Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayani a taƙaice, nan da nan kuma ta ɗan sakar mishi fuska. Ko babu komai ta ji dadin mutunta da ya yi a wancan ranar wanda tun daga shi, Musaddam bai ƙara gigin shiga hurumin Raihana ba. Ba ta da masaniyar ko Fadeel mai yawan kiranta shi ne tsaye a nan ko kuwa dai wani abokin na Ibb ne daban kusa da ita hakan yasa ta gaishe su a jam'u. Suka amsa, Fadeel kam lebbansa ne suka motsa amma tuni ya yi nisa a kallonta, bai san lokacin da ya ƙara mayar da hankalinsa kacokam kan kyakkyawar fuskarta ba.

'Wallahi ina sonta.' Ya yi furucin a can ƙasan ransa kafin ya sa haƙori ya cije lebbansa ya sauke numfashi nannauya.

A cikin ɗakin taron kuwa, Tasleem da Futuha suka hana Ummita zuwa ga Mami, karshe suka ce ta zauna su za su je su shigo da Humairar wurin taron. Suka fito suka kara amsar katinsu suna dariyar mugunta, kawai burinsu su ga fuskar Humaira a karshe su ce Mami ta ce ta wuce gida ba za ta sanya ta roƙon kati a nan ba. Haka suka fito su na ta rarraba idanu, Futuha idanunta ya kai kan Ibb dake tsaye yana zuba wannan murmushin nasa mai tsada, a gefensa kuwa wani haɗaɗɗen matashi ne da ya zarce shi a haɗuwar. Ta dan murza idanu tana kara dubawa, tabbas Ibb ne.

"Ke, zo ki raka ni. Wayyo zuciyata, me Ibb ke yi a wajen bikin nan? Ko abokin Ango ne?"

Tasleem ta juyo, tuni Futuha ta soma tafiya ganin haka kawai ta mara mata biya.

Shi kuwa Ibb babu abin da ya sanya shi murmushi illa gani da ya yi Humaira ta ɗan saki jiki da shi tana sanar mishi cewa ai kam daga ranar Musaddam bai ƙara shiga rayuwar ƴar uwarta ba.

"Alhamdulillah. Hakan na da kyau. Sai ki ci gaba da yi mata nasiha. Allah ya ƙara nesanta ta da ire-irensu."

Murmushi Humaira ta yi lokacin da ta ke amsawa da amin. Kallon Fadeel ba ta ƙara ba balle ta fahimci hankalinsa kacokam a kanta yake. Har za ta tafi sai kuma ta kara duban Ibb.

"Yauwa, nikam ranar da abin ya faru, akwai wanda ka ba lambata?"

Fadeel ya yi saurin dubansa, girgiza masa kai ya yi don haka ya dube ta kamar bai fahimce ta ba.

"No, meyasa zan ba wa wani lambarki alhalin ko ni ban taɓa kira ba?"

Ta ɗan yi shiru, haka kawai ta ji abin kamar rainin hankali amma ta rasa tsakaninsa da wancan Fadeel din me kiranta a waya wane ya raina mata? Don haka ta ce.

"Ba ka da aboki mai suna Fadeel?"

Fadeel dake tsaye ya ji tamkar ta ci gaba da ambaton sunansa sanadiyyar hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mishi ba. Ibb ya ɗan yi gyaran murya domin ankarar da Fadeel ganin yanda ya harɗe hannuwa a ƙirji yana faman zabga murmushi. Sai kuma ya ce.

"Yau na fara jin sunan gaskiya, wani abun ya faru ne?"

Ta girgiza kai.

"Aa ba komai."

"Humaira."

Gaba daya suka juya ga inda kiran ya fito, Tasleem ce. Futuha kuwa idanunta sun cicciko da kwalla, ji take kirjinta na wani zafi. Mutumin da take kwana da tashi da tunani, shi dai wanda ya gagari kowace budurwa da ma zawarawa a jami'arsu, shi ne tsaye a gaban Humaira kucakar da ba ta kamo sawunta a kyau da hasken fata ba yana mata murmushinsa mai tsada da take ji a ranta za ta iya kashe ko nawa ne ganin ita ta sami wannan damar. Amma a banza gashinan ya na jifan Humaira da shi. Tasleem kuwa ta yi mutuwar tsaye wajen kallon Fadeel, sai yanzu take jin ba son Hamza D take yi ba, son ƙarya ne. Wannan abin da take ji game da Fadeel a yanzun shi ne so, soyayya kuwa ta haƙiƙa.

Fadeel ya nanata sunan da ya ji Futuha ta ambata. Humaira, shakka babu ta dace da masu sunan. Ibb kuwa ganin Futuha ya sanya shi tamke fuska kamar ba shi ke yiwa Humaira murmushin ba. Sai gaba daya matasan suka yi musu kwarjini, ita Futuha da ta yi niyyar wulaƙanta Humairar a gabansu sai ta yi laushi, yayinda Tasleem dama tuni miyan bakinta ya kafe, tunani take irin wadannan tsadaddun ai sai irin su masu zubin larabawa.

Dakyar Futuha ta yi magana.

"Mami ta ce ki wuce ki tafi gida tun da dai kin manta katinki."

Jin haka sai ta ji babu dadi kadan, ta kwallafa ranta a bikinnan ba don komai ba sai na son ta ga yanda tsarin biki yake a nan. Hatta da fuskarta ta nuna rashin jin dadinta.

Tasleem kuwa da sauri ta gaida Ibb da Fadeel har da ɗan ladabin ƙarya. Suka amsa.

"Sorry to ask, ba ta samu shiga wurin event din ba ne?"

Fadeel ya tambaya a sanyaye, tun zuwansu wurin sai a sannan ya yi magana. Humaira ta dube shi, kamar muryar mutuminta na waya, ya kauda kai ya kara shan mur kar ta samu fuskar tambaya. Tasleem da ta kusa shiɗewa jin ya yi mata magana duk kuwa da cewa akan Humaira ne ya sa ta saurin tankawa da wata murya cike da yanga.

"Eh ta bar katin nata a gida ne, so shi ne Maminmu kawai ta ce ta koma tunda ba za ta samu shiga ba."

Humaira ta tsaya kallon ikon Allah kawai, mamaki da haushin irin wannan karairayar murya na Tasleem ya cika ta. Har sai da ta ja guntun tsakin da sautinsa bai fito sosai ba.

"Muje."

Yana  fadin haka ya yi gaba, Ibb ya kalli Humaira.

"Ku je za ki shiga yanzu in sha Allah."

Ta amsa da toh, ta bi bayansa ita da Tasleem, ita kuwa Futuha ta ja burki gefen Ibb. Ya kauda kai tamkar bai san da ruwanta ba.

"Amm, Malam ba ka gane ni ba ko? Ni ɗalibarka ce a.."

"Ban sanki ba." Ya tari hanzarinta da sauri, daga nan ya taka ya nufi wurin motarsa ya tsaya. Futuha ido ya raina fata, ta dubi wasu maza a gefe tsaye da wasu ƴanmata da ma matan auren da ba su kai ga shiga ciki ba suna mata dariya, tana kallonsu suka ɗauke kai. Gwuiwa a sake ta kama hanya ta bi bayan su Tasleem, ranta ya yi tsananin ɓaci.  Ita kam ta soma gajiya da wulakancin Ibb, amma za ta yi hakuri tunda Anti Jannat ta haɗa ta da wata ƙawarta dake garin za ta yi mata rakiya gurin wani Malami a yi musu aiki a kansa. Amma zuciyarta na kokwanton aikin don ta ji wadanda sun buga sun kasa a kanshi.

Humaira kuwa na tsaye gefe Tasleem na tambayarta inda ta san su Ibb ta yi banza da ita kamar ba ta ji ba. Hankalinta na ga Fadeel dake magana da ɗaya cikin masu tsaron wurin. Ba ta san ya aka yi ba sai juyowa ya yi wannan karon gilashin da ya rufe ƙwayar idanunsa ya cire, lumsassun kyawawan idanun suka bayyana, suka kusan susuta Tasleem har ba ta san ta ce "Masha Allah." a fili ba sai da Humaira ta ɗan dube ta. Shi kuwa cikin ido ya kalli Humaira ya mata alama da ta zo. Sai da ta karasa dab da  shi kafin ya samu damar magana.

"A sha biki lafiya. A gaida Mami."

Ta ji dadi sosai ganin da ta yi an ba ta damar shiga. Ta kuwa buɗe masa haƙoranta har wushiryarta na bayyana a fili.

"Nagode sosai."

Ga Fadeel shima murmushin ya bita da shi, ji yake kamar ya jawo ta jikinsa ya rungume. Da ace shari'a ta halarta masa ita ma, sai ya sumbaci kuncinta wadanda har gani ya yi kamar su na sheƙi idan ta murmusa. Bai taɓa ganin murmushinta ba sai a yau, sai ya ji inama za su dauwama ta na jifansa da shi.

"Always welcome."

Ita dai ta yi gaba don bai san ba ta jin turanci bane, ta dai tsinci welcome din. Zuwan Mubarak ta ji yanda su Tasleem ke faman welcome welcome har ta nemi fassararsa a wajen Ummita. Babu wani iyaka kuwa aka bari ta shige, tana ɓacewa ganinsa ya maida gilashinsa. Ganin Tasleem tsaye tana kallonsa ya dauke kai, har zai wuce sai kuma dabara ta faɗo masa. Ya dubeta.

"Gidanku ɗaya?"

Ta yi wani farr da idanunta.

"Eh, babanmu ɗaya da ita."

Ya ɗan jinjina kai.

"Idan ba damuwa, ko zan iya samun full address na gidan naku?"

Ba musu jiki na rawa ta hau yi mishi kwatance, ta kara da fadin.

"Ko na ba ka phone number dina kaga ko da ace ba ka gane ba sai na yi maka bayani ta waya idan ka tashi zuwa."

Kamar ya ce aa, sai ya tuna ba lallai ya samu cikakken bayani daga Humaira ba dalilin haka kawai ya amince. Wayarsa ya ciro ya miƙa mata. Tasleem ji ta yi kamar ta daka tsalle ta yi rawa da juyi, hannunta har rawa yake yi. Ya dubi yanda take danna wayar cikin rawar jiki ya ɗan taɓe baki. Ya fahimci inda ta dosa kwarai amma ya basar. Babu gurbin wata ɗiya mace a rayuwarsa, madallah da Humaira da ta ciri tuta har ta yi nasarar sace zuciyarsa.

Ya karɓi wayar kafin ma ya tambayi sunan da zai yi saving da shi ta riga shi.

"Sunana Tasleem. Kar ka manta ka yi flashing ɗina kaga koda ka kira zan gane kai ne saboda ban fiye ɗaga unknown number ba."

Bai sake kallonta ba kuma bai tanka ba ya fice yana zura wayarsa cikin aljihu. Ta bishi da kallo kamar ta haɗiye shi. Futuha ita kuwa tuni ta shige ciki saboda kunyar yanda Ibb ya yi watsi da ita. Ta kuma rantse koda ace son Humaira yake, sai ta yi yanda ta yi ta raba su har abada. Tana ji a jikinta ba lallai ta sami Ibb ba, toh kuwa Humaira ta yi kaɗan ta samu abinda ita din ta rasa shi. A ɓangaren Tasleem kuwa gani take yi kawai ta tsinci dami a akala, ta samu mijin aurenta. A farko har ta amincewa Hamza D da zuwa gaishe da Abba, amma yanzu kam za ta dakatar da shi tunda ga Fadeel nan.

Wannan kenan.

***
Tun daga wannan ranar Futuha ke tsananin sanya idanu akan Humaira. Daidai da wayarta idan ta yi ƙara sai ta yi saurin kallonta ta ga wane ne. Rannan ta titse Raihana sai da ta titse wai wato Ibb ke kiran Humaira amma ta nuna mata sam ba shi ba ne, tsabar ta koyi munafunci.

Raihana rai a ɓace ta amsa.

"Wai ke meyasa kin fiye son kanki ne? Toh koda ace soyayyar ce tsakaninsu ai ke kin fi sauran masu haukar sonsa cin riba tunda ko ba komai ƙanwarki yake aure."

Wannan magana ta fusata zuciyarta nan kuwa ta hau kilar Raihana kamar an aiko ta. Lokacin Humaira na can gidan koyon girkinta. Ita kuwa Tasleem ba ta dawo daga asibiti ba don yanzu su na asibiti an tura su daga makaranta. A falon daga su Muhsin sai Ummita. Hankali tashe Ummita ta ruga kicin ta kira Mami. Ganin abin da ke faruwa yasa Mami dakawa Futuha tsawa. Sai a sannan ta miƙe daga ruwan cikin Raihana, gaba daya fuskarta ta yi tabo. Kuka kawai take da ihun fadin Allah ya isa, raini kam ta daɗe da raina su.

"Wane irin hauka ne wannan? Kashe ta kike son yi?!"

Cewar Mami tana duban Futuha dake faman huci. Sai kawai ta fashe da kuka.

"Wallahi Mami ba don kamannin yarinyar nan da mu ba sai ince ba ƙanwata ba ce! Wai saurayina ne Humaira ke so har da karɓar lambar wayarsa suna waya. Raihana ta san komai tsakaninmu, kema Mami kin san shi, wai shi  ne take fatan da ace ya auri Humaira. A gaban idanuna."

Mami ta saki baki galala tana duban irin kukan da Futuha take yi, lallai abin da zai sa ta kuka har haka ba ƙaramin abu ba ne. Tana da taurin zuciya a wasu lokutan, ita kanta zancen ya shige ta don ba ta mance yanda ta sha ba ta labarin wani Ibrahim ko kunyarta ba ta ji. Daidai da Anna ta san da zaman soyayyar da Futuha ke yiwa Ibb, sun kuma ji daga bakin Tasleem da ma su Yassar cewa mutumin bai damu da ita ba. Ta sauke ajiyar zuciya.

"Allah ya kyauta, shi ne akan wanda bai damu da ke ba za ki kashe yar uwarki? Kar ku kuskura na ƙara ganin wannan rashin hankalin."

Haka kawai ta fadi ta juya, madadin kicin ta wuce dakinta. Futuha ranta ya yi baƙi, wato ma abin da Mamin za ta ce kenan? Ita dai ta tsani halin rashin kulawar da Mamin ke nuna musu. A fusace ta yi sashin Anna har tana bangazar Raihanar. Ita dai Ummita ba ta ce uffan ba, toh ban da abin Futuhar ma, koda ace son Humaira yake, ta tabbatar ba zai samu fuska ba. Ita ta lura kowa ma Humairar ta tsana muddin zai furta mata kalmar yana sonta.

***
Anti Amarya ta ƙurawa Murja dake zaune tana faman jijjiga ƙafafu ido waya ta ke amsawa amma gaba daya fuska a jagule sai bayan ta kammala ta ajiye wayar, sannan Anti Amarya ta soma magana.

"Yanzu ke wannan Idris din kinsan matsayin babansa kuwa? Meyasa Murja ba ki da wayo da tunani? Kin maƙale akan yaron da idan ya shigo gidan nan kallo ba ki ishe shi ba? Komai kika yi ba ki iya ba, amma Idris tun haɗuwarku a bikin Fu'ad ya manne maki kuma dagaske aurenki ya ke son yi. Kinga ina raba ki, wannan fa shi ne saki reshe kama ganye. Kin gani sarai da idanunki yanda Ubansa ke ji da shi kamar ba shi da wasu yaran bayan sa, ko a haka ya dace ki fahimci babu wanda zai yi mishi auren dole. Ko da ace kuwa ba namiji ba ne, tun da ya sa ƙafa ya dawo ƙasar nan, Alhaji ke gudun abin da zai ƙara sanya wa ya yi nesa da shi. Toh kuwa ki kama kanki tun wuri ina shawartarki, soyayyar Fadeel ba za ta kai ki ko'ina ba. Ina kara faɗamaki wallahi ba ya sonki ba ya kaunarki."

Ta sani gaskiya ne tsagwaronta yayarta ke faɗi, amma ina, ta riga ta yi nisa da son Fadeel. Ta gama tsara yanda za su yi rayuwar aurensu wannan ya sa maganganun ke shigarta su na fita ta kunnen hagu. Ta furzar da huci.

"Shikenan, na yanke shawarar abin da zan yi."

A zaton Anti Amarya, ta dauki shawararta don haka ta murmusa.

"Ko kefa."

Ita kuwa murmushi ta ɗan yi, ta kuma ƙudurta a ranta za ta tari Fadeel kawai ta ce mishi tana sonsa. A yanda ta ga yana ganin mutuncin Antinnasa, ba zai watsa mata ƙasa a idanu ba.

***
BAYAN SATI ƊAYA...

A wani yammacin ranar Juma'a ne, Humaira na tsaye tana ninkin kayanta tana jerawa a sif. Futuha kuwa ta ƙure volume ɗin waƙar Kalmar So na breaker tana bi tana daukar bidiyo na kanta a tiktok. Riga gown ne a jikinta lemon green fuskar ta sha make up. Gashinta a waje ko ɗankwali babu, sai raye-raye take. Raihana da Ummita na zaune su na aikin lissafi na makaranta da aka ba su, su na ɗan taɓa hira jifa-jifa da Humaira. Su na yi suna kallon ikon Allah wajen Futuha da ta saita Camera ta waya sai raye-raye ta ke yi. Wannan karon ta sauya waƙar zuwa Warr na Ado Gwanja.
Kusan yanzun aikinta kenan, ta yi rawa ta ɗora a Tiktok da Instagram, babu laifi kuma ta samu mabiya sosai, wannan ya kara fasa mata kai, a farko hotunanta kawai take ɗorawa iri-iri a instagram, amma ba ta jima da soma Tiktok ba ta ga ta samu karɓuwa wannan ba karamin ɗauke hankalinta ya ke ba a yanzu. Su na a haka sai ga Tasleem ta faɗo ɗakin da gudu. Jiki na rawa ta karasa sif din kayanta ta bude. Futuha wacce ta kammala tana editing kafin ta dora ta dakata tana dubanta.

"Ke kuma lafiya?"

Ta juyo da wani irin zumudi.

"Kalau, babban baƙo zan yi fa. Kin tuna guy dinnan da na hadu da shi ranar bikin Shema'u? Abokin Ibb?"

Futuha ta gyada kai. Tasleem ta daka tsallen murna.

"Shi ne ya yimin waya ya kara neman kwatance, yau zai zo."

Ita kanta Futuha ta jiye mata dadi, amma haka nan ta ji ɗan kishin yar uwar a ranta. Me Tasleem ta fi ta da har za ta yi kamu me zafi haka lokaci ɗaya amma ita kuma ta kasa samun Ibb? Tun su na yara an sha cewa ta fi Tasleem kyau, balle kuma yanzun da suka girma. Kowa ita ya fi kira kyakkyawa a kan dai Tasleem. Wannan ma na daya daga cikin abin da ya fasawa Tasleem kai a yanzun, itama tana jin takaicin kusheta da yan uwan Mami har ma da na Abba ke yi a lokuta da dama su ce wai Futuha ta fi ta kyau. Sai Futuha ta kasa ce mata komai bayan "Inyee, na maki murna." Daga nan ta ci gaba da latse-latsen wayarta tana murmushin da bai kai zuci ba. Tasleem ta maida hankali ga duban sif dinta, ta san Futuha mace ce mai kishi, ta fi kaunar komai ta fi kowa, kuma sai gashinan nasarar a kanta take. Tashi guda ta yi kamun babban kifin da ya fi wanda Futuhar ke hari.

Raihana kuwa duban Ummita ta yi. Cikin sanyin muryar da ba lallai su Tasleem su ji ba ta ce.

"Kada dai ace Fadeel me son Humaira ne zai zo?"

Ita ma Ummita hakan ta ke zargi, Humaira na jin su ta yi kamar ba ta ji ba. Ta sani tabbas shi ne, sai bayan sun rabu ta kara tabbatarwa shi ne mai kiranta adalilin saƙon da ya turo mata bayan shigarta wurin bikin Shema'un, inda ya ce mata ta yi kyau kuma ya yaba da murmushin da ta yi mishi a lokacin. Sannan bayan sallar juma'a a yau din, ya bar mata saƙo inda yake shaida mata batun zuwansa gidansu a yau. Ya kuma roƙe ta kar ta ƙi fitowa. Ita kuwa a take ci kanka ba ta aika mishi ba balle ta kira ta dakatar da shi daga zuwan, ta fi kaunar ya zo ta jaddada masa ido cikin ido cewa ita ba ta soyayya, kuma ba ta sonsa ya rabu da ita.
Tunano hakan sai ta ji dariya ya kama ta, dakyar ta danne ta hanyar murmusawa. Wato dai yau din akwai kallo kenan. Ta kara duban Tasleem da ta sauya kaya zuwa wani leshinta ja mai ɗigon baƙi a jikinsa mai ɗan karen kyau, murmushin ta kara saki wannan karon har da sautin dariyar da ya sa su Raihana dubanta, suka kuma dubi junansu, sun tabbatar Fadeel ɗin Humaira ne a hanyar zuwa. Akwai dai matsala kenan.

©️Rufaida Umar.

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645


Wayar Tasleem da ta ɗau ƙara ne ya sa ta saurin jifa da kwalbar turaren dake hannunta a saman gado, ta zari mayafinta da ya hau da leshin ɗan firit wanda ko kirjinta bai gama rufewa ba, ficewa a dakin ta yi bayan ta kara wayar a kunne tana fadin ga ta nan fitowa waje. Futuha ta mike ta bi bayanta wai za ta gani ko dagaske Tasleem din ta ke. Suna fita Humaira ta tuntsire da dariya har da faɗawa saman gado. Raihana da Ummita su ma dariyar suka shiga yi.

"Ni dama ya ce yana son nata dagaske ai da naji dadi, ko ba komai na huta da alaƙaƙai. Haba, ina dalili mutum ana korarsa yana mannewa sai ka ce mayen ƙarfe."

Ta ja guntun tsaki ta mike ta ci gaba da ninkin.

"Kai Humaira anya a duniya za ki yi aure kuwa? Wannan abu har ina wai? Duk kyau da kwalisa na saurayi ba kya sonsa? Meke damunki?"

Ummita ta ce tana duban ta, ji take kamar ta kai hannu ta buge ta tsabar haushi. Itama Raihana ta cafe

"Rabu da ita Ummita, ai kanta akwai alamar kuncewar notina. Da ace ma ni ce ke, ko don na nunawa Tasleem ita ɗin ba komai ba ce a wurin Fadeel ai wallahi da hannu bibbiyu zan tarbe shi, shima dai Fadeel din da ba shi da zuciya ya kyaleki ya ƙi, ya bari kina ta wulaƙanta shi son rai. Da ni ce shi ko?"

Ta yi ƙwafa amma ba ta ce komai ba, Humaira wacce tun soma maganarsu take kwaɗa musu harara, ta ja tsaki.

"Matsalarsa, ni dai ai ban yaudareshi ba, tun farko kuma na faɗamasa ya rabu da ni, ya ficemin a rayuwa amma ya ƙi. Aikuwa babu abin da zan ce mishi, ya je can ya ƙarata da Tasleem."

Ba su ce uffan ba sai kallon mamaki da suke mata, dagaske dai take ko a jikinta don ba su ga wani ɗigon kishi a saman fuskarta ba.

A ɓangaren Tasleem kuwa, tana ƙarasawa falon ta ci karo da Mami a zaune tana amsa waya. Ganin ta da shirin fita ya sanya ta yi sallama da abokiyar wayar ta dube ta dakyau.

"Ke kuma sai ina haka?"

"Mami baƙo fa nayi, bari na shigo da shi falon saukar baƙi sai na zo."

Ba ta ma kara jin abin da zai fito a bakin Mamin ba ta yi wuf ta fice, Mami ta yi kasake tana duban hanya, fitowar Futuha ya sanya ta maida akalar tambayar a kanta.

"Wannan wane baƙon ta ƙara yi a yanzu ne? Duka-duka yaushe shi Hamzan ya zo da har zai ƙara zuwa?"

Taɓe baki Futuha ta yi cike da jin kishin ƴar uwarta ta amsa.

"Uhum, wai fa abokin Ibb ne yake sonta shi ne take wannan rawar jikin."

Wani ɗan murmushi Mami ta yi.

"Wato dai ruwan ido ne abin nata kenan? Ya za ta yi da shi wanda ta yiwa iznin zuwa su gaisa da Abbanta?"

"Mami, wannan fa ya fi Hamza kudi da haɗuwa, na tabbata abin da ya ruɗe ta kenan."

Mamin ba ta ce komai ba face Allah ya kyauta.

***
Yana zaune a cikin motar hankalinsa rankatakaf akan ƙaton ƙyauren gidan da Tasleem ta yi mishi kwatance, ji yake tamkar ya yi tsuntsuwa ya shiga ya yi ido huɗu da abar ƙaunarsa, ganin ya kwashi mintuna babu alamar Tasleem sai ya ji gaba ɗaya ya karaya. Kodai ba gidan ba ne? Waya ya fiddo da niyyar ƙara kiranta sai ya hange ta ta fito daga gidan. Da farko sam bai gane ta ganin tamkar wannan ɗin shirin fita unguwa ta yi, ga dukkan alamu ma ba gidan ba ne. Amma a hankali tana matsowa ya gane ita ce don haka ya sauke tinted glass din motar wanda ya katange ta daga ganinsa sai waige ta ke.

Tasleem kuwa yana saukewa ta ji numfashinta na barazanae ɗaukewa ba don tsoro ba sai domin tsananin burgeta da ya yi, ga kuma wani irin kyau da ya yi mata. Shadda ce a jikinsa coffee colour, ya ɗora hula a kansa, wannan karon babu gilashi a idanunsa don haka kyawun fuskar ya ƙara bayyana muraran. Ta kasa furta koda harafi har sai da don kansa ya fito daga motar ya rufe. Murmushi mai tsada ya sakar mata.

"Ashe kin iya kwatance."

Ta yi farr da idanu haɗi da sakarmasa nata kalar murmushin itama. Cike da yanga da kwarkwasa ta ce.

"Kai kuma kana da basira tunda har ka iya ganewa. Barka da zuwa, bismillah mu shiga daga ciki."

Ba musu ya karɓi tayinta, bayan sun gaisa da maigadi dake zaune a benci, tana gaba yana biye da ita yana ƙarewa gidan kallo. Hatta da gidan sai da ya ji kaunarsa a zuciya, ya kuma rantse albarkacin masoyiyar tasa ce.  Falon suka shiga ya zauna bayan ta mishi bismillah, sai ƙamshi kuwa ke tashi a ciki don dama tunda ya yi mata kiran farko ta ba mai wankin Abba dari biyu akan ya taimaka ya kara share mata a sa turaren wuta.

"Ina zuwa." Ganin ta furta haka tana niyyar ficewa sai bai ce mata uffan ba, ba ya son ya yi garaje da tambayarta Humairar, tunda har ta ce tana zuwa to ya sani ba zai wuce ita za ta rako ba.

Ya lumshe idanunsa kafin ya buɗe ya sauke saman hoton Abban dake maƙale jikin bangon. Ko wani bai faɗamasa ba, wannan mahaifin Humaira ne, kamannin ya ɓaci kwarai. Sai ya

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment