Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai dawo ba?"

Yassar ya taɓe baki yana zura hannu a aljihun wandonsa.

"Mami ina magana ba ki amsamin ba, koda dai nasan wannan halin na Abba zai wahala ma ya siyamin. Amma fisabilillah ina ɗan jami'a ina kallon abokaina har ma da matan da na raina su a makaranta su na da motocin kansu ni kuwa ko keke Abba ya kasa siyamin saboda mammaƙo."

Ran Mami a ɓace ta dube shi.

"Yassar ka shiga taitayinka, mahaifin naka kake yiwa waɗannan kalaman marasa daɗi? Toh ya yi maku mammaƙon, kai ai namiji ne, namiji kuma da nema aka san shi. Guminsa ne ya gina wannan gidan, ya kuma mallaka mishi motocinsa, kai ma ka yi zuciya ka mayar da hankali a karatunka watarana ba Abbanku ba, da kanka sai ka siyawa kanka motar, ba na son shirme. Ni kiramin Yakubu a waya ka ce ya yi sauri ya ƙaraso, ina Humairar take ne..."

Ba ta ƙarasa zancen ba ta waiga, Humaira na tsaye a gefensu kasancewar su na magana ba su ko lura da ita ba. Itama ta yi shirinta tsaf cikin atamfarta koriya wacce tana ɗaya daga cikin ɗinkunan da aka yi mata. Ta yi kyau sosai, murmushi ta ɗan yiwa Mamin.

"Mami na fito ai."

Yassar ya ja tsaki ya bar wajen don takaicin Mamin da kuma na ganin Humairar da yake jin haushi da kishin tattalinta da iyayen nasu suke yi sai ka ce su ba ƴaƴa ba ne, Mami na kwala mishi kira amma bai ko waigo ba sai amsawar da ya yi da ƙarfi.

"Zan je na ɗau wayar ne na kiramaki Yakubun."

Daga haka ya ci gaba da tafiyarsa, Mami ta girgiza kai fuskarta ɗauke da matsanancin damuwa. Sai jikin Humaira ya yi sanyi, wannan kalar zamantakewar mutanen gidan na ba ta mamaki, ace ƴaƴa ba sa ganin iyayensu da gashi, kowace magana ta fito a bakinsu hakanan za su watsa musu ba tare da taunawa ba, toh wace riba ake samu a hakan? Ita tunda ta zo ma ban da Ummita da Raihana sai Muhsin masu ƙokarin zuwa islamiyya, ba ta ga wani cikin su Tasleem na zuwa ba. Bar su dai da yawon gidan ƙawaye a ɓoye Abban bai sani ba. Itama dai Raihanan ba zama take sosai ba amma takan tsaya har a biya karatu da ita,  wasu lokutan sai dai ta ji tana amsa wayar zasu haɗu da wani saurayin idan ta fita makaranta.
    A yanzu kuwa daga maganganun Mamin ta fahimci watakila Yassar kuɗi ya nema ko wani abin da bai samu ba ya faɗi abu game da Abban shi ne take goranta mishi.

"Muje Humaira, ya zo."

Ta amsa da toh ta bi bayan Mamin cike da jin tausayinta, kowace uwa na son ta ga nata na bin ta sau da ƙafa, amma Mami ba ta samu wannan biyayyar ba na yara. Daga manyan har ƙananan, koda dai ta ji Ummita na cewa shi dai babban ɗan nasu ya bambanta da sauran, kuma su na masifar shakkarsa, akwai abubuwa da dama wanda idan yana nan ba sa aikatawa. Ta ce daidai da hantarar da suke yi mata idan har yana nan ba sa yi.

Har dai suka soma tafiya a titi tunane-tunane take yi, hankalinta jiya bai kwanta ba sai da ta tsinkayi Tasleem na hira da Raihana su na tsokanar Futuha akan marin da ta sha har su na faɗin gobe ma ta ƙara. Daga baya dai ko don tana ɗakin ne sai suka juye harshe zuwa turanci, ta lura ba su fiye yin buzanci ba su kam, a yadda Ummita ta ce ma, ba komai suka iya faɗi a yaren ba, sun dai fi ganewa idan an musu magana ba su iya mayarwa yadda ya kamata ba. Wannan sai babban yayansu. Shi dai yana ji sosai.

