Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba zan taɓa nunamasa zazzafar kishina ba saboda a lokacin labarin komai da na aikata a baya ya je kunnensa ta wurin munafukai, wannan ta sanya ya yimin gwaji kala-kala kamar ya yimin wasan yana da mata auren haɗi, yana da budurwa da dai sauransu. Ni kuma na danne bana nuna masa ɓacin raina har sai da ta kai ya ƙaryata zantukan mutane a kaina. Amma fa duk radda ya yimin irin wannan idan na koma gida ranar ko tsinke ba zan ɗauke da sunan aiki ba, kuka kuma zan yi shi. Babu wanda ya isa ya taɓa ni a ranar ya sha. Mahaifina ya rasu dab da aurena da Yusuf. Bayan aurenmu babu irin faɗi tashin da ba mu sha ba saboda rashin kuɗi. Soyayyar da nake yiwa Yusuf ta sanya ban taɓa gujemasa ba daidai da kwayar zarra. Kasuwanci iri iri babu wanda bai yi ba har siyar da kayan miya, gwanjo, da dabino. Kowanne sai an fara rimi-rimi sai lamarin ya ɓaci."

Mami ta haɗe girar sama da ta ƙasa ta juyo tana duban Futuha dake tsaye tana sauraronta ta cigaba da magana.

"Mahaifin Ummita ya fi mijina rufin asiri sosai, shi mutum ne mai arziƙi, matarsa duk sabgar dangin miji ta fi kowa gayu da kuma kyauta saboda mijinta yana da kuɗi. Ba ta da taƙama balle wani abu wai shi girman kai, wannan kyawawan ɗabi'unta da na tsana, da su ne ta siye zuƙatan uwar mijina kafin ta rasu, ta yi bake-bake a wurin yan uwan Yusuf, ba a ganina da mutunci sai ita. Duk yawan kirkina saboda mijina ba shi da kudi sai na zama tamkar mujiya. Eh uwar mijina tana sona amma soyayyar da take yiwa Jamila ya wuce gejin nawa. Saboda tsabar yanda tsanar Jamika ya rufemin idanu har gani nake yi ba a nunawa yarana kauna a lokacin alhalin ita ko haihuwar ba ta samu ba daga ta samu cikin sai ya ɓare. Haka na jero yara biyar Mubarak,Yassar, Dawud, Ƙassim da kuma Ke. Wannan  lokacin ne kuma Yusuf ya zo min da labarin ƙara aure bayan mutuwar mahaifiyarsa, a sannan kuma ba laifi asirinmu a ɗan rufe yake. Yusuf har shago yake da shi a kasuwa yana siyar da kayayyakin agogo wanda ƙaninsa Muntari ya buɗe mishi. Wannan ma ya ƙara tsananta tsanar Jamila da Muntari a zuciyata ganin wato dai arzikinsu muke ci, da azumi haka Muntari ke sauke mana kayan abinci, da sallah, Jamila ke zuwa ta kawomana kayan fitar sallah wannan abu ya tsayamin a ƙahon zuci. Maijidda ita ce macen da ta soma lura da tarin ƙiyayyar da nake yiwa yar uwarta, akwai sadda ta taɓa ganina muraran ina yiwa Jamila barbaɗen magani a abinci wanda daga shi ne ta tsane ni ta kuma ce Jamila ta yi hankali da ni.
  Toh zuwan da Yusuf ya yi da batun ƙara aure ya yi mugun ɗagan hankali amma damuwa ko ta ɗigo ban gwada masa ba, a farko da na ɓata rai, sai ya rude da rarrashina, sai kawai na fashe da dariyar baƙin ciki na nunamasa tsokana ce kawai amma nikam bani da matsala da aurensa. Da wannan ya auro Fatima wacce ya haɗu da ita a kasuwa ta rako Dadarsu siyayyar kayan auren dan uwanta Umar. Shikenan soyayyar ta kai su ga aure. Anna ba ta tare da ni a sannan saboda mijina ba shi da kudi babu wurin da zamu ajiye ta, ita kanta a sannan zagina take yi wai don me zan maƙale nace sai Yusuf da ba shi da ko keken hawa. Nidai son da nake yi masa ya hana ni karɓar ƙorafe ƙorafenta. Ba ta damu da zuwa gidana ba a lokacin.
Aka yi auren Fatima da Yusuf, jininta ya hadu da Jamila. Madadin ni da muke dan shiri da Jamilar a baya, sai suka dinke da Fatima suka zama tamkar wasu ƙawaye, a sannan ina da cikin Tasleem, na kai zuciyata nesa na danne da taimakon shawarar sabuwar ƙawata Lubna da muka hadu a wurin wani bikin tsohon ubangidan Yusuf na kasuwa, mijinta mai arziki ne lokacin yana rike da matsayin Chairman. Da taimakonta na san Boka Babandi, muka niƙi ƙafa daga nan har Katsina wajensa ba tare da sanin Yusuf ba. Na samo magungunan hana Fatima daukar ciki muka dawo.
Cikinta na farko kuwa ya bi rariya, ni ce mai jinyarta da nuna mata ƙololuwar kulawa. Dadarta koda ta zo ta dinga sanyamin albarka da yabona. Yusuf kuwa tamkar ya haɗiyeni ganin a lokacin ko arba'in din Tasleem ban yi ba na haihuwa amma ina fama da kula da Fatima, wannan dalili ya siyomin sabuwar kauna a zuƙatan yan uwan Yusuf.
  Kamar kuma a mafarki ina dauke da karamin cikin Raihana sai ga Fatima da ciki har watanni biyar ya soma fitowa a jikinta, ba karamin firgita nayi ba da na gani saboda ko kadan ban ga wasu alamomi ba. Kuma na rasa yanda aka yi ko a hira ba ta sanar da ni ba. Hankalina ya yi mugun tashi, sai da na kai zuciyata nesa sosai kafin na iya danne damuwata. Ga wani irin soyayya da Yusuf ke nunawa Fatima har a gabana wanda nake ji kamar na shaƙe su duk biyun na huta. Ganin haka ni da Lubna muka ƙara miƙar hanya wurin Babandi, anan ne na je masa da buƙatar jefa tsanar Yusuf a zuciyar Fatima yanda ko sunansa aka ambata sai ta ji haushi. Babandi ya ban tabbacin ba ma Yusuf ba, kowane namiji sai ta tsane shi a rayuwarta muddin ya haɗa ta da wani arnen aljani. Da wannan na tattaro duka chanjina na ajiyemasa. Muka rabu da zummar zan ga aiki da cikawa, ya kuma ban wani hayaƙi yace duk sadda ta shiga halin ƙunci da kuka marar iyaka na yi mata hayaƙin. Wannan zai ƙara tasirin tsanar a zuciyarta. Da wannan muka rayu, Yusuf ya shiga tashin hankalin sauyin Fatima. Akwai radda ta taɓa shaƙe masa wuya dakyar aka ɓamɓare ta sai da na nemi taimako a waje, daga wannan ne kuma ya aikawa Dada saƙo ta zo takanas daga Nijar aka tafi da Fatima saboda ta rantse muddin aka bar ta ta cigaba da rayuwa a gidan za ta kashe shi ko kuma ta kashe kanta. Na yi kuka sosai kamar raina zai fita a gabansu, na ce su kyale ta ayi mata magani a nan idan har larura ce, Dada ta dinga rarrashina ta ce gwara ta tafi da ita. Daga wannan ranar ne na rabu da Fatima, rabuwar da har gobe ba ta ƙara tako Nijeriya ba. Wannan abu ya yimin masifar dadi, cikina nada watanni shida, Jamila ta haifi ɗiyarta mace mai sunan mahaifiyar Jamila, Rahina suke kiranta da Ummita. Sun yi gagarumin sunan kashe kudin da naji tamkar na dora hannu a ka nayi ihu da kuka  ina ji inama Yusuf keda kudin Muntari. Da wannan na soma tunanin duk runtsi sai dukiyar Muntari ta zama rabon Yusuf watarana."

Mami ta numfasa ta karasa ta zauna gefen gado, ganin haka Futuha itama ta nemi wuri ta zauna, wasu abubuwan za ta iya tunawa wasu kuwa ba ta da wayo. Ta dai san Mubarak na yawan yabon mahaifiyar Humaira da kaunar da ta nunamasa, yayinda su Yassar suka tsaneta saboda tsanar da ta yiwa Abbansu. Maganar Mami ya katse tunaninta.

"Haka rayuwar ta cigaba har na kusa haihuwa, Yusuf gaba daya ya rame ya tashi hankalinsa saboa Fatima, ya kai mata ziyara har sau biyu daga nan ne hankalina ya yi mugun tashi, wato soyayyar da Yusuf ke yiwa Fatima ya ninka nawa kenan? Ban yi ƙasa a gwuiwa ba, ban kuma damu da cewar tsohon ciki gareni ba, na bi shawarar Lubna na niƙi ƙafa na koma wurin Babandi. Nan na nemi a yimin aikin da zai sa a raba Fatima da abinda ke cikinta da duniyar ma baki daya. Ya nunamin yanzu haka da muke magana Fatima naƙuda take yi, ya tabbatarmin zaa turamata baƙaƙen aljanun da za su yi sanadin rayuwarta. Na yi murna kwarai, amma abin baƙin ciki ya cemin abin da za ta haifa dole zai rayu a doron ƙasa, nidai ban wani damu sosai ba. Koda ya gama dubansa ya ce aikin zai yiwu haka na tattara na tafi da farin cikin Fatima za ta bar duniyar baki ɗaya. Za ta bar mijina. Sati uku da haihuwar Fatima, labari ya zo mana na rasuwarta. Zo ki ga kuka a wurina kamar zan shiɗe. Na nuna zan je gaisuwa, amma Yusuf ya hana ni saboda cikina ya shiga watan haihuwa, da wannan hujjar ya tafi har ina ce masa ƙafarsa ƙafar jaririyar Fatima ya kawomin ita zan riƙe. Wannan ya sa Yusuf ya ji dadi sosai ya dinga yimin godiya bisa kaunarsa da nake. Har a zuciyata addua nake kada a ba shi Humaira ya kawomin. Aikuwa haka ya dawo babu ita ya cemin wai Dadar ta daukarwa Fatima alƙawarin kula da Humaira, ya yi hakuri. Daga nan fa rayuwa ta dawomin sabuwa fil a gidan mijina. Daga ni sai yarana, na haifi Raihana bayan Jamila ta haihu da kusan watanni shida, Humaira na da watanni hudu itama lokacin. Shekaru suka tafi har aka shekara biyar, zuwa lokacin rayuwar kunci da talaucin ya ishe ni, samun Yusuf ya ja baya sosai. Gaba daya ya zamana hatta kudin makarantar yara daga aljihun Muntari yake fita, wannan ya kara sanyamin ƙiyayya mai tsanani na Muntari da Jamila. Ban samu sukuni ba har sai da na biya wasu yara suka haɗa gobarar da ba a fitar da komai a gidan Muntari ba sai Ummita."

Idanu waje Futuha take duban Maminta wannan karon.

"Ma..ma.." Ta ma kasa magana taabar firgicin da ta shiga da tsananin ruɗani. Tana kara tabbatar da nisan da mahaifiyarta ta yi a fannin da suke ganin sun fi ta. Mamin ta yi yar dariyar mugunta.

"Yes, ni na sanya aka ƙona iyayenta, aka kashe jaririyar da Jamila ta haifa da Jamilar ma. Ban san ya aka yi shegiyar yarinyar ta tsira ba. Haka labarin gobarar ta zo mana, hankalin kowa ya tashi ciki har da ni da na nuna ban san komai ba. Shegiya Maijidda tun a sannan ta nuna ita wallahi ba ta amince gobarar gaske ce ta kashe Jamila ba. Ta ce a bincika amma kowa ya yi burus da ita ga tunaninsu kawai zafin mutuwar Jamila ne saboda irin shaƙuwar da suka yi da juna. Da nayi wani tunani akan dukiyar Muntari sai na shawarci  Yusuf akan ya ɗau riƙon Ummita kar a raba ta da dangin mahaifinta. Nan fa ya amince, ya kuwa dage akan lallai shi sai an ba shi Ummita. Sun so yin fada da Maijidda wacce ta dage lallai ita za ta dauketa, a karshe dai da Kawunnansu suka sanya baki dole ta hakura ta kuma kalleni ta bini da Allah ya isa. Na fashe da kuka ina nunawa jama'a Maijidda ta tsane ni, nan aka hau rarrashina har yan uwan Jamila ana ganin baƙin Maijidda. Yusuf har kusan faɗa ya yi da Maijidda a kaina dakyar dai komai ya lafa. Wannan shi ne silar dawowar Ummita hannuna, daga baya kuma Humaira ta zo wannan kin sani."

Futuha ta ja dogon numfashi.

"Tab! Mami kina da abubuwan mamaki sosai. Wallahi ba don ke da bakinki kike fadamin ba, da ace a wani wurin na ji dukkan wadannan zan ƙaryata ko waye ya faɗi."

Murmushi Mami ta yi.

"Ku ne ba ku san rayuwa ba, yanzu da ace wani mugun halin na nuna a zahiri, kuna zaton Abbanku zamu kai yanzu da shi ba tare da mun rabu ba? Ko kuwa kuna tsammanin a baya ida  kishi ya kwashe ni na kashe Fatima da hannuna yanzun zan cigaba da rayuwa a duniya? Ai hakan ba zai taɓa afkuwa ba, komai ɗan hakuri ne da bi sannu-sannu. Ka yi siyasa a komai, ka shanye komai ka danne sai ka ci riba. Ina dab da cin ribar kwace dukiyar Yusuf saboda na faranta maku, na ba yarana maza jari su huta daga maƙon da Yusuf ke yi musu, na kuma nunawa Anna ba Firdausi Jannat ce kaɗai ɗiya ba, nima na san yanda zan iya kwatar kaina a wurin miji, wannan ne dalilin daya sa na sanya aka sace yarannan, sai dai kuma kuɗaɗen su na dab da samuwa, komai ya rushe saboda zuwan ƴan sanda. Amma ban saduda ba, ban kuma karaya ba, har gobe ba zan fasa yunƙurin ƙwatarwa yarana haƙƙi ba tunda ubansa marowaci ne mai shegen maƙo."

Fuska a sake Futuha ta rungume Mami kafin ta saketa ta ce.

"Wai Mami ashe daman kina kaunarmu?"

Harararta ta yi.

"Wa ye ba ya kaunar nasa? Na fadamaki ai duk duniya wanda za ki ga ya nuna ba ya son nasa ya fi kaunar wasu toh ƙarya yake yi, munafuki ne."

Jinjina kai Futuha ta yi tana washe baki.

"Hakane, Mami na kara sonki wallahi. Kin wanke tunanin dake zuciyata na ganin bakya kaunarmu. Ni fa lallaɓa Humaira nake yi so nake ta zo gidana ta koyawa yar aikina girke-girke. Shiyasa kika ga ina ta janta a jiki da kissa."

Mamin ma dariya ta ce.

"Sai ki bada himma."

Sai kuma ta daure fuska sosai.

"Ina kara jaddada maki, koda wasa kika yi yunkurin sanar da wani ko wata labarinnan wallahi zan iya kashe ki."

Sosai furucin ya tsoratar da Futuha, ta yi saurin rike hannunta.

"Aa Mami, wallahi na rantsemaki babu wanda zai ji. Ai ina sonki, ba zan so hukuncin shari'a ko yaya ya hau kanki ba."

Sai anan ta saki fuska ta shafa kan Futuha. Daga haka suka bar zancen suka koma falo inda Tasleem suke zaune da su Mubarak ana cin abinci. Ko kallon Futuha ba ta yi ba, tsanarta take ji a zuciya, wato saboda tana da kudi shiyasa har wani shiga daki suke su rufe su na kwasar hira ita da Mami. A duniyarta ko a mafarki aka ce Futuha za ta samu miji wanda ya fi nata za ta ƙaryata. Ga Hamza yanzu ya sauya mata, zamansu gaba daya babu dadi hatta a bangarenta da uwar mijinta da ma yan uwansa. Albarkacin cikin jikinta kawai take ci ta san da wannan. Don ma dai Anti Jannat ta ce ta kwantar da hankalinta har ta haihu sannan su san yanda za su ɓullowa lamuran. Wannan ne kadai ya sa ake ganinta cikin nutsuwa, kuma ita dinma ba ta ragawa Hamzan.

***
  Da yammacin ranar daidai lokacin da su Futuha suka fito da zummar tafiya gida har da Tasleem wacce za ta sauke nata gidan sanadiyyar Hamza da ba  zai samu zuwa daukarta ba, sai ko Humaira wacce a dole ba don ranta ya so ba bisa umarnin Mami za ta bi Futuha gidanta ta yi zaman sati biyu kawai don ta koyawa yar aikinta girke-girke, su Raihana sun yo musu rakiya farfajiyar gidan. Humaira tana tuno Fadeel wanda ya ce yana hanya, tana son ta dakata ta jira shi amma wata zuciyar na kwaɓarta da nuna mata babu amfanin sauraronsa tunda ba aurensa za ta yi ba. Suna nan tsaye, tana sanye da yadi mai taushi maroon colour wanda ya fiddo tsantsar kyawunta da hasken fatarta, ta ɗora karamin mayafi a kanta golden colour. Babu kwalliya ko na ɗigo a fuskarta amma kuma sosai kalar ta karɓe ta, zama wuri ɗaya babu fita ya sanya har wani sheƙi fatarta ke yi. Daidai sadda Futuha ta bude ƙofa tana shirin shiga, daidai lokacin maigadi ya wangalewa Fadeel ƙofa ya turo da hancin motarsa ciki. Bisa umarnin Abba, Fadeel ya zama ɗan gida, duk sadda ya zo yana da damar da zai yi parking a farfajiyar gidan. Ya kuma shiga idan an mishi izni su gaisa da mutane. Shi din ne dai ya zaɓi rashin zuwan akai-akai saboda gudun kada ya baƙantawa Humaira ta ga kamar yana neman shigarmata hanci da ƙudundune alhalin gidansu ne.

"Wannan motar kuma fa?"

Fadin Futuha tana karewa motar kallo, lexus Ls blue black sai sheƙi take yi, daga gani ba a moreta sosai ba don ba ta nuna alamun tsufa ba.

"Wannan motar Fadeel ne. Na gane, ya taɓa zuwa da ita sau ɗaya wurin Abba."

"Fadeel?" Tasleem da Futuha suka nanata sunan a zahiri. Aikuwa kafin su rufe bakunansu haɗaɗɗen matashin nan mai sa numfashin yan mata tsayuwa na wucin gadi ya fito daga cikinsa. Sanye yake cikin maroon tshirt da baƙin wandon jeans kamar da hadin baki shi da masoyiyartasa. Ya rufe idanunsa da baƙin gilashi yana wani murmushi mai ruɗar da zuƙata. Duhun kayan da ma motar da yake jingine a jikinta sai suka kara fiddo da tsantsar farinsa na usulin bafalutani ɗan asalin garin Yola. 

Gaba daya Tasleem ta yi wani shock, suka yi mutuwar tsaye. Idanunta har wani ruwa-ruwa yake yi saboda tsabar kallonsa da ta shagala yi ga wani irin so da kauna dake fisgarta har ta mance da wasu igiyoyi masu ƙarfi da suke nannaɗe da ita suka yi mata shamaki da dukkan wani ɗa namiji da ba muharraminta ba. Shi kuwa Fadeel idanunsa a saman na Humaira har dai su Yassar suka karaso aka yi musabaha.

Humaira kuwa ta yi wani irin dauke kai daga kallo daya ba ta ƙara ba.

"Wajenki ya zo ne?" Futuha ta wurga mata tambayar tana ɗan murmushin yaƙe, a ranta kuwa jinjinawa Mami ta yi, tabbas ba karamin kokari tayi wurin danne abin da ke ƙasan ranta ba, akwai masifar wahala. Sosai itama ta ji kishin ace Humaira ce ta samu wannan kyakkyawan matashin kuma mai rufin asiri.

"Ban sani ba." Amsar da Humaira ta bayar kenan tana ƙara tamke fuska. Tasleem kamar ta shaƙe ta, yarinyar ta samu dama amma tana nuna girman kai. Ita da ace itace da wannan damar ai sai inda ƙarfinta ya ƙare.

"Assalamu alaikum."

Sallamarsa ta katse musu tunani, Raihana ta jingina jikin Humaira dab da kunnenta ta ce.

"Ki riƙe wannan bawan Allahn sosai idan kuwa ba haka ba ni zan maye gurbinki."

Ba ta san ya aka yi ba sai tsintar idanwanta ta yi da wurgawa Raihana wata muguwar harara mai nuni da tsantsar kishi, Raihana ta sa dariya tana riƙe kunnuwa gami da ɗan jujjuya kai alamun ta tuba. Tana kuma kara gasƙatawa Humaira na son Fadeel, ba kuma ta san abin da ya danne wannan soyayyar ba.

Tasleem ta amsa sallamarsa ciki ciki yayinda Futuha ta saki fuska sosai aka gaisa sannan ya dubi Humaira da shanyayyun idanunsa bayan ya cire gilashin.

"Boddo, barka da yamma."

Ya fadi yana mai ɗan dunƙule hannu da ɗan ranƙwafar da kai kaɗan tamkar wani basarake. Nan fa gaba ɗaya idanun ya koma kansu ana ganin ikon Allah.

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645



Ba ta ce uffan ba sai idanuwanta da ta sauke a cikin nasa. Ya ji kallon har a ƙasan ransa.

"Sauri fa muke yi." Tasleem ta furta cikin ɗaure fuska, gaba ɗaya wani irin mugun kishi ke cin zuciyarta. Fadeel bai ko kalle ta ba ya dubi Futuha.

"My sis, ko za ki ban aron ƙanwartaki for just 5mins?"

Murmushin da bai kai zuci ba Futuha ta yi.

"Ba ka da damuwa. Humaira jeki."

Humaira da ke jin kamar ta shaƙo wuyan Fadeel amma sai ta kasa yi mishi musu ta bi bayansa sadda ya yi gaba zuwa inda ya ajiye motarsa. A jikin motar suka tsaya su na hangen su Futuha da ke hira sai ko Tasleem da ta zubamusu idanu tamkar makauniyar da ta samu ido.

"Ka kirani kuma sauri muke za mu tafi."

Ya ji babu dadi daga yanayin muryar da ta yi mishi magana, ya dai daure ya haɗiye kamar koyaushe.

"Humaira kina addu'a sosai kuwa? Kina nafilfiloli da sallar dare? Kina mayar da hankali wajen yawan karatun Alkur'ani?"

Ta yi shiru kamar ruwa ya cinye ta, ta sani tana sallolinta biyar akan lokaci, tana kuma addu'a daidai gwargwadon yinta, amma yawan karatun Alkur'ani da kuma sallolin dare da ma nafila ba za ta iya buɗe baki ta ce mishi aa a kansu ba, kawai sai ta ji hakan ya yi mata nauyi a saman harshenta.

Ya tsinci amsoshin tambayarsa daga shirunta, don haka ya cigaba da magana a nutse ba tare da ya dauke idanu daga saman fuskarta ba.

"Salollin farillah wajibi ne Humaira, amma su Nafiloli neman ƙarin lada ne da kusanci ga Ubangiji. Za su buɗemaki ƙofofin rahma wadanda ba ki taɓa zato ba. Hakanan shi kansa karatun Alkur'ani, yawan tilawarsa da yin azkar safe da yamma zai ba ki kariya daga shaiɗanu da ma jinnu. Babu wani ko wata ko kuma wani abun da zai cutar da ke. Ina roƙonki ki yawaita addu'a, ina kuma ba ki shawarar yawan hailala, istigfari da salatin Annabinmu s.a.w. Ki ɗauka tamkar wani ɗan uwa ne gareki na jini yake ba ki wannan shawarar. Kin yarda kin amince za ki amfani da ita?"

Ba ta taɓa jin wani irin sanyi da nutsuwa tattare da kasancewarta da Fadeel ba sai a yau kuma a yanzun da yake kwararo mata waɗannan shawarwarin. Sai gaba daya ya tuno mata da Kawunta da ma Dada, ta tuna da kalar rayuwarta a Nijar, koda wasa idan ta idar da sallah, Dada ba ta barinta ta bar saman darduma sai ta yi nafila ta kuma tsaya ta ga ba ta yi wasa da addu'a ba, hakanan tilawar Alkur'ani, duk juma'a Kawunsu na tattara su har yaransa su yi tilawa, kowacce ta biya inda ta iya. Shaiɗan kwarai ya yi tasiri a zuciyarta da har ya sanya ta yi watsi da dukkan wannan, ta zama daga ta idar da sallar asuba sai bacci ba kamar a farkon zuwanta Kano ba da ma rayuwarta a Nijar inda koda wasa ba ta isa ta koma shimfaɗarta ba har sai rana ta fito bisa koyarwar Dada. A farko tana yi daga baya duk ta watsar. Ummita duk ta fi wannan kokarin. Ita kuwa kasala ya mata yawa.

"Kinji? Please."

Ya kara nanatawa. Ta dube shi sai ta yi murmushin da rabon da ya gan shi saman fuskarta har ya mance. Ta gyada mishi kai.

"Naji, nagode sosai da tunatarwa kuma zan kiyaye in sha Allah."

Ai sai ya ji tamkar an jefa shi wata duniyar ta nishadi da farin ciki, sai kawai ya rasa me zai ce ban da leɓe da ya ɗan lasa yana maida mata martanin murmushin. Ƙarar hon da aka danna da ƙarfi ya sanya suka dubi wajen, har ga Allah shi Fadeel ya ma mance adadin mintocin da aka yi mishi alfarmarsa, balle kuma Humaira da ta lula tunanin sakancin da take yi da addu'a tun zuwanta garin. Tasleem ce da wannan aikin ranta a mugun ɓace.

"Nagode, kije suna jiranki. Sai mun yi waya ko?"

Ta ji tamkar ta ce eh, sai kuma ta fasa ta juya kawai ta kama tafiya, ya bita da kallo sai kuma ya buɗe motarsa ya shiga, ya sani Abba ba ya nan balle ya shiga su gaisa. Don haka ya yi ribas aka buɗe gate ya fice. Itama tana shiga gaban motar kusa da direba, direban ya ja suna ɗagawa juna hannu ita da Raihana.

Tasleem da Futuha a bayan motar zaune sai yare suke yi. Ita kuwa duk ta tsargu amma ta haɗiye ɓacin ranta.

Tasleem ke mitar dole ne ma Humaira ta rabu da Fadeel tunda har ita ba ta same shi ba to kowa ma ya rasa. Yayinda Futuha ta ce ta kwantar da hankalinta soyayyar babu inda za ta kai. Haka suka yi ta gulmar Humaira ba tare da ta tsinci ko harafi ba. Ba ta da haɗi da buzaye balle ta fahimci akan abin da suke tattaunawarsu.

Har aka sauke Tasleem, ba ta da walwala, ganin haka itama Humaira ta ja jikinta ko ki gaida gida ba ta ce mata ba.

A gidan Futuha, ɗakin dai da ta taɓa sauka wannan karon ma shi ne ya kasance masaukinta. Ta ajiye jakar kayanta ta faɗa ta ɗauro alwala ganin ana dab da kiran sallar magriba, sai a lokacin ta jawo waya ta kira yar uwarta Ummita. Suka ɗan taɓa hira don ta ƙara kwantar mata da hankali, cikin ikon Allah ma sai ta ga ko a muryarta babu wata damuwa. Koda ta ajiye ta kara tsunduma da tunanin Fadeel, wai me ya yi mata ne ma da har ta

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment