan, kullum oga this oga that, oga yace kaza oga yayi kaza, I wonder me suke yi a office din bayan zaman hira.

Manage this please. Ina dan busy ne kwana biyu but I promise you a sweet episode tomorrow insha Allah.
[2/9, 9:39 PM] +234 706 813 0709: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Thirty Nine : The Boss

Bayan Shekara Biyar
Shekaru biyar suka zo suka wuce. A cikin su abubuwa da dama sun faru, na farko Hardo da Uwani duk sun rasu sati daya a tsakaninsu, Hardo ne ya fara rasuwa munje Kollere zaman makoki itama uwani ta kama jinya sannan ta rasu ranar sadakar bakwai dinsa. Naji mutuwar Uwani sosai kusan fiye da yadda naji ta Hardo.

Rayuwata a gidan Saghir babu abinda ya chanza sai abinda ya kara gaba, ya dawo da shaye shayensa, ya kuma mayar da neman matansa openly wanda da yana dan boyewa amma yanzu kiri kiri yake yi musamman tunda kudade suna shigo masa, har gida mata suke zuwa neman Saghir, tun yana yi min karyar cewa abokan aikin sa ne har ya daina. Lokuta da dama kuma yana dora min laifin neman matansa, yace nice na gaza sauke masa hakkin sa shi yasa yake zuwa yake nema a waje wanda ni kaina nasan ina da laifi ta wannan bangaren, nayi nayi in tursasa zuciyata ko yayane in saka Saghir a cikinta amma taki yarda, Sadauki ya riga ya chika duk wani lungu da sako na zuciyata yadda babu wani bugawar da zata yi wanda babu tunanin sa a ciki. It was so hard living with a man while my heart belongs to another. Another din da ban ma san inda yake ba, babu amo babu labarin sa daga shi har yaya ladi. Sometimes sai in samu kaina da tambayar ko wanne hali yake ciki? Ko ya samu admission din yayi karatun? Ko rayuwa tana tafiyar masa dai dai ko kuma akasin haka?

Amma kuma hausawa sunce idan bera da sata daddawa ma da warinta. Ina da laifi a zaman mu da Saghir na sani amma shima ai da laifinsa, at least da ace yana treating dina well da ko ban so shi ba bazan ki shi ba, da zan iya managing in faranta masa as long as nima yana faranta min amma Saghir was doing total opposite of faranta min. Tsawa, hantara, bakar magana and occational duka duk ina samu daga gurin Saghir. Yana ciyar dani, barely, dan duk ranar dana ganshi da leda a hannu ko kuma naga yana yi min murmushi to nasan wani abun yake nema a gurina ni kuma a lokacin zan tayar da tawa tsiyar har sai mun rabu baran baran.

Na koma makaranta bayan na yaye Subay'a, shima da kyar Saghir ya bari har saida na hada shi ta Hardo lokacin yana da rai sannan ya saka ni a wata government school anan bayan layin mu. Na fuskanci challenges da yawa a lokacin musamman saboda kasancewa ta matar aure a makarantar yan mata, kuma duk yan class din na girme musu dan ma bani da girman jiki dan haka da wahala ma ka gane shekaru ma, babu kuma wanda yake yarda nina haifi subay'a musamman saboda tana da girma sosai ita. Har nuna ni ake yi, ni kuwa sai naja kaina gefe nayi facing karatuna kadai wannan yasa har na kammala banyi wadansu kawaye ba sai dai gaisawa kadai.

Inna tana ci gaba da kasuwancin ta, dashi suke ci, sha da sutura ita da Asma'u kuma dashi take biya wa Asma'u kudin makaranta, ta gaya min cewa tunda ta bar gidan Alhaji Babba, kaf yanuwan Baffa babu wanda ya taba daukar kwandala ya bata yace ki siyawa Asma'u ruwa, komai ita take yi musu wani lokacin ma harni take dan dinkawa kaya ta aiko min dashi tunda nawa mijin ba mai yi bane ba. Zai dai dinkawa kansa suttura kamar banza, yayi ta shiga yana fita, mayukan shafawarsa da turarukansa ma kadai abin jinjinawa ne amma ni kayan kyalliya tun na lefe na, da suka kare da wahala yake siyamin wani abu dana yi maganar kayan lefe na ma sai cewa tayi "da uban waye ya siya miki kayan?".

A lokacin da nayi candy a lokacin nake da shekara ashirin da daya, Subay'a tana da shekaru biyar. Har lokacin kuma ina nan jiya iyau, babu abinda na kara a girman jiki sai ma kara motsewa da nayi wadda rannan da Inna take mita naji Mama tace yana da dangantaka da planning din da nake yi, maybe in ya barni zan yi kibar. Sometimes Saghir ma da kansa yana complain "Diyam kina da kyau sosai a fuska, mu maza kuma ba wannan kadai muke bukata ba muna son mace mai lady body parts" yana magana yana nuna irin parts din da yake nufi, nakan bashi amsa da "ai bani na halicci kaina ba, dan haka bani zakayi wa complain ba".

Ranar nan nayi bakuwa, Maman Iman, tazo ta wunar min ita da yaranta da Asma'u na wadda ta shiga ss2 yanzu. Sai Maman Iman ta dauko wasu kulle kulle a leda ta jani bedroom dina ta fara tsaramin

"kinga wannan garin da nono zaki ke sha ko da madara, kamar bayan la'asar haka yadda kafin dare ya fara aiki. Shi kuma wannan gumba ce ki adaba kina cin kayar ki a hankali tana da amfani sosai, wannan kuma na tsuguno ne, ki barbada shi a garwashin wuta sai ki tsugunna a kai ya shiga jikin ki sosai"

Nasan magungunan menene dan kusan duk sanda naje gida sai ta bani irinsu, wani lokacin ina fitowa nake zubawa a kwatar kofar gida inyi tafiya ta. Amma sai nace "maganin menene wannan maman iman? Maganin tajika ne ko kuma na mayu" ta harare ne "a'a maganin sihiri ne. Kar ki raina min hankali mana Diyam, kinsan nawa na saka na sayi maganin nan kuwa? Wannan na tsugunnon da kyar ma na same shi shine na raba biyu na kawo miki rabi amma zaki raina min hankali" nayi dariya nace "maida wukar yayata ta kaina. Amma ki tafi da kayanki kar inyi miki asarar kudi dan wallahi ba amfani zanyi dasu ba" na fada ina dora mata akan cinyarta, ta dawo min dasu kan tawa cinyar tace "wallahi ki gwada ki gani, matar data bani ta tabbatar min da cewa indai kika yi amfani da wannan yadda kika san cingam haka mijin ki zai manne miki" nayi dariya na sake mayar mata nace "bana son ya manne min kamar cingam, ki kara akan naki sai abban iman ya kara manne miki kamar superglue" kafin ta bani amsa aka budo kofar dakin da kallo, Saghir ya tsaya yana kallon mu sannan yace "dan wulakanci kinsan ma dawo amma kika yi zaman ki ba zaki zo ki bani abinci ba" Maman Iman ta gaishe shi, yayi mata kallo daya ya dauke kai fice. Na mike nabi bayansa idona blurry with tears, yaushe wannan zubar hawayen nawa zai kare? Indai har nayi baki, ko kuma shi yayi baki, to kuwa tabbas sai ya wulakanta ni a gabansu, shi yasa har banaso inyi baki indai tana gida.

Washegari muna kasa ina taya Subay'a yin homework dinta sai gashi ya dawo daga office. Ta tashi da gudu ta tafi gurinsa shi kuma ya daga ta sama yana juyata suna dariya. Na gaishe shi ya amsa ciki ciki sannan direct ya wuce dining ya zauna ya zaunar da Subay'a a kan table din ya fara zuba abinci suna hira. Na taso na karba ina zuba masa nace "Subay'a sauka ki zauna akan kujera, na hana ki zama akan table ko?" Ta kwabe fuska tana kallonsa yace "ita da gidan ubanta, table din ubanta kuma abincin ubanta" yana fada yana yi mata chakulkuli tana babbaka dariya, garin dariyar har ta zubar da abincin dana fara zuba masa. Nayi ajjiyar zuciya na zagaye su na wuce kitchen na dauko duster nayi clearing gurin, sannan na sake zuba masa wani. Ban mayi mata fada ba dan nasan indai yana gurin to ban isa ba, maybe a karshe ya kare da zagina a gabanta. Sai daya gama sannan ya kama hannunta suka yi sama sannan suka sake saukowa tare, ya chanza kaya, yace min "zan koma office, muna ta shirye shirye oga zai dawo office ranar monday" na gyada kai nace "a dawo lafiya" a raina ina cewa "gyara ya dawo din ai ko ka mayar da hankali gurin

Please Login or Register in order to submit comment