Daidai wani babban gida motar ta tsaya, suka fito suka nufi ciki. Kyau da tsaruwar gidan har ya so ya kere na su. Da murmushi Mami ta dubi Humaira lokacin da suka shiga farfajiyar gidan.

"Gidan aminiyata kenan Hajiya Lubna, ita ce za ta kai ki wajen koyon girki. Ƙanwarta ke yi."

Humaira ta gyaɗa kai ranta ya yi fari sol, ta san dai Mamin ta ce ta shirya zasu je unguwa amma ba ta kawo a rai fitar ta shafe ta ba. Daidai za su shiga babban falon suka yi karo da ɗan Hajiya Lubna shi kuma zai fito, matashin saurayi mai jini a jika, ya sha ƙananun kaya abinsa ya yi tsaf. A fuska ba za ka kira shi da kyakkyawa ba sai dai hutu da jin dadi ya sa fatarsa murmurewa. Gaisawa ya ke da Mamin amma hankalinsa kacokam na ga Humaira wacce daga kallo ɗaya da ta yi mishi ta kauda kanta don ita kam a duniya ta tsani kallo. Mami na lura da yanayin kallon da yake jifan Humairar da shi, ita kanta bai mata ba don haka don ta katse shirun ta ce.
 
"Hajiyar dai na ciki ko? Don na san ta yanzu sai ta iya ficewa ta bar ni zaman jira."

Dariya ya ɗan yi yana shafo ƙeyarsa.

"Tana ciki Hajjaju. Ku shiga kafin na shigo."

Ta amsa mishi ta yi gaba Humaira ta bi bayanta da sauri har tana tuntuɓe saboda kallon da yake bin ta da shi. Mami ta kalleta kawai ta kauda kai ba ta ce uffan ba. A falon gidan suka iske ƴan mata da yara ana kallo ana hira, wuta tarr a gidan madadin gidansu wanda idan har ba wutar Nepa aka ci sa'a suka kawo da rana ba, zai yi wahala ka ga hasken fitila a gidan sai Magriba zuwa ƙarfe sha biyun dare.

Gaba ɗayansu suka gaida Mami, ta amsa. Ta dubi Humaira.

"Ki zauna ki jira ni bari na ƙarasa wajenta." Ta amsa da toh ta nemi wuri ta zauna. Ta lura gidan dai ƴan boko ne, ba su ko damu da ita ba sai mai aikin gidan da ta miƙe ta kawo mata ruwa da lemu ganin da ta yi tare suke da aminiyar uwar ɗakinta. Godiya ta yi mata amma ba ta sha ba, hankalinta kacokam na garesu, wani shiri suke kallo na india, sun maida hankalinsu kacokam. Itama sai nata hankalin ya tafi can. Ta shafe mintuna goma a nan tana jiran Mami, can sai ga wani ɗan yaro ya sauko daga benen da Mamin ta hau.

"Ki je ana kiranki a sama."

"Toh" Kawai ta ce ta miƙe ta nufi hanyar da yaron ya fito, kafin ta ƙarasa ta tsinkayi wata muryar babbar mace na faɗin.

"Ke dai ki bi a hankali, kar ki yi garaje kamar yadda ki ka so yi a wancan lokacin."

Sallamarta yasa suka kalli hanyar da sauri, ba ta lura da yanayinsu ba ta karasa ta durkusa gefe ta gaida matar wacce kamanninta sak da wannan matashin da suka gani ɗazun. Matar ta amsa mata fuska a sake.

"Ah Maryam, ki ce ɗiyar tamu kyakkyawa ce masha Allah. Humaira ko?"

Humaira ta gyaɗa kai tana sunkuyar da kai murmushi a saman leɓbanta.

"Masha Allah, Allah ya yi albarka kin ji? Allah ya gafartawa Hajiya Fatima, idan kika biyo halinta kin more. Mace mai hakuri da kawaici. Allah ya gafarta mata."

Ta ji wani sanyi a ranta, a duniya tana jin daɗin a yabi Mahaifiyarta. Ta amsa da amin ita da Mami.

Mamin ta dube ta.

"Toh Humaira, gobe idan Allah ya kaimu koda ba ni ba, sai ku zo da Ummita a kaiki gidan koyon girkin. Na faɗamaki ta gida ce, ƙanwar Hajiya Lubna ce. Sai ki mayar da hankali ga abin da ya kai ki. Nasan kina da fahimta da saurin ɗaukar abu, don Allah kar ki ba mu kunya kin ji ko?"

Ta amsa da toh Mami. Kafin Mami ta ɗora daga inda ta tsaya wannan saurayin na ɗazu ya hayo. Suka maida duba gareshi. Wani irin ajiysr zuciya ya sauke yana duban Humaira sannan ya maida kallonsa ga Mami.

"Ai na ɗauka har kun tafi."

Mamin ta ɗan yi murmushi kaɗan ta girgiza kai.

"Ina nan Kabeer, amma yanzun za mu tafi. Abban yara ya kusa komawa gida."

Ya karasa ya zauna. Hajiya Lubna nan da nan fuskarta ta sauya ganin kallon da yake jifan Humaira da shi. Mami ta dubi Humaira ta bata umarnin ta koma ƙasa ta yi jiranta za ta sauko su tafi. Daga fitarta shi ma ya miƙe caraf ya bi bayanta. Hajiya Lubna za ta yi magana, Mami da sauri ta hana ta ta hanyar ɗan dafe kafaɗarta. Dole ta fasa. Amma ta kudurce a ranta lallai za ta yiwa abin tufka don ita kam ɗiyar ubangidan mijinta take so ya aura, ta kuma lura da yadda yake bin Humaira kamar jela to akwai wata a ƙasa. Ƙwafa kawai ta yi ta watsar suka ɗora hirarsu daga inda suka tsaya.

A can kuwa Humaira duk ya takura mata, ita ba ta saba da wannan rayuwar ba. Kawai wani garjejan saurayi ya zauna yana jan ta da hira ba hadin uwa da uba, ita kam abin ya girmi kanta. Ta kula bai ko damu da jama'ar falon ba waɗanda su din ma kallonsu kawai suke jifa-jifa su na mayar da hankalinsu ga tv.  Tambayoyi yake mata iri-iri, amma ba ƴar Mami ce ke ba? Yaushe ki ka zo? Karatu  kike? Da dai sauransu ita dai eh ko aa kawai take ce mishi duk ta takura. Haka Mami da Hajiya Lubna suka sauko, ganinsu ya sa ya miƙe yana shafar ƙeya.

"Wai Kabeer ina aiken da na maka ne? Idan ba za ka je ba, ka fadamin na aiki Bala direba."

Hajiya Lubna ta faɗi rai bace tana watsa mishi harara, sarai ya gane manufarta, amma shi kam yana ji a ransa ko karatu Humaira take yi zai iya dakon jira ta kammala ya aure ta. Ya lura auren jari Hajiyartasa take so ya yi.

"Sorry Hajjaju, bari na tafi. Mami ku gaida gida, sai na tako har falonki na ƙara gaida ki."

Mamin ta yi dariya.

"Ai babu laifi Kabeer, ko da wacce ka zo ka shiryawa amsar da za ka samu."

Ganin ta ɗago shi ya fice yana ƴar dariya gami da faɗin.

"Na shirya Maminmu, amma dai ba zan ja baya ba."

Mamin ta ƙara darawa. Humaira ta miƙe suka kara yin sallama da Hajiya Lubna, har farfajiyar gidan ta rako su. Humaira dai har ta ɗan kwashe mintuna a mota ba su gama tsayuwarsu a bakin ƙofar falon su na tattaunawa ba, ba ta san me suke cewa ba dakyar dai Mamin ta taho ta shiga motar suka tafi.

***
 

05

Humaira ce zaune a falo da safe, yaran gidan duka sun fice makaranta kasancewar sun soma jarrabawar zango na uku (Raihana da Ummita kenan), a yadda Ummita ta ce mata, daga jarrabawar to aji na gaba za su je.
Kallon tashar Arewa24 take inda ake hasko wani wasan kwaikwayo na marigayi Ibro. Ta shagala gaba daya tana tuntsira dariya ta ji ɗif, wuta ta ɗauke. Guntun tsaki ta ja, ita kam ba ta san matsalar wuta a nijar ba domin koyaushe akwai. Ba ruwanka da tayar da janareto. Ganin haka kawai sai ta miƙe da zummar komawa ɗaki.

"Humaira."

Muryar Ladidi ta katse ta, ta juyo ta amsa. Tire ne a hannun Ladidin ta karaso gareta. Fuskarta duk ta yi narai-narai alamun roƙo.

"Ki taimakamin don Allah ki miƙa sashen Anna, kinga suyar agadar Mami nake kada ya ƙone. Kuma Annar za ta sha magungunanta ne lokaci na tafiya."

Kirjinta ya ɗan buga dam, ta kasa magana. Toh akan me za ta cewa Ladidin ba ta taɓa shiga sashin Anna ba? A ganinta hakan su ta shafa. Ganin yadda Ladidin ke magiya yasa ta karɓa, godiya ta yi mata ta koma kicin. Ita kuwa ɗan hanyar da take ganin su Muhsin na yawan zirga-zirga zuwa wajen Annar ta zubawa ido sannan ta sauke ajiyar zuciya ta nufi wajen. Anna ɗin ai mutum ce ba aljana ba balle ta illata ta, za ta je ta ga me zai faru idan ta yi karo da ita. Koro ta za ta yi daga ɗakin ko kuwa dai duka za ta yi mata. Da haka ta tunkari hanyar.

A hankali ta tura ƙofar ɗakin da sallama, jin shiru yasa ta maimaita. Wata murya ta amsa, ta tabbatar ba shakka muryar ta Anna ce. Shiga ta yi ta karasa ta ajiye saman ƙaramin tebur dake wurin. Anna dake zaune gefen gado ta soma magana tana laluben gilashinta.

"Ladidi sai yanzu ake kawomin abin karin? Yau me ya tsaida ki haka? Ina gilashina na jefa?"

Humaira ta hadiyi miyau, kenan dai Anna ba ta san ma wace tsugune a gabanta ba. Ta daure ta ce.

"Ina kwana. Ya karfin jiki?"

Jin  baƙuwar murya ya sa Anna saurin sanya medicated glass ɗinta wanda da shi ne ta ke gani sosai ba dishi-dishi ba. Yarinya budurwa ce durƙushe a gabanta, fara sol. Kanta duk da cewar akwai hula, sumarta ba ta ɓuya ba don hatta da goshi da bayan ƙeyarta sumar ce kwance. Ta ƙuramata idanu tana ƙokarin tuno inda ta san fuskar. Sai dai a ɗan lokacin ba ta ankare ba don ita shaf tuni ta mance da wata wai Humaira a gidan tunda ba su taɓa karo ba. Ba ta damu da shiga sashin ɗiyarta ba, ya fi rayuwa anan dai ɓangarenta.
Daidai lokacin Mami ta shigo ɗakin kamar wacce aka jefo, ta samu labari daga Ladidi cewar Humaira ta tura kai wa Annar kari. Shigowarta ya sa Anna mayar da dubanta gareta.

"Ina kika samu yarinya ha..."

Sauran kalaman Anna suka maƙale a fatar bakinta, shakka babu ta tuno komai. Ta tuna ashe akwai wani ran bayan jikokinta a gidan da aka ce tsatson Fatima ce. Ta tuna Humaira kamar yadda ta ji sunanta a bakin su Yassar masu yawon kawo ƙorafi a kan fifikon da Mami ke yi mata sama da su. Nan da nan ta haɗe girar sama da ta ƙasa. Daidai lokacin Humaira ta ƙara gaidata wannan karon muryarta har ɗan rawa yake. Ta nuna Humairar da yatsa idanunta akan Mami.

"Me wannan abar ta zo yi wurina? Me na faɗamaki? Ban ce maki ba na son ganin baragurbi  a wurina ba? Ke don uwaki wa ya ba ki iznin zuwa wurina, ko ni na haifi uwarki?!"

Maganar sosai ta daki Humaira, nan da nan idanunta suka cicciko da kwalla, uwarta kuma? Uwar dake kwance a kushewarta? Mene dalilin sanyo ta ciki? Ba ta jira umarnin Mami ba ta miƙe a zuciye ta kama hanyar fita daga ɗakin, Mami ta riƙe hannunta wannan ya dakatar da ita sai dai ba ta ko juyo ba. Daidai nan kuma hawayen suka sauka saman kuncinta. Da harshen buzanci Mamin ta yiwa Anna magana, Annar kuwa cikin harshen da Humairar za ta ji ta amsa a fusace cikin ɗaga murya.

"Au! Don na zage ta kike kirana marar adalci? Ni Maryama kike kallon idona ki ce ba na adalci? Toh anyi rashin adalcin. Idan maye ta manta ai uwar ɗa ba ta mance ba. Ke da kika ga za ki iya haɗiye duk baƙin cikin da kika risƙi kanki a baya, ki yi. Nikam ba da ni ba, kuma ke duk radda kika kuskure ki ka ƙara gangancin takowa ɗakin nan sai na sa jikokina sun nakastamin ke. Sauran yunwa kawai."

Humaira tuni ta janye hannunta a na Mami ta bar ɗakin da sauri.
Kai tsaye ɗakinsu ta nufa ta zube saman kafet ta shiga kuka kamar ranta zai fita. Ita fa duk abin da matar ta ce bai dame ta ba kamar sanya uwarta da ta yi a ciki. To me Mamarta ta yiwa Mamin da har Anna ke batun ba za ta mance ba? Wane irin zama suka yi a baya? Ita Mami da ma ƴan uwan Abba, sun yiwa Mahaifiyarta kyakkyawar shaida, amma me Anna ke nufi da kalamanta? Ko kuwa dai ita ke taya ɗiyarta kishin kamar yadda Ummita ta taɓa faɗi?

Ba ta ji shigowar Mami ɗakin ba sai ji ta yi an kama hannunta an ɗaga ta. Ta miƙe tsaye, Mami ta yi mata murmushi.

"Ki yi hakuri Humaira, kin san iyaye ne sai mun yi hakuri da su mu samu a rabu lafiya. Ki taya ni yi mata biyayya,  kar ki kara zuwa ɗakinta har sai don kanta ta nemi hakan wataran wanda in sha Allahu nake fatansa nan kusa. Kar ki sa komai a ranki, ki kuma shirya anjima da kaina zan kai ki gidan koyon girki. Ki cire komai a ranki ki mayar da hankali, ni kuma anan gida idan kin dawo zan dinga iyakar ƙokarina wurin ganin an samar maki dukkan kayan girkin da ki ka koyo a can ki yi a nan mu ci mu ɗanɗana, kin ga daga haka hannunki zai miƙa. Wataran sai a wayi gari kina odar biki da suna har ma da wuraren party ko? Kin zama Hajiya."

Zancen Mamin ya sanya ta murmushin da har wushiryarta ta bayyana. Mamin ma murmushin ta ƙara yi. Daga haka ta fice a ɗakin. Humaira tuni ta share batun Anna ta tattara ta watsar.

***
Sun je gidan Anti Laila ƙanwar Hajiya Lubna tare da Mami, ta ba da form bayan sun biya komai, Mami da kanta ta cikewa Humairar. Anan aka ajiye ranar litinin matsayin ranar da za ta fara zuwa koyon girkin. Daga nan suka yo gida ranta fari sol.

Kai tsaye ɗaki ta nufa hannunta riƙe da na Waleed wanda zuwa yanzu daga shi har Muhsin sun sake da ita,  fuskarta a sake, zuciyarta wasai. Ummita ce kaɗai zaune tana karatun jarrabawa, ganin haka Humaira ta dubi Waleed.

"Tafi wajen Muhsin ku yi wasa ka ga Adda Ummita karatu take yi. Anjima sai ka zo ka koyamin turanci ko?"

"Okay! Bye."

Itama ta amsa da bye din tana dariyarsa, ya dage a lallai zai koyamata turanci, haka za ta biye mishi tana ɗan tsintar wasu abubuwan da ya iya. Ummita ta kalle ta tana murmushi.

"Yau dai fara'arki ta musamman ce. Kada dai ki cemin har kin soma shiga aji?"

Dariya Humairar ta yi daidai sadda take zama a gefenta.

"Aa fa, amma an gama komai an biya, litinin zan soma zuwa."

"Kai naji dadi wallahi. Allah ya nuna mana."

Ta amsa da amin, ta mike ta hau cire kaya da zummar shiga wanka. Ta dai kula kamar Ummitan ranta a jagule ya ke, ba ta ce mata komai ba har ta shiga wanka ta fito. Anan kuma ta ga ta amsa waya ta yi jifa da wayar saman gado tana ɗan goge fuska. Jiki a sanyaye ta ƙarasa gareta ta zauna.

"Ummita, lafiya? Meyafaru?"

Ummita tana kallon littafin amma ta kasa karatun sai kawai ta girgiza kai tana shirin cewa ba komai amma tuni hawayenta ya zuba saman littafin. Humaira ta janye littafin.

"Don Allah meke faruwa? Anyi wani abu ne bayan fitar mu?"

Nan ma girgiza kan ta yi. Ganin haka sai kawai Humaira ta mike ta nufi sif dinta, har ta sanya kaya jiki a sanyaye Ummitan ba ta da niyyar cewa wani abu. Ganin haka sai ta ƙarasa wajenta karo na biyu.

"Na tambayeki mene ne kin kasa cewa komai, kuma kina kuka." Jin ta yi shiru ne yasa Humaira fadin.

"Toh bari na kira Mami mai yiwuwa ita za ki faɗamata."

Har ta miƙe da sauri Ummita ta riƙe hannunta. Suna haɗa idanu ta girgiza mata kai, itama Humaira tuni idanunta sun cicciko don a duniya ta tsani kukan mutum. Kuka ma irin na waɗanda  ta ke yiwa ƙauna domin Allah. Duk abin da ya shafi irin mutanen nan tana jin abin a ranta tamkar ita ya shafa.

"Kar ki je, zauna na faɗamaki." Ta koma ta zauna tana mai zuba mata ido bayan ta share kwallarta.

"Yayar Mamana ce ta kira ni daga Bichi, kwanakin nan duk sun takura akan lallai sai na fiddo miji na yi aure wai karatun ya isa hakanan. Su sam hankalinsu bai kwanta da zamana a gidannan ba. Ita Babbar yayar Mamana, Anti Maijidda cewa take yi wai har mafarke-mafarke take yi a kaina don haka za su yiwa Abba magana a dakatar da karatun nan, ida n ma aure ne dai a yimin. Ni kuwa na dage akan ba zan yi aure yanzu ba, na ce musu ko zance ba na yi, sun ce ai kuwa anan da Bichi ba zan rasa mijin aure cikin ƴan uwa ba, Anti Maijidda har cewa ta yi ga babban ɗanta Yusuf nan, wai ya kammala  gininsa za ta turo shi ya zo mu yi hira mu fahimci juna. Kin taɓa jin wannan irin abu don Allah Humaira? Duka-duka nawa nake da za su ce za su aurar da ni yanzu? Zangon karshe nake a Ss1 zan wuce Ss2, idan ma auren suke buri su ga na yi, ai sa bari dai shekaru biyun da suka ragemin a sakandire na kammala su. Haka kawai don wasu mafarke-mafarken da ba su da tabbas ku rushemin ginin rayuwata? Sun bi sun kafawa Mami karan tsana, ban san hawa ba ban san sauka ba, amma nima su na hantarata akan na mayar da ita tamkar uwar da ta haife ni, gani suke na fifita dangin Babana sama da su. Toh don Allah faɗamin, mutanen nan sai na je wurinsu duk shekara a can nake hutun dogon zango da ake ba mu na makaranta har ya ƙare, amma su ko sau ɗaya ba su taɓa zuwa garin nan da zummar ganina a gidan nan ba acewarsu su da Mami har abada don ba su yarda da zuciya ɗaya ta ke riƙe da ni ba. Akan Mami na sha duka a wajensu idan na je domin duk wanda ya aibata  ta zan buɗe baki nace sam ba haka take ba, to fa anan sai na ɗanɗana kudata. Yanzu wannan matsalar auren da ta taso ki faɗamin Humaira, ta ina zan kashe ta ba tare da na samu matsala da su ba, nikam wallahi gaba ɗaya kaina ya ƙulle."

Humaira ta sauke ajiyar zuciya.

"Wai Allah!" Shi ne abin da ta furta don ita komai ma ya tsaya mata cak, ta rasa me za ta cewa Ummita. Mamaki take yi na yadda suke yiwa Mami kallon baibai alhalin matarnan iyakar kokari tana yi a kansu, irin kokarin da ko mahaifansu na usuli sai haka. Can kuma ta dubi Ummita.

"Toh kodai ki yiwa Abba bayanin komai? Na tabbata zai fahimceki kuma ba zai rasa matakin ɗauka ba yadda zumuncinku ba zai taɓu ba."

Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce.

"Ko? Nima na yi wannan tunanin, wallahi maganganunsu ke hargitsa ni tun wancan satin su ke huran wuta, tun fa ina dannewa har suka soma sanya ni kuka. Amma hakan zan yi kawai, zan faɗawa Abba komai, ke nasan ma kai tsaye zai nemi Kakana wanda ya haifi Mama ya yi mishi magana. Shi kaɗai zai iya tsawatar musu, daman tsoro ne ya sa na kasa faɗa mishi, amma na tabbatar zai magancemin."

Humaira ta jinjina kai.

"Sai dai don Allah kar ki faɗawa Abba zargin da suke yiwa Mami."

Ummita ta kama baki.

"Rufamin asiri Humaira, dama me zai kai ni?"

Murmushi Humaira ta yi. Suka ɗan taɓa hira sannan ta kyale ta don ta yi karatu.

  Aikuwa a daren Ummita ta samu Abban ta zayyane mishi komai, ransa ya ɓaci. Ƙarshe dai ya ce ta tashi ta wuce zai san matakin da zai ɗauka. A ranar kashe wayarta ta yi ta kuma yi alƙawarin ba za ta kunna ba har sai komai ya wuce don ta tabbata zagi ne dai za ta sha a wurin su.

***
BAYAN WATA BIYU...

Gadan-gadan Humaira ta fara zuwa koyon girki, abin da ya burge su Abba da Mami bai wuce irin hazaƙarta ba na saurin ɗaukar abu. Ita kanta Anti Laila sosai take yabawa da Humairar. A farko-farko ne dai idan aka koyar da su ta zo gida ta yi sai ya kasance bai yi dadi ba ko gishiri ya yi yawa ko dai wani abin, har su Tasleem na ci don su yi mata dariya da kuma kushe. Har su na cewa Abba ya yi asarar kuɗinsa. Amma yanzu kam duk da su na kaucewa ba su son nunawa a fili yana musu dadi, to fa a ƙasan zuciyarsu su na son su ɗanɗana idan ta yi. Amma fa ana ci ana yamutse fuska ana nuna ba laifi ya ɗan yi dadi. Ita dai ba ta tanka musu tunda har Abba da Mami da Ummita su na yabon girkinta.

A farko direba ke kai

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment