Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana ta haɗa masa kunun aya wai taga yana so, ta dama masa fura itama ta saka a fridge ni dai ina ta kallonta. Yamma tana yi, dama nasan da yamma yake zuwa sai na saka hijab dina na tafi gurin Maman iman muka kafa hirar mu. Bana son ganinsa yanzu kuma nasan kona zauna a cikin daki in yazo sai Inna tace in fito in gaishe shi. Amma muna zaune kawai sai ga baban iman da baki sunzo, dan haka dole nayi musu sallama na fita na koma gurin Inna. Ina shiga naga takalmin namiji a kofar palo, sai na jawo farar kujera na zauna a tsakar gida amma ina zama inna ta kira ni, na bata rai kamar zanyi kuka na tashi na shiga. Yana zaune a kasa, Asma'u kusa dashi da wata takarda a hannun ta tana nuna masa wani abu suna magana a nutse. Ga kunun ayansa nan a cup a hannunsa yana sha. Na zauna a gaban Inna nace "sannu da zuwa" ya dago ya min kallo daya ya mayar da kansa yace "sannu maman Subay'a" sai ya cigaba da yiwa Asma'u bayanin wanda na fahimci kamar takardar jamb ce take kokarin cikewa. Na mike na shiga daki nayi kwanciya ta. Sai naji Inna tace masa "Diyam fa sun rabu da Saghir" naji yace "rabuwa Inna" cikin mamaki, Inna tace "rabuwa fa, ya sake ta" yayi dan shiru sannan yace "ya Salam. Subhanallah. Abu baiyi kyau ba. Allah yasa hakan shi ya fi musu alkhairi" Inna tace "ameen" Asma'u tace "ai rabuwar ma itace alkhairi hamma, wannan auren na Adda ai dashi gwara babu" Inna tace "rufe min baki sarkin magana. Waye ya tambaye ki? Tashi ki fita" ta tashi ta fita. Sadauki yace "na dauka ai ko ganin ku tazo yi" Inna tace "uhm uhm, ai satinta biyu kenan anan. Tun sanda nayi maka wayar nan ai bata koma ba dama. Nan yazo har gabana ya sake ta yasa hannu ya dauki yarsa" yace "Subay'a? Ita ta bashi ita ko kuma shine kawai ya dauke ta?" Inna tace "ina kuwa zata bashi ita? Gata nan tunda ya dauki yarinyar nan kullum sai na ganta tana kuka kuma nasan kukan yarta take yi amma ya zanyi?" Yace "a'a in dai ba ita ta bashi ita ba to zata iya karbar yarta. Ai both islamically da constitutionally bashi da right din daukar yarinyar" Inna tace "to ta yaya za'a karbo ta kenan?" Yace "ba wahala ai. Ko hisba akaje akayi reporting zasu karbo yarinyar a hannunsa su kawo mata" Inna ta jinjina kai tace "mutanen nan sunyi mana ba dai dai ba daga ni har yaran nan, amma yanuwan mune. Bana son cigaba da rigima dasu so nakeyi a samu fahimta a tsakanin mu. Amma zabin Diyam ne" sai ta saka baki ta kira ni. Na gyara hijab dina na fita, sai na ganshi a zaune yana daddanna waya kamar ba shine yanzu suke magana rai rai da Inna ba, na zauna a gabanta nace gani, tace "Sadauki yace za'a iya karbar Subay'a a hannun Saghir in aka gayawa hisba. Kina so a karbo miki ita?" Na juya na kalle shi busy with his phone, at least a matsayin da yake dashi na yayana da muka tashi tare kuma Inna ta bashi wannan labarin ai ya kamata ko magana mai dadi ce yayi min, sai na dauke kaina nace "ina son karbar Subay'a Inna, kuma zan karbo ta insha Allah amma bana bukatar taimakon sa. I can do it on my own" sai naga yayi sauri ya dago kai yana kallona. Yace "how?" Nace "ba kace hisba ba? Ai nasan hanyar hisba din kuma ina da bakin da zanyi musu bayani in naje" Na daga kafada na mike na komawa ta daki.

Daga nan babu wanda ya sake maganar karbar Subay'a ni kuma kullum yarinyar tana raina, kullum zan kwanta bacci sai nayi tunanin ko tayi bacci? In ina cin abinci sai na tunanin ko taci in na tashi da safe sai nayi tunanin ko an tashe ta an shirya ta zuwa makaranta? Kullum kuma a kowacce Sallah sai nayi mata addu'a amma kuma kamar yadda Inna ta fada bana son cigaba da rigima dasu Alhaji Babba, so nake a samu daidaito. Amma daidaiton da baiyi involving komawa ta gidan Saghir ba.

Lokaci ya cigaba da tafiya, har nayi wata biyu a gida. Duk sati ranar Monday sai Sadauki yazo gidan da yamma, in kuma ba zai samu zuwa ba to zai kira Asma'u ko Inna yace musu ba zai zo ba amma ni ko zuwa yayi gaisuwa ce kawai a tsakanin mu, sai sometimes ya kan tambayeni ko da abinda nake so to which I always reply "babu komai. Nagode".

Su Alhaji basu sake kallon inda muke ba ballantana Saghir. Ni kuma sosai na kwantar da hankali na babu abinda yake damuna sai kewar Subay'a. Har yar kiba ta nayi na kara haske.

Ranar nan na hada kayan Subay'a da muka taho dasu gidan, nima kuma ina bukatar kayan amfani dan wadanda nazo dasu sunyi min kadan ga kuma har phone dita tana gidan Saghir. Amma sam bana son zuwa gidan Saghir, duk kuwa da cewa ina son ganin Subay'a amma bana jin zan iya taka gidan dan haka sai na bawa Asma'u ta kai mata sannan na lissafa mata abubuwan da zata dauko min kafin a debo kayana. Tunda akayi sakin inna take cewa za'a debo kaya amma jin su maman iman suna shirin tashi saboda sun kammala ginin su yasa Inna tace a bari sai sun tashi tukunna saboda a samu gurin ajiye kayan.

Asma'u ta shirya taje ta dauko min duk kayan da nake bukata, amma sai tace min Subay'a bata gidan, daga alama gurin Hajiya Babba ya kaita. Sai na fara tunanin to chanza mata school yayi ko kuma dai tana gida kawai? Sai kuma tace min Fauziyya tace in na kunna waya ta zata kirani. Kuma ta bani labarin cewa "kinga gidan nan kuwa Adda? Gaba ki daya ya lalace har wani karni yake marar dadi. Kayanki kuwa in ba'a je an debo su ba to kuwa sai dai a wuce dasu bola. Na tarar da Saghir a gidan ma, yana kwance a palo ni ko kallon sa banyi ba na shiga na dauko abinda zan dauko na fito".

Da yamma nayi charging wayata da daddare kuma na kunna. Fauziyya ta kirani few minutes after na kunna. Muka gaisa tace "Halima yanzu wai da gaske ba zaki dawo ba?" Nayi dariya nace "my fight is over Fauziyya. Na gama. Bai gaya miki ya sake ni ba?" tace "ya gaya min amma ai saki daya ne dan haka akwai chance na zaki dawo din. Ya gaya min komai bayan kin tafi, kuma ni zanji dadi in kika dawo gidan nan. He loves you da gaske, in ma da baya sonki yanzu gaskiya yana sonki. Ya gaya min dalilin da yasa ya aure ni. Ni kuma na aure shine saboda ina son inyi settling down sai yazo da maganar aure ni kuma na karba. But a yanzu halin da yake ciki bayan tafiyarki I don't think Saghir is the right person to settle down with. Sun daura abota shi da shaye shaye. Most of the time ma baya kwana gida, kullum masifa kullum zage zage. Shi ne na kira in gaya miki, for the sake of your only daughter ki dawo maybe zai dawo hankalinsa in kina nan".

Nace "kiyi hakuri Fauziyya, but kamar yadda na fada miki. Na gama. For more than eight years nake tare da Saghir amma babu abinda muka tsinta a ciki auren mu daga ni har shi in banda wahala. Rabuwar insha Allah itace alkhairi. And kar kice baya sonki, tunda har ya zabeki a cikin sauran mata ya aure ki to kuwa tabbas yana sonki. Ki ci gaba da kokarin ki, it will be okay with you insha Allah".

And then one day, lokacin har nayi period biyu ina jiran daya. Monday, ranar da Sadauki yake zuwa sai Rufaida tayi rashin lafiya dan haka Mama ta tafi dubata ta barmu gida ni da Asma'u. Ni nama manta ranar Sadauki yake zuwa dan haka ina zaune a palo ina kallon wani film din hausa da na aro a gurin maman iman kawai sai jin sallamar sa nayi. Na tashi zaune sosai na gyara hijab dina sai gasu sun shigo shida Asma'u tana ta zuba masa surutu shi kuma yana mata dariya. Ya zauna ta gaishe shi ya tambaye ta ina Inna ta gaya masa bata nan. Sai ya dafe kai "kash, yau kice bani da kunun aya kenan" Asma'u tace "lah, sai da tayi maka ai kafin ta fita" sai ta tashi ta dauko masa ta zuba masa yana sha sannan na gaishe shi "sannu da zuwa. Ya office?" Ya kalle ni yace "yauwa. Lafiya lau" and that was all. Naji wani makokon takaici ya tokare ni. It really does hurt to be ignored, especially by someone da kuka saba sosai.

Sai kawai na kara volume din kallo na a raina ina fatan karar zata dame shi ya tashi ya fita amma sai ma naga sun dauko takardu shida Asma'u suna dubawa suna ta magana, kallo nake amma hankali na yana kansu sai na fahimci maganar ssce suke yi tana cewa "ni dai dan Allah hamma ka cire ni daga makarantar mu ka saka ni a government school in yi exams dina a can, wallahi government anfi ci, private basa bayarda da amsa" yarike baki "au kenan amsa kike so a baki? Maimakon kiyi karatu kici da kanki?" Tace "chaf, wadanda ma suka fini kokari basa ci ballantana ni? Yanzu kuma kaga in banci ssce din nan ba jamb dina ta tashi a banza kenan fa sai na sake wata" yayi dariya yace "kinsan kuwa sau nawa na zana jamb? Kuma a karshen karshe dai ban samu admission din dana ke nema ba" sai ta juyo ta kalle ni tace "Adda kema da kin sani kin cike form din jamb din. Kinga sai muyi tare in ba haka ba sai next year kuma" nayi kamar ban jita ba sai naji yace "in kina so sai a kawo miki gobe" na juyo na kalle shi naga yana kallona sai na kalli sides dina kamar me neman wani abu sannan na nuna kaina nace "are you talking to me?"

Sai yayi kamar zaiyi dariya amma ya wani maxe ya dauke kai yace "kina so ko ba kya so?" Nace "ina so, amma karka wahalar da kanka gurin kawo min, zan kira yaya Mukhtar ince ya siyo ya kawo min" ya daga kafada yace "duk daya. Tunda kinci waec dinki ba sai kin sake ba" sai na kalle shi da mamaki, I don't remember telling him cewa nayi waec ballantana zancen naci, nace "ya akayi kasan naci waec?". Sai kawai ya zauna yana kallona. And then all of a sudden sai ganin Saghir mukayi ya shigo palon hannunsa rike da Subay'a. He looked at me then at Sadauki and then at me again. Subay'a ta saki hannunsa ta taho gurina da gudu na bude hannuna na rungume ta ina jin dadi har cikin raina.

Saghir yace "what the f....." Sai nayi sauri na mike nace "Asma'u dauki Subay'a ku fita" dan nasan halin Saghir zai iya fadin komai ko yin komai a gaban Subay'a shi babu ruwansa. Ai kuwa tun kafin su fita ya fara "wato na matsa na baku dama ko? Shine wato zaku cigaba daga inda kuka tsaya? Ba kwajin kunyar duniya ba kuma kwajin ta Allah ko?" Sai Sadauki ya gyara zamansa ya dora kafa daya akan daya yayi folding hannunsa yana kallon Saghir. Ni kuma sai na mike, gabaki dayan su basa gabana dan haka baxan tsaya su bata min raina a banza ba. Nazo zan wuce Saghir ya kamo hannuna "ina zaki je? Munafuka kina wani saka hijabi kamar mumina" nayi kokarin kwace hannuna nace "don't touch me" ya maimaita "don't touch me, don't touch me kullum don't touch me." Sai ya juya yana kallon Sadauki yace "but I did touched her. Dan haka gwanjo nace. Duk inda zaka shiga babu inda ban shiga na fita ba and I left my foot print there" raina ya kai kololuwar baci, ban ma san me zance ba sai ji nayi Sadauki ya danyi dariya yace "are you sure about that?" Na kama kokawar kwace hannuna daga rikon Saghir zuciyata tana tafasa, zan so ace na fisu karfi in hada su duk su biyun inyi ta duka, how dare they talked about me like that.

Saghir yace "of cause am sure kasan a ledarta na bare ta. Sabuwa fil aka kawo min ita and I took her virginity" I froze. What? Ba zan ma iya kallon side din da Sadauki yake ba amma sai naji yace "ita nake so, not her virginity so...." Na kwace hannuna da sauri nayi bakin kofa hawaye yana bin fuskata, kafin in fita Saghir ya finciko hijab dina ya dawo dani cikin palon, ya hada ni da jikinsa muna facing Sadauki, Sadauki ya mike tsaye, Saghir yace "me yasa zaki gudu ne? Dan ke fa ake wannan taron ai ya kamata ki tsaya ki saurara kema ki tofa albarkacin bakinki a ciki. For example, tell him about our first night, tunda yace bai damu ba tell him how I did it maybe zai damu" na fara girgiza kaina da sauri. It is either Saghir is drunk ko kuma kwakwalwar sa ta fara tabuwa. And he said it. "I raped her" and then I saw a flash of fire a idon Sadauki. Saghir ya sake maimaita wa "I raped her the first night da aka kai min ita gida na. That was how she got pregnant for me har ta haifa min twins".

Sadauki took one step sai nayi saurin kwace jikina daga Saghir na tari gaban Sadauki na daga masa hannu "don't. Kar kace wani abu kar kayi wani abu just go" Saghir yace "yeah. Just go. But before you go, listen to this. Na mayar da ita dakinta." Na juyo da sauri ina kallonsa zuciyata tana bugawa kamar zata bar kirjina nace "no, no" yace "yes. Na mayar dake tunda dama saki daya nayi miki kuma shima bada son raina ba. Na mayar dake saboda ina son ki sannan kuma saboda I want him to think of you every night of every day when laying on his empty bed har zuwa ranar da zaki bar duniya ko kuma shi zai bar duniya. Sai inga karshen soyayya".

Inna ce ta shigo dakin da sauri, daga alama taga motocinsu a waje kuma tayi sensing something is wrong. Tana zuwa bata ce komai ba sai ta kama hannun Sadauki ta ja shi da sauri ta fitar dashi daga palon. Kafin su fita ya juyo ya kalleni and I saw a look on his face similar to wanda na gani ranar da zamu rabu a gidan Alhaji Babba. Na juya da gudu na shige bedroom din Inna na rufe kofa.
[2/23, 9:26 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Fifty One : The Will

A jikin kofar na zame na zauna ina jin zuciyata tana wani irin bugawa, ji nake yi kamar zan mutu, kaina yayi wani irin zafi kuma hawaye ya tsaya a ido na. Ban taba tunanin it's possible ka tsani mutum kamar yadda naji na tsani Saghir a lokacin ba. Na fara girgiza kaina ina cewa "no no no" kamar mahaukaciya. I can't even imagine komawa gidan Saghir a matsayin mijina, I can't imagine him touching me again. I would rather die. Ina jiyo maganganu a palo kamar muryar inna amma bana gane me take cewa, sai naji ta taba kofar amma da yake ina jikin kofar sai ta kasa bude wa sai naji tana kiran Asma'u. Sai kuma naji ana knocking kofar. Da kyar na bude idona na matsa daga jikin kofar sai suka bude suka shigo su biyu sannan Subay'a ta shigo itama tana kallo na sai naga Asma'u tayi sauri ta dauke ta sun sake fita.

Inna ta durkusa gabana tana taba wuyana tana magana a hankali amma ni bana jin ma me take cewa. Sai kuma naga ta kama ni ta mayar dani kan gado ta kwantar dani ta juya na riko rigarta sannan cikin muryar da naji kamar ba tawa ba nace "Inna bazan koma ba. In na koma mutuwa zanyi" ta juyo tana kallona sai ta zauna tace "komawa ina?" Sai kawai na bita da kallo, wato Saghir saboda bai daraja ta ba bai ma gaya mata cewa ya mayar dani ba? Sai ta gane me nake nufi tace "cewa yayi ya mayar dake?" Ban iya bata amsa ba sai kuka, sai ta mike tsaye "wannan wanne irin abu ne? Wanne irin ya mayar dake kuma? Suzo nan su kare mana cin mutumci sannan kuma ya mayar dake bayan babu wani mataki da aka dauka? To babu inda zaki koma. Yanzu fa Hafsa take bani labarin wai kawun ku Isa ya bashi Suwaiba" Suwaiba yar kawu Isa ce itama kuma kusan set din mu ce, mun dan girme ta kadan. Lokacin muna yara ita da Rumaisa ne suke crushing on hamma Saghir, murja tana yawan gayamin cewa har yanzu suwaiba tana son Saghir amma ni ban taba ko saka abin a raina ba.

Inna tace "wato su suna can suna kokarin yi masa huce haushi shine shi kuma zai zo nan yace ya mayar dake? To ku biyu yake so ya hada a gida daya ko kuma ya yake so ayi? Ai indai kinga kin koma gidansa to ki tabbatar an zauna ne an hada ku anyi muku fada kowa an bashi laifin sa bawai kullum ace kece da laifi ba" tayi ta fadanta ni dai ina jinta kawai. Amma ni a raina nasan ko anyi mana fadan bana jin zan iya sake zama da Saghir, not after what he did today, not after what he said a gaban Sadauki.

Tuni da Sadauki da nayi sai naji wata irin fargaba ta shige ni. Tsoro nake ji sosai, tsoron abinda Sadauki zai iya yi akan furucin da Saghir yayi a gaban sa. Ina tsoron zuciyar Sadauki, ina tsoron zafin sa, ina tsoron rashin tafiyar sa, considering abinda yaji da kuma yanayin da ya fita a ciki, bansan hukuncin da zai dauka ba. Sai na samu kaina dayi masa addu'ar Allah ya taushi zuciyarsa Allah ya hane shi ga aikata abinda zaizo yayi nadama.

Sai magrib na tashi. Nayi alwala nayi sallah nayi kuka sosai a cikin sujjada ta na roki Allah ya kawo haske a cikin al'amura na. A lokacin ne Asma'u suka dawo ita da Subay'a. Subay'a ta taho gurina da gudu ta fada jikina tana kallona tace "Mommy kin daina kukan? Dazu naga kina kuka" nace mata "na daina subis" sai tayi dariya tace "Daddy ya tafi ko? Dama cewa yayi zai kawo ni gurinki in kwana biyu sai mu koma gidan mu tare" bance komai da akan wannan sai tace "Mommy kullum sai nayi kuka nace da Hajiya ta kawo ni gurinki ita kuma taki. Mommy dan Allah ni kar a mayar dani can gidan gwara in zauna a gurin ko kuma mj koma gidan Daddy na tare" sai na daga ta nace taje tayo alwala tayi sallah.

Na lura ta rame, ta fada sosai tayi baki. Kamar ba'a kula da tsaftarta sosai sannan idonta ya nuna alamar damuwa. Sai na yanke wata shawarar, bawai ni kadai ce bazan koma gidan Saghir ba har da Subay'a ma ba zata koma ba, tazo kenan.

Da dare ina jin Inna tana cewa Asma'u ta kira mata Sadauki, kamar tasan ina son in tabbayda lafiyar sa. Asma'u ta kira switched off, a raina nace nasan za'a rina, amma ban furta komai ba nayi shiru kawai. Nan fa hankalin Inna ya tashi tace "wai me ya faru ne mai zafi a tsakanin su? Ni sam banji dadin yadda naga Sadauki ba tunda kuma ya fita hankalina yana kansa wallahi" ta juyo tana kallona tace "me Saghir din ya gaya masa me zafi haka?" Na sunkuyar da kaina kawai, ni ba zan iya gaya mata kalaman Saghir ba. Jin nayi shiru sai tayi ajjiyar zuciya tace "Allah ya kyauta".

Washegari babu kunya babu tsoron Allah sai ga Aunty Fatima nan da Hajiya Yalwati da kanwar Hajiya Babba wai Alhaji Babba ya turo su su gaya wa Inna cewa Saghir ya mayar dani, a gaya min in shirya sai mu saka rana ni da Saghir din sai yazo ya dauke ni. Ni kawai kallon su na tsaya ina yi cike da mamaki. Inna tace "yanzu Fatima har da ke? Har dake za'a ci amanar marigayi dan bashi da rai?" Aunty Fatima tace "me akayi Amina? Yanzu mayar da auren shine cin amana?" Inna tace "ba mayar da aure ne cin amana ba, rashin kulawa da nuna son kai shine cin amana" sai ta lissafa musu dukkan laifuffukan Saghir wanda ni na gaya mata tace "ni ba wai goyon bayan Diyam nake yi ba ko kuma bana so ta koma dakinta ba, a'a, so nake a zaunar da Saghir shima ta fadi laifin Diyam din sai a hada su kowa ayi masa fada a bashi laifin sa. A ja masa kunne akan dukanta dan ni abinda yafi komai daga min hankali kenan" sai Aunty Fatima ta nuna itama bata ji dadin abin ba tace "ni duk fa bansan wannan ba, ni cemin sukayi Diyam tana kula Sadauki shi kuma Saghir yaji haushi ya saketa. Kema yadda muke dake ai kamata yayi duk abinda ya faru ki kira ni ki gaya min. Da Diyam da Saghir duk yayana ne ai". Amma ita kanwar Hajiya sai ta kama fada, ita wai lallai nayi wa Saghir sharri "babu wani shayeshaye da yake yi balle neman mata" sukayi ta bugawa da inna har tayi zuciya ta tashi ta tafi Aunty Fatima ma ta tafi sai Hajiya Yalwati ta zauna tace sai anjima zata taho. Daga jin haka nasan tsegumi ta zauna yi.

Tace "wallahi Amina karki mayar da yarinyar nan. Yaron nan fa bawai gyaruwa yayi ba. To yaron da baiji kan iyayensa ba ina zaiji kan wani. Shaye shayen nan fa munsan yanayi amma sai a rufe ido ace bayayi. Neman matan nan kuwa yinsa yake yi kamar babu gobe. Ita kanta Fatima da take wannan maganar rannan a gaba na naji tanayiwa Minal yarta fadan kar ta kuma kula shi. Dama Suwaiba ce tasa kuma yanzu sunce sun bashi dan haka ku rabu dasu, in dai abinda Diyam ta fadi gaskiya ne in ya auri Suwaiban ai zasu gani" Inna tace "za kuwa su gani. Ai ni zanso ayi auren nan ma ko dan gaskiya ta bayyana" Hajiya Yalwati tace "gaskiya kam zata bayyana. Tun yanzu ba gashi nan muna gani yana zuwa yana daukan ta a mota ba? Ahau, lokaci kadai muke jira".

Har tana shirin tafiya kuma sai cewa tayi "ni Diyam kuma ta wani zubin banji dadin tahowar nan taki ba. Dama ke ce mai dan saka shi yana dan kawo mana abinci gidan. Yanzu kuwa shiru. Rannan har ya fara zancen aurar dasu murja yanzu kuwa yadda yake a rikicen nan nasan ba lallai ne yayi ba". Inna ta dauki yan kudade ta bata tace ta siyawa yara sabulu.

Da dare sai ga wayar Saghir. Na kalli wayar kawai na dauke kai. Yayi ta kira sai na saka a silent sai ya turo min message "ki shirya. Rana ita yau zan zo mu tafi". Sai na kashe wayar gaba-daya na ajiye.

Washegari wai dan rashin kunya sai ga Hajiya Babba da kanta. Ina ganin ta nayi wa Asma'u text. "Ki dauki Subay'a ku bar gidan nan, sai na kira ki zaku dawo". Ina kallon su suka fice. Tazo ta saka inna a gaba "yanzu ya za'ayi ace kince ba zata koma gidan taba? Yanzu zumuncin kenan? Koma menene ya faru a tsakanin su shi ya hakura ita me yasa ba zata hakura ba?" Inna tace "tace ba zata koma ba. Ni kuma baxan matsa mata ba, matsantawar da nayi mata a wancan karon ma da ace zan iya dawo da hannun agogo baya da banyi

Please Login or Register in order to submit comment