Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kana nufin ka kira ta?"

Cikin ido Fadeel ya dube shi.

"Yes, mun yi waya, amma duka ba masu dadi ba ne."

Ya kora mishi bayanin duk abin da ya faru, Ibb ransa ya ɓaci.

"Unbelievable! Yanzu akan mace ne ka shiga wannan yanayin? Fadeel kai ne dagaske dai wanda na sani? Mutumin da gaisuwar kirki abu ne mai wuya a ganka kana yi da wacce ba muharramarka ba, kai ne yau da bakinka ka ke faɗin cin kashin da wata shashasha can take maka? Kuma har ka ke tolerating in the name of love? Is this love or madness?"

A fusace Fadeel ya soma magana, tun da Ibb ya jefi Humaira da kalmar shashasha ya ji ransa ya yi masifar zafi.

"Oho! Idan ma haukan ne naji ni na jefa kaina ai ba da sa hannunka ba ko? Ban damu da duk wani tunani da za ka yi ba. Ina sonta, ka zo gabana kana kiranta da shashasha ba zan iya jura ba Ibb! Ina haɗa ka da Allah, idan har ba goyamin baya za ka yi ba toh kada ka kara kuskuren zaginta a gabana. Kawai dai ina ji a jikina wataran za ta gane ni din masoyinta ne na gaskiya."

Yana kaiwa nan ya mike ya nufi hanyar ɗaki, Ibb kuwa baki a wangale yake binsa da kallo har ya ɓace masa. Meke damun Fadeel? Ya jefawa zuciyarsa tambaya, a take kuwa amsar ta zo masa, Soyayya ce. A fili ya ce.

"Idan kuwa har wannan ita ake kira da soyayya, ina nemawa kaina tsari da ita. Kai kuma Fadeel ina roƙon Allah ya yayemaka wannan haukan son."

Daga haka ya mike ya fita a dakin domin shi har ga Allah ba ya fatan wannan rashin hankalin da mace za ta zage shi ya kasa daukar mataki a kanta. Ko ƴar uban wace ce ba zai ƙara yi mata kallon wata abar so ba, ballantana har ta ci galabar yi mishi son ranta.

***
Humaira na  kwance a yammacin ranar juma'a ta ji ihun ƴan matan gidan ya karaɗe falo, ta mike zaune tana mutsistsiƙa idanu. Hayaniyar ta mene ne? Kafin bacci ya gama wartsake mata sai ga Ummita ta shiga fuska ba yabo ba fallasa.

"Wai hayaniyar me ake yi?" Fadin Humaira. Tsaki Ummita ta ja haɗi da taɓe baki.

"Aunty Jannat ce ta zo, kanwar Mami."

Humaira ta zaro ido, ba ta taba zama da ita ba amma ta sha jin labarinta a bakin Ummita na irin uƙubar da ta sha a wajenta sadda tana rayuwa a gidan.

"Dagaske? Ki ce mun shiga uku."

Ganin ruɗewae Humairar har ya so ya fi nata ne yasa ta dariyar dole wanda ba ta shirya masa ba.

"Ke da ba ki taɓa zama wuri guda da ita ba? Ba lallai ki fuskanci matsalar da na fuskanta ba ai."

Ita dai Humaira ta ji ne kawai ba don ya zauna a kwakwalwarta ba.

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*






Suna nan zaune Humaira na cewa  ita kam za ta so ganin ya wannan Jannat din take mai shegen son mulki sai ga Muhsin da Waleed sun faɗo ɗakin a  guje. Kira ne daga Mami akan su fito a gaisa da Jannat. Ummita ta dafe kirji, yayinda Humaira mikewa ta dube ta.

"Wai ya haka, kinsan fa yarannan akwai daukar zance yanzun sai su fasalta musu yanayinki."

Ummita sai ta maze ta mike. Suka kama hanyar falon, tun kafin ma su kai ga ƙarasa shiga ta hange ta. Kamanninta sak da Mahaifiyarsu wato Anna. Kusan har ta so ta fi Mamin hasken fata, siririya ce ba ta da tsawo duk kuwa da cewar tana daga zaune ne. Yaranta ƴan biyu tamkar an tsaga kara an karya, ba su wuce sa'o'in Muhsin ba. Wato shekaru goma a duniya. Riga da wando ne a jikinta sai abaya dake ajiye a hannun kujera wanda ga dukkan alamu cire ta ta yi. Gashinta ya sha kananun kalba an tufke a tsakiyar kan ya yi kamar ta sa ribos din acuci. Gaba daya iyalan Mami na falon ciki kuwa har da Anna wacce ba kasafai ta fiye fitowa ba. Humaira ita kanta sai da ta sha jinin jikinta ganin Anna a falon, sai da itama ta ji kamar ta ja hannun Ummitan su juya. Aikuwa su na ganinsu Anna ta tamke fuska gami da juya harshe zuwa buzanci. Ko me ta fadi oho, gaba daya suka kalli su Humaira, matasan suka gimtse dariyarsu sakamakon Mubarak dake zaune, sun tabbata muddin suka ce fiddo shi waje to fa kashinsu ya bushe wurinsa.  Hatta da Raihana ba ta ji dadin zancen Anna ba domin har ga Allah yanzu ba ta da matsala da su, ta riƙe su ƴan uwan na gaske kuwa.

Ita kuwa Jannat kallon Humaira ta ke yi kamar wacce ta ga kashi. A yatsine ta amsa gaisuwarta, Ummita kuwa gaisuwar ma ba ta samu ba sai harara da ta watsa mata ta ja tsaki.

"Wai Anti Jannat har yanzu wato kina nan yadda na sanki."

Mubarak ya fadi ransa duk ba dadi, tun daga kalmar agolar da Anna ta kira Humaira da shi har zuwa yanda Jannat ta karɓi gaisuwarsu.  Rai a ɓace ta amsa.

"Toh ko za ka sa hannu ka buge ni ne? Dama ai kai na faɗa can dai dangin uba ka biyo ba mu ba."

Zai yi magana da sauri Mami ta ɗaga mishi hannu, aikuwa abin da take gudu shi ya afku domin Anna faɗa ta hau yi kamar ta ari baki wai laifin na uwarsa ce da ta fifita bare a kan nata. Ganin dai abu ya ƙi ƙarewa Humaira ta miƙe tana mai jan hannun Ummita, itama ba shiri ta miƙe sun kama hanya tana ji Jannat ta kwalawa Ummita kira tana ba ta umarnin ta ja Hassan da Hussein ɗakin su Muhsin ta musu wanka. Ita dai Humaira a fusace ma ta karasa ɗakin don ta matsu ta daina jin muryar tsohuwarnan da ma Jannat din wacce ta ji tsanarta lokaci guda ya rufe ta. Me ake da wanda bai san daraja ta DAN ADAM ba?

Ita kadai a dakin ta yi ta mita tana tsaki. Ji take kamar ta je ta shaƙe wuyansu baki ɗaya. Sai kuma ta yi kwafa tana cije lebbanta, ita kadai ta san damuwar da take dannewa a ranta, amma a kwanakin nan abin yana neman fin karfin zuciyarta. Damuwar bai wuce Abba ba, mutumin da ya kasance bango majinginarta a gidan, wanda shi take yiwa kallon uwa kuma da uba. Wannan kauna da soyayyar da ya nuna mata a farkon zuwanta gidan yanzu ta rasa laifin da ta yi mishi ya sauya. Hira ma ya ƙi ba da fuskar ta ja shi da shi, idan har ita ɗaya ce a falonsa, nan da nan zai hau wasu ƴan aikace-aikacensa kamar gyara takardu ko kuma kiran abokan cinikayya, shaida dai ta cewar ba ya son ta ja wani dogon zancen. Ba dai za ta ce ba ya mata fara'a ba ne, sam a'a, sai dai babu ja a jiki balle har su shaƙu tamkar yanda ya nuna a farkon zuwanta. Toh wanda ma ka ke taƙama da shi bai wani damu da sha'aninka sosai ba ina kuma ga wasu can da har gobe sun ƙi karɓarta matsayin ƴar uwa ta jini? Kewa, kewar Dada da Kawunta duka suka mamaye ta, ba ta san cewar ta soma zubar da hawaye ba sai bayan ta sa hannu saman fuskar ta ji danshin lema. A hankali ta share su, ya kuma yi daidai da shigowar Raihana ɗakin. Ganin hawaye a fuskarta gaba daya sai ta ji ba dadi, ko ita ce ake yaren da ba ta ji tsarguwa yake sanya ta ballantana kuma wannan da dama din sun san ba da kowa ake ba sai su.

"Humaira kuka? Don Allah ki yi hakuri."

Ta fadi a sanyaye gami da zama a gefenta. Jin haka ta yi murmushin da ya fi kuka ciwo lokaci guda tana gwale idanun da hannu tana share su.

"Ke ba fa komai, ba kuka nake ba. To me aka yi da zan yi kukan?"

Raihana itama murmusawar ta yi ba don ta yarda ba, ta sani Humaira akwai juriya da nuna jarumta, sai dai kuma itama ai ƴar adam ce, tana da zuciya ta kuma san meke ma ta zafi. Kafaɗarta ta dafa.

"Na sani su Anna ba su ..."

"Raihana mu bar zancen, ya wuce wallahi. Ai komai mai ƙarewa ne. Lokaci ne." Cewar Humaira da sauri tana katse Raihana don a duniya yanzun idan da abin da ta tsana bai wuce a ambaci sunan Anna ba. Ta tsani mutum da ba ya ganin kowa da gashi. Tsohuwar sam ba ta riƙe girmanta.

"Kinga kuwa mutuminki koda wasa bai ƙara gangancin kirana ba?"

Maganar Raihana ya katse tunaninta. Cikin rashin fahimta ta ce.

"Wa fa?" Ta yi tambayar don har ga Allah ta mance, sai kuma bayan ta yi ta tuno da Musaddam din. Ta ɗan ɗaga gira.

"Au, ɗan iska za ki cemin."

Suka ɗan yi dariya. A haka su Tasleem suka shigo ɗakin suka iske su.  Zuwa yanzu Raihana ba ƙaramin haushi take ba su ba don haka daga kallo daya ba su kara bi ta kansu ba. Tasleem ta nufi sif din kayanta ta buɗe  ta sa hannu a ƙugu tana kallo.

"Oh God! Ni wane kaya ma zan saka? Wallahi gaba daya na diririce."

Futuha da ta faɗa saman gadonta ta yi dariya.

"Atoh, sai ki ƙure a daka ko ba komai dai wannan ne first meeting ɗinku."

Raihana na jin haka ta mike da sauri ta karasa ga Futuha.

"Wai Hamza D ne zai zo?"

Harararta suka yi a tare, Tasleem ta ja tsaki.

"Ina ruwanki? Ai ke yanzu munafuka kika zama. Ba a sirri da ke."

Humaira ta yi tsam ta mike ta fice a dakin ba ta ko kalle su ba. Cin fuska ne ta san za a yi mata.

***
Rayuwar ta ci gaba da gudana, Humaira tun tana ganin ire-iren bautar da Jannat ke sanya su na ƙare ne abin dai ya ci tura. Daidai da wankin pant da rigar mama su take ba, Mami ke tsawatarwa a wasu lokutan shiyasa kawai su ke hakuri. Idan kuwa ta kai Humaira abin ya ishe ta rantsuwa take yi da ƙari cewar ita ba za ta wanke ba, sai Ummita ke tausarta ta karɓa ta wanke gudun samun matsala.

A wannan gaɓar kuma ba irin takurawar da Fadeel ba ya yiwa Humaira, iyakar ƙularwa ya yi mata, ta yi bakaken maganganun amma ko gezau, kusan kullum sai ya aiko mata da saƙonninsa da ke yiwa Raihana dadi. Ita ke karɓa ta yi ta karantawa har a wasu lokutan ta yi yunkurin ba shi amsa, Humaira ta nuna ba ta so.

Jannat ba ta bar gidan ba sai da ta yi wata ɗaya cif. A sannan tuni Mubarak ya tattara ya koma, shima daf yake da kammala Masters. Yayinda  Yassar da Dawud suka soma jarrabawar ƙarshe na kammala degree dinsu a jami'a. Su Ummita ma tuni an koma karatu, Humaira kam ta yi nisa a fannin girke-girke don yanzu girki ɗaiɗaiku ne ba ta iya ba, kama daga cimar fulawa har dai sarrafa shinkafa da sauran kayayyakin abinci. Girkin gidan zuwa lokacin ya koma kan ta rankatakaf don kowa burinsa ta girka ya ci. Ita kam ko a jikinta, za ta yi girkin ba son jiki amma fa ba ta yarda da wulakancin su Yassar da Tasleem masu cewa su na son cin wani abu daban. 

Yassar su na dab da kammala jarrabawarsu ne suka tada hankalin Mami lallai sai ta tambayar musu Abba kuɗin da za su haɗa party da abokan karatunsu sai dai duk inda  suka ɓullo Mamin ta ƙi asalima cewa ta yi su tuntuɓi Abban da kansu.

Yassar ya mike tsaye yana huci.

"Shikenan, idan Abban ya zo zamu yi mishi maganar. Mu dai gaskiya wannan karon ya sakar mana mu fita kunyar abokai. Wannan rayuwa har ina."

"Ni ban san irin Abba ba wallahi, Mami ke ma ba kya mishi magana, tun farko ai Anna ta fadi, ke kika ba da damar ba ya hidimta mana sosai. Nifa Allah kuwa har kunyar nace Babana mai kudi ne nake, saboda ba a gani a jikina."

Dawud ya fadi yana daga tsaye dafe da kujera. Mami ta yi mishi daƙuwa.

"Karɓi nan Dawud, shi uban naku sa'anku ne da ku ka tsaya ku na wannan ɓarin zancen a kansa? Kuna maganar kamar yau idan kun je gabanshi za ku iya maimaitawa? Kunsan Allah ku kiyaye ni, gaba daya zan tattaraku na kai kararku wajensa tun da dai shi kuna shakkarsa."

Suka ƙara tunzura, Humaira na gefe tana gogewa Mami mayafi bayan ta kammala goge nata kayan dalilin wutar nepa da aka kawo, biki ne Mamin za su je har da ita na ɗiyar mijin Anti Laila malamar girkinta. Katin gayyatar har ita aka ba da ta kuma tabbata saboda mutuncin da suke yi da Shema'un ne, sannan Anti Lailar ma ba ta da matsala ko kaɗan.  Gaba ɗaya hirarsu babu wanda ba ya shiga kunnuwanta, tana mamakin irin wannan rashin tarbiyya na su Yassar da ba sa tauna zance kafin su furzar kan kowa ma. Haka suka yi ta mita a karshe dai kiran sallar la'asar ya sanya su tattarawa su bar falon.

"Allah ya shiryamin ku."

Humaira jin furucin da Mami tayi kafin ta wuce dakinta yasa ta amsa da amin, zuciyarta sai ta cika da tausayin Mamin. Matar dai na iyakar kokarinta a kansu. Ba zato ta ji an watso mata kaya saman kafafunta da ke miƙe a harɗe. Ta ɗaga kai ta dubi mai wannan aiki. Futuha ce tsaye daga ita sai vest da leggings. Gashinta a barbaje a gadon bayanta take duban Humairar fuska a yamutse.

"Ɗan dannemin kayan nan kafin su dauke wuta." Kallonta ba ta kara yi ba ta hadiye zafin da ta ji na wannan kalar rashin mutuncin na Futuha. Itama daga haka ta juya zuwa daki, ƙwafa ta yi ta kuma rantse ba za ta yi ba. Hakan yasa tana kammala na Mamin, ta hada da nata kayan da ta goge ta miƙe bayan ta ɗauke dutsen gugar a wajen gudun kar su Waleed su taɓa.
   Dakin Mamin ta soma shiga, sallah ta iske ta tana yi don haka ta ajiye mata a saman gadon kusa da wani haɗaɗɗen leshinta peach colour da ya sha adon duwatsu, ya hau sosai da mayafin. Humaira har sai da ta murmusa don tuni ta hango Mamin a ciki, karshen kyau ko ba a faɗa ba ta sani kalar da kuma kayan za su karɓe ta. Abar ka da farar mace.

Koda ta shiga ɗakinsu Tasleem na tsaye tana fente fuskarta da hoda. Ita kuwa Raihana tuni ta shirya tsaf cikin wata maroon atamfa mai haske an yi adon yellow colour jikinta sai dai bai yi dau ba. Tana tsaye ta karkace sai hotuna ta ke yi a gaban window. Futuha da alama tana bandaki. Suka dubi juna da Raihana, da wani irin zumudi ta karkace hadi da ɗan ɗaga gira.

"Ya? Na yi kyau?"

Humaira ta yi mata murmushinnan nata mai fiddo da zahirin kyawunta.

"Kin fito tsab. Masha Allah."

Raihana ta yi dariya, ita kuwa Tasleem dogon tsaki ta ja. Ba wanda ya ce mata ci kanki a cikinsu. Kasancewar ta yi wanka kafin zaman guga kuma ba ta da sallah hakan yasa ta kawai ta shiga sauya kaya. Itama atamfar ce amma nata dark brown ce mai haɗe da milk colour. Tana cikin shafa hoda Futuha ta fito daga wanka tana baza ƙamshin sabon showergel da suka ci arzikinsa a zuwan Antinsu Jannat gidan. Kallon Humaira ta yi kafin ta kalli gadonta ta gani wai ko ta ajiye mata kayan amma wayam. Don haka a fusace ta dube ta.

"Ina kayan da na ba ki guga?"

Humaira ta kalle ta da irin kallon wulakancin da suka saba yi mata itama.

"Ai gugan Mami kika iske ina yi ko?"

"Shekara kika yi kina gogewa Mamin mayafi? Don tsabar is..."

Ba ta kai ga ƙarashewa ba ɗif aka ɗauke wutar, aikuwa Raihana ta tuntsire da dariya itama Humaira sai da murmusa a ranta tana fadin Allah ya ƙara.

Nan fa Futuha ta hau zuba fada wai Humaira na sane iskanci ne ta fara sabo, tunda har ba a isa a sanya ta aiki ta yi ba. Ta tattara ta ba banza ajiyarta duk da cewa ranta wani irin tafarfasa ya ke yi na irin zagin da Futuha ke yi mata. Korar yunwa dai ya ƙi fita a bakinsu, ta kasa jurewa ta juyo, kamar ta maida martani da cewa su dinma asalin uwar Maminsu Nijar din ne, daga can suka fito can kauyen Agadas sai dai ta haɗiye tuna albarkacin Mami. Ummita ta shigo dakin, ita tuni dama ta shirya cikin atamfarta mai kyau ruwan sararin samaniya. Fitar da ta yi aiken Mamin ne zuwa siyan kati.

"Mami ta ce ku yi sauri."

Wannan ne ya katse zancen, kayan da Futuha ba ta sanya ba kenan sai kuwa wani ta sauya. Ba wata kwalliyar hayaniya Humairar ta yi ba amma iyakar kyau ta fito tsaf. Ba su suka yi haramar tafiya ba sai biyar da kusan rabi.

Koda suka fito baki daya, Ladidi kawai aka bari tana musu a dawo lafiya sai kuwa su Muhsin dake can ɓangaren Anna, Ummita ta dube ta da murmushi.

"Kin yi kyau sosai."

Ta riƙe haɓa.

"Idan babu wadannan buzayen a kusa ko?"

Suka yi dariya. Anan farfajiyar gidan suka sha hotuna a wayar Raihana dake faman jan su, su Tasleem na gefe su na kallonsu ita da Futuha, ko me suke tattaunawa?

Mami na fitowa suka shiga mota, kai tsaye ƙawataccen hall ɗin Marhaba suka nufa inda anan ne taron bikin.

"Ba ku mance katinanku ba dai ko? Ba na so a je wurin taro mutum ya yi tsaye kamar wanda ya zo gayyar soɗi."

Tasleem ta haɗiye dariyar muguntar da ya so kwace mata har sai da Futuha ta ɗan zungureta akan ta nutsu. Katin Humaira tun fitarta kiran Mami, ta ɗauke shi ta raba gida biyu ta wurga shi bayan gadonta.

Ummita da Raihana suka amsawa Mamin bayan sun duba sun ga katinansu, ita kuwa Humaira ko jakar ba ta buɗe ba tunda dai ta riga ta sani duk wani abun buƙatarta ta jefa a ciki.

"Humaira, Tasleem da Futuha fa?"

Suka amsa da eh su ma yana nan.

Su na isa bakin ƙofar kowaccensu ta fito, motoci ne na alfarma fake a wurin. Yanmata har ma da manyan mata ƴan gayu kawai kake gani a wurin, kasancewar Angon Shema'u ɗa ne ga kwamishinan ƴan sanda hakan yasa motar ƴan sandan har biyu a wurin su na lura da shige da fice.

Mami ce ta soma gaba suna gaisawa da wata ƴar uwar aminiyarta ta miƙa kati ta shige. Hakan ba karamin dadi ya yiwa Tasleem da Futuha ba sanin muguntar da suka shiryawa Humaira. Suka shige abinsu zuciyarsu fari kal bayan sun miƙa katinansu, Raihana ma tuni ta yi gaba. Ummita kuwa ganin yanda Humaira ta rikice da bincike jaka ya sa ta tsayawa gami da ja baya ta ba wasu hanya.

"Lafiya? Ya kika tsaya?"

Humaira ta ja guntun tsaki.

"Wallahi ban ga katina ba. Kinga ba ya cikin jakar."

Ta dafe kirji.

"Ba dai a gida kika bar shi ba?"

Ta girgiza kai cike da takaici, ta kasa cewa uffan ma. Ganin su na tsaye kawai ya sanya ta duban Ummita.

"Shiga ciki kawai, ni sai na koma gida."

Girgiza kai Ummita ta yi.

"Aa wallahi, sai dai ni na koma. Keda Shema'u da kanta ta damƙa maki kati?"

Nan fa suka yi ta ja in ja a ƙarshe dai Humaira ta ce.

"Toh naji, shiga ciki sai ki sanarwa Mami mu ji me za ta ce. Allah kuwa ba inda zan je ina nan zan jiraki."

Ummita duk sai ta ji ba dadi, sosai Humaira a daren jiya ta ci burin bikin ba don komai ba sai cewa da ta yi tana so ta ga ya ake gudanar da biki a ƙasarnan. Ba ta taɓa halarta ba. Ganin ta tsaya yasa Humaira dafa kafaɗarta.

"Rantsuwa fa nayi, kinsan ina nan din babu inda zan je."

Jin haka yasa ta gyada kai ta juya ta shige ciki ita kuwa ta ja baya ta koma can gefen titi jikin wata baƙar mota me tinted ta tsaya.

FADEEL....



©️RUFAIDA UMAR

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645


Fitowarsu kenan daga Bristol Palace dake kam titin farmcenter, Ibb ke jan motar yayinda shi kuwa ya kwantar da kai jikin kujera idanunsa lumshe. Babu abin da ya kai su face gaishe da abokin baban Ibb da ya zo daga Kaduna zai tashi zuwa Egypt sakamakon rashin lafiya.

"Hall dinnan ba ya rabo da biki."

Jin haka ya sa a hankali Fadeel ya buɗe idanunsa. Cikin iko da hukuncin Ubangiji, dubannasa ya sauka kan Humaira dake tsaye ta harɗe hannuwa a kirji fuskar nan a ɗaure kamar koyaushe.

"Wait please."

Yanda ya yi maganar da sauri ya sa Ibb shima soma tafiya a hankali gami da neman wurin parking. Sai da ya daidaita motar a gefe kafin ya dube shi da alamar tambaya.

"Lafiya?"

Fadeel ya soma kokarin cire seat belt.

"Ita ce. Ba na so na ƙara rasa damar da za ta kubcemin."

Ganin yana kokarin bude ƙofar yasa Ibb saurin dafe hannunsa. Fadeel ya dube shi.

"What? Kana nufin kar na je?"

Girgiza kai Ibb ya yi.

"No, ba haka nake nufi ba. Sai dai ina so ka ba ni damar muje tare, idan kuma da hali kar ka ce komai. Ma'ana kada ka yi mata zancen soyayya da ma sauransu. Ni zan san ta yadda zan ɓullo mata, ok?"

Fadeel ya sauke ajiyar zuciya yana hangenta ta jikin side mirrow. Ba tare da ya dauke idanunsa ba ya amsa.

"Ok."

Daga haka Ibb ya kashe motar, suka fito kusan lokaci guda. Gaba ɗayansu ƙananun kaya ne jikinsu. Fadeel baƙar tshirt ne a jikinsa mai ƙaramin hannu sai blue jeans.  A tsintsiyar hannunsa kuwa, agogo ne ɗaure na fata baƙi, sumar kansa baƙa wuluk sai sheƙi take yi. Ya fiddo gilashinsa baƙi a aljihu ya rufe ƙwayoyin idanunsa, a yanda ya karanci Humaira a farkon haɗuwarsu hatta da kallo ta tsana. Ba ya jin kuma abu ne da zai iya jure bari ne, wato kallonta, musamman ma da ya kasance sun fi watanni biyu ba su sake haɗuwa ba.

A ɓangaren Ibb kuwa, blue tshirt ya sa da baƙin wandon jeans. Kallo ɗaya idan ka yi musu sai ka kara. Fadeel fari ne tas kuma dogo, har ya so ya fi Ibb tsawo. Shi kuwa yana da ɗan duhun fuska balle idan ya jera da Fadeel, kai tsaye za a kirashi baƙi.

Tana nan tsaye ba ta motsa ba har suka ƙarasa wajenta. Wani irin bugu kirjin Fadeel ke yi, kallonta yake tun daga sama har ƙasa, ba ya jin ta haura shekaru sha takwas, idan ma ta cika hakan kenan, amma ƙirarta ko a yanzun abin a kalla ne ina kuma ga nan gaba? Ya ja numfashi daidai sadda suka ci burki a gabanta. Sallama Ibb ya yi gareta, ta bar duban wayar da take yi a kokarinta na kiran Mami ta ce mata ita kam gida za ta koma. Zaratan samarin suka sanya wani irin kwarjini ya mamayeta da har ta kasa tantance su ɗin ko su wane ne, ta mance ma a inda ta san su. Daƙyar ta amsa sakamakon nauyi da harshenta ya yi, daga haka kuma ta  dauke kai ta raba jikinta da motar da nufin barin wajen.

    "Kamar ba ki gane ni ba ko?"

Cike da ƙosawar ta tafi ta dube shi. Kallo na ƙurilla don ta fahimci ko dagaske yake ta san shi ɗin, duk da cewa ba wannan ne karon farko da samari suke mata irin rainin hankalin nan ba idan sun ga ba ta kula su ba, amma hakanan a ranta ta ji wannan dai ya yi kama da kamilallan mutum, ba ta jin zai yi mata ƙarya. Bayan gama kallonsa ta maida kwayar idanunta kan Fadeel, ba ta ci nasarar ganin halittar kwayoyin idanunsa ba, shi kuwa wani yarr ya ji tun daga tafin ƙafarsa har tsakar kansa. Dakyar ya iya jarumtar juya fuskarsa gefe kafin ita ɗin ta kai ga ɗauke nata kwayar idanun a kansa. Ta tsuke baki ta ce.

"Ban gane ku ba."

Ibb ya yi mata

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment