Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta koma mata Mamin da ta fara cin karo da ita a ranar farko na zuwanta gidan. Kirjin Humaira ya hau dukan tara-tara, ta runtse idanu saboda ta gama hasaso abin da zai afku, wato mari za ta sha a wajen Mami, sai dai ga mamakinta ta ji akalar faɗan sam ba a kanta yake ba, su Tasleem ta shiga yiwa tamkar za ta ari baki.

"Ashe rashin mutuncin naku ya kai har haka? Raini ne wannan ku ka yimin ko mene? Ban hana ɗayanku yiwa Humaira maganar abin da ya faru ba? Ina ce har ɗaki ke Futuha kin biyo ni akan sai an ɗauki mataki na ba ki saƙo ga ƴan uwanki cewar na kashe maganar kada wanda ya tayar? Oh saboda ku nunamin ni banza ce wurinku, hukuncina ma na banza ne shi ne dalilinku na yin watsi da zancena a kwandon shara ko?! Toh wallahi ku fita idona tun wuri, kuma daga rana irin ta yau ku ka ƙara tada wannan batu sai na saɓamaku kamanni."

Tana kai wa nan ta ja hannun Humaira zuwa ɗakinta. Ta bar yarannata a tsaye tamkar su haɗiyi zuciya su mutu don haushi, Yassar ne ya soma jan wani dogon tsaki kafin ya sa kai ya bar falon, Dawud ya mara mishi baya. Tasleem kuwa ƙwafa ta yi.

"Innalillahi, ke Futuha na soma tsoro, na yarda dagaske ne da ake cewa ƴan ƙasarsu na da asirai, anya wannan shu'umar yarinyar da Kawunta hakanan suka  bar mana uwa? Anya ba sai da suka shuka tsiyarsu sannan ta dawo wajenmu ba?"

Futuha da ta kasa magana kawai sai ta ja tsakin itama ta ɗauki wayarta ta wuce sashen Anna idanunta cike da kwallar baƙin ciki.

***
A gefen Mami kuwa, su na shiga ɗakinta ta rungume hannuwanta a kirji ta daure fuska tamau har sai da Humaira ta sha jinin jikinta.

"Zauna." Ba musu ta zauna a saman kafet, ita kuwa ta hakimce a gefen gado.

"Na tsawatarwa yarannan saboda na riga da nasan takun saƙar da ke tsakaninku, ba na son a samu fuskar da za su ƙara ɗora maki karan tsana a matsayinki na yar uwarsu ta jini. Wannan ɗin ma da suke gwada maki fatana su daina na kashe shi gaba ɗaya. Amma meyasa haka Humaira? Har yanzun ina kokwanto akan kin aikata wannan laifin na ɗaukar kudi a ɗakina, amma idan  na tuna ganin da na yiwa kuɗin a cikin kayanki sai zuciyata ta tsinke. Ki faɗamin iyakar gaskiyarki, kamar yanda idan na ci karo da ɗaya cikin su Tasleem sun aikatamin laifi zan hukunta su, kema matuƙar da zuciya ɗaya nake zaune da ke ya zama wajibi na dauki mataki idan kin yi ba daidai ba."

Humaira ta ja majina tana kallon Mami. Girgiza kai ta soma cikin muryar kuka ta ke magana.

"Wallahi Mami, Allah ɗaya, ba zan yi wasa da Ubangijina wurin yi maki ƙarya ba, ban taɓa ɗaukar ko abin sakacen haƙori a ɗakinki ba tare da izninki ba ballantana kuma kudin da ba nawa ba. Mene ne bakya kokarin yimin a gidannan da zan yi maki sakayya da hakan? Kina yimin kyautatawar da ko na rayu da mahaifiyata abin da za ta yimin kenan. Toh a wane dalili zan zama butulu har na ɗauka daga asusunki? Mami wallahi ban ɗauka ba, ba ni kuma da masaniyar yanda aka yi kudin suka je cikin kayana, nidai na san na maki gyaran ɗaki, na kuma adana su a inda na gansu, na fita zuwa gidan Anti Laila."

Mami ta yi shiru tana nazarinta, duk kushen mai kushe ba zai taɓa zama da Humaira ya ji ta masa karya ko sau ɗaya ba. Toh wannan dabi'a ce ta mahaifiyarta, ta sani sarai mahaifiyar Humaira haka take da faɗar gaskiya. Ta san kuma ko a gaban Abban maganar ba za ta chanja zani ba. Sai ta yi nufin kasheta a yanzu ta hanyar numfasawa ta dafa kan Humairar cikin taushin murya ta ce.

"Ya isa hakanan, bari kukan kar ya ja maki ciwon kai. Na yarda dake ai dama, sai dai kin san kudi ba zai kai kansa cikin kayanki ba ko? Koda ace ba ke kika kai ba akwai yadda aka haihu a ragaya, kin ga kuwa dole na bincika matsayina na matar gida ko?"

Humaira ta gyaɗa kai har sannan tana sauke hardadden numfashi irin na wanda ya ci kuka ya ƙoshi. Mami ta dora da fadin.

"Toh don haka kar ki fahimce ni baibai don na tuhumeki, ya zama dole na aikata hakan ne ko don sauke hakki, yanzu kuma da ya kasance ba ke ba ce, zan bincika a sannu gaskiya za ta yi halinta. Tashi ki je ki ci abinci ki huta."

Humaira ta gyada kai kawai ta mike ta fita. Har sannan jikinta bai bar ɓari ba, sharri ya fi komai ɗaga mata hankali, ta tsani sharri, ta kuma ci alwashin ita kanta za ta dage da addu'a har sai gaskiya ta yi halinta don a yanzu kam ba ta da amsar ba su Tasleem sai lokacin da komai zai bayyana muraran.

A can ɗaki ma Ummita ta tarar tana nata hawayen, sai ya zamana ita ce mamai rarrashin Ummitan da nuna mata ai Mami ta fahimce ta. Ummita ta labarta mata yadda komai ya faru. Ta kara da fadin.

"Ba ni da tabbaci akan ko su Tasleem ne da aikata hakan, amma shakka babu ina zarginsu."

Murmushi Humaira ta yi.

"Kar ki damu yar uwa, idan ma su ne ina mai tabbatar maki wataran gaskiya za ta bayyana."

Daga haka suka bar zancen, koda Abba ya zo, babu wanda ya tunkareshi da zancen don ba karamin gargadi da jan kunne Mami ta yi musu ba, koda Anna ta hau faɗa, sai Mami ta sanyayar mata da jiki da faɗin abin da ta fi tunanin akan sharrin da aka yiwa Humairar. Dole itama Anna ta lallaɓa su akan zanceya mutu. Daga ranar kuwa ba a kara tayarwa ba kuma basu fasa kiran Humaira da wannan sabon suna na ɓarauniya da suka laƙaba mata ba. Wanda hakan ya fi komai yi mata zafi, duk kuwa da Mami ta tsawatar amma a fakaice a bayan idon Mamin ba sa fasa faɗi.

***
WATA BIYU BAYAN HAKA...

Ranar ta kasance yammacin Asabar, gaba ɗaya ahalin gidan su na nan idan ka cire Abba wanda ya fita zuwa kasuwa tare da Dawud. Fuskar Mami a kallo daya za ka shaida tana cikin farin ciki. Su Tasleem dai murnarsu ba yabo ba fallasa. Humaira kuwa da Ummita aiki suke tare da Mami ba kama hannun yaro, Raihana na can ɓangaren yayannasu tana aikin gyara bisa dole don ba yadda za ta kaucewa umarnin Mami, sai dai rabin aikin tana yi ne amma hankalinta na ga chatting din da take yi da sabon saurayinta wanda ya kasance abokin yayan ƙawarta.
Humaira ta zage damtse wurin yin kayan snacks yayinda Mami da Ladidi su ke aikin girka masa dambun shinkafa da kuma kunun aya, kamar dai yanda ya buƙata. Sun kammala da wuri suka jera komai a saman tebur, Humaira a gajiye ta nufi hanyar ɗakinsu da zummar watsawa jikinta ruwa adalilin zafin da ke tasomata, Mami ta dakatar da ita ta hanyar kiranta. Juyowa ta yi gami da amsawa.

"Maza je dakin Yayanki ki dubamin waccan mashiriciyar ko ta kammala gyaran nan, idan ta kammala ki dawo ga charcoal ki kunna a sanya turaren wuta."

Ta amsa da toh sannan ta juya cikin bin umarnin Mamin. Tana zuwa daidai kofar dakin Yaya Mubarak ta ji muryar namiji kamar ta waya ya na fadin.

"Um um sweetheart, ban gaji da ganin su ba, ni da ace za ki ɗan buɗemin ko saman ne kaɗai na kalla zai taimakamin ya magancemin wani abin. Please taimakamin kin ji? Gaba ɗaya ta miƙe wallahi."

Humaira ta zaro ido, sam ba ta fahimci komai ba, ta na shirin faɗawa ɗakin don ta ga meke gudana ta tsinkayi muryar Raihana na amsawa da wata murya tamkar ba nata ba tana wata iriyar shagwaɓa.

"Um um Baby, ba zan iya buɗemaka ba ina jin kunya."

"Toh naji, ki yimin hotonsu na miki alkawari ina kalla zan goge, nima zan aikomaki da hotona nikam ko ace ba ki goge ba ba zan damu ba saboda ina maki son da nake jin cewa komai na jikina mallakinki ne koda ba mu yi aure ba. Uhum?"

Humaira ta dafe kirji, yanzu kam ta fahimta, ta gane komai. Nan da nan ta nemi gajiyar da ke ɗibanta tana tafiyar rangaji ta rasa, da wani irin azama ta daga labulen dakin ta fada ba ta ko tuna da sallama ba. Raihana da ke fuskantar madubin dakin rike da waya tana videocall da wanda ta kira Baby, ta hango Humaira ta cikin madubi, ba ta san lokacin da ta kashe kiran gaba daya ba gami da saurin ajiye wayar saman madubi. Cikin rawar baki da danne firgicin da ta shiga na irin kallon zargin da Humaira ke watsa mata ta ja guntun tsaki tana kama gefen bedsheet wanda tuni ta kammala gyaransa amma ta hau kara cusawa.

"Ke kuma Malama kawai sai ki faɗomin haka babu sallama babu komai?"

Humaira ta karasa, ita ban da haushin Raihana da ta ji, har da wani irin bakin ciki da tsanar saurayin da Raihanan ta yi waya da shi ta ji. Ta yarda ba su ga maciji da yan uwanta, amma fa tana kaunarsu kuma tana ji a jikinta sai inda karfinta ya kare matukar ta ga ɗayansu zai cutu. Don haka tana zuwa saitin Raihana ta fizgo hannunta suka kalli juna, Raihana har sai da ta yi taga-taga za ta fadi kafin ta warce hannunta a tsorace, da karfi ta ce.

"Ke kuma Malama wai mene haka? Me na yi maki za ki nunamin hauka?"

Ta fadi ne cike da karfin hali domin a tsorace take, tana gudun ace aljanun Humairar ce suka tashi. Humaira wacce idanunta har sun rine tsabar bacin rai ta kalleta sosai.

"Raihana kina da hankali kuwa? Kin san me kike shirin aikatawa kanki? Ɓangare masu muhimmanci da girma a jikinki wani jakin banza ya ke so ki tura masa? Kina hauka ne? Wannan saurayi ne da za ki kula? Toh wallahi muddin kika yarda kika aikamasa kin gama cutar da kanki har abada, balle kuma akai ga ya nemi ku hadu da shi a waje. Ina iliminki ya tafi? So ba hauka ba ne ki bude idanuwanki ki fidda baragurbi cikin rayuwarki."

Raihana da tun da ta fahimci dagasken Humaira ta ji dukkan hirarsu sai ta hau borin kunya ga zufa na yankowa saman goshinta har yana jiƙa sumar dake kwance a wurin.

"Me kike nufi? Ni ba ni da hankali ne da zan tura masa? Ko kin dauka shashasha ce ni? Toh ni nasan yanda nake tafiyar da ire-irensu don haka ki rabu da ni. Wannan rayuwata ce. Zan gudanar da ita ne yanda na so. Bai shafeki ba."

Humaira ta yi shiru, can ta nisa za ta kara magana wayar Raihanan ya hau kara, aikuwa da azama ta nufi wayar har tana ture Raihana. Ɗagawa ta yi ta sa a kunne, Raihana na son dakatar da ita amma tana tsoron kar ta sha duka a hannunta.

"Sweetheart na ji shiru, muna waya..."

"Ba ita ba ce, wannan yayarta ce. Zan kuma yi maka gargadi da babbar murya. Wallahi wallahi ka kara gangancin neman yar uwata da tura maka wani hoto na sassan jikinta sai na nunamaka ba kowace mace ake taɓawa ba a sha ba. Sai ka raina kanka. Banza dan akuya kawai! Tirr da matasa irinku wadanda ba su ajiye komai a cikinsu ba sai tsabar iskanci da baɗala. Mu zuba ni da kai mafashi ya fasa!"

Ba ta saurari me zai ce ba ta datse kiran ta wurgawa Raihana wayar tana jifanta da muguwar harara, Raihana dai kasancewar ta yi amannar wannan jinnun Humairar ne ke magana ba ita ba, ta kasa kataɓus sai rawar jiki tana ji kamar ta saki fitsari a gefe guda tana jin bacin rai da tsanar shiga hanci da kudundunen da take mata amma ba dama ta yi magana, ta kuma sa a rai za ta yi duk yadda za ta iya ta ga ta ba shi hakuri kar ya kai zancen Humaira zuci.

"Idan kin kammala wayar ashararancin sai ki yi sauri ki kammala aikin Mami na jira. Shashasha da ba ta san ciwon kanta ba."

Daga haka Humaira ta ja tsaki ta fice cikin zafin rai. Wayar Raihana na ta ƙara amma ta kasa ɗagawa don gani take yi da zarar ta ɗaga aljanun Humaira za su isar mata da saƙo ta kuma dawowa, wannan karon kam ta sani lugudar ta za ta yi mata. Hawaye na zubomata tana ci gaba da gyaran dakin, hawayen na bakin cikin abin da Humaira ta yi mata ne, tun da take samari a duniya ba ta taɓa yin wanda har a zuciya ta ji tana mishi son aure ba irin Musaddam, yanzu ga shi nan ta ɓata mata shirinta. Tana mishi so da zuciya daya wanda take jin ko mene ne za ta iya yi a kansa. Don haka a gaggauce ta share dakin ta fice zuwa bangaren Anna domin ta samu damar ba shi hakuri sosai.
Ai kuwa duk kalar hakuri da karyar taɓin hankalin da ta dorawa Humaira duk domin ya aminta da ita ya kasa, cewa ya yi shi din son da take mishi bai je ko'ina ba tunda har za ta bari wani ya ji sirrinsu. Raihana kamar ta mutu don bakin ciki, ta tsinewa Humaira ya fi a ƙirga.

Ita kuwa Humaira umarnin Mami ta cika ta sanya turaren wuta a dakin ta fice nasu dakin. Koda Ummita ta nemi sanin abin da ya jefa ta cikin ƙunci, cewa ta yi babu komai. Har ta yi wanka ta shirya ba ta cikin walwala.

Misalin karfe takwas da mintoci Mubarak ya iso gidan. Su Muhsin suka cika gidan da Oyoyo, Tasleem su ma duk yanda su ke ganin yayannasu da shige musu hanci da kudundune sun yi murna da ganinsa. Humaira na gefe tana murmushi ba ta karasa ba tana karemishi kallo. Shi kam kammaninsa da Abba har ta ɓaci, shima dai ba ya kama da Mami, sai ko baƙi da laushin gashi irin na yan uwansa da ya dauko. Kansa cike taf da suma ya tara. Bayan ya zauna ganin Ummita ta karasa ta gaida shi ya amsa cikin sakin fuska ne ya sa itama karasawa su gaisa. Ya nunata da yatsa ya yi shiru alamar dai so yake ya tuno wani abin. Can kuwa ya ce.

"Humaira, right?"

Ta dai fahimci so yake ya tabbatar ko haka sunan ya ke sai ta gyada kai. Su Tasleem suka kwashe da dariya, ya tambayi dalili suka amsa da ba komai. Mami ta fito fuskarta cike da fara'a, ganin mahaifiyarsa ya mike tsam ya karasa ya dan rungumo kafaɗarta, ta dan tureshi tana murmushi.

"Ba ka girma ko?"

Ya kuwa kara marairaicewa.

"Girma fa kika ce Mami, yaushe rabonki da ni don Allah?"

Har lokacin murmushin take yi ta amsa.

"Amma ai ana waya da videocall ko?"

Da wasa ya sake ta ya juya.

"Shikenan bari na koma inda na fito tunda kin ƙoshi da ganina."

Da sauri ta riƙo rigarsa har duka falon aka dara. Ya ja hannunta suka nufi bangaren Abba su na hira.

Abba ya yi murna da ganin ɗan nasa, ya kasa rufe baki. Nan suka hau taɓa hira karshe kuma Abban ya ce ya je ya kimtsa ya ci abinci tukunna. Da wannan ya mike ya fita, daga uwa har uban suka zuba mishi ido cike da kauna kowannensu kuma da abin da yake ayyanawa a ƙasan rai.

***
Zaune yake a babban falon dake cikin Airport din Abuja, ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa mai cike da gargasa ya fi a ƙirga, ya maida duba saman wayarsa yana latsawa. Cikin sa'a kuwa ya ji muryar ma'aikaciyar ya karaɗe wurin inda take umartar fasinjojin da za su je Kano akan su nufi ciki. Ya mike kuwa don dama abin da ya zaunar da shi kenan. Hannunsa ɗaya riƙe da trolley ɗinsa yana ja, tafiya yake da sassarfa. Bayan komai ya kammalu jirginsu ya ɗaga. Isar su keda wuya, ya yiwa abokinnasa IBB GUSAU waya. Kafin ya kai ga magana ya ji saukar muryarsa daga gefe.

"Barka da zuwa."

Juyawa ya yi yana dubanshi da idanunsa dake ɓoye cikin wani arnen baƙin gilashi, sai kuma ya ja guntun tsaki yana ɗan murmushi, lokaci guda ya ba shi hannu suka yi musabaha kafin su rungume juna suna cike da farin ciki. Bayan sun saki juna da mamaki ya ga idanun Ibb sun kaɗa, nan da nan ya daure fuska.

"Ok, hakan na nufin ba ka yi murnar ganina ba kenan na koma inda na fito ko?"

Girgiza kai Ibb ya yi ya sa hannu yana karɓar trolley dinsa yana fadin.

"Hakan ba zai taɓa faruwa ba, in sha Allahu ka dawo kenan. Tafiyar kuma daga ni har Alhaji ba za mu ƙara bari ka yi irinta ba. Shekarun da ka yi sun isa hakanan."

Ya shafi sumar kansa bai ce komai ba ban da baki da ya ɗan taɓe ya yi gaba kai kace ya san inda mazaunin motar amininnasa ya ke. Ibb da murmushi ya mara mishi baya. Suka jera su na gifta filin wurin, Ibb ba gajere ba ne, amma fa duk tsawonsa bai kama ƙafar abokinnasa ba, kusan su biyun duka sai ka rantse ba su ne suka gama yiwa juna murmushi da runguma ba, tafe suke su na kallon hanya kai ka ce ba su san juna ba, duk inda suka gifta sai an bi su da kallo, ƴan matan dake wurin kuwa ji suke inama inama, inama za su yi nasarar samun sa'a a cikinsu ɗaya ya yaba, da sun tabbata masu sa'a. Shi yana sanye da ƙananun kaya yayin da Ibb ke sanye cikin manyan kaya dinkin babbar riga har da hula kai kace wani Ango.

"Ina ka nufa?" Ya yi tambayar fuska a haɗe a sadda Ibb ya murza sitiyari ya nufi gate din Airport din, shi ma ba tare da ya kalle shi ba ya amsa.

"Ka fi kowa sanin inda ya dace mu soma manufa. Tushiya masomin dawa."

Girgiza kai ya yi.

"No Ibb, i am not ready for it, muje ka kai ni hotel. Hakan na fi buƙata. Please."

Ba musu Ibb Gusau ya amsa da Alright, ba ya so fadi tashin da ya jima su na yi da Alhaji ya tashi a tutar wofi, ai an yi mai wuyar da suka samu ya dawo garin. Don haka kai tsaye Bristol Hotel ya kai shi ya kama mishi masauki, da wani irin walwala da annuri dauke saman fuskarsa ya fito ya rabu da shi ya kama hanya don ya je ya ba Alhaji kyakkyawan albishir. Lallai ya san da zuwan ɗan nasa, amma bai taɓa kawo wa a rana irin ta yau ba da ake shagalin bikin ƙaninsa mafi soyuwa ba a rai.

08

Kasancewar gidan cike yake da jama'a ƴan uwa, makwafta har ma da abokan arziki ne ya sanya Ibb zagayawa ta ɓangaren Alhajin ya shiga ainahin falonsa na karɓar baƙi. Kamar yanda ya yi tsammanin hakan ya tarar, wato dai Alhajin ba shi ɗaya ba ne a falon, yana tare da babban yayansa Baffa Gidado sai ɗan gidan Baffa Gidadon, Harɗo. Sai ko ƙannensa guda biyu dake zaune  su ma a gefe ana ɗan taɓa hira, kallo ɗaya za ka yiwa fuskokinsu ka fahimci su na cikin annashuwa. Sallamarsa ce ta katse hirar tasu wadda ke gudana da harshen fulatanci, suka dube shi gaba daya, ya karaso yana ƙara miƙa gaisuwa a karo na biyu domin dazun daga gidan ya fita. Alhaji ya amsa gaisuwar yana bin fuskar Ibb da kallo ganin yadda yake wata irin fara'a na musamman wadda rabonsa da ganin kwatankwacinta tun a baya kafin afkuwar wasu lamura marasa daɗi. Ganin bakin Ibb na ta motsi amma ya kasa magana ya sanya Alhaji miƙewa tsaye wannan karon kirjinsa bugu yake da sauri-sauri.

"Muje." Shi ne kawai abin da Alhajin yace, aikuwa kamar jira yake har da tuntuɓe a kokarinsa na bin bayan shi. Wata ƙofa suka bi wacce kai tsaye main parlour din Alhajin na cikin gidan suka faɗa. Ko zama Alhaji ya kasa hakurin yi su na karasawa tsakiya ya juyo gaba ɗayansa.

"Ibrahim, ya ake ciki? Meke faruwa?"

Madadin ya amsa sai kawai ya rungume Alhajin kafin ya sake shi yana dariya.

"Mafarkinka ya tabbata zahiri Alhaji."

Alhaji hannunsa har rawa yake ya kama kafaɗun Ibb har idanunsa sun cicciko da kwalla.

"Ya..ya..ya..da..wo?"

Ya yi maganar da rawar murya, jinjina kai Ibb kafin ya amsa.

"Eh, FADEEL ya dawo."

Alhaji ya sauke nannauyan ajiyar zuciya.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah. Yana ina yanzu? Muje ka kai ni na gansa."

Ibb zai musa amma babu dama domin dagasken dai ba abin da Alhaji zai saurara. Don haka sai kawai ya juya, Alhaji biye da shi suka fito. A farfajiyar gidan suka yi kiciɓus da Ango Fu'ad wanda shigowarsa gidan kenan daga Hotel din da abokan karatunsa suka sauka. Ya karasa ganin irin rawar jikin da Alhajinsu ke yi, ga Ibb na kokarin buɗe mota.

"Alhaji, fita za ku yi ne?"

Alhaji ya dafa kafaɗarsa fuska a sake ya ce.

"Maza shiga mota." Ba musu ya zagaya ya shiga har sannan fuskarsa dauke da mamaki, ya kuma kasa tambaya. Ibb bai ko hana Alhaji wannan yunƙuri ba don ya sani Fadeel zai yi farin ciki kwarai da ganin ƙaninnasa.

***
  Ya yi wanka ya shirya tsaf cikin riga body hug fara ƙal sai blue jeans. Yana zaune yana kurɓar ruwan shayin da aka kawo mishi, hankalinsa kaf yana wajen Mahaifinnasa, wata zuciyar na ce mishi ya je ya gan shi, wata kuma na kwaɓarsa. A hankali ya ajiye mug din dake hannunsa ya jingina kai jikin kujerar yana mai lumshe idanunsa. Dogayen gashin idanun suka kwanta luf saman fatar wurin. Ji ya yi ana buga ƙofar, ya buɗe su kafin ya miƙe. Yana da tabbacin Ibb ne. Hakan yasa koda ya bude bai tsaya kallonsa ba ya juya ya koma cikin ɗakin gami da faɗin.

"Wato gadina ka koma kenan?"

"Muhammadu." Ya tsaya cak a tsakar ɗakin, kaf duniya mahaifinsa kaɗai ke kiransa da ainahin sunansa, da hanzari ya juyo, tuni lumsassun idanunsa sun kaɗa. Alhajin ya taho da sauri ya rungumeshi, shi kuwa ya tsaya kamar wanda aka dasa a wajen ya kasa motsi. Fu'ad da bai san wainar da ake toyawa ba sai yanzun, kawai kuka ya sanya tsabar murnar ganin yayannasa da ya nisanta da su saboda wasu dalilai. Ya karaso da sauri ya haɗa daga Alhajin har Fadeel ya rungume yana kuka. Duk jarumta irin ta Fadeel sai kawai ya ji hawayensa sun zubo. Suka saki juna Alhaji da kansa ya sa hannu yana share masa hawayen.

"Ashe da raina da lafiyata ban mutu ba zan ga wannan rana? Alhamdulillah."

Abin da Alhajin ya furta kenan. Fadeel ya yi murmushi da gefen kumatu yana dafa kafaɗar Fu'ad.

"Ango, har ka girma za ka yi aure."

Suka yi dariya har Ibb, Fu'ad kuwa yan sunkuyar da kansa gami da shafar ƙeya. Nan fa Alhaji ya matsa akan lallai sai ya tattara sun tafi gida da shi. Anan ne kuma ya tamke fuska kwarai, ya koma Fadeel ɗinsa na ainahi.

"Muddin tana gidan nan ba zan iya shiga ba. I am sorry Alhaji."

Jin haka Fu'ad da Alhaji suka kalli juna suka yi murmushi. Shi sai a lokacin ma ya ji nauyin Fu'ad din, wai uwarsa yake ikrarin ba zai shiga gidan idan tana ciki ba.

"Yaya Fadeel, Mama ba sa tare da Alhaji, tayi wani auren a garin Kogi. Sai dai ko Anti Amarya our new Mum."

Sai Fadeel ya kasa cewa komai, ya maida dubansa ga Alhajin, ya gyaɗa masa kai don ya ƙara tabbatar da abin da Fu'ad ya faɗi.

"Yanzun ka shirya bin mu?"

Ya jinjina kai yana murmushi. Ibb tuni ya soma haɗa mishi shirginsa. Fu'ad ya karɓi akwatin suka fito baki ɗaya, suka yi mota yayinda shi kuma Ibb ya tsaya a reception.

Isar su gidan kai tsaye suka nufi sittingroom wajen su Kawu Gidado, sai dai tuni sun fice masallaci gabatar da sallar La'asar. Koda dawowarsu ganin Fadeel gaba ɗaya dakin ya kaure da murna. Magana dai ta bazu a gidan Fadeel ya dawo, babban ɗa namiji a wurin maigidan. Nan fa mata gwaggonninsa ƴan

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